gidan
ba tare da ta nemi izinin ta wajen fitar ba.
"Ina ki ka je Nana?" Ba tare da da ta kalleta
ba ta ce mata gidan su Nura.
"Gidansu Nura?" Hajiya Salma ta tambaye ta
cikin hanzari da kuma zare ido saboda mamakin
amsar da ta ba ta, Nana ta juya za ta nufi dakinta,
Hajiya Salma ta sake daka mata tsawa ta kirata, ta
nufi dakinta, itama ta bi bayanta zuwa dakin nan
ta da duruksa a Kasa, Nana ni ki ke baiwa amsa
kan ki tsaye ba ki damu da ko raina zai baci ba."
Nana ta soma kuka, kuka mai tsanani tsawon
lokaci Hajiya Salma tana kallonta cikin mamakin
dalilin kukan nata, sai da ta yi ya isheta ta yi shiru
62
Da kamar wuya.... Hufsut C. Sodangi
ta mike za ta fita sai ta ce mata "A'a ai babu inda
za ki sai kin gaya min abinda na yi miki da ya saki
wannan kuka da ki ka yi wanda da ganinshi an san
bakin ciki ne ya sa kika yi shi."
Shiru Nana ta yi ba ta tamka mata ba, tsawon
lokaci tuni ta na mata fada har ta koma rarrashinta
Nana ta bude baki a hankali ta ce mata babu
komai Innarmu kawai na tuna, tana fadin hakan
wasu hawayen suka sake zubo mata ta ci gaba da
wani sabon kukan, jikin Hajiya Salma ya yi
matukar yin sanyi ta kalli 'yar kanwar tata ta ce
mata "Nana menene damuwarki? Wannan kukan
da ki ka yi da alamar akwai 6acin rai mai tsannai
a dade ina bata miki rai ba ki gaya min ba. In
kuma ki ka yi min haka ba ki min adalci ba don
kuwa a zaman da na yi dake na jawoki a jikina ta
yanda za ki maidani tamkar mahaifiya ki saki
jikinki dani ki sani cewar baki da wata wacce ta fi
ni tunda mun riga mun rasa mahaifiyarmu ni din
mamadinta nake a wurinki don kuwa danma
Hausawa suna cewa wai babban ya uwa ce, wato
ba ki daukeni a haka ba."
Nana nta kara sunkuyar da kanta kasa cikin
rawar murya, ta ce mata "Haka ki ke a wurina
Anti." 63
Da kamar waya.... Hafsat C. Sodangh
Hajiya Salma ta gyara zama ta ce "Ko haka
nake Nana akwai wani abinda na gane ba k gamsu
da adalcina a kanshi ba don haka ina so ki gaya
min shi in gyara." Ai tsawon zamana dake ban
taba ganin kin yi kuka na tambaycki dalilin kukan
ki ka ce min Inna ki ka tima na sai yau, na kuntata
miki da yawa, a d'an tsakanin nan ko?"
DA sauri Nana ta ce "A'a ba ki taba kuntata
min ba ni dai kawai..." Ta sunkuyar da kanta kasa
ta yi shiru.
"Yi magana mana ki gaya min abinda ke
ranki."
Hajiya Salma ta bata umarni. Nana nta ci gaba
da yin shiru. "To kina dai so kenan sai raina ya
baci ina ganin dama bukatarki kenan, ta ce "A'a to
in ba haka ba ne gaya min." A hankali cikin
sanyin murya ta ce mata ni dai kawai Anti da na
so ne ki yi min nima irin yanda Innar mu ta yi
miki.
Hajiya Salma ta zuba mata ido tana kallonta
jimawa kadan ta ce mata "To Nana tunda abinda
ki ke so kenan in kyaleki ki auri Nura ko?"
Nana ta sunkuyar da kanta kasa, ta yi shiru
"To ai kin gani in na yi magana sai ki yi sauri ko
kuwa akwai wani wanda ki ke sone bayan Nuran?
64
Da kanar waya.... Hafsat C. Sodangi
Cikin sauri ta ce mata a'a Hajiya Salma ta ce to in
dai maganar Nura ce, zan iya barinki ki aurcshi
Nana tunda abinda da ki ke so in yi kenan, to
amma fa ki sani Inna ta goyi bayana ne na auri
mutumin da bai da wata matsala in ba ta abin
hannu ba, ke kuwa kin fini sanin irin mutumin da
ki ke son aura. Kina ganin nan gaba in kin yi
hankali ba za ki zargeni kan barinki da na yi ki ka
yi hakan ba? Nana ta če "A'a ba zan taba zargin ki
ba, sai dai kullum in kara daukanki a matsayin
mai tausayi da kyautatawa ga komai karamai gana
kasa da ke don kuwa na yi imani kina tsaye wajen
ganin na samu alheri in har wani abu sabanin haka
ya faru dani to ba zan taba zarginki ba don kuwa
na san in na yi miki haka ban yi miki adalci ba,
tsawon zamana dake alherinki na sani ban tabа
ganin wani abu sabanin hakan ba, don kullum
abin da ki ke nufi dani kenan in kuwa na ga wani
abu saba wa haka to ba daga gareki ba ne, Hajiya
Salma ta kalleta yayin da ta ke jero mata dadadan
kalamai da take ganin zasu kara sanyaya mata
zuciya game da al'amarinta, ta ce "To ai shi kenan
Nana ni madadin Inna ce a wurinki ina kuma fata
in ci gaba da zame miki hakan a kowane lokaci
ban ki Nura don komai ba sai don ganin rashin
65
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
dacewarshi dake don kawa kin cancanci samun
kowane irin miji d azai kula dake ba wanda zai
zamo ke ce mai zuwa kina kula da shi ko
dawainiya da shi ba, amma tunda ba ki fahimce ni
ba har kina ganin tamkar rashin mahaifiya ne ya
saki rasa abinda ki ke so, to na daina daga yau zan
sakar miki marra zan tayaki son abinda ki ke so
zan kuma yiwa Alhaji bayanin yanda muka yi
dake don ya sani. Na kuma san shi al'amarinshi
mai sauki ne kwarai in dai a kanki ne ko da ya sa
rana ki k ace ba kya son wanda zai ba ki zai iya
fasawa, balle bai riga ya furta ba, don haka daga
yau kar ki sake damun kanki har ki shiga cikin
damuwa don kuwa ni da shi dukanmu masu
tausayin ki ne ba masu nufin kuntata miki ba, don
haka ki saki ranki ina miki addu'a tare da
kyakkyawan fata na wannan zabi naki ya zamo
miki alheri."
Nana ta sunkuyar da kai kasa cikin hawaye
saboda farin cikin da ya kamata babu abinda ya fi
tsaya mata a rai irin tausayin Antin nata da ta
rinka zarginta cikin ranta cewar tana kin Nura ne
don kawai ta ga shi ba mai wani abu bane ga shi
kuma gurgu, ita kuma tana sha'awar ta auri mai
abin duniya, a yanzu ta gane abinda duk Antinta
66
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
take yi tana yi ne don amfaninta ita kanta ba don
bin son zuciyarta ba.
Tun daga wannan lokaci da ta yi mata wannan
bayani sai ta sakarwa Nana mara kan takura mata
da take yi da kuma yawan yi mata magana kan
samarin dake zuwa wurin ta,.tana kin fita a yanzu
tana ji tana gani za a yi sallama da Nana ta ce ba
za ta ba, ba za ta daga ido ta kalleta ba, balle ta
tambayi dalili, sai dai ma da ta ga kwana da
kwanaki tun maganar da suka yi da ita ba ta ji an
ce Nuran ya zo ba, shi ne ta ce mata "To wai ke
yaya ne? In an zo an yi sallama dda ke ki ce ba za
ki ba, shi kuma wanda ki ke so din ban ga yana
zuwa ba, ko kuwa ya yi fushi ne ya ce tunda dama
Antinki ta koreshi to shi kenan ya hakura."
Nana ta yi murmushi ta ce "To menene in ya
yi hakan? Da sauri Hajiya Salma ta ce "A'a ai sai
in tura mishi jama'a su je su ba shi hakuri."
Nana ta kyakyale da dariya ta ce "Tafdijan."
***
Nura yana zaune kan keken guragunshi kan
hanyar da ya ke daidaita yana zama don ya rinka
ganin Nana suna gaisawa, sai rarraba ido ya ke yi
yana tunanin wai ko da ya ga ta biyo ta wata
'hanya cikin hanyoyin da yake zaunc a tsakiyarsu,
67
Da kamur wuya.... Hafsat C. Sodangi
cikin zuciyarshi kuwa lissafin rabonshi da ganinta
yake'yi, to ko lafiya? Wannan ita ce tambayar da
ya kasa amsawa, kanshi gaba daya ta dauke kafa
ta daina biyowa ta wannan hanyar hatta yaran
gidan su da yake gani yake samu yana tambayarsu
lafiyarta suma ya dana ganin su to ko dai bata da
lafiya ne? Ko kuwa Antinta ta dauki wani
tsattsauran mataki a kanta? Ya tuna rabonshi da
ganinta tun daga lokacin da ta je gidansu ne
Umma Talatu ta bata fura gaban shi ya yanke ya
fadi, daya tuna irin kashedi mai tsanani da Antinta
ta tura aka yi mishi, to ko dai ranar ta gane ta je
wurinshi ne ta dauki wani mataki mai tsanani a
kanta? In kuwa haka ne ya zama dole ya nemi
labarinta koma ya je har gidan don neman sanin
halin da take ciki. Bai damu ba in ya so in Antin
ta ji labari ta cika alkawarin da ta yi na Karasa
mishi 'yan kafafuwan nashi, inma da wani tanadi
da ta yi mishi wanda ya wuce haka duk ta aiwatar
a kanshi in dai bayan ya san halin da Nana take
ciki ne, to ya yarda don kuwa ya fiye msihi sauki
akan ya yi ta zama ba tare da ya ji wani labari
game da ita ba na dalilin da ya sa da baya ganinta.
Ci gaba da zama a wurin ya yi har lokacin
tasowarta a makaranta ta yi bai ga ta zo ta wuce
68
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
ba, a hankali cikin sanyin jiki ya tura kckenshi
wasu yara da ya riga ya yi sabo da su a wurin suna
tayashi suna kuma yi mishi hira har suka isa kofar
gidan su Nana, suna tsaye a wurin suna tunanin
yanda zasu fitowa lamarin shi da yaran don kuwa
wancan korar da aka yi mishi ma yana tare da
yaran aka koreshi mu koma ne daga can
lungunmu koma ne daga can lungu mu boyeka sai
mu dawo mu m shiga gidan mu tambaya ina ta
ke? In san gaya mana shi kenan sai mu zo mu
gaya maka in kuwa sun ganemu sun biyomu sai
kawai mu fito da gudu ma zo mu turaka da gudu
mu fice musu daga cikin layinsu in kuma muka
riga muka bar layinsu ai shi kenan me suka isa su
mana ai kaima kana da sojojin ka Nura ya kalli
yaran cikin murmushi ya ce "Ina sojojin nawa
suke?"
Da sauri suka ce mishi gamu in sauranmu
suka ji labari, suka fito ai ba zasu iya damu ba."
Nura ya yi murmushi ya ce "Ai ba zan so ace
mun yi hakan da su ba, yanzu dai kawai kai
Babawo kai ka tsaya daga zaure kai Bala sai ka yi
sallama ka shiga ciki ka tambaya, Nana tana
nan?"
Bala ya ce "A'a ni ba sai ya bini ba zan je ni
69
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangı
kadai, Babawo a wurinka in kun ga na fito da
gudu sai ya turaka da gudu kawai ku bar wurin."
Suna cikin haka sai ga Nana ta bullo ta wata
sabuwar hanya da ta koma bi cikin wani lungu da
sauri Babawo ya ce "Yauwa ga ta can ma." Tun
kafin ya gama rufe bakinshi ya ji umarnin da za a
bashi ya ruga da gudu ya karasa gareta cikin haki
ya ke mata magana, ta juyo a hankali ta kalleshi
ya nuna mata Nura zaune cikin keken guragunshi,
ta ja ta tsaya ta ce "To gaya mishi ya zo nan mana
gani ina tsaye."
Babawo ya kalleta ya ce "An fa ce in muka
kara takowa kofar gidan nan komai ya samemu
mu muka ja."
Та се "Ва ga abin da na ce ba? Ba zani can
inda ku ka tsaya ba ku karaso nan." Ya juya da
gudu ya koma, suka karaso tare.
Nana ta zuba ido tana kallon yanda yaran ke
turoshi kan keken cikin raha da farin ciki, kome
yake gaya musu oho? Sai kyalkyalewa da dariya
suke yi, a dan zaman da Nura ya yi a wurin gaba
daya yaran unguwar ya sayesu, a yanzu yana
fitowa wurin za su zo su kewayeshi su zauna su yi
ta hira, maimakon da dashi kadai Nana take
wucewa suka iso wurinta yaran suka saki kcken
70
Da kamar wuya.... lafsat C. Sodangi nashi suka koma gefe suna hidimarsu suka ba su baya ya zubawa ido yana kallonta cikin nutsuwa don tabbatar da yanayin ta.
"In ce ko dai lafiyarki kalau Nana? Nana da kwanaki ban ganki ba hankalina ya tashi na ce ko ba ki da lafiya ne, ko kuma wani abin ne ya faru a
cikin gidan da ya hanaki fitowa?"
Ta ce "A'a daina biyowa ta can kawai na yi."
Ya dan turo keken nashi ya matso kusa da ita "Haba Nana me ya sa ki ka mun haka kin yi min rowar wadannan kyakkyawan idanuwan naki
masu kama da an diga musu ruwan zaiba, kin
kuwa sani sarai in ban gansu ba hankalina baya kwanciya."
Ta ce "Yanzu ba ka gansu ba?"
Ya ce "E amma ai sai da na zo nan kin ga kuma karya dokar da aka sanya mun na yi wanda
bai dace ba kullum mutum ya kan yi kokarin bin
umarnin na gaba da shi ne don ya samu ko zai yi dace ya gama lafiya."
Ta се "Haka ne to yanzu ni zan shiga gida ya
yi maza ya ce "To Nana sai yaushe? Sai yaushe
zan sake ganinki."
Ta ce "Duk lokacin da ka ke son gattirna kana
iya zuwa kofar gidanmu kamar yanda yanzu ka zo
71
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
ta wuce ta shiga ta barshi anan yana bin ta da
kallo, da sauri su Babawo suka iso suna
tambayarshi ya ya dai Mai nasara ta bata maka
ne? A koya mata darasi? Nura ya dora hannu a
baki cikin nuna girman maganar da suka yin yа се
"Har da ita sai ku iya bata mata a kaina? Da
saurinsu suka ce to in ta bata maka mu meye
gaminmu da ita da ba zamu rama wa maigidanmu
ba?"
Nura ya ce "To ai ita wannan da ku ke gani
zamanta nake yi akan kujerar nan in ban da
saboda da ita da ba kuma ganni anan ba don haka
a tayani girmamata."
Gaba daya suka hada baki suka ce "Yanda ka
ce haka za a yi." Suka kama hannun keken suka
shiga turawa, suka maidashi gida har yamma Nura
yana tunanin abinda Nana ta yi mishi na tafiya da
ta yi ta barshi ba tare da ta tsaya ta saurareshi ba,
ya yi kamar ya danne ya hakura sai kuma ya ji ba
zai iya ba ai zamanta yake yi a garin in ba ta
harkarshi ta daina sonshi to ya canza wurin mana
don haka nan take ya yanke shawarar komawa
gidan nasu tunda ta ce duk lokacin da yake son
ganinta ya je can in ma gatse take yi to shi kam a
kanta bai san gatse ba, bari ya je ya gani.
72
Du kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
Lunguna ya bi a hankali yana tura kekenshi
don kar yaran unguwar su ganshi su bashi shi
kaďai yake son tafiya, yana isa kofar gidan ya ga
Rahma tana fitowa daga ciki da gudu ta karaso
wajenshi cikin murna ya ya Nura ina ka je?"
"Ban je ko ina ba Rahma." Yana bata amsar
yana kokarin debo mata cakulet daga aljihun
keken nashi ya miko mata hannayenshi biyu a
cike, tana murna ta karba da gudu kuma ta koma
cikin gida don ta shaida wa Nana isowarshi
jimawa kadan sai gata ta fito wai ka shigo Nura
ya zuba mata ido cikin shakku in shigo Rahma?
Ya yi murmushi koma dai ki sake jiwowa da
kyau, kafin Rahma ta amsa umarnin da ya bata sai
gashi an leko an ce mishi wai ka shigo daga nan."
Ya yi kamar yanda aka gaya mishi yana shiga
dakin wanda dama don baki aka tanadeshi Rahma
ta bi bayanshi tana mishi hira, Nana ta shigo
dakin dauke da kayan ciye-ciye iri-iri ta ajiye
mishi yanda zai rinka jin dadin cі.
Nana ta koma kan wata kujera ta zauna ya
zuba mata ido cikin mamaki "Nana ya ya aka yi
wannan abin mamakin ya auku?"
Ta yi murmushi ta ce "Ikon Allah kenan." Ta
ja bakinta ta yi shiru ya ce "To in kin amince da
73
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
wannan nasarar da muka samu Nana to in je in
gayawa Ummana mana don a shirya turo
magabata na?"
Ta ce "In ka yi hakan ma daidai ne."
Ya ce mana "Nana ni kuwa me zan ce miki a
rayuwa? Kin soni so na hakika kin soni duk da
lalurar da nake tare da ita, ni kuwa in Allah ya
yarda zan nuna miki halaccina."
***
Cikin sati biyu kawai sai magana ta yi karfi
tsakanin Nura da Nana har mijin Umma Talatu da
aminanshi sun zo wurin Alhaji Sani kan maganar
ta su, ya kuma amince ya sanya musu rana inda ya
gargadesu da bai son komai na hidimar al'ada da a
ka san ana yi in banda sadaki shima ya yankeshi a
matsayin Naira dubu biyar, kayan aure ma ya ce a
barshi, in ta je dakinta a yi mata ya yi wannan
karancine bisa dalilin sanin da ya yi mijin Umma
Talatu, Malam Mudi ba wani abu ne da shi ba,
don haka ya ga tunda ita Nana ita ta zabi dansu a
haka to ya kamata komai a yi musu shi bisa
adalci.
Shi kuwa Nura bai yiwuwa a tsaya kwatanta
farin cikinshi a yanzu kusan ko wane lokaci yana
gidansu Nana suna hira shi da Hajiya Salma kuwa
74
Da kamar wuya.....Hafsat C. Sodang!
sun yi matukar sabawa ta maidashi tamkar kaninta duk lokacin da ya tura keken guragunshi ya shiga cikin gidan don gaisheta in ya juya ya fita sai ta bi shi da kallo cikin zuciyarta tana fadin iko sai Allah mutum har mutum komai nashi gwanin kyau an yi mishi Tubarkallah sai dai kuma
babu kafa, ko haka aka haifeshi ko kuwa da girmanshi lalurar ta sameshi, oho. Daga dukkan kallon da take mishi dai ta kasa gano ta inda ya yi mata alama da gurguntaka a jikin nashi haka nan in banda Malam Mudi da Umma Talatu ne suka
tsaya suke gabatar da komai na hidimar auren nashi to da bata yarda da cewar su din yana da gami da su ba don kuwa ba ta ga ta inda ya dauko
su ba.
Kwanaki suna ta matsowa shirye-shirye sun yi karfi sosai kusan duk wani abinda ake bukata
na shirin auren ya kammala babu abinda Alhaji
Sani da Hajiya Salma ba su tanadar mata ba sun
iyakar yinsu don su nuna mata irin gatan da take
dashi, don ma suna yi suna tunanin irin gidan da
zata zauna a cikin komai-da Nana kc bukata na
shirin baki Antinta ta bata don kar ta je tana
neman wani abu a wurin angon ba tunda an san
baidashi daga shi har iyayen nashi.
75
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
Nura yana zaune kan keken guragunshi a
dakin da ya saba sauka a yanzu gidan su Nana
abincin "da Hajiya Salma ta aiko a kawo mishi ya
ke ci yana kuma sauraron shigowar Nana, jimawa
can ta shiga cikin kwalliya sosai, sannan da zuwa
.ya daga ido ya kalleta cikin murmushí ni in ce ko
har kin soma cin kwalliyar bikin ne? Ta tayashi
murmushin ta ce "Da aka yi me?"
Ya ce "To gani na yi Nana sai wani kara
kyalli ki ke yi kina kara washewa, gashi kullum
na ganki cikin wata sabuwar kwalliyar zan gan
ki."
Nana ta yi murmushi ta sunkuyar da kanta
kasa cikin nuna alamar jin kunya."
Sun dan zauna shiru saboda kunyar shi da
take ji sai ya kawar da zancen da cewa "To ni
Nana kullum ina tambayarki shirye-shiryenki na
biki don in ga abinda zan iya tanadar miki amma
kin ki yin magana, ko kuwa ba za ki yi komai ba
ne?"
Ta ce "Walima kawai zan yi."
Ya ce "Ai dama ita ce muhimmiya sauran
duka ai kwaikwayon dabi'un turawa ne, wanda bai
da wani amfani."
Та се "Нaka ne."
76
1
1
a
Da kamar wuya... Hafsat C. Sodangi
Ya ce "To amiha ita ma walimar ai da
gindinta take zaune don haka nake so in san
abinda zan samar miki na yin walimar ko?"
Ta girgiza kai nuna alamar "A'a." Ta ce "Anti
ta riga ta gama komai ta kuma yi min kashedin
kar in ce zan dora maka wani nauyi don haka
bana bukatar komai."
Ya ce "To Allah ya sakawa Anti da alheri
Nana."
Nana ta ce "Amin."
東車車
Ranar daurin auren ta kasance ta Asabar cc
saboda aminan Alhaji Sani da ya gayyata yakc
kuma sa ran zuwansu.
Tun kwana uku kafin ranar kuwa gida ya cika
makil da jama'a 'yan uwa da abokan arziki na
nesa da na kusa sun hallara, ranar daurin auren da
misalin karfe goma sha biyu daidai aka daura
auren wanda ya samu halartar mutane, dabandaban na nesa dana kusa wadanda aka yi zato
dama wadanda ba a yi ba da daddare aka kai
amarya dakinta a gidan Umma Talatu wanda ko
kayan jeren bai dauka ba saboda kankantarshi sai
katifa kawai aka jefar musu a kasa aka dai
kawatashi da labulaye sai ko kafct.
LL
Da kamar wuya... Hafsat C. Sodangi
Umma Talatu ta yi hidimar biki fiye da duk
yanda aka zata abinci dana sha babu kama hannun
yaro, duk nau'in da ka ke so akwai tun daga na
gargajiya dana zamani. Hidima dai gwanin
sha'awa sai kwalliyarta take yi ta shiga wannan ta
fita ta shiga wancan, kuma masu tsadar gaskc
kowa sai kallonta yake yi yana mamakin
al'amarinta ita da mijinta.
Ranar budar kai tun da yamma Umma Talatu
ta sallami kawaye ta shaida musu cewar kowacce
ta nufi gidansu tunda an yi biki an gama ta kuma
basu abinda suka nema na sallama babu maganar
jiran sayen baki, don angon ba mai irin wannan
hidimar bane tun da ma shi ba wasu abokai ne
dashi ba, da zasu rakoshi.
Sukan kawaye tun da an basu abinda suka
nema ko a jikinsu, suka yi sallama suka tafi suna
murna cikin zuciyarsu suna cewa iko sai Allah
Nana nta auri dan gurgu amma hidimar bikinta
komai tubarkallah.
Gaba daya 'yan biki sun watse an bar Umma
Talatu daga ita sai amarya wacce ke zaune a
dakinta cikin shirin taryen angonta.
Idar da sallar isha't kawai ta yi ko gama jan
carbinta ba ta yi ba ta ji sallamarshi a bakin kofar
78
dakinta.
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
Sai da ta shafa Fatiha sannan ta amsa sallamar, ta shiga kokarin yin kaye-kayen abinda take ganin yana bukatar kawarwa don ta samar
mishi inda zai ajiye keken shi na guragu, ya sake yin sallama ta amsa tare da ba shi izinin shigowa,
ya tura kai ya shiga cikin dakin. Nana dake tsaye
a gefe tana jiran shigowar shi don ta taimaka mishi fitowa daga cikin kenan nashi ta ja baya
cikin sauri saboda razana da ta yi a dalilin ganin
angon nata tsaye kyam akan kafafunshi.
Nura ya sakar mata wani lallausan murmushi
ya ce Nana amaryar gurgu.
Mu hadu a littafi na biyu don jin ci gaban
labarin.
Taku
Hajiya Hafsat C. Sodangi.
79
Da kumar wuya.... Hafsut C. Sodangi
80
AKARA CITY
OKSHOP
08027014161
Tsarin Bango:
ANKA- GRAPHICS FAGGE
07030319787
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels