mara fara'a haka nan bai cika sakin fuska ga na kasa da shi ba, ke ni wani lokaci ma ban cika son ganinshi a
gidanmu ba, saboda zuwan na shi ya kan takura ni.
"Ina ajin karshe na secondary school shi kuma ya tafi bautar kasa lokacin nan kuwa na
zama budurwa, tafiyarshi babu dadewa muka zana jarrabawar fita daga secondary school na kuma yi sa'a sakamako ya yi kyau har ina cikin murnar zan
23
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sødangi
samu wucewa jami'a don karo ilimi na. Kwatsam
ranar wata Juma'a ba zan taba mantawa ba
Babana ya shigo gida cikin fara'a yana kwalawa
Innata kira, Ramatu! Ramatu!! kina ina ne? Inna
ta fito da dankwalinta rike a hannu tana kokarin
daurawa sannu da zuwa Malam, har ka dawo ko
kuma ba ka je kasuwar ba ne? Baba ya yi
murmushi ai ban sami zuwa kasuwa ba, gidan
yaya na je muka yi hirarmu saboda dama kin san
aikenshi biyu yana nemana kin ji wai dama aiken
saboda yaran nan ne wai yana so zai hada Umaru
da Zuwaira, na ce ko in ban da yaya wannan ai ba
sai an yi sharawa da ni ba, Inna ta ce haka ne
Allah dai ya tabbatar mana da alheri ni kam ina
dakina hankalina ya kai matuka wajen tashi ji
nake kamar in tsoma baki cikin maganar ta su, in
shaida musu cewar bana sonshi sanin halin Baba
da na yi ya sanya na ja bakina na yi shiru na
hakura na koma bakin gadona, na zauna ina
sauraron irin bugawar da kaina ya ke yi a dalilin
kalaman da na ji mahaifina yana fada, ban san
sanda hrawaye suka soma zubowa daga idanuna
ba.
Umma ta shigo ta sameni cikin wannan hali ta
tsaya tana tambayata menene ya sameki? Na cc
24
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
mata babu komai Umma: Ta tsaya tana kallona, babu komai kamar ya ya? Kina kuka kina fadin babu komai, na cc ba kuka ba ne wani abu ne ya fada min a idona, ta ce to madalla ta juya ta fita,
ta barni ina share hawayena. Abu biyu ya fi kona
min rai gashi dai za a haďani da mutumin da ba na
so ga shi kuma karatuna zai katse.
"Kin san na fada miki halin danginmu
musamman irin matsayin da baban Umar ya ke
dashi a cikin dangi don haka maganar ma in ce
ban yarda ba ko in nuna bijirewata bai taso ba,
zan bata goma ne kawai daya bata gyaru ba, don
na san babu mai goyon baya na sai dai kawai in
tada hankalin iyayena, ran nan kwana na yi idona
biyu saboda tsananin tunani, da asubar fari na fito
na yi alwala na koma dakina na yi sallah na koma
kan gadona na kwanta a raina ina fatan Allah ya kawo wani dalili da zai sa a fasa wannan auren.
Gari ya gama wayewa na fito na gama 'yan ayyukana dana saba na koma dakina na kwanta ba
tare da na saurari wani abin karyawa ba, sai wajen
azahar na fito na yi alwala na yi sallah nja je na yi
wanka na shirya na roki Umma ta barni na je gidan wani aminiyata Nadiya. Umma ta kalleni ta
cc dama kin nutsu kin san abin da duk za ki yi ba
25
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
za ki wuce abinda aka shiryo miki ba.
"Ban yi magana ba na juya na koma dakina
na zauna zuciyata kuwa sai sakc-sake ta ke yi kan
abinda ya kamata in yi, kwana biyu bayan nan
Umar ya zo gidanmu sai da ya gama duk abinda
zai yi sannan ya shigo wurina ya zauna muka
gaisa a yanayin da muka saba kullun bai sakc ce
mun komai ba ya tashi ya yi tafiyarshi, hakan da
ya yi mun ya kara sani na tsaneshi, na jí babu abin
da nake so irin in sameshi in gaggaya mishi
maganganu marasa dadi, ko zan ji sanyi cikin
zuciyata.
Dare na yi na kira layinshi a wayata bayan na
boye lambata yana dauka na ce mishi ya ya Umar
ni ce. Ya ce na ganeki menene? Na ce bugowa na
yi in rokeka ka yi min wata alfarma, ya ce kamar
wacce iri kenan? Ban 6oye mishi ba na gaya
mishi gaskiya ni ina da wanda nake so, nan take
ya katse layin bai sake sauraron maganar ba ban
kuma san yanda aka yi ba sai dai kawai na ji
maganar ta watsu a cikin dangin, dangi sai dai
kuma hakan bai hana yin aurenmu ba an yi
shagalin biki ni da Umar aka kuma kawoni
gidanshi, sai dai kuma ina tabbatar miki tun daga
ranar da aka kawoni gidan har yau din nan bai
26
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi taba daga ido ya kalleni da wata manufaba ballc wata mu'amala ta hadamu tun ban damu da hakan
ba har na shiga damuwa, har na zo a yau na hakura ke dai bar shi duk abinda na ce ina so zai
yi min dana bukaci shiga makarannta ya samar
min haka nan hidimomina kullum bai gajiya dasu
amma iyaka kenan."
Nana ta zuba mata ido cikin nutsuwa ta ce
"Ke Zuwairiyya to duk wannan kyallin da ki ke yi
na mene ne?"
Ta yi murmushi ta ce "Nana kenan kyallin
hakurino da muguwar kaddara."
Nana sake yin wata ajiyar zuciya mai karfi
ta ce "Amma ai gara ki je gida ki sanar da
iyayenku, don su san halin zaman da ku ke ciki."
Тa сe "To akan me zan yi hakan? Mu dai yi ta
zaman a haka har mu ga iya inda abin zai tsaya."
***
Kan hanyar Nana ta dawowa gida ta sake
ganinshi zaune kan keken nashi na guragu, tun
daga nesa ta hangi kyakkyawar fuskarshi mai cike
da fara'a da walwalar da ta zamo ta halittace,
Allah da iko yake wannan kyakkyawan saurayi
kome me sanadin gurguntakarshi oho? Kusan
kullum anan wurin take ganin shi tun daga ranar
27
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
da ta soma ganin shi kuwa zuwa yau din nan babu
wata rana da ta biyo ta nan bata sameshi zaune
anan wurin ba sai dai kuma ba ta ga kamar bara
yake yi ba, don ba ta ga alamar hakan a tare da shi
ba.
Nana ta iso wurin cikin yanayinta na nutsuwa
da kamun kai, "Malama barka da dawowa." Ba
tare da ta yi zaton jin gaisuwar ba ta amsa tare da
waiwaye kadan don ganin mai gaisuwar,
idanuwansu suka hadu yayin da ta yi maza ta
kawar da kanta ta ci gaba da tafiya, cikin
zuciyarta kuwa tunani take yi, rayuwa da wuya
take shi kuma wannan ko me ye sanadin wannan
gurguntaka na shi? Tun da ita dai bata ga alamar
Kafafuwan nashi a shanye suke ba, yau da gobe
kullum ta zo wucewa zasu gaisa dashi tun yana
fadin Malama barka da dawowa, har suka zamo
rige-rigen gaida juna suke yi a hankali kuma
shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, ta yanda
ko Nana ba za ta makaranta ba zata san abinda ya
biyo da ita ta zo ta nan layin suka gaisa ta koma
gida. Daga baya har ta zama ko wani abu aka yi a
gida ta ji dandanonshi ya yi mata dadi, za ta ce
wa yayarta Hajiya Salama a zuba mata a kwano ta
je ta kai mishi, tun tana zubawa ba tare da nuna
28
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
son sanin wanda ake kai wa ba har dai ran nan ta
bukaci sani, Nana ta yi mata iyakacin bayanin da
za ta yi mata sai dai ba ta ganc mutumin da akc
gaya mmatan ba, ni fa ban san wani gurgu anan
wurin ba, watakila dai daidaitar lokacin zuwanki
yake yi ya fito."
Fadın hakan da Hajiya Salma ta yi ya sa Nana
ta sa ido kan mutumin da suke gaisawar kullum
wanda ko sunanshi ba ta sani ba, sa idon da ta yi
kuwa ya sa ta gane gaskiyar 'yar uwartata, ba
kowane lokaci ake samunshi ba zaune a wurin ba.
Sai dai kuma ai bai yiwuwa ace mutum ko wane
lokaci yana zaune a wuri daya baya motsawa dole
yana da wasu al'amura da zai yi na hidimomin
rayuwa, ita kam ba kamar yayar ta ba da take
cewa mata kila ita kadai ke ganinshi ko kuma don
ita yake fitowa ya zo nan wurin ya zauna.
Sabo ne mai karfi ya shiga tsakaninsu tuni har
zuciyarta ta soma raya mata in da zai daure ya
bude baki ya ce yana sonta ita kam da shi ta aura,
don ya fiye mata duk samarin nata da take dasu
kwanciya cikin ranta, sai dai yayarta anya Hajiya
zata yarda ace gurgu ta aura, ace gurgu ne mijinta,
ita kam ko a jikinta, abinda ta sani kawai shi ne
tana son shi za kuma ta iya aurenshi ta bar masu
29
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
Kafafu biyu.
Sun dauki lokaci mał tsawo cikin, wanan hali
kafin ran nan Nana ta dawo daidai lokacm da ta
saba biyowa, ganewar da ta fi yana da lokacin
fitowar shi nan wurin ya sanya bata yarda ta tsaya
ta bata lokaci bayan tashinsu baa dawo ba, don
kar ya yi ta zaman jiran dawowar ta Kamar
kullum yau ma ta biyo cikin sauri ta ke tafiya doh
ta san ta dan yi latti kadan a dalilin wahalar &
motocin haya suke yi hankalinta bai kai gane baya
wurin ba sai da ta iso saboda tafiyarta take yi ba
tare da tana kalle-kalle ba, sai da ta iso gab da
wurin lokacin ne ta daga ido ta kalli wurin babu
shi babu keken guragun nashi cikin kaduwa ta ja
ta tsaya, ina ya tafi ko dai ya ga na yi lattia zuwa
ne ya tafi tun ban zo ba? Tambayoyin da suka zo
cikin zuciyarta kenan, ta yi waiwayen da za ta yi
ko za ta hango wani wanda za ta iya tämbaya
wani abu game da shi babu to in ta ga wani ma me
za ta cc musu wa za ta ce tana nema? Tun da ko
sunanshi ba ta sani ba, balle sunan unguwarsu, a
hankali cikin sanyin jiki da rashin jin dadi ta wuce
nufi gida da niyyar an jima ta sake fitowa don
ta gani ko ya canza lokacin fitowa ne.
ta
A gida hankalinta bai kwanta ba sallah kawai
30
Ракаркt wte Sehag
ta yi ba ta ma duba inda abincinake ba, balle ia je ta kan shi tana idar da sallah ta je ta yi wanka. ta fito tana shafa mai cikin sauri da sauri Hajiya Salma ta ke kwala mata kira.
"Latiya Nana ba ta zo ta dauki-abincinta ba?"
Tana daga cikin dakinta ta ce.
"Ban jin ci ne yanzu." Ta fito tsakar gida rike
da gyalenta a hannunta cikin shirin fita, Hajiya Salma ta daure fuska "Mc ki ke nufi? Ina za ki
yanzu daga dawowarki bayan ko abinci ba ki ci
ba."
Ta ce "Nan za ni yanzu zan dawo."
Hajiya Salma ta ce "Ai ko kofar gida ba za ki
leka ba sai kin nemi abinda ki ka ci tunda tun safe
ba kya gida yanzu kuma kin dawo daga zuwanki
za ki sake fita saboda ba ki damu da yunwar
cikinki ba."
Nana ta dawo cikin sauri ta shirya abinda za
ta ci ta yi maza ta gama ta fita don ganin ko
mutumin da take nufin ya fito, ta sake isowa
wurin babu shi babu dalilinshi ta juyo ta dawo
gida hankalinta da zuciyarta babu nutsuwa sosai.
Washegari tana shüri tana kallon agogon
Kosa Kwarai lokcin fitarta va yi in ban da tana
tsoron kar ta vi samnakon fitowa ta samu bai fito
31
Da kamar wnya... Hafsat C. Sodangi
ba da tuni ta yi sallama da yayar tata ta fito ta
daďe da kammala shirinta tana jiran lokaci ya cika
gani take tamkar agogon bai tafiya daidai
Da kyar ta samu lokaci ya cika ta fauko
jakarta ta fito ta yi sallama da Hajiya Salma ta fito
zuciyarta cike da fatan ta sameshi zaune kan
keken guragun nashi, tun daga nesa ta gane babu
shi a dalilin daga ido da ta yi ta kallo wajen
gabanta ya yanke ya fadi, kar dai ya canza wani
wurin zaman ne? Wani ne ya yi mishi laifi ko
kuwa dai dama shi haka dabi'arshi ta ke? In ya
zauna anan ya kwana biyu gobe kuma sai ya
canza ya koma wani wurin, tun da ai ita da kanta
ta sani shi din bai wani dade yana zama a wurin
ba, to kuwa in zai canza wuri me zai sa ba zai
gaya mata ba? Tunda dai ya san akwai mutunci
mai Karfi a tsakanin su.
A makaranta tun daga zuwanta Zuwairiyya ta
kalleta ta ce "Yau kuma me ya faru na ga kamar
ba kya cikin nutsuwar ki? Kwanakin baya dai kin
dan wartsake, amma yau kam abin ya dawo don
da ganinki na san ba kya cikin nutsuwar ki."
Nana ta zuba mata ido tana kallonta, jimawa
kadan ta nisa ta ce mata ko aikin dana tfi gida
dashi jiya ban samu na yi ba.
32
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
Zuwairiyya ta sake kallonta ta cc "To wai mc
ya sameki ne?"
Ba ta boye mata ba, ta bata dukkanin labarin
dake tsakaninta da mutumin, to ko dai bai da
lafiya ne Nana? Gabanta ya yanke ya fadi jin
maganar Zuwairiyya ba ta kawo haka ba cikin
rainta, in har ta shi zai yi ai ya kamata ace ya yi
sallama Zuwairiyya ta ci gaba da bayani.
Nana ta zaro ido tana kallonta cikin fargaba
da faduwar gaba, ta yi kuskure da ba ta yi wannan
tunanin ba wanda kuma shi ne farkon abin da ya
dace ya zo cikin zuciyarta da ba ta ganshi ba a
wurin, ji ta tamkar za ta tashi ta koma gida a
wannan lokacin sai dai kuma yin hakan bai da
wani tasiri sosai za ta fi son ta tashi a daidai
lokacin da ya ke fitowa don ta gani za ta sameshi
ko ba za ta sameshi ba, in dai a yanzu ma ba ta
sameshi ba to ta tabbatar kenan babu lafiya, ya
zama dole ta dauki matakin neman inda yake don
ta san halin da yake ciki.
***
Yana kwance a dakin zaure cikin matsanancin
hali a dalilin tsananin ciwon kan da yake ciki, sai
dai kuma ba halin rashin lafiyar dake damunshi ba
ne matsalar da ta fi damunshi, halin da yarinyar za
33
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
ta kasance a dalilin rashin ganinshi na kwana biyu
da yarinyar ba ta yi ba, shi ne babbar damuwarshi.
Tsohuwar da take kula da shi ta yi sallama a
hankali ta shigo dakin bayan ta ji ya amsa mata
sallamar ta ta ta Karasa wurin shimfidar ta shi tana
tabashi don jin yanayin dumin jikin nashi, sannu
Nura ya ya jikin naka? Cikin sanyin murya ya
amsa da sauki Umma. Ta sa hannu ta bude
kwanon dake ajiye kusa da shi ta mayar da murfin
kwanon ta rufe, ta maida hankalinta a gareshi
yanzu nan kunun ma ba ka sba ba Nura? Ace sai
ka kauraccwa cin komai kamar wani dan yaro? А
ina ka ga ana kin cin abinci don ana rashin lafiya?
Ai ko ba dadi sai ka ci ko kadan ne don maganin
da ka ke sha ya yi amfani. Ta shi ka ga ni maza
sha kunun nan ko kadan ne ga maganin ka ka sha,
Nura ya mkie ya zauna a tsakiyar katifar tashi da
kyar ya ke iya bude ido saboda tsananin ciwon
kan dake damunshi.
"Umma ban san sunan yarinyar ba ne dana
aika an nemi gidansu, an gaya mata kar ta ga ba ta
ganina a wurin da ta saba ganina bani da lafiya
nc."
Umma Talatu ta yamutsa fuska "Kai rabani da
zancen wata yarinya kana fama da kanka kana
34
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
zancen wata can da ba ta dammu da kai ba, in ta
damu da kai ka kwana biyu ba ta ganka ba ita ba
za ta nemi inda kake ba ta ga halin da ka ke ciki?"
Cikin sauri ya ce "A'a Umma ai yarinyar mai
mutunci ce, ba ki ga yanda take amsa gaisuwata
ba, abincin nan da wani lokaci nake dawowa dashi
ai ita take kawo min, ina ganin inda ta san ba ni
dá lafiya da za ta nemeni ta ga halin da nake ciki."
Umma Talatu ta miko mishi kwanon sha ta ce
"Maza karbi ka sha." Bai yi musu ba, ya sa hannu
biyu ya karba cikin ladabi da nuna girmamawa ya
kai bakinshi ya sha daidai gwargwado sannan ya
maida kwanon ya ajiye, ya ce "Alhamdulillahi
bayan ya share bakinshi, to ungo maganin ka sha."
Ta miko mishi kofin ruwa, ya sha ya gyara
kwanciyar shi tare da gyara rufuwarshi.
***
Hankalin Nana ya kai matuka wa wajen tashi
kasancewarta yau ma ba ta sameshi wurin zaman
nashi ba, gashi kuma Zuwairiyya ta ce mata bai
zamo lallai ace canza wuri ya yi ba watakila
lalurar rashin lafiya ce ta hanashi fitowa. Wai me
ya samu Nana ne, ni fa ba na son ace mutum yana
cikin wani hali amma ba zai fada a sani a yi mishi
maganin damuwarshi ba, sai dai ya yi ta wani
35
Da kamat wuya... Hafsat C Sodangi
kumburc-kumbure, Ilajiya Salma kenan lokacin
da al'amarin na Nana ya soma wuce saninta. "Za
ki gaya mini ne abinda ya dameki ko kin fi so sai
Alhaji ya shigo na gaya mishi." cika ta dauko
Rahma tana daga gefe ta yi maza ta ce
"Umma ai dazu da na ga Antin tana kuka naKall
tambaycta abinda yake mata ciwo ta ce mun wai
kanta ne."ijn daed ien
Nana ta gallawa yarinyar harara yayin da
Hajiya Salma ke fadin kuka Nana? Kina cikin
halin da damuwa ke sanyaki zubar da hawaye
amma ni 'yar uwarki ba za ki gaya min ba? Laifin
mc na yi miki da za ki dauki wannan matakin a
kaina ko kin taba kawo min damuwarki ne ban yi
wani abu a kanta ba?"
Cikin sauri Nana ta ce "A'a Anti ba fa haka ba
ne ni bani da wata damuwa ni dai mutumin nan ne
dana gaya miki rashin ganinshi yake hanani jin
dadi sai ma ganin kamar wani abu ne ya sameshi,
don ina ganin kamar haka kawai ba zai daina
fitowa wajen ba."
Hajiya Salma ta zuba mata ido cikin damuwa,
"Ni fa har yanzu ban gane wannan mutumin da ki
ke fada ba, kuma 'yan samarin da suke shigowa
gidan nan da na yi musu magana a kan shi sun cc
36
Dä kamar wuya.. Hafsat C. Sodang!
ba su gane shi ba, kar dai fa dama ke kadai ki ke ganin shi in kuwa haka ne kin san ba na kirki ba ne?"
Nana ta yi maza ta ce "Haba Anti wannan
mutumin bai yi kama da wanda zai iya cutar da dan Adam ba, na san shi din mutum ne kamar
kowa illa iyaka dai yana da lalurar kafa tun da da
keken guragu ya ke amfani wannan kuwa bai
canza mishi komai ba daga kyakkyawar halittar shi."
Hajiya Salma ta ce "To ki dai yi a hankali, ki
dan yi bincinke kadan ta nan inda ki ka saba
ganinshi ko ba ki san sunanshi ba in dai da gaske
ne yana zama a wurin kamar yanda ki ka fada ai
ba za a rasa wanda zai gane kwatancenshi ba da
za ki yi ba, don kin san halin da yake ciki
hankalinki ya kwanta, ina dai ce ba wani abu ne a
tsakaninku ba?"
Ta yi maza ta ce "A'a babu komai." Ta се "Shirya ki rike Rahma ku je ta yi mikį rakiya ku
dan yi binciken kadan a kanshi kar ku yarda ku yi nisa."
Ta ce "To ba zamu yi ba."
***
Tsayuwarta a wurin ta kai kusan minti uku
37
Da kanyaWepaHalsat Sedangl
kafjg U fuhitu da a ta lambaya ta yi
tambayniwajgngau, uku ba ta, samu wanda ya ce
ya gancshi ba, duk da su din ga dukkan alamu
sumamezaa unguwar ne.
Blankalinta Ya soma Jashi, Jashi, isoro soro ma ya somare
kamatkar daifa zancen Antinta ya zama
gaskiya ila kadaj ke ganinshi, ta yi kamar ta juya
ta nufi gida sai,kurum ta i kai ko dama hakan ne
ba mai cutarwa ba ne aa gareta ya kamata ta
nemeshi ta ji menene dalilin da da yake fitowa
tany ganinshi yanzu kuma ta daina bayan ya riga
ya sa sun gaba ita da shi? Ci gaba da nema da ta yi
shi ns dalilin da ya sanya ta yi nasarar gano inda
gidan Basu yake cikin wani lungu, tana, tsaye a
kofar zaurgn, gidan nasu mai tsananin duhu saboda
tsukewar shi, tana tana nazarin nazarin zauren kafin ta shiga
cikinshisaboda bata jya hango112.00 komai daga nan
inda take tsaye, yaron da ya rakotan ya sake ce
mata in dai ani saurayi mai yawo a
a keken
gidansu, idan ma ya guragyike nema to nan ne gidan
nuna miki, wani gida ba wannan ba akan shi ne
nasu to karya ya yi miki don na ga alamar
wumin dan ashana ne, kullum ka ganshi da
nkakkun kaya kuma yana fama da kanshi çikin
uragi amma sai ka ga ya fito daa safeafe yanа
38 Γε
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
rabawa masu kafa biyu sadaka bayan shima wurin
bara yake wuni.
Nana ta tura kai zuwa cikin zauren saboda
bata jin dadin bayanin da yaron ke mata in kin shiga ciki ki ce ina babar Nura? Sunan Mamanshi kenan yaron ya sake mata bayani duk da ba neman hakan ta yi ba.
Suna shiga cikin zauren Rahma ta buga tuntube da wani katon turmi dake kafe a gefe, a
firgice ta kwallara kara da sauri Umma Talatu ta fito daga dakin cikin zauren tana fadin "Subhanallahi, wacece wannan? Kin yi tuntube ne da turmin nan ko?"
Cikin ladabi Nana ta soma gaisheta, cikin
ladabi ita kuma tana amsawa, tare da nuna
kulawarta ga 'yar karamar yarinyar, to ki yi hakuri
mana ya ya budurwa kamar ki kuma da raki? Yi
hakuri, yi hakuri, sa hannu biyu ki share hawayen
naki, kar Malam dina ya fito ya ga hawayen naki,
ya ce baya auren saboda baya son raguwar mace,
hannu biyu Rahma ta saka tana share hawayenta,
yayin da Nana ke ta faman murmushin al'amarin
nasu.
"In ce ko ku baki ne?" Ta yi tambayar bayan
ta maida hankalinta wurin Nana. Nana ta ce "A'a
39
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
anan unguwar muke ta can sama kadan wajcn
gidan Alhaji Sani."
Tsohuwar ta ce "To, to to na ji wa ku ke
nema?"
Nana ta ce mata "Babar Nura nake nema."
Та се "То ai ni ce babar Nura, sai dai kuma ba
ki sanni ba nima kuma ban gane ki ba."
Nana ta ce "E wani mutum nake nema ta
shiga siffanta mata shi sai da ta yi shiru sannan ta
ce "To ai ina jin dai Nuran kenan ki ke nama ko
kuwa shima ba ki san sunan nashi ba ne?"
Nana ta yi murmushi ta ce "E."
"To in ce ko dai lafiya?"
Nana ta sake cewa "E, zuwa dai na yi in ji ko
lafiya ba na ganinshi a wurin zamanshi shi ne na
ce bari in tambaya saboda jiki da jin dadi ya
kama." ২
Umma Talatu ta ce "Ai kuwa Nura yana nan
kwance kwana ukun nan duka jikin nashi babu
dadi, shiga nan bayan ki yana ciki ku gaisa."
Ta waiwaya ta kalli kofar ta ce "A'a ba ma sai
na shiga ba a dai gaya mishi ina gaisheshi
Ubangiji Allah ya ba shi lafiya."
Umma Talatu ta ce "To me kenan kuma aka
yi kin zo har gida amma ba za ki shiga ki ga jikin
40
Da kamor wuya.... Hafsat C. Sodangi
na shi ba? Ai ko daga tsayc ne kya shiga ku gaisa."
Ba ta yi musu ba saboda ganin girman
shekarunta, a bakin kofar ta yi sa!lama daga ciki
ta ji an amsa sallamar tata don haka a hankali ta
tura kofar ta shiga dakin wanda shima duhun
cikin shi bai barin a fahimci abinda ke cikinshi
cikin gaggawa sai da suka zauna kan wata
tabarma dake shimfide cikin dakin na dan wani
lokaci kafin ita da Rahma su ka fahimci abinda ke
cikin dakin a dalilin sabawar da idanuwansu suka
yi da yanayin hasken dakin, daga katifar da yake
kwance akai sai ko keken shi na guragu dake ajiye
a gefe, cikin sauri ta juyo gareshi bayan ta dan
juya idanuwan ta zuwa kallon yanayin dakin,
idanuwansu suka hadu cikin nutsuwa da jin kunya
ta tambayeshi ya ya jikin naka?"
Da kyar ya iya bude baki ya amsa mata da
sauki saboda tsananin farin cikin da ya samu
kanshi a ciki ya sakarwa Rahma murmushi tamkar
ba rashin lafiya yake yi ba "Yan mata ya
sunanki?"
Rahma ta bude baki a hankali ta ce mishi
"Sunana Rahma."
Ya ce "A'a suna mai dadi Baba ya zabar miki
41
Da kamar wuya.... Hafsat C. Nodang!
in ce ko dai yana sonki da yawa ne?"
Rahma ta gyada kai nuna alamar lallai baban nata
yana sonta, ya sake wani murmushin to matso
daga nan mu dan yi hira mana
Ba ta yi gardama ba, ta je kusa da shimfidar
tashi ta zauna, yana dan wasa da 'yan yaisunta
yana kuma fakon Nana yana satar kallon ta sai ya
ce "Ni Rahma ya sunan Antin naki ne?"
Ba tare da ta dan yi jim ba ta bude baki ta ce
mishi "Sunanta Nana."
Ya yi murmushi ya ce "Nana Asma'u ko Nana
Aisha ko Nana Fatima?"
Rahma ta ce "NIma ban sani ba."
Ya kalli Nana ya ce "Don Allah Nana taimaka
min cikin aljihun kekenan nan nawa akwai cakulet
dan mikowa Rahma."
Cikin sauri da nutsuwa ta mike ta nufi kan
keken nashi ta sa hannu a aljihun keken kamar
yanda ya gaya mata ta jisu da yawa a ciki, ta debo
kwaya uku cakulet ce masu tsadar gaske zuciyarta
ta raya mata ta mika mishi. "Haba debo mata da
yawa mana wannan me zai mata." Ya fada yana
mai kallon fuskar Rahma. Ta sake karo mata
sannan ta koma wurin zamanta ta zauna.
"Sai ki ka ga bana fitowa." A hankali ta cе
42
Da kamar waya, Masat C Sadang mishi e, dama na ce watakila ba ka dda lafiya ne?"
а лсс "ВBari kawai gNanawaniiiy sb matsanancin ciwon kai ne nake fama da shi in yaub
tashi sai an yi ta dora min kankara a kaina sabodaitr
tsananin ciwo, na so kwarai a ce na yi jarumtakar
da na fita na je can wurin in jira zuwanki in yi
miki