An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
DA KAMAR WUYA..HAFSAT @. SODANGI
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
DA KAMAR WUYA....
Littafi na daya
na
Hajiya Hafsat C. Sodangi
1
Da kamar wnya... Hafsat C. Sodang!
Gaisuwar sada zumunci garesu
Bilkisu Ibrahim Jalo
Unguwar Tutsen Tanshi cikin garin Bauchi.
Asma'u Keffi
Fatima Sulaiman Maiduguri
Zainab Zubair Bello
Ummulkhairi Inusa
Fatima Umar
Asma'u (brahim W.T.C. Katsina
Hafsa Mali Bauchi
Maimuna S. Musa
Bilkisu A. Mani
Hadiza a Kurawa
Hauwa'u Maiduguri
Hindatu Mansur
Farida Yahaya Ahmad
Hauwa A. Garba (Hauwan Coach) A Bauchi
Aisha Umar daga Yola
Nafisa Yahaya el-Yakub Azare
Shafa'atu Husaini Babura
Jamcela A. Umar
Ummu Maryam Kano
Fauziyya Wada Sulaiman
Zainab Mahmud Aliyu
2
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodang! Hauwa B. Sulaiman
Hafsat Barister Yusuf
Zaliha Abubakar Datti
Zainab Musa Kallaři
Hadiza Muhammad Bello
Na gode, Ubangijinmu Allahu ya sadamu cikin
aljannarshi ta Firdausi don rahamarsa.
YABO
Littafin yabo ne gareki aminiyata.
Hajiya Jamila Ibrahim Nabature
Na gode, Allah ya raya mana iyali, amin.
FATAN ALHERI GAREKU
Yahaya Mahi Bookshop, Bakin Kasuwar
Kauran Namoda, Local Gobt., Zamfara State.
TUKWICIN LITTAFIN
Na ka ne mijina, Babansu Maryam Aisha
Yunus da Abdulmajid Alhaji Yunusa Abdullahi
Dabai na gode da kulawarka a gareni kullum.
SADAUKARWA
Na sadaukar da littafin ga iyayena.
3
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodang
Alhaji Cindo Sodangi
da Hajiya Fatima C. Sodangi
Ubangiji Allah ya saka muku da alheri, bisa
dawainiyarku a gareni.
JINJINA
Jinjinar littafin taku ce makaranta littattafaina
maza da mata na ncsa da na kusa na gode, da
kokarinku Ubangiji Allah ya kara kaunar dake
tsakaninmu daku.
Hajiya Hafsat C. Sodangi.
TA'AZIYYA
Ina kara mika sakon ta'aziyyata ga aminiyata
Hajiya Rabi'atu Abdul (one) Muhammad bisa rashin
da aka yi mana na rasuwar mijinta.
Major General Abdul One Muhammad (Rtd).
Allah madaukakin sarki ya ji kanshi da rahamar
sa iyalin da ya bari a baya Allah ya amfana su mu
kuma in tamu ta zo Allah ya azurtamu cikawa da
imani.
Amin summa amin.
4
Da kamar wuya.....Hafsat C. Sodangi GODIY A
Godiyata kullum ga Allah take masanin yau da gobe mai kowa mai komai wanda ya halicci mutum
da aljan don su bautata mishi.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakin
Annabawa shugaban Manzanni, Annabi Muhamad (SAW) da alayenshi da sahabbanshi da wadanda
suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar alkiyama.
Bayan haka godiyata mai yawa gareku
wadanda nake yin rubutun saboda ku makaranta
littafan Allah ya kara zumuncin dake tsakaninmu,
na gode kwarai da kulawarku.
Hajiya Hafsat C. Sodangi.
Na gode.
5
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
Littattafan Sodangi
Uwar Miji
Na ga ta kaina
Rabon Kwado
Wayyo Duniya
Tabbataccen Al'amari
Yiwa Wani
Abu Naka
Nufin Allah
Kifi Na Ganinka
Me zamu ce da maza?
Gani gareka
Mata masu duniya
Biyan Bukatar Rai
Hattara
Duk Daya
Littattafan Sodangin basu nufin yi da wani ko
habaici don haka ana neman afuwa ga duk wanda ya
ga wani abu ya yi daidai da abin da yake ciki ba da
shi ake ba dace ne kawai, na gode.
6
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
H
arabar cikin makarantar cike take da
dalibai maza da mata,w asu na kokarin
shiga aji wasu kuma fitowa suke son yi wasu na
zaune a gindin bishiyoyin dake zagaye da harabar
suna hirarrakinsu.
Yayin da wasu suna kebe kansu can gefe suna
tattauna al'amuransu, ga alama dai zangon karatun
ya fara nisa.
Tana zaune akan dan karamin dakalin dake
karkashin bishiyar magaryar da ta saba zama ta
dora littattafanta akan cinyoyin ta ta baiwa
daliban dake hayaniya kusa da ita baya, ta maida
hankalinta kan karatunta sai dai kuma tunanin ta
baya tare da karatun don haka ba wani fahimta
take yi ba.
A 'yan kwanakin nan tana fama da wata
damuwa dake sanyata tsunduma cikin tunani mai
tsananin gaske, dake hanata nutsuwa ko maida
hankali kan abinda ta sanya a gabanta, ba zato
babu tsammani ta ji an dora hannu akan kafdarta
ana girgiza wa tare da kiran sunanta "Nana"
Firgigit ta yi ta wartsake, cikin nutsuwa ta
juyo gareta "Na'am."
7
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
Zuwairiyya ta zuba mata ido cikin kulawa da
tausayawa "Me ya samcki haka Nana?"
Nana ta yi murmushi cikin nuna jarumta da
Karfin hali ta ce "Babu komai."
Zuwairiyya bta 6ata rai ta ce "Ai kuwa ban
dauka akwai 'yar haka a tsakaninmu ba."
Nana ta yi wani murnushi cikin karfin hali ta
ce "Hadda nake son yi."
Zuwairiyya ta nisa ta ce "Ai kuwa dai ban ga
dalilin yin hakan ba don kuwa ni na fi gane yin
karatu ta hanyar fahimtar abin da ake yi
maimakon hadda wanda kema na san abinda ki ke
yi kenan ba hadda ba."
Nana ta mike suka kama hanya suna tafiya
cikin nutsuwa da kwanciyar hankali "Amma dai a
'yan kwanakin nan yanayin ki yana canzawa Nana
fara'arki ta ragu murmushinki ya takaita in an
tambayeki kuma ki ce ba ki da mas'ala illa ta
karatu."
Nana ta kawar da kanta cikin murmushi yayin
da ta ci gaba da murmushi tare da kallon wani
saurayi da budurwarshi da suke wasan guje-guje a
tsakanin bishiyoyi a kokarin da yake yi na son ya
kwace wani abu a hannun yarinyar, ko wannan shi
ne dalilin da ya sa wasu iyaye suke kyamar turo
8
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
'ya'yansu mata zuwa jami'a don yin karatu? Tambayar da ta zo cikin zuciyar kenan. 'Yan
matan jami'a. Nan ata sake fadin hakan cikin
zuciyarta, 'yan matan dake fakewa da wayewar
jami'a waye aiwatar da fitsarar su, a wurinta
rashin kunya da rashin mutunci da ake nunawa da
sunan jami'a wani abu ne da yake samun asali a
dalilin rashin wadataccen ilimin addini a wurin
'yan matan wanda yake haifar musu da rashin
sanin darajar kai mace da aka mutuntata aka
darajantata wajen bata umarnin suturta jikinta wai
ita ce a yau ta ke bayyana kanta ga kowa wasa da
maza kuwa ba a bakin komai yake ba.
"Nana yau dai ina ganin akwai wani abinda ke
damunki ko dai zan rakaki gidane?" Ta yi maza ta
ce "A'a Zuwairiyya gara dai mu karasa zuwa a ji
tunda naga alamar lokacin daukan darasinmu ya
kusa."
Nana da Zuwairiyya aminan juna ne da suka
fara kawancen su tun farkon shigarsu jami'ar.
Nana doguwa ce mai dan kauri kadan wankan
tarwada tana surar jiki mai kyau gata da
madaidaitan idanuwa masu tsananin fari. Ita kuwa
Zuwairiyya fara ce mai matsakaici tsawon tun
shigowarta jami'a matar aure ce don haka za ta
9
Da kamar wnya.... Hafsat C. Sodangi
girmi Nana da shekaru biyar ko uku yabawa d
halayyar Nana da ta yi ya sanya ta amince da ita
suke mu'amallarsu tamkar dukkansu 'yan mata ne
ko kuma sa'o'in juna, komai zasu yi tare suke yi, а
aji suna tare a waje suna tare, ranakun da babu
makaranta kuma suna ziyartar juna. Nana ita ce
kawar Zuwairiyya da Faruk mijin Zuwairiyya ya
fi amincewa da ita don haka mutunci sosai suke
yi.
***
Tun da ya lura lokaci ya kusa sai ya fito bakin
hanya inda ya saba tsayawa, ya shiga jiran
bullowarta. Tsawon lokaci bai hangota cikin tsoro
da fargaban ko dai har ta zo ta wuce ne? Ya shiga
kallon agogon hannun shi don tabbatar da abinda
ya ke zato na wucewar lokacin wucewar nata fiye
da makonni uku kenan tun da ya fara dora
idanuwanshi a kanta tun daga wannan lokacin
kuma ya maida tsayawa a wurin don ganin
wucewarta dabi'a saboda ganewar da ya yi ba ta
da wata hanya da ta wuce wannan hanyar, haka
nan kullum ne za ta zc ta wuce, gane hakan da ya
yi ya sanya lokutai guda biyu suka zamo mafiya
dokantuwa a gareshi lokacin wucewarta da safe
zuwa bakin hanya don shiga mota da kuma
10
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
lokacin dawowarta inda takc sauka ta taho da kafa
zuwa cikin lungun unguwar tasu.
Anya ba ta wuce ba kuwa? Ya sake tambayar
kanshi saboda ganin lokacin sai kara tafiya yake yi, ko kuwa ta canza wata hanyar ne? Zuciyar shi
ta sake raya mishi haka to ai kuwa ba ta taßa fasa biyowa ta nan ba, to in ta canza wannan wcсе
kenan ta biyo, ga dai lungun da na saba ganin tana
bi can ya zubawa lungun ido yana kallon shi, ji ya
ke tamkar ya je ya tambayi lungun ko yarinyar ta
riga ta wuce ta cikinshi in kuma ta wuce to wane
gida take zuwa a ta nan wurin?
To ko dai wani abu ne ya faru da ita? Jikinshi
ya dauki rawa saboda abinda zuciyarshi ta raya
mishi. Kai a'a babu abinda ya sameta tana nan
kalau dinta da sannu zan ganta ta zo ta wuce.
Yanzun nan zan ganta yanzu za ta zo ta wuce,
yanzun nan yanzun nan bai ankara ba cikinw
annan hali ya ga wucewar tata, bai samu ganin
fuskarta ba a yau a dalilin zubawa lungun gidansu
da yake yi bayanta kawai ya gani sai dai kuma ya
iji kamar gaisuwa da ta yi mishi ita ce dalilin
ankara da ya yi na wucewar tata, da gaske ne ta
gaishe shi ko kuwa jin kunne ne kawai.
Yana cikin wannan hali ta wuce cikin lungun
11
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
nasu ta barshi nan yana ci gaba da kallon lungun
da ta shiga. Tun daga ranar da ya fara dora ido a
kanta ta canza lamarin al'amuran shi. Duk da halin
da yake ciki ya kasa kawar da kai daga al'amarin
yarinyar ya kasa danne zuciyar shi ya yarda
Kaddarar da ta sameshi Kaddara ce da ta zama
dole ya runguineta ya hakura dama duk wani
abinda zuciya za ta raya mishi tana so, a kowane
lokaci ya samu kanshi cikin halin tuna baya da
kallon kanshi a hafin da yake ciki sai ya ji gaba
daya illahirin jikinshi ya canza ya kwabi kanshi
da sake kwadaita da wani al'amarin rayuwa amma
yana hango yarinyar sai ya samu kanshi cikin
dimauta da tunanin ina ma dai zai sake samu wata
dama to da ya nuna wa yarinyar irin matsanancin
son da yake mata.
***
Nana ta isa gida cikin gajiya da kasala ga
kuma yunwar da ta dawo da ita tana isa ta tsaya
tsakar gida ta yi alwala sannan ta wuce dakinta ta
yi sallar La'asar a dalilin ba ta samu yinta ba cikin
makarar. Tana idarwa ta tashi ta nufi kicin inda ta
yi zaton yayarta tana can, cikin murmushi da
fara'a Hajiya Salma ta tambayeta kar dai acc kin
dade da shigowa ban sani ba? Nana ta ce a'a ban
12
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangt
wani dade ba na dai tsaya ne na yi sallah ta ce с,
to kin kyauta shigo daga nan ki shirya abincin ki,
ta wuce ciki ta shirya abincin ta ta zauna tana ci
tare kuma da hira tsakaninta da 'yartata bata kai
abinda ya fi cokali biya bakin ba ta tambayeta ina
Zuwairiyya? Nana ta yi murmushi ta ce, lafiyarta
Kalau.
***
Alhaji Sani Isa dan kasuwa ne, dake sai da
kayan provision a cikin kasuwar garinsu mutum
ne da ya samu shaida a wurin makwabtanshi na
gida da na kasuwa, ya auri matarshi Salma wacce
take ya ga Nana tun a lokacin ne bai mallaki wani
abin a zo a gani ba, duk abinda ya samu na alheri
ya sameshi suna tare don haka yake matukar
mutuntata da ganin girman iyayenta da suka
kawar da kai ga dimbin maneman da ta yi musu
hannu da shuni a wancan lokacin suka dauketa
suka bashi ita.
Ga shi kuma ya yi dace ya samu Salma
yarinyar ce mai tarbiyya da nutsuwa mai girmama
aure, tun zamanshi da ita bai taba ganin wani abu
tare da ita ba na bacin rai don haka babu wanda ya
taba jin tsakaninshi da ita, wannan dalili ya sa
suka kwashi shekaru bakwai cus ba tare a an taба
13
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
yin koda bari ne ba a gidanshi amma hakan bai
daga mishi hankali ba, balle ya shiga neme-nemen
karin wani auren duk da shawarwarin da 'yan uwa
da abokan arziki suka yi ta bashi a haka suka
zauna har Ubangiji ya azurtasu da haihuwar 'ya
mace mai na Rahma daga ita suka samu
Mubarak, sai kuma yanzu da take goyon
AbdulRahman, don haka sai ta kara mike kafa a
gidan mijinta ta kuma kara himma wajen kyautata
mishi da 'yan uwanshi don kara samun zaman
lafiya da kwanciyar hankali.
Nana kuwa Kanwarta ce, da take rike da ita su
biyu ne kadai mata a wurin iyayensu, sauran duk
maza ne. Kasancewar nana ita ce kadai 'yar
uwarta mace ya sa Salma take nuna mata
matsanancin gata tun tana 'yar karama kwarai
rikonta ya dawo hannun yartata a dalilin rasuwar
mahaifiyar su.
Nanna ta taso cikin kulawa da gata ta yadda
ba ta ta6a zama tana tunanin maraicinta don ta
rasa wani abu ba, sai dai ta fi hakan don yiwa
iyaycnta addu'a, ko shima Alhaji Sani ya riketa ne
irin rikon da uba ke yiwa 'yar shi don ita da
'ya'yan da yarta ta haifar mishi ganinsu yake yi
duk daya, yadda Nana ta taso cikin tarbiyya da
14
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
nutsuwa ga riko da addini ya sa Alhaji Sani ya yi
nufin bayar da ita aure ga dan amininshi sai dai
bai furtawa kowa ba, ko ita matar tashi ba ta sani
ba tukuna, jira yake yi sai lokacin ya yi sannan ya
sanar da su.
***
Cikin rubibin dalibai da suka fito daga daukar
lakca ita da Zuwairiyya suka fito suna tafiya cikin
nutsuwa tare da tattaunawa kan yanda lakcar tasu
ta tafi, suna cikin haka ta jiwo wani daga bayanta
yana kwala mata kira, gaba daya suka ja suka
tsaya duk da ba waiwayarwa suka yi ba.
Zuwairiyya ta kalleta cikin nutsuwa da
kulawa a hankali ta bude baki ta ce mata "Da dai
kin saurari mutumin nan kin ji abinda zai ce miki,
ni ban cika son wulakanta dan Adam ba,
musamman mutųmin da ya ce yana sonka ai ina
ganin ya fi wanda bai ce yana sonka ba. Don haka
ni dai ki tsaya ki saurareshi."
Ta yi maza ta yi gaba ta barta a tsaye yayin da
ta tabbatar shi din tahowa yake yi.
"Ran Hajiya Nana ya dade." Ya fadi hakan
daidai isowarshi "Ina fatan an fito lafiya." Ya sake
fadin hakan cikin murmushi, ba tare da ta saki
fuskarta ba, ta amsa gaisuwar da ya yi mata.
15
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
"Allah dai ya sa ba sauri ki ke yi ba, don ina
so ne mu dan gaisa." Ta kara yamutsa fuskarta ta
ce "Gaskiya yanzu gida nake nufin zuwa."
Ya cc "Haba Nana gaisuwa dai ta minti biyar
ai bai kamata ta gayara ba tsakanina dake
musamman da yakc na dauki lokaci mai tsawo ina
neman ganin mun samu damar yin hakan."
Ta kawar da kai gefe ta ce "Ai mun gaisa."
Ya yi murmushi "Nana kenan yi hakuri Nana
mu dan koma daga can gindin bishiyar can akwai
maganar da nake so mu yi bayan gaisuwar."
Ba ta yi musu ba ta bi bayanshi a hankali
ganin ya nufi gindin bishiyar da yake nufin "Nana
ina gajiya?"
Ya sake tambayarta cikin murmushi ganin
yanda ta yi nesa da shi kafin ta zauna a hankali ta
amsa "Lafiya kalau."
Ya sake kallonta "Amma a irin wannan
zaman da ki ka yi ba kya ganin kamar duk masu
wucewar nan zasu iya jin maganar tamu?"
Ta ce "Uh ai babu komai ko sun ji in dai ba
wani mugun abu kake shirin fada ba."
Ya cc "Ko kadan Nana bakina ba zai iya
fadin mugun abu ba, in dai har kina tare da shi."
Musa ya gyara zama da kyau kafin ya tambayeta
16
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
"Amma dai Nana ai ina jin dai kin san ya kamata ki yi aure ko?"
Tambayar ta shi ta zo mata a bazata don ba
abinda ta zaci zai tambayeta ba kenan. "Ban gane
ba ta ce mishi."
Ya ce "E, to Nana yanda na lura ne ba ki da
lokacin kowa ba kya sauraron kowa in dai ba kin
san miji ne da ku a gidan ba ai ina ganin ya
kamata ki yi sassauci."
"Shawara dai kenan dama ka ke son bani?"
Ya ce "E amma ba ita kadai ba ce so nake in
gaya miki Nana ina da damuwa kwarai kan
al'amuranki a kowane lokaci idona zuciyata da
nutsuwata duka a kanki suke ki taimaka ki mun
kwatancen gidanku ta yanda zan samu damar da
zan rinka zuwa muna dan tattaunawa kan
al'amuranmu har kafin Allah ya sa mu fahimci
juna."
Nana ta bude baki kamar za ta yi magana sai
kuma ta yi shiru a dalilin bugawar da ta ji
zuciyarta tana yi cikin sauri tamkar dai tuni take
yi mata kan wani hali da ta dade da samun kanta a
ciki.
Musa ya zuba mata ido a hankali cikin sanyin jiki ya tambayeta "Don Allah Nana gaya min an
17
Da kamar wuva.... Hafsat C. Sodangt
yi miki miji ne?" Ta girgiza kai nuna alamar a'a,
ya ce "To ni ne ba kya so?"
Ta sunkuyar da kanta kasa cikin nutsuwa ta
ce "Akan me zance ba na sonka?"
Ya cc "To in ba haka, ba menene Nana?
Mutumin da ka kc so ai baka kaurace mishi gaba
daya in dai ba ka gane yana da wata murmmunan
manufa bane a kanka. Ko kuwa sonki nake yi
takanina da Allah son ki nake yi da zuciya daya
saboda na yaba da hankalinki da nutsuwarki sonki
nake yi saboda na yaba da tarbiyyar da aka yi
miki, zan yi farin ciki kwarai in har za ki amince
min in zo gidanku."
Kafin ta yi magana sai ga wani yaron ajinsu
Nura da suke mutunci dashi ya iso wurin cikin
murmushi da sakin fuska ya yi musu sallama
Musa ya amsa, sannan ya iso ya mika mata
takardun da ya ke rungume da su. Da dai ban san
ki da yawan mantuwa amma a yanzu abin yana
nema ya zama miki jiki kusan kullum sai kin baro
wani abu na ki a aji karewa ma jiya har jakar
hannunki ki ka manta bayan kowa ya sani ba
dabi'ar 'yan mata bane mance jakar hannunsu a
wani wuri."
Nana ta yi murmushi ta ce "Kai dai sannu
18
Da kamar wuya.....Hafsat C. Sodangi
Nura an gode maka." Ta karbi takardunta shi kuma ya juya ya tafi bayan ya yi wa Musa sallama. Yana barin wurin Musa ya sake taso da maganar da ke gabanshi "Ya ya Nana kin amince
in fara zuwa gidan naku?" Ta yi shiru na wani lokaci jimawa kadan ta ce mishi gaskiyar magana.
ita ce ka yi hakuri ba wai ina nufin bana sonka ba
ne sai dai magana guda daya ita ce har yanzu din
nan ni ban fara hira da samari ba don ka yi hakuri
zuwa nan gaba tukuna."
Ya yi murmushin Karfin hali nan gaba zuwa
yaushe Nana? A yanzu kina nufin ba ki isa yin
hirar bane ko kuwa? Ni da fitowa fili ki ka yi ki
ka gaya min gaskiyar lamarinki watakila da na fi
saurin yarda da kuma yin hakuri ba wannan
kwana-kwanar da ki ke yi min ba. A wurina kin
kai lokacin da ya dace a ce in dai ba kya dakinki
to ya zamo kina gaba da shiga ya sake gyara zama
ya ce "Nana ki soni mana ki amince in aureki
zuciyata tana son ki fiye da duk yanda ki ke zato."
Ta kara sunkuyar da kanta kasa ya ce "Yi
magana mana."
Bakinta ya yi nauyi game da maganar da ta ke
nufin gaya mishi a hankali ta ce "Gaskiya ba zan
iya ba kunya nake ji."
19
Da kamar wnya.... Hafsat C. Sodangi
Dadi ya kamashi cikin murmushi ya cc mata
"To ai soyayya ta gaskiya kenan Nana mai dauke
da kunya da ganin darajar juna don haka na godc
miki Allah ya saka miki da alheri suka yi sallama
ta tashi ta tafi.
Nana ta dawo wurin Zuwairiyya wacce ke
zaman jiranta "Ya ya na ganki haka? An yi hirar
soyayya amma fuska a murtuke."
Nana ta yi tsaki "Hirar soyayya aka ce miki
na yi?"
uwairiyya ta zuba mata ido "To hirar me ki
i? Musa dai kin san ba irin samarin da za ki
ywa ırin wannan wulakancin naki ba ne sai dai
kon ba aurenn za ki yi ba don kuwa shi kowa ya
san mai mutuncine ban kuma ga makusa a tare da
Nana ta sake wani tsakin a hankali ta ce "Ni
kawai kin gane? Ni soyayyar ce kawai bana so ni
karatuna ne a gabana yanzu."
Zuwairiyya ta ce "A'a kina dai da wani dalilin
amma ba karatu ba tunda ni ai ganau ce ba jiyau
ba na cewar karatu bai hana aure, ke ni in kin
barni ma sai in ce miki karatun a gidan miji ya fi
dadi musamman ace kin yi dace kin samu mai
20
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangl
kara karfafa miki gwiwa, sai ki yi karatunki
hankalinki a kwance na iyayenka kwance kar ki
bari ki yi irin kuskuren da na yi a lokacin 'yan
matancina."
Da sauri Nana ta tambaye ta "Wane irin
kuskure ki ka yi Zuwairiyya?"
Zuwairiyya ta yi murmushi ta ce "Ke dai
kalleni kawai Nana shi ya sa ki ke ganin ina
yawan yi miki magana saboda ina tsoron abinda
ya sameni kar ya sameki."
"To gaya min mana Zuwairiyya a yanda nake
kallonki din nan nake ganin tamkar komai naki a
daidai yake tafiya me za ki yiwa kanki na kuskure
da har ki ke tsoron kar in yiwa kaina nima?"
Zuwairiyya ta ce "Ke dai bari yau lokaci ya
riga ya yi nisa don haka gara mu tashi mu tafi
wani lokacin muka samu lokacin da bamu da wani
darasi zan ba ki labari."
Nana ta ce "To Allah dai ya kaimu da haka
suka kama hanya gidajensu.
***
Yau ma yana zaune kan kekenshi na guragu
sauraron wucewar nata yake yi ya zubawa hanyar
da ta saba fitowa ido yana kallo cikin zakuwa da
jiran ganin fitowarta yau kam ya yi niyya in ta zo
21
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi
wucewa ba zai bari ta wuce shiru ba tare da ya се
mata komai ba. Zai yi kokarin ganin ya mika ko
da gaisuwa ce a gareta ya kuma lura da irin
amsawar da za ta yi mishi in har za ta amsa din.
Har dare yana nan zaune a wurin ba tare da ya ga
wucewarta ba, ranshi ya 6aci hankalinshi ya tashi
ya rasa abinda zai yi ya ji dadi, ya kuma rasa
wanda zai tambaya haka ya hakura ya juya gida
cikin takaici da bacin rai na rashin ganin abinda
zuciyarshi ta ke so.
***
Nana ta shiga gidan Zuwairiyya cikin
kwalliyarta ta burgewa, kamar kullum ta yane
jikinta da gyale mara nauyi ya kuma saukar mata
sosai a tsakar gidan ta gamu da Umar, mijin
Zuwairiyya cikin ladabi da raha suka gaisa,
sannan ta wuceshi ta shiga cikin gidan wurin
Kawartata.
"Yanzu muka gaisa da Umar." Ta gayawa
Zuwairiyya hakan cikin murmushi, Ta ce "E sauri
ya ke yi zai je wurin Ummanshi yanzu ta yi waya
tana son ganinshi, amma in banda haka babu inda
za shi." Gaba daya suka wuce dakinta suka zauna,
suna hira tare. Motsa baki cikin murmushi Nana
ta ce "Zuwa fa na yi ki bani labarin kuskuren da ki
22
Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi ke cewa kin yi don in ji." Zuwairiyya ta yi murmushi ta cc "Nana kenan,
ina
to mu je kicin ina aikin abinci kina tayani kuma baki labari."
Ta mike zumbur ta cc "To mu jc." Tare suka shiga kicin din suna aiki suna hirarsu. "Nana ina jin dai ai kin san ni da Umar 'yan uwan juna ne?"
Nana ta gyada kai nuna alamar e, haka ne. "Ni da Umar iyayenmu wa da kani ne mahaifinshi shi ne babba, shi ke aiwatar kuma da duk wani muhimmin al'amari a zuriyarmu. Na san Umar tun ina 'yar karamata, saboda yawan mu'amalarshi ta gidanmu, Allah ya sani tun tasowata ba wata jituwa mai yawa сe а
tsakaninmu ba don ko kadan jinina bai hadu da shi ba, don kuwa shi din mutum ne