Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
bayani don kar ki ganni shiru amma hakan bai yiwu ba don ina cikin inuwa ma fama da kan Kn nawa nake yi balle kuma ace na fita cikin rana saj, in ji kamar wuta aka dora min akan. Don Allah ki yi hakurin wahalarwar daRre na yi miki tun da ga shi 2. na saki kin taso kin zo har wannan lungun namu mai matsatsi da yawan kwatause sos) sna nТ Ta ce "Kai daina fadin haka don Allah yanzu ka je asibitinc?ded su ni owst gy ៩៦ ទចននិនយ Ya girgiza kai ya ce A'a ban je ba amma Ummana ta yi min jike-jiken wasu saiwoyi suK ALSАВП CE nake sha kuma ina jin dadin su don na dan jiі dadi" for evabad evilslead rinsg sasi gix Ta ce "To Allah ya kara maka lafiyaa En esnision Ya ce "To na gode Nana na gode, kwarai da kulaward da ki, ka nuna min na gode Allah KO. 2 Ubangiji ya saka miki da-alherHM" 5 sA ILUS2 SD *** 43 POKS KE ME KOMI IS THIRAT Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodang! Tun daga wannan ranar kullum Nana za ta sa a kawo mishi abin karyawa da safe abincin rana da kuma na darc ba ta dai sake zuwa gidan don duba shi ba, to amma kowane lokaci tana cikin yi mishi aike har dai ya samu lafiya ya fara fitowa. Tun daga ranar da ya soma zuwa kofar gidansu Nana ya aika ya kirata ta fito bai sake komawa bakin hanyar da yake zama ya zauna ba, kullum ya kan je gidan su Nana ne da yamma ta fito su sha hirarsu sai dai kuma babu zancen sosai ya cikin hirar tasu mafi yawancin kalamanshi sukan tafi ne ga yin godiya ga karancin da ya се wai Nana ta yi mishi. Tun Nana tana sauraronshi har dai ta gaji ta ce ita kam ta rufe wannan zancen tsakaninsu in da maganar da ya kawo in kuma babu to sai ya yi murmushi ya ce "To ai shi kenan Nana yanda duk ki ka ce a yi ai hakan za a yi amma in ban da haka i da ba zan gaji da gaya miki wannan alherin ki ba kin taba ganin tsaleliyar budurwa kamarki tana sauraron gurgu?" Nana ta yi tsaki ta ce "Kai kuwa Nura me ya sa ka ke yin haka ne shi gurgu ba mutum ba ne? Da sauri ya ce "Mutum ne ma cikakke amma ai irinku ne kawai suke kallonmu a haka." 44 Da kamar wuya. HafsatC. Sodangi da Ta çev"To ni dai a kashe irinm wannanji maganar a tsakaninmu on baki. dama kuma na riga na Ya ce "Nima na bári ba zan sake yi ba tundaa kin ce ba kya so."ki ke mikewa cskin sauri ki tafi Soyayya ce mai karfi ta kullu a tsakanin Nura da Nana duk da dai ba furtata ba illa dai dukkan alamominta sun bayyana haka nan su da suke jin abin a jikinsu suna ji babu abin da Nana ke son jin ya fito daga bakin Nura illa gaskiyar abinda ta sana shi ne a tsakaninsu don ta samu damar yiwa yayarta bayani a kan shi ta ji abinda za ta ce, amma shi ya ki kullum sai dai ya turo kekenashi ya zo ya yi hirarshi ya kama hanya ya tafi wani lokaci ma ko da ya san ba ta nan a gidan zai turo keken nashi ya zo kofar gidan ya kira su Rahma da Kannenta su zo su yi hira ya kuma ba su cakulct da sauran tsaraba yara su karba suna murna shi kuma ya tura kekan shi ya tafi.a Kalaa" Hankalin Nana ya kai matuka wajen tashi akan dabi'un Nura na kin furta soyayyarshi gareta ko kuwa yana nufin ya ce shi bai san halin da suke ciki ba ne? Ko kuwa jira yake yi sai ita ta yi mishi nuni kan hakan, ta jinjina hakan cikin zuciyarta ta ce kai ita kam ba za ta iya ba don ita kam a wurinta ba ta taba daukar wayewar kan 45 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodang! 'yan matan yanzu dake cewa samari suna sonsu a matsayin wayewa ba don haka ba za ta iya ba, in shi bai ga dacewa ya yi magana ba to shi kenan su yi ta zama a haka ai kowa yana jin jiki. Shi kuwa Nura yana kwance a dan tsukakken dakinshi da bai ko isarshi mike kafa sosai saboda tsawonshi cikin dare ne amma idonshi biyu ya kasa yin barci saboda tsananin tunani, lokaci ya yi da ya kamata ya furtawa yarinyar nan gaskiyar lamarinshi tun da dai zuwa yanzu ya tabbatar alamomin da yake gani a tare da ita na so ne abinda wani sashin na zuciyar ke gaya mishi kenan, yayin da daya 6angaren na zuciyarshi ke mishi kashedin maza ka je ka wargaza 'yar alakar da ku ka soma samu garin saurinka da бабare, yanzu haka wannan sakin fuskar da take maka na tausayi ne bisa halin da ta ganka a ciki kana furta wata kalma mai kama da soyayya a gareta al'amarin naku ya watse gaba daya, shiru ya yi yana kallon saman dakin duk da bai iya hango komai saboda tsananin duhun dake ciki rayuwa yake tunawa da yanda al'amura ke juyawa suna canzawa a kowane lokaci, ya lumshe idanuwanshi a hankali cikin tunanin al'amuranshi da yake gani tamkar a mafarki yake. 46 *** Da kamur wuya.... Hafsat C. Sodangi Nana tana gida a yau kasancewar ranar ta Lahadi ce tun safc take tare da Antinta a kicin suna faman shirya abinda karyawa kasancewar maigidan ya dawo daga tafiya ga kuma baki da ke ta faman shiga da fita sai wajen karfe goma Nana ta kammala ta shiga bandaki ta yi wanka ta fito ta shirya tsaf, bayan ta gama shafe-shafenta ta yi shiri cikin wata atamfa da ta yi matukar dacewa da ita ta shigo falon Antinta ta sameta ta nemi wuri ta zauna tana tambayarta. "Za ki karya yanzu ne?" Cikin sauri Hajiya Salma ta ce mata "Karyawa kai Nana kalli agogo fa wajen sha daya ne yanzu." Nana ta tashi ta fita ta je ya kawo musu suka zauna suna karyawa cikin mu'amala mai dadi da kauna mai yawa. Hajiya Salma ta kalli Nana ta ce mata "Ina ganin fa kamar nan ba da daďewa ba Alhaji zai yi aurenki don na ji ya fara yin maganar." Nana ta dago ido ta kalleta cikin nutsuwa ba tare da ta nuna damuwa game da maganartata ba, cikin shagwaba ta ce mata "To na kawo saurayi ne Anti da za a fara zancen aurena?" 47 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi Hajiya Salma ta yi murmushi "Shi kam Alhaji ko ki kawo saurayi ko kar ki kawo ina ruwanshi, tun da shi dama ina ganin kamar yana da wanda yake son baki." Gaban Nana ya yanke ya fadi ya ke son ba ní fa ki ka ce?" Ta yi tambayar .cikin nuna alamar tashin hankali. Hajiya Salma ta yi maza ta tsuke fuka ta ce "Bai isa ya yi hakan ba ne?" Nana ta sunkuyar da kai cikin sanyin jiki da sanyin murya ta ce "Ya isa Anti." Ta mike za ta fita, ta ce mata "Dawo ki zo ki zauna ki gaya min mene ne?" Nana ta dawo ta zauna tana sauraron 'yar uwar tata kan ta ce komai aka shigo aka yi sallama, Nana ta amsa yaron da ya yi sallamar ya ce "Wai Nana ta zo in ji Nura." Ta сe "To gaya mishi ina zuwa." Ya juya ya tafi, ita kuwa Hajiya Salma ta zuba mata ido cikin nutsuwa a hankali ta bude baki ta ce mata "Ni me ke tsakaninki da wannan mutumin ne?" Nana ta yi shiru cikin tunanin abinda za ta се mata sai ta ji ta ce "Ina fata dai ba shi ki ke shirin kawowa gidan nan ba? Don na lura da irin zaburar 48 Da kumar wuya.... tafsat C. Sodangi da ki ka yi da na ce miki ina ganin kamar Alhaji yana da wanda yake son baki, dama kuma na riga na lura da ke duk lokacin da aka ce yana kiranki a waje zumbur ki ke mikewa cikin sauri ki tafi sabanin su Musa da in sun zo sai an yi kamar anan yi da ke kafin ki fita." yi Nana ta yi shiru ta sunkuyar da kanta kasa ta shiru tana sauraron yayar tata dake ta faman tashin hankali sai da ta gaji ta yi shiru don kanta sannan ne Nana ta mike tsaye ta nufi kofar gida, Nura yana zaune cikin kcken shi yana sauraron fitowarta. "Barka da fitowa, ranki ya dade." Ya fadi cikin murmushi da murnar ganinta. Ta amsa mishi sai dai bata maida mishi murmushin ba kamar yanda ta saba abinda ya sanya gabanshi faduwa, in ce ko dai lafiya Nana?" Ta dan kalleshi a hankali ta ce "Lafiya kalau." Ya ce "Haba Nana ai ba haka na sanki ba, ba haka na saba ganinki ba taimakeni ni dai ki gaya min in dai wani laifi na yi don in yi sauri in ba ki hakuri." Ta dan saki fuska cikin kokarin da take yi na ganin ta nuna mishi babu damuwa, ta ce "To ni laifin me za ka yi min?" Ya ce "Haba Nana in ki ka fadi haka ai sai in 49 Da kumat w Hasged ga kamar ban isa in yr muki lartin ba ne Та се "Ba haka ba ne ot dat kawat ba ka mun komai na laifi ba ne sht ya sa na gaya maka haka " Ya.ce "To at shi kenan ba na javayya da ke tunda kin ce ban yi mikı komar ba na yarda ban yr miki ba, amma duk da haka ma rokonki gafara m har abinda ya sosa mikı ran ya shafeni" Ta dan yi murmushi kawai ta yi shiru suka dan shiga hira sai dai ta kasa sakin jikinta su yı hirar sosai kamar yanda suke, haka Nura ya gajı duk kokarinshi na ganin ya rabata da damuwarta. hakan bai yiwu ba. *** Washegari a makaraula suna zaune a dakin karatu suna nazarin littattafansu saboda gab suke da soma jarrabawar su Kwatam sai ga wani yaron ajinsu Ans ya shigo ya ja ya tsaya a kansu yana murmushi "Nana wurinki fa na zo." Ba tare da ta daga ido ta kalleshi ba ta ce 'AGani ai Allah ya sa lafiya, ya ya." "A'a lafiya Kalan zuwa dai na yi in rokeki wata alfarma." Ta bar abinda take vi ta dago tana kallonshi ya sake wani mumushn kafin ya sassauta 50 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodang! muryarshi ya ce mata "Kin san yau sha hudu ne ga watan biyu, wato ranar valentine tun safe nakc nemanki don in rokeki tunda yau ranar masoуа сс kin kuma sani dama ni masoyinki ne ke ce dai kawai ba ki bani hadin kai ba, amma tunda yau rana ce ta musammán ki bani hadin kai mu raya ranar ta zamo mai tarihi da ba za mu manta da ita ba, kamar yanda ni kullum ki ke cikin raina ba zan taba mantawa da ke ba." Ya zuba mata ido cikin sauraro don ganin irin lalataccen kallon da ta ke mishi, ya dan saki wani murmushi na sakarci tare da tsaki "Ni ke Nana kamar ba 'yar jami'a ba." Ya sake kallonta ya ga ko inda yake ba ta kallo balle ta saurareshi, sai Zuwairiyya ce ma ta ce mishi. "Ai sai ku je ku yi ta yi duk wata eda da ba ta ku ba ba ku san asalinta ba suma ma yin nata ba su san dalilinsu na yinta ba amma kun ara kun yafa, wai ku ga wayayyu 'yan boko tö yana da kyau ku rinka tunaw ada cewar ku Musulmi ne." "Ai kuma shi kenan tunda ke ma kin min fuck-up"Ya jiuya ya fita ya bar su suka ci gaba da abinda suke yi bayan sun tashi daga makaranta ne, suna dawowa gida Nana ta ke baiwa Zuwairiyya labarin abin da ya faru. 51 Du kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi Cikin sanyin jiki Zuwairiyya ta ke ee mata "To ki dai sani cewa, mijin Anti tamkar uba yakс a wurinki, don kuwa babu abin da bai yi miki ba cikin abubuwan da uba ke yiwa 'yar shi." *** Kwana da kwanaki Nana tana gida cikin matsanancin hali da damuwa saboda rashin sanin halin da take ciki ga dai maganar da Antinta ta yi mata wanda tun daga ranar ba ta sake ce ata komai ba, ga shi kuma wani dalilin da ba ta sani ba ya sanya Nura ya dauke kafa ya daina zuwa gidansu ya koma zaman kan hanyar da dama can yake yi sai in ta zo wucewa ya fan rusuna yana daga kan keken guragun ya ce mata "Barka da fitowa ranki ya dade a dawo lafiya." Abin da yake matuka bata takaici da kona mata rai me ta yi mishi ya ke mata irin wannan cin zarafin? Ko kuwa dai wani ne ya yi mishi wani abu a kanta ba ta gaya mishi ba, ko kuwa dai haka ya yi sha'awar yi mata don ra'ayin shi na kanshi wadannan sune tambayoyin dake kai kawo cikin zuciyarta. A wannan lokacin ne ta gane tsananin shakuwar da suka yi kafin dauke kafar da ya yi don kuwa ba karamar wahala take yi ba, ta rasa 52 7 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi inda za ta yi ta san me ke faruwa, wata zuciyar tana raya mata ta samu Antinta ta ji inda wani abu ta san ba za ta kasa sani ba. Kuma wata kila in ta yi sa'a ma sai ta ji duk wani abin da ake ciki. Da daddare ta samu Antin nata a dakinta cikin shirin kwanciya ta nemi wuri ta zauna yayin da Hajiya Salma ta maida al'amarinta garcta in ji ko dai lafiya na ganki yanzu ba ki kwanta ba bayan kin wuni kina wahalar makaranta? Nana ta ce ba komai Anti lafiya kalau, so dai kawai na ke yi Anti da in sani ko an yi wani abu ne?" "Wani abu kamar ya ya?" Hajiya Salma ta zuba mata ido. Nana ta dan sunkuyar da kanta Kasa ta ce "A'a gani dai kawai na yi Nura ya daina zuwa kofar gidan nan ban kuma san abinda ya sa hakan ba." Hajiya Salma ta zuba mkata ido cikin nutsuwa ta ce mata "Ni na sa aka hana shi saboda na gane hikimarshi na zuwan da yake yi din bai wuce ya yaudarcki ba, ya sa ki bijirewa iyayenki, tun da shi ban ga alamar ya tsaya matsayinshi ba." Nana ta dan kalleta a hankali ta ce "Matsayinshi kamar ya ya Anti?" Cikin takaici ta ce mata "Ba kin ce mun gurgu 53 ba ne?" Da kamar жига.. Нafsat (. Sodang Та се "Е,." Ta ce "To shisshige mikin me ya ke yi kullum sai ya je ya yi bararshi ba zai ajiye 'yan kudinshi ya samu na cin abinci ba shi da tsohuwar shi sai ya je ya sayowa yara kayan ciye-ciye masu tsadar gaske ya kawo musu wane irin gurgu ne wannan da-budadden ido haka? To ba na so bana so maza ki fita hanyar shi, tun ba mu kai ga samun bacin rai ba, su kansu su Rahma in aka ce musu gashi nan yana kiransu sun rinka tsalle kenan suna murnar zuwanshi wato shi kuma tashi hikimar kenan ya saye zuciyarki, ta alawar da yaek baiwa 'ya'yanki to na ki." Nana ta dan yi shiru zuwa can sai ta се "Amma fa Anti shi Nura wannan mutumin ni ban taba ganinshi yana karbar sadaka ba ba na zaton yana bara, ni ban ma taba ganin wani ya zo wuce wa ya mika mishi wani abu ba, iyaka dai in ji suna gaisawa da jama'a." Ta ce "Ba ya bara me ye sana'arshi?" Nana ta ce 'Nima ban sani ba." Ta ja tsaki ta ce "Ahau to ai gara ki yarda yana barar akan ki ce ba ki san abinda yake yi ba, tun da dai ga shi yana kashe kudi ko jiya fa ga 54 Da kamar wuya... Hafsat C. Sodangi abubuwan da ya baiwa wani dan almajiri ya kawowa su Rahma, can na kwace na ajiyc in kuma bai bari ba da kaina zan je in samu ita Umma Talatun in ja mata kunne danta ya fita hanyarki, tun muna shaida juna da ita cikin mutunci." Ta dan yi tunani kadan zuwa can ta ce "Ni Umma Talatu ma fa ban santa da wani da ba nata na cikinta don bana zaton ta taba haihuwa na dai santa da yaya me yayumen 'ya'yan jama'a to zan gaya mata kul ta fita hanyata, tun rai bai kai ga baci ba, ko kuwa kin ga rashin kyautawa na ne don na lura tunda na fara magana ki ke kallona?" Cikin nutsuwa Nana ta ce "A'a." Ta ce "Yauwa ai kema kin san ba zai yiwu ace kin auri gurgu ba ko? In ban da rigimama irin ta shi ina zai kai tsaleliyar budurwa kamar ki?" Nana ta tashi ta fita ta koma dakinta ta kwanta cikin takaici da 6acin ran abinda Antinta ta sa aka yi wa Nura, duk da ba ta shirya yin jayayya da mijin yarta akan wanda aka cc mata zai bata ba ko da kuwa wane ne abinda Antin nata ta yi ya yi matukar 6ata mata rai kuma in da za ta samu damar zabar wa kanta miji to da gurgun ta zaba ta bar masu Kafafuwan. 55 Du kumar wuya.. Hafsat C. Sodangi Gari na waye ba ta ma tsaya yin atkin komar ba don kar Nura ya kai ga fitowa kan hanyar da yake zama ya zauna. Ta yafa hijabinta ta yi maza ta kana hanya ta nufi gidan nasu kai tsayc ta shige cikin zauren nasu ta yi sallama a bakin kofar dakin shi daga ciki ya amsa ya kuma ba ta izinin. shigowa, a hankali cikin sanyin jiki da nutsuwa ta shiga yana kwance kan 'yar shimfidarshi ya kudunduna cikin lallausan bargonshi ga wani kamshi mai ni'ima da ya gauraye dakin yana ganinta ya yi maza ya tashi zaune, yana kallonta cikin nutsuwa sosai Nana ta kawar da fuskarta daga kallon da ya ke yi mata yayin da zuciyar ta ke tunanin mutum mai tsabta da son jin dadi dubi halin da ya ke ciki amma komai nashi tsab komai nashi mai kyau, ga shi kyakkyawa in ban da lalurar gurguntaka da yake ciki ai kuwa da babu wata uwa da za ta ganshi ba ta yiwa diyarta sha'awar aure shi ba. "Nana in ce ko dai lafiya?" Ya yi tambayar bayan ya gama nazarinta, ta sunkuyar da kanta kasa cikin rawar murya ta ce mishi "Na zo ne in ba ka hakurin abinda Antina ta sa aka yi maka." Da sauri ya kalleta ya ce "Antinki kuma Nana me za ta min da har za ki zo kina bani hakuri a 56 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi kanshi? Ai ni ba ta min komai ba" Nana ta daga ido ta kallesh ta cc "Ba ta ma komai ba ka daina zuwa gidatanu? Ko kuwa kawai ka yi hakan ne don kana bukatar bata min rai?" Da sauri ya ce "Haba Nana me zai sa ni kuwa in bata miki rai, to a kan wane dalili zan yi haka? Menene jin dadina idan na bata miki? Ai ni tunanina da burina bai wuce ace na samu damar da zan faranta miki rai ba in kyautata miki in sanyaki farin ciki, in ga murmushi ya bayyana a fuskarki." Та се "То in haka ne menene ya sa ka daina zuwa gidanmu sai ka zauna a hanya idan na zo wucewa ka ce min Malama barka da dawowa irin gaisuwar da ka ke min a lokacin da ba ka sanni ba." Ya ce "E, Nana gaskiyar magana ita ce an hana ni zuwa gidanku bisa kashedi mai tsanani ban yarda Anti ce ta bayar da wannan umarnin ba kuma ba zan yarda wani ya ce min ita ce ba don haka kema kar ki yarda ace miki ita ce, babu mamaki nema ake a hadamu da ita. To amma ya zama dole in kiyaye zuwa gidan saboda tsoron abin da zai shafi lafiyata, tuni kuwa kin ga duk 57 Da kamar wuya.... Hafsut (. Sodangi abin da zai shafi lafiyata ai dole in tsorata da shi tun yanzu ma ya ya? Ballc ace wani abu ya sake samuna shi ya sa na koma zaman kan hanya in da zan rinka ganinki tunda Allah ya jarrabi zuciyata da son ganinki. Kwana faya in ban ganki ba sai in .rasa nutsuwata in kasa fahimtar al'amurana in rasa inda zan tsoma raina, in ji dadi. To ni kuma ga yanda nake yanda duk na kai da sonki dole ne in hakura in danne zuciyata in ja bakina in yi shiru tunda a ina ki ka taba ganin an baiwa gurgu tsaleliyar budurwa kamar ki? Don haka ni ban ga laifin masu yi min kashedi a kanki ba, son ki suke yi sun kuma ga ba ki dace da ni ba, don kuwa dama ai kin san an ce wai da kamar wuya, gurguwa da auren nesa. To nima na yarda da kamar wuya gurgu da auren tsaleliyar budurwa..." Umma Talatu ta tsaya a bakin kofa tana tambayar "Kai da waye kake magana Nura?" Da sauri ya ce mata "Umma Nana ce ta shigo yanzu, dama zan ce mata ta shigo ta gaisheki." Da sauri Umma Talatu ta ce "A'a ba na so ban ce ta shigo gaisheni ba bana bukata kai dai da yake baka da zuciya to ka je ka yi ta yi tunda an cc ka fita hanyarta in kuwa ba haka ba a karasaka amma ta zo yanzu ka tasata a gaba tana maka 58 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi iyayi me za ta gaya maka? Mc za ta gaya maka da za ka tsaya kana sauraronta? In dai ba nema ka ke yi sai ka ja mana abinda zai damemu ba?" Cikin nutsuwa ya ce mata "Ki yi hakuri Umma? Ba laifin Nana ba nc ita ma ba ta ji dadin abinda ya faru ba, ai tun da ma ta zo har gida Umma ina ganin babu wani zargi a kanta." Та се "Кai tafi can don Allah kai kana da ma ai ba zaka ga laifinta ba tun da idonka ya riga ya rufe a kanta in babu ruwanta ai da ruwan 'yar uwarta tunda ita ce ta turo a yi maka kashedin, ko yanzu ma ni ban yarda da ita ba watakila wani abin aka hado har da ita ya sa ta yi sammako ta zo mana gida ka ga in sun turo wani yanzu ya zo ya duba sai ya zo ya sameta su sami damar yi mana cin zarafi, tun da mu ba masu shi ba ne, ka san su mutane yanzu in mutum ba wani abu ne da shi ba, to ba komai ba ne, wasu ma kallonshi suke yi tamkar shi din ba cikakken mutum ba ne, don haka ta tashi ta fita." Da sauri Nura ya ce mata "Yi hakuri Umma, ai ke ba mai dabi'ar wulakanta bakonki ba ce ita Nana ai baukwarki ce ki yi hakuri." Umma Talatu ta juya ta koma cikin gida ta bar su nan tana barin wurin Nura yà shiga baiwa 59 Da kamar wuya... Hafsat C. Sodangi Nana hakuri, "Ki yi hakuri Nana ta Umma wai babu dama wani ya yi min wani abu komai Kankantarshi sai ta ce dole sai ta ji zafinshi. Ki yi hakuri don Allah kin ji." Nana ta sunkuyar da kanta kasa ta yi kokarin boyc fuskarta daga hawayen dake zuba saboda tausayi, "To wai in mutum yana da wata matsalar rayuwa shi kenan komai kyan halinshi da dabi'ar shi wai shi din kuma shi kenan ba zai mallaki abinda yake so ba?" A hankali ta mike ta sake gyara hijabinta ta ce mishi "Zan tafi." Ya ce "To Nana na gode, Allah ya saka miki da alheri don Allah. ki yi hakuri kan abin da Ummana ta yi ba ta yi miki hakan don kiyayya ba " ne." Nana ta ce "Ba komai ta juya ta fita daga dakin sai dai maimakon ta yi waje sai ta shiga cikin gidan Umma Talatu tana tsakar gida tana faman shura furar sayarwar ta, ta amsa sallamar Nana cikin fara'a tamkar ba ita ce ta gama balbala masifar nan ba dazu-dazun nan, Nana ta nemi wuri ta tsugunna don ta gaisheta Umma ta yi maza ta tkatseta ta hanyar mikewa ta nufi dakinta tana fadin shigo mana shigo daga ciki." Ba ta yi musu ba ta bi bayanta dakin nata dan 60 Da kamar weya.., Hafsat C. Sodang! tsaf yake an maleleshi da kafet ga kuma kusurunta guda biyu manya ga kayan mutanta daga waje ba za ka taba zaton haka dakin tsohuwar ya ke ba. Nana ta zauna a kasa duk da umarnin da tsohuwar ta bata na ta hau kujera ta zauna cikin ladabi ta gaisheta, itama kuma ta amsa cikin sakin fuska da walwala har tana tambayarta ya ya mutanen gidan naku?" Ta ce mata "Lafiyarsu kalau." Ta mike da nufin tafiya "Baba Talatu ta yi maza ta mike ta je ta shura mata fura katon mulmule ta nade a takara ta sanya a leda ta miko mata ta ce "Ta kaiwa Antinta hannu biyu Nana ta sa ta karbi furar cikin yanayin godiya da girmamawa, ta juya ta fita a kofar gida ta tarar da Nura yana zaune kan keken guragun shi ta nuna mishi furar da Umma Talatu ta bata ya yi murmushi ya ce "Ina ruwan Umma." Ya sake kallonta cikin murmushi ya ce "Kin ga in ban dda akan keken guragu nake ai da sai kawai in mike in taka miki, to babu hali." Nana ta kalleshi ta ce "Ba ka dai yi niyya ba kawai tunda ai kana tura keken naka ka je ko ina." Nura ya ce "A'a Nana ba zan rinka bin ki da wannan keken ba a rinka kallonki ana nuna wa 61 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi ana ccwa wancan yarinyar saurayin ta gurgu ne bayan kuma ba hakan ba ne." Ta ce "Kai ne ka ke ganin kamar hakan matsala ne ni a wurina ba komai ba ne tunda na san kowane mutum da darajar da Allah ya yi mishi." Ya girgiza kai a hankali nuna alamar hakan ne, ta ci gaba da tafiyarta yayin da shi kuma ya ci gaba da bin ta da kallo. a *** Nana tana isa gida ta tarar da Antinta a fusacе dalilin neman ta da ta yi ta rasata a cikin

Chapter 3 of 4