Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels DA KAMAR WUYA..HAFSAT @. SODANGI Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi DA KAMAR WUYA.... Littafi na daya na Hajiya Hafsat C. Sodangi 1 Da kamar wnya... Hafsat C. Sodang! Gaisuwar sada zumunci garesu Bilkisu Ibrahim Jalo Unguwar Tutsen Tanshi cikin garin Bauchi. Asma'u Keffi Fatima Sulaiman Maiduguri Zainab Zubair Bello Ummulkhairi Inusa Fatima Umar Asma'u (brahim W.T.C. Katsina Hafsa Mali Bauchi Maimuna S. Musa Bilkisu A. Mani Hadiza a Kurawa Hauwa'u Maiduguri Hindatu Mansur Farida Yahaya Ahmad Hauwa A. Garba (Hauwan Coach) A Bauchi Aisha Umar daga Yola Nafisa Yahaya el-Yakub Azare Shafa'atu Husaini Babura Jamcela A. Umar Ummu Maryam Kano Fauziyya Wada Sulaiman Zainab Mahmud Aliyu 2 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodang! Hauwa B. Sulaiman Hafsat Barister Yusuf Zaliha Abubakar Datti Zainab Musa Kallaři Hadiza Muhammad Bello Na gode, Ubangijinmu Allahu ya sadamu cikin aljannarshi ta Firdausi don rahamarsa. YABO Littafin yabo ne gareki aminiyata. Hajiya Jamila Ibrahim Nabature Na gode, Allah ya raya mana iyali, amin. FATAN ALHERI GAREKU Yahaya Mahi Bookshop, Bakin Kasuwar Kauran Namoda, Local Gobt., Zamfara State. TUKWICIN LITTAFIN Na ka ne mijina, Babansu Maryam Aisha Yunus da Abdulmajid Alhaji Yunusa Abdullahi Dabai na gode da kulawarka a gareni kullum. SADAUKARWA Na sadaukar da littafin ga iyayena. 3 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodang Alhaji Cindo Sodangi da Hajiya Fatima C. Sodangi Ubangiji Allah ya saka muku da alheri, bisa dawainiyarku a gareni. JINJINA Jinjinar littafin taku ce makaranta littattafaina maza da mata na ncsa da na kusa na gode, da kokarinku Ubangiji Allah ya kara kaunar dake tsakaninmu daku. Hajiya Hafsat C. Sodangi. TA'AZIYYA Ina kara mika sakon ta'aziyyata ga aminiyata Hajiya Rabi'atu Abdul (one) Muhammad bisa rashin da aka yi mana na rasuwar mijinta. Major General Abdul One Muhammad (Rtd). Allah madaukakin sarki ya ji kanshi da rahamar sa iyalin da ya bari a baya Allah ya amfana su mu kuma in tamu ta zo Allah ya azurtamu cikawa da imani. Amin summa amin. 4 Da kamar wuya.....Hafsat C. Sodangi GODIY A Godiyata kullum ga Allah take masanin yau da gobe mai kowa mai komai wanda ya halicci mutum da aljan don su bautata mishi. Tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakin Annabawa shugaban Manzanni, Annabi Muhamad (SAW) da alayenshi da sahabbanshi da wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar alkiyama. Bayan haka godiyata mai yawa gareku wadanda nake yin rubutun saboda ku makaranta littafan Allah ya kara zumuncin dake tsakaninmu, na gode kwarai da kulawarku. Hajiya Hafsat C. Sodangi. Na gode. 5 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi Littattafan Sodangi Uwar Miji Na ga ta kaina Rabon Kwado Wayyo Duniya Tabbataccen Al'amari Yiwa Wani Abu Naka Nufin Allah Kifi Na Ganinka Me zamu ce da maza? Gani gareka Mata masu duniya Biyan Bukatar Rai Hattara Duk Daya Littattafan Sodangin basu nufin yi da wani ko habaici don haka ana neman afuwa ga duk wanda ya ga wani abu ya yi daidai da abin da yake ciki ba da shi ake ba dace ne kawai, na gode. 6 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi H arabar cikin makarantar cike take da dalibai maza da mata,w asu na kokarin shiga aji wasu kuma fitowa suke son yi wasu na zaune a gindin bishiyoyin dake zagaye da harabar suna hirarrakinsu. Yayin da wasu suna kebe kansu can gefe suna tattauna al'amuransu, ga alama dai zangon karatun ya fara nisa. Tana zaune akan dan karamin dakalin dake karkashin bishiyar magaryar da ta saba zama ta dora littattafanta akan cinyoyin ta ta baiwa daliban dake hayaniya kusa da ita baya, ta maida hankalinta kan karatunta sai dai kuma tunanin ta baya tare da karatun don haka ba wani fahimta take yi ba. A 'yan kwanakin nan tana fama da wata damuwa dake sanyata tsunduma cikin tunani mai tsananin gaske, dake hanata nutsuwa ko maida hankali kan abinda ta sanya a gabanta, ba zato babu tsammani ta ji an dora hannu akan kafdarta ana girgiza wa tare da kiran sunanta "Nana" Firgigit ta yi ta wartsake, cikin nutsuwa ta juyo gareta "Na'am." 7 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi Zuwairiyya ta zuba mata ido cikin kulawa da tausayawa "Me ya samcki haka Nana?" Nana ta yi murmushi cikin nuna jarumta da Karfin hali ta ce "Babu komai." Zuwairiyya bta 6ata rai ta ce "Ai kuwa ban dauka akwai 'yar haka a tsakaninmu ba." Nana ta yi wani murnushi cikin karfin hali ta ce "Hadda nake son yi." Zuwairiyya ta nisa ta ce "Ai kuwa dai ban ga dalilin yin hakan ba don kuwa ni na fi gane yin karatu ta hanyar fahimtar abin da ake yi maimakon hadda wanda kema na san abinda ki ke yi kenan ba hadda ba." Nana ta mike suka kama hanya suna tafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali "Amma dai a 'yan kwanakin nan yanayin ki yana canzawa Nana fara'arki ta ragu murmushinki ya takaita in an tambayeki kuma ki ce ba ki da mas'ala illa ta karatu." Nana ta kawar da kanta cikin murmushi yayin da ta ci gaba da murmushi tare da kallon wani saurayi da budurwarshi da suke wasan guje-guje a tsakanin bishiyoyi a kokarin da yake yi na son ya kwace wani abu a hannun yarinyar, ko wannan shi ne dalilin da ya sa wasu iyaye suke kyamar turo 8 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi 'ya'yansu mata zuwa jami'a don yin karatu? Tambayar da ta zo cikin zuciyar kenan. 'Yan matan jami'a. Nan ata sake fadin hakan cikin zuciyarta, 'yan matan dake fakewa da wayewar jami'a waye aiwatar da fitsarar su, a wurinta rashin kunya da rashin mutunci da ake nunawa da sunan jami'a wani abu ne da yake samun asali a dalilin rashin wadataccen ilimin addini a wurin 'yan matan wanda yake haifar musu da rashin sanin darajar kai mace da aka mutuntata aka darajantata wajen bata umarnin suturta jikinta wai ita ce a yau ta ke bayyana kanta ga kowa wasa da maza kuwa ba a bakin komai yake ba. "Nana yau dai ina ganin akwai wani abinda ke damunki ko dai zan rakaki gidane?" Ta yi maza ta ce "A'a Zuwairiyya gara dai mu karasa zuwa a ji tunda naga alamar lokacin daukan darasinmu ya kusa." Nana da Zuwairiyya aminan juna ne da suka fara kawancen su tun farkon shigarsu jami'ar. Nana doguwa ce mai dan kauri kadan wankan tarwada tana surar jiki mai kyau gata da madaidaitan idanuwa masu tsananin fari. Ita kuwa Zuwairiyya fara ce mai matsakaici tsawon tun shigowarta jami'a matar aure ce don haka za ta 9 Da kamar wnya.... Hafsat C. Sodangi girmi Nana da shekaru biyar ko uku yabawa d halayyar Nana da ta yi ya sanya ta amince da ita suke mu'amallarsu tamkar dukkansu 'yan mata ne ko kuma sa'o'in juna, komai zasu yi tare suke yi, а aji suna tare a waje suna tare, ranakun da babu makaranta kuma suna ziyartar juna. Nana ita ce kawar Zuwairiyya da Faruk mijin Zuwairiyya ya fi amincewa da ita don haka mutunci sosai suke yi. *** Tun da ya lura lokaci ya kusa sai ya fito bakin hanya inda ya saba tsayawa, ya shiga jiran bullowarta. Tsawon lokaci bai hangota cikin tsoro da fargaban ko dai har ta zo ta wuce ne? Ya shiga kallon agogon hannun shi don tabbatar da abinda ya ke zato na wucewar lokacin wucewar nata fiye da makonni uku kenan tun da ya fara dora idanuwanshi a kanta tun daga wannan lokacin kuma ya maida tsayawa a wurin don ganin wucewarta dabi'a saboda ganewar da ya yi ba ta da wata hanya da ta wuce wannan hanyar, haka nan kullum ne za ta zc ta wuce, gane hakan da ya yi ya sanya lokutai guda biyu suka zamo mafiya dokantuwa a gareshi lokacin wucewarta da safe zuwa bakin hanya don shiga mota da kuma 10 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi lokacin dawowarta inda takc sauka ta taho da kafa zuwa cikin lungun unguwar tasu. Anya ba ta wuce ba kuwa? Ya sake tambayar kanshi saboda ganin lokacin sai kara tafiya yake yi, ko kuwa ta canza wata hanyar ne? Zuciyar shi ta sake raya mishi haka to ai kuwa ba ta taßa fasa biyowa ta nan ba, to in ta canza wannan wcсе kenan ta biyo, ga dai lungun da na saba ganin tana bi can ya zubawa lungun ido yana kallon shi, ji ya ke tamkar ya je ya tambayi lungun ko yarinyar ta riga ta wuce ta cikinshi in kuma ta wuce to wane gida take zuwa a ta nan wurin? To ko dai wani abu ne ya faru da ita? Jikinshi ya dauki rawa saboda abinda zuciyarshi ta raya mishi. Kai a'a babu abinda ya sameta tana nan kalau dinta da sannu zan ganta ta zo ta wuce. Yanzun nan zan ganta yanzu za ta zo ta wuce, yanzun nan yanzun nan bai ankara ba cikinw annan hali ya ga wucewar tata, bai samu ganin fuskarta ba a yau a dalilin zubawa lungun gidansu da yake yi bayanta kawai ya gani sai dai kuma ya iji kamar gaisuwa da ta yi mishi ita ce dalilin ankara da ya yi na wucewar tata, da gaske ne ta gaishe shi ko kuwa jin kunne ne kawai. Yana cikin wannan hali ta wuce cikin lungun 11 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi nasu ta barshi nan yana ci gaba da kallon lungun da ta shiga. Tun daga ranar da ya fara dora ido a kanta ta canza lamarin al'amuran shi. Duk da halin da yake ciki ya kasa kawar da kai daga al'amarin yarinyar ya kasa danne zuciyar shi ya yarda Kaddarar da ta sameshi Kaddara ce da ta zama dole ya runguineta ya hakura dama duk wani abinda zuciya za ta raya mishi tana so, a kowane lokaci ya samu kanshi cikin halin tuna baya da kallon kanshi a hafin da yake ciki sai ya ji gaba daya illahirin jikinshi ya canza ya kwabi kanshi da sake kwadaita da wani al'amarin rayuwa amma yana hango yarinyar sai ya samu kanshi cikin dimauta da tunanin ina ma dai zai sake samu wata dama to da ya nuna wa yarinyar irin matsanancin son da yake mata. *** Nana ta isa gida cikin gajiya da kasala ga kuma yunwar da ta dawo da ita tana isa ta tsaya tsakar gida ta yi alwala sannan ta wuce dakinta ta yi sallar La'asar a dalilin ba ta samu yinta ba cikin makarar. Tana idarwa ta tashi ta nufi kicin inda ta yi zaton yayarta tana can, cikin murmushi da fara'a Hajiya Salma ta tambayeta kar dai acc kin dade da shigowa ban sani ba? Nana ta ce a'a ban 12 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangt wani dade ba na dai tsaya ne na yi sallah ta ce с, to kin kyauta shigo daga nan ki shirya abincin ki, ta wuce ciki ta shirya abincin ta ta zauna tana ci tare kuma da hira tsakaninta da 'yartata bata kai abinda ya fi cokali biya bakin ba ta tambayeta ina Zuwairiyya? Nana ta yi murmushi ta ce, lafiyarta Kalau. *** Alhaji Sani Isa dan kasuwa ne, dake sai da kayan provision a cikin kasuwar garinsu mutum ne da ya samu shaida a wurin makwabtanshi na gida da na kasuwa, ya auri matarshi Salma wacce take ya ga Nana tun a lokacin ne bai mallaki wani abin a zo a gani ba, duk abinda ya samu na alheri ya sameshi suna tare don haka yake matukar mutuntata da ganin girman iyayenta da suka kawar da kai ga dimbin maneman da ta yi musu hannu da shuni a wancan lokacin suka dauketa suka bashi ita. Ga shi kuma ya yi dace ya samu Salma yarinyar ce mai tarbiyya da nutsuwa mai girmama aure, tun zamanshi da ita bai taba ganin wani abu tare da ita ba na bacin rai don haka babu wanda ya taba jin tsakaninshi da ita, wannan dalili ya sa suka kwashi shekaru bakwai cus ba tare a an taба 13 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi yin koda bari ne ba a gidanshi amma hakan bai daga mishi hankali ba, balle ya shiga neme-nemen karin wani auren duk da shawarwarin da 'yan uwa da abokan arziki suka yi ta bashi a haka suka zauna har Ubangiji ya azurtasu da haihuwar 'ya mace mai na Rahma daga ita suka samu Mubarak, sai kuma yanzu da take goyon AbdulRahman, don haka sai ta kara mike kafa a gidan mijinta ta kuma kara himma wajen kyautata mishi da 'yan uwanshi don kara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Nana kuwa Kanwarta ce, da take rike da ita su biyu ne kadai mata a wurin iyayensu, sauran duk maza ne. Kasancewar nana ita ce kadai 'yar uwarta mace ya sa Salma take nuna mata matsanancin gata tun tana 'yar karama kwarai rikonta ya dawo hannun yartata a dalilin rasuwar mahaifiyar su. Nanna ta taso cikin kulawa da gata ta yadda ba ta ta6a zama tana tunanin maraicinta don ta rasa wani abu ba, sai dai ta fi hakan don yiwa iyaycnta addu'a, ko shima Alhaji Sani ya riketa ne irin rikon da uba ke yiwa 'yar shi don ita da 'ya'yan da yarta ta haifar mishi ganinsu yake yi duk daya, yadda Nana ta taso cikin tarbiyya da 14 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi nutsuwa ga riko da addini ya sa Alhaji Sani ya yi nufin bayar da ita aure ga dan amininshi sai dai bai furtawa kowa ba, ko ita matar tashi ba ta sani ba tukuna, jira yake yi sai lokacin ya yi sannan ya sanar da su. *** Cikin rubibin dalibai da suka fito daga daukar lakca ita da Zuwairiyya suka fito suna tafiya cikin nutsuwa tare da tattaunawa kan yanda lakcar tasu ta tafi, suna cikin haka ta jiwo wani daga bayanta yana kwala mata kira, gaba daya suka ja suka tsaya duk da ba waiwayarwa suka yi ba. Zuwairiyya ta kalleta cikin nutsuwa da kulawa a hankali ta bude baki ta ce mata "Da dai kin saurari mutumin nan kin ji abinda zai ce miki, ni ban cika son wulakanta dan Adam ba, musamman mutųmin da ya ce yana sonka ai ina ganin ya fi wanda bai ce yana sonka ba. Don haka ni dai ki tsaya ki saurareshi." Ta yi maza ta yi gaba ta barta a tsaye yayin da ta tabbatar shi din tahowa yake yi. "Ran Hajiya Nana ya dade." Ya fadi hakan daidai isowarshi "Ina fatan an fito lafiya." Ya sake fadin hakan cikin murmushi, ba tare da ta saki fuskarta ba, ta amsa gaisuwar da ya yi mata. 15 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi "Allah dai ya sa ba sauri ki ke yi ba, don ina so ne mu dan gaisa." Ta kara yamutsa fuskarta ta ce "Gaskiya yanzu gida nake nufin zuwa." Ya cc "Haba Nana gaisuwa dai ta minti biyar ai bai kamata ta gayara ba tsakanina dake musamman da yakc na dauki lokaci mai tsawo ina neman ganin mun samu damar yin hakan." Ta kawar da kai gefe ta ce "Ai mun gaisa." Ya yi murmushi "Nana kenan yi hakuri Nana mu dan koma daga can gindin bishiyar can akwai maganar da nake so mu yi bayan gaisuwar." Ba ta yi musu ba ta bi bayanshi a hankali ganin ya nufi gindin bishiyar da yake nufin "Nana ina gajiya?" Ya sake tambayarta cikin murmushi ganin yanda ta yi nesa da shi kafin ta zauna a hankali ta amsa "Lafiya kalau." Ya sake kallonta "Amma a irin wannan zaman da ki ka yi ba kya ganin kamar duk masu wucewar nan zasu iya jin maganar tamu?" Ta ce "Uh ai babu komai ko sun ji in dai ba wani mugun abu kake shirin fada ba." Ya cc "Ko kadan Nana bakina ba zai iya fadin mugun abu ba, in dai har kina tare da shi." Musa ya gyara zama da kyau kafin ya tambayeta 16 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi "Amma dai Nana ai ina jin dai kin san ya kamata ki yi aure ko?" Tambayar ta shi ta zo mata a bazata don ba abinda ta zaci zai tambayeta ba kenan. "Ban gane ba ta ce mishi." Ya ce "E, to Nana yanda na lura ne ba ki da lokacin kowa ba kya sauraron kowa in dai ba kin san miji ne da ku a gidan ba ai ina ganin ya kamata ki yi sassauci." "Shawara dai kenan dama ka ke son bani?" Ya ce "E amma ba ita kadai ba ce so nake in gaya miki Nana ina da damuwa kwarai kan al'amuranki a kowane lokaci idona zuciyata da nutsuwata duka a kanki suke ki taimaka ki mun kwatancen gidanku ta yanda zan samu damar da zan rinka zuwa muna dan tattaunawa kan al'amuranmu har kafin Allah ya sa mu fahimci juna." Nana ta bude baki kamar za ta yi magana sai kuma ta yi shiru a dalilin bugawar da ta ji zuciyarta tana yi cikin sauri tamkar dai tuni take yi mata kan wani hali da ta dade da samun kanta a ciki. Musa ya zuba mata ido a hankali cikin sanyin jiki ya tambayeta "Don Allah Nana gaya min an 17 Da kamar wuva.... Hafsat C. Sodangt yi miki miji ne?" Ta girgiza kai nuna alamar a'a, ya ce "To ni ne ba kya so?" Ta sunkuyar da kanta kasa cikin nutsuwa ta ce "Akan me zance ba na sonka?" Ya cc "To in ba haka, ba menene Nana? Mutumin da ka kc so ai baka kaurace mishi gaba daya in dai ba ka gane yana da wata murmmunan manufa bane a kanka. Ko kuwa sonki nake yi takanina da Allah son ki nake yi da zuciya daya saboda na yaba da hankalinki da nutsuwarki sonki nake yi saboda na yaba da tarbiyyar da aka yi miki, zan yi farin ciki kwarai in har za ki amince min in zo gidanku." Kafin ta yi magana sai ga wani yaron ajinsu Nura da suke mutunci dashi ya iso wurin cikin murmushi da sakin fuska ya yi musu sallama Musa ya amsa, sannan ya iso ya mika mata takardun da ya ke rungume da su. Da dai ban san ki da yawan mantuwa amma a yanzu abin yana nema ya zama miki jiki kusan kullum sai kin baro wani abu na ki a aji karewa ma jiya har jakar hannunki ki ka manta bayan kowa ya sani ba dabi'ar 'yan mata bane mance jakar hannunsu a wani wuri." Nana ta yi murmushi ta ce "Kai dai sannu 18 Da kamar wuya.....Hafsat C. Sodangi Nura an gode maka." Ta karbi takardunta shi kuma ya juya ya tafi bayan ya yi wa Musa sallama. Yana barin wurin Musa ya sake taso da maganar da ke gabanshi "Ya ya Nana kin amince in fara zuwa gidan naku?" Ta yi shiru na wani lokaci jimawa kadan ta ce mishi gaskiyar magana. ita ce ka yi hakuri ba wai ina nufin bana sonka ba ne sai dai magana guda daya ita ce har yanzu din nan ni ban fara hira da samari ba don ka yi hakuri zuwa nan gaba tukuna." Ya yi murmushin Karfin hali nan gaba zuwa yaushe Nana? A yanzu kina nufin ba ki isa yin hirar bane ko kuwa? Ni da fitowa fili ki ka yi ki ka gaya min gaskiyar lamarinki watakila da na fi saurin yarda da kuma yin hakuri ba wannan kwana-kwanar da ki ke yi min ba. A wurina kin kai lokacin da ya dace a ce in dai ba kya dakinki to ya zamo kina gaba da shiga ya sake gyara zama ya ce "Nana ki soni mana ki amince in aureki zuciyata tana son ki fiye da duk yanda ki ke zato." Ta kara sunkuyar da kanta kasa ya ce "Yi magana mana." Bakinta ya yi nauyi game da maganar da ta ke nufin gaya mishi a hankali ta ce "Gaskiya ba zan iya ba kunya nake ji." 19 Da kamar wnya.... Hafsat C. Sodangi Dadi ya kamashi cikin murmushi ya cc mata "To ai soyayya ta gaskiya kenan Nana mai dauke da kunya da ganin darajar juna don haka na godc miki Allah ya saka miki da alheri suka yi sallama ta tashi ta tafi. Nana ta dawo wurin Zuwairiyya wacce ke zaman jiranta "Ya ya na ganki haka? An yi hirar soyayya amma fuska a murtuke." Nana ta yi tsaki "Hirar soyayya aka ce miki na yi?" uwairiyya ta zuba mata ido "To hirar me ki i? Musa dai kin san ba irin samarin da za ki ywa ırin wannan wulakancin naki ba ne sai dai kon ba aurenn za ki yi ba don kuwa shi kowa ya san mai mutuncine ban kuma ga makusa a tare da Nana ta sake wani tsakin a hankali ta ce "Ni kawai kin gane? Ni soyayyar ce kawai bana so ni karatuna ne a gabana yanzu." Zuwairiyya ta ce "A'a kina dai da wani dalilin amma ba karatu ba tunda ni ai ganau ce ba jiyau ba na cewar karatu bai hana aure, ke ni in kin barni ma sai in ce miki karatun a gidan miji ya fi dadi musamman ace kin yi dace kin samu mai 20 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangl kara karfafa miki gwiwa, sai ki yi karatunki hankalinki a kwance na iyayenka kwance kar ki bari ki yi irin kuskuren da na yi a lokacin 'yan matancina." Da sauri Nana ta tambaye ta "Wane irin kuskure ki ka yi Zuwairiyya?" Zuwairiyya ta yi murmushi ta ce "Ke dai kalleni kawai Nana shi ya sa ki ke ganin ina yawan yi miki magana saboda ina tsoron abinda ya sameni kar ya sameki." "To gaya min mana Zuwairiyya a yanda nake kallonki din nan nake ganin tamkar komai naki a daidai yake tafiya me za ki yiwa kanki na kuskure da har ki ke tsoron kar in yiwa kaina nima?" Zuwairiyya ta ce "Ke dai bari yau lokaci ya riga ya yi nisa don haka gara mu tashi mu tafi wani lokacin muka samu lokacin da bamu da wani darasi zan ba ki labari." Nana ta ce "To Allah dai ya kaimu da haka suka kama hanya gidajensu. *** Yau ma yana zaune kan kekenshi na guragu sauraron wucewar nata yake yi ya zubawa hanyar da ta saba fitowa ido yana kallo cikin zakuwa da jiran ganin fitowarta yau kam ya yi niyya in ta zo 21 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi wucewa ba zai bari ta wuce shiru ba tare da ya се mata komai ba. Zai yi kokarin ganin ya mika ko da gaisuwa ce a gareta ya kuma lura da irin amsawar da za ta yi mishi in har za ta amsa din. Har dare yana nan zaune a wurin ba tare da ya ga wucewarta ba, ranshi ya 6aci hankalinshi ya tashi ya rasa abinda zai yi ya ji dadi, ya kuma rasa wanda zai tambaya haka ya hakura ya juya gida cikin takaici da bacin rai na rashin ganin abinda zuciyarshi ta ke so. *** Nana ta shiga gidan Zuwairiyya cikin kwalliyarta ta burgewa, kamar kullum ta yane jikinta da gyale mara nauyi ya kuma saukar mata sosai a tsakar gidan ta gamu da Umar, mijin Zuwairiyya cikin ladabi da raha suka gaisa, sannan ta wuceshi ta shiga cikin gidan wurin Kawartata. "Yanzu muka gaisa da Umar." Ta gayawa Zuwairiyya hakan cikin murmushi, Ta ce "E sauri ya ke yi zai je wurin Ummanshi yanzu ta yi waya tana son ganinshi, amma in banda haka babu inda za shi." Gaba daya suka wuce dakinta suka zauna, suna hira tare. Motsa baki cikin murmushi Nana ta ce "Zuwa fa na yi ki bani labarin kuskuren da ki 22 Da kamar wuya.... Hafsat C. Sodangi ke cewa kin yi don in ji." Zuwairiyya ta yi murmushi ta cc "Nana kenan, ina to mu je kicin ina aikin abinci kina tayani kuma baki labari." Ta mike zumbur ta cc "To mu jc." Tare suka shiga kicin din suna aiki suna hirarsu. "Nana ina jin dai ai kin san ni da Umar 'yan uwan juna ne?" Nana ta gyada kai nuna alamar e, haka ne. "Ni da Umar iyayenmu wa da kani ne mahaifinshi shi ne babba, shi ke aiwatar kuma da duk wani muhimmin al'amari a zuriyarmu. Na san Umar tun ina 'yar karamata, saboda yawan mu'amalarshi ta gidanmu, Allah ya sani tun tasowata ba wata jituwa mai yawa сe а tsakaninmu ba don ko kadan jinina bai hadu da shi ba, don kuwa shi din mutum ne

Chapter 1 of 4