Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Sarauta Publishers Yar Aljanna CeALAWIYYA WADA ISAH AWIYYA WADA ISA 'YAR ALJANNA CE- 2 onyislise sb aabi alamd eYARALJANNA CE 2 daya bangaren kuwa, tunda ta wdaina ganin kyalln motar su ta tsaya nan a soro cike da tunani, cikin ranta take fadin "Gaskiya mutumin nan ya burgeni matuka, na dade banga saurayi da ya hada komi da ake bukata kamar wannan, lallai Auwalu ya kawo mini babban Kifi. Ta saki murmushin jin dadi wanda ya ratsa zuciyarta da ruhinta, wata irin iska ta daban ce ta ratsa ta, ta juya ta shiga gida don kar wani ya shigo ya taddata. seaKai tsaye alwala ta dauro ta hau kan abin sallah tana dakon ta ji kiran sallah domin lokacin yayi, can kasan ranta kuwa tunani Sadik ne zokar cikin ranta ta dade tana ganin maza kala-kala suna neman auren ta amma ba ta ga wanda ya hada komi, kuma ya kwanta mata a rai lokaci daya ba. 5M sb Kiran sallar da aka yi ne ya katse mata s UGIUsus KIKO tunaninta, sai da aka kammala aka-tada salbab GE GIKG TDI B sannan ta mike ta bi jam'i. 3 AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE-2 Bayan sun kammala idar da sallah ne ta koma kan aikinta na abinci wanda dama ita kc yi da aka yi sallama da ita ne Babuita ta karba taci gaba dayi. Tana Kokarin kada miyar ne kamar daga sama ta jiyo sallamar aminiyarta da sauri ta juyo suka hada ido ta sakar mata murmushi gami da fadin "Salama yanzu kike tafc? Barka da zuwa, kamar kin san ina nemanki." Salama ta yi dariya, ta ce mata "Ki сe nazo a dai-dai, Allah ya sa dai babbar samuwa ce. Suka yi dariya sannan ta nufi inda Babar Mero ke zaunc tana lazimi, ta durkusa ta gaishcta, sannan ta nufi inda Mero take. Da sauri ta ajiyc abin kadin ta rufe tukunyar miyar sannan ta marci Salama da su shiga daga cikin daki. Kan wasu kujeru yagulallu da suka sha jiki suka zauna, suna fuskantar juna cike da zumudi Salama ta ce da Mero "Kawata bani labarin abin da ya faru kike nemana, Allah yasa dai babbar karuwa ce?" ta fadi cike da zolaya. 4 AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE-2 Mero ta yi dariya ta ce mata "Kc daí bari kawata ai na yi babban kamu yau dinnan, na samo zankafedc kuma mai hali, hatta motar da ya zo a cikinta abar kallo ce, ga kudi ga kyau ga kuma daukar wanka. Nan take fuskar Salama ta sauya, ta harareta da gefen ido gami da kwabe baki ta ce, "Shine duk kika firgice haka akan namiji?" Mero ta yi saurin bata amsa "Haba kawata ya ba zan firgice ba kuwa? Na tabbata ko kece kika sami irinsa sai kin ruďe." Salama ta sake harararta sannan ta ce "Haba Kawata kar ki zubda ajinki a gurin namiji mana ki tuna fa ko ke wacece, ki tuna yanda maza ke karakaina akanki, amma yau kina nema ki firgice akan mutum daya, gaskiya wannan ba girmanki bane, kar dai ki manta halinsu, in suna son su aureki tammkar su hadiyeki ko su sake naki sai don so, amma da zarar sun sameki 5 AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE-2 bukatar su ta biya, to sai kuma wulakanci da mugun hali ya bayyana. Da alamun maganganun Salama sun fara tasiri a gareta don haka jikinta sanyaye ta ce mata "To ya kike ganin za ayi Salama? Ko dai ma na sallame shi ne kawai na huta tun ba ayi nisa ba." Maganar kawar tata, ta yi mata dadi cikin ranta dama da haka take samun lagonta ta dinga sarrafata, don haka sai ta 6oye jin dadinta ta ce mata. "A'a ni bance ki shareshi ba Mero, amma ni dai shawara ce na baki ki rage wannan zumudin, wallahi ina tabbatar miki namiji ko aurensa kika yi ki iya takunki da shi, in kuwa ba haka ba sai kin koma abar tausayi a cikin jama'a. domin yana gama cin Biredi zai yaga ledar ya watsar a kwandon shara, ya barki da takaici, shiyasa ni kin ganni nan tsakanina da namiji sai dai na karbe abin hannunsa 6 AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2 na barshi da hamma amma ba dai nayi zakwadi akansa ba." Tana kaiwa nan zata mike tsaye tana fadin "Kinga tafiya ta ina da abubuwa da yawa da zanyi a gida kada na shantake anan. Itama Mero mikewa ta yi jikinta ya gama yin sanyi ta ce mata "Shikenan Salama na ji shawararki kuma Insha Allah zanyi aiki daita BY ol ollWani dadi ta ji cikin ranta, har dadin ya bayyana kan fuskarta, cike da fara'a tace mata "Yauwa Aminiyata shiyasa nake sonki wallahi domin kina daukar shawarata matuka." Mero ta yi dariya, ta bi bayanta sallama kawai ta yi da Baba da sauri ta fice tana 233 fadin "Mero sai munyi waya. Haka nan ta barta cikin tunani da saka da warwara, ko ishasshen bacci ranar bata samu ba domin abin ya zame mata 7 AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE- 2 cankacakare, tana matukar jin kaunar Sadik fiyc da komi cikin ranta amma kuma hudubar Salama na yi mata yawo cikin kwanyarta wacce ke neman yi mata tarnaki a cikin tafiya. Shi kuwa gogan bai zame ko ina ba sai gidansu, a falo ya tadda Hajiya Saudc zaunc ita da kanwarsa Ramla suna kallon tibi. Da sallama ya shiga suka amsa masa cike da fara'a, kai tsaye ya nufi kujerar da ke kusa da Hajiya ya zauna. Bayan sun gaisa ne, Hajiya ta dubeshi cike da damuwa tace masa "Wato maganar auren nan dai da na yi maka ka sa kafa ka shureta ko" na kula ko hira muke yi idan na sako maganar auren sai kawai 8 AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2 ka bata rai ka tashi ka fice, wai me ke damunka ne?" Murmushi ya yi sannan da sauri yace mata "Hajiya ki kwantar da hankalinki dama can lokaci ne bai yi ba, to yanzu ina mai sanar dake cewa na samo matar da zab aura, a takice ma naje har gidansu mun gana, don haka sai ki shirya ki bimu da addu'a domir ba wani lokaci za a dauka ba komai zai kasance. Bata san sanda dariyar farin ciki ta subuce mata ba, farin ciki bayyananne akan fuskarta ta ce masa "Haba ko kaifa, gaskiya yau ka faranta mini sosai, to ina yi maka fatan alkaíri, Allah ya sa albarka ya sa an dace da ta gari." Da sauri Sadik ya amshe shima farin ciki bayyane a fuskarsa "Amin, Hajiya." Ramla ce ta matso kusa da shi cike da zumudi ta ce masa "Yaya dafatan dai ka 9 AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2 dauko mana wacce ake ya yi kalar zamani wacce zamu shiga ko ina da ita ba raini." Gaba daya suka yi dariya Hajiya ta ce mata "Kai Ramla baki da dama, wato kenan kina layin masu cewa su dai fara ko mayya ce ko?" Suka sake yin dariya, Sadik ya mike daga kujerar sannan yace wa Ramla, "Ki kwantar da hankalinki Ramla idan na koma zan dauko miki hotonta a waya sai kiga irin zabin Yayan naki." Suka yi dariya sannan yayi sallama da su ya fice, Hajiya na yi masa addu'a Allah ya tsare. Washe gari tun da la'asar yake zumudin tafiya gurin Mero. Karfe shida dai dai ya fito tsaf cikin wata shadda Getzner 'yar Dubai kalar sararin samaniya ta yi masa kyau matuka, zaren da aka yi dinkin shaddar dashi kalar blue ne don haka ya saka hula da takalmi blue. Turaren 10 AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2 out wood na maza ya feshe jikinsa da shi sai tashin kamshi yake yi. Ramla ce take zolayarsa tana fadin "Yaya da alama yau gurin Yayar tawa za kaje na ga sai zumudi kake yi ga wata kwalliya ta musamman ka dauka haka...." Ya katseta ta hanyar kai mata mangara yana fadin "Kaji marar kunyar yarinya, kina nufin bana yin kwalliya irin יי wannan sai yau. Wata kara ta saki ta nufi Hajiya ta buya a bayanta. Ita kuwa Hajiyar dariya kawai ta saki tana fadin "Kar ka dokar mini 'ya, ai ba cewa ta yi baka yi ba, amma dai ba a irin wannan lokacin la'asariyya ba." Kwafa ya yi kawai ya girgiza kai ya fice cikin daga murya ta ce masa "Yaya kar ka manta ka taho mini da hoton nata." Bai ko tanka mata ba ya nufi motarsa wacce ta sha wanki da guga sai daukar ido 11 AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2 take yi. Ya tada ita ya hau bisa titi yana jin wani irin nishadi yana ratsa shi har cikin ransa. Kai tsaye shagon da ake saida wayoyi ya nufa, sai da ya samu wacce ake yayi mai tsada sannan ya siya, yana fitowa ana kiran sallar magriba, don haka ya karasa masallacin da ke kusa ya sauke farali, sannan ya kama hanyar zuwa gidan Mero. A kofar gidan ya ajiye motar tasa ya aika yaro kamar yanda ya saba. Cikin 'yan mintuna ta fito tana sanye da wata atamfa wacce ta dansha jiki ta yafa mayafinta bisa kafada. Duk da ba wata kwalliya ta yi ba amma ta matukar birgeshi domin ko yaya ta yi kyau take yi. Ya bude motar ya fito fuskarsa cike da walwala suka hada ido gami da sakarwa 12 AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE 2 juna murmushi, ya birgeta matuka komi na sa daukar hankalinta yake yi. Ta risina ta ce masa "Barka da zuwa, dafatan kana lafiya." Daddadar muryarta ta doki kunnensa wani dadi ya ji ya ratsa shi, idanuwansa kyas a kanta ya amsa mata "Barkanmu dai Maryamu dafatan kowa da komi lafiya?" Kanta a sunkuye ta amsa masa "Lafiya kalau ya mutanen gida?" "Suna lafiya suna gaisheki. Da sauri ta dago cike da mamaki ta dubeshi ta zaro idanuwa amma ta kasa cewa komi. Dariya kawai ya yi domin ya gano me take so ta ce don haka ya taimaka mata wajen fadi tunda ita ta kasa "Kina mamaki ko? Don nace mutanen gida na gaisheki?" Ta gyada kai sannan tace masa "To ai naga basu sanni ba ne ya za ayi harsu san zaka zo gurina kuma sucea gaisheni?" 13 AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA СЕ- 2 Ya saki faffadan murmushi sannan yace mata "ke ce kike tunanin haka Maryam amma labarinki ya riga yaje inda bakya tsammani domin ni bana yin abu da wasa, da ace babu wani kudiri mai karfi a gareni ba zan taba zuwa kofar gidanku ba don haka idan ma kina kallon abin da wasa gara ma ki daina ki mai da shi babba." Girgiza kai kawai ta yi, cikin ranta kuwa mamaki ne ya cikata domin bata taba haduwa da mutum mai magana daya kai tsaye ba irin Sadik. Motarsa ya bude ya dauko mata 'yar karamar leda mai kyau, ita kuwa kanta na kasa tana wasa da 'yan yatsunta. "Gimbiya ga wannan wata 'yar kyauta ce na kawo miki, kin san bahaushe yace tukwicin so kyauta." Ta amsa cike da murna duk da bata san ko menene be ta hauyi masa godiya. 14 AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE-2 Ya ce mata "Bana son wannan godiyar יי taki, ki bude dai kiga ko menene. Nan take ta bi umarninsa ta bude,hadaddiyar waya ta gani wacce ko a mafarki bata taba tunanin mallakarta ba, cike da mamaki ta bude baki tana kallon wayar, bata san sanda ta zube a kasa don ta yi masa godiya ba, da sauri ya dagota yana fadin na gaya miki bana son godiyar nan amma kin ki ki daina." Cike da kunya ta mike, ya amshi wayar ya hau nuna mata yanda zata yi amfani da ita, a haka har dare ya soma yi, ya yi sallama da ita ya nufi gida ba tare da zukatansu sun so rabuwa da juna ba, sai dai don babu yanda zasu yi, amma fa sun raba dare suna magana a waya, suna musayar kalmomin soyayya, har sai da `bacci yaci karfinsu sannan suka hakura.. 15 **** AWIYYA WADA ISA-‘YAR ALJANNA CE-2 Zaune suka a falo shida Hajiya da alama suna tattaunawa ne akan wani muhimmin al'amari, dukkansu sun maida hankalinsu guri daya suna fuskantar juna. Bayan shiru na dan sakanni ne Sadik ya cewa Hajiya "Ni abin da nake gani Hajiya klu zauna ke da Ramla ku tsara duk abin da ya dace a siya, inyaso sai mu sanya lokaci daya muje mu siyo komi a zo a hade su guri daya, ni nafi bukatar a kai komi rana daya kar a tsaya wani rabe-rabe inyaso da ankai ranar biki kawai za a dawo a sanar dani." Hajiya ta girgiza kai ta ce masa "Ni kaina na fika bukatar hakan domin akwai halin yin hakan, amma abin da nake hange, an sanar da lyayen yarinyar domin gani nake zasu ce anyi gaggawa, da an bari sai nan da wata biyu, kaga idan ya cika na uku sai ya zama shine na bikin ko kuwa?" 16 AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2 Sadik ya girgiza kai yace mata "Haba Hajiya na yi maki bayanin nan fa tun farko, sai da na jaddadawa yarinyar tace babu matsala, kuma na je mun gana da mahaifinta ya ce ai ba komi, su albarka kawai suke bukata, shiyasa na ce miki aje kawai a tambayo sanda za a kai kudi, da an kai sai kuma batun kai kaya shikenan ni gaskiya ba zan juri har wata uku ina zuwa gidansu yarinya da sunan soyayya kawai ba. Dariya Hajiya ta yi sannan ta ce, "Ikon Allah, Ashe dama matar ce bata zo ba, shiyasa kake gudun zancem aure, yanzu da matar tazo gashinan har kafi kowa zakwadi da zumudi, to ai shikenan Allah ya sanya alkhairi tunda Iyayenta sun amince ai magana ta kare." Bai kara ce mata komi ba illa mikewa kawai da ya yi yana fadin "Ina sauraronku zuwa yamma don na san me ake ciki." Yana fadin haka ya fice, ita kuwa Hajiya Saude binsa kawai ta yi da kallo cike da jin dadi cikin ranta, tana kuma godewa 17. AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE-2 Allah da ya nuna mata wannan rana da dan nata ke zumudin aurensa har yana nema ya fita. Maganar aurc kam ta kankama domin an kammala komi na aure, an kuma saka ranar aurc uzuwa yanzu saura sati guuda don haka kowanne bangare suna cikin hidima Amarya kan ta sha gyara ta fito fes sai daukar ido take yi, ga kamshi na binta ta ko ina, nera kam ta yi kuka domin Sadik ya yiwa Mero 6arin kudi kamar debo su kawai yake yi ba nemansu yake yi ba. Hakan ba karamin batawa Salama rai ya yi ba, a fuskarta ne kawai take yake ake ganin kamar tafi kowa murna, amma cikin ranta baki ne kirin domin ji take yi kamar ta maida auren Sadik kanta ba Mero ba, a ganinta itace tafi cancanta. тв1 dirAcikin taron bikin kuwa duk inda Mero ta saka kafa Salama ke bibiyarta har lokacin da za a kaita dakinta ob srrunGY.BWUS Fes ta fito cikin wani swiss lace pink mai zanen manyan flawers blue, duwatsun jiki suma kalolin. r iio ibeb nij sb 18 AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ 2 Ya matukar amsarta dinkin da aka yi masa tamkar dama a jikin ta aka halicce shi, ya bi jikinta lif, tun daga mayafinta kuma har yarin kunnenta da sarka zuwa abin hannu, da takalmi da jaka duka kalar Blue ta sanya, hakan ya sake fiddo da kyawunta karara. Tana zaune bisa kujera ta lulluße kanta da mayafi, Salama na kusa da ita tana gaya mata wasu maganganu a kunnenta wanda ba kowa ke iya jinsu ba. A haka Baba kande ta shigo ta same su tana fadin "Ke Mero ke ake jira tun dazu anzo daukar amarya mutane duk suna waje suna dakon fitowarki." Da sauri Salama ta amshe cike da 99 fara'a "To Baba bari mu fito yanzu. Ta kamo hannun Mero tana fadin "Та so muje amarya kar a gaji da jiranki. Ta shi kawai ta yi ta bita ba tare da tace komi ba, hawaye na bin idanuwan Mero tana waiwayen mahaifiyarta haka ta fito daga mahaifarta. 19 AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNА СЕ-2 Har suka isa cikin dakinta Salama ce dai ke rike da ita, sai da ta zaunar da ita bisa gadonta sannan itama ta zauna kusa da ita. Irin gadon da taga an kawo Mero a matsayin gidan aurenta, ya tsaya mata a rai, domin gidane wanda zaka iya mantawa da talauci idan har ka shigeshi. Duk wadanda suka rako amarya sunyi mata fatan alkairi sun tafi, illa Salama da wasu daga kawayenta da suke jiran ayi sayen baki suma su kama hanyarsu. Ba dadewa angwaye suka bayyana a gidan, Auwalu ne a hannun damar ango sannan wasu daga abokansa don haka bayan sunyi masu sallama sun gaggaisa. Sannan Auwalu ya fara da fadin "Alhamdulillah yau Allah ya kawo mu auren Sadik da Maryam, masoyan da suka kafa tarihi a wannan yankin namu, don haka muna musu yi musu addu'a Allah ya basu zaman lafiya da kuma kazantar daki." Dukkansu suka yi dariya sannan suka amsa masa da "Amin." 20 AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2 Auwalu ya sake duban ango cike da zolaya yace masa "Ango ai ka bude kan amaryar taka don muyi sauri mu tafi mu baku waje ko? Don na tabbatar yanzu kafi kowa so mu tafi mu baku gidanku." Dukkansu suka sake dariya, Sadik da sauri yace masa "Wallahi abokina kamar ka shiga zuciyata dama zaku kyale siyan bakin nan na sayi abina da kaina da yafi. Mamaki ya cika Auwalu, da sauri ya ce masa "Af haka kace" To shikenan bari mu tashi mu barku tunda korarmu kake yi.' Zai yunkura ya ta shi daga inda yake zaune, da sauri Salama ta ce masa 'Haba dai ka zauna mana Auwalu a karasa ai shima zolayarka yake yi kawai." Auwalu ya yi murmushi sannan yace "Ai nima na san zolayar tawa yakeyi. Ya dauko kudin siyan bakin ya mikawa Salama yana fadin "Ga kudin sayen bakin ki nan, da sauri ta amshe bandir din kudin, amma ranta yana tafarfasa da takaici. 21 AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2 Ta daga kudin ta juya sannan ta ce, "То mun amince ango ya bude fuskar amaryarsa. Gaba daya suka yi dariya, shi kuma Sadik cike da zakwadi ya hau cire mayafin kan Mero a hankali, tana dago idanuwanta suka yi ido hudu, sannan suka sakarwa junansu murmushi. Auwalu cike da fara'a yace "To amarya ga amanar ango nan, kaima ango haka, mu zamu wuce yanzu don mu barku ku sake don nasan zuwa yanzu kana kan gwiwa tamkar mai nakuda. Sadik ya yi dariya ya ce masa "Kai dai baka rabo da zolaya, amma ba komi zan rama ne. Suka yi sallama da su ya tafi ya rakasu, ita kuwa Salama matsawa ta yi kunnen Mero ta sake yi mata huduba, sannan daga karshe ta ce mata "Kar fa ki 6ata mana shirinmu." Mero ta girgiza kai sannan ta ce mata ina sane kawata kar ki ji komi. Sai da ta jiyo karar horn din mota sannan ta fito da gudu ta same su suna jiranta. 22 AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE 2 :Sai da suka fice aka rufe kofar gidan sannan ya koma cikin gidansa cike da zumudin mallakar Mairamunsa a matsayin matarsa ta sunna. id:Kai tsaye dakin Mero ya nufa amma abin mamaki sai ya ga kofar dakin nata а rufe, ya murda cikin kwarin gwiwa amma sam kofa bata bude ba, hankalinsa ya ta shi ya hau buga kofa yana kiran Mero, amma shiru. fsRaiCikin daga murya ya ce "Mero ya ka yi kofar ta rufe da ke? Ki jeho mukullin ta taga na budeki." 110 oav Shuru dai ba wani motsii, ya ci gaba da kiranta yana fadin "Ko bandaki kika shige ne Mero? Har tsawon mintuna amma shiru babu ko motsi, wannan abu ya matukar daurewa Sadik kai, don haka ya hau buga kofar da karfi yana kiran sunanta amma san babu alamarta. Cike da dacin rai ya hau za gayawa falo yana faman huci, ya dunkule hannunsa ya 23 AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE2 doki dayan yana furzar da hucin bacin rai da takaici. A haka har ya gaji ya kwanta bisa doguwar kujera cike da dacin rai, sakamakon gajiyar da ke jikinsa ne bacco ya dauke shi а nan, haka ya kwana cikin bakin ciki da taraddadin rashin sanin dalilin faruwar hakan. **** Alhaji Sadik yana dai zaune bisa kan gadon Asibitin yana fuskantar Alhaji Aliyu, ya na kaiwa nan ya yi ajiyar zuciya sannan ya יי rufe idanuwansa ya sake budewa kana yace Haka nayi aurena na farko babu bincike na dai biyewa son zuciyata ne kawai da kyale kyale sannan kuma na sake samun goyon baya daga gidanmu wadanda ke fifita kyau da יי wayewa fiye da komi a wajen aure.' Alhaji Aliyu ya girgiza kai cike da jmami yace masa "Wannan shine kuskuren ka na farko Alhaji Sadik." 24 AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2 Ya sake yin ajiyar zuciya sannan yaci gaba da daga inda ya tsaya. **** Washegari da safe Alhaji Sadik ya gama shiryawa tsaf ya fito falo ya zauna cike da jimami da takaicin abin da Mero ta aikata masa jiya. Motsin tahowarta ya dinga jiyowa daga dakinta, ya sanya ido bisa hanyar, ita din ce kuwa, a shirye tsaf cikin wasu engllish wears da suka amsheta matuka, ta yi matukar kyau. Da sauri ya dauke kansa daga inda take ya koma kallon film din da yake kunne a falon. Kusa da shi ta zo ta zauna cike da fara'a tana gaisheshi. Harararta kawai yayi ya kawar da kansa gefe ya ci gaba da kallon da yake yi. Ta rusina har kasa tana sake gaishe shi, cike da takaici ya sake kallonta, sake kawar da kansa gefe yace mata "Yanzu ke dan Allah abin da kika yi jiya kin kyauta kenan?" 25 AWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE- 2 Ta sunkuyar da kai kasa ba tare da tacc masa komi ba, ya sake tambayarta cike da damuwa "Kiyi magana nace kin kyauta kenan haka ya kamata kiyi ko?" Ta girgiza kai ba tare da tace komi ba. Ya sake watso mata tambayar tya ce "To me ya sa kima aikata abin da kika san bai dace ki aikata ba?" Cikin muryar neman afuwa ta ce, masa "Ka yi hakuri ba zan kuma ba Insha Allah kuskure ne nayi." Ya girgiza kai gami da kwaße baki yace mata "Allah yasa abin da kika fada gaskiyane." Ya duba agogonsa sannan yace "Ai ya kamata mu karya domin ni da wuri nake son na fita sabida ana sauke kaya yau." Mero ta marairaice murya ta ce, masa "Da wuri kuma Alhaji? Ko hutun aure ba za ka yi ba? Duk ango yana hutawa a gidansa amma banda kai." Cike da mamaki ya dubeta yace mata. "Mero kenan, kina bukatata ne a cikin gidan 26 6 AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2 na? ki kyaleni na tafi gurin aikina mana sai kifi sakewa a gidanki ko? Tunda bakya bukatata a kusa da ke." Girgiza kai ta yi sannan cikin shagwaба tace masa "Wallahi ba haka bane, don Allah ka yi hakuri ka zauna mu wuni tarc." Bai tsaya sauraronta ba kawai ya mike ya nufi kan teburin cin abinci. Ta bi shi a baya tana isa ta hau zuba masa karin kumallon sai da ta kammala ta bashi sannan ta zuba nata ta zauna ta fara ci. A tsanake yake dubanta cike da kulawa ya ce mata "Amarya kinsha kamshi kinyi kyau matuka sai daukar ido kike yi sai dai rowar kyan naki kike yi." Dago kanta ta yi suka hada ido ta sakar masa murmushi tana fadin "Kaima aika zuba kyau tamkar wani Dawisu." Ya saki murmushi da alamun magannarta ta faranta masa ya ce mata "Dagaske kike?" 99 Ta girgiza kai tana fadin "Sosai ma." 27 AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE 2 Alhaji Sadik yace mata "Amma kike nema ki kawo mana cikas a farin cikinmii da cikar burinmu." Ta sunkuyar da kanta a kasa ta ce "Ai ba zan kuma ba." Cike da fara'a ya ce mata "Ko ke fa, banda abinki kin taba ganin a wannan zamanin mace na gudun mijinta? Musamman 99 wadan da suka yi auren soyayya. Murmushi ta yi ta sunkuyar da kanta, kar ka damu zan baka mamaki." a Wata dariya ce ta subuce masa mai bayyanar da jin dadinsa da farin cikinsa a fili, daidai lokacin da ya ke mikewa daga kan teburin yana kallonta "Allah yasa da gaske kike yi.' Murmushi kawai ta yi ta ce masa "Zaka tabbatar da gaske nake yi idan na shayar da kai mamakin." Cike da

Chapter 1 of 5