zai kwanta ba."
Inna Laure ce ta sake binta ta riketa
tana fadin "Haba Sadiya ina yi miki
magana kina sake zabura? Banda abinki
duk wanda ya zagi uwar wani ai tasa ya
zaga, daga gani ai kinsan babu tarbiyya,
wuce mu tafi daki."
Ba ta ko musa ba ta tabi bayanta
suka nufi dakin Sadiya. Ba ta bari sun
shiga ba ta biyo bayansu da muciya a
hannu tana faman huci tana fadin "Aikin
banza, har Kura ce zata ce da Kare maye?
Za a samo mai tarbiyyar dai a cikin mu.
A fusace Sadiya ta juyo tana fadin
"Inna kina jinta fa abin da take gaya miki, don Allah ki barni nai mata jini da
majina a jikinta kinga sai ta shiga taita yinta."
1.07
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CЕ
Da sauri Innar tata ta sake riko
hannunta tana fadin "Na dai gaya miki ki
shige muje ďaki ko?"
Ran Sadiya a 6ace domin ba haka
ta so ba. Za ta mazgawa Lami rodin dake
hannunta da sauri Lami ta kaucewa
Rodin dan haka bai sameta ba sai kawai
ya yi tsalle ya tadda Mero ya sameta
gefen jikinta.
a
Da sauri ta kalli inda rodin ya
sameta, a fusace ta ce, "Wallahi ba zan
yarda ba, haka kawai ni ba da ni ake fada
ba a nemi a cutar dani?" da sauri ta nufi
inda Sadiya ke tsaye, itama Lami ta
nufeta gami da damko wuyanta, nan take
kokawa ta ta kufce a tsakaninsu su duka
ukun.
Da kyar Inna Laure ta kwato
Sadiya daga' hannunsu, tana faman janta
108
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
tana dagewa sabida taurin kai, duk kuwa
da har su biyu suka hadar mata.
A fusace Inna Laure ke fadin
"Yanzu Sadiya abin da na gaya miki ba
zakiji ba kenan? To'shikenan bari na yi
tafiyata tunda ban isa na fadi ki ji ba."
Lami cikin huci da mai da
numfashii ta ce, "kyaleta mana in ba
tsoro ba walląhi muyi mata wanka da jini
in yaso yau duk mu kwana a bayan
kanta."
Meroviceta amshe da fadin
"Ganemin hanya yar uwa wallahi ni
yanzu zan iya kaiwa dare ina wannan
fadan kuma ban gaji ba, ke idan ma
kwana za ayi ana yi Bissimillah dan
halak ka fasa."
Ran Sadiyayya cika da daci
sakamakon maganganun da suke gaya
mata dan haka ta hau kokarin kwace
109
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
rikon da Innar ta yi mata tana fadin "Don
Allah Inna bari na nunawa wadannan
Kananan 'yan iskan basu isa komi ba a
gurina."
Ita kuwa Innar bata saurareta ba,
illa janta da take kara yi har suka isa
kofar dakinta tana fadin "Ba komi muje
cikin dakin ai da sauran lokaci da
kwanaki a duniya, kada ki damu in sun
san wata ai basu san wata ba.
Da haka har suka shige cikin dakin
suka barsu suna faman hayaniyarsu.
Bayan sun shiga dakin ne Inna ta
hau azalzalarta da ta sallameta ta tafi don
kar azo a tadda ana fada ace ita ce, ta
haddasa.
Da sauri ta dauko kudi ta mika
mata, ta kirga, sannan ta dago ta kalli
'yar cike da tuhuma "Ya na ga haka
110
ALAWIYYA WADA ISA 'YAR ALJANNA CE
kuma Sadiya? Kin sani fa na riga na yi
lissafin abin da zamuyi da kudinnan.
Sadiya ta kalleta kawai tana fadin:
"To Inna abin da na samu kenan, dama
yanzu niyyata naje dakinsa na samo miki
wasu, shine wannan "yar bakin ciki ta
hanani shiga dakin."
Da sauri ta mike ta saka kudin
cikin riga tana fadin "Ba komi Sadiya
bari na tafi ke dai ki kara hi,ma kuma ki
daina bari ana fada dake domin garin
neman gira sai azo ana rasa ido."
Tana kammala fadin haka ta fice da
sauri ba tare da kowa ya a cikinsu ya ga:
fitarta ba, domin da suka gaji da
maganganunsu babu wanda ya tanka
musu, sai kowacce ta nufi shashenta iАg
111
****
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
Tafe yake a kan titin wanda ke
kunshe da motoci a gefe sun cunkushe
titin, haka Alhaji Sadik ya dinga ratsa
motocin cikin kunar rai da tashin
hankali, sambatu yake yi amma shi kansa
in akace ya maimaita abin da yake fadi
ba zai iya ba.
Bai san inda ya dosa ba, shi dai
kawai yana tafiya ne, tun yana ratsa cikin
gari har yaje ya riski daji, ga kuma wani
gudu da yake yi ba na wasa ba, yana
cikin gudun ne sitiyari ya kwace masa ya
je ya doki Bishiya kansa ya bugu, nan
take ya suma.
A kan hanyarsa ta zuwa kauyensu
ne ya kula da wata mota a lalace daga
gani hatsari ne ya sameta musamman
yanda ta bugi bishiyar nan gabanta ya yi
kwatsa-kwatsa.
112
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNACEA
T6 Hardzai wuce sai wata zuciyarstay
gargadeshi da cewar bai halatta gareshi
ya wuce wannan gurin bai je ya dubaikos)
akwai wani mahalukida cikin motar nan
basg don hakayav samu nguri yamajiyels
motarsa ya gangara inda, motar takesd
aikuwa yana isa ya leka Motar sai gas
mutum/a sume jini ya wanke masa fuska,
nan ntakes yarhau kokarin ceto rayuwar
Alhaji Sadik. EN sb nids ub sb usyd ism
Sai da ya /kwantars dashioa bayänA
motarsa sannan ya rufe motar ya shiğa ya
tayare yanjuya kan Motar zuwasAsibitid
yaria naddu'ar Allahyasvbawazwannansa
mutumins lafiya,ryasas yanandairsauranls
numfashi. nitidiaA
SBaiv bar Asibitin banesaig da ya
tabbatar an bawa Alhaji Sadik duk watas
kulawa da ta dace a bashi.cHar ya farfadole
daga suman da ya yi amma kumä yasgig
113
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
gaba da bacci yana fidda numfashi kamar
na kowa sakamakon ruwan allurai da akai
ta bashi.
Sai da ya tambayi likita lokacin da
ake sanya ran zai ya farkawa daga
baccin, ya gaya masa sannan ya juya ya
tafi.
Gida ya koma ya sanar da Mama
sannan ya umarceta da ta shirya abinci
mai kyau da duk abin da za a bukata a
Asibitin domin ya kaiwa Alhaji Sadik.
Haka kuwa aka yi, duk abin da za a
bukata ta hada masa, sai da ya fuskanci
sauran kusan awa guda daga lokacin da
aka bashi sannan ya kama hanyar tafiya
Asibitin.
A gabansa Alhaji Sadik ya farka
amma zafin buguwa da ke kansa ta hana
shi yin kwakkwaran motsi, magana ma ta
gagara illa kallo kawai da idanuwa, don
114
ALAWIYYA WADA ISA. YAR ALJANNA CE
haka basu iya cewa komi ba,, illa kallon
kallo da suke yi, sai Alhaji Aliyu ne ke ce
sannu, shi kuma ya amsa da kansa wanda
shi kansa baya iya bude shi sosai.
Da ya fuskanci Alhaji na jin jiki sai
ya kira Likita ya shawarceshi da ya yi
masa allurar bacci, ko ya samu saukin jin
zogin ciwon, haka kuwa aka yi sai da ya
tabbatar bacci ya dauke shi sannan ya
kyaleshi ya tafi daga asibitin tare da
nema alfarmar a dinga kula da shi kafin
ya dawo.
Kwanansa üku a Asibitin ya samu
sauki sakamakon kulawa ta musamman
da yake samu, har ana iya yin hira mai
tsawo da shi, sannan yana iya tashi ya je
har badaki ba tare da an kai shi ba.
Ranar da ya cika kwana hudu ne
Alhaji Aliyu ya shiga Asibitin. Zaune ya
taddashi bisa kan gadon ga goshinsa
115
ALAWIYYA WADA ISA 'YAR ALJANNA CE
daure da bandeji, ya saki dariyar jindadi
yana fadin "Masha Allahu, Alhaji naji
dadin ganinka a yau domin sauki ya sake
samuwa kwarai.
Ya isa ya zauna kusa da shi yana
dubansa cike da jin dadi.
Alhaji Sadik ya maida masa da
martanin murmushinsa sannan yace masa
"Alhaji ina godiya matuka, Allah ya saka
maka da alkairi, ka taimaki rayuwata ka
cetoni daga halaka domin ba don Allah
ya kawoka ba zan iya mutuwa, Allah ya
saka maka da Aljannar firdausi.
Alhaji ya sake fadada murmushinsa
ya ce masa "Ai ba komi Alhaji wanda ya
taimaki wani shima Allah zai taimakeshi,
ni kaina ina cike da farin ciki sakamakon
samun saukinka, sai dai abin da yafi
damuna bai wuce rashin sanin inda
Iyalinka suke ba ballantana na sanar da
116
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CЕ
su halin da kake ciki, kuma su san inda
kake su zo su gana da kai."
Bai iya ce masa komi ba illa
hawaye da ya fara kara kaina a fuskarsa,
hankalin Alhajji Aliyu ya yi matukar
tashi nan take ya hau fadin "Subhanallah
Alhaji ya kake hawaye? Me ke faruwa?
Ko suma iyalin naka sun shiga halin da
ka shiga ne? kake tunanin su?
Hankalina ya tashi matuka, domin
kukan babban mutum bashi da kyau."
A hankali ya girgiza kai yana fadin
"Ko daya Alhaji ban rasa kowa daga
Iyalina ba, sai dai babban rashi na zama
lafiya da kwanciyar hankali da nayi a
cikin gidana, gidan ya zama tamkar
sansanin yaki, babu wata rana ko wani
lokaci da zan iya warewa nace ana zaune
lafiya a gidana, hatta ranar da wannan
tsautsayin zai sameni ina bacci da safe
117
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNAА СЕ
nake mafarkin gidana na ci da wuta,
jama'a sun taru suna zuba ruwa amma
kamar suna kara mata fetur, kowa ya
kasa kasheta."
Ya ja dogon numfashi gami da
goge hawayen da ke zubo masa.
Alamun damuwa ya bayyana a idon
Alhaji Aliyu cike da kulawa yace masa
"Assha, Alhaji lallai kana cikin musiba
da tashin hankali, rashin samun
kwanciyar hankali daga Iyali illa ce
babba ga namiji domin hatta tattalin
arzikinsa karyewa yake yi, Alhaji ya aka
yi haka ta faru?"
Alhajin ya dago kansa ya dubi
Alhaji Aliyu sannan yace masa "Wato
Alhaji lamarin ya samo asali ne tun daga
farkon neman aurena, wani abin ya faru a
idona wani abin kuma labari ne aka
bani."
118
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
LABARIN ALHAJI SADIK
Tsaye suke a jikin motarsa shi da
babban amininsa Auwalu suna hirar
yaushe gamo kasancewar Alhaji Sadik
din ya yi tafiya ta tsawon wata guda.
Fuskokinsu cike da fara'a, Auwalu
ne ke zolayar Sadik din da fadin "Wato
Alhaji wannan kasuwancin na fita China
dinnan ya karbeka matuka, sai. wani
kyalli kake kana sheki daga ganinka nera
ta riga ta zauna, ka shiga sahun matasan
miloniyoyi, mu kuwa ka barmu muna ta
bin Inuwa har sai dare ya yi sannan mu
nemi makwanci.
Sadik ya yi dariya cike da farin ciki
ya ce masa "Gaskiya dai Alhamdulillahi
sai godiyar Ubangiji kam, an samu rufin
asiri."
119
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ
1
'a
ar
ak
ge
haj
Ss
wal
abt
rzil
ih
Alh
All
farl
ido
bal
Auwalu ya dubeshi da alamuu
tambaya a fuskarsa ya ce masa "Rufin
asiri kawai? Ai wannan ya wuce a tsaya a
rufin asiri, har da arziki ka duba fa kaga
abin da ka mallaka a lokaci daya, ya
kamata in an kai matsayi a yarda an kai."
Sadik ya yi dariya yace "Gaskiya
ne to Allah ya wadata mu gaba daya ya
bamu yanda zamu iya."
Auwalu ya amshe da "Amin"
sannan ya dora da fadin "Yanzu abin da
ya rage maka kawai ka samo abokiyar
zama sai komai ya kammala cika."
Sadik ya kalleshi cikin mamaki
yace masa "Kai ma ka bi layi kenan,
kullum zancen Hajiya kwaya daya ya
2, kamata nayi aure.
Auwalu ya yi murmushi yace masa
"To ai abin da ya kamace ka kenan,
shekarunka sun kai kuma halinka ya kai
120
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
ka rike mace ko guda ce ma ballanta
daya."
Da sauri Sadik ya bude baki yana
fadin "Ko guda nawa? Na samu na aura,
dayar ma ai abin ba akudi yake ba?
Auwalu ya yi dariya sannan yace
"Abokina ka tsorata kenan, to yanzu me
ka shirya akan maganar auren?"
Sadik ya gyara tsayuwarsa sannan
yace " Ni ban shirya komi ba wallahi,
shirina abin da na mallaka a hannuna
wanda ni aka ce ga auren to zan kashe su
ba tare da jin komi ba."
Auwalu ya yi dariya sannan yace
"Kana nufin ko yarinyar da zaka aura
baka tana da ba?" ya sake yin dariya yace
masa "A ina fa na tanada? Ni fa babu
abin da ke gabana illa neman kudi, ina
ma na samu damar da har zan zauna na
121
F
ALAWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE
kalli mace balle har na tantance wacce ta
dace dani?"
Auwalu ya kwashe da dariya har da
hka kafa sannan yace masa "Gaskiya
abokina baka da dama to banda abinka
zaka auri kudi ne?"
Sadik yakatseshi da fadin ga
mutumina yanzu dai ka bar wannan
maganar in dai kanada wata da kake
ganin ta dace dani mai dan dama-dama
kawai ka hadani da ita, in naga ta yi mini
sai kawai mu daidaita."
Auwalu ya ce masa "To banda
abinka ka taba ganin wani ya zabawa
wani mata?"
Sadik yace "Ai ba kaine zaka zaba
mini ba, kai mai samowa ne idan ka samu
sai ka kaini mu gana idan tai min
shikenan in Allah ya yi sai kaga ta zama
matata ko?"
122
ALAWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE
Auwalu ya amsa da cewa "Gaskiya
ne abokina ai kuwa akwai wata yarinya
da nake gani zaku dace domin yarinyar
matar manya ce irinku don komi ya ji.""
Da sauri Sadik ya tambayeshi
"Allah Abokina?"
Auwalu ya yi dariya ya nufi
kunnensa ya yi masa rada, gaba daya
suka yi dariya suka tafa, sannan suka nufi
cikin motar suka shiga, Sadik ya tada
motar suka bar gurin.
To sun sanya lokaci zuwa gurin
wannan yarinya da Auwalu ya
kwadaitawa Sadik ita, don haka suka yi
sallama da juna suka yi alkawarin sai
wannan rana za su sake haduwa.
A kofar gidansu ya saukeshi ya yi
masa ihsani da ya saba kana ya ja
motarsa ya nufi inda ya yi niyyar zuwa.
123
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
****
Yammaci ne mai cike da ni'ima
wanda ke ba da iska mai sanyi da ratsa
jiki. A kofar gidansu Auwalun ya tsaya
ko fitowa daga motar bai yi ba, hatta
'yan majalisarsu ma hannu kawai ya daga
musu, da sauri Auwalun ya bude ya shiga
shi kuma ya ja motar suka kama hanya.
A kofar gidansu yarinyar suka
tsaya da motar, Auwalu ne ya fara fitowa
shi kuma sai da ya kashe motar sannan ya
fito ya zo kusa da Auwalun suka jeru
jikin motar suna kallon kofar gidansu
yarinyar. Suna nan a tsaye wani yaro
yazo zai wuce, Auwalu ya yi sauri ya
tsaida shi ya aika shi domin ya kirawo
musu ita.
Bayan 'yan mintuna kalilan yaron
ya fito ya sake nufo inda suke yace musu
"Wai ance tana zuwa" da sauri Auiwalun
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СЕ
ya ce masa "Yauwa yaro mun gode kaji,
ya sanya hannu a aljihunsa ya dauko
Naira dari ya mikawa yaron yana fadin
"To ga wannan ka kaiwa Mamanka ka ji
dan albarka."
Cike da murna ya amsa yana duba
kudin sabuwa ce kal, yana fadin
"Nagode Allah ya saka da alheri."
Sannan ya falla da gudu ya nufi gida.
Dai dai lokacin da Mero take fitowa daga
gidan tana takawa a hankali, ta yi
kwalliya daidai gwargwado.
Kai tsaye inda suke tsaye ta nufo
tana isowa gurinsu ta dan risina sannan ta
יי ce, "Barkanku da zuwa.'
Cike da fara'a Auwalu ya amshe da
Maryama, Maryama, barkanki da yamma
gamu yau a gidanku ba zato ko?"
125
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ
Murmushi kawai ta yi shi kuwa
gogan idanuwansa na kanta yanayi mata
kallon nazari.
Auwalu ne yaci gaba da fadin
"Maryam na san zaki yi mamakin ganin
mu a daidai wannan lokaci, to kamar
yanda kika sani ni Jakadan alheri ne, ga
abokina nan dan uwana kuma aminina na
kawo miki dafatan zaki karbeshi
hannuwa bibbiyu."
Da sauri ta daga idanuwanta ta
kalli Sadik, nan take suka yi ido hudu,
murmushi ya sakar mata, ita kuwa
kunyace ta kamata ta yi saurin sunkuyar
da kanta,shi kuwa gogan sam idonsa ko
motsawa bai yi ba domin shi kansa ya
tabbatar da cewa Maryam din tasa ta yi.
Auwalu ne ya ya fito shi da hannu
cike da zolaya yafe fadin "To kai
Abokina na gama nawa aikin bari na
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
zagaya baya na barku ku tattauna don kar
naji sirrinku."
Dariya ya sakar masa gami da
harara yace masa "To dama ya za'ayi mu
bari ka ji sirrin mu ka kwantar da
hankalinka tunda na san inda take ai ba
sai ana wani labe labe ba sanda zanzo ma
kana ina."
Aljihunsa ya sanya hannu ya dauko
kudi masu yawa ya mikawa Mero ya ce
mata "Ki rike wannan kinga yanzu
magariba ta kusa, idan Allah ya kaimu
gobe da dare zan dawo Insha Allahu."
Da sauri ta gyada kai alamun ba za
ta karba ba, Auwalu ne ya tirsasata ta
karba, sannan suka yi sallama da juna ta
juya ta nufi gida su kuma suka tashi
motarsu, a soro ta labe tana lekensu sai
da ta daina ganin motar sannan ta shiga
gida.
127
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
Shi kuwa Auwalu zolayar Sadik ya
hàu yi yana fadin "Abokina gaskiya kai
mishan ne, kai fa kace mini baka iya ko
kallon mata, ka sanyani nemo maka mata
amma yanzu daga ganin 'yar mutane ka
rude ko maganar arziki ka kasa yi, har da
wani cewa gobe da daddare zaka koma."
Sadik ya kwashe da dariya yace
masa "Haba Abokina kai dai tunda ka
cika aikinka ai shi kenan, yarinyar ce ai
ta yi, shi yasa ka ga na kasa ce mata komi
kallonta kawai nake yi don ma talauci ya
yai mata cikar tana jikuwa, da kudi zata
zama babbar yarinya."
Dariya Auwalu ya sake yi yace "Ai
mu zama damu yana da amfani matuka
domin idanuwanmu suna zagayawa ko
ina a cikin garin nan lungu da sako." Ya
ci gaba da zolayarsa.
128
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
"Abokina kawai ka ce ciniki ya
fada." Auwalu ya fadi yana dariya. Sadik
ya yi saurin amshewa "Mai kyau ma, ai
kawai sai shirin aure, kana ganin yarinya
ta hada komi da komi babu makusa, ai
yanzu ina sauke ka gida na nufa na sanar
da su labari mai dadi, musamman
Hajiya."
Da haka sukaci gaba da tattaunawa
har ya isa gidansu Auwalu ya saukeshi ya
karawa Motarsa wuta ya nufi hanyar
gidan Hajiya kai tsaye.
Anan zan dakata a cikin littafi na
daya sai mu nemi littafi na biyu domin
jin yadda zata kaya.
Taku har kullum, mai debe muku kewa
Alawiyya Wada Isa.
129
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
2
Π
TALLA! TALLA!! TALLA!!
"Abban Ilham yau ina zuwa ne da
sanyin safiya haka.?"
Ya dubi Agogon Bangon dake dakin
tara da 'yan mintuna. "Me ki ka ga ni.?"
Shi ma ya tambaye ta.
"Na ga ne ka ci ado kamar wadda za
ka fita wani taro na musamman."
"An ce ba kullum ake kwana a gado
ba, kuma haka ne wadannan masana fadin
magana sun fadi gaskiya, yau kai ne a can
وو gobe kai ne a nan.
1
130
ALAWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE
Ta bishi da kallon mamaki domin
amsar tasa bata fuskanci ainihin abin da take
son ji ba."
"Uhm sai an karya min harshe kuma,
ni dai tambaya na yi amsa nake bukata
kawai ina zuwa yau da safe.?"
"Neman aiki.?"
Ta jima ta na kallon sa da mutukar
mamaki.
"Neman Aiki.?"
Ta fada da mamakinta.?"
"Zan je neman aiki ne saboda
al'amura sun fara yawa, duniya ta na da
girma, haka hanyoyin samu na da fadi, babu
mamaki idan can ta ki ka koma can, fadi ta
shi dai dama bawa bai isa ya ce yafi karfin
131
ALAWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE
yi ba, in har ina busar numfashi. Zan je ko
Allah zai sa a dacс." יי
"Me ne ka rasa.?"
"Me ne na samu.?"
Ya dawo mata da tambayar ta kai
tsaye. Ita kuma ta saka masa ido cikin
mutukar mamakin kalamansa."
"Ban samu komai ba, Hafsa ídan ki ka
auna cewar idan Allah ya ba mu aron rai
gobe ba irin yau ba ce jibi ba rin gobe bace
haka gata citta, don haka ya zama dole na
shiga duniyar neman abin rufin asiri
abubuwa sun cunkushewa rayuwa ta, na ga
alamar baki san da haka ba."
132
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ
Ta mike daga in da take ta dawo kusa
da shi "Mai yasa kake yanke kauna da
daukaka ta."
Ya zuba mata ido kafin ya ce komai
sannan ya gyara murya ya cc, "Daukaka
lokaci ne da ita, ki na nan za ta zo ta
turmeshi. ki, kuma kada ki manta ba a
rayuwa a dakushe."
"Kamar yaya.?"
"Da ni na ke shuhura, yanzu kuma ke
ce, gobe ba fa ba ke bace, to ya za mu yi da
wannan rayuwa, lokacin da duniya take yi
da kai, lokacin jama'a ke yi da kai. In kin ji
an ce duniya. To ba duniyar ba ce jama'ar
cikinta ne. Ranar da jama'ar suka koma kan
wata, kaka ke nan.?"
133
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
"Amma dai ka san duk lalacewar dan
zaki yafi karfin kadangare, ko da a ce ban
da wani abu da zan tabuka mahaifina mai
kudi ne, ba kuma zai hanani duk abin da
nake bukata ba."
Ya dora hannuwansa a kai, daga bisa
ni wani murmushi ya kubuce masa "Da a сe
zan fadi na mutu. Wannan shi ne abu mafi
soyuwa a cikin zuciyar iyayen ki, ni kuwa
don me zai sa na zauna ina barautar abin da
za su ba ni, wadanda ko kauna ta a raye ba
sa su. Hafsa ki rike daukakar ki, ni ma zan
je na nemi abin da zai rufamin asiri, daga
rana irin ta yau na rabu da harkar rubutu, har
Abada kuma ina mai nadamar kasancewa ta
marubuci.
134
ALAWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE
Tirkashi, in ba ka yi ba ni guri. Wani
Kasaitaccen labari, mai sa ka zubar kwalla,
mai fauke da wata sha'umar soyayya,
wannan labarin ya kasaitu ya samu ingancin
aiki, sabon salo a cikin rubuce rubucen
zamani, ka da ka saki a baka labarin wannan
Kasaitaccen littafi mai suna.
BA ALJANNA BACE.
Matashiyar marubuciyar nan 'yar uwa ga
Hadiza Adam shi shitu wato Rabi'atu wacce
ta rubuto littafaina kamar haka
BAKIN JINI NА.
TAKAICINA FARIN CIKINA.
MURAIDIN RAINA
DAN KUKA,
135
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
ki
d
k
ALKIBLATA
NI CE NA DACE
ZANEN DUTSE TA KARA
YUNKURAWA TA KAWO SABON
LABARI MAI SUNA ...BA ALJANNA
BACE, KI NEMI NAKI A KASUWA DA
ZARAR YA FITO. Kada ku manta da sunan
BA ALJANNA BACE
S
a
136
Littartafan marubucivar:.
SHARRIN ZUCIYA
..RABIN JIKI
GUGUWAR ZAMANI
RUWANIDO
DUNIYAR MAKARANTA CE
YAR ALJANNA CЕ
YarAjanna Ce
ALAWIYYA WADA ISAH
BUGAWA DA YADAWA:
Printing & Publishing by:
SARAUTA PUBLISHERS
A
08034255307
Cover Graphics
Anka-Graphics Fagge 07030319787
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels