gaishesu, suma
cikin fara'a suka amsa mata. Alhaji Aliyu
ne ke tambayar ta "Hanan ince ko kin
karya?" cike da ladabi ta amsa masa
"Baba na karya tun dazu, dama ina sone
na je gidan Baba Alhaji domin yana ta
mita wai har yanzu banje na gaisheshi ya
ganni ba."
37
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
Ya fadada fara'arsa ya ce mata
"Gaskiya ya dace kije Hanan tunda duk
kinga Iyayenki shima datijo ai sai kije ki
bashi nasa hakkin."
Ta mike tana fadin "To Baba nagoe
sai na dawo kenan."
Baban ya amsa da cewa "Si kin
dawo Hanan Allah kiyaye ki gaishe da
Baban, idan zaki dade sai Direba ya
dawo inyaso sai ki sanar da shi sanda
zaki dawo sai ya koma ya daukoki."
A risine ta amsa da cewar "To
Baba nagode." Sannan ta juya ga Maman
tata "Mama na tafi." Ta dago ta dubeta
fuskarta cike da walwala ta ce mata
"Allah ya tsare, ki gaishe da kowa."
Ta amsa da "Amin." Ta juya ta fita.
Unguwar Dukawa suka nufa gidan
Kakanta, sunci sa'a yau babu cunkoson
abin hawa a titi don haka ba dadewa suka
38
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CЕ
isa kofar gidan Direba ya tsaya ta fito da
sauri ta nufi cikin gidan cike da zumudi,
sannu a hankali ta dinga wuce manyan
sorayen gidan tana gaisawa da masu
zama a soron har sai da ta isa cikin gidan
ta riski Kakanninta mata kowacce a
dakinta, sunyi barkwanci yadda suka
saba da hirar yaushe gamo, sannan ta nufi
sashen kakan nata.
Dan farin Dattijo ne, mai alamun
shekaru da yawa fuskarsa da kansa
cunkushe da furfura yana zaune bisa buzu
hannunsa rike da carbi yana lazimi, ga
littafan ilimi nan kewaye das hi, haka duk
kewayen dakin gaba daya littafai ne na
ilimin addini, a hankali ta isa inda yake ta
zauna kusa dashi tana jira ya kammala.
Sai da ya hada laziminsa ya daga
hannu itama ta daga ya yi addu'a suka
shafa a tare sannan ya juyo gareta,
39
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
fara'arsa ta fadada domin yana matukar
kaunar jikar tasa ya ce mata cikin zolaya
"A a bakuwar garin masa yaua gari inji
maki bako? Ai ni nayi fishi dake sai yau
kika ga dammar zuwa ki gaisheni?
Ta yi dariya sannan ta ce, masa
"Haba dan tsoho mai ran karfe ka taба
jin inda miji ya yi fishi da matarsa, ai mu
auranmu auren zobe ne ba rabuwa, kai
min afuwa kasan ina ta Iyayena ne kafin
na zo ga 'yan karo, na tsayane na kwashi
albarkar rayayyu kafin nazo ga wanda ko
yau ko gobe za a iya fasa kukan
mutuwarsa."
Ya saki murmushi wanda ya
kawata fuskarsa sannan ya ce "Amma
wannan yarinyar kin iya shakiuiyanci, to
ai ba wanda ya san gawar fari sai Allah,
niď in da kike gani sai Allah ya barni ya
40
ALAWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE
dauke miki lyayen naki sai kuma kice da
Allah me?"
Cikin barkwanci ta ce, "Ai bani da
ja akan maganarka domin kai ai ran karfe
gareka don haka don kowa ya mutu ya
barka ba mamaki kaga sai kai mana jiran
duniyar."
Dariya ta subuce masa ya ce "Kai
Hanan baki da dama, ina nan kin banni
da kewa wai sai dai na jiki ta waya? To
yaya 'yan samarin naki abokan nawa mai
tsoron aure ko dai har yanzu ni kika
mannewa wannan farar furfurar tawa tana
birgeki kо?
To tunda yanzu kin kammala
karatun naki sai a zo a daura auren zobe,
na san ko ban bayar da sadaki ba babu
komai, in kuma kin matsadubu daya ai ta
isheki, ke sai n agama kamar kin yi tsada
a dubu dayan nan.
41
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
Harararsa ta yi a wasance ta cc,
"Allah ya yi mini tsari da auren tsoho
kamar kai, ka hadani da wadannan
tsofaffin matan naka da ko tafiya da
kafafuwansu basa iya yi, har dama dama
ma kai ka dan fisu kwari kaima din
kadan....."
Karar wayarta cc, ta katse mata
hirar tad ago ta duba don tag a ko wanene
"shinc dai" ta fadi cikin ranta, sannan ta
daga wayar.
Cikin tausasa murya ya ce mata
"Hanan ya kike?" cikin sanyin jiki ta
amsa masa "lafiya kalau nake." Ya danyi
jim sannan ya ce "Dama naje gidanku ne
yanzu don na ganki sai aka ce ai kin taho
gidan Kakanki, shine na sa aka kwatanto
mini inda yake gidan ba 6oyayye bane
وو ban sha wahala ba na samu.
42
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CЕ
Mamaki ya cikata ta dan yi jum, cikin ranta take fadin "Wannan wacce
irin bibiya ce wannan mutumun yake yi
mini ne?"
Shiru din da ya yi ne ya sanya ya
sake cewa "Hello Hanan ba kya jina?" A
kasalance ta masa da cewa "To yanzu
kana kofar gida kenan?"
"Da sauri ya amsa "Eh, hakane. Ta
kwabe baki sannan ta amsa masa "To ba
99 matsala gani nan zuwa.
Tun da ta fito take sakawa tana
tufewa cikin ranta har sai da tai so kofar
gida ta fito waje.
Jingine a jikin motarsa ta hango shi, cikin shigar wani Yadi dan ubansu na
manyan mutane, kalar ruwan kasa ne anyi masa dinkin boda ya yi matukar yi
masa kyau, kamar kullum komai nasa
ruwan kasa ne, har gilashin idonsa,
43
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ
hannunsa rungume a kirjinsa sai daukar
idon duk wanda ya ratsa ta gurin yake yi.
Ya sakar mata murmushi a yayin da su ka
yi ido hudu da shi, ita kanta ya birgeta
matuka domin ko ba komai tana so taga
mutum wayayye kuma dan gayu.
Cike da nutsuwa da takun ta dai
dai ta iske shi a in da yake tsaye. Shi
kuwa idonsa na bisa kanta yana faman
aikin nasa, ji yake kamar ya dauke ta su
tafi a yau, amma ina ya san ba hali. Dan
haka ya maida hankali ga tsantsar
kallonta kana ya fara da cewa.
"Sarauniyar mata kinyi kyau fa, kin
92
zama tauraruwa a cikin taurarin duniya.'
Wani dadi taji cikin ranta domin tana son
namiji mai yabawa mace, ga dukkan
alamu dai Alhaji Sadik yana neman hade
duk halayen da Hanan ke so daga namiji.
44
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
こ
Kanta a sunkuye idanuwanta na
kallon kasa saboda kallonta da yake yi ta
ce masa "Nagode fa."
Ya gyara tsayuwarsa sannan yace
"Hanan gaskiya ke 'yar gata ce, yau kuna
nan gobe kuna can, kina jin dadinki,
inama so na da kaunata ne suka samu
wannan gatan cikin zuciyarki, da na
kasance namijin da yafi kowanne sa'a a
rayuwa, da na zamo dan gatan da babu
kamarsa.
Hanan ina dai miko sakon kokon
barata gareki a ko yaushe, har gobe ina
nan ina dakon irin sakamakon da kokon
nawa zai barato mani, Allah ya say a
kandamo mini babban Alkairi wanda zai
zamo haske a rayuwarmu gaba dayanta.
Tuni kalamansa suka fara kasha
mata jiki, taushin muryarsa kamar bat a
namiji ba, da maganganunsa masu ratsa
45
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
zuciya sun shige ta sosai, tabbas namijin
da ya iya soyayya yana matukar birgeta.
Ba ta iya ce masa komai ba illa "Ya
kamata muje ka gaishe da Baba Malam
ko?"
Hakan ya yi matukar yi masa dadi
cikin ransa, domin ya san da ba amshe
shi ba ko gaisuwarsa ba za a amsa ba
balle har a shigar dashi gurin wanda yake
Uban kowa cikin zuri'ar, don haka babu
ko ja ya bi bayanta suka tafi. Farin
cikinsa ya fadada day a gansu sun shigo
gaba daya, da sauri ya mike yana yi wa
Alhaji Sadik barka da zuwa. Da sauri ya
zube a gabansa yana gaisheshi, cikin
fara'a da murna ya ce, "Af kace kai ka ji
tsoro ka ba da kai, baka san ni ma dan
takara ba ne, ka ke durkusa mini?"
Suka yi dariya gaba dayansu
sannan suka zauna suka gaisa. Cikin
46
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
zuciyar Baba Malam fadı yake "Allah
yasa dai yarinyar nan ta amince da
mutumin nan domin ga dukkan alamu ya
yi kamannin kammala da kyakkyawan
asali, amma in ba a yi sa'a ba Hanan sai
ta gujeshi.
Hanan din ya kalla ya ce mata "Ai
sai kije ki samo masa lemo da dan ruwa
ko?" ta mike ba tare da ta ce, komi bat a
fita.
Baba Malam ya maida hankalinsa
ga Alhaji Sadik yace masa "kai yaro daga
ina kake ne kuma menene sana'arka?
Alhaji Sadik ya gyara zama gami
da fadada murmushinsa domin tambayar
ta yi masa dadi, cike da ladabi ya ce masa
"Sunana Alhaji Sadik, mahaifina kuma
sunansa Alhaji Muhammad dan gidan
Alhaji Ahmad mai kamshi......
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
Da sauri ya katseshi da fadin "A a
Ahmad mai kamshin dai nawa na
unguwar Dala cikin Makwalla? Ko kuma
ne mai irin wannan sunan?"
Da sauri Sadik ya amshe cike da jin
adi "shine dai, Alhaji ai babu wani mai
wannan sunan a nan nahiyar sais hi."
Alhaji Sadik ya fadi cike da zumudin
ganin wata hanya mai kama da samun
nasara ta samu.
Baba Malam ya sake duban Sadika
karo na barkatai fuskarsa cike da alamun
tausayawa yace,"Yaro ashe kai jikana ne
ban sani ba, Allah ya jikan Ahmad
aminina ne tun muna kananan yara tare
muka yi karatun allo mu ka yi sauka, kai
tare ma aka sha mu, duk wani wasa na
kuriciya irinsu langa da tamaula, da duk
wani kiriniya ta kuruciya tare muka yi da
Ahmadu, abin day a faru amintarmu ta
A
48
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
fara sanyi bai wuce harkokin kasuwancin
mu da ya banbanta ba, domin shi
Ahmadu yana shigo da turare kowanne
irin nau'i shine sana'arsa, dan haka ba
kasafai ya fiye zama a Nigeria ba, ni
kuwa da yake Malanta ita ce, gadon
Iyayena don haka sai ya zama
kasuwancin nawa na cikin gida nake yi,
sai dai na tura a shigo mini da atanfofi da
shaddodi a sai da saboda ko yaushe ina
tare da mahaifina ina daukar ilimi, dan
haka sai mu kan dade bamu gana da juna
ba.
To ka san idan sana'a ta banbanta
to ba kasafai mu'amala ke dorewa ba,
gashi a lokacin babu hanyoyin sadarwa
kamar yanzu, don haka muka nisanci
juna kwarai sai ya zamana sai sanda
Allah ya so haduwarmu sai kaga mun
hadu a wani guri, da haka dai har girma
49
ALAWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA СЕ
1
ya fara cimmana Iyayenmu da suka rasu
muka yi 'ya'ya nauyi yah an kanmu
sosai ban Ankara ba sai kawai naji
hatsarin jirgi ana lissafa wadan da
su sai naji har da Ahmadu na wa
da dansa, ranar da na ji tashin hankali
wanda ya kasa gushe mini cikin raina.
Yana zuwa nan ya fara shesshekar
kuka, Alhaji Sadik ya yi sauri ya share
kwallar da ke zubo masa, sannan yace
"Baba sai hakuri don Allah kada ka yi
kuka, in ka yi kuka mu kuma mmuyi
me?"
Da haka ya rarrashe shi ya hadiye
kukan da ya zo masa, Alhaji Sadik ya ce
masa "Baba ai shi wannan dan nasa shine
mahaifina, ni kadai ya Haifa a lokacin da
yake da shine yake taimaka masa wajen
kasuwancin dan haka ya zama tare suke
zuwa ko ina don ya fahimci harkar shi
50
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
kuma ya zauna a gida ya huta mahaifin
nawa ya zama shine ke yin komi, to da
yake kana taka ne Allah na tasa sai duk
suka cimma ajali a lokaci daya."
"Allahu akbar, Allah ya ji kansu,
nayi rashin aboki na kuruciya, amma
kuma yau na yi farin ciki matuka da na
sake yin tozali da irin tsatson Ahmadu,
Allah ya yi muku albarka, Allah ya tsara
mana alkairi a cikin wannan lamari."
Da sauri ya amsa da "Amin Baba."
Tuni zuciyarsa ta cika da farin'ciki domin
da alamun jiyo kamshin Hanan zata iya
zama mallakinsa. Da sallama ta shigo
hannunta dauke da lemon Izotik da robar
ruwa faro a kan faranti sai kuma kofin
sha a gefe, a gabansa ta ajiye masa
sannan ta koma kusa da Kakan nata ta
zauna.
51
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CЕ
Ya dubeta da kulawa yace mata
"Ke Hanan bayan duniya kika tafi kawo
lemon ne?" Ta yi murmushi ta gyada kai
ta ce, masa "Wadannan tsofaffin matan
naka kasan ba gani suke yi ba sosai ba,
wai su ba su ma san lemon ya kare ba, sai
da na duba ko ina ban samu ba, sannan na
aika aka siyo shi yasa kaga na dade."
Ya yi murmushi yace mata "Af
haka kikace da su? Zaku hadu ne ai, ni
ma ban san ya kare din ba dake ni ba son
zakin nake yi ba dama don baki ake
ajiyewa.
Ya yi murmushi domin yanda suke
yi da Kakan nata yana birgeshi, bai damu
bay a bude da kansa ya tsiyaya a kofi ya
sha domin ya san har yanzu Hanan bat
agama sakin jiki da shi ba, balle hart a
tsaya zuba masa lemon.
52
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ
Yana kammala shan wanda ya zuba
ya mike yana fadin "To Baba ni zan
koma." Baban ya amshe da sauri "To
Saddiku Allah ya yi maka albarka nagode
matuka."
Nera dubu ashirin ya ajiye masa a
gabansa da wani tirare mai kyau yacе
"Baba wannan kaci goro." Bai kara
tsayawa bay a fice.
Hanan bata iya ce masa komai ba
illa biyo shi da ta yi a ranta tana jaddada
kyautatawarsa a gareta, lallai ya fara
kamo tasharta domin tana matukar son a
kular mata da dan tsohon nan domin shi
ma ya kula da ita a rayuwarsa.
Ba su yi wata doguwar tsayuwa ba,
godiya kawai ta yi masa, ta kuma isar
masa da godiyar Baba Malam sannan
suka yi sallama tajuya ta kooma cikin
gidan, shi kuwa bai tafi ba har sai da ya
53
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
daina ganinta sannan ya ja motarsa ya
wuce zuciyarsa cike da shauki da murnar
alamun samun nasara.
Baba Malam ne ya dubeta, duba na
nutsuwa da babu wasa a cikinsa, ita kanta
ta karanci cewar ba was an don haka
dolente ta shiga nutsuwarta ta tattara
masa hankalinta guri guda.
Baba Malam ya fara da cę mata
"Hanan ina mai baki shawara sannan ina
umartarki da ki yarda da batun Yaroon
nan ki aureshi ba don komi ba sai don ya
cancanta, ina so na nusar da ke cewar
"auren mutumin da ya mallaki hankalin
kansa ba daidai yake da na yaro karami
ba, kina dai kallon yanda zamani ya zama
samarin nan sai fama akeyi da su, a kan
su rike matan nasu da gaskiya amma ina
da anyi aure haihuwa daya biyu sai saki,
shi kuwa Babba ya san darajar iyalinsa da
54
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СЕ
darajar rikon aurensa don haka za ki ga
ya jure ya hakura da duk wani abu da zai
faru, da wuya ki ji an rabu sai dai wata
kaddara ta Ubangiji.
Dan haka ni dai ina rokon ki
arzikin da ki daure ki amince da shi,
gashi kyakkyawa yaro, gashi da karamci
da girmama na gaba, ke hasalima
Kakansa da ya haifi ubansa aminina ne
tun tale-tale."
Dariya kawai ta yi cike da zolaya ta
ce masa "To waye yace maka bana
sonsa?" shima dariyar ya yi yace mata "A
haf! Hanan har sai angaya min, ni da na.
san halayyarki sai kace wata mai aljanu,
ko aljanu ne dake ne yanzu na yi miki
rukiyyar ko kya dawo hayyacinki ki yi
aure.
Bata ce masa komai ba illa mikewa
da ta yi tana dariya tana fadin "Bari ka ga
55
ALAWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA СЕ
na zo na koma gida saboda ina so na je
gidan Daddy, kullum sai ya yi mini waya
yana tambayara yaushe zan dawo."
Murmushi ya yi yace nata "Ai duk
wani goce godenki na gano inda kika
dosa, ni nasan aid a wuya na fada maki
abu ki ki yin aiki da abin, don haka ni
zan tattauna da Dadyn naki a kan
maganar Insha'Allahu, ki gaishe mini da
kowa nagode, Allah ya maki albarka."
Ta amsa da "Amin"
Sannan ta dauko goronta da
turarenta ba ka'ida da take kawo masa ta
bashi ya karba yana sanya mata albarka
suka yi sallama ta tafi, dama tuni ta kira
direba a waya yana waje yana jirsnts don
haka sai ya dauketa suka tafi gida.
56
****
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
Alhaji Sadik kam ya riga ya rikice
akan soyayyar Hanan domin a ganinsa
Hanan dince kadai zata iya magance
masa matsalarsa da ke addabarsa a cikin
gidansa.
Tafe yake a mota yana shirin
komawa gidansa bayan wuni da ya yi
yana hidimomin neman kudinsa, iskar da
ke busawa a wannan dare ta yi masa dadi
matuka domin tana kunshe da tarin
ni'ima a cikinta, mutane na ta gudanar da
harkokinsu cikin nishadi saboda dadin da
yanayin yayi musu.
Yana ta kallon yanda mutane ke
harkokinsu amma a badini tunani ne iriiri cunkushe cikin zuciyarsa.
Cikin ransa ne yake fadin "Ina ma
Hanan ta zamo mallakinsa a wanna rana
da yanayinta yake matukar birge kowa,
lallai kam yanayin ya dace da masoya, sai
57
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
dai kash tashin hankalinsa baii wuce
halin da zai tadda gidan nasa ba domin ya
sani babu wani sauyi cikin al'amarin
gidan sai ma dai abin da ya karu, nan
take nishadin da yake tare da shi ya sauya
zuwa takaici da tarin nadama a haka har
ya isa gidan.
sbKamar yanda ya saba sai da yayi
hon dinsa na ka'ida sannan kowa ya san
ya dawo, Yaransa suka fito suka yi masa
barka da zuwa, sannan kowa ya nufi
daakinsa shi kuma kai tsaye dama
dakinsa ya wuce.
Saida ya kammala komi na
bangaran wanka. Cin abinci da sauran
duk abin da ya dace yayi sannan ya
kwanta bisa doguwar kujera yana kallon
tashar Al-jazecra har bacci yafara
daukarsa sai kawai ya farka firgigit dab
tunanin Hanan dinsa, dama tuni ya bawa
58
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
matansa hutun zuwa dakinsa a matsayin
horo bisa wani laifi da suka yi masa, dan
haka sai kawai ya tsinci kansa da son ya
ji muryarta ko ya kara samun saukin abin
da ke ransa.
Ringing uku ta daga wayar, cikin
tattausar muryarta ta amsa "Hello Alhaji
baka yi bacci ba cikin wannan daren?"
Wani sanyi yaji cikin rana,. Can
kasan makoshinsa ya amsa "Ina ni ina
samun damar bacci Hanan bayan sonki
da tsananin Kaunarki sin hana ruhina da
gangar jikina sakat, idan har banji ki ba
bana iya aiwatar da komi a rayuwata."
Ta yi wani sassaukan murmushi da
alamun kalaman nasa sun ratsata, sannan
ta ce, masa "To ni dai kar ka hadani da
matana domin magidanci kamar kai a dai
dai wannan loakci ya dace a ce yana tare
da matarsa.
59
ALAWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE
Shi kansa ya san hakan ya dacc,
amma sai dai shi kuma bai dace ba da
haka sai ya wayance yace mata "Hanan
ba zan kira ki ina tare da Matata ba
domin idan nayi hakan ya zama cin
fuska, matata ta kammala duk abin da
zata yi mini, ta je sashenta ta duba
Yaranta kuma sai can dare zata dawi
shine nayi amfani da wannan damar na
kiraki don na rage kewarki."
Cikin nutsuwa ta tausasawa suka
dinga musayar zantukan soayya
musamman bangaran Alhaji Sadik wanda
yake jin Hanan din a can cikin ransa da
ruhinsa, duk da dai har yanzu bata saki
jikinta yanda ya dace ca amma shi kansa
ya san an samu ci gaba a tafiyar tasu
sosai.
60
ALAWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE
Sai da dare ya raba sannan Hanan
ta fara Hamma sannan Alhaji ya yi
sallama da ita ya kashe wayarsa.
Kwanan Hanan biyar a gidan
Mamanta ta yi sallama da su da nufin ta
komawa gidansu domin Dadyn nata ya
damu da ta zo ya ganta.
Suma su Alhaji Aliyu da kannenta
har ma da Maman nata basu so tafiyar
tata ba domin suna jin dadin zama da ita.
sai dai dole suka hakura suka yi sallama
da ita sai dai ta basu tabbacin cewar ba
zata dade ba zata dawo.
Haka nan suka tsattsaya a farfajiyar
gidan suna yi mata sallama har sai da
motar ra fice daga gidan, 'yan kannen
nata har da hawaye suka koma cikin gida
rayuwarsu sam babu dadi.
Shi kuwa Alhaji Hafiz wannan rana
sai ta kasance masa ranar farin ciki a
61
ALAWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE
gareshi domin dawowar Hanan cikin
gidansa, ranar wuni ya yi a gida suna
shan hirarsu da diyar tasa, hatta abinci
tare suka ci dai da dare ya yi sannan ta yi
wa Dadyn nata sallama ta nufi dakinta
domin runtsawa, ita kanta rayuwar tana
yi mara dadi domin tana da cikakken gata
ta kowanne bangare.
Kwananta daya a gidansu Alhaji
Sadik ya bayyana a can, karfe biyar na
la'asariya ya yi parking da motarsa a
kofar gidansu, ya fito ya jingina a jikin
motarsa kamar yanda ya saba, yayi
amfani da wayarsa domin sanar da ita
cewar ya iso.
Bata dauki tsayin lokaci ba ta fito
sanye da doguwar riga 'yar saudiyya
kalar kofi, ta yi mata kyau matuka, shi
ma din sut ne a jikinsa kofi kala sunyi
matukar amsarshi sosai.
62
ALAWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE
sw Cikin takunta na nutsuwa ta iso
gareshi fuskarta cike da murmushi ta yi
masa sallama sannan ta yi masa barka da
zuwa, idanuwansa sun kasa dauke kansa
daga barin kallonta, cike da nishadi yace
mata "Lallai akwai alamu zuciyoyinmu
sun fara zamowa daya domin gashinan
mún sanya kaya kala daya ba tare da
kowa ya san dan uwansa zai sanya ba."
Ya fadi yana ci gaba da kallonta, kallon
da tun yana damunta har ma ta saki
jikinta da shi, izuwa yanzu domin ba zai
taba iya dainawa ba.
ST Murmushi kawai ta yi wanda ke kara kawata fuskarta ta ce masa "Lallai
kam akwai alamun faruwar hakan."
Amsar tata ta yi masa dadi, don
haka ya sake gyara tsayuwarsa ya zuba
mata idanuwańsa, komi nata birgeshi
suke yi matuka.nit nadd
63
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
Basu dauki tsayin lokaci ba a waje
ta yi masa iso zuwa babban falon gidan
na su, suka zauna bisa lintsima lintsima
kujerun da ke cikin falon, suna fuskantar
junansu. Har izuwa wannan lokacin
Sadik ya kasa dauke idonsa daga kallon
Hanan, ita kuwa kanta na sunkuye sai jefi
jefi take daga idonta suyi ido hudu da
Alhaji, duk sanda hakan ta faru kuwa,
wani irin yanayi take tsintar kanta a ciki,
izuwa yanzu kam ta fara samun
nuutsuwar zuciyarta a kan Alhaji Sadik
domin duk wasu halaye da ake son
Namiji dasu yana da su, a bangaren
halittarsa kuwa dama sam babu makusa
ballantana kuma bangaren mu'amala,
uwa uba kuma kyautatawarsa da yake yi
mata ba tare da nuna gazawarsa ba.
Ya kara tattara hankalinsa guri
guda yana duban Hanan din da kulawa,
64
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ
can kasan makworonsa ya kira sunanta
"Hanan ina so a yau na san halin da nake
ciki a game da ke, har izuwa yanzu fa ban
fuskanci wata kalma kwaya daya wacce
zata tabbatar mini da kina sona da aure ta
fito daga bakin ki ba, Hanan kin sani ina
kaunar mallakarki a matsayin matar
aurena ta sunnah, kinga ni ba yaro bane
da zan yi ta zuwa gurinki babu wata
kwakkwarar magana tsakaninmu ba
kimata ba се.
Ina neman alfarmarki a yau daki
sanar dani matsayina a cikin ranki, idan
har banyi miki bane ki sanar dani, sai na
hakura na mika lamarina gurin Allah, na
san ba zi wofintar da ni ba." Yana kaiwa
nan ya dakata jikinsa a sanyaye, tamlar
wanda aka zarewa laka.
Itama dai Hanan. din tuni an
kwashe lakar jikinta domin da zaka daga
65
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
danyatsanta daya a wannan lokacin
komawa zai yi dan kansa sabida tsabar
rashin kuzari, maganganunsa sunyi mata fata-fata.
A cikin ranta take fadin "Lallai
Alhaji Sadik sjine namiji wanda ya dace
a so shi so mai inganci, shine kuma
namijin da ya cancanci ya kasanco abekin
zamantakewar aure na har abada lallai
tabbas ya cancanta kamannir
halayensa sun done, halayyarsa ta zame
masa ado, juriyarsa kuwa ta ame
jagora zuwa nasararsa da
kalamansa kuwa ya zame masa tauraro
mai kyalkyali akan fuskarsa, tabbas idan
nace bana son Alhaji Sadik to na yi wa
Ubangijina butulci domin shine ya zabo
mini shi ya hadani da shi, idan ma na
guje shi to ban san irin wanda zan ci karo
da shi a gaba ba...."
66
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
Gyaran muryar Alhaji Sadik ce ta
katse mata dogon tunaninta, bayan da
shiru ya ziyarci dakin na tsayin lokaci,
har yanzu Hanan ke nake saurare shin
kina ganin kin amince na ci gaba da zuwa
gurinki kuma na saka dan ba akan
maganar aurenmu ko kuwa na dakata?"
Kanta sunkuye ta masa masa "Ва
komi Alhaji ka ci gaba akan niyyarka,
Allah yasa mu dade ya sanya mana
alkairi da abin da yafi alkairi a
rayuwarmu."
Wani irin sanyi yaji cikin ransa ya
tsirga masa, ya rasa wanne irin yanayi
yake ciki dadi, murna ko farin ciki, ya
daga hannunsa yana godiya ga Allah,
sannan daga bisani ya juya ga Hanan din
yana fadin "Hanan nagode da kyautar
soyayyarki gareni nagode da samarwa
kaunata gurbi a cikin zuciyarki, nagode
67
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
da amincewarki dani a matsayin abokin
rayuwarki, bani da abin da zance sai dai
na yi godiya ga Ubangijina domin shine
silar komi, sannan kuma a yi mana
kyakkyawan fatan alkairi a rayuwarmu
baki daya."
Bata dago kanta ba, illa murmushi
da ta yi ta amsa da "Amin."
Zumudi ya hana shi ci gaba da
zama domin gani yake gara kawai yaje ya
fara shirin duk abin da ya dace ya yi
akan batun aurensu.
Ya ajiye mata kudi yanda ya saba,
sannan ya yi mata sallama, cike da
nishadi ya tafi yana fadin sąi sunyi waya.
****
Tana kammala cin abincin dare, kai
tsaye falon mahaifin nata ta nufa kamar
68
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ
yanda ta saba a kullum don ma yau bata
son cin abinci tare da shi da nan zata je
suci.
Da sallama ta shiga ta iske shi
zaune bisa kujera idanunsa sanye da
medical Glass, hannunsa rike da jaridar
Daily trust yana karantawa, yana jin
sallamarta ya ajiye Jaridar a gefe ya amsa
mata, sannan ya tattara hankalinsa gareta
gaba daya. Gabansa ta je ta zauna ta ce,
masa Dadday sannu da hutawa da kuma
יי
karatun news paper."
Ya yi murmushi ya ce mata "Sannu
dai Hanan, na kuwa ji dadin ganinki
yanzu domin dama ko baki zo ba zan
sanya a kirawo mini ke idan na kammala,
na zauna.
Gaba daya ankalinta ya koma
gareshi cike da zakuwa ta ce, masa
69
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
"lafiya Daddy?" me ya faru? Ko wani
laifin nayi maka ne?
Ya yi murmushi ya cewa Hanan
din kwantar da hankalinki diyata
,ba ki yi mini laifin komai ba,
Baba Malam ne ya sanar da ni cewa
akwai wani Yaro jikan amininsa da yake
zúwa wajenki kuma ya yaba da komi na
mutumin, shine yace na sameki na
tambaye ki shin ko kin amince da
maganarsa?
Ta yi dariya ta sunkuyar da kai
kasa amma ba ta ce, masa komi ba.
Shima dariyar ya yi yace "Lallai wannan
wanne mai sa'a ne haka Allah ya kawo
shi, har kika amsa maganarsa kai tsaye ba
tare da wahala ba?"
Ta ďago ta dubeshi fuskarta cike da
fara'a ta ce, masa "Daddy ni fa wallahi
baku fahimce ni ba, ba fa wai ina gudun
70
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
aure bane, A'a halayyar mazan ce ta fita
a raina shi yasa na kasa saurarar kowa na
kwammace na bawa karatuna
muhimmanci, domin yanda nake ganin
jawarawa barkatai a gari, abin ba a cewa
komi.
Daddy ya yi dariya ya ce "Hanan
kenan kinyi tunani mai kyau, amma
kuma kuntatacce domin