An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Sarauta Publishers
Yar Aljanna CeALAWIYYA WADA ISAH
ALAWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE
HAKKIN MALLAKA
ALAWIYYA WADA ISA
SHEKARAR BUGU 2014
GODIYA
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga
tsarkakakken sarki mai kowa mai komai. Tsira
da amincin su tabbata ga shugaban halitta
Annabin karshe Annabi Muhammad (S.A.W).
JINJINA
Gareka balarabe kurmi mai littafi
kasuwar kurmi
(BUGAWA A COMPUTER)
SARAUTA
08034255307
(BUGAWA DA YADAWA)
NAJIB SARAUTA
08034255307
yar Aljanna anna ce
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
dalibai.
arfajiyar Jami'ar Abubakar FTafawa Balcwa da ke garin
Bauchi, ta cika makil da
Yawanci masu masu burin barin
Jami'a a washe gari domin kammala
karatunsu na Digiri da suka yi a wannan
makaranta.
Sanyayyar la'asar ce mai kunshe da
ni'ima wacce ke bayar da iska mai dadi
da sanyaya zuciya, bishiyoyi sai rangaji
suke, da alamar suma suna ta ya dalibai
murna ne.
"Da alama yanayin ya yi musu da
di domin suna ci gaba da gabatar da
sabgoginsu cikin nishadi. Daga masu
daukar hotuna, sai masu shirye-shiryen
dansewa da za suyi da daddare, wato
sand up party domin bankwana da
junansu.
3
ALAWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE
"Can gaban mass communication
department kuwa wasu 'yan mata ne
zaune cike da nishadi, da alama suma
masu tafiya goben ne. suna ta faman
zabga musų kamar zasu tsaga gurin, da
ma su wadan nan 'yan mata ya zame
musu tamkar al'ada, idan har za su hadu
to aikinsu baya wuce suyi ta musu, har
ma sauran dalibai 'yan uwansu sun rada
musu suna Argument group.
Wanda bai sansu ba sai ya dauka
fada suke yi, amma ina tuni sun riga sun
fahimci junansu, har su gama musun su ta
shi ko harara bata wanzuwa a tsakaninsu.
"Yau din ma dai aikin nasu suke yi
da suka saba, musu ne ya karke a
tsakaninsu, sannan kuma kowacce na
tsaye akan ra'ayinta tana kare kanta.
Ta tsuniyar gizo dai bata wuce koki, domin wadan nan 'yan matan babu
ALAWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE
abin da suke tattaunawa akai illa batun
aurensu.
Wanda ya kasance shine agendarsu
ta gaba bayan sun kammala karatunsu.
Tafe take tana takawa dai dai
kamar ba zata taka kasa ba, cike da
nutsuwa take tafiyarta.
Riga da siket ne a jikinta da su ka
yi mata kyau suka bi tsarin jikinta. Sai
kuma karamin mayafi da ta yane kanta
das hi, bayan ta kuma jelar gashinta da ta
tufke ya fado bisa gadon bayanta.
Hankalinta na kan 'yan uwanta
'yan Argument group.
Ta kagu ta same su ta ji abin da ya
saka wannan fitaccen musun da kowa ya yi
shuru yake sauraronsu domin ita ma ta samu
damar sanya musu albarka a wajen fadin na
ta albarkacin bakin.
Ko kuma layin da alama ita ma
yanayin yana yi mata dadi, shi yasa take
5
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNACE
takawa sannu a hankali tana jin ita ma
tana rangaji kamar yanda bishiyun daji ke
yi.
Musun na su da alama ya dauki
zafi domin har ta iso gurin ba su Ankara
ba, sai da tattaba kawunansu tukunnan
suka Ankara da ita, Hanan kenan.
Cikin yauki take fadin "to
sarakunan musu, ana sana'ar ne?
Me ya tufke musun naku haka har
baku san na iso gareku ba, sarakan
hayaniya."
Dukkansu su ka yi dariya gami
da cewa "zauna 'yar uwa ki ji kan
topic din da muke tattaunawa ke ma ki
dora naki ra'ayin sai muga wanda zai
יי yi nasara."
Ta samu guri ta zauna tana
sauraron yanda bayanin kowa yake
kasancewa.
6
ALAWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE
Nafisa ce ta fara fadin "Aure fa
Sunnah ce ta Annabi Muhammad
(S.A.W) wanda kuma muka wayi gari
muka tsinci Iyayenmu da
Kakanninmu a ciki, sannan kuma
karshen maganar mu ma karan kanmu
shine duk wani dan adam da ya samu
ba ta hanyar aure ba ya shiga uku da
musiba da bakin cikin rayuwa da
rashin kyawun asali.
"Dan haka dole ne na zama mai
son aure da kaunarsa har ma da
muradin yinsa."
buWannan shine dalilin da yasa na
dagen wajenganin na kammala
karatuna akan kari domin na cikawa
mahaifana burinsu, shima kuma ya
cika mini nawa burin na auren abin
sona Muhammad, domin kuwa tuni
7
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
muka matsu da juna har ma muka kosa."
Fauziyya ta amshe da sauri ta ce,
"abin da ki ka fada Nafisa haka ne."
Amina ni zumudin da kike yi shine
yake bani mamaki, idan kuma zumudi
akan aure ne ina matukar mamaki, yanzu
dan Allah ni ban isheku misali ba?"
Kuna fa gani ko waya mu ka yi
Bello ta wadatar da mu, idan kuka kula
ma yana kwana biyu bai shigo ba, ni
kuma bana damuwa.
Wani sa'ilin ma har na fi Kaunar
Yayana ma akansa.
Kuma kamar yanda kuke zümudin
auren nan da soyayya haka muma muka
yi, amman abin da nake so ku gane
99 "dokin na lokaci daya ne."
Da kunyi auren kun kusanta da
juna shi kenan zaku samu gamsuwar da
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
S
dokin zai tafi, saura kauna da shakuwa
ita ce ma zata yi aiki.
"Ni kam dagewata akan karatuna
bai wuce na kammala na samu sakamo
mai kyau domin na samu damar wucewa
Masters dina kai tsaye, sirrin yin hakan a
gurina shine ya zama ina da zazzurfin
ilmi da duk wata mace da Bello zai yi
gangancin aurowa, kafin ta kamo ni sai ta
ci kwa-kwa kuma tana kokarin kamoni ni
na sake yi mata nisa."
Amina ta yi saurin amshewa da
cewa kun ji ko, ke ma dai duk kaucewar
ki auren na ki kike kokarin kasawa
domin so kike kifi duk wata mace da zata
wayi gari ta ganta a gidan mijinki
haskawa da kuma matsayi. Mu kuwa
tunda ba taba yin auren muka yi ba ai
dole ne mu zo muji yanda yake.
9
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СЕ
Ke kuwa kin riga kinyi kin san ko
ma menene a cikinsa, shi ya sa ki ke
ganin bekon mu don muna zumudin
yinsa, kuma ke ma din idan aka yi bibiya
kan ra'ayinki za a ga cewa kuskure ki ke
so ki yi masa da dagiya don ki sake
samun jin dadin rayuwar zaman auren
naki, kuma ki kare kimarki da Yaranki
29 duk dai ta gidan auren.""
"Hanan ta yi murmushi cike da
yauki tana kallonsu daya bayan daya,
yanda kowa ke tsaye kan ra'ayinsa babu
sassauci shine abin da yafi birgeta da
su.
Ta faďada murmushinta sannan ta
ce, musu "duk ku tsaya ku saurara da
wannan musun naku, kun san ni
mamakin da kuke bani baya wuce kullum
zancen aure da Samari. Kun ganni nan
babu abin da ya dameni da wani saurayi
10
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
ko alkawarin auren wani, dan haka nake
rayuwata hankalina kwance.
Na sani aure lokaci ne, idan lokacin
ya zo kuwa babu tsimi balle dabara, dan
haka ni bana soyayya, don bana san
matsala a rayuwata, shirin dagewata a
karatuna kuwa bai wuce na cikawa
Babana burinsa ba akan nasihar da yake
yi mini a kullum yana nunamin cewa ilmi
security ne ga rayuwar diya mace, domin
yakan zame mata jagora a rayuwarta
duka, ko ta gidan Iyayenta ko kuma ta
gidan aurenta, kai duk ma inda ta tsinci
kanta a rayuwa. Don haka ni ina ganin
nawa ra'ayin shine daidai da rayuwata."
Haka nan suka ci gaba da musayar ra'ayi a tsakaninsu har suka koma
dakinsu basu daina ba, sai da suka kusa
raba dare sannan kowacce ta yi shirin
kwanciya cike da kewa dan jimamin
11
ALAWIYYA WADA ISA- YAR ALJANNA CE
washegari za su rabu da juna kowa ya
kama hanyarsa ta komawa gidan
mahaifansa.
"Haka kuwa aka yi, domin gari na
wayewa kowacce ta fito da kayanta suka
hade guri daya suna jiran azo daukarsu,
babu abin da sukeyi sai jaddada rikon
amana da zumunci mai dorewa a
tsakaninsu tunda ga whatsapp ga
facebook chat sannan ga Istagram kuma
zamu dinga musayar hotunan juna kunga
musu bai kare ba kenan.
A hankali aka kwashe su daya
bayan daya, yau 'yan Argument sun kare
babu group dinsu kowa ya nufi
muhallinsa cike da kewar juna, da
zumudin riskar iyayensu da 'yan uwansu.
12
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
Tun a hanya take yiwa Dadynta
waya tana sanar masa cewar sun kusa
karasowa, shi kuwa Dadyn ya kasa zaune
balle tsaye saboda dokin zuwan 'yar
lelensa.
Tamkar ta balle murfin motar ta
fito tun bata yi parking ba haka ta ji
saboda ganin Dadynta a farfajiyar gidan a
tsaye yana jiran zuwanta.
Da sauri ta bude kofar ta fito da
gudu ta nufeshi, jikinsa ta fada tana
hawayen farin ciki, shima sahafata kawai
yakeyi yana fadin "Alhamdulillah," ina
godewa Allah da ya nufa kika kammala
karatunki, yau burina ya cika a kanki
Allah ya bada sakamako mai kyau.
"Amin Daddy" ta amsa masa a
daidai lokacin da ta baro jikin Dadyn take gaisawa da sauran mutanen gidan da suka
13
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
fito domin tarar ta, kasancewa Hanan din
'yar gidance.
Soyayyar tata ta samo asaline da
soyayyar da mahaifinta Alhaji hafiz ke
yiwa mahaifiyarta Binta, duk da cewa ba
sa tare da ita amman kaddarar rabon
haihuwa a wani gida ta hadasu, zumunci
kuma kullum karuwa yake yi a
tsakaninsu.
Kwananta biyu da dawowa tana ta
shan gata da lele daga kowa na gidansu
musamman Dadynta.
Ranar da ta cika kwana na biyu ne
ta sanar da Dadynta, tana so ta je gurin
Mamanta domin ta ganta.
A zahiri Dadyn nata bai so tafiyarta
ba domin shima har yau dokin ganin
Hanan yake yi amma dole ne ya hakura
ya barta ta je, domin yanda yake son ya
kasance tare da ita mahaifiyar ta ta ma za
14
2
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
taso hakan, dan hakama ya amince mata
tare da yi mata addu'ar Allah ya tsare
masa ita. Da yammaci su ka yi sallama
Direba ya tafi kaita.
****
SILAR KOMAI
A babban falon gidan ta sameta
zaune tare da 'yan kannenta suna kallo. A
guje suka taro ta suka runngumeta suna
fadin "Aunty oyoyo".
a
Farin ciki da murna suka cikata
domin tana kaunar 'yan kannen nata, ta
dinga shafa su tana sake ji kaunar sun karuwa cikin ranta. Ita kuwa Maman tasu
kallonsu kawai take yi tana jiin wani irin dadi cikin ranta, kaunar 'ya'yan nata na
Kara ratsa ruhinta.
15
ALAWIYYALWADAISAYAR ALJANNA CLA
sismsunaimasalesanjikinitasta isalini des
mahaifiyar dtába takebstastedurkusab tasi
gaishetscike ta girmamawa, ital maicikem
da farin ciki take amsawansmutadoni
Bauchi saukar yaushe dafatan kunzo
**** lafiya?"
Ta amsa da "lafiya kalau Mama
sannan ta samu urtalzdundle
Suka ci gaba hirar yaushe gamo. Bayan ta
hutomeztastireslkayamastarshigadkitchen
domini alywmahaifyand tata aikinrabinciss
dareve stor Bue st onst salue sing
Karfe takwas nodarer ramar sunsi
kammalasdua komuin scha itiuneira falo
sura.kalloniashal Dadi korea, It Mob
s ni Maingidai panyi sailama arthingprib
Yaran suka shirdahudtosunalii нasas
barka idavzuwä, shyaiyamstgowsyarzauriask
yana wasarda yaramsmwsk sins nilio ibeb
SIMILINI SIST SISA
16 21
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
Cikc da ladabi ta ce masa "Baba
barka da dawowa. Da sauri ya dago
idona su ka yi ido biyu da Hanan yд
fCua murmushinsa yana fadinAa
Hanan saukar yaushe?"
Itama cike da fara'a ta ce, "yau امام
nazo Baba. Ta gaishe shi cike da ladabi
shima ya amsa da fara'a. ya maida
kallonsa ga Mamarsu yace “Ashe yau
munada babbar bakuwa a gidannan, da
latan dai anyi mata kyakkyawar tarba?
Wani sanyi ta ji a ranta domin tana
jin dadin yanda yake nuna Kaunarsa ga
diyar tata, kamar shine ya haifeta. Cike
da jindadi ta ce "mun bata tuwo taci." Su
ka yi dariya gaba dayansu.
Suka ci gaba da tattaunawa kan
karatunta, ya tayata murna day a ji cewar
ta kammala karatunta, haka suka ci gaba
da hira cikin nishadi da kaunar junansu.
17
ALAWIYYA WADA IBA- 'YAR ALJANNA CE
Ai dauki tsawon lokaci da shigowa
gidan ba akan şanar da shi cewar ana
sallama das hi a waje, kai tsaye yace a
cewa bakon ya shigo domin yasan ko
wanene, daman yasan da zuwansa, don
haka Mamansu ta mike kuma ta umarci
yaran da su tashi su koma karamin falo
su bar musu nan.
Bayan 'yan mintina ne suna zaune
a karamin falon suna kallo, Hanan ta jiyo
Karar wayarta ana kiranta. Ta duba ko ina
bala ganta ba sai ta dinga jiyo sautin
kiran wayar da ga babban falon da suka
baro, don haka ta nufi falon kai tsaye
cikin hanzari domin ta dauko wayar tata.
Cike da nutsuwa ta shiga falon ta tsaya
bakin kofa ta yi sallama, sai da suka
amsa sannan ta shiga cike da ladabi ta
durkusa, Baba ne yace mata "Yauwa
Manan kin bar wayarki rana Kara, dama
18
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
yanzu nake shirin na miko miki. Ta yi
murmushi kanta a kasa ta amshi wayar
sannan ta gaishe da bakon, kana ta mike
tana fadin "dan karta dameku da kara
shiyasa na taso na dauka, tan agama
fadin haka ta fice."
Tuni ya zurfafa cikin tunanita
domin ta yi matukar birgeshi tun daga
ladabinta da nutsuwarta, ballantana kuma
kyawun surarta duk da dai Hijabi take
amma fuskarta kadai ta dauki
hankalinsa.
Tuni jikinsa ya mutu, komai ya
tsaya masa cak, nan take ya mata da duk
abin da ya kawo shi ya tsallaka wata
duniyar.
Da kyar Alhaji ya dawo da shi daga
zurfin tunanin da ya afka, cike da zolaya
domin tuni ya riga ya dagoshi. A
daddafe suka kammala maganar da
19
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СЕ
sukeyi. Da sauri ya shigar masa da
maganar Hanan, da tambayar sa ya fara.
"Alhaji dama kana da Yarinya
kamar wannan ban taba ganinta ba?"
Gata nan kuwa ka ganta?" amma ba anan
gidannan take dab a, domin lokacin ina
Asibinta ne, tinnan duk dan da ka Haifa
agidannan ka je da shi gurina, kuma na
tabbata da tana gidan nan da kaje daa
ita."
Alhaji Aliyu ya yi dariya "Ai
lookacin tana makaranta ne, yau dinnan
ta zo ta dawo daga Unibersity ta can
Bauchi ta kammala Karatun Digirin ta
akan Islamic studies." 7
Alhaji Sadik cike da mamaki ya
zaro idanuwa, "Digree Alhaji? Kuma a
fannin ilmin addinin musulinci? Amma
Alhaji ka rufeni matuka domin kai ne fa
da kanka ka bani shawara na nemi irin
20
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
wannan yarinyar na aura domin na samu
maslahar gidana, gata kuma a gidanka
amma baka sanar dáni ba?"
Alhaji Aliyu ya yi dariya yace
masa "Kaima kasan zance kake yi, Alhaji
ya ya za'ayi na baka wannan galleliyar
diyar tawa alhalin ka tsufa, ko ka manta
matanka guda uku ne ga kuma 'ya'ya,
cike da zolaya yake maganar.
Shima cikin fara'a da kwantar da
kai ya amsa masa "ai ba anan take ba
Alhaji Sadik, abin ai dacewa ne ba a
saurayi ko babba take ba, kuma Alhaji
kamar yanda na gaya maka aure shigar
sauri ya yi mini, duka ban wuce shekara
arba'in ba a duniya. A wannan zamanin
kuwa ka san akan samu saurayin da bai yi
aure ba wanda ya fini shekaru."
Alhaji ya fadada murmushinsa ya
ce, masa "Nima ina zolayarka ne, ai shi
21
ALAWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE
aure lamari ne na Allah don haka kada ka
damu zamu tattauna kan maganar ka
insha'Allah kuma zakaji duk yanda ake
ciki."
Dai dai nan su ka yi sallama ya
raka shi har waje suna tattaunawa kan
maganar Hanan, har sai da ya shiga
motarsa ya ja sannan suka rabu.
Karfe sha daya na dare suna shirin
kwanciya ne Alhaji ya sanar da Mama
duk yanda su ka yi da Sadik kan
maganar Hanan, sannan ta umarci
maigidan nata da ya samu lokaci ya sanar
da mahaifin Hanan din.
Ya ji dadin hakan matuka, shima
albarkar ya sanyawa al'amarin sannan ya
kwanta domin rintsawa. Ita kuwa Mama
ko da ta kwanta baccin kinz uwa ya 'yi
domin tunaninta gaba daya ya kare a kan
yan da Hanan zata amince da wannan
22
ALAWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE
maganar, domin ta san kowacece diyar
tata.
Yau kwanaki uku kenan da yin
maganar Alhaji Sadik da Hanan, abin
yana damun Maman matuka cikin ranta,
domin ta rasa ta ina zata 6ullowa Hanan
domin ta sanar da ita halin da ake ciki.
Shi kuma Alhaji Sadik ya dami
Alhaji Aliyu da maganar, don kusan
kullum sai ya kirashi a waya ya fi a kirga
akan maganar. Hakori dai yake ta ba shi
tare da tabbacin za a duba yiwuwar
maganar.
Ranar da aka cika sati ne Mama ta
yi kundunbala ta nufi dakin da Hanan
take. Kwance bisa gado ta taddata ta yi
nisa cikin chatting da 'yan Argument
23
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СЕ
group. Dan haka bata so koda sakan daya
ta dauke idonta daga kan wayar
ballantana kuma ta ajiyeta, domin tuni
musun nasu ya dauki zafi.
Yau kuma suna tattaunawa ne akan
amfanin auren mace mai ilimi.
Dole ba dan taso bat a dakata ta
ajiye wayar tata domin amsa sallamar
Maman nata, domin ta kula a fuskar
Maman sam babu wasa a tattare da ita.
A kujerar dake gefen gadon ta
zauna ta kira sunanta cikin tausasawa
"Hanan ina so ki saurareni ki bani
hankalinki, kinga dai yanzu ke ba yarinya
ba ce, tuni kin mallaki hankalin kanki,
kuma kinyi ilimi mai zurfi ta kowanne
bangare, kin kuma san abin da Allah ya
hukunta akan duk dan adam din da ya
zama baligi mace ko namiji, kinfi kowa
sanin cewa aure shine daraja da martabar
24
ALAWYYAWADA ISA. YARALJANNA CE
diyadmavé şduma kinssan dai mune mukad
zamorsitaroziwankis duniya don haka ba.b
zamu thbh/yi miki abin da zai cutar da ke
ba.
DITI ISUS FTICKS
idsInar sosnasbsanars da ke cewa
waimd mutumin da ya zo gurin Alhaji
rariarndaskika zöji har kika shiga dauko 2
wayarki. BdShine yd zoclyanad sohkib dab
aurevlsm яр эллslsd sb ida eb snct6}
sb iKufin ta kammala ta katseta ta Zaros?
idorigamis da bude bakista dafe kirjintai
cikesda mamaki ta kalli mahaifiyar ta tan
amma.kuma sai ta kasa furta komisnsi i
Uwar ta karanci me ke zuciyartas
domhaka ta tare ta da cewa "Na san dama
zaiskib yi mamakinsewannan Maganasb
domin násan ke a tunaninki idan zabiakas
baki to saurayi zaki so mai kananan
shekaru, sai dai ina so ki gane cewa shi
aure zabin Allah ake nema ba na mutum
252S
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ
ba, ba kuma son ranka kake zaba ba, abin
da yafi muhimmanci a aure shine ka nemi
zabin Ubangiji to sai kaga Allah ya
haneka dana sani.
Kuma ni abin da yasa na karbі
maganar ba wani tantama sabida Alhaji
Sadik mutum ne mai kirki da karamci,
duk da dai basu dade da Alhaji ba amma
a tattare da shi da halayyarsa ba makusa
sai alheri don haka nake shawartarki da
ki yiwa kanki fada kiyi nazari akan abin,
mu ba zmu yi miki dole ba, ki yi tunani
ki tattauna da zuciyarki, sannan yace
yana nan zuwa ku gaisa.
Tana kaiwa nan ta tashi ta fice daga
dakin bata tsaya ta saurari abin da diyar
ta ta za'ta ce ba domin ta san ma ba zata
ce din ba.
26
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
take yi bisa gadonta amma bacci ya ki
daukarta, sai da ta kusa raba dare a haka
sannan barci barawo ya yi awon gaba da
ita.
****
Washegari haka ta wuni ba wani
ishasshen kuzari a jikinta.
Maman tata ta fahimci halin da ta
shiga don haka ta kyaleta take ta gudanar
da harkokinta gabanta. Girki ma ita ce, ta
yi abin ta domin Hanan din ta koma
tamkar wata marar lafiya.
A wannan yanayin ta wuni har
zuwa dare. Tana zaune a dakinta ta yi
zurfi cikin tunani Maman nata ta daga
labulen dakin ta ce, mata " kina da baki a
falo:" Bata tsaya ta ko da kalli fuskarta ta
juya ta ficce..
28
ALAWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE
Gabanta ya fadi ras, ta mike da
sauri a rude ta fara zagaye a dakin nata,
sannan daga bisani ta dangane da gaban
Mudubin dake dakin, ta kalli kanta sana
da kasa. Doguwar rig ace a jikinta ta
atamfa super Yaluwa, dinkin ya amshi
jikinta ya yi mata das, daga kasa an buda
rigar komai na jikinta kalar Yalo ne, babu
dankwali a kanta don haka a sanyaye ta
dauko wani dan karamin Hijabi mai tạf
da nayafi ta saka ta zagayo da mayafin ta
gyara shi yai mata das, tamkar Wata
Balarabiya, babu wata kwalliya a fuskarta
amman kuma da yake ta saba kwalliyar
sam babu muni a fuskar ta ta.
Da sallama ta shiga.
A rude ya dago ya kalleta su ka yi
ido hudu.
Nan take ta tafi da imaninsa domin
ta yi masa matuka, kamshin turarenta
29
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СE
Different Women wanda ya kama jikinta
ya doki hancinsa. Hankalinsa ya tattara a
kan kallonta ji yake kamar ya hadiyeta
don so.
Cikin nutsuwa ta sanu guri ta zauna
cike da ladabi ta gaisheshi da muryarta
mai kasha masa jiki, ya amsa a tausashe
idanuwansa na kanta har wannan lokacin.
Shiru ya dan ziyarcesu na dan wani
lokaci sannan ya fara da yi mata Magana
da cewa "Malama Hanan ya gida ya
karatu?" kanta na sunkuye ta amsa
da"Alhamdulillah."
A yanda take amsa masa babu yabo
babu fallasa, bai damu ba domin shi
mutum ne mai hakuri da saurarawa, don
haka kawai yaci gaba da yi mata Magana.
"Na sani kin samu labarin komai
nawa daga mahaifanki, to daman a zo ne
don mu ga juna kuma mu samu fahimtar
30
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CЕ
juna, ya yi ajiyar zuciya gami da tattara
muryarsa sannan yaci gaba da fadin
"Hanan hakika tun ranar da na ganki naji
kin kwanta mini a raina, komi naki ya
birgeni musamman iliminki da kuma
nutsuwarki gami da tarbiyya da kika
samu daga Iyayenki, ba sai na gaya miki
ba, kin san wasa ba zai kawo ni gurinki
ba dan haka ina mai tabbatar miki da
cewa ina kaunarki matuka, kuma aure ne
ya kawo ni ba maganar wasa ba, fatana
shine na samu wani bigire a cikin zuciyar
ki wanda zai zamo muhallin soyayya' ne
ka dai, hakika idan na samu hakan to
zan kasance mai matukar farin ciki a
cikin rayuwata sannan kuma mai matukar
sa'a da dacewa.
Akwai alamun maganganunsa sun
ratşa zuciyarta, tausayinsa ya kwarara
cikin zuciyarta ganin yanda ya nuna
31
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAK ALJANNA CE
Kaunarsa Karara gareta sai dai ita kam har
yanzu ba zata iya tantancewa shin tana
son sa ne ko a'a, duk kuwa da cewa a
zuciyarta ta tabbatar Alhajin ya yi yanda
mace ke bukatar namiji domin sam ba shi
da wata makusa a tare dashi.
Tsayayyen namiji ne dogo kuma
mai matsakaicin fadi fadi ba mai kiba ba,
fari ne tas mai madaidaiciyar fuska
cikakkiya, yana da kwarjini da cikar
kammala gami da zafi, tsayin fuskarsa ya
dace da zubin da jikinsa.
Yana da manyan idanuwa da kuma
dogon hanci hade da kyakkyawan baki,
yana da yalwataccen gashin kai da na
gira, ga sajensa ya kwanta lub-lub akan
fuskarsa wanda ya kara masa kyau, dan
gayu ne na ajin karshe domin duk shigar
da zai yi tun dag asana har kasa kala
daya ne hatta gilashin idonsa kalar
32
ALAWIYYA WADA 1SA- ‘YAR ALJANNA E
kayansa ne, gashi wayayye irin namijin
da ake ya yi.
Da ganinsa kudi sun ratsa shi, ba
kudin na sa ba, duk da ta fusknaci bai yi
wani zurfin karatun boko ba, da alama
dai yafi zurfi ga bangaren kasuwanci
amma kuma gogewa da wayewarsa tafi ta
wanda ya yi Digiri.
Maganarsa ce ta. katse mata
tunaninta cikin dadin muryarsa yace mata
"Hanan zan koma ina ganin ya kamata
na kyaleki, ki samu dammar yin nazari
don ki fiddoo da hukunci kyakkyawa
wanda nake fatan zamanto alkhairi a
gurin mu duka."
Tamkar kurma haka ta zamo a
gaban Alhaji Sadk sai kace ba itace a
cikin Argument group ba.
Rafar 'yan dari biyar ya ajiye mata
a gabanta sannan ya umarceta da ta ba shi
33
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ
karasa, daman na kira ne nace miki sai da
safe."
Ta gyada kai cikin ranta ta ce,
"amma zumudinka ya yi yawa." Can ta
amsa masa da cewa "to shikenan mu
kwana lafiya." Da sauri ya amsa "Nagode
Asuba ta gari."
Wani irin yanayi ya ji ya ratsashi,
ya bi wayar da kallo tamkar Hanan din
yake kallo a jikin hoton wayar. Cike da
dumbin tunaninta ya isa cikin gidansa,
haka ya raba dare yana suranta Hanan
cikin idanuwan zuçiyarsa. Muryarta na yi
masa amsa kuwa a kunnuwansa, har
6arawon dare yazo ya sace shi ba tare da
ya yi shawara dashi ba.
Ita kwa Hanan mamajin irin
zumudin da Alhajin ke yi a kanta takeyi,
ko dai ba komi tana son namiji mai sonta
da nuna kulawa a gareta, kuma mai
36
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СЕ
lokacinta, ta wannan bangaren dai Alhaji
Sadik babu makusa.
****
Washe gari da safe ta shirya tsaf
cikin wasu English wears Riga da wando
jeans sunyi matukar yi mata kyau sai
kuma ta dora After dress baka a kansu.
Kai tsaye teburin cin abinci ta nufa
inda ta iske Iyayen nata suna karyawa.
Cike da ladabi ta