abin da ke baki
gane ba shine ba duka aka taru ka daya
ba, dole komi lalacewa akwai nagari,
kuma idan kana addu'a kana mika zabi
na alkairi ga Allah sai kiga yayi maka
zabi na alkairi, ga shi kuma muna zaune
kin samo na gari ko?" ya fada tare da
zolaya.
Kunyar Dady ce ta kamata dan
haka ta sunne kai ta tashi ta fita da gudu
tana dariya.
71
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
Shi kuwa Dady dadi ne ya kama
shi da murna, domin kullum addu'arsa
kenan Allah ya nuna masa auren diyar ta
sa don har ma ya fara fidda rai da batun
auren ta domin halayyar da take nunawa
kan maganar mijin aure abin yana bashi
tsoro domin har ya fara tunanin ko ba
lafiya take ba.
****
Abu kamar wasa karamar magana
ta zama babba, maganar auren Hanan da
Alhaji Sadik ta kankama domin tuni Baba
Malam ya kirawo Sadik ya tabbatar masa
da cewar ya kamata ya turo magabatansa
kan maganar. Hakan ba karamin dadi ya
yi wa Alhaji Sadik ba, don haka bai yi
kasa a gwiwa ba ya hado komai na aure
ya sanya ranar kawowa.
72
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
Sati biyu aka sanya za a kawo komi
na auren, don haka Alhaji Bashir ya sanar
da shi, ya yi murna matuka, amma da yaji
cewar mutumin yana da uku ita ce ta
hudu nan da nan ransa ya baci, ya dubi
Alhaji hafiz ransa a bace ya ce masa
"Yanzu kai Hafiz ya za'ayi ace Yarinya
kamar Hanan a aura mata mutum mai
mata uku, ai an kware ta saboda Allah
menene gaggawar sai anyi mata aure a
bari mana har Allah ya bata saurayi dai
dai ita sai a aura mata."
Alhaji Hafiz ya nisa sannan yace
"Tabbas abin da Yayan nasa ya fadi
gaskiya ne to amma ya zai yi da hukuncin
da Ubangiji ya zartąarai ba tsumi babu dabara.
Ya fuskanci Yayan nasa sosai yace
masa "Ka kwantar da hankalinka Yaya,
abin da duk ka fadi gaskiya ne amma al
73
ALAWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE
ta yi auren kudi Allah ya sauwake wai
kuma ita ce ta hado abin da zaben nata ya
zabo mata kenan?
Ita dai kam biris ta yi da zantukan
mutane ta kankame Ubangijinta domin
dai ita kam ta san tafi karfin ta yi auren
kudi domin kowa yasan cikin kudi ta taso
gaba da baya.
BIKIN AURE
Shagalin bikin auren Alhaji Sadik
da Hanan ya kankama, duka bangaren
biyun komi ya kankama, saura sati biyu
duka-duka a fara shagalin dumu-dumu.
Iyayen Hanan kam bakinsu har
kunne domin ganin Allah ya kawo musu
lokacin auren diyar tasu, Gangaren
Mamanta kuwa abin ba'a cewa komai,
domin yanda take cikin farin ciki tamkar
75
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
ita kadai ta fi kowa kaunar Hanan din,
ballantana kuma Alhaji Aliyu wanda ya
zamo shine silar komi.
Sai dare ta samu damar, kuma da ta
online kai tsaye Group Argument na
whatsapp ta nufa, said a ta kammala
karanta sakonnin da suka wuce ta sannan
ta fara tura musu da tsarin ranakun
aurenta, daga kasa kuma ta ce, tana
gayyatar kowa da kowa, wanda bai samu
dama ya yi mata addu'ar fatan alkairi.
Nan da nan ta fara samun amsoshi
na karyatawa musamman Fauziyya da
Nafisa domin su sun hakkake cewar
zolayarsu kawai take yi amma ba wani
batun aure tare da ita a kwanan nan.
Fauziyyar ce ta fara aiko mata da
amsar cewa "haba mai tsoron aure, mu
zaki zolaya? karfa ki manta mun san ko
76
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
ke wacece a bangaren maganar aure don
haka babu wabi kife mu da zaki yi.”
Tana kammala karantawa dariya ta
subuce mata har tana shirin fadowa daga
kan gadon da take a kwance dan dariya,
bata kammala dariyar ta ta ba, wani
sakon ya shigo.
Nafisa ce ta aiko da cewar "Hahah!
Hanan kenan kice yau Allah ya kawo mu
lokacin da kike jin sha'awar aure a kanki,
tunda har kike karyar fadin ranar aurenki,
a hankali wata rana sai kiga har kin samu
nutsuwa a 6angaren auren har kin aiko
mana da takardar gayyata ta gaske ba ta
zolaya ba, kinga sai muzo mu sha bikin
gaske ba na tatsuniya ba."
Dariya ce ta sake cin karfinta, ba ta
iya cewa komi ba, wani sakon ya sake
shigowa.
77
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СЕ
Amina ce ta ke ce mata "Na
fuskanci inda kika nufa Hanan, ba wani
kike zolaya ba illa mu masu zumudin
komawa gida muyi aure, kinji munyi
shiru ba muce ga ranar auren ba ko?
Shine kika biyo ya wata hanyar don ki
zolaye mu, to kisha kuruminki nan ba da
dadewa ba zaki ji kiranmu sai ki shiga
Jaka ki taho biki, kinga daga ranar
shegantakar da kike yi mana ta kare, ke
kuwa ki yi ta zama a gida ki zama
daddawar daka."
"Kun fi kowa sanin cewa ni Hanan
ba halina ba ne zolaya, sannan ban iya
karya ba ko da wasa, kun san idan ba da
gaske nake ba babu yanda za ayi na
shirga karya na sanar daku, kunga ko
wannan kadai ya isheku ishara ku gane
cewar shi aure fa lokaci ne, da sonka da
kinka da zumudinka da kuma ko in kula
78
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
dinka babu ruwan Allah, wallahil azim
kun san idan na rantse da Allah a kan
karya na san makoma ta, to wallahul
azim aure zanyi, kuma yanda na turo
muku tsarin komai haka abin yake,
afuwarku kawai zan nema na rashin sanar
daku da banyi da wuri ba, wallahi nima
haka nan auren ya zo mini ba shiri,
shiyasa ban samu damar sanar da kowa
ba, sai yanzu da abubuwa suka saukaka,
ina zuba idanuwana a bisa hanya sai na
ganku."
Halin da suka shiga na mamaki ne
ya sanya suka kasa ce mata komi, illa yi
mata addu'ar fatan alkairi kadai.
Ranar Alhamis ita ce ta kama ranar
kamu dan haka tun kafin ranar aka shiga
hidimar gyaran jikin amarya, ana gyaraya
ana kuma tsumata ga turaruka da akeyi
don haka duk inda ta gilma wani kamshi
79
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
ne ke fita daga jikinta mai dadi da daukar
hankali, jikinta kuwa sai wani sheki yake
yi da silbi, ga wani taushi tamkar jikin
Jaririya.
Biki kam ya kayatar, guri guda aka
tanada dan yin kamu sannan da aka gama
kamun kuma aka yi gadar kauyawa, abin
ya kayatar matuka, 'yan Argument ne
Amarori domin sune a kan gaba a komai.
Kyawun da amarya ta yi kuwa fassara shi
a nan kauyanci ne. Washegari kuma
dinner aka shirya lafiyayya wacce ta
amsa sunanta, duk wani abokin arziki ya
halatta ya kuma taya ango da amarya
murna.
Ana kammala dinner ne kuma aka
dawo da amarya gida ta shirya domin
kaita dakinta
Tamkar a mafarki take kallon alamarin wai ita ce yau za a kaita gidan
80
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
aure, haka ta dinga shiryawa tana cike da
mamakin hukuncin da Allah ya kaddara
bisa kanta.
Daddynta ya yi mata nasiha matuka
akwaialamun kuma duk abin da ya gaya
mata ya shiga cikin kunnenta matuka, da
kuka suka rabu da Daddy, yana sanya
mata albarka da yi mata fatan alkairi, kai
tsaye gidan mahaifiyarta aka zarce da
ita,ida da Baba Aliyu suka hadu suka yi
mata nasiha, nan ma dai da kukan suka
rabu, sai gidan Baba Alhaji kuma, duk da
dai yana zolayarta amma ya gaya
abubuwa masu matukar fa'ida da idan ta
rike za suyi mata jangora zuwa ga
kyakkyawar rayuwa da cimma nasara a
cikin rayuwar aurenta.
Cikin nasara sa sa'a ta shiga gidan
mijinta, sashen nata kam ya tsaru tamkar
Aljannar Duniya, babu ce kawai babu a
81
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CЕ
sashen, komi ka kalla na waje ne babu
wani abu dan gida Nigeria, Hanan kenan
'yar gata.
A babban falon gidan suka taddasu
wanda zai sadaka da sashen kowa a gidan
har da na mai gidan.
Bayan sun gaisa ne suka damka
amanar Hanan a hannunsu.
Uwargida wacce dama ita ce ta
amshi dariyarsu tun farko ita ce, ta sake
yin murmushi ta ce,"Ai ba komi da ai
duk na kowa ne, wannan ai 'yar uwace a
gurin mu, insha Allahu zamu riketa da
amana da gaskiya Allah ya bamu zama
lafiya ya kawar mana sherrin shedan-a
tsakaninmu."
Gaba daya suka amsa da Amin.
Ana shirin yin addu'a ne Lami wacce ke
cika tana batsewa, cike da tsiwa ta ce,
"A'a Maman Nabila gara kawai ki fito ki
82
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
fadi gaskiya kishiya fa ba 'yar uwa ba ce,
in ke kin amsa to ni dai gaskiya ban amsa
ba don amana wahala gareta."
Ta juya ta kalli Sadiya ta ce mata
"ko kuwa 'yar uwa, ki ya kika ce? Ko
kema kin bi sahu?"
Sadiya ta yatsine fuska ta ce, "ai
kema kin san tankawa ma yabawa ce, ina
ni ina amsar amanar kishiya, gidan miji
ne gashi nan aure ta zo yi kamar yanda
mu ma shi muke zaune muke yi don haka
ta share guri itama ta zauna kowa ya taka
irin rawarsa a kalla."
Gaba daya gurin suka cika da
mamakin abin da ya fito daga bakunansu
don haka ba shiri suka dauki amarya
zuwa sashenta jiki a sabule kowa na
fadin albarkacin bakinsa, suna kuma kara
yiwa Hanan nasiha akan hakuri da taka
tsantsan a zaman takewarsu.
83
ALAWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE
Bayan dan lokaci 'yan kai amarya
suka watse, sai 'yan Argument aka bari
suma sun jira ne a sayi baki sannan su
koma gida, suna cikin jimamin abin da
kishiyoyin suka yi matane sakon ango
ya shigo wayarta ta buda da sauri ta
hau karantawa.
"Amarya ki kara hakuri gani nan
zuwa gareki, zuciyata cike take da
zumudin riskarki, idanuwana cike suke
da dokin ganinki cikin siffar amarci, ki
وو shirya gani nan zuwa.
Nafisa ce ta karbe wayar ta
karanto musu abin da ya aiko, tana
kammalawa suka saki ihu da tafi suna
fadin "kai wannan ango naki Hanan
gwanin iya soyayya ne, kinga yanda
yake tattalinki tamkar wani kwai! Dole
84
ALAWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA СЕ
kishiyoyinki su yi kishinki, ai kin
amshe zuciyar mai gidan gaba daya."
Cike da zumudi Alhaji ya shigo
ciki, farar shadda kal Getzner, Babbar
riga aka yi masa da 'yar ciki da wando
da bakin zare aka yi dinkin jikin
shaddar don haka hattta agogon
hannunsa baki ya sanya, ya yi matukar
kyau da daukar hankali.
Abokansa ke biye da shi dauke
da 'yar karamar akwati cike da kayan
siyen baki. Fara'arsa taki karewa,
idanuwansa kuwa na kan gimbiyar
tasa. Allah -Allah yake a kammala
siyen bakin ya sallami kowa a barshi
daga shi sai amaryarsa, don haka ya
dinga jin komi a takaice, ba dadewa
suka kammala suka yi sallama dasu
suka barsu suna zolayarsu.
85
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
Dakin amarya ya rage daga ita
sai angonta, ya bi ko ina da kallo
shirin dakin ya matukar birgeshi ya
sanyawa' aurensu albarka sannan ya
umarce ta da su tafi sashensa, ba tare
da gardama ba ta mike ta bi bayansa
har zuwa sashen nasa.
Yanda ta ga tsarin 6angaren nasa
ya matukar kayatar da ita, bata taba
zaton Sadik arzikinsa ya kai haka ba,
sai a yau da ta zo muhallinsa, gaskiya
gidansa ya tsaru, gida ne na babban
maikudi ba dan karami ba.
Kai tsaye ya umarceta da dauro
alwala, shima ya yiwo ya fito daga
bedroom din sanye da doguwar riga
sassauka, ya yi mata jagora zuwa
bedroom dinsa sannan suka tada sallah
85
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
raka'a biyu daga koyarwar Annabi
(S.A.W) don neman tabarrakin auren.
Bayan sun kammala ne ya kama
kanta yayi addu'a, sannan ya janyo
Kazar day a zo da ita ya bude yah au
bata tana ci shima yana ci, tana
matukar daukar hankalinsa.
Sai da ta koshi don kanta sannan
ya umarceta da ta cire kayan jikinta
masu nauyi sannan ya dauko mata
masu sauki ya bata ta amsa ta hau
cirewa cike da kunya.
Abin da ya faru a wannan dare
dai mai matukar girman gaske ne,
Alhaji Sadik ya yi farin ciki matuka
domin ya samu matarsa cikakkiya
kuma kamilal mace, wannan ba
karamin kara mata daraja yayi a
idanuwansa ba.
87
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СЕTА
Washe gari ruwan dumi ya cikal
mata kwamin wanka domin(vgasa) jikinta sosai, ta ko ji dadin hakan matuka. λυλε καυμε
Tsaf ta fito cikin wata doguwar
rigar shadda kalar purple wacce aka yisd
wa aikin duwatsu daga Dubai,uyarı
amsheta matuka ta kara wani kyau da
sheki ga kamshi na tashi mai daukar
hankali. Bisa abin sallah ya taddatarı bayan ta ida tana zaune bisa kai batar
ko motsa ba, shima yayi kyau cikinio
farar shadda doguwar riga da wando
sai sheki yake yi. ment isri isb
dibse isilA
Ya sakar mata murmushin farinb
ciki da tsantsar kauna, da siririyar
muryarta mai dauke hankalinsa sta
amsa masa martanin murmushin dabi
88
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
cewa "Barka da safiya Alhaji." Ya
sake fadada murmushinsa yace mata
"Barkanmu dai Hanan ya bakunta?"
Murmushi kawai ta yi bata iya
amsa masa kanta na sunkuye, ya sake
sakin murmushi cike da jin dadi yace
"Hanan kina burgeni matuka, kunyarki
na matukar kayatar dani domin kara miki
ado take yi."
Ya ajiye mata plate dauke da
farfesun kaza da kuma shayi a kofi mai
dumi ya ce mata "Ga shayi nan na hado
miki ga kuma farfesun Kazan an ki daure
ki cinye duka sai ki sha wannan
دو maganin." Ya mika mata Brustan da
Ampeclos, sannan ya mike gami da fadin
وو" Ina zuwa.
A hankali ta dinga kurbar shayin
zuciyarta na dawo mata da abin da ya
faru gareta daren jiya, cikin ranta take
89
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
fadin "Lallai ta dace da miji, tabbas
Alhaji ya san ta kan soyayya, ya iya
tatti da kulawa da tausayawa, ashe
aka soyayya take dadi?"
Da ace ta san haka rayuwar aure
take da dadi da tun asali bata dinga
gudun auren ba.
Da wannan tunanin ta kammala
karya kumallo, a daidai lokacin Alhaji ya
turo kofa ya shigo da sallama, suka yi ido
hudu suka yi murmushi, Alhajin yace
"Ince ko dai kin cinye tas kin sidi
kwanon?" cike da zolaya yake fadin
hakan.
Ta sake yin murmushi ta ce masa
"A'a na dai ci abin da ya sauwaka. Ya
sake fadada murmushinsa yace mata
"Hana zan fa yi miki dura idan baki
cinye ba" kanta na sunkuye bata iya ce
masa komai ba, dai dai kunnenta ya
N
90
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
matso ya saita bakinsa cikin taushin
murya yace mata "Hanan ina matukar
kaunarki, kina daukar hankalina kina
sanyani nishadi kin tafi da imanina gaba
daya, anya kuwa zaki barni na dinga
tafiya nemo mana na tuwo kuwa Hanan?"
Maganganun nasa sun matukar
birgeta sun ratsa kwanyar ta, ji take yi
tamkar ita kadai ce tafi kowacce mace
sa'a a duniya. Haka suka 6ata lokaci suna
nunawa juna kauna, har said a baki 'yan
uwan Hanan suka fara zuwa, sannan yayi
Karfin halim barin sashen nata ba don
ransa na so ba.
ASALIN ALHAJI SADIK
To kamar yanda muka ji daga bakin
Baba Malam, Alhaji Ahmad maikamshi
shine Kakan Alhaji Sadik wanda ya haifi
mahaifinsa mai suna Alhaji Muhammad.
91
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
Alhaji Muhammad sanannen dan kasuwa
ne wanda kasuwancinsa ya bunkasa ba a
cikin gida Nigeria kadai ya tsaya ba hard
a kasashen waje, Babbar sana'arsa ita ce,
safarar turare daga kasashen waje zuwa
gida Nigeria, wannan sana'a tasa ta
bunkasa matuka domin ya kasance babu
inda ake zuwa neman turare kowanne irin
nau'I sai gurinsa tun daga kan diloli har
masu karamin jari.
Alhaji Muhaimınad ya kasance
shine babban da agurin Aihaji Ahmad
wanda matarsa uwargidansa ta Haifa
masa, don haka ya dorashi akan komi na
sana'arsa har ta kai ta kawo ma duk kasar
da zai fita das hi yake fita, domin so yake
yi ya bude ido da kasuwancin sosai idan
girmaya-zo masa shi kuma sai ya huta.
Shekarar Alhaji Muhammad talatin
da biyar a duniya aka aura masa wata
92
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
'yar uwarsa ta nesa mai suna Sauda,
suna nan zaune cikin rufin asiri, Allah
ya azurtasu da samun da namiji wansa
suka sanyawa suna Sadik.
Kasancewarsa babban Jika yasha
gata matuka a gurin Kakansa Alhaji
Ahmad, domin bai bar mahaifinsa ya yi
komai na haihuwarsa ba, haka kuma ya ci
gaba da hidima dashi har sai da Allah ya
karbi rayuwarsa.
Shekarar Sadik bakwai a duniya
Allah ya kawo wani mummunan al'amari
na hadarin jirgin sama wanda ya hada da
Alhaji Ahamad da babban dansa
Muhammad a kan hanyarsu ta zuwa india
daga nan zasu wuce France domin shigo
da turaruka.
Ba karamin tashin hankali suka
shiga sakamakon wannan mummunan
93
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
rashi da ya samesu, wanda ya haddasa
Kakar Sadik da mahaifiyarsa yin takaba.
Sun samu shekaru cikin wannan
jimamin sannan daga bisani suka
dangana, an raba gado kowa ya samu
abin da ya samu, Kakar Sadik bata bari
gadonsa yaje hannun ko da mahaifiyarsa
ba, said a Allah ya say a isa shekarun
hankali sannan ta danka masa dukiyarsa,
ba a dade ba itama ta ce, ga garinku nan.
Ya ji mutuwar Kakarsa domin ya
shaku da ita, wannan yasa dole ya dawo
hannun Mahaifiyarsa gaba daya ba don
ya so ba, domin mahaifiyar tasa tuni ta yi
aure har ma ta haifi diya mace.
Haka suka ci gaba da rayuwa, shi
kuma ya durfafi kasuwanci ba kama
hannun yari músamman da ake ya gaji dukiya mai tarin yawa, don haka ita ya
juya ya fara neman arziki.
94
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
Allah ya sanya masa albarka a
kasuwancin domin yana faraway ya
dinga samun alkairi mai dinbin yawa.
Bayan shekaru sunyi ni sa mijin Babar
tasu yayi wata rashin lafiya kwanza
takwas a asibiti yace ga garinku nan,
wannan ya tilastawa Sadik daukar nauyin
komi na mahaifiyarsa da na kanwarsa,
wannan ya sanya yana matukar ji da
mahaifiyar tasa sam baya son abin da zai
6ata mata ko kaďan.
TUSHEN KOMІ
Kwance yake a katafaren gidansa
wanda za a iya cewa na mashahurin mai
kudi ne, dakin da yake kwance ciki ya
wadatu da kayan more rayuwa ga
wadataccen sanyin A.C a dakin, gaba
raba ce kawai take sauka ta ko ina, ga
kamshi ya wadata cikin dakin, cikin
baccin nasa ne mai cike da rudani yake
95
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
ganin gidansa naci da wuta sosai, yana
tsaye kofar gidan cike da jimami da
tashin hankali ya kasa aiwatar da komi,
sai makwaftansa ne ke yin iya kokarinsu
wajen kasha wutar, amma kuma idan
suka zuba ruwa tamkar fetur suka zuba
nata sai kara tsiri takeyi.
Motsi yake yi bisa gadonsa
sakamakon wannan mummunan mafarki
da yake yi, sau biyu yayi juyi sannan ya
farka firgigit tamkar wanda aka tsikara!.
Sai me? Hayaniya ya jiyo a bakin
kofar dakinsa, ya saurara yana jin abin da
yake faruwa. Muryar Lami ya jiyo a sama
cikin fada da hakikancewa tana fadin
"Wallahi Sadiya duk nacin ki baki isa ki
shigo mini dakin miji ranar girkina ba."
A daya bangaren kuma ya jiyo
Sadiya na masa mata da fadin "ban
fahimce ki ba me kike nufi ba Lami, ni da
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
dakin mijina kice ban isa na shiga ba?
Kika san uzirina da ke tafe dani gurinsa?"
Lami ta yi shewa gamida tafa
hannu "Uzuri? Allah yasa kece tattabara
karewar aure wallahi ba zaki shiga ba,
domin kuwa yau ikona ne sai ki bari sai
ranar girkinki sannan kya gaya mmasa ko
ma menene amma banda yau din.
Ran Sadiya ya yi matukar 6aci
takai makura a fusata don haka kai tsaye
ta nufeta tana shirin tureta tana fadin "To
wallahi baki isa na uban kuturu ma ya yi
kadan balle na makaho, kai tsaye ta
dauko wuyanta suka fara kokawa."
Mero c eta nufo su. da sauri
sakamakon hayaniyarsu da ta jiyo tana
fadin "kai kai kai, wai mi ke faruwa ne?
nake ta jin hayaniya haka taki ta kare?"
Sadiya da ke rike da wuyan Lami
ta waigo ga Mero tana fadin "Wai
97
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
wannan 'yar rainin wayon ce take neman
shiga dakin mijina bayan bata san uzurin
da zai kai ni gurinsa ba"
Da sauri Lami ta amshe da
hannunta na, tokare a jikin kofa tana
girgiza cike da tsiwa "Wallahi babu mai
shiga yau sai dai ayi 'yar rotse-rotse a
gidannan akan na daba dama shigar min
don kuwa nima ba a barina na shigarwa
kowa ehe."
Mero ta maida kallonta ga Sadiya
ta ce, mata "A gaskiya Sadiya ba kiyi
gaskiya ba, ko nice b azan yarda a shigar
min, haka kawai da sassafen nan mijinka
yana bacci ko tashi bai yi ba azo a shigar
maka gurinsa ai dda matsala, ki bari dai
ya fito sai ki sameshi a waje ki gaya masa
ko menene.
Bin bayan da Mero ta yi shi ya
kara mata karfin gwiwa don haka ta sake
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
kwabe baki ta saki tsaki sannan ta ce, a ki kyaleta mana karta bari ya fito, ke
wallahi idan na ga dama ma ko a wajen b
azan bari ta ganshi ba sai dai ta kirashi
waya."
a
Ran Sadiya ya kara baci cike da
mamaki ta kalli Mero ta ce, "Af kema
mara mata baya kika yi? Lallai
munafuncin gidannan kullum karuwa
yake yi." Ta girgiza kai sannan ta ce,
"Yanzu kuwa za ta ji a jikinta." Da sauri
ta sake damkota suka kama kokowa.
Merro kuwa sai ta koma gefe tana kallonsu tana fadin "Babu wacce zata
hana, idan kukaji ciwo a jikinu zaku daina ne, don nima ba wuce ku yi min na
yi ba, kuma ko na hanaku ba zaku hanu
ba." Basu Ankara ba suka ga Alhaji
Sadik tsaye a gabansu, ransa ya dugun
99
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNА СЕ
zuma, cikin karaji da tashin hankali yake
Magana.
"To sarakan bala'i da masifa
sarakunan tashin hankali, dan masifa da
sassafen nan kun hanani na huta, yan
zunnan a cikin baccina nake mafarki ana
gobara a gidana, ana ta zuba ruwa amman
wutar taki mutuwa, ashe bala'I da
masifarku ake nuna mini wacce kowa ya
kasa maganceta, yanzu ku ko kunya ba
kwaji a dinga jiyo masifar ku a
makwabta?"
Zasu yi sauri su saki juna a tsorace
su koma su tsaya kai a sunkuye da
alamun rashin gaskiya tattare da su. Mero
ce ta yi tsagal ta ce, "Allah ya sa dai ni
babu ruwana, ni ma zuwa nayi na rabasu,
naga abin ya fi karfina, wai akan shigowa
dakinka ne suke wannan tashin hankalin
وو da sassafen nan.......
100
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA Е
Da sauri ya katseta a fusace cikin
daga murya "Rufe mini baki dalla, har
akwai wata abar yabo a cikin ku wacce za
a ce gara ita?"
Ya maida kallonsa ga Lami da
Sadiya sannan yah au yi musu gargadi da
fadin " Ku kuma sarakan rashin mutunci,
shine don ku tozarta ni kuke min masifa
haka da sassafe akan shiga dakina kawai,
to daga yau duk ku ukun bana bukatar
ganinku a dakina, kuma ko abinci kuka yi
ku cinye abin ku ku da 'ya'yanku ni bana
bukata."
A tsorace Lami ta bude baki za ta
yi Magana ya yi saurin gwaleta da fadin
"Rufe mini baki, bana bukatar maganar
kowa daga cikin ku, ku bace min dagani
yan zunnan shashashai kawai."
Dukkansu jikinsu ya yi sanyi
gwiwoyinsu sam babu kwari suka juya
101
ALAWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE
sim-sim suka nufi waje, shi kuwa Alhaji
cikin dakinsa ya koma yana faman huci
tamkar zaki.
Haka zai zi ya wucesu a tsakar gida
cike da dacin rai hannunsa rike da
mukullin mota fuskarsa sam babu sauran
annuri, idanuwansa tuni sun kada sunyi
jawur, kai tsaye wajen motarsa ya nufa ya
tadata a fusace ya fice da gudu.
Ita kuwa Lami tamkar dama jira
take ya fita ai kuwa sai ta nufi kofar
dakin Sadiya wacce ta nufi sashenta
tuntuni, ta tsaya a kofar sashen nata ta
rike kugu tana fadin " Ina kike munafuka
kin shige daki kina dariyar farin ciki ko?
Burinki ya cika kin tarwatsa min kwanaki
na d azan yi da mijina, dama abin da kike
wa bakin ciki da kishi kenan, to wallahi
ina tabbatar miki da cewar bashi kia
6
102
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
dauka don lowa yaci tuwo dani wallahi
miya yasha mai barkono ma kuwa."
Da sauri Sadiya ta bude kofa ta fito
tana huci, ta galla mata harara sannan ta
amsa mata da cewa "Ke Lami ki dubeni
da kyau, kin san baki isa nayi maki
kyashin akan miji ba, domin banga abin
da zan yiwa kishin ba a tare da ke."
Ran Lami ya kara baci, ta yi
dariyar bacin rai da mugunta sannan ta
ce, "Shiyasa naga kina bakin ciki da ranar
kwanana har kina kasa bacci, da sassafe
kina shigo mana, wa ya sani ma ko har
laße kike yi mana?"
Sadiya ta kara fusata ta damko
wuyan Lami sannan ta ce, "Yanzu kuwa
za kici na Jaki." Dukkansu zasu fara
kokowa kowacce na kokarin huce
haushinta jikin 'yar uwarta. Mero dake
shara a tsakar gida ta jiyo su ta nufosu
103
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CЕ
hannunta rike da tsintsiya tana fadin "Af
ke Lami baki san Sadiya tana yi miki
labe ba? Ai kullum in kina girki a tafe
take kwana, ta je ta labe ta dawo ta shiga
daki, haka take fama har gari yaw aye,
abin da tyasa bana gaya miki sabida bai
shafeni ba kar ace na hada fada.
Da kyar ta kwato kanta daga
hannun Sadiya ta nufi inda Muciya take
ta dauko ta nnufo Sadiya da ita gadan gadan tana huci tana fadin.
"Wallahi tunda kika: tarwatsa min
farin ciki na yau sai na tattaka ki."
Da sauri Sadiya ta dauko Rodi ta
nufo Lami itama tana fadin "Kafin ki
illatani ke, ni bara na fara illataki mu
zuba dan halak ka fasa..."
Sallamar Inna Laure ce ta katse ta,
tana ganinsu da makamai a hannu, ta nufi Sadiya a rude ta kwace Rodin tana fadin
104
ALAWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, Sadiya
me ya kai ki ga aikata haka? Ai wannan
ba shine makaminki ba sam bai dace
dake ba, fada da kokawa ai ba naki ba ne
Sadiya."
A fusace Sadiya ta ce, "Inna
wannan 'yar rainin hankalin ce da
sassafen nan take neman bala'I dani ta
dagulamin lissafi." Lami ta kalleta
shekeke cike da tsiwa ta ce, "Ga rainin
hankali nan a tare dake, da sassafe an zo
mana gida ko karyawa ba mu yi ba. Sai
yanzu na sake tantance inda kika koyi
zuwa dakin mijin mutum da sassafe ashe
iyalan sammako ne ban sani ba."
Da sauri Mero ta amshe "Kamar
kin shiga zuciyata cam abin da nake so na
ce kenan, bamu isa mu sake a cikin
gidanmu ba sai a doka mana uban
sammako haka."
105
ALAWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE
Lami ta harareta ta gefen ido
gamida kwabe baki tana nunata da
muciyar dake hannunta "Dallacan rufe
mini baki, ca na yi maki'ina neman mai
tare mini zaki wani sako mini bakinki, ki
kalleni da kyau babu wanda nake shayi a
gidannan warki nake daidai kugun kowa
don haka ki kama bakinki, tunda ba dole
akeyi ba, tun dazu sai wani shisshigewa
kike yi kina so ki ce zaki tare mini. Ta
saki wani wawan tsaki.
Ita kuwa Mero tsayawa kawai ta yi
tana kallonta, ta tabe baki ta girgiza kai
sannan ta koma gefe tana kallonsu.
Itama dai Inna Laure mamakin ne
ya cikata kallonsu kawai take yi domin
bata san me zata ce ba.
Sadiya ce ta fizge hannunta da ga
hannun Inna a fusace ta nufi Lami tana
fadin "Mahaifiyar tawa kike gayawa
106
ALAWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA СЕ
haka? Yau idan banga jini ya yi miki ado
a jikinki ba hankalina ba