suke tafiyar da al'amuran su, daga shi har Naja'atu basu zafafa ba, basu dauka da zafi ba, cikin ruwan sanyi suke nuna ma junan su kauna,
63
sai taga sun fi dacewa da junan su, akan Daddy da
Naja'atun ke kwakwa, gani take ma Khalid yafi
sonta akan Daddy.
Da suka fito Naja'atu tayi mshi rakiya, aya ce
"Yanzu yaushe kike ganin ya dace muje
Katsinar?" Tayi murmushi tana kallon shi, ta ce
"Idan ka samu lokaci ko?" Ya ce "To aini duk
lokacina naki ne Naja'atu, kuma duka baifi sáti
biyu ya rage mani ba in tafi, kinga cikin wannan
lokacin ne ya kamata muje, idan Baba ya amince
mani shi kenan, idan kau bai amince ba, to
gaskiya sai dai inyi hakuri da tafiyar, don wallahi
kin fiye mani tafiyar."
Naja'atu tayi murmushi ta ce "Insha Allahu
ma ba zaya ki ba." Ya ce "To Allah ya nufa, sai ki
zama cikin shiri, ranar asabar sai mu fitada wuri
mu isa washe gari sai mu dawo." Ta ce "Shi kenan
zani sanar da Mummy." Su kayi sallama ya shiga
mota. Yana shirin fita sai ga Daddy ya iso, don
haka ya fita ya isa inda ya aje motar shi. Daddyn
ya fito suka gaisa, sam bai nuna mashi komi ba,
suka tako har wajan motar shi ya shiga, sannan ya
daga mata hannu ya fita. Yayin da shi kuma
Daddyn ya shige cikin gida. Itama sai ta tabe baki
tabi bayan shi zuwa cikin gidan.
NE
an
ga
cik
shi
SOS
bas
Suna nan falo tare da Zainab ya fito ya
zauna, bai yi ma kowa magana ba, sai ma ya rinka yal
64
bata dariya, fushin nashi har ya wuce, kuma ita bata san laifinta ba, to daga ita har Zainab din babu wanda ya kulashi. Zainab ta juyo tana kallon Naja'atu, ta ce "Wai yaushe ne tafiyar Dr?" Naja'atu ta ce "Wai fa duka saura sati biyu." Та се
"Sai kice tafiyar ta matso, amma gaskiya zakiyi
missing dinshi." Naja'atu tayi murmushi ta ce "To
ya na iya Zainab? Amma ai ya ce kwas din duka
wata tara ne, inda rai sai kiga kamar gobe ne."
A hankali Daddy ya juyo yaa kallon ta, cikin
sa'a itama ta kalle shi, sai tadauke kanta kamar
bata san yanayi ba, suka ci gaba da hirar su tana
sanar da Zainab cewa ranar sabar za suje Katsina
tare dashi. Zainab ta ce "To gaskiya dani za'aje,
yaushe rabona da zuwa Katsina? Wallahi har na
manta." Naja'atu ta ce "Ai kau naji dadi, kwana
daya kawai za muyi mu dawo."
Jikin Daddy yayi sanyi, ya rinka kallon
Naja'atun yana son ya isar mata da wani sako,
amma fir taki bashi dama, yanzu laifin ta yake
gani sosai, bai san yana kaunar yarinyar ba sai
cikin 'yan kwanakin nan da suka samu rashin
jituwa, daidai da abinci baya samun zama ya ci
shi cikin kwanciyar hankali, abun ya dame shi
sosai, yana son yayi mata magana amma taki
bashi fuska, yana wahala sosai akanta, karshe ji
yake yi ma idan har zaya same ta to wallahi zaya
65
iya yin hakuri da Faridar kanta, yanzu ne yake
ganin banbanci tsarin rayuwar ta, wasu abubuwa
da take yi da sunan wayewa, shi bai dauke sui
waycwa ba, kuma bata daukar gyara, idan anyi
mata, ga rashin kunya, duk maganar da ta fito
bakintga zaya fada mashi, akasin Naja'atu, wadda
komi nata yake tsab-tsab, ga nutsuwa da hankali,
idan tana yi mashi magana muryar ta kasa-kasa,
tana kwantar da kanta sosai gare shi, gashi ta iya
tattalin shi, yanzu haka tunda ta daina zama tare
dashi yaji ya tsani komi, hatta abinci baya iya
zama ya cishi cikin dadi.
Ya runtse idanuwan shi, shi kadai yasan
yanda yake ji cikin zuciyar shi, ya kasa daurewa.
A hankali ya zuba ma Naja'atu ido, dan hankalin
na kan Zainab suna dariyar su, ya kirta "Naja'atu."
Ta juyo a razane tana kallon shi. Rabon da taji ya
anbaci sunan ta har ta mance. Ya ce "Jeki debo
mani abinci." Ta zuba mashi ido cike da mamaki,
sai kuma taji tausayin shi. Bata ce komi ba ta tashi
ta nufi teburin cin abinci, ta zubo cikin filat ta zo
ta aje kan tebur, sannan ta kuma kicin ta dauko
mashi kwalin lemo da kofi ta aje ta jawo teburin
gaban shi. Sannan ta dube shi ta ce "Gashi." Ya
zuba mata ido. Taji wani iri a jikin ta, sam ta kasa
dauke idanuwan ta akan shi tana mamakin irin
ramar da ta lura yayi, yayin da shi kuma ya kara
66
marairaice mata, duk sai tausayin shi ya kamata,
bata yi magana ba ta koma ta zauna.
Ya tusa farantin abinci bai fara ci ba. Zainab
ta mike zata shiga daki, itama Naja'atun ta tashi.
Ya juyo yana kallon ta, ya ce "Ina zaki?" TТа се
"Daki." Ya ce "Zauna magana za muyi." Zainab
tayi tafiyar ta. To sa dai ita kantga har mamakin
irin damuwar da ta lura ya shiga take yi. Naja'atu
ta koma ta zauna sam ba zata iya yi mashi
gardama ba. Ya ci gaba da kallon ta yana jinjina
kai, sannan ya ce "Naja'atu baki tausayina ko? So
kike yi sai kin jagoranci rushewar rayuwa ta? Ki
kalle niu sosai, haka nake da? KI duba yanda nake
ramewa, kuma ba komi bane, zafin da kika hada
mani ne, na shiga damuwa saboda ke, amma baki
damu ba, kin juya mani baya." Zuciya ta ta karye
sosai, hawaye suka cika mani ido, ta rinka
sharewa, tana so ta danne zuciyar ta, bata san
yanda zata yi mashi bayani ba ya fahimta, kuma
ita tana fa ganin laifin shi tunda shine ya fara yin
fushi da ita.
Muryar ta kasa-kasa ta ce "Kayi hakuri." Ya
zuba mata ido, sai yayi murmushi ya ce "Shi
kenan, amma don Allah kada ki kara yi mani irin
haka, na wahala da yawa." Ya fara cin abincin shi
yana kallon ta. Ga mamakin shi sai da ya cinye
shi tas, yayi mamaki kwarai, saboda cikin
67
kwanakin nan ko rabin shi baya iya ci. Naja'atu
hankalin ta ya kasu kashi biyu, bata son Mummy
ta fito ta same su tare, haka nan bata iya tafiya ta
barshi ranshi ya 6aci. Don haka ta dan zauna yana
tayi mata korafi, tare da lissafa mata irin
adamuwar da ya shiga. To Naja'atu dai ta dauki
laifi ta rinka bashi hakuri, a ganinta duk abin da
zata fadi mashi ba zaya yi tasiri ba, lokaci ya dan
ja ta fara hamma, barci ya taho, don haka ya
sallame ta ta tafi, akan sharadin cewa da safe
kafin ya fita ofis zta fito ta bashi kalace. Bata da
zabi, don haka ta amince.
Bayan kwana biyu, su kayi shirin tafiya
Katsina, Mummy ta cika ta da abun arziki da zata
kaima iyayenta, to shima a 6angaren shi Dr
Khalid yayi rawar gani, ya sami turamen atamfofi
manya da bandiran shadda, da zaya kaima su. Su
uku su kayi tafiyar, Daddy kallon su kawai yake
yi bai nuna damuwar shi ba, saboda yasan dole
Khalid din tafiya za yayi ya barshi da Naja'atun,
kuma dole tafiya ta canja salo, yana cikin gida
suka tafi amma bai fito ba.
Tafiya a nutse cikin kwanciyar hankali, basu
isa Katsina ba sai yamma likis. Khalid ya ce "Sai
fa kinyi mani jagora, kin san ni makaho ne cikin
garin, an samu ci gaba sosai." Naja'atu tayi
murmushi ta ce "Ai mu ba abin da zamu cewa
68
shugabannin mu sai dai addu'a da fatan alkairi,
nan ma kake gani, idan kika shiga wani wajan sai
dai kiyi shiru." Khalid ya jefeta da wani irin
mayataccen kallo, ya ce "To ai ba gun Katsinar
kadai ya hada ba, har da mutanen cikin ta, ni kam
na shaida da haka." Sai tayi murmuhi ta ci gaba da
yi mashi kwatance har kofar gidansu.
Kamar ko da yaushe kofar gidan an share shi
fes-fes, tun jiya dama ta kira Mas'ud ta sanar dashi
zuwan su, dan haka dukkan shirye-shiryen da
suka kamata sunyi. Mas'ud yana gida, dan haka
suna tsayawa ya fito ya tarbesu, yanda ya lura da
tsabta, kamun kai da halin dattaku na masu gidan,
sai yaji ya kara son Naja'atu. Cikin falon su
Mas'ud aka shiga dashi, yayin da su Naja'atu suka
shiga cikin gida, ana ta murnar zuwan su. Sai da
aka nutsu, sannan Naja'atun da kanta ta shiga
cikin dakin Baban su ta sanar dashi komi game da
Dr. Yayi murna kwarai, yana sanya ma Hajiya
albarka, musamman yanda yaga Naja'atu ta canja,
tayi kyau sai kyalli ta keyi kamar tana rayuwa a
turai, ga kuma lbari mafi dadi tazo mashi dashi na
aure, burin shi kenan ko da yaushe addu'a Allah
ya bata miji dan albarka.
Ya ce"Babu damuwa ta shiga dashi." Sai ta
dauki mayafin ta, ta fita ta same shi yana dakin su
Mas'ud, Rabiu uban 'yan hidima, ya kawo mashi
69
ruwa na roba da lemon kwali sun sake suna ta
hira. Ya dube ta tayi murmushi, ta ce "Ka shigo
ku gaisa da Baban yana gida." Ya zuba mata ido
ya ce "Naja'atu har ciki?" Tayi dariya ta ce "Тo
meye? Shifa Baba ba ruwan shi simple man ne."
To sai ya samu kwarin guiwa, ya dauki hular shi
da ya cire ya maida bisa kanshi, ya taso ya biyo
bayan ta har cikinb dakin Baba. Bayan sun gaisa
itama Inna ta lullu6o hijabinta ta shigo ita da
Naja'atu, sai kayi tsammanin cewa yayarta ce, ba
ita ce ta haife ta ba. Hankali kwance ya nutsu yana
yima Baba bayanin abin da ya kawo shi. То
gaskiya da farko Malam Abdu yaso ya dan turje,
yana jinjina watanni tara a ranshi, kila ma sai an
cika shekara, to sai dai lura da yanayin yaron ta
sanya ya amince yayi mashi fatan alkairi. Ya jima
yana yi masu nasiha, sai Khalid ya kara son
dattijun yana tuno nashi mahaifin.
Har dare yana gidan sun karbe shi hannu
bibbiyu, nan yayi hira sannan ya tafi masauki,
yayin da Zainab da Naja'atu su kayi kwanciyar su
dakin Inna, bayan sun sha hirar su.
Washe gari da ya iso, kalace kadai yayi su
kayi sallama, banda iyayen kayan da ya zo dasu,
ya kuma kawo kudi ya kara masu, hatta su
badiyya sun sheda. Baba ya rinka sanya mashi
albarka, idanuwan Khalid suka yi jajir, da ya tuno
70
cewa mahaifin shi bai mori arzikin shi ba, hakа nan yaji nashi, na samun albarkar su, insha Allahu zaya riki surukin shi da hannu bibbiyu, albarkar irin su bin mutum take yi.
Ta Kano suka bi ya nuna ma kannen shi Naja'atu. Suma sunyi murna da ita, sannan suka dauki hanya zuwa Abuja. Cikin farin ciki da kwanciyar hankali, sai yaji kamar an sauke mashi wani nauyi.
Don haka da karfin shi ya ci gaba da shirin
tafiyar shi, ba tare da tunanin komi ba, yasan dai
Naja'atu ta zama tashi, ko ba komi Baba ya tabbatar mashi da haka. Tun ana saura kwana biyu
tafiya ya zo su kayi sallama ta karshe, saboda
washe gari Lagos zaya tafi daga can zasu tashi, ya rinka nanata ma Naja'atu kalma daya, cewa ta jure
duk runtsi ta jira shi, ta dasa ma zuciyar ta cewa
shi kaďai take so, shi kuma zaya cika mata
alkawari. Sai ya rinka bata tausayi, ya shiga damuwa sosai, don haka ta ci gaba da karfafa
mashi züciya, ta ce "Insha Allahu babu abin da
zaya faru."
Washe gari da ya zo, har da su aka tafi yi mashi rakiya filin jirgin sama, sai lokacin Naja'atu taji kuka, daga shi har Zainab suka rika bata hakuri, shi kanshi ji yayi kamar ba zaya iya tafiya ya barta ba, duk ya rikice da kyar ya shawo kanta
71
tayi hakuri. Tana tsayc tana kallon shi har ta daina
ganin shi, sai ta girgiza kai, suka koma gida, inda
ta tarar da wata rigimar jikakka tana jiranta.
To ku biyoni cikin littafi na uku dan jin
yanda zata kaya. Shin Khalid din zata jira? Ko
kuwa Daddy zaya rinjaye ta. Mu hadu cikin
SIRRIN ZUCI na 3.
Masha Allah
Taku
Aunty Uwanin Kankia
72
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels