Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
Ya yi murmushi ya ce, "Doctor ne, na ce ya shigo ciki, ya ce a'a." Kunya ce ko mi, duk sai ta ji ta takura gashi Mummy na wajen, don haka ta kasa ce mashi komi. Mummy ta yi murmushi ta ce, "Wai ke Naja'atu wace iri ce? Idan ba ki sake a gidan nan ba, sai yaushe? Tashi ki shigo dashi don mi za ki rinka aje mutum waje? Wannan ba kima ba ne." Jikinta ya yi sanyi, ta mike ta shiga cikin daki, ta dauko mayafi ta fita zuwa wajen. Yana tsaye jingine da mota, rike da waya yana magana, don haka da ta isa sai ta tsaya gefe guda minti daya ya yi sallama ya rufe wayar yana kallonta, sai suke yi murmushi ba ki daya ya се, "Naja'atu yaya gari.?" Ta ce, "Alhamdulillahi, ka yini lafiya.?" Ya yi murmushi yana kallonta ya ce, "Lafiya lau sai alkairi." ta ce "ka shigo daga ciki." Ya ce, "Tun yanzu Naja'atu.?" Ta yi murmushi ta ce, "To meye? Mummy da kanta ta ce ace ka shigo." 16 Ya yi murmushi gaskiya ya ji dadi har cikin ranshi, alamun samun nasara kenan." Don haka ta shiga gtaba yana biye da ita har cikin falon, yau kuma ya yi shiga sosai, ta boyel fari sol, yana daukar ido, shigar ta sauka kasa sosai, da hula kube, ya yi kyau daidai gwargwado ba ya da makusa don haka itama Mummy ta yaba dashi, suka gaisa cikin mutunci, sannan ta tashi ta koma cikin daki, ba'a jima ba ki kira Naja'atu ta shiga, ta ce "Ki shiga kicin ki samo mashi abin da zaya ci." Ta yi murmushi ta fito ta bashi hakuri, sannan ta shiga kicin cin ta yi tsaye tana tunanin me zata ba shi, sai ta bude firij ta fiddo lemun kwali ta aza kan faranti da kofi ta bude wani bokiti ta debo cake din da suka yi ranar demick ta zuba a filed ta hada ta dauko ta fito. Yana zaune hankali kwance ta yi sallama ta aje gabanshi bisa tebir, ya zuba mata ido a hankali ya ce "Na gode." Ta yi murmushi ta duka tana fasa lemun, ta zuba mashi a kofi sannan ta koma ta zauna ya dube ta farin ciki cike da zuciyarshi, ya ce "To ai ni Naja'atu duk kin rikita ni, na ma rasa ta ina zani fara." Та се, "Me aka yi.?" Ya jinjina kai ya ce, "Meye ma ba'ayi ba, kin karrama ni da yawa na ji dadi kuma na gode Allah yasa tafiya ta yi tsawo." Ta ji nauyinshi tana murmushi ya dauki lemun yana kurba a hankali, sai ya rike kofin ya kirata. "Naja'atu." Ta dago kai tana kallonshi, ya ce "Kina ganin kin amince dani in ci gaba da zuwa.?" Ta yi shiru, ya ce "Magana za ki yi, ni dai Allah yasan manufata akanki, fatana Allah 17 S ya hada kanmu in ga mun zama mata da miji, muna raya sunnar Manzon Allah, don haka ki saki jiki muyi magana ta fahimta, kada ki ji shakkun komi ki fito fili ki fadi mani abin da ke cikin ranki, ni kam na gamsu dake kuma nasan nayi zae mai kyau, ban sani ba ko ke kina da wani ra'ayin daban." Ta yi murmushi ta ce, "Haka ne, sai dai kamar yarda na fadi maka ina son mu samu lokaci mu fahimci juna, kafin maganar aure ta shigo, kasan komi a hankali yafi." Ya ce, "Haka ne, yanzi kina jin in ci gaba da zuwa ko kuwa so kike yi in daga maki har sai kin gama nazarin.?" Ya tsare ta da ido, sai taji nauyinshi, ya cika saurin karya mata zuciya, ta yi murmushi ta ce, "Babu damuwa, zaka iya zuwa." Daidai lokacin Daddy ya kunno kai cikin falon, bai lura da abin da ke faruwa ba, sai da yazo tsakiyar falon, sannan yaga Dr. Khalid, bai san dalili ba, sai ya ji wani irin faduwar gaba da tsananin kishi. Dr. Khalid ya mike da sakin fuska ya mika mashi hannu suka gaisa haka nan ba don Daddyn yaso ba, cikin hikima ya yi satar kallon Naja'atun ya sakar mata wata muguwar harara, sai tasha jinin jikinta, bai ce mata komi ba, ya raba su ya shigc dakinshi, sai ta saukar da ajiyar zuciya, tana kallon Dr. Khalid shima kallonta yake yi bai ji dadin yarda ya karbe shi ba, ya koma ya zauna yayin da wajen ya dan dauki shiru, sai ya yi gyaran murya ya kirata "Naja'atu." Ta zuba mashi ido ya ce "Kiyi hakuri da ni kada ki yi tsammanin ina neman takura maki, ki fadi mani yaya kikc da wannan 18 mutumin.?" Ta yi murmushi ta ce "Daddy dan gidan nan ne." Ya ce, "Kc fa.?" Ta zuba mashi ido, ta ce "Ni ce bare a gidan, mahaifiyata ce 'yar'uwar Mummy, don haka ta dauko ni ina zaune tare da ita asalinmu 'yan Katsina ne, kamar yarda ka sanar dani mahaifanka Talakawa ne, to nima haka nawa suke, mahaifina Masinja ne, sai dai ni ban sha wahalar rayuwa ba, saboda daidai gwargwado mahaifinmu tsaye yake kanmu, koda yaushe, don haka ba zani ce rayuwa ta yi mani wahala ba, yanzu haka ina da takardun shaidar kammala karatuna na NCE, nice babba a gidanmu, haka sauran 'yan'uwana ma suna nasu karatun, cikin wannan yanayin ne Mummy ta roki alfarma aka bata ni ina zaune tare da ita, saboda cikin 'ya'yanta mata Zainab ce ta rage bata yi aure ba, tana karatu a A.B.U Zaria. Kuma gaskiya ina jin dadin zamana tare dasu tana da fahimta kamar yarda ka gani." Yayi dariya yana jinjina kai, ya ce "Lallai kam na gani kuma na yaba, haka nan naji dadi kwarai, da ya kasance matsayinmu daya, a kalla zaki ga kima ta haka nima za ni ga taki saboda wani lokaci da kaina nake tunanin "Anya ban kai kaina inda Allah bai kaini ba, karfina kasancewata dan talakawa." Ta yi murmushi ta ce "To ai ni ma 'yar talaka wance kamar ka, kuma kana manta wani abu, yanzu fa babu matsiyaci sai wanda baya da ilimi, baya da zuciyar nema, kai kau gashi daidai gwargwado kana da na rufin asiri, kuma tsaye ka ke koda yaushe kana neman 19 na kanka, kaga wannan shi ne arzuki." Ya yi dariya, ya gamsu da bayaninta, sai ya ji ta kara shiga ranshi, yarinyar tasan ciwon kanta, kuma tana da hankali sosai, irin matar da yake nema kenan, Allah ya amshi addu'arshi, ya hada shi da ita, sai ya fara addu'a akan Allah ya ida mashi nufin shi. Ya gyara zama yana fuskantar ta, ya ce, "Sai abu na biyu, tsakaninki da Allah kada ki 6oye mani komi, shin kin taba soyayya.?" Naja'atu ta dube shi tar cikin ido, tambayar ta dan yi mata nauyi, sai dai ya daure ta da igiya, kuma ma ai fahimtar juna suke so suyi, don haka ta saki jiki dashi sosai, tana kallonshi ta ce "me ye soyayya.?" Ya yi dariya ya ce, "Kada ki maida kanki Karamar yarinya Naja'atu, a tunanina yanzu ko yarinya 'yar Primary aka yi ma wannan tambayar zata iya bada amsa kai tsaye." Ta yi murmushi ta ce "Na sani, sai dai kasan kowa da irin tashi fahimtar? Ya ce "To ina saurarenki ke yaya ki ka fahimci kalmar.?" Ta ce, "Yarda na dauki soyayya, shi ne ka so wanda-yake sonka, ya kasance ku duka kuna son juna." Ya jinjina kai ya ce "Haka ne." Ta girgiza kai ta ce "To gaskiya in dai wannan ce soyayya zani iya ce maka ban taba yinta ba." Ya ce "Na yarda dake sai abu na uku, ina son ki fadi mani gaskiya tsakaninki da Allah, koda wasa Daddy bai taba gaya maki yana sonki ba." Ta yi murmushi ta ce "Ka damu da maganar Daddy, to gaskiya bai taba cewa yana sona ba, idan ma ba ka sani ba mun dade bamu shiri dashi, babu zancen soyayya tsakanina dashi, sai na zumunci, 20 kuma bani tsammanin idan har zata faru, saboda yau din nan sai da muka fita kasuwa muka yo sayayyar kayan baiko na aurenshi ina tsammanin nan da kwana biyu za'a sanya lokacin bukinsu, kaga kenan babu komi, sai dai za ni so ka sanar da ni dalilin da ya sanya kayi mani wannan tambayar? Dr. Khalid ya yi murmushi ya ce "Ba za ki fahimce ni ba, amma tunda kin ce ga matsayin da ake, na gamsu." Ya zuba mata ido, suka yi murmushi ba ki daya. Mamakin kanta take yi, yarda mutumin yake neman canza mata ra'ayi lokaci daya, koda yake idan ma bata soshi ba, wa zata so? Daddy ne yanzu ya fi karfinta dole ne ta cire zuciyarta akanshi, amma Daddy? Sai ta girgiza kai "Da kamar wuya." Cikin hikima Dr. Khalid ya rinka kokarin janyo hankalin ta gare shi, kuma ya ji dadin yarda ta bashi hadin kai sosai, suka yi hira ta fahimta, hakan yaja suka dauki lokacin mai tsawo da su kansu suka yi mamaki. Yana shirin tafiya, ta je kwankwasa kofar Mummy ta sanar da ita za ya tafi. Don haka Mummynta fito, suka yi sallama, ya ji dadi kwarai suka fito tare da Naja'atun ta yi mashi rakiya har wajen motarshi sai da ya zauna ciki, sannan ya dube ta ya ce "Kiyi mani wata alfarma guda.?" Ta zuba mashi ido tana jiran taji abin da zaya fada, ya ce "Lambar wayarki nake so ki bani ina jin dadin sauraron muryarki kinga ko banzo ba, zani iyab kiranki mu gaisa. Ta yi mumushi ta yi tsammanin wani abun ne can daban zaya tambaya, sai ita fadi mashi ya saka a 21ΟΓ ا Naarshh Aansaka ya Sat, kara,lavA MAXADAANtinkdkbiytn gade eni bThinoukd NinaallamaBјA Wufinta, ta lura dai kishin Likitan nan yake yi, ta cе, "YanXMnidapi ,erawaleikýn falak Mmamyna Faa saiaVikmurmuslnita ydan jin nauyia Mu BiajaaB iGr isata zanaa kaisa4layiinatass9a"Uaakanirki AANMARGIN, deriva Mummyya samaraa maganga kradakt,ridanha,kiaafo rtani hsamaaa kidadh ya Pista" Sehata sdaga memalkai,zMumikta i "a saskivanaiew" naa yaba Aledabanshazdoahaka ki kwader ida hansalinki kw fabimoniunaridantAlah ya nufa mjigkgnakinimere eurn gin radanuani dasuka son cawonakansu, Rahama neekuma aakidjalfabatirda hakaaydon haka kicire komi kbkahialkibladai Ki maki bayaninkanshi ko"kana sona, kuma ina na sanyakajaias batafrre dnatakorRáda eabata labarda dakraytmer denitavdangenqnda raguwenshifaMuraa itinearein ancllabbae vabbalarirmananda iba shi, saboda shi ba jinina ba ne, amma kauna ta sanyaDeally ya fito daga joikinadakinshtaakowkallonsu Paini da Manufa tabusingain abinaiiyourag ta ban mekaboazarinshi fi yeantegarosai. zkanmakewa dabawnshihaByatdinke ma kowarhaidhanaac takeavafkidalblak ibalgindaka a caоуь Каа baSan ba kiabkawndazsbigatahiaginyhiwaukansá zake Bathirac hedellunmbanaialfahatiudanirinuvadA 22 10 mata Mummy take janta jikinta, ko mahaifiyarta bata yi irin haka don haka kullum rana suke Kara shakuwa, tana son matar har cikin ranta, tana bata hakkinta, da 'yancin kanta, da wuya Mummy ta yi mata abin da zaya 6ata mata rai, ko wani abu ta yi ba daidai ba, cikin lallashi zata nuna mata kuskurenta, kuma ta sanya ta ta gyara to itama ko da yaushe cikin taka tsan-tsan take, bata son ta kuskuro ta, duk lokacin da ta yi waya da su Inna, suna kara gargadinta akan ta iya kanta, ta tsaya matsayinta, kada ta kuskura su ji wani abu marar kyau ya taso daga gare ta. Dare yaja sosai, suna ta hirarsu, karfe sha daya ta shiga daki ta yi shirin kwanciya, sai ta janyo wayarta zata rufe, nan taga miscall goma na bakuwar lamba, babu shakka lambar Dr. Khalid ce, bata ji dadi ba, zaya yi tsammanin ko ta ki dauka ne. Ta dauka ta yi serving din lambar, bata kai ga rufewa ba, sai ga kiranshi ya sake shiga, ta yi murmushi ta dauka, muryarta kasa-kasa ta amsa mashi da sallama, ya ce "Naja'atu kina so ki rinka wahalar dani ko.?" Та се, "Kayi hakujri, ina falo tare da Mummy muna hira, yanzu na shiga zani kwanta, naga miscall din ka har guda goma." Ya ce, "To kuma ba za ki kirani ba.?" Ta yi murmushi ta ce "Ka yi hakuri na amsa laifina." Ya saukar da ajiyar zuciya, ya ce, "Shi kenan kin fi karfin komi a wajena, amma hankalina har ya tashi, naga lafiya lau muka rabu, yanzu kuma ina ta kira anki daukar wayata." Ta ce, "To na ce ka yi hakuri, Allah kuwa 23 gaskiya na fadi maka, ba ni cikin daki ne." Ya ce "Na yarda, dama na kira ne in ce maki Good night, in kuige ji sassanyar muryarki nasan za ni samu barci mai dadi." Naja'atu ta yi shiru tana jinshi, duk sai ya dora mata nauyi bata saba da irin wadannan kalaman ba, ya ce "Kin yi shiru ba ki ce komi ba." Ta cе, "То me zani ce maka? Ka sanya na ji nauyin ka ma." Ya ce, "To gaskiya ki daina, Naja'atu kalmar so ce fa ta hada mu, wata rana ma tare zamu zauna mu zama hanta da jini, idan ba mu fahimci juna ba tun yanzu can gaba zaman ba zaya yi mana dadi ba, don haka ki saki jiki dani, ina son mu samu shakuwa tsakaninmu ta haka ne za ki fahimce ni da halayyata, haka nima zani san me kike so da kuma abin da ba ki so." Tа се "Shi kenan, Allah ya bamu iko." Ya yi murmushi ya ce "To na gode, kwanta kiyi barci, Allah ya bamu alkairi." Ya rufe. Naja'atu ta zuba ma wayar ido, sai ta yi murmushi ta rufe ta aje ta gefe guda ta kwanta tana karanto addu'o'i, data natsu sai ta rinka gani fuskar Dr. Khalid yana yi mata murmushi. Ta lumshe ido tana tariyo kalamance "Simple man yana da saukin kai da dadin zama, tana sha'awar halayyarshi. Amma kuma da ta tunu Daddy, sai ta ji gabanta yana faduwa, bata san abin da ta yi mashi ba, yake yi mata fushi, koda yake ba ya rasa nasaba da ganin Dr. Khalid, ta rasa abin da yake damunshi ya tsani Dr. Khalid, ko maganarshi aka yi idan yana wuri sai yasha mur baya cewa komi. 24 Mamaki yake bata sosai, ita bata ga dalilin nuna kishi akanta ba, tunda baya sonta, hasali ma ga wadda yake so yana shirin aurenta, to so yake yi yaga ta zauna tana wahala a kanshi alhalin shi bai damu da ita ba, baya sonta? Insha Allahu zata yi iya bakin kokarinta taga ta cire shi, daga ranta. Ta ci gaba da tunaninta, a hankali ta dan ja tsoki, sharrin zuciya kenan, idan ta tashi kamuwa da son abu, bata sauraren mai ita, idan bacin haka ita kanta tasan Daddy ba ajinta ba ne yanzu ne ta gane kuskuren da ta yi, da ta dasa ma kanta kaunarshi, kila saboda haka ne yake neman ya rinka juya ta. Mamakin kanta take yi da har ta fada cikin irin wannan makauniyar soyayyar ta son maso wani. Da wannan tunanin barci ya dauke ta har cikin mafarki ta rinka ganin mutanen biyu, kowa yana fadi mata asirin zuciyarshi. To na Dr. Khalid dai tasna gaskiya ne, amma na Daddy, sharrin zuciya ne bata tsammanin har abada zaya iya fitowa ya ce yana sonta. Sai ta rinka jin tausayin kanta. Washe gari ba ta tashi da wuri ba, don haka har Daddyn ya fita ofis, basu hadu ba. Sai da yamma da ya shigo suna zaune falo tare da Ibrahim suka yi mashi sannu da zuwa, ko kallon sashin da suke ba yi ba, ya raba su ya wuce zuwa dakinshi. Ibrahim ya juyo yana kallonta, cike da mamaki ya ce, "Wai me ke damun man din nan ne? Tun safe yake fushi, yau bai jira ya sauke ni, makaranta ba sai dai direba ya kaini." Naja'atu ta yi murmushi ta ce "Me yiwuwa ofis ne aka 25 Sata mashi rai ko." Ya ce "To amma Anty Naja ina laifin mu da abun zaya shafc mu.?" Naja'atu ta yi murmushi ta ce, "Kasan kowa da irin halayyarshi." Ya cc, "To Allah ya kyauta." Та се "Amin." Suka ci gaba da hirar su, ya dauki tsawon lokaci cikin dakin, sannan ya fito. Kai tsaye ya nufi kicin ya fito rike da kwalin lemu da kofi, ya zauna yana cin abinci shi sai dai fuskarshi a daure, Naja'atu ta rinka nazarinshi tana mamaki ita bata ga dalilin wannan fushin ba, duk ya takura kanshi kuma ta yi imanin ita abun ya shafa. lya tunanin da ta yi bata ga laifin da ta yi mashi ba, idan ba shigowa da Dr. Khalid ba, wannan kuma ba laifinta ba ne, Mummy ce ta ce ya shigo, don haka sun fi kusa "To waj ma menene dalilinshi na neman takura mata.?" Da ya karc cin abincin ya shiga cikin daki bai dade ba ya fito ya fice daga gidan baki daya. Abu kamar wasa cikin kwanaki biyu Naja'atu ta gaya kan Daddy, bata fahimci in da ya dosa ba fushi yake yi sosai, tsakaninshi da ita sai harara yana magana da kowa a gidan, amma ban da ita idan ta gaida shi baya amsa ba, ko hira suke yi da Mummy idan ta fito sai ya daure fuska baya kara yin magana. Tun tana kokarin danne wa har takai abun ya zauna mata cikin rai, ita kanta takura sosai, bata sake wa hankalinta ya tashi matuka gabaki daya sai ta fara tsanar zama gida kara ta yi tafiyarta ta huta, zata samu lokaci ta yi ma Mummy magana ta shirya mata tafiya. Ranar Asabar aka kai kayan baiko gidan su 26 Farida, kannen Mummy su biyù suka zo daga Katsina, da kanwar Babansu dake zaune Kaduna, sai matar Alhaji Isa, da Anty A'isha, sai sauran kawayen Mummy da abokan arzuki, sune suka hadu suka kai kayan. Lallai Mummy tayi hidima Farida mamaki ta rinka yi abun na manya ne, sun dauke shi da girma lallai kam Daddy ba ajinta ba ne, saboda a bangaren su Faridar ma sunyi hidima sosai, tayi imanin idan ita ce zaya aura ba za'a yi masu irin yarda taga an yi ba. Sai tasha jinin jikinta. Mummy da kanta ta debi lokacin bikin wata biyu masu zuwa, kowa ya yi na'am da hakan, ana ta sanya albarka. Yinin ranar bata ga angon ba, bata damu da son ganinshi ba kuma. Washegari da wuri ta tashi ta yi wankin underwears cikin kewaye, sannan ta shiga goge-goge cikin dakin, ta 6ata lokaci sosai karfe tara ta gyara komi fes, sai ta fito don ta samu abin da zata sanya ma cikinta, yunwa take ji daren jiya bata ci abincin ba haka nan ta kwanta. Gidan shiru kamar babu kowa, Mummy bata tashi ba saboda bata ji motsinsu ba, haka nan bakinsu ma, Ibrahim kuma tasan ya tafi lesson sai ita kadai ke hidimominta, ta shiga kicin tana ta harare-hararen abin da zata ci. Babu komi sai sauran abinci, ita kuma kunyar girka wani abu takc yi, sai ta jawo filas ta hada tea mai kauri ta tsaya nan tana sha. Hankalinta ya yi nisa bata ga shigowarshi ba, sai da ta daga kai sannan ta ganshi tsaye jikin kofa, ya rungume hannayenshi akan kirji yana jifarta da 27 3 mayataccen kallonshi da take dauka harara ce sai ta dan ji tsoro yayin da shi kuma ya ida shigowa ciki sosai, sai ta yi amfani da wannan damar zata fice, yasha gabanta da sauri a tsorace taja da baya tana kallonshi fuskarta babu walwala, ya ce "Naja'atu kina ganina shi ne ba za ki gaishe ni ba?" Ta sarda kai kamar ba da ita yake ba, ya ci gaba da kallonta ya сe "Da ke nake magana fa?" Zuciya tazo mata iya wuya, ta ce "To me kake so in ce maka Daddy? Idan ma na gaishe ka ba amsawa kake yi ba, ka tsiri fushi da ni." Ya yi murmushi ya dafa firij ya ce "Yanzu laifina kike gani kenan?" Ta ce "Dole in ga laifinka mana, idan wani abu na yi make ka fito ka fadi mani mana, sai in baka hakuri, amma ban san laifina ba, ka tsanani. Idan na gaida ka baka amsawa, ba ka zama in da nake kayi hakuri insha Allahu na kusa tafiya in bar maka gidan baki daya". Zuciyarta ta kare, hawaye cike da idonta, ta sake raba shi zata wuce, ya ki bata hanya, ya tsaya kawai yana kallonta, sai ta bashi tausayi, shi kanshi ba zaya iya cewa ga takamaimai abin da ta yi mashi ba, illa dai kawai yasan ya ji zafin zuwan da ya yi ya same ta da Likitan nan har cikin falo. A hankali ya saukar da ajiyar zuciya, ya ce, "Amma Naja'atu ni nafi ganin laifinki." Ta ce "Da na yi maka me?" Ya ce, "Uhm, kin san munyi magana da ke baki-da-baki na ce zani kawo maki saurayin da ya dace dake har nan gida ko?" Ta ce "Ni kuma nace maka ban yarda ba, kuma bani so". Ya ce "Kenan shi ne dalilin da ya sanya kika 28 kawo wannan guy din har cikin gida ko?" Ta ce "K.e da kaga laifina kan shigowar Dr. Khalid cikin gida, Mummy ce da kanta, ta aika ta ce ya shigo, don haka bani na shigo da shi ba." Ya ce "To amma tun farko me yasa kika tsaya kika saurare shi". Zuciya ta kara cika ta, bata ga dalilin wannan iko da yake neman yi mata ba, ta cce "Amma kasan cewa I'am matured enough, da ya kama ta in zabi abin da yake daidai dani ko?" Ya jinjina kai, ya ce "Haka ne, kenan shi yasa da na bata raina akan abin da kika yi, kema sai kika dauki fushin dani." Ya girgiza kai ta ce "Ni ban yi fushi da kai ba Daddy, kaine kake yin fushinka, naga idan nace zani ci gaba da kula ka, sai ka wulakanta ni a banza don haka naja jikina". Ya ci gaba da kallonta yana mamakin bakin yarinyar, ya ce "To ni dai na fadi maki ba fushi nayi dake ba, na fadi maki ne don ki gane kuskurenki". Ta ce "Ni fa Daddy idan zaka maida jikina kunnuwa, ba zani yarda nayi maka laifi ba, Daddy kayi mani adalci mana, kowane dan Adam yana da ra'ayin kanshi a rayuwa, don mi zaka tursasa ni akan abin da zuciyata take so". Ya zuba mata ido ya ce "Kenan kina so ki fadi mani cewa kina son Dr. Khalid?" Ta ji nauyinshi sai ta sarda kai ta ci gaba da juya shayin da cokali, ya ce "ki fadi mani in ji da bakin ki". Sai ta saukar da ajiyar zuciya, ta ce, "Daddy mu bar maganar nan, duk abin da zani fadi maka, ba zaka fahimce ni ba, amma ni na sani kai ba zaka iya yin abin da kake son ni in yi 29 3 ba." Ya ce "Ban fahimce ka ba.?" Ta ce "Nasan kana son Farida ko ba haka ba.?" Ya jinjina kai yana kallonta, ta ce "A matsayin da kuke yanzu, yaya zaka ji idan tashi daya Mummy ta ce ka rabu da ita?" A hankali ya yi murmushi ya ce, "Shi kenan na fahimce ki, komi ya wuce, amma duk lokacin da na samu dama, ina son mu zauna mu yi wata magana ta fahimta tsakanin mu". Ta jinjina kai ta ce "Ва damuwa". Ya ce, "To nima hada mani tea din, yunwar nima ta fiddo ni, duk kin sa Pressure ta yi mani yawa yunwa tana neman kamani". Ta yi murmushi kawai, ta daha mashi tea din ya karba yana sha, ita kuma ta yi sauri ta ida shanye nata, ta aje kofin, ta fice. Da ta shiga daki ta koma ta kwanta, tana tunanin rigamar Daddy sai abin ya rinka sanyata dariya, zuciyarta tayi sanyi. To yinin ranar lafiya lau suka yini, amma da daddare da Dr. Khalid yazo, Mummy na cikin daki, haka nan shima Daddy ba ya gida, don haka bata shigo dashi ba, nan waje suka zauna suna hirarsu, ya ce "Jiya kunsha hidima, yaushe ne lokacin bikin?" Ta ce, "Nan da wata biyu". Ya yi murmushi ya ce, "Ya ji dadi, nima da za ki amince mani da an hada har da namu anyi baki daya". Naja'atu ta dube shi, sai tayi murmushi tana girgiza kai, a cikin zuciyarta ta shiga tunanin, "ita dai tasan tana ra'ayin Dr. Khalid, tana sha'awar ta zauna tare da shi suna hira, yana sanya zuciyarta cikin nishadi tare da debe mata kewar abubuwa da yawa, amma bata taba jinshi a cikin 30 1 zuciyarta ba, balle har ta yi tunanin yin aure dashi, matsalarta kenan ta dasa ma zuciyarta kaunar Daddy ta yarda ita kanta tasan tana cutuwa, saboda son maso wani take yi, kuma ta cire tunanin zata same shi, amma duk irin yarda taso taga ta rabu da kaunarshi abun ya faskara, wannan wani sirri zuciyarta ne da take ganin ita kadai ya shafa, babu mai iya yi mata maganinshi sai Allah". Ta saukar da ajiyar zuciya tana kallon Dr. Khalid shima ita yake kallo, sai ta yi murmushi ta ce "kana daukar aure abu mai sauki alhalin ba saukin ne dashi ba." Ya ce "Meye wuyar shi Naja'atu? Nayi tsammanin abin da ake so shine ya zamto ma'aurata suna son juna." Ta ce "Akwai wannan, sai dai fahimtar juna tana gaba da komi a cikin lamarin aure, dukkan yanda zamu so junan mu, matsalar akace babu fahimta, to zaman ba za ya dore ba, don haka nake son mubi komi a hankali, ko shi Daddy da kaga za yayi aure, tare yake da yarinyar, ance tun tana karama sun jima suna son juna, akalla ya fahimce ta, itama haka, to mu fa, duk yaushe ne muka hadu?" Yayi murmushi ya ce "Na fbahimta malama, idam kina jawabi sai ka ce 'yar jarida, ince kina karatun littafi ko?" Tayi murmushi ta ce "Ina tabawa, amma masu ma'ana, wadanda nasan zasu amfaneni ba wadanda zasu 6ata mani lokaci ba." Ya ce "Yana da kyau, kuma na gamsu da jawabin ki, na yarda da ke, Allag ya shige mana gaba." Tayi murmushi da amsa mashi da "Amin." Kadan kenan daga irin halayen shi 31 da take so, bai cikia jan abu ba, yana da saukin kai da saurin fahimta, cikin nutsuwa suke hirar su. Karfe tara da rabi yayi mata sallama zaya tafi, sai ga Daddy ya dawo, ya shigo da motar ya ajeta can nesa dasu bai zo inda suke ba, sai dai ya daga masu hannu ya shiga gida. Naja'atu bata ji dadin abin da yayi ba, to sai ta lura shi Dr Khalid bai damu ba, yayi matga sallama yaja mota ya fita. Da ta shiga cikin gida, ranta ya dan

Chapter 2 of 5