ta tashi zata tafi, dan haka Mummy
ta fita yi mata rakiya, yayin da shi kuma ya zauna a
gajiye, yunwa da gajiya na cin shi. Sai ya laluba
wayar shi yana neman layin Naja'atu ta fito ta bashi
abin shi. Mummy ta shigo ta zauna, ta ce "Sai yanzu?"
Ya lumshe ido cike da gajiya ya ce 'Wallahi kuwa,
motoci sunyi yawa a wajan wankin, duk can na 6ata
lokaci na."
47
Layin Naja'atu da yake nema shine bai shiga ba,
ya sakc kira a karo na biyu, nan ma shiru. Dan haka
ya rufe wayar yana kallon Mummy ya ce "Wai yaran
nan basu gidan ne?" Mummy ta ce "Wai sun je saloon
nc, daga can zasu biya gidan A'isha su karbo mani
sako, hala abinci zata zo ta baka?' Ta tsare shi da
idanuwa. Sai yayi murmushi yana shafar kai. Ta се
"Nema dai kake kai maida mani diya 'yar aikin ka
ko?" Yayi dariya ya ce "A'a Mummy ba haka banc."
Та сe "To fadi mani menene? Dama akwai maganar
da nake son yi da kai, kada ka 6oye mani, ka fadi
mani gaskiya, me ke faruwa tsakanin ki da Naja'atu?"
Shima ya zuba mata ido yana murmushi, to
amma shi baiga dalilin da zaya sanya ya tsaya wani
boye-boye ba, ya jinjina kai ya ce "Mummy idan zaki
tuna kwanakin baya kin taßa yi magana kan cea ko
zani nemi Naja'atu ne?" Ta ce "Uhm." Ya се "То
gaskiya Mummy son ta nake yi, kuma auren ta zani
yi." Dariya ta kusa kubce mata, saboda yanayin da
yake maganar, amma ta dake ta ce "Ita Faridar kayi
yaya da ita, gashi ka ce kai mijin mace daya ne?"
Yayi murmushi ya ce "Wannan ta wuce, maganar
gaskiya nifa da gaske nake." Ta ce "Naji da gaske
kake, na ce ita Farida fa?" Ya cc "Maganar ta tana
nan, idan na aure ta daga baya zani auri Naja'atu,
kuma munyi wannan maganar da ita ta amincе." Та се
"Ita Naja'atun ta yarda ta zauna jiran ka sai ka auri
wata sannan daga baya ka aure ta?" Ya ce "Eh
Mummy." 48
Ta jinjina kai ta ce "To ni ban amince ba, kuma
ina son ka rabu da yarinyar mutane, kada ka yaudare
la, ka barta tayi auren ta." Daddy ya girgiza kai, ya се
"Allah kuwa Mummy da gaske nake, babu yaaudara
tsakani na da Naja'atu har abada." Ta daure fuska ta
cc "Watau so kake yi ka watsa mani kasa a ido ko?"
Ya ce "Mummy kamar yaya?" Ta cc "To ni dai nasan
matsawar Farida taji zaka auri Naja'atu bayan auren
ta, ba zata yarda ba, ita kuma wannan ka zo ka rabata
da mai sonta, a zo abu yha ki yin dadi, wa kunya zata
karem mawa?"
Ya saukar da ajiyar zuciya yana kallon ta. Yaа се
"Mummy nifa mijin mace hudu ne, kiyi hakuri ki
yarda da maganar nan, Allah kuwa babu yaudara ko
makamancin haka a ciki, idan kika ce dole in rabu da
Naja'atu kin dora mani aiki babba, saboda ban san
yanda zanyi da kaunar ta ba, ni kaina ban san lokacin
da kaunar ta ta dasu cikin zuciya ta ba, kiyi hakuri
Mummy."
Та се "То amma Daddy kai ka baribida baya, sai
da nayi maa magana kan yarinyar nan, ka ce ba haka
ba, sai yanzu da abubuwa suka rikice sannan zaka
bullo da wata magana, to ni dai na fada maka bani so,
ka rabu da ita ta ta samu miji tayi aurenta, an fada
maka tara mata sauki ne?" Ya karkace kai da sigar
lallashi, ya ce "Mummy na sani ba sauki bane, sai dai
ban san yanda zani yi da kaunar ta ba, ki ci gaba da yi
mana addu'a, insha Allahu komi zaya warware." Babu
49
yanda za tayi dole ta rabu dashi. Sai dai har cikin
ranta ba'a son ranta ba.
Amma da daddare mai wanki ya shigo da kayan
guga na Hajiya, Naja'atu ta karba ta shigar mata dasu,
Hajiyar na zaune ta gama sallar isha'i tana lazumi.
Tayi sallama ta shiga da kayan, sannan ta bude dirowa
tas hirya mata su. Tana shirin fitowa ta daga kai tana
kallon ta, ta ce "Zo nan Naja'atu, zauna magana zanyi
dake." Taji zuciyar ta na bugawa da sauri, duk sai ta
tsorata, jikin ta babu karfi ta zauna tana kallon
Mummy, yayinda ita kuma ta ida shafa addu'a.
Sannan ta juyo tana fuskantar ta, tare da "Wata
tambaya nake son yi maki, kuma tsakanin ki da Allah
kada ki 6oye mani ki fadi mani gaskiya. Me ke
tsakanin ki da Daddy?"
Da farko tambayar ta bata tsoro har ta rasa abin
da zata ce, to sai dai kuma da matsayin Mummy a
gare ta ya wuce ta boye mata wani abu, don haka ta
sarda kai tana wasa da zoben azurfa dake manne a
hannun ta. Ta ce "Sona yake yi." Mummy ta jinjina
kai ta ce "Kuma kema kina son shi?" A hankali ta
daga mata kai. Mummy tayi murmushi ta ce "Hakan
ba laifi bane, sai dai baki yi mani wayau ba Naja'atu,
keda saurayi yana son ki, kuma daidai gwargwado
yana da na kanshi, ga ilimi yana dashi, sai ki tsaya
kina jiran Daddy, dake shirin auren wata?" Ta ce
"Mummy nima ya ce aurena za yayi."
Tayi murmushi ta ce "Na sani, amma ba wai
bani sonki da Daddy bane, kinga ni na haife shi, kuma
50
bry sonanhi, fetoj soo dilk albeshkoyavanicikimefalayi imanavktn albei asparsebodai dari hisa dari namaprekiakan rcn Farida lo ammahze podusan Ji kin shiga wanihali pnawyyasi babana in pata
kuma
hada
zaya
su, ta sonkle yan s
cikin kwanakin iya.aurcen ta
kısamu ya hada ku biyu, tunda namyi yake, saı nutsuwa da Dr Khalid vana samun dai
ifa kanta can
bangaren yarınyar zata. yarda ayi mata sosai sa kişhiya dake yan watanhi ta yin auren su? Ko l a VA i kamar deZe ki haka idan kika tsaya
ya tafi ganm
Hniixei bayaninda balainkishi sakiyihm ajayki mashirafatata Kllanidi.daga togaata kataadamla badayr, skineawsanyahafeukiinujim zukiaciygabawda Mmamiya taa yraşinshekargakian jirarashi?" amma ya tabbataramata tdiii cowalkaddabbasanabultwaruwda
MsmanAllaHudemaskinn aesho tahdaivana klavida Kanarahar mpted Tewavir shi ta keiy muddinnla rabu shiga damu Ratten Bridatashi grdall Ran ER THE P
eaniy cikin halin dae ma funda
fatan Mummy alkairi. ta kawo hujjojin ta tasan dole ne tayi bıyayya Zainaq ta fito suka ci gaba da hrar gare ta, tunda tasan ba zata cuce ta. ba, ko kuma ta Su. cuci Den danta, haka gaskiya-ta Hauva ta koma cikin daki ta basu tada, saf ta rinka jin, tausayın W Har suka game hirar su Daddy bai dawo ba, hakarMRaw ury shaihinarau, feredaRaiwaPbani sonki da Daddy bane Naja'taingdba halia hangehniwkir dokakadHa mtsDdalyubagannykanikakayaudawouyalngmehiihgn
Najayithakası yayfama baridmakaakiakuinazhaizbya
otbin bauvkamsakgidsuromvoná magánernagudäishaие
63
ce maganar Farida tana nan, daga baya ne zaya aure
ki, shi kuwa Khalid jira yake yi kowane lokaci kice
kin shirya ya aure ki, to sai ki tsaya jiran wanda shi
kanshi baisan tsawon lokacin da abun zaya dauka ba?
Kilama daga baya ya zo ya ce ya fasa."
Naja'atu ta dago kai tana kallon ta, ta ce "Kwarai
kuwa kadan kenan daga halayyar maza." Sai taji
tsoro, ta saukar da ajiyar zuciya, ta ce "Shi kenan
Mummy na fahimta, zaniyi kokari in rabu dashi."
Tayi murmushi ta ce "Yauwa, sai ki kwantar da
hankalin ki, ki tsaya kan Khalid ku fahimci juna, insha
Allahu zaki ga hasken abun." Ta jinjina kai sai ta
sanya hannu ta goge fuskarta. Mummy ta sallame ta ta
taso ta fita.
Da wuri taje ta kwanta, sabi da bata son su zauna
hira Daddy ya tsare ta, don haka ta shiga daki tayi
kwanciyar ta, zuciyar ta cike da tunani iri-iri, ta kulla
wannan ta kwance, bata san yanda zata yi ta raba
zuciyar ta da kaunar Daddy ba, ko da can da bai fito
ya ce yana sonta ba, ta kasa hakura dashi, balle kuma
yanzu da ya hure mata kunne da kalamanshi na
soyayya masu dadi, bata ki ace koda yaushe tana tare
dashi ba yana jifarta da mayatgaccen kallon shi, yana
tsananin yin tasiri a kanta. To sai dai tasan dole ne
tabi umarnin Mummy, bata son ta saba mata.
Hawaye ta rinka yi sosai, tun tana kukan zuci
har ta kai ya fara fita, saukin ta daya da yake ita kadai
ce cikin daki, sai tayi mai isarta, a karshe ta hakure ta
barma Allah komi. Zainab ta shigo cikin dakin tana
52
kallon ta, amma ita Naja'atu sai ta lumshe ido kamar
tana barci, dan haka tayi tsammanin tayi barcin, ta
juya tasanar da Daddy ccwa barci take yi, dama shine
ya turo ta kiran Naja'atun yaji ta shiru, kuma ya kira layin ta shima a rufe. Da ta kuma ta sanar dashi ya zuba mata ido cike da damuwa, ya ce "Kin tabbata
lafiyar ta lau kuwa?" Zainab tayi murmushi ta ce
"Allah kuwa lafiyar ta lau, ta ce mani barci take ji zata
kwanta da wuri." Ya jinjina kai bai sake magana ba.
Ba'a jima ba aka kira wayar Zainab din, ta dauka
ta duba sai taga Dr Khalid ne, tayi murmushi ta amsa
mashi da sallama. Ya ce "Zainab me ke damun
Naja'atu ne, ina ta kiran layin ta tun dazu na gaza
samu?" Tayi murmushi ta ce "Lafiya lau, ta kwanta ne
da wuri, ina jin layin a rufe yake." Ya ce "To ki bata
wayar ina son in ji muryar ta atleas in samu peace of
mind." Ta kyalkyale da dariya, ta ce "Yes sir." Sai ta
tashi ta nufi dakin, tà shiga ta dan bubbuga Naja'atun,
ta dago kai tana kallon ta. Ta ce "Dr ne ya a waya duk
kin rikita shi, kin kama waya kin rufe."
Ta amshi wayar, tayi mashi sallama. Zainab ta
fice tana yi mata dariya. Yayin da ita kuma ta tashi
zaune tana gaida shi, yanzu kam dole shi zata rike
tunda tasan ba zata samu Daddy ba. Ya saukar da
ajiyar zuciya, ya ce "Naja'atu me yasa kike son
wahalar dani ne? Kin san tsawon lokacin dana dauka
ina neman layinki ban samu ba? Gashi na kwanta
amma na gaza samun barci saboda banji muryar ki
ba." Ta ce "Kayi hakuri don Allah, kaina ne yake yi
53
mani ciwo nasha magana na kwanta." Ya cc "Ayya
sorry nayi tsammanin baki da loakaci na ne, in ce
abun har ya kaimu ga haka? Banda sauye-sauyen da
nake fuskanta daga gare ki ace har an fara rufe mani
waya, wai dan Allah Naja'atu me yake faruwa ne?"
Ta kwantar da murya ta ce "Allah kuwa babu
komi." Ya ce "To amma yanda kike sakin jiki dani
kwanakin baya yanzu bani samun shi, wani laifi
nayi?" Ta ce "Ai baka laifi waje na, balle kuma iya
sani na babu wani abu." Ya ce "Na amince dake, gobe
insha Allahu zan dawo, zan zo muyi wata shawara
mai muhimmanci." Та се "To Allah ya kawo ka
lafiya, na gode Allah ya bamu alheri." Yayi murmushi
ya ce "Na gode Naja'atu, kinga irin abubuwan da kika
saba mani dasu, shi yasa duk dare idan banji muryar
ki ba ba zani iya runtsawa ba, yanzu haka barcin nake
ji, amma rashin jinki ya sanya na kasa barci." Та се
"To ka kwanta kayi barcin ka, sweet dreams." Sai ta
rufe wayar tana murmushi.
Dagowar da zata yi sai taga Daddy tsaye a kanta
ya zuba hannuwa cikin aljihu, fuskar shi a daure yana
kallon ta. Duk sai ta tsorata, ta aje wayar gefe daya
tare da sarda kanta. Tsahon lokaci sukayi shiru,
sannan ya saukar da ajiyar zuciya, ya ce "Kinyi
daidai." Bai sake magana ba ya juya ya fice. Hankalin
ta ya kara tashi, sai ta koma ta kwanta, bata san yanda
zatayi ba, domin ko ta fito ta bishi, sai taga yanda
ranshi ya baci idan ta haye mashi wulakanta ta za
yayi, dan haka ta rabu dashi din ya fiye mata sauki,
54
kada ta kara ma kanta wani zafin, ko da yake ko ta tashi ta bashi hakuri tasan dai dole rabuwar za suyi,
dan haka hakurin da zata je ta bashi ma ba za yayi wani tasiri ba.
Da kyar ta samu ta runtsa, hankalin ta ya tashi sosai, tunda Allah ya halicceta bata taba shiga mayuwacin hali ba irin haka, sai taji gabaki daya ta
tsani zaman ta Abujar, idan gidan su ne ba zata
fuskanci matsaloli irin haka ba, sai ta rinka ganin
laifin Daddy, ita dai iya tunanin ta bata yi mashi laifin
komi ba, bai san cewa ita ta fishi damuwa ba, shine za
yayi fushi da ita.
Da safe ma har rana tayi sosai tana cikin daki
bata fito ba, tana ta shirya kayan su na sanyawa.
Zainab ta shigo tana harararta, ta ce "Ki tashi ki fita
kiyi ma Daddy hidimomin shi, kin shagwaba shi komi
sai kinyi mashi, yanzu tunda na fita baibar ni na huta
ba, sai ya ce inyi wancan da na gama kuma ya се
wannan." Naja'atu ta kalle ta tana murmushi, ta ce "To
ai kin samu lada ko?" Ta ce "Wace lada? Tunda duk
abin da nake yi bai san inayi ba, komi nayi sai ya ce
baiyi mashi ba." Naja'atu tayi murmushi kawai. Sai ta
taso ta fito, can ta hango shi bisa teburin cin abinci
yana kalace, bata yi mashi magana ba, ta shiga dakin
Mummy ta gaida ta, sannan ta fito ta nufi inda yake.
Ko kallon ta baiyi ba har ta isa, ta dan dafa
kujera ta ce "Ina kwana?" Ya zuba mata ido yana
kallon ta fuskar shi babu walwala. Sannan ya amsa
kamar dole, sai tgaji zuciyar ta ta dan taßu, ta tsani a
55
dauri mata fuska, musamman nashi da yafi komi
saurin tayar mata da hankali, amma da yake ta saba da
halinshi bai iya fushi ba, baya iya boye damuwar shi.
Sai ta sassauta tana kallon shi, ta ce "Daddy fushi
kake yi har yanzu?" Ya jefe ta da muguwar harara, ya
mike a fusace ya nufi dakin shi. Naja'atu tgayi tsaye
sororo tana mamakin fushin Daddy, sai ta jinjina kai
ta koma cikin falo ta zauna. Bai jima ba ya fito, daidai
nan aka kira wayar shi ya tsaya yana magana. Farida
ce akan wayar. Naja'atu ta zuba mashi ido cike da
tsana, tana jin matsanancin kishi a zuciyar ta. Ya ce
"Kiyi kokari ki shirya zani fito yanzu muje, ina son in
dwo gida da wuri."
Naja'atu ta runtse ido kamar za ta fasa kuka, tana
jin shi ya zo ya rabata ya fice, sai ta bishi da ido har
ya fita, sannan ta jinjina kai. To amma sai zuciyar ta
tayi sanyi sam bata damu da abin da yayi ba, tasan dai
dole rabuwa za suyi, kuma ko kwanciya zata rinkayi
Kasa yana taka ta sai ya shiga wannan damuwar, don
haka ta kudurfe zuba mashi ido kawai ba zata sake
shiga harkarshi ba balle yayi mata wulakanci,
matsalar Daddy kenan bai iya bacin rai ba.
Har yamma bai dawo gidan ba, sai taji dadin
haka, kara shi da kanshi ya juya mata baya sai su rabu
cikin ruwan sanyi. Da maraice ita Zainab suka fita
zuwa gidan Aunty A'isha, daga can zasu shiga super
market suyi saye-sayen kayan amfani a gidan. Da
suka isa gidan Aunty A'isha ta rinka kyalkyar dariya,
ta ce "Dama yanzu nake shirin tura direba ya dauko
56
mani ke Naja'atu, Daddy bai jima da barin gidan nan
ya kawo mani karar ki." Sai taji zuciyar ta tana
bugawa, ta tsani ko sunan Dadday taji an ambata, so
take yi da karfin tsiya ya yakuce shi. Zainab tayi
dariya ta ce "Ai dama zuba mata ido nayi tun jiya na
lura babu jituwa tsakanin su, amma ta rinka kokarin
6oye mani, Naja'atu kin cika zurfin ciki."
Naja'atu tayi murmushi kawai. Suka zauna
A'isha ta umarci Zainab ta shiga kicin ta ida hada
mata girkin da ta keyi, yayin da ta zuba ma Naja'atu
ido ta ce "Daddy ya kawo mani karar ki cewa kin
canja mashi, yanzu ko magana baki son yi mashi,
kuma baiyi maki laifin komi ba." Naja'atu tayi
murmushi ta ce "Aunty A'isha rabu da Daddy rigimar
shi tayi yawa, matsalar shi daya ce ya cika zafin kishi
da saurin fushi, ni banga laifin da nayi mashi ba, ina
cikin daki Zainab ta kai mani waya ta Dr ne ya kira,
ina magana dashi ban sani ba ashe ya shigo cikin
dakin, da na gama magana ne na ganshi, sai cewa yayi
na kyauta ya juya ya fita, tun daga nan ya dauki fushi
dani ko da na gaidashi da safe da kyar ya amsa mani,
da nayi mashi tambaya sai kawai ya tashi yayi tafiyar
shi cikin dakin shi, kuma ina zaune ya zo ya rabani ya
fita ko kallona baiyi ba, to yaya yake so inyi?"
A'isha tayi murmushi ta ce "Nasan halin Daddy
da saurin fushi, don haka sai kin rika yin hakuri, sai
abu na biyu, ya ce baya son yaga kina kula Dr Khalid,
ranshi 6aci yake yi, to sai dai da kaina na bashi amsa.
Gaskiya banji dadin yanda kika yi saurin amsa
57
maganar Daddy ba, ke kiyi tunani mana, idan dai
sonki yake ya donmi ba zaya hakura da auren Faridan
ba, tunda ai ba daura masa aure akayi ba, don ya raina
ki sai ya ce ki jira sai ya auri wata sannan ke ya aure
ki, ke kuma har kin yarda da haka, sai kace shine
autan maza. Me Daddy ke dashi wanda Dr baya dashi
da har zaki yarda da wannan rainin wayau? To sai dai
na gaya mashi idan dai ke yake so to ya tsaya a kanki,
idan kau ya ce sai ya auri Farida to wallahi ba sonki
yake yi ba sai kiyi ta kanki."
Naja'atu ta jinjina kai ta ce "Na ruga na fidda
maganar Daddy a raina, kamar yadda kika fada mani
haka Mummy ta fada mani, kuma na yarda, don haka
sai ku tayani da addu'a Allah yayi mani zabi mafi
alkairi." A'isha ta ce "Insha Allahu, kuma sai ki kama
kanki ko auren zaki yi zaya fi ganin ki da mutunci,
amma matsawar ya fahimci cewa kina son shi sosai,
da kuwa ya rinka wahalar dake kenan, matsala ce
babba mace ta nuna ma namiji matsanancin so, har
kara ki bari nashi yafi naki." Naja'atu ta jinjina kai ta
amince da abin da suka fadi mata.
Dr Khalid ya kira ta ta waya, sai ta tashi ta fita,
sannan ta amsa mashi. Ya sanar da ita ya iso lafiya,
don haka zuwa dare yana nan fitowa. Ta ce "To Allah
ya kawo ka lafiya." Ya ce "Me kika tanadar mani?"
Sai tayi murmushi ta ce "Sai ka iso dai." Su kayi
sallama ta dawo ciki. Zainab nayi mata tsegumin ta
cika jin kunya. 58
Basu dade ba suka fito suka yima Mummy saye- sayen ta, suka koma gida. Motar Daddy na nan, amma da suka shiga ciki basu ganshi ba, don haka Naja'atu taji dadi, hakan yafi mata sauki, kara ta rinka nesa- nesa dashi.
Da Dr Khalid ya iso ta fita ta same shi zaune waje, da fara'ar shi ya tarbeta, sai taji duk wata damuwarta ta yaye Khalid abin so ne ga duk wata
macen da ta san ciwon kanta, haka nan daga ita har yaransu zasu samu kyakkyawar kulawa, sai ta rinka gode ma Allah cikin zuciyar ta da yayi mata baiwa da
samun masoyi kamar shi. Kamar kullum, hirar su cikin nutsuwa da ma'ana, sai da ya tattara hankalinta gare shi sannan ya fuskanci ta sosai, ya ce "Maganar da nace maki ina so muyi, ko kin manta?" Tayi murmushi ta ce "Tana raina, naji baka ce komi bane shi yasa na kyale ka." Yayi murmushi ya ce "Dadina dake kenan kin cika jan aji." Ta ce "Babu zancen jan aji anan, kaifa kace zaka zo muyi wata magana, to kuma ka zo baka ce mani komi ba, sai in tambaya?
Tunda ban san abin da zaka ce mani ba, na sani ko
cewa zakayi-zakayi aure."
Yayi dariya yana kallon ta, ya ce "Aure da wa Naja'atu?" Ta ce "Na sani ko kana da wata budurwa a
Kano." Khalid ya rinka dariya, ya ce "Ban taba sanin kina da kishi ba Naja'atu sai yau, in banda abinki ina naga wata budurwa? Ke kadai ce kwallin kwal, kuma baki da kishiya." Dadi ya rufe Naja'atu. Ta ce "Cika baki dai, kada fa na shiga da wata daya ace mani za'a
59
cika alkawarin da akayi ma wata?" Ya zuba mata ido
ya cc "Idan haka ta faru yaya zaki yi?" Ta daga sama
tana tunani, sannan a hankali ta zuba mashi ido, ta се
"Allah kuwa ba zani zauna ba gidanmu zani koma."
Ya ce "Ni kuma ba zani iya hakura dake ba, kinga kau
zancen inyi maki irin abin da zuciyar ki bata so bai
tasò ba, bari kiji in gaya maki, ni ra'ayina daban yake
dana sauran maza, Allah bai zuba mani jarabar dake
din nan ba zaki isheni ba, da har zani tara mata da
yawa, burina kawai mu fahimci juna, ta yanda zamu
ba 'ya'yanmu tarbiya mai kyau, su tashi cikin rayuwa
mai albarka, bawai in tara mata ba suyi ta haihuwar
'ya'yan, ta yanda ba zani iya sauke nauyin su da Allah
(S.W.T) ya dora mani ba, a karshe ma su dawo suna
tsine mani."
Naja'atu ta jinjina kai tana murmushi, sai taji ya
burge ta, ko ba komi ya nuna yana da zurfin tunani, ita
kanta tana yin wannan tunanin akan Daddy da yake
neman hadasu su biyu ita da Farida, alahalin shi
kanshi shekarun shi ba wasu bane, a ganin ta bai isa
hada mata biyu ba ya rike, to sai dai kaunar shi data
dauka ta dasa ma zuciyar ta ita ke wahalar da ita, ta
yanda bata ganin aibunshi ko kuma hangen abin da
zaya faru matsawar zata same shi.
Khalid ya gyara zama yana kallon ta, ya ce "Mu
koma kan tushen maganar mu, shawara ce za muyi,
kuma ina son ki taimaka mani don muga komi ya tafi
yanda nake sonshi. Watau kwanakin baya gwamnati
ta dauki likitoçi hamsin cikin fadin kasar nan, inda ta
60
tura su kasashen waje su kayi kwas akan 6angarori da dama, yanda idan suka dawo zasu ci gaba da taimaka ma al'umar kasar ta yanda za'a
samu saukin kashe kudi wajan fidda marasa lafiya waje, kinga wannan ba karamin ci gaba bane, to
yanzu ma kashi na biyu za'a fidda, kuma ina sanya
ran cewa ina cikin wadanda za'a tura, sai dai kwas
din duka na wata tara ne, kuma gaskiya da ci gaba
ne sosai, don haka nake son muyi magana ta
fahimta dangane da lamarin mu."
Naja'atu ta jinjina kai ta ce "Gaskiya ci gaba
ne sosai, Allah ya tabbatar da alkairi." Ya zuba
mata ido ya ce "To yanzu yaya kike ganin za'ayi?"
Tayi murmushi ta ce "Kai wane tsari kayi?" Ya ce
"Abin da na kasa shiryawa kenan, don bukatar ki
ina bukatar ki kusa dani, ko da yaushe, to sai dai
idan nace muyi aure kafin mu tafíi, ko na tafi
hankali na ba zaya kwanta ba, saboda kinga halin
da nake ciki, iyayena sun rasu balle in ce in barki
hannun su, idan kuma na tafi na barki abubuwa
zasu rinka wahala, kuma gaskiya ni ina da
tsananin kishi, ba zani iya barin amanar ki hannun
wani aboki na ba, mutane basu da tabbas yanzu,
duk wanda kace zaka bashi kayan ka, to nema
yake yaga bayan ka, don haka kikaga ban taba
kawo wani aboki na wajan ki ba, yanzu ma kenan
balle kuma munyi aure kina matsayin matata, ba
61
zani iya barin ki hannun wani wanda ba jinina ba,
kinga nan ma akwai matsala. Haka nan ina
shakkun in tafi in barki ba muyi aure ba, kina
ganin za'a barki har zuwa lokacin da zani dawo, to
kuma ke zaki iya jira ne?"
Ya ci gaba da kallon ta yana son yaji abin da
zata fada. To ita kanta bata san abin da zata ce ba,
sai dai hujjoji da ya kawo suma abin dubawa ne.
Ta jinjina kai ta ce "Shi kenan zanyi kokari inga
na jira, kaima fa ka rike alkawari?" Yayi
murmushi ya ce "Ni ke nafi ji Naja'atu, insha
Allahu zaki same ni mai alkawari." Ta ce "Sannan
ina son ka samu lokaci muje Katsina kayi magana
baki da baki da Baba, idan ya amince shi kenan,
saboda yana yawan yi mani maganar aure." Ya
jinjina kai ya ce "Nima dama nayi tunanin yin
hakan, don haka kada ki samu damuwa idan komi
ya kankaman zani fidda lokaci sai kiyi mani
jagora." Tayi murmushi ta ta yanda ta tsara shi.
Da zaya tafi ya fiddo mata tsarabar Kani, tayi
godiya, su kayi sallama ya tafi.
To kuma bayan kwana biyu da yin maganar,
yana ofis ya kirata yana yi mata albishir din
magana ta tabbata, ta taya shi murna da fatan
alkairi. Yanzu kam hankalin ta ya karkata ga
Khalid, saboda har yanzu Daddy fushi yake yi da
ita, ko zama gidan baya yi, idanma yana gidan
62
baya zama falo, ko da yaushe yana cikin dakin shi, kwata-kwata ta daina ganin sakin fuskar shi, to itama sai taja jikinta, idan ma taga lokacin fitowar shi tayi sai ta tashi tabar falon, ko hanya bata hada su, ta tabbar baya ra'ayinta, don haka cikin kwanakin ta samu nutsuwa da Dr Khalid, yana samun kanta sosai, sai ya rinka jin kamar bazaya iya tafiya ya barta ba.
Da yamma da izo ciki ta shiga dashi, yayi ma Hajiya bayani da bakin shi. Tayi murna, sannan atayi mashi fatan alkairi. Ya gabatar mata da bukatar shi cewa ayi hakuri, auran su sai ya dawo. Mummy ta jinjina maganar a ranta, amma ya tabbatar mata da cewa kada ta samu damuwa, insha Allahu zata same shi mai rikon alkawari,
kuma ya sanar da ita cewa "Yana so suje har can
Katsina gidan su Naja'atun yayi magana baki da baki da iyayen ta." To sai ta amince tayi mashi
fatan alkairi. Zainab ta fito suka ci gaba da hirar
su. Don haka Hajiya ta koma cikin daki ta basu waje. Har suka game hirar su Daddy bai dawo ba, hakan yayi mata dadi, don haka suka sake suka sha hirarsu tare da Zainab.
Zainab ta rinka saha'war soyayyarsu, cikin
nutsuwa