baci akan
abin da Daddyn yayi, wulakanci baya da dadı. Yana
zaune cikin falo, ta share shi bata shiga harkar shi ba,
shi kuma ya rinka janta da hirfa, amma ta share shi, ya
Sata mata rai da yawa, duk da cewa Dr. Khalid baiyi
mata magana akan abin da yayi ba, ta sani ranshi ya
6aci. Tana ji suna maganar buki dca Mummy, yana yi
mata bayanin yaje yaga gidan, yana sanya ran cikin
satin za'a fara gyara. Ta ce "Ya maida hankali ayi a
gama susan sun jure wannan." Sai ya waigo yana
kallanta, ta daure fuska sosai.
Bata jima da zama ba ta tashi ta shiga kicin, ta
hado tea ta sha, ta dawo tgayi ma Mummy sai dasafe,
sai ta kalle shi kawai, bata ce mashi komi ba, ta shige
cikin daki. Ta shiga kewaye ta dauro alwala ta dawo
tayi nafilar shafa'i da wutiri, sannan tayi shirin
kwanciya. Bata kai ga kwanciya ba, taji wayar Daddy,
ta zubama wayar ido tana kallon sunan shi "Me zaya
ce mata?" Abin da ta fara tunani kenan. Don haka ta
share wayar har ta tsinke, abu guda ya hana ta rufe
wayar gaba ki daya, saboda Dr. Khalid kullum dare
32
sai ya kira ta yayi mata sai da safe, idon bacin haka ta
rufewa tayi baki daya bata bukatar jin komi da gare
shi.
Bata gama wannan nazari ba, wayar shi ta sake
shigowa, sai ta kasa daurewa ta zauna bakin gado, ta
dauki wayar ta amsa. Ya ce "Ba dai har kinyi barci
ba?" Ta ce "Banyi ba." Ya ce "Fushi kikeyi dani,
laifin me nayi maki?" A hankali ta saukar da ajiyar
zuciya. Ta ce "Abin da kayi ma Dr dazu banji dadin
shi ba." Ya ce "Da nayi me?" Ta ce "Ka shigo muna
tare, kuma duk ba wani tazara ne inda kake da inda
muke ba, akalla sai ka daure ka zo ku gaisa. Amma
sai ka daga mashi hannu kawai kayi shigowarka, kayi
imanin idan kai akayi ma haka ba zaka ji dadi ba, shi
kanshi yana (Complening) kan cewa baka bashi fuska,
ko dazu nasan ya bata mashi rai, kawai dai yayi shiru
ne."
Daddy yayi shiru yana saurarenta. Hakan ya
sanya tayi tsammanin ko ya aje wayar ne, sai da ta
duba taga bai aje ba, dan haka ta ci gaba da magana.
Ta ce "Irin haka babu dadi, mutum ko yaya yake idan
ya zo inda kake ai ya dace ka mutunta shi, to baka yin
haka Daddy, yaya kake so inyi? Idan kuma kana ganin
baka son zuwan shi gidan nan, kada ka boye ka fadi
mani sai inyi mashi magana ya daga ma zuwan." Ya
saukar da ajiyar zuciya. Ya ce "Ba haka bane Naja'atu,
kin kasa fahimta ta ne, ko da yake na sani wannan
wani sirrin zuciyata ne, ban san dalili ba, Allah ya
sanya mani kishi akan shi, wallahi na tsani in ganki
33
1
tare da wani da namiji." Ta ce "To amma Daddy
wannan ba hujja bace, tunda kasan dole wata rana
wani zani aura."
Ya ce "Na sani, sai dai ina son ki fahimci bani da
nufin takura maki akan wani ra'ayi da kike dashi,
nima ina da nawa ra'ayin, a hankali zaki fahimta, don
haka ki ci gaba da hakuri dani." A hankali ta saukar
da ajiyar zuciya. Sai yayi mata sallama ya rufe wayar.
Tayi shiru tana kallon wayar, ta rasa gane kan Daddy
da inda ya dosa, nema kawai yake yayi mata yawo da
hankali, amma insha Allahu zata yi kokari ta danne
zuciyar ta, me yiwuwa don ya fahimci tana sonshi shi
yasa yake neman yayi mata yawo da hankali.
Ta kwanta shiru kan gado, tana tunanin lamarin,
matsalar ta guda, kaunar Daddy tayi nisa cikin zuciyar
ta, ta yarda sai ta sha wuya kafin ta samu ta rabu da
ita baki daya, jin dadin ta daya shine da Allah ya hada
ta da Dr Khalid, yana son ta tsakani da Allah, tayi
imanin idan ta bashi hadin kai yanda yake so, to kuwa
zaya sota kamar yanda take mafarkin samun Daddy.
Allah ya tabbatar da haka.
Ranar laraba tunda safe direba ya tafi Zaria zai
dauko Zainab, basu iso ba sai yamma sosai. Naja'atu
bata da aboki sai Ibrahim idan dai yana gida, to kuwa
suna tare, barci kadai ke raba su don ma ta samu
Mummy tana da saukin kai, tana janta jiki. Amma ba
kamar Zainab din ba, kusan tsararta ce, kuma
hankalin su ya zo daya, Zainab na kaunar Naja'atu
sosai, jin take kamar 'yar uwar ta ciki daya. Ranar
34
kusan kwana su kayi zaune suna hira, da suka taso daga falo suka shigo daki, nan ma suka dasa wata sabuwar hirar, don haka washe gari har rana basu fito ba, sai da Mummy ta shigo tana yi musu magana.
Da yamma kuma fita su kayi zuwa gidan Aunty A'isha, Zainab ke jen motar, Naja'atu na zaune gefenta, suna hirar su har suka isa. Aisha ta rinka
yima Naja'atu korafin bata son zuwa gidantga, tasan
yauma Zainab ce ta jawo ta. Naja'atu tayi murmushi ta
ce "Kiyi hakuri, idan na fito na bar Mummy ita daya a
gidan bata jin dadi." Tayi murmushi ta ce "Ba wani,
ke dai kin fi son ki zauna gida, ko da yake rannan
Daddy ya zo nan yana yi mani korafin wai kin samu
wani mekwakwancin saurayi, ko da yaushe yana like
da ke, duk yabi ya damu sai mita yake yi, na ce mashi
to kai ina ruwan ka? Kai da ke shirinyin aure? Ko ko
shiga zaka yi? Sai dai yayi murmushi, shine na ce ai
naje gidan in ganki in ji maye sirrin abin?"
Naja'atu tayi tsuru-tsuru, duk sai taji nauyin Aisha,
yayin da Zainab ta zuba mata ido, ta ce "Wai haka ne
Naja'atu?" Tayi murmushi ta ce "Allah kuwa Aunty
babu konai tsakani na da Daddy, kai ni na rasa gane
matsalar shi, ya tsani Dr Khalid, har bani son ya zo
gidan idan Daddy yana nan, ko kuma ya zo ya same
shi, duk yanda za yayi sai yayi mashi wani abu da
zaya taba mashi zuciya, nayi mashi magana na ce idan
wani abu yayi mashi ya sanar dani, ya ce babu komi,
to yaya yake so inyi?" 35
A'isha ta zuba mata ido, ta ce "Kuma ke tsakani
da Allah baki fahimci wani abu game dashi ba?"
Naja'atu ta girgiza kai ta ce "Babu komi, kuma ma
Aunty Aisha yanzu ina saura?" Zainab ta ce "To nima
abin da nake hange kenan, amma da zaya hakura da
Fardar nan ya dawo wajan ki ai da munfi murna, to
shi ya wani nace mata, ni banga abin so ba." A'isha
tayi dariya, ta ce "Ke dama ai baki kaunar Farida, to
Allah ya kaddara ita ce matar yayan ki, don haka sai
dai hakuri." Zainab ta tabe baki, ta ce "Allah ya
kyauta, sai dai ni kaina Naja'atu, don dai kina kokarin
boye maganar nan, amma yanda na lura da Daddy jiya
da yanda yake kallon ki anya babu wata a kasa?"
Naja'atu tayi murmushi ta ce "Ai sai ki fassara abin da
kika gani." Su kayi dariya baki daya.
Sai dare suka bar gidan, da suka koma gida basu
dade ba Dr Khalid ya iso. Suna falo suna hira Daddy
ya kira ta a waya ya sanar da ita, sai ta dubi Zainab
tana murmushi ta ce "Muje ku gaisa." Zainab ta ce
"Likitan ne?" Tayi murmushi kawai. Suka mike zasu
fita, ta dan kalli inda Daddy yake zaune, sai ya dauke
kai kamar bai san abin da su keyi ba, don haka su kayi
tafiyar su. A can waje Dr Khalid ya saki jiki sosai
suna hira da Zainab sai ka ce sun dade da sanin juna,
musamman da yake Zainab na karatu a A.B.U, shima
can yayi, sai suka rinka labarin makaranta. Itama
Zainab ta yaba kwarai, tayi ma Naja'atu fatan alkairi.
Da ya tafi suka koma cikin gida. Zainab ta wuce
cikin daki yayin da ita kuma Naja'atu ta shiga ciki
36
zata sha tea, sai ga Daddy ya shigo, ya tsaya kawai yana kallon ta, sai tayi murmushi, idan da sabo yaci ace ta saba da wannan mayataccen kallon nata, shi yasa mutane ke zargin cewa sonta yake yi, ita kau tasan ba haka bane, kallon rainin wayau ne. Ta karkace kai tana kallon shi ta ce "Wani abu kake so ne?" Ya zuba hannayen shi cikin aljihu tare da cije lebe. Kamae baza yayi magana, sai kuma ya dube ta
ya ce "Magana nake son yi dake." Ta danyi jim,
amma sai ta jinjina kai ta ce "Ina sauraren ka." Ya ce "Muje fali mu zauna maganar tana bukatar nutsuwa."
Bata yi musu ba, ta biyo shi suka fito, ya dauki
remote ya rage maganar talabijin.s Sannan ya zauna
yana kallon ta, yayin da ita kuma ta ce gaba da kurbar
shayin ta tana sauraren abin da zaya fada. Ya gyara
zama ya ce "Kin san rannan na ce zani samu lokaci
muyi wata magana ko?" Ta jinjina kai ta ce "Haka ka
ce." Ya ce "To yanzu ita nake so muyi, sai dai ina son
ki sanya fahimta a ciki." Ta ce "Ina jinka." Ya danyi
shiru yana kallon ta, sannan ya kira ta "Naja'atu." Ta bude idanuwan ta tar tana kallon shi. Ya ce "kin san
farkon haduwa ta dake rigima ce ta fara hada mu ko?"
Naja'atu ta ci gaba da kallon shi. Ya ce "To sai dai
wani sirri na zuciya ta da na kasa ganewa, shine tun a
ranar kika zauna mani cikin rai, na kasa yin barci, da
na runtse ido ke nake gani kina yi mani bala'i, gaskiya
lokacin raina ya baci, to amma a hankali sai na daina
ganin laifin ki, har na rinka tunanin ina ma Allah ya
37
sake hada ni dake, ban san dalili ba, zuciya ta da
Kwayar idanuwa na suna mradin ganin ki.
Da wannan tunani na kwana a raina, don haka
washe gari da na ganki babu zato cikin gidan mu, sai
abu ya daure mani kai, to amma sai na lura cewa har
zuwa lokacin kina cikin zafin na abin da ya faru jiya,
don haka nayi kokarin zuba maki ido inga inda kika
dosa, amma ke kanki idan zaki tuno, a lokacin ni ban
dauki abun da zafi ba, tun kafin in baro Katsina naso
mu zauna mu sasanta kanmu, to baki bani damaba, sai
dai wani abu da ya tsaya mani cikin zuciya, shine
yanda kika mamaye dukkan tunani na, ko bayan na
dawo nan na ci gaba da muradin son sake ganin ki,
cikin sa'a saio gashi munyi waya da Mummy ta sanar
dani cewa tare dake zata taho, gaskiya nayi farin cikin
haka.
Lokuta da dama na kanyi zargin kaina akan
dalilin da ya sanya zuciyata ta cika damuwa dake,
wanda ni kaina ban san dalilin haka ba, sai dai cikin
wannan lokacin da kina na fahimci cewa kaunar ki
nake yi. Naja'atu ina sonki, son da ni kaina ban san
lokacin da ya dasu cikin zuciya ta ba, na shiga rudani
sosai a kanki." Naja'atu ta rufe ido tana girgiza kai,
yayin da hawaye ke neman cika mata ido. Sai rinkа
dauka kawai dai yana son yaudarar ta ne, me za yayi
da ita alhalin yana shirin yin auren shi?
A hankali ta bude kwayar idon ta ana kallon
shi, ta ce "Daddy kanká daya kuwa? Kasan abin da
kak fada?" Ya koma ya zauna sosai cikin kujera yana
38
kallon ta, sai yayi murmushi ya ce "Kwarai kuwa na sani, cewa nayi ina sonki, don haka ki tsara mana mafita." Ta girgiza kai ta ce "Ba zaya yiwu ba, yaya zaka yi da farida, me zaka ce mata?" Yayi murmushi ya ce "Matsalar Farida ni ta shafa, kuma ai ba cewa nayi ba zani aure ta ba ko?" Ta ce "Kenan ni kake so ka bata ma rayuwa." Ya ce "Allah 'ya sauwake, ban taba yaudara ba, kuma ba zani fara ta a kanki ba, ina
neman tsari ga Allah, sai dai kada ki manta, nifa namiji ne, kuma mijin mace hudu ne. Naja'atu ni
nasan abin da na keyi, baki san tsawon lokacin da na dauka ina nazari akan wannan al'amarin ba, don haka ni dai ki daure ki saurare ni mu fahimci juna."
Ta girgiza kai ta ce "Gaskiya Daddy kayi hakuri,
ba zani iya ba." Ya ce "Saboda baki sona? Baki son kwanciyar hankali na?" Ta sarda kai bata ce komi ba.
Ita tunanin ta daya, kada ya sanya ta rabu da Dr Khalid daga baya ya zo ya juya mata baya, tunda
tasan yafi son Farida akanta, kuma idan ma wannan
maganar ta fito yaya Hajiya zata kalle ta. Idanuwan ta
taf da hawaye ta dago tana kallon shi, ta ce "Don Allah Daddy kayi hakuri ka janye maganar nan, ka auri wadda kake so kawai." Ya dan cije lebe yana kallon ta, sai kuma yayi murmushi ya ce "Kema ina sonki, kume na san. kema kina sona, ko ba haka ba?" Ya zuba mata ido yana jifarta da mayataccen kallon shi. Jikin ta yayi sanyi va ita iya da rayuwarta, sai ta sanya kanta cikin cinyovin ta, nauyin shi take ji sosai, gashi ya tsare ta da ido, ba zata iya furta kalmar ki
39
gare shi ba, saboda tayi imanin cewa kaunar tash take
yi, kuma har abada ba zata iya rabuwa da ita ba. To
sai dai a yanzu wuri ya kure, idon ma ta amsa mashi
cewa tana son shi, a me take? Hakurin da take
kokarin yin dai shine abinyi, shine abnyi, shine mafita
gareta, yanzu sai take jin tausayinta.
Daddy ya zuba mata ido tana duke, ya riga ya
gama fahimtar ta, don haka abin da tayi ko ta fada bai
daga mahi hankali ba, cikin ruwan sanyi yasan zaya
samu kanta. Sai yayi murmushi ya ce "Kina neman ba
kanki wahala Naja'atu, na sani kina sona, kuma ina
sonki, ki ture duk wani abu da kike hange mu tsara ma
kanmu yanda zamu tafiyar da al'amuran mu, wannan
shirmen jin kunya da kike yi ba zata fishe mu ba." A
hankali ta dago kai tana kallon shi. Ta ce "Daddy na
sani ina sonka, to amma ka duba yanda abin nan ya
taho, kowa ya sani ga wadda aka tsaida maku rana da
ita, kuma da bakin ka ka fabdi mani kana sonta, yanzu
idan ka kawo wannan maganar wacce irin fahimta
kake tunanin Mummy zata yi mana, gani zata yi muna
neman yi mata yawo da hankali, tunda nasan bata kai
kayan baikon ka gidan su Farida ba, sai da ta tambaye
ka ka amince, haka nima tasan ina tare da Dr Khalid,
ba sau daya ba munsha yin maganar shi da ita, yanzu
idan muka zo mata da wannan maganar kuma wanne
irin duba zata yi mana?"
Ya ce "Amma kin sani Mummy tana sonki ko?
Don haka zata yi farin ciki sosai, idan aka ce nine na
aure ki ba wani bare ba, duk wani abin da zaki duba
40
sai da na duba shi kafin inyi maki magana, sai dai kawai idan baki yi, wanen nasan bakyaji ne on your own, amma ba da wani hujja ba." Sai tayi shiru tana kallon wani bangare. Ya jima yana sauraren abin da
zata fada bata ce komi ba, don haka ya dan duba
agogo, sannan ya dubé ta ya ce "Kije ki kwanta dare
ya fara mikawa." Ta mike jikin ta bubu karfi, tayi mashi sallama ta nufi daki.
Da ta shiga Zainab na zaune kan gado bata yi barci ba, tana duba wani littafi, sai ta rike littafin tana kallon Naja'atu, suka yi murmushi baki daya. Tga ce "Ni kau idan nice ke Naja'atu ina da kamar Dr Khalid wallahi ba zani 6ata ma kaina lokaci ba wajan
sauraren Daddy, dake shirin auren watga, idan har
sonki ya keyi ba gida daya kuke zaune ba, donmi ya
amince aka sanya mashi rana da Farida?" Naja'atu ta
zauna bakin gado, bakin ta ya mutu. To sai dai duk
wani laifin da take kokarin dora ma Daddy ita bata
ganin shi, abin da ya bata mamaki ma shine yanda
akayi Zainab ta san maganar da suka yi.
Ta jinjina kai tana kallon Zainab din, ta ce "To
Zainab yayha zanyi? Kin san dai ba yanda za'ayi in
fito ince ma Daddy bani son shi." Ta ce "Kuma kin
san duk irin yanda zaya soki bai kai yanda Dr yake
son ki ba, tunda shi raba maku son za yayi ku biyu,
wannan kau ke kadai ke dashi." Tayi murmushi ta ce
"Haka ne, to sai dai Zainab yaya zanyi da Daddy?"
Zainab ta tuntsere da dariya, ta ce "Matsalar kenan,
kuma kina son shi, dan haka ba zki hango abin da
41
nake nuna maki ba, sai dai idan zaya hakura da
wancan auren." Naja'atu tayi murmushi kawai. Ta
tashi tana canja kaya yayin da Zainab ta ci gaba da yi
mata korafin cewa "Dr Khalid yafi dacewa da ita." Ita
kam ta yaba da mutumin simple man, ba kamar
Daddy ba.
Naja'atu ta ce "To wai ke dca kike ta faman
karafi, kin ji da baki na nace ina son Dr Khalid ne?
Ko kuma na ce maki zani aure Daddy? Ko shi da yake
maganar shi ai na fada cewa ba zaya yiwu ba." Zainab
tayi murmushi ta ce "Amma kin san na fiki sanin
Daddy, wallahi tunda ya furta wannan maganar
tsakanin ku nayi imanin cewa abin cikin ranshi yake,
kuma duk yandca za yayi yaga ya samu za yayi, bake
ke ba za ya sha wahala ba, wajan karkato zuciyar ki,
tunda kema kina sonshi." Naja'atu tga jinjina kai
kawai. Ya ta iya da rayuwar ta? Batag da zabi sai abin
da Allah yayi, don haka tayi kwanciyar ta tana jin
Zainab na ta faman yi matga korafi akan kada tga
biyhe ma zuciya ta rabu da Dr Khalid, to itama tana
hangen haka, sai dcai zuciyar tga tafi yarda da Daddy,
amma dai batga zafafa ba, ta barma Allah komi.
Sai da akayi kwana biyu Daddy bai sake
tuntubar ta da maganar ba, sdai dai ga baki daya
hidimomin shi ya dora mata, kafin ya fita da safe,
ka'ida ne ya tasa ta ta bashi kalaci, haka nan idan ya
dawo ma duk inda take za ya nemo ta, gyaran dakin
shi da sauran hidimomi ita yake sanyawa, abun yakа
ba Zainab haushi, ta rinka yi mata fada, amma sai ta
42
Jura Naja'atu tayi nisa bata jin kira, idan ma tana yi mata fadan sai ta nuna bata so, don haka ta rabu da ita, ita dai tasan tafiyar ba mai tsawo bace, saboda in dai Naja'atu tasan ciwon kanta, muddin taga Daddy ya auri Farida, to kuwa zata san cewa yawo da hankalin
ta kawai ya keyi.
Cikin hikima da sigar yaudara ya janyo Naja'atu sosai cikin jikin shi, yanzu gaban kowa magana yake yi mata, shi kanshi wasu abubuwan idan yayi Zainab
mamaki ta keyi, abun nasu da daure kai, da gaske yake nuna mata kauna. Mummy na lura da takun su, da farko sai take tsammanin abun na wasa ne, amma
yanda taga Daddy ya rufe ido abu babu was, sai ta
fara jin tsoro tana zargin wani abu, me yiwuwa so
yake yi ya sanya ta taji kunya kan maganar da akayi
gidan su Farida, abun ya fara damun ta, amma ta zuba
ido taga iya gudun su.
Yau da safe da yake sabar ce, Naja'atu ta fito
daga cikin daki, Daddyn na kwance cikin kujera yana
kallon wasan kwallon kafa. A hankali ya sauke
kwayar idonshi akanta, sai tayi murmushi ta ce mashi
"Ina kwana?" Ya ce "Good morning my angel, ya kike?" Tayi murmushi kawai. Ya ce "Kawo mani tae
nan, ki zo muyi wata magana tsakanin mu tana kurewa." Ta girgiza kai ta wuce kicin ta shirya kayan
tea kan tire ta fito ta aje, sannan ta hada ta mika mashi. Yana kallon ta ya karba, a hankali bakin shi ya
furta "Na gode." Sai ta yi dariya, irin abubuwan dake
43
burge ta kenan ga Daddy, duk abin da tayi mashi sai
yayi mata godiya, komin kankantar shi.
shan Ya nuna mata kujera ta zauna, yana tea
dinshi, shiru bai ce mata komi ba. Sai ta dube shi ta ce
"Ko dai in koma in kwanta, in anjima munyi
maganar?" Ya girgiza mata kai ya ce "Har yanzu kin
kasa fahimta ta Naja'atu, ban san dalili ba, nema ki
keyi ki canja mani halayya, nafi son duk lokacin da
zan ci abinci ya kasance kina kusa dani, sai in samu
kuzari in ci abincin fiye da kima, amma wallahi idan
baki kusa dani sai in ji duk ya gundure ni. Wai dan
Allah menene sirrin hakan?" Naja'atu tayi dariya, ta ce
"Kai zani tambaya, sai dai mamaki kake bani idan
kana yin wannan maganar, Daddy kada fa ka manta
cewa ba nice matarka ta farko ba, idan kana fadın irin
haka akaina, idan ka aure ta yaya za kayi?" Ya dan
lumshe ido yana murmushi. Ya ce "Addu'ar da nake yi
kenan, Allah ya sanya ta rinka yi mani irin yanda kike
yi yanzu, Allah kuwa dadi nake ji idan na ganki fesfes
kina tare dani, musamman lokacin da nake cin abinci,
wannan ba karamar kulawa bace, ki lura da yanda
nake kara budewa, kuma duk kece."
Tayi murmushi kawai, ta saba da cika bakin
Daddy, sai yayi auren shi ya manta da ita, kilama ya
ce bata taba yi mashi komi ba, halin maza sai su,
Allah yayi musu baiwar iya tsara mace, don haka suke
iya aje mata hudu, kuma ko wace da abin da suke fadi
mata. Har yanzu tana shakku akan lamarin, amma da
tayi mashi magana sai ya bata rai baya so, ya sha fada
44
mata cewa matsayin ta daban gare shi, haka nan itama
Farida nata daban, ko wace da irin muhimmancinta
gare shi.
Dai dai lokacin da suke kwarara hirar su, Zainab
ta fito ta shiga dakin Mummy. Itama ta tashi, sai dai
bata ko yi wanka ba, tayi sallama ta shiga, Mummy ta
amsa mata. Ta ce "Mummy ina kwana?" Ta amsa
mata "Lafiya lau, yau kuma da wuri kuka tashi? Ina
Naja'atu?" Zainab ta zauna bisa wata kujera dake cikin
dakin, ta ce "Itama ta tashi, gata nan falo tare da
Daddy." Mummy ta jinjina kai tana kallon Zainab,
amma sai ta kasa daurewa ta ce "Wai me yake faruwa
tsakanin Daddy da Naja'atu ne?" Zainab tayi
murmushi ta ce "Gaskiya Mummy Daddy neman
Naja'atu ya keyi." Mummy ta ce "Kuma ita ta
amince?" Та се "Тa amince tunda itama tana son shi,
har alkawari yayi mata cewa zaya aure ta."
Mamaki ya cika Mummy, yanzu ta san cewa
daga Daddy din har Naja'atu basu da hankali. Ta ce
"Amma Naja'atu bata yi mani wayua ba, idan shi baya
da tunani, don mi zata biye mashi? Duka yau kwana
nawa da sanya mashi rana, ko auren bai yi ba, zaya
sanya wata maganar? Kuma kafewa ce irin ta Daddy,
tun kafin aje ayi magana gidan su Farida sai da nayi
mashi magana, kan cewa ko zaya dawo ya nemi
Naja'atu ne? Ya ce ba haka ba, aishi yayi ma Farida
akwari kuma ba zaya saba ba, shine ba'aje ko ina ba
zaya bullo da maganar? Itama har da ita, me yaron dia
ke zuwa wajan ta ya rasa da zata nema wurin Daddy"?
45
Zata biyc mashi yana bata mata lokaci. To ba zani
yanrda da wannan sakarcin ba, tun wuri zani taka
mashi burki."
Zainab ta rinka tausar Mummy tayi shiru kada
Daddy yaji ya ce ita ce ta sanya Mummy take fadan,
da taga ranta ya 6aci sosai sai ta taso ta fito ta koma
cikin dakin su tayi kwanciyar ta, a zuciyar ta ta rinka
dariyar keta, tunda fada Naja'atu gaskiya taki ji,
yanzu idan Mummy tayi magana dole ne yaji.
Cikin falo suka ci gaba da hirar su cikin
kwanciyar hankali, har zuwa lokacin da Mummy ta
fito suna tare. Gabaki daya suka gaida ta. Naja'atu ta
shiga kicin dauko mata kalaci, to shima Daddyn bai
zauna ba, ya ce za yaje cikin gari yayi aski, daga can
zaya bada motar shi wajan wanki, dan haka sai dai sun
ganshi. Da ya bar falon sai ya nufi kicin inda Naja'atu
ke tsaye tana juye dankali a filet, ta juyo tana kallon
shi sai tayi murmushi, shima ya taya ta ya ce "Ayi
mani lamuni zani fita cikin gari?" Tayi dariya ta ce
"Don Allah ka rufa mani asiri Daddy, Farida ce ke da
wannan ikon a kanka bani ba."
Sai ya rinka yi mata dariya. Ya ce "Inda rai wata
rana zaki kai ga wannan matsayi, bari dai barki kiyi
aikin ki, me zani taho maki dashi?" Ta zuba mashi
tana murmushi. Sai ya jinjina kai ya ce "Shi kenan na
fahimta, zani shiga Sahad in taho maki dasu." Ta ce
"Sai ka dawo." Yayi murmushi yana tafiya da baya.
Sai da ya kai kofa, sannan ya juya ya fita. Tayi
murmushi tana jinjina kai, "Daddy a lamrin shi sai
46
shi." Zuciyar ta ta sanya ta ci gaba da godiyar Allah cikin zuciyar ta da ya tabbatar imata da mafarkin da ta jima tana yi, wai yau ita ce Daddy yake nuna ma so irin haka? Dadi take ji sosai.
Mummy zaune cikin falo, ta fito ta zo ta aje mata
farantin gabanta bisa tebur. Mummy tayi mata godiya,
tana jin dadın yarinyar, tana kula da ita sosai, duk
wani abin da ya shafe ta tana daukar shi da
muhimmanci, sai taji ba zata iya yi mata magana ba
kamar yanda tayi niyya, ko ba komi 'idan tayi mata
magana zata ga kamar tayi mata cin fuska, kuma zata
sanya taji kunyar ta, dan haka ta rabu da ita ya fi,
Daddy din ya kamata tayi ma magana.
Dan haa bata ce ma Naja'atu komi ba, suka ci gaba da
zama cikin faton, sai da Dr Khalid ya kira ta, sai ta
tashi ta shiga dakli ta zauna bakin gado suna magana,
yaje Kano duba kannen shi, ya sanar da ita cewa ya
isa lafiya.
Da yamma Daddy ya shigo gidan, lokacin su
Zainab basu nan sai Mummy da wata bakuwa. Yana
shigowa bakuwar