An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
SIRRINZUCI
SA'ADATU SAMINU KANKIA
(Mrs. Sani Abbas)
Hakkin Mallaka (m) Sa'adatu Saminu Kankia
Copy right (c) Sa'adatu Saminu Kankia
An rubuta a shekara ta: 2008
GODIYA TA MUSAMMAN
Ga daukacin masoyana, makaranta littattafaina,
fatan alkairi a gare ku baki daya, ina godiya, akan
addu'ar da kuke yi mani da fatan alkairi, Allah (S.W.Т)
ya bani ikon ci gaba da yi maku yarda kuke so, kuci
gaba da yi mani addu'a, shi ne fatana. Ina alfahari daku
koda yaushe.
2
SIRRIN ZUCI - 2
Z
uciyarta cike da sake-sake na tunanin Likitan da labarin da ya bata, sai ta rinka jin tausayinshi, ta yi sallama ta shiga, daga murmushi, ta raba su zata wuce cikin daki. Daddy ya dago kao yana kallonta, ya ce "Zo nan Naja'atu." Ta tsaya cak tana
kallonshi, to bata yi musu ba sai ta koma ta tsaya kusa da kujera, yayin da shi kuma ya dan hada rai ya ce,
"Zo zauna, ki fadi mani abin da ya ce maku." Mummy dake zaune gefe daya tana kallon su, ta kasa daurewa
cike da mamaki ta kalle shi ta ce "Wace irin tambaya
ce haka Daddy, kanka daya? Ina ruwanka da zaka ce
sai ta fadi maka abin da ya fadi mata sai kace karamar
yarinya.?"
Ya kara daure fuska ya ce, "Amma Mummy
yaya za'ayi daga zuwan mutum a yarda dashi ba'a
tsaya wani bincike ba." Mummy ta yi dariya, ta cе
"To ai dama shi aure ya gaji haka, kana ina mace
auren mutumin da ba ma jinsu daya ba, bata son shi
ba balle in da ya fito, in dai soyayya ta hada su ya
aure ta a zauna lafiya har da zuri'a balle ni banga
laifin wannan Likitan ba, Musulmi ne kuma bahaushe
irin mu rashin saninshi kuma ai ba matsala ba ce duka
yaushe suka hadu? Ka bari tafiya ta yi tafiya mana
kana nan zaya kawo 'yan'uwanshi, kuma ka ji duk iya
abin da kake so ka ji a akan shi."Ya ce, "Ni Mummy
kin kasa fahimta ta ne, rayuwa ta canza, yanzu dole ne
sai an sanya ido fa." Ta yi murmushi ta ce, "Idan dai
3
bayanin da na yi maka bai gamsar da kai ba, to ba zani
taba fahimtarka ba, sai dai abin da nake so ka fahimta
shi ne, babu dalilin da zaya sanya ka zuba ma yarinya
ido alhalin kai babu wanda ya zuba maka, ko kuwa shi
kenan ta ci gaba da zama kenan ba zata samu miji ta
yi aure ba, saboda wani ra'ayinka can daban, ko
kwanaki da kaga na zuba maka ido ka kawo wannan
yaron da ya fara zuwa wajentga, don nima ban yarda
da take-taken shi ba ne, amma wannan na fadi maka
babu ruwanka ka rabu da ita, ai ta mallaki hankalinta,
kuma tasan abin da yake daidai da ita, sai ka bari idan
ta yi abun magana sannan kayi, amma ni bani son
tsangwama irin haka."
Sallamar maigadi ta katse Hajiya, yayin da ya
shigo da iyayen kaya cikin ledoji ya aje ya ce, in ji
wannan bakon da yazo na Naja'atu ne." Daddy ya
kara hade rai, yayin da idanuwanshi suka kada suka
yi jajir, sai huci yake yi, ya wurga ma Naja'atun
harara, bai yi magana ba, ya jefa remote din dake
hannunshi bisa kujera ya mike ya nufi daki. Hajiya ta
yi dariya cikin zuciyarta ta ce, "Kayi ka gama, ka
dawo bisa hanya." Ta juya tana kallon Naja'atu da ke
tsaye cikin damuwa, ba ta ji dadin abin da Hajiya ta yi
ma Daddyn ba, duk sai ya bata tausayi, kai sai ta rinka
ganin laifin kantga, da ta sani bata fita ba, bata son
ganin bacin ranshi. Hajiya ta ce, "Zo kwashi kayanki
rabu da shi kinatsu ki kwantar da hankalinki ku
fahimci juna, idan Allah ya kaddara shi ne mijinki
zani yi murna." 4
Jikinta ya yi sanyi, ta duka ta kwashi ledar kayan ciye-ciycn ta kai kicin, sannan ta debi na kayan shafa
ta nufi daki, hirar ranar ta ruguje gashi Daddy ya yi
fushi, gaba ki daya sai ta ji ta tsani kayan, kai shi
kanshi Likitan ji take yi zata iya rabuwa da shi tunda Daddy ba ya so. Dare ya fara mikawa tana kwance
kan gado, sai juyi take yi, kalaman Likitan suka rinka
dawo mata cikin kai daya bayan daya, ta gamsu da
abin da ya fadi mata, kuma ga alama manufarshi
akanta alkairi ce, irin mijin da take mafarkin samu
kenan, watau zasu fahimci juna su gini zuri'arsu bisa
tsarin kansu, to amma da ta tuna Daddy da yanayin da
ya shiga, sai ta ji damuwarta ta karu, har ta rinka jin ta
rabu da Likitan kawai shi yafi. Daddy shu'umin
mutum ne, ya iya birkicewa, ita kuma da zaran taga ya
canza, shi kenan sai hankalinta ya tashi.
Har kuka ta yi damuwa ta yi mata yawa, ta
lalubo wayarta ta bude da nufin ta kira shi ta ba shi
hakuri, amma sai ta kasa, tana gudun kada ya fadi
mata bakar magana, balle yana cikin fushi, da wuya
ya dauki wayar, ta maidata ta aje gefen filo, ba'a jima
ba, ta ji kira ya shigo jikinta na rawa ta tashi zaune ta
dauki wayar, sai taga sunan Daddy zuciyarta ta rinka
dakan uku-uku, kamar kada ta dauka, sai taga rashin
daukar ma wani laifin zaya janyò mata, kara ta dauka
ta ji meye ra'ayinshi, idan ya ce ta rabu da Likitan shi kenan sai ta ba shi izinin ya sallame shi ba tare da
Mummy ta sani ba.
Ta bude wayar ta manna a kunne. Muryarshi a
5
dusashe alamar har yanzu bai warware ba, ya ce
"kema bake yi barcin ba? Ta amsa mashi "Eh." Ya ce,
"Me zaya hana ki barci Naja'atu.?" Ta runtse ido tana
jin zuciyarta na yi mata wani irin tukuki, a hankali ta
ce, "Babu komi ina shirin yi yanzu." Sai ya yi shiru
kamar ya aje, ta dan saurara ta ji shiru, ta ce "Daddy
ka aje ne.?" Ya ce, "Ina saurarenki, kin gane ko, kiyi
hakuri kan abin da na yi maki dazu, naga daga ke har
Mummy ranku ya baci, ni kuma akwai abin da na
duba ne shi yasa na yi maki magana, amma tunda
Mummy ta ce in rabu dake shi kenan." Ta ce, "Daddy
fushi kayi kenan.?" Ya ce, "Ko daya, na yi tunani ne
sai naga abin da Mummyn ta fada gaskiya ne don
haka ina yi maki fatan alkairi."
Ta saukar da ajiyar zuciya, hankalinta ya kwanta
ta ce, "Daddy na gode." Ya ce, "Kada ki samu
damuwa, kwanta kiyi bacci, Allah ya ba mu alkairi."
Ya rufe wayar, itama ta tsaya tana kallon wayar sai
tayi murmushi ta rufe baki daya ta jefa karkashin
filonta. ko ba komi ta samu natsuwa, don haka cikin
kwanciyar hankali ta yi barcinta. Washe gari bata fita
da wuri ba, har Daddy ya fita ofis don haka ta kara
samun natsuwa.
Da yamma ne suka yi bako gidan kanin mahaifin
su Daddy, Alhaji Isa, yazo kan maganar da suka yi da
Hajiya ta waya kan zuwa neman auren Daddy gidan
su Farida. Har zuwa lokacin Daddy yana ofis bai
dawo ba, Hajiya ta fito suka zauna falo, ana gaisawa
sannan ta kira Naja'atu taje ta kawo mashi kemu da
ruwa, ta gaidashi to sai ta komi kicin suna aiki tare da mick.
Mummy ta ce, "Yau da nayi niyyar fita in same ka, saboda mutanen nan tunda suka aiko ba'a tura
masu da wani bayani ba, sun ji shiru, kada su dauka
ana wasa da maganar ne, don haka na ce kara mu
zauna asan meye abin yi". Alhaji Isa ya gyara zama ya
ce, "Haka nc, rannan mun yi magana da shi Daddy din
kuma ya sanar dani cewa, ita dai wannan yariyar yake
so, to gobe nake sanya ran zuwa tare da wani abokina,
a tsaida magana shi kenan".
Hajiya ta ce, "Haka dai ya kamata ayi, ni kaina
nafi samun kwanciyar hankali." Daddy ya bude kofa
ya shigo, ganin Baban nasu ya sanya ya saki fuska
yana dariya, ya iso ya zauna yana gaida shi. Alhajin
ya ce, "Yaya ofis din yau?. Ya ce, "Alhamdulillahi
komi lafiya." Ya ce "Ya yi kyau, dama yanzu magana
muke yi akanka, dangane da maganar nan dai, ka dai
amince ita ka ke so ko.?" Ya dubi Mummy sai ya yi
murmushi, Alhaji ya ce "Magana zaka yi kada sai
mun kashe magana kazo da wata kuma." Ya shafa
kanshi yana dariya ya ce, "Babu damuwa, ku ci gaba
kawai nan din dai na tsaya." Alhaji ya dubi Hajiya ya
ce, "To kin ji, don haka goben insha Allahu zani je, sai kayi kokari ka sanar da su, su san da zuwanmu,
duk abin da muka yi zani biyo in sanar da ku." Hajiya
ta ce, "Shi kenan Allah ya tabbatar mana da alkairi." Alhajin ya mike yana shirin tafiya, Daddy ya bi bayan shi suka fita, yayin da ita kuma ta tashi ta koma
7
cikin daki. Yana tarc da Alhajin har ya tafi, sannan ya
dawo cikin gida, cikin falo ya hadu da Naja'atun ta
fito daga kicin zata nufi daki, duk maganganun da ake
yi tana jinsu tsab cikin kunnenta, yau kam ta ida
tabbatarwa Daddy ba ya ra'ayinta. Zuciyarta ta kare
sosai, ta dauke kai kamar bata ganshi ba, shima
kallonta yake yi yana lura da yanayinta tana shirin
murda Kofa ya kirata Naja'atu sai ta tsaya cak ba tare
da ta juyo ba, ya cc, "Yau kuma ko sannu da zuwan ba
zani samu ba.?" Shiru ta yi ba ta ce mashi komi ba, ya
ce, "To zo ki kawo mani abinci yunwa nake ji." Ba ta
yi musu ba ta nufi teburin cin abinci, yayin da shima
ya wuce cikin dakinshi, har ta gama zuba mashi
abincin yana ciki bai fito ba, don haka ta sanya wani
filet din ta rufe mashi tana shirin tafiya sai gashi ya
fito har ya canza kaya ya ce, "Sorry na barki kina jira
ko.?" Muje ki kai mani cikin falo."
Ta dauko ta bi bayanshi zuwa cikin falon, sai ta
ajc kan tabur, sannan ta janyo shi gabanshi, ta koma ta
bude firij ta fiddo lemuna kwali da robar rujwa ta aje
kan faranti ta hado da kofi, ta kawo ta aje mashi yana
kallonta ya ce. "Sannu na gode." Sai ta dan saki fuska
tana kokarin boye damuwarta. Ba ta zauna ba ta juya
zata tafi, ya ce "Zo zauna mu yi hira mana, wai saurin
me kike yi haka.?" Ta dube shi tsab cikin ido, yayin
da shima ya zuba mata nashi, zuciyarta ta yi sanyi, sai
ta yi murmushi ta dawo ta zauna, tana kallo yayin da
shi kuma ya fara cin abincin yana nazarinta yanzu
tausayinta yake ji, saboda iya nazarin da ya yi mata ya
8
fahimci tsananin kaunar da take yi mashi, to shi
kanshi ya rasa abin da yake damunshi dangane da ita,
kai matsayin da komi yake yi tana cikin zuciyarshi,
yarda yake jinta a ranshi yanzu nema take yi ta take
Farida, abun har tsoro yake ba shi, musamman ganin
yarda abubuwan da suke ta kara tsananta ko daren jiya
sai da ya yi mafarki da ita, abun ya tsaya mashi cikin
rai, ya yi imanin matsawar bai dauki mataki ba,
al'amarin zaya iya canzawa, don haka ne ya amince da
auren Faridar, me yiwuwa idan yaga an tsaida lokacin
aurensu zaya yi kokari ya cire Naja'atun a ranshi,
baya son ita Farida ta zarge shi da cin amanarta, tunda
har magana ta kai gaban iyaye, dole ne da itan za'ayi.
Ya dan lumshe ido, sannan a hankali ya sauke
kwayar idonshi akan Naja'atun, cikin sa'a itama ta
kalle shi, sai suka yi murmushi ya ce, "Naja'atu matar
Likita, gashi kina tsoron allura, idan kuka yi aure yaya
kenan.?" Itama ta taya shi dariyar, tunda ta lura hirar
yake ji, ta ce, "Ai in dai yana sona ba zaya yi mani
allura ba." Ya zuba mata ido ya ce "ko.?" Ta cе,
"Sosai ma, ba ka gani ba, ko da bani da lafiyar da nace
bani son allurar kyale ni ya yi bai yi mani ba." Ya
jinjina kai ya ce, "Na yarda meye sunanshi.?" ta ce,
"Sai ka saya." Ya ce, "Kenan dai kina sonshi.?" Ta yi
murmushi ta ce, "Idan ban so shi ba in so wa? Ina
laifin wanda yazo ya ce yana sonka." Ya ce, "Babu
tunda kema kina so." Ta yi dariya ta ce "wa ya fadi
maka.?"
Ya ce, "Ai ba sai an fadi mani ba, alamunki
kadai sun isa su sa in sani, jiba dazu ba, fushi kike yi,
amma yanzu daga fara maganar shi kin saki kina
dariya kamar ba ke ba."Ta sunne kai tana murmushin
mugunta, ta lura dai kishin Likitan nan yake yi, ta ce,
"Yanzu kai don Allah idan aka yi maka maganar
Farida yaya ka ke ji.?" Ya zuba mata ido yana
tuhumarta, sai ta yi murmushi ta ce, "Ni ban ce ina
son Doctor Khalid ba, sai dai yana daya daga cikin
mutane masu muhimmanci a rayuwata, saboda ya so
ni a zuciyarshi, kuma ya fito ya sanar da ni, kaga
wannan shi ne dmauwa, ko da wasa idan mutum ya
furta yana sona, wallahi zani dauke shi da
muhimmanci." Ya ce "Ashe nima yanzu idan na ce
ina sonki, za ki bani irin wannan muhimmancin.?"
Ta girgiza kai, ta ce, "Ba ka fahimce ni ba, kai
son da zaka yi mani so ne na zumunci da kuma
matsayin da muke a yanzu, don haka ko baka fito fili
ka sanar dani ba, na sani kana sona, kuma ina na
sanyaka cikin mutanen da nake kauna kamar son da
nake yi ma 'yan'uwana da muka fito ciki daya. Kaga
irin wannan muhimmancin daban yake da irin wanda
zani ba shi, saboda shi ba jinina ba ne, amma kauna ta
sanya yazo in da nake, har ya nuna sha'awar muyi
zama dashi na rayuwa, gama nashi muhimmancin da
ban ne saboda ya shafi wani bangare na zamantakewa
daban, kamar yarda zaka auro Farida ne, kaga can
take waje daben ba jininka ba ce, amma so da kauna
ya sanya kayi sha'awar zama da ita na rayuwa, kuma
zaka bata muhimmanci daban da na sauran mutanen
10
da ka ke zaune tare da su tsawon lokaci."
Ya jinjina kai ya ce, "Na fahimce ki, sai dai kin
san cewa nima zani iya cewa ina sonki, kuma ki bani
wancan matsayin da kike magana.?" Ta yi murmushi
ta ce "Da kamar wuya Daddy, tunda zuciyarka wani
ruhin take so daban." Ya saukar da ajiyar zuciya, ya
ce, "Amma kinsan ni mijin mace hudu ne.?" Ta dube
shi da sauri, shima ita yake kallo, a hankali ta sauke
kwayar idonta tana kada kai ya ce, "Ko kina ganin
haka ba za ta yiwu ba.?" ta ce, "Zata iya yiwuwa,
amma akan wata." Ya ce, "Me zaya hana ke.?" Ta yi
murmushi ta ce "Mu bar maganar nan Daddy, yanzu
fa aka gama magana kan aurenka." Ya cem "To shi ne
me? Namiji nake fa.?"
Sai ta yi murmushi ta tashi ta bashi waje taga
yana neman kauce hanya, anya kan Daddy daya?
Yanda yake doki kan Farida ace har ya fara magana
kan wata? Ko da yake ita kanta tasan zolayarta kawia
yake yi, amma a cikin zuciyarta ji take yi, idan har
zaya yi mata hakan ta ji dadi.
Da dare ta yi zamanta cikin daki bata fito ba, saboda
Daddy na gidan, bata son ganinshi balle ya fama mata
gyambon da ke cikin zuciyarta, ta lura nema yake yi
ya yi mata yawo da hankali. Da safe ma har ya fita
tana cikin daki bata fito ba, da rana ne Alhaji Isa yazo
wa Mummy da labari mai dadi, cewa yaje ya gana da
mahaifin Farida, kuma sun yi murna da hakan, don
haka sun bada izinin akai kayan sanya rana, da na
neman aure baki daya." Mummy ta yi murna kwarai,
11
ita kanta idan taga Daddyn ya yi aure hankalinta zaya
fikwanciya, soyayya idan ta yi tsawo matsala take
ko kuma su janyo masu abin magana a gari.
Bayan Alhaji Isan ya tafi, ta yi shiri ita da
aja'atu suka tafi kasuwa, duk wani abin da za'a nema
cikin kayan baiko sai da suka sawo shi, har Naja'atun
tarinka jin haushin Mummyn ita ma ta cika zakwadi
kan auren. Ba su dawo gida ba sai yamma likis, loka
cin Daddy ya dawo gida, har ya sake shiri zaya fita,
cidn falo suka hadu da shi, Naja'atu ta dauke kanta
tana rike da jikkar Mummy, ta shiga daki ta aje mata
samman ta fito ta wuce su Mummy na yi mashi bayanin
salfon da Alhaji yazo dashi da kuma ita matakin da ta
dauka, sai yayi murmushi kawai ya yi mata sallama
ya fice wajen Farida zaya je.
Tafiya a tsanake bisa titi har ya isa gidansu,
maigadi ya bude mashi ya shiga, iyayen duka sun fita
don haka cikin falo ta shiga dashi. Hankalinta ya
kiyanta, murna fal da cikintga Daddy ya zama nata, ya
irra zaune cikin falon yayin da ita kuma take ta zurga
zurgar hada mashi abin motsa baki, sai da ta kimtsa
komi sannan tazo ta zauna, sanye take da wando na jin
ruwan bula, ya matse ta dam, ya fiddo surar jikinta
kar kalmar daya da lissafi, haka ma rigar ta tsuke ta
ta dda sassan wuyanta waya, har kana gano kirjinta,
sai ya dan lumshe ido har kullum yana da takaicin
irin, suturun da Farida ke amfani da su akasin Naja'atu
da koda yaushe take yin cikakkar shiga ta mutumci,
irin tamu ta Hausawa.
12
Ya dago yana kallonta sai ta lumshe ido tana
murmushi ta ce, "My man yaya ka ke.?" Ya dan saki
fuska ya ce, "lafiya lau Farida, ya jin dadi.?" Ta kara
fadada murmushinta, ta ce, "Lallai kam ina cikin shi
yau kasan wani abu.?" ya ce, sai kin fada." Та се,
"Allah duk da kkake cewa zaka aure ni, zaka aure ni,
wallahi jinka kawai nake yi gani nake yi kamar kana
shafa mani mai ne, ashe dai da gaske mafarkina zaya
zama gaskiya.?" Ya yi murmushi ya ce, "Har yanzu
kin kasa fahimtata Farida, ni magana daya nake yi,
bani son wani ya saba mani alkawari, kamar yarda
bani son in saba ma wani idan zaki tuna tun ba ki
mallaki hankalin kanki ba, ba ki ma san meye son ba,
ni na yi maki alkawarin cewa zamu yi aure, to meye
dalilin da zaya sanya yanzu da rana tsaka in saba
alkawarin? Alhalin ba ki ce baki sona ba.?"
Ta yi murmushi ta ce "Haka ne kuma na gode,
ka nuna mani cewa kana da alkawari, ba kamar, yarda
wasu mazan suke ba." Ya ce "Ke da Mummy ban san
wanda ya fi wani zumudin abun nan ba, yanzu itama
ta dawo daga kasuwa ita da Naja'atu, wai sunje
sayayyar kayan baiko." Farida ta yi dariya ta ce,
"Naja'atun tana nan bata tafi ba kenan.?" Ya yi
murmushi ya ce, "Tana nan, dama an fadi maki tafiya
zata yi ne? ta dan tabe baki ya ce "Wai ke don Allah
mcye dalilin da ya sanya ki ka tsani Naja'atu alhalin
ita kuma koda yaushe tana karfafa mani guiwa akan in
soki, da wuya muyi hira da ita bata yi mani maganarki
ba."
13
A
Don da nan Farida ta canza fuska, ta ce "Ni ba
wai damuna ta yi ba ne, abu guda nake dubawa
yarinyar tana da kyau, gashi kuna zaune wuri daya sai
na rinka ganin kamar yau da gobe idan kuna tare zata
iya janye mani kai ka koma wajenta." Daddy ya rinka
Kyalkyatar dariya, ya ce "Ashe ba ki yarda da kanki
ba kenan.? Та сe, "Bа haka ba ne, halinku nake ji
Daddy, idan ku ka ga jar fata balle wadda take
kwaskwas irin Naja'atun, ba wuya kun canza." ya ce,
"Amma ka da ki manta in da na yi zama can ma ne ke
da jajayen na usuli." Ta jinjina kai ta ce, "Share
wadannan ai su ba jinsika ba ne, amma ita wannan da
bambance, tare ka ke da ita koda yaushe, cikin zaman
da kuke yi zaka iya ganin wani abu wajenta da zaya
iya daukar hankalinka. Ba zani 6oye maka ba, wallahi
tunda nake ban taba jin kishin wata diya mace ba irin
Naja'atun, har barci take hana ni, kai wani lokacin ma
cikin mafarki ganinta nake yi muna fada saboda kai."
Daddy don dariya har da hawaye, ta ce, "Kana
daukar maganata wasa, Allah kuwa abin da ke cikin
zuciyata ne na fadi maka, don haka ko lokacin bukin
nan na gaya ma Mama a sanya lokaci kadan, idan
muna tare zani fi samun kwanciyar hankali." Daddy
ya ce, "To wai menene kike gudu.?" Ta ce "Tsoro na
guda kada ka ce zaka so yarinyar don gaskiya muddun
ka ce zaka so ta, ba karamin rikici rayuwata zata shiga
ba." Daddy ya yi tsuru yana saurarenta, saboda yanzu
haka yarda yake jin Naja'atun cikin zuciyarshi, abun
har ya fara bashi tsoro, idan ta fahimci haka yaya zata
14
yi kenan.?" Wannan wani sirri ne da ya bar ma zuciyarshi.
Hirarsu mai dadi cikin tsananin nuna kulawa ga junansu, hakan ya sanya Daddyn ya dauki lokaci sosai tare da ita, har Mama ta dawo. Suka kara tattauna maganar da ita, an fara kiran sallar magaruba, Farida
ta yi mashi rakiya har bakin motarshi, kamar yarda ya saba, sai da ya zauna sannan ya fiddo mata ledar da ya yi mata tsaraba, ya bata ta yi godiya, suka yi sallama ta shiga gida cike da zumudı yayin da shi kuma yaja
motar ya fita, kan hanya ya tsaya masallaci ya yi sallah, bai koma gida ba ya wuce asibiti duba mahaifiyar wani abokinshi da suke aiki tare, ba ya da aboki kamar Aliyu, sun damu da juna. Shi Aliyu asalin mutumin Funtuwa ne, jininsu yazo daya suna tafiyar da harkokinsu tare to mahaifiyarshi ce bata jin dadi aka kwantar da ita, jiya yau wajen aiki yake fadi mashi.
Da ya shiga cikin asibitin ta waya ya kirawo Aliyu sai gashi ya fito sannan suka shiga tare, ya jima tare da su da aka yi kiran Sallah suka fito suka yi sallah masallacin dake bakin get din, sannan suka koma ciki. Aliyu ya ji dadi kwarai musamman ganin yarda Daddy wanda ya fi kira da ainihin sunanshi Saddig, ya nuna damuwarshi akan abin da ya dame shi ga uwar hidimar da ya yi masu, haka nan ya jima tare da shi sannan ya yi masu sallama suka fito har wajen mota, ya nufo gida.
To kuma nan gida daidai lokacin Dr. Khalid ya
15
isa gidan Ibrahim na waje lokacin da ya iso, don haka
shi ya tarbe shi suka gaisa ya tambaye shi "Naja'atu na
nan kuwa.?" Ya ce, "Eh tana nan." Ya ce to ka fadi
mata ta yi bako". Ibrahim ya yi murmushi ya ce, "Ва
damuwa, ka shigo ciki kawai." Ya yi murmushi ya сe,
"Ba komi nan ma ya isa, shiga ka yi mata magana."
To bai yi musu ba, ya shiga cikin falon in da Naja'atu
ke zaune tare da Hajiya suna kallon wani film da ake
nunawa a tashar Nollywood, ya dauki hankalinta sosai
bata ji shigowar Ibrahim ba, sai dai ta ji maganarshi in
da ya ce, "Anty Naja'atu, kina da bako.?" Ta zuba
mashi ido a razane, ta ce "Ni?