Reading Deen Marshal By Mamuhgee Chapter 21 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇


09134848107






*_DM 49_*
Washe gari tun 7 na safe Bata qarasa bugawaba tadawo sashen hajjo bayan ya rakota har bakin kofar palon tashige ta Hana Masa shigowa ta hanyar rufe kofar bayan tashige sbd karyace zai bita dakinta yayi baccin safe hajjo tagansa,
Lallabawa Tai tashige dakinta tareda rufo kofar dakin ta Isa gadonta tafada sbd baccin dake idonta take bacci yadauketa ba Bata lokaci Dan yau din Kamar wadda wani Abu ya sameta tashinta kusan biyu cin abincin dare na farko cake da yoghurt Tasha na biyun Kuma kishirwane kawai ya tada ita duk shine yayi yawon dauko Mata daga kitchen zuwa bedroom shiyasa baccin nasu yake guntu guntu.
Bata farka ba Sai guraren karfe goma lokacin hajja batanan ta fita tareda Dad Alfa zuwa wani gurin,Bata fitoba Saida tayi wanka ta Sanya dogon skinny jeans daya lafe jikin siraran cinyoyinta da farar free long sleeves riga ta sako qaramar hula ta fito tana qamshin body mist kawai da bayama tashi sosai,yunwa takeji Sosai Dan Haka Kai tsaye dining ta nufa tana Dan qwala Kiran sunan ruqayyat ahankali Anatse.
Tana Isa dining din ruqayyat na isowa gabanta cikin tsananin girmamawa tace"


Gani Ma.


Ruqayyat ki bani tea me zafi sosai ki hadomin da sauran samosas din jiya.


To"ruqayyat din tace tana juyawa ta nufi kicin
Ita Kuma zama tayi tana janyo plate tareda zuba soyayyan dankali da aka hada da kayan miya ta kidney ta saka fork tafara ci tana Jin matsuwar akawo Mata tea din tafara Sha cikinta ya sake da ruwan tea din masu zafi.


Haniface ta fito daga dakinta tana kallon Naj din tace"


Barka da tashi Matar Marshal.


Da ido Naj din ta amsa Mata tana qin amsawa.


Dariya Hanifa tayi tana fasa wucewa ta dawo gurin Naj din tana cewa"


Da ido fa Kika amsa Uwargidan Marshal.


Kallonta Naj tayi bayan tagama Kai fork din Irish bakinta ta Dan bude Baki tace"


Wayene Amaryan to??


Daga bayanta taji an ranqwafo ya zuro Kai yayi kissing gefen fuskarta da kamammiyar muryarsa Yace"


Kece,
The only Mrs DEEN ALFA.


'yar dariya Hanifa keyi tana cewa"


Karka yaudari qawata fa JALAL,
Kafada Mata gskia,
Hannah na.....


Kallon da Naj Tai Mata na yaushe Kika daina Sona yasata dakatawa tana dariya tace"


Ban daina sonki ba my Naj gaskia nake fada Miki fa.


Zama yayi a kejeran dake kusa data matarsa Yana riqo dayan hannunta ya sarqe da nasa Yana kallon Hanifa yace"


Zaki hanata cin abinci ne?
koda wata ko Babu she is the only one a zuciyan JALALUDDEEN MARSHAL ALFA....the only Mrs DEEN ALFA.


Atareda Hanifan suka kallesa alokaci daya zuciyan kowannensu daukeda yanayi na farin ciki daga Hanifa,ita Kuma mamaki ne me girma da wani sabon yanayi Dake shigarta wadda takasa gane farin cikine kokuwa?


Kallonta yayi kamar bashine yagama maganarba Kai tsaye yace"


Sakamun abincin zanci Zan fita.


Sai data Kuma kallonsa kafin ta dauke idanuwanta daga kansa sbd yawan kallonsa Yana karya dukkanin qwarin qarfin halinta na kame kanta.
Zare hannunta tayi daga nasa ta Dan miqe tana daukan wani plate din tazuba Masa daidai ruqayyat na kawo tea din ta karba ta zuba Masa itama ta zuba Takoma ta zauna tana cigaba da cin abincinta zuciyarta cikeda sabon yanayi data kasa fassara hakan da komai face nutsuwar zuciya datake ji.


Yanda takecin abincin a yanayi na sanyi da tunanin da zuciyarta tayi nisa akai yasa harya Gama ya miqe ya Dan kalleta cikin kulawa yace"


Nafita ki kula." Ya wuce Yana daga wayarsa da ake Kira sbd harkan maganar Visa dinta ne na tafiyarsu Wanda shine yakawo Masa delay na tafiyar da tun jiya zai wuce Amma yanxu Sai jibi su tafi.


Bayan tafiyarsa ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda Dan rufe ido ta bude tana daukan ruwa Tasha itama ta miqe tabar gurin ta nufi dakin Hanifa tana zuwa ta zauna gefenta tayi shiru tsawon mintuna ba mgn kafin ta Dan motsa tareda bude Baki a natse tace"


Hanifa kina ganin Zan iya?


Sauke numfashi Hanifan tayi ahankali kafin itama a natse tace"


Naj idan kinason samun nutsuwar aurenki da rayuwar kwanciyar hankali tareda riqe zuciyar mijinki Zaki saka kanki Dole iyawa,
Zuciyarki na son mijinki meyasa bazaki bawa kanki qwarin gwiwaba da qarfin hali ki aje komai ki gwada sakewa kuyi rayuwar aure me cikeda kulawa da soyayya ahakan Zaki samu dukkanin soyayyarsa wadda ma bakinsa bazai iya fadaba.
Hannah na Tsananin son Auren Marshal Kuma zata iya maida kanta komai akan ya sota ya aureta Amma hakan bazai samuba sbd sonki da yayi Masa mugu shigarda har baya iya ganin laifinki ko fushi Dake akan duk abubuwan dakike Masa tun a farko,
Bansan yaushe,Kuma a Ina yafara sonkiba Amma dai ayanzun shine Yana tsananin sonki saidai irinsu idan baka riqe abinka ba zaka iya rasasu sbd yanada masu sonsa,masu jiran irin damar da kika samu ta zama matarsa,
Ina fada Miki hakan ne amatsayin qawarki Kuma Yar uwarki ba amatsayin Yar uwarsaba,
Samunki da yayi shima yayi dacenda wasu basuyiba Amma gskia wasu daga halayenki zasu Hana rayuwar aurenku sakewa idan har Baki daure kin ajeba,
Marshal kinsan a inda yatashi yake Kuma rayuwa acan yasaba da rayuwar sakewa ta turai shiyasa baimasan wani yin kawaiciba idan yatashi yin abubuwansa akanki
Dole kema Zaki Ari rayuwar dayakeson din ki sake jiki kuyi rayuwan kwanciyan hankali.


Bata iya cewa komaiba saima sake Shiga tunani datai sbd babban abin dayake juyi a zuciyarta shine kalmar sonta agurinsa,har tun yaushe yafara sonta?dama soyayya zata iya Shiga tsakaninsu me qarfi irin Hakan.


Sai kusan maraice hajjo tadawo lokacin suna can gidansu gurin umma suna cin abubuwa kala kala da anty Amina Bata fada musu Kona menene ba musamman Naj da idan taji zata iya qin cin duk da ba wani hadin me qarfi bane sbd ciki da Naj din takedashi Hanifa kuwa tun faraci tasan menene Amma itama tayi shirunta taqi fada,
Dambun Naman kaza ne da akaiwa Hadi da kayan gyara mace,sai kwakwa da aka soya itama da kayan gyaran dakuma lafiyayyan fura dataji fresh nono da yoghurt me shugar aka zuba wasu garin magani masu kyau da tsafta Kuma cikin sa'a Naj din Tasha sosai taci komai sosai sbd sun Mata Dadi abaki.


Tana sane dazasu tafi bayan sallar ishai ta sulale batareda sanin Dadah ba ta fito kafin taji Tai Mata abin data Saba.
Suna Isa gida hajjo Dake zaune Palo ta kallesu cikin kulawa tana cewa"


Fatima ta sakaltaku da qwadayi shiyasa kwana biyun Nan kuke yawon zuwa can Kuna dare,
Hanifa bakinki Nan Sam ko Babu ciki baya daina kwadayi.


Murmushi Naj tayi tana qarasawa kusada hajjon ta zauna tana cewa"


Hajjo barka da dawowa,
Da bakya Nan ne ba Dadi gidan sai muka fita,Amma dai Hanifa ce tajani Ni banmayi niyar fitaba.


Dariya Hanifan tayi tana zama tace"


Ciki dama harda sharri Yana sawa,
Dadah dai da gskiyarta kinci Amanarta gashinan Nima kin......


Matse fuskar da Naj tayi yasa hajjo Hana Hanifan qarasawa ta katseta da cewa"


Karna kumaji kina Mata tunin maganganun Dadah,
Dadan ma zanje na rufe Miki bakinta kinji Najma wannan gorin lagudan zancen ta taimaka tabarshi Haka.


Maganar hajjon tasake sakata Jin kunya ta fuske tana kallon Hanifa tace"


Hadda Hanifa hajjo kifara rufe bakinta kafin na Dadah din.


Hanifa Kika Kuma tada maganar Nan Zan Saba Miki kokuma ayau basai kin shiryaba ki tattara kibi mijinki.


Najma tashi kije ki dan gyara kizo ki kaiwa mijinki abinci yanacan yauma da ciwon Kai yadawo.


Sunkuyar da Kai Naj din tayi tana kasa amsawa hakama tana kasa tashi Saida hajjon takuma maimaita zancen kafin ta miqe ta nufi dining zata dauka takai tadawo
Hajjo tace"


Aa kindawo a gajiye ahakan Zaki?
Kije ki Dan gyara duk qamshin kwakwa ma kukeyi
Tashi kema,kuje kuyi wanka kafin taje takai Masa.


Tashi tayi ta wuce dakinta bayan tagama fadan sbd Naj tasamu sakewar wucewa wankan dakinta.


Saida hajjo ta shige kafin ta juyo ta nufa hanyar dakinta tanajin Hanifa na cewa"


Saida safe Naj.


Bata kulataba ta shige dakinta dama Kuma wankan takeson Yi har cikin ranta.
Wanka tayi tana fitowa ta saka kayan bacci riga da wado dogo har qasa kafin ta saka doguwar hijab Nayan ta shafa khumrah me sanyin qamshi ko wayarta Bata daukaba ta fito ta dauka abincin ta wuce zuciyarta na ingizata ga son sanin halinda yake ciki na ciwon Kan.


Tana isowa kofar palon sashen nasa ta tararda Hannah tsaye tana Shirin buga kofar.
Tsayawa tayi sukaiwa juna kallon mintuna biyu kafin Naj ta dauke nata idon tana juyar da kanta zuwa ga kallon kofar Shiga zuciyarta data sauya tana ingiza kanta ga juyawa ta komawarta Amma zuciyar ta hanata hakan sbd rashin sukunin ta tafi tabar Hannah din agurin,
Hannah ta juyar da fararen idanuwanta tana yiwa Naj din kallon mamaki tace"


Lafiya dai kuwa??


Dan qaramin numfashi ta sauke a boye kafin ta sake kallon Hannah da itama tsoron Allah daya kasheta da mamakin Naj din a natse cikin sanyinta batareda tabi takan abinda Hannah din ta tambayaba tace"


Bayajin Dadi ko kinyi knocking ba lallai yabudeba.


Sake kallon kayan dake jikin Hannah din tayi sbd wata doguwar straight gown ce data lafe jikinta dakyau ta fidda da shape dinta ba laifi kanta babu komai sai wata qaramar hula data saka wadda kusan Rabin gashinta ya fito itama qamshin take fitarwa Sosai.,dauke kanta tayi Anatse kafin ta qarasa jikin kofar takai hannu ahankali ta bude kofar Kai tsaye tashige tareda rufowa tasaka lock.
Jingina tayi jikin kofar tareda rufe ido tana Dan sauke numfashin dazai rage Mata nauyin da zuciyarta tayi.


Hannah kuwa kasa motsawa tayi agurin sbd al'amarin yafara Mata yawa, zuciyarta gap take da bugawa da halinda Marshal dama wannan Naj din suke sakata,
Cikin baqin ciki da takaici dama bacin ran daya qulleta tace"


Ubanwa ya tambayeki idan baida lafiya ko lafiyarsa kalau¿
Juyawa tayi Rai baqi qirin ta wuce tanajin Kamar tatashi kowa daga bacci gidan yafito sbd masifa.


Barin jikin kofar tayi ahankali tana Dan kallon palon da wutarsa take kashe saita gurin dining ce kawai a kunne Wai AC Dake aiki ta nufa hanyar kicin tana tafiya jiki amace
Takai Kan dining ta aje tareda sauke qaramin numfashi tana Dan rintse ido kafin ta waiwaya ta kalli hanyar bedroom dinsa tana juya yanda zata Kai kanta da kanta bedroom din.


Bama kanta qwarin gwiwa tayi tareda Dan taqaita Jin nauyinta da kunyarta ta nufi dakin zuciyarta na tsalle sbd haryanxu takasa sabarwa da kanta sakewa akan duk wani al'amarin daya shafesa ko yashigo dashi ciki.


Saidata Kuma sauke numfashi da ajiyar zuciya kafin takai hannu ta Murda kofar dakin a natse ta bude tana kallon Dan duhun daya gauraya dakin sbd wutan a kashe sai hasken bedside lamp na gefe daya dake kunne Wanda yabata Daman ganin fuskarsa Dake bacci cikin nutsuwa da alama baccin yasa ciwon Kan tafiya.


Kasa dauke idanuwanta tayi daga kan fuskarsa zuciyarta na gauraya da dukkanin nutsuwa da wata irin alkunya duk da bacci yake.


Bakin gadon ta tsaya saiti da kansa tareda durqusawa takai hannunta kan goshinsa ahankali ta Dan dafa saikuma ta dauke da sauri tana miqewa tsaye zata juya taji anriqo hannunta.


Kasa waiwayo tayi saima idanuwanta data rufe Jin kunya da mamakin ba baccin yakeba kenan.
Batareda ta waiwayoba ta bude Baki a natse cikin qaramin sauti tace"


Hajjo tasa akawo maka Abin......


Cikin muryar bacci da 'yar kasala ya katse da cewa"


Kullum komai hajjo ke sakaki Yi,yanxu kiyi Wanda hajjon Bata sakakiba ki hadamun ruwan zafi zanshiga cikinsu nayi wanka tunda nayi bacci yanzu jikina zai sake.


Sakinta yayi Yana tashi zaune ya jingina jikin gadon Yana kallon qatuwar hijabin dake jikinta.


Kasa juyowa ta kallesa tayi ta bude Baki ahankali tace"


Hajjo zataga na Dade.


Batareda ya kalletaba ya zuro qafafunsa daga kan gadon yana zare qaramar shirt din Dake jikinsa dukkanin jikinsa ya bayyana ya nufi toilet din Yana cewa"


Ki koma gurin hajjon idan nagama zanzo da kaina gabanta na daukoki da hannuwa.
Shigewa toilet yayi yabarta tsaye tana bin kofar daya shige din da kallo
Ta kujera ta zauna tana tunanin tsaf zai aikata abinda yafada din Dan Haka zata jira yafito taji me zatai masa ta koma.
##MAMUH#






********************
*_MG's skin care_*
Hi team no makeup
Ina kanawa mutanena🗣️
Shin Ina masoyan mg's ina ma'abota ado da kwalliya kusaurara kuji dame nazomuku 💃
Nasan dayawa kunsiya kayanmu Kuma kunshaida yadda suke gyaranjiki cikin lokaci kalilan Koda iyasabulun kikayi anfani dashi sekinyaba balle kankat wato beauty kit dinmu toh inamaitabbatar muku cewa ynx kayanmu ankaramasu kayayyaki Wanda zasu Kara gyara fata fiye da tsammanin Mai tunani within 2weeks zakicanza kiga duk inda kikayi se anbiki d👀 domin ynd fatanki zaikoma Shar kamar madara bawanda zemiki kallo daya yadauke idanunshi😃😍
Hajiyata shin menene matsalanki, pimples ne?
Spot? sunburn,acne, stretch marks, knuckle, wrinkles, Black head,ko kinshafa Maine yabatamiki jiki
Inamai shaidamiki cewa ynx ne lokacin dayakamata kiyake dukkan wadannan kema kidinga fita sakayau abunki baruwanki da kunshe fuska ko kice sekinyi makeup hjy fita zar abunki kinuna ainihin natural beauty dinki😍domin kayanmu gbdynsu organic ne babuna bleaching zssu sa ki haskaka fatarki tayi ta kyalli kamar madubi ze fiddomiki d ainihin natural beauty dinki ne😘kunaji barin fadamuku wani Abu billah wannan prdcts damuke dashi ynx Koda kudinki seda rabanki domin duk sunzarce nabaya ankaramasu abubuwa dayawa masu matukar anfani agyaran fata🤗Ina Wanda basasan shafa Mai koda sabulun kawai kike anfani dashi inamai tabbatar Miki zkg ynd jikinki zekoma luwai luwai😘
Soap:3k
Beauty kit:12k
Chat:08062991549
07066210195
Call :07046881166
08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
amare inakara shaidamuku duk wacce tayi anfani d kayanmu Bata bukatar gyaranjiki sedai ra'ayi🥰
Masoya kunanan kauna yanda nakwashe aljihu domin nafarantamuku kuyi achieving goal dinku pls Nima kunanan kauna kufarantamin😪🤠aljihuna yafarfado hilis karnakoma kauyenmu🥲
Yar shawarmannan duk nasaba😤 hilis kugarzayo arabani da kaya🤝
Nd guest what🤩
Duk Wanda yy siya 10k zuwa sama zesamu Karin gift😃
Pamper your skin🧖‍♀️
Shine like a bride👰🏻
Glow🧚🏻‍♀️






*********************************
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇


09134848107






*_DM 50_*
Tunani tashiga na son tafiya Amma tana shakkar maganarsa datafi kowa sanin zai iya aikata abinda yafada din Wanda ba hajjo kawai ba kila ko Dad Alfa zai iya ganinsu ta samansa idan suka fito harabar gidan ahakan Dan Haka ta daure tasake bawa kanta danganar zaunawa jiran nasa..
Bude kofar toilet din yayi yafito daureda towel a qugu,ta dan dauke kanta tana kallon wani qaramin farin frame me kyau Dake gefen kujeran datake hotonsane tareda Hanifa aciki suna wata qasar turawan Wanda kayan jikinsu ne ya tabbar Mata da hakan ta qurawa fuskarsa ido tana sake qare Masa kallon da bazata iya yimasaba a fili dukkanin zuciyarta da gangar jikinta na tsayuwa akan Abu daya data kasa yadda yasameta wato shine SO,
Son JALALUDDEEN,qanin qawarta dasuka taso tare,
Tayaya?
Yaushe?
Kuma garin Yaya duk hakan ya shammaceta yashige......


Zama yayi kusada ita Yana zuro fuskarta kusada tata Yana kallon hoton data zubawa idon fuskarta na tona asirin zuciyarta ya bude Baki zai magana qamshin mouthwash dinsa na mint ya daki hancin Yana shigewa ta zuciyarta tasake raunana a hankali yace"


Ni din daine qanin qawarki aminiyarki Kuma mijinki uban babyn Dake cikinki,
Yaya??kin bada garine kokuwa inada sauran aikin daban qarasa?" Yafada Yana zura hannunsa cikin hijabinta ya Dora kan cikinta dayayi tauri ya Dan taso Yana shafawa fararen idanuwansa masu kwarjini Kan fuskarta Yana Jin qaunarta da Sonta daya riga yayiwa jarumtarsa da kemewarsa illar da Babu gyara.


Yanda yake shafa cikin cikeda kulawa yasata kasa jurewa ta dago ta kalli fuskarsa da har lokacin ita yake kallo cikin yanayi kulawa da so me girma.


Babyna yafara motsi?" Ya tambaya yaba kallon cikin.


Ahankali ta girgiza Masa Kai jikinta na mutuwa da yanda yake binta da wasu kallon kasalan da Bata Gama sakinsaba shima.


Amma Yana lafiya ba right?


Da mamakinsa take sake kallonsa Dan tarasa ta Yaya babu ruwansa Kai tsaye yake maganarsa duk yanda tazo Masa arai Kuma ko agaban waye.


Kama lips dinta yayi da hannunsa ya shafa Yana Dan daga mata ido alamar ta amsa Masa tambayarsa.
Dole ta bude Baki ahankali tace"


Lafiya kalau.


Kissing hannunta yayi Yana cewa"


Hakan nada kyau,yanzu muje kiban abinci inajin yunwa.


Miqewa sukai ya zare Mata hijabin ya aje a kujeran dasuka tashi suka fito Palo tana gaba Yana bayanta hannunsa riqeda Nata Yana biyewa tafiyar saibinta datakeyi a natse da sanyi Wanda ke sake shigarda ita ransa sbd a ra'ayinsa Yana qaunar mace me sanyi da nutsuwa shiyasa tayiwa zuciyarsa kamunda ba fili tako Ina.


Zama yayi Yana duba agogon yaga qarfe goma Sha daya takusa Dan Haka yace kadan zata saka Masa bayason nauyin abincin tunda dare yayi har Haka.
Kadan din tasaka Masa takawo Masa drink tana kokarin komawa ta zauna ya janyota ya zaunar a Kan cinyarsa Yana cin abincin da ita ahaka ta ringa binsa da idanuwa tako Ina Yana sake cikata da mamakinsa da girman abubuwan dayake Wanda basa boyuwa.


Koda yagama suka Gama samun bakinta tayi da kasa tambayarsa akan komawan datakeson Yi takama hannunta suka koma daki da kansa yakaita har toilet sukai brush suka fito ya hau gado ya kwanta tareda miqa Mata hannu da ido yace Mata zo Nan Kamar wadda aka daga hannunta aka miqa Masa Haka tasamu kanta da hannun nata akan nasa ya jawota ya kwantar gefensa Yana Dora kanta kan pillon da kansa yake suna fuskantar juna ahankali ya lumshe idanuwansa Yana rungume hannunta daya a kirjinsa yace"


Goodnight Mrs DEEN.


Lumshe nata idanuwan tayi itama tana sauke qaramin numfashi Dan baccin ya dauketa itama.


Bacci Sosai sukai musamman bayan sallar asuba dasukai sallah suka koma Dan kuwa yau Kai tsaye ya hanata guduwa sashen hajjo Kamar yanda take data nacewa komawan sai kawai ya sake yayi Making love da ita Wanda yadaukesu lokacin har gari yagama wayewa sukai wanka sbd tsananin gajiyan datai Dole tana kwantawa baccin wuya ya dauketa.


Bata Farkaba saida wata yunwa me qarfi ta tasheta,ta Dan motsa tana bude Idanuwanta ahankali tana Dan kallon gabanta ta tuno a inda take sai kawai taji jikinta yakuma sakewa da mutuwa sbd tariga tasan yanzu Kam hajjo tagama gane Bata Kwana acan ba.
Dan Haka yaye bargon datake rufe dashi tayi tana tashi zaune tareda zuro qafafunta qasa tana son sanin menene time.
Baya dakin ita kadaice
Ta Dan kalli wayarsa dake aje Kan drawer na gefen gadon ahankali takai hannunta ta taba screen din yayi haske Dan taduba time sai kawai tayi arba da hotonta akan wayar dayayi kyau sosai tana sanye da riga da wando da wula qarama dukkaninsu fararene Banda gashin kanta daya fito shikadaine baqi yayi kyau sosai da Dan boyayyan murmushi a fuskarta da tsananin mamaki take kallon hoton tanason tuna yaushe tayisa Amma takasa tunawa saidai tanada tabbacin koma dai yaushene ba yanzu bane Kuma a qasar turawane duba da yanayin shigarta dakuma mutanen dasuka fito bayan hoton,
A iya saninta kafin aurenta duka duka zuwanta qasashen waje baifi so uku suma duk sbd issues na ciwon Hanifa ne sai Wanda suka tafi kwanaki na dashen last cikin Nan nata daya bare Wanda shikuma bayan aurenta ne,
A dukkanin tafiyar Nan dasukai nataredashi sukajeba bayan wannan ta qarshen wadda Kuma tanada tabbacin Bata saka kayan nanba saidai idan ta mantane,
A Ina yasamu wannan hoton????


Koma dai a inane hakan yasaka zuciyarta cikin wani irin hali na kasa danne abinda yake ranta,fuskarta na bayyanarda sirrin ciki wanda yake saukarda wata walwala farin ciki akan fuskar.


Qarfe goma da mintuna ashirin da bakwai Kai tsaye ta miqe tana nufar toilet tabude tashige hankalinta nakan tunanin ko harya fita.
Brush din tayi tareda sake shiga ruwan zafi bayan tayi fitsari ta Danyi mintuna aciki kafin tafito tana gyara wuyan rigarta da har lokacin maballanta suke abude wasuma sun fincike sun fita sbd yanda ya ciresu bayan sallar asuba dazai rabata da rigar.


Tana fitowa ta hangosa zaune a palon Yana duba sako a laptop gabaki daya hankalinsa nakan laptop din ya aiki da ita Jin rufo kofar bedroom dinsa yasashi sanin ta farka Amma Bai tashiba baikuma dauke idanuwansa da hankalinsa Dake kan aikin gabansa ba saidai ya Dan bude Baki cikin kulawa da kwarjini tareda Kamala yace"


Good morning Mah lady,
Xo nan naji Yaya Kika tashi.


Ba musu ta qaraso tana kokarin zama gefensa ya kamo hannunta ya jawota ya Dora Kan cinyarsa Yana barin aikin dayakeyi ya maida hankalinsa kanta Yana shinshina gashinta daya tayata drying dake qamshin _Elvive extraordinary oil_ na _L'Oreal Paris_ ya gangaro da hannunsa ya Kama nata hannun ya Dora Kan cikinta natane aqasa sai nashi asaman natan cikin kulawa da tsananin son cikin dama ita dake daukeda cikin yace"


Hey little Alfa,good morning.


Bakinsa dake maganar take kalla kafin yasake mgna akai knocking ta waiwaya ta kalla kofar tana kokarin sauka daga jikinsa ya riqeta Yana hanata damar hakan sbd yasan haniface yayi waya da ita kafin yabaro bedroom cewan takawowa Naj din abincin Dan yasan takusa tashi baccin.


Ahankali ya 'dan daga murya kadan yace tashigo kawai.


Hanifa najin hakan ta saki numfashi Dan kuwa tasan da wuya idan ba ajikinsa Naj takeba tunda taga Bai taso ya bude Mata kofarba da kansa,
Marshal bayajin kunyarta,ta kowama bayaji kila Banda iyayen Naj din Suma Babu ruwansu da yanayin rayuwarsa Amma Naj din dayake neman zararwa da kunya yakamata ya ringa raga Mata.


Murda kofar tayi taturo tareda shigowa ta maida ta rufe tana kallon Naj da tun tanajin kunyar Hanifan yanzu ta rage tunda ta fahimci shikuma Haka Allah yayisa da sakewar fuska batareda ta nuna taga zaman dasukaiba tace"


Barka da safiya sirikita.


Da wani irin kallo yabita Yana sakin boyayyan numfashin daya sakata sake baje idonta akansa Jin sunan da Hanifa takirata dashi yace"


Da gaske ke sirikartace?
Na dauka qawartace,
Hanifa sirikata na nufin matan dana right?


Aje kayan da Hanifan ta shigo dasu tayi a dining tana cewa"
Eh matan Dana ko matan qanin ko Matan yayana duka suna nufin sirikata.


Wani murmushin yakuma saki Yana Kai bakinsa kunnenta ahankali yace"


Kin zama sirikatanta kenan no more my qawa ko my aminya right?


Wani kallon daya kusan kashesa da mamaki Tai Masa ta bude Baki cikin taushin muryarta tace"


Zata cigaba da zama qawata Aminiyata har abada,
A alaqana da ita bandauketa sirika....


Murmushin dayan sakarwa zancen yasata kasa qarasawa tana miqewa da sauri tabar jikinsa ta nufi gurin Hanifa wadda ta juyo zata baro gurin ta nufi kofa tana cewa"


Inada abin Yi natafi.
Hajjo Kuma na gaidaki...


Ko tsayawa Jin abinda Naj zata fada bataiba ta nufi kofa tafice tareda rufowa.


Tasowa yayi yaqarasa janta zuwa dining din sbd sandarewan datai a tsayen Jin gaisuwar hajjo data Aiko Mata idan ba tsokanarta Hanifa keyiba da gaske ne tashiga uku da kunyar Hajjo.


Batasan lokacin data kallesaba cikin damuwa tace"


Yanzu shikenan hajjo tasan inda nakwana?


Zama yayi yana zaunar da ita yayi kissing hannunta Yana cewa"


Harma da Wanda Kika kwana taredashi tasani da......


Rufe Masa Baki tayi da sauri tana kallon idonsa Dan tasan zai iya fadar komai batareda shakka ba.


Zame hannunta yayi daga bakin nasa Yana nuna Mata abinci da ido.


Kusan shine yaciyar da ita abincin a baki duk da tana Dan kaucewa har Dole ta ringa ci daga hannun nasa suka gama yajata suka koma daki.


Cikin black _Balenciaga_ short sleeve da wando,
Sai agogon _Emporio Armani_ dake hannunsa Wanda yakeda tsananin tsada yafito Kai tsaye ya nufeta tana tsaye gaban mirror tana sake busar da kanta daya sakata Kuma jiqawa ya Dan kamota ta baya yayi kissing wuyanta ta lumshe ido Yana shaqar qamshin turensa daya shigeta sosai yace"


Zanfita saina dawo ki shirya gobene tafiyanmu da qarfe goma na safe.


Juyawa yayi yafice yabarta tsaye tana kallon fuskarta dake blushing ta cikin madubi kafin taci gaba da busar da kanta da dryer.


Riga da skirt na lace maroon tasaka Wanda hanifa takawo mata tayi sai turarensa datai amfani dashi tuna nata basa Nan din ta fito tana Jin kunyar kanta sbd yau kayan data saka din Kamar sun bayyanarda Dan kumburin cikin nata.


Palon tafara gyarawa kafin tadawo bedroom dinsa din tagyara takira Hanifa aka Aiko Mata ruqayyat ta taimaka Mata da gyaran kicin ita Kuma tayi sauran.
Qamshi koina ya dauka ta ragewa AC din palon qarfi ta dangana ta rungumi kunyarta ta fito bayan ta rufo ta zaro key din tayo cikin gida tunda dai Dole ta taho din komai kunya.


Cikin tsananin rashin sa'arta hajjo na Palo tareda Dadah datazo bankwanar tafiyar tasu gobe Dan shi Marshal din yashiga kafin ya fita zuwa inda zashi Dan zai iya dawowa kurarren lokaci shiyasa yashiga yayi musu sallama ya wuce shine Dadahn tazo sallama wa mutuniyar tata.


Tana ganin Dadah ta dauke Kai tana saddaqarwa da abinda zai biyo baya tafara qarasowa jiki amatuqar sanyaye.,
Cikin mamaki Dadah ke kallonta lokacinda ta bude Baki ahankali tace"


Hajjo Ina wuni?
Dadah sannu da zuwa.


Dadah da bakinta baya shiru da barin zance tace"


Wannan daga ita

Please Login or Register in order to submit comment