Reading Deen Marshal By Mamuhgee Chapter 20 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Haka tana saukowa gado wanka tafara Yi Dan tasamu qarfin jikinta yadawo,
Tashirya cikin riga da skirt na atampa me coffee brown ta fito Palo
Ruqayyat ta kawo Mata Cocoa Krispies dayaji madarar ruwa data gari sosai Babu sugar sbd batason zaqi cikin farin glass bowl ta karba tana gefen hajjo data damu da yanayinta da tunanin batada lafiyane akwai wani matsalar Kuma.


Ki kawo Mata samosas dinda anty Amina ta Aiko mata dazu" Hanifa dake zaune tafada tana kallon yanda Naj din ke Shan Cocoa Krispies din ahankali kamar baya Mata Dadi bayan itace tace akawo Mata shi zatasha.
Samosas din aka kawo cikin plate manya manya da ita tacika da nama Amma batajin cinta taci gaba Shan abinda takesha tana amsa tambayoyin hajjo ahankali na cewan lafiyanta kalau...


Shigowarsa palon ne yasata tsarguwa taqi dagowa duk da tanajinsa gefenta ya zauna Yana kallon hajjo da itama shi din take kallo ganin fuskarsa na wani sheqin annuri duk da fuskarsa yawanci koyaushe a kame take yau dinma a kame take saidai tana iya hango nutsuwar da zuciyarsa ke ciki a fusakarsa cikin tambaya tace"


Ka fitane yau kaima baka fito da wuriba ko breakfast baka samu zuwaba kaci?


Kafin yabata Hanifa ya kalla da hankalinta Yana Kan qawarta yace mata"


Zanci wannan yanzu da normal drink Mara gas.


Maida hankalinsa Kan hajjo yayi yana cewa"


Bansamu bacci bane da wuri jiyan shiyasa yau da safen na kwanta nasamu hutawa.


Tissue Hanifa taje ta dauko Masa tareda orange juice dinda Babu abinda matarsa Kesha a drink bayanshi takawo Masa ya karba Yana cewa"
Thank you.


Zama tayi tana cewa"


Anjima Zan shiga gurin umma na dubo anty Amina ta kone a hannu Amma inaga ba sosai bane tunda itacema da kanta take fadamun.


Cikin mamaki da 'yar damuwa Naj ta kalli Hanifa din da muryarta me sanyi tace"


Yaushe ne ta kone?


Dazu da safe tace,taface ba wani sosai bane Dan konewa ne a yatsanta ahaka gurin aikin snacks dinta.


Zanje Nima na dubata nagani....


Kallon Marshal hahifa tayi Dake cin samosas dinsa tayi Yana jinsu Yana Kuma kallon yanda take juya abincin Bata wani ci Hanifa zatai mgn ya katseta a cikin Isa da nutsuwa da cewan"


She's not going anywhere until she finish all the Krispies Dake cikin abindake gabanta.


Tsit tayi tana son satar kallon yanayinsa Amma kunyar hajjo ta hanata ta share tana cigaba da sha tabatareda tasan umarninsane take cikawaba,
Hajjo kuwa cewa Tai"


Idan kunje Ina gaisheta anjima zanjira Dr sa'id yazo ya duba Mata hannun tunda konewa ce ba'a Wasa da ita.


Babu Wanda yayi tunanin zata iya shanye bowl din duka sbd yanayin cin abincinta dasuka sani Amma saigashi ta shanye hajjo batasan lokacin mamakinta yasata cewa"


Sannu Najma,yasaki Dole kin...


Girgiza Kai tayi ahankali tana cewa"


Dama adadin Wanda Zan iya shanyewa ne.


Sabon mamakine yakuma Kama hajjo dama shi kansa uban gayyar Hanifa kuwa qaramar dariya tasaki tana cewa"


To yanzu zamu iya zuwa tunda kace idan ta shanye Kuma ta shanye din.


Kamar jira Naj din keyi Yana cewa suje din ta miqe ta nufi dakinta tashige.
Saidata zauna abincin ya Dan fada cikinta dakyau sbd yawan dayayi Mata taji cikinta yamata daidai kuma jikinta ya Dan sake ta miqe ta dauko mayafi ta fito riqeda wayarta Hanifa Daman a jallabiyace ajikinta da qaramin mayafinta.


Hajjo saimun dawo tafada tana nufar kofa ahankali ta riga Hanifa ficewa Yana bin tafiyarta da wani irin kallon dayasa hajjo sauke ajiyar zuciyan kada kawaicinsu yaqare aringa abun kunya agabanta wata rana shiyasa zataso su tafi taren sugama zazzage Amarcinsu acan Dan taga alamar tunda aka samu ciki a sashenta batada labari komaiba zai iya biyowa baya.
Suna fita ta Dan sauke boyayyan numfashin da ajiyar zuciyanda Hanifama Dake kusada ita batajiba suka nufa gidansu Kai tsaye.


Suna shiga Dattijo zai fito Yana sauri yana sanyeda farar shadda da babbar riga da hula cikin girmamawa Naj ta gaidatasa tana basa hanya ya kalleta har Cikin ransa Yana Jin dadin ganinta da albarkar aure data samu saidai Bai Gama saukowa dukaba akan laifinta ya amasa gaisuwar Yana kallon Hanifa ma Dake gaishesa ya tambaya hajjo Yana cewa a gaida Masa ita ya wuce sbd jiransa ake
Naj tabisa da kallo bayan sun wuce tana tunanin gurin neman neman aure kokuma saurin auren zashi Dan kullum Dattijo agurin harkar aure hidimarsa tafi yawa.


Suna Shiga sashen umma habiba suka fara leqata Naj ta gaidata ta fito Asmau na biyeda ita suna mgana Hanifa na gabansu.
Suna Shiga sashensu Dadah dake zaune zainaba na Danna Mata qafafu ta kallesu bayan ta amsa gaisuwar hanifa tana kallon Naj dake qarasowa gurin fuska hade sbd Kar Tai Mata maganganun datake Mata akan cikin tace"


Wani borin kikazo gidan Yi bakyason auren da mijin kike hade mun fuska?
Tun wuri ki saki fuskarki zai fi Miki Dan Ni kingama cin Amanata da sakani koke koken wahala akan ki hkr tunda dai dama ihu muke bayan Hari,
Na are na yafe akan baza'a takurakiba lallabaki za'ai Ashema naquda nake bayan haihuwa,Kika kasa ko Jin Dan tausayin tsufana da kukan danake ki fadan na daina kingama daidaitawa.....


Anty Amina ce ta katse Dadahn da cewa"


Dan Allah Dadah kibar Naj akan maganar Nan tunda ta wuce,
Kiyi hkr ansan taci Amanarki yanda kike cewa.


Naj data rasa ina zata saka kanta sbd takaici da kunya ga qanwarta Asmau a gurin ga zainab din Anty Amina harda ma umma na gurin
Dakin ummanta ta wuce Kai tsaye tana Jin dadar na kwabe Anty Amina tanaci gaba dayi ummansu duk da Bata wani sakarwa Naj fuska haryanzu Saida zancen yasata dariya ta girgiza Kai tana Yi sbd Dadah Bata dagawa kowa kafa basuba da jikokin ba.
##MAMUH#




################################


*DATA!!DATA!!DATA!! PROMOπŸ˜πŸ˜‡πŸ€—πŸ’ƒπŸ’ƒ*
*Assalamu Alaikum*
*Batools Net.S
*muna sayarda DATA bundle akan farashi mae sauki, tuntubemu dumin yin subcription dinku*
*πŸ’ƒπŸ’ƒ
*πŸ“ΆMTN DATAπŸŒ•*
*500MB πŸ‘‰β‚¦140
*1GB πŸ‘‰β‚¦ 240
*1.5GB πŸ‘‰β‚¦ 400*
*2GB πŸ‘‰ ₦500*
*2.5GB πŸ‘‰ ₦650*
*3GB πŸ‘‰ ₦750*
*3.5GB πŸ‘‰ ₦900*
*4GB. πŸ‘‰N1000*
*5GB πŸ‘‰β‚¦1250*
*6GB πŸ‘‰β‚¦1500*
*10GB. πŸ‘‰N2500*
*15GB. πŸ‘‰ N3800*
*20GB. πŸ‘‰ N5000*
*30GB. πŸ‘‰N7500*
*(Valid for 30days)*
Balance, *461*4#* OR
*131*4#*
πŸ’ƒ
Airtel data plan
1gbβ€”550
1.5gbβ€”750
2gbβ€”1100
2.5gbβ€”1350
3gbβ€”1550
4gbβ€”2100
5gbβ€”2400
6gbβ€”2750
10gbβ€”3300
Balance*140#


Glo Data price
1.gbβ€”550
2.9gbβ€”1000
4gbβ€”1500
5.8gbβ€”2000
7.7gbβ€”2300
10gbβ€”3000
Balance *127*0#


9mobile Data price


1.5gbβ€”1000
2gbβ€”1250
3gbβ€”1550
4.5gbβ€”2250
11gbβ€”4750
15gbβ€”5500
Balance *228#
(All valid for 30days)
*CALL/SMS/WHATSAPP -* *08034450108
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
*MTN 1GB @ 240


*Ana biyan kudi taβœ”Bank*
*ACCOUNT NUMBER:*
1130713591
*ACCOUNT NAME : Fatima Abubakar Ibrahim,
*BANK NAME :Polaris BANKπŸ‘‡*
*








*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*




*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡


09134848107








*_DM 48_*
Tana Shiga dakin umma ta zauna kan kujera tana Dan rintse ido ta bude tareda sauke boyayyan numfashin damuwa da takaici me girma na Dana sanin zuwanta yanzu data sani a waya takira anty Aminar sbd Dadah tasamu ta daina Mata wannan mugun gorin kafin tasamu ta manta abar tada maganar tukuna tazo cikin rufin asirinta.
Shigowar umma tareda anty Amina da Hanifa ne yasata Dan dagowa kadan batareda ta kalla ummanba sosai sbd girman kunyar zancen Dadah da har lokacin tana tsakar gidan tana jeho zancen Bata Bari ba,
A natse cikin sanyi tace"


Umma ya gida?
Ina wuni?


Zama umman tayi Kan kujerarta datafi zama a palon tana cewa"


Lfy kalau,ya hajjo?


Wata sabuwar ajiyar zuciya ta sauke ranta na samun sauki da sanyi me yawa Jin umman ta amsa Mata cikin yanayi me Dadi batareda bacin raiba acikin zancen
Sbd wautarta saita kasa yin shiru ta kalla umman da farin ciki bayyane a fuskarta tace"


Umma kin yafemun?
Kin daina fushi Dani?


Wani kallon sakarya umman Tai Mata tana cewa"


Albarkanci mijinki kikaci daya kasa sukuni sai daya nema Miki gafara agurinmu,
Mutuncinsa yasa muka yafe Miki yanzu Amma gaba Kika Kuma makamancin Haka wlh Najma Ni kadai nasan hukuncin dazan Miki,
Yanzu meye amfanin wannan tonan bankada asirin na Dadah duk Dan sbd kinki yiwa kanki fada ki yadda da qaddara ki runguma aurenki Kuma umarnin iyayenki ko nace zabin iyayenki,Kika ringa borin bakyaso anata tashin hankula gshi Nan Dadah tanata Miki bankada Kuma wlh idan ba Allah Kika roqaba yasamata rikicin mantuwar wannan alamariba har tsufa taringa Miki fadensa,
Dan Haka kiyi wa kanki fada ki runguma aurenki sbd kinsamu mijin Dake tsananin sonki da qaunarki Sam bayason damuwarki,
Haka ya ringa zarya a gidan Nan Saida Dattijo ya sauko tas akan fushinsa Dake badan hakaba da yanzu dagake harni muna cikin bacin ransa da fadansa a kullum.


Cikin son bawa umman hakuri da kawar da damuwar zancen Dake neman dawowa sabuwa Hanifa ta kalla umma tana cewa"


Umma ai ta tuba tuni wannan ya wuce yanzu hakama binsa zatai tare zasu koma inasa ran sai takusa haihuwa zata dawo.


Anty Amina Yar dariya ta sake tana cewa"


Naj Wai binsa Zakiyi??


Shareta Naj din Tai kamar bataji me tafada ba ta basar da zancen tana kokarin yiwa umma mgn anty Amina takuma cewa"


Umma Dan Allah kiyi Mana gyaranta na amare masu ciki....


Wani kallo umman Taiwa anti Aminar tana cewa"


Amina kin Gama rainani ko?sbd Kinga muna goga kafada acikin gidan nan.


Dariya Hanifa da Anty Aminar sukai anty Amina na cewa"


Yi hkr umma Amma Allah gskia nake fada ayi Mana Dan gyara......


Jefa Mata sabuwar tissue din hannunta datake kokarin budewa Tai tana cewa"


Yaushe nafara Wasa dake.


Hanifa ce tace"


Dan Allah umma kiyi Mata,
Itama fa Kinga Amarya ce wancan na farko da akai na auren Abbas ne yanzu na auren 'danki Zakiyi umma.


Hanifa kema zama da Aminar kwana biyun Nan yasa kin lalace da rashin kunya ko??


Naj dataga zasu kasheta da sauran ranta da zantukansu ta miqe zata bar dakin umma tace"


Gwara Miki kunyar nan da wadda Dadah zata ringa sakar Miki a tsakar gidan.


Fasawa tayi tadawo ta zauna tana hadewa Hanifa da Anty Aminar fuska ko zasu bar zancen umman tasu ma dayake dama ba ruwanta akwai sakewa sosai a tsakaninsu Banda matsalolin rashin auren Naj din dasukaita shigowa rayuwarsu.


Fira suka hau sunayi suna jeho maganar tafiyarsu Naj din Wanda duk kusan sanarwace suke Mata tareda gargadi akan saken datake dashi akan girman banza data dauka ta sakawa kanta bayan itama Hannah din bawai girmanta Marshal din yayiba kusan shekarunta daya dashi idanma itama Bata girmensa ba sbd kamar shekarunta daya da Hanifa Kamar yanda Hanifa ta taba ji agurin hajjon Amma dai ba maganar shigarsu bace Dan Haka koma dai yayane ta aje abinda takeji ta Kama mijinta da aurenta idan ba uwargida takeson zama da wuri wuri ba,
Cikin neman mgn Anty Amina tace"


To ai bawai fasa auren akaiba nashi da Hannah din kamar ji nai hajjo tace idan sun dawo za'ai Auren.


Murmushi Hanifa tayi tana kallon Naj tace"
Eh to kusan hakanne Amma ganin nake sukai tafiyar Nan Naj kafin kudawo ki sauya ra'ayinsa akan auren Nan kawai.


Umma dataga rainin wayon dasukewa Naj din tace"


Kyalesu Naj,
Kawai dai kiyi kokari ki kafa zamanki a gidansa da zuciyarsa maganar aure Kuma ai basai kin hanaba shi da kansa yace.........


Umma kibari ta tashi tsaye akan mijinta da kanta Mana basai kin Bata kwarin gwiwan zama da kishiya ba."" Anty Amina ce ta katse umman da hanata fadawa Naj ba maganar aurensa da Hannah,
Umma ta sake kallon fuskar Naj datai wani irin kalar tausayi duk jikinta yayi sanyi da maganar
Take tausayin Naj din yakama umman ta dafata cikin kulawa tana murmushin farin ciki tace"


Inshallah Zaki zauna gidanki ki Mori rayuwar aurenki ke daya ba takurawa,
Kishiya idan ba alkhairi bace agareki Allah ya nesanta mijinki da Miki ita,
Karki saka damuwar wainnan biyun Dake zugaki aranki kibi mijinki kawai ki Masa biyayyar data kamata ahakanma saiki riqesa,
ALLAH yayiwa auren Albarka ya saukeki lafiya.


Amin suka amsa gabaki daya Banda Naj da zuciyarta ce ta amsa da Amin din Amma Bakinsa yakasa furtawa.
Kunun gyada da Madara Umma tayi masu sbd Naj
Kuma tashasa sosai sai bayan sallar magriba suka fito gidan bayan umma ta hadawa Marshal lafiyayyan Macaroni salad da kunun gyadar shima aka jerasu a basket ta miqawa Naj wadda ta karba daqyar tana Jin kamar ta kwanta agurin tayita ihu ko zataji saukin halin kunya da takaicin datake ciki sbd Dadah data Kuma bude Mata wani babin data karba basket din harsaida takasa jurewa ta miqawa Hanifa kwandon tana dan dauke fuska.
Hanifa taqi karba tana cewa"


Ba nauyi Zaki iya riqewa ai.


Gaba ta wuce bayan tayiwa umma Saida safe sbd masifar Dadah duk da hakan tanayin gaban Dadah tace"


Eh ai Zakiyi sauri ki koma sbd duk ranarda Kika Kuma kawo zancen banza akan rashin yarda da auren wlh zagewa zanyi na kwada Miki Mari,
Ana tareki akan kiyi hkr kina zuba rashin arziki kala kala akan bazakiyi auren qanin kawarkiba gashi Nan Zaki haifawa kawar Taki 'da a bakyason, za'a gida kina wucewa kece a gaba,jibi idan shegen haukarki ya motsa kidawo kice bakyaso mijin da auren to anshani na warke fes nake kallonki keda Fatiman Dan itama ban yarda dabatasan da cikin ba kuka barmu nida Dattijo bawan Allah muna gwara Kai gurin tunanin mafitar ki hakura ki zauna da auren.


Naj dai gaba tayi Bata waiwayoba tanajin su Anty Amina na shiga maganar suna tausar Dadahr da bakinta yaqi shiru Hanifa ma Saida safe Tai musu ta wuce Tani bayan Naj din suka fito tana 'yar dariya tace"


Naj kin shiga Tara da goma gurin Dadah.


Bude Baki tayi tana cewa"


Dadah ai dama yanzu tasamu abin fada kenan,dama kwana biyu Bata samu Wanda ta maqalewaba duk yashigo ayita Jan riqe magana anayi yanzu tasamu ta maqale mun.


Kofar gate aka bude musu tun kafin su qaraso suka Shige securities din na gaidasu cikin girmamawa musamman Naj din datake Matar ogansu Kuma sunsan yanzu yashige Yana harabar gidan.


Hankalinta na Kan gabanta tana sauraren zancenda Hanifa ke Mata fuskarta daukeda Dan qaramin murmushin zancen me neman auren anty Amina da Hanifa ke fada Mata yanda akai jiya shida Dattijo kaca kaca Wai tsohon class mate dinsane.


Wani sabon murmushi tasake dayayi Kama da 'yar dariyarta me burgewa har tana Dan dagowa sbd sosai labarin ke Bata dariya Dan anty Amina da Hanifa sukai zancen ita Bata samu sunyi zancenba.


Akansa idanuwanta suka sauka dagowar datai,
Yana sanyeda farar jallabiya data qara Masa kamala da kwarjini
Idanuwansa akanta sbd yaune Karo na farko dayake ganin murmushinta harma da dariyarta tun bayan lokaci me tsayi daya Santa,
Waya yakeyi Amma gabaki daya hankalinsa yakoma kanta tunda suka shigo harabar gidan,
Hannah dake gefensa tsaye cikin riga da skirt na atampa itama ba dankwali akanta sai wani Dan siririn mayafi data yafa akan tana ganinsu ta Dan dauke Kai tana saka Kiran qarya a wayarta tafara wayar itama Dan batason su tsaya ko da nufin gaisawa da ita gwara su wuce ciki tasamu yau zata dage saisunyi fira da Marshal din da Allah yasa tagansa yanzu tana dawowa daga anguwa shima Yana dawowa.


Dan sauke Kai Naj tayi daga kallon dayake Mata,
Tana ganin Hannah gefensa ta Dan sake kawar da Kai tana tafiyarta cikin nutsuwa batada Niya ko tunanin tsayawa Dan Babu dalilin yin hakan Dan Haka ta wucewarta Kai tsaye sabanin Hanifa data Dan kallesa tana daga Masa hannun itama tana wucewar ganin waya yake.


Riqo hannunta Wanda baya riqeda basket yayi tana gap da wucesu.
Dakatawa tayi ahankali batareda ta juyoba sbd tasan shine ba kowaba.
Dawo da ita yayi gefensa har lokacin Yana waya ya kalli Hanifa data tsaya kallonsa itama ahankali yaja hannun Naj din suka nufa hanyar sashensa Yana cewa Hanifan"


Zanci abincin Umman a part Dina anako mun tea da snacks sbd yunwan dare na baby.


Kasa magana Hanifa tayi sbd Dadi da mamakin daya Gama cikata hannu kawai ta daga Masa alamar ok angama,ta juya ta wuce tana Dan dagawa Naj hannu ahankali tace"


See you.


Hannah dake wayar qarya batasan ma Ashe upside down take riqeda wayarba ta bisu da kallo dukkanin jikinta na saki har suka Isa babbar kofar palonsaba suka shige ya rufo kofar duk da har lokacin waya yakeyi.


Daqyar ta iya durqusawa ta dauka key din motarta daya Fadi daga hannunta ta daga qafafunta dasukai nauyi ta nufi hanyar nasu sashen.


Suna Shiga palon Kai tsaye kicin ya nufa da ita har lokacin hannunta na riqe cikin nasa Kuma Bai Gama wayar ba har lokacin.
Da ido ya nuna Mata ta aje kwandon.
Ta dago kwandon ta aje suka fito suka nufi hanyar bedroom dinsa ta Dan kallesa da sauri tana neman zamewa ya girgiza Mata Kai suna qarasawa ya suka shige ya nufi sofa ya zauna tareda zaunar da ita gefensa Yana sake sarqe hannayensu Yana cigaba da wayar dayakeyi akan aikinsa
Yanayi Yana Dan juyowa ya kalleta da Idanuwansa da duk suka hanata sakewa sai sauke Kai takeyi tana kallon hannuwansu Dake sarqe.


Ya Dan Jima Yana wayar kafin yagama ya kashe wayar tareda ajewa ya waiwayo ya kalleta taqi dagowa ta kallesa ya Dan matsa hannunta kadan Yana sakin boyayyan murmushi yace"


Zanci abincin Umma kafin ya huce,muje.


Miqewa sukai suka fito tare yakaita kicin har gaban basket din data shigo dashi din kafin yasaki hannunta ya Dan rankwafo yayi kissing kumatunta ya fito Yana cewa"


Ina jira.


Dining ya nufa ya zauna Yana jiranta.
Numfashi ta sauke ahankali tareda Jin nauyin kanta gabaki daya da tata rayuwar auren tazo ahakan,
Batada zabin daya wuce dauko plates da spoons dasu cups da serving spoon ta Dan sake daurayesu duk da fes suke a jere,ta goge da sabon qaramin towel ta fito dasu a sanyaye ta aje a dining din Takoma kicin din ta dauko kayan abincin daya bayan daya ta jere Masa tana Jin yanda idanuwansa ke yawa ajikinta Yana binta da wasu irin kallo Amma taqi dagowa ta kallesa Dan idan ta kalli idanuwansa zata iya kifewa agurin Dan hakan taqi kallonsa harta Gama zuba Masa komai cikin sanyin jikinda yake sake kashesa Dan daukan hakan yake amatsayin yangar datake masa.


Janyota yayi ya zaunar akan cinyarsa Yana kallon hannuwanta dasukai aikin ya kamo yakai bakinsa yayi kissing nasu ahankali yace"


Maman junior Alfa tagaji ko??


Dagowa tayi ta kalli bakinsa da yayi maganar sbd Sam shi Babu ruwansa komai fada yakeyi Dan yasata Jin kunya.....


Matsoda fuskarta yayi kusada tasa sosai har numfashinsu na haduwa yana kallon tsakiyar idonta da wata murya me tsananin rashin fita sosai yace"


Go ahead,kiss me as much as you want, I'm all yours,ki daina kallon bakin kiyi abinda kikeso kawai.


Tsabar tsananin masifar kunyar dataji batasan lokacin data daga siririn hannu zata daki kirjinsa ba ya riqe hannun yana kallonta da wani irin murmushi Yana cewa"


Ok,ok sorry nine Mara kunyar zanyi duk lokacinda kikeso basai ke kinyiba.


Tashi tayi daga jikinsa tana barin gurin batareda ta waiwayoba ta nufi kitchen tashige da sauri,sai data Isa bakin fridge ta tsaya tana sauke numfashi da Ajiyar zuciya wani boyayyan murmushi nason saukar Mata tana tarewa sbd kunyar kanta.


Sai data dauki mintun biyu zuwa uku tasamu daidaita nutsuwarta duk da har lokacin tana blushing kafin ta bude fridge din taga gabaki daya REDBULL energy drink ne a fridge din sun dauka sanyi ta dauko guda daya da robar ruwa daya ta fito takawo Masa lokacin yafara cin abincinsa a natse kamar wani babban Dattijo sbd yanda yake cin abincin a natse.


Hajjo dataga lokacin cin abincin dare yayi bataga fitowar Naj ba tunda suka dawo Dan Koda suka shigo tana dayan palonta da baqi ta kalli Hanifa tace"


Lafiyan Naj kalau kuwa?
Kidubota ko lafiya haryanxu Banga ta fitoba.


Batareda Hanifa ta kalli hajjoba tana zama Kan dining tace"


Tana gurin JALAL acan zasuci abincin inaga Dan umma ta Aiko Masa da abinci,
Idan mungama Zan Kai Mata snacks tea Dan yunwar dare.


Shiru hajjo tayi duk da mamakin zancen sai dayasata sakin murmushinda Bata shiryaba ta zauna tana cewa ok kawai suka bar zancen daga Nan.


Daya Gama cin abincin barin dining din yayi yakoma Palo ya zauna yana duba sako a waya ta tattara gurin tamaida kayan kicin ta gyara gurin tana hada na kicin din Hanifa tayi Knocking kofa yabata izinin shigowa batareda ya tashi ba tana shigowa Kai tsaye ta nufi dining takai kayan hannunta ta aje kafin ta nufa kicin gurin Naj tana dariya tana cewa"


Mrs DEEN ALFA aiki kikeyine?


Banza Naj tayi Mata lokacinda tagama hada kayan umma a basket dinta ta wanka hannuwanta ta goge da towel tana kallon Hanifa tace"


Nagama mutafi naje nayi sallar ishai nayi wanka na kwanta.


Fitowa sukai ta nufi wayarta da mayafinta Dake kusa dashi zata dauka Hanifa ta zauna a kujera tana kallonta lokacinda ta dauka wayarta tana kokarin daukan mayafin ya jawota ahankali ya zaunar kusada ita Yana kallon Hanifa yace"


Yarana bazasuyi halin qawarki ba zasu dauko dadynsu suyi wayo sbd idan suka biyo mamansu zasu zama Kaman....


Kallon datai Masa yasashi kallonta Yana fasa fada ya saki murmushi Yana cewa"


Shikenan ya isa.


Maganar tafiyarsa sukeyi da Hanifa dakuma maganar wani qanin mum dinsu da Marshal din ya dauka nauyin rashin lafiyan data samesa zuwa ganin likita India sukeyi
Taso tafiya tabasu guri Amma ya hanata ta hanyar riqe hannunta cikin nasa Yana cigaba da magana da hanifar da itama ta kallesa tace"


Bayan kun yafi ma Nima munyi mgn da Zawj akan Zan koma can gurinsa gabaki daya shima an maidashi LA so munyi mgna min yanke shawaran nabisa can Zan ringa ganin likita Nima.


Cikin farin ciki Naj ta Dan kalleta tana Jin tausayin kadaicin juna da zasuyi tun yanzu da ido Tai Mata Ina tayaki murna sweetheart.


Gyada Mata Kai Hanifa tayi tana cewa"
Nayaki murna kema da fatan rayuwar farin ciki me albarka da 'dan uwana.


Shi kuwa hakan yayi Masa Dan dama yanason tabi mijin nata Koba komai zasufi kusa idan tabi mijinta acan zaifi saurin zuwa ganinta hajjo ma idan ta yarda yanason takoma Hawaii kodan sbd manyanci zatafi hutawa acan.
Miqewa tayi tace zatai waya ta nufi kofar fita Hanifa tace"


Kishiga ciki kiyi wayar kafin nagama din saimu tafi tare,
Ba musu ta nufi hanyar dayan dakinsa Dake palon ta shiga tana amsa wayar Sarah data shigo wayarta.


Bata ankaraba ta Bata lokaci sosai gurin wayar tabarsu suna magana dama tayi niyar Basu gurin suyi maganganunsu na tsakanin 'yan uwa shiyasa tasaki jiki suna waya da Sarah ko data kashe taji Kamar tana jiyo maganar Hanifa har lokacin sai tayi alwala a toilet din tafito tayi sallar ishai tana kallon koina a dakin dayake komai na dakin shikuma golden ne ba kamar na dakin baccinsaba Dake komai milk.
Jin tanajin bacci bacci yasata miqewa ta fito Kai tsaye da niyar tafiya ko Basu gamaba ga mamakinta Hanifa Bata palon saishi kadai yagama rufe kofa yadawo ya kalleta ganin tana kallon palon da mamakin rashin ganin Hanifa ta daga kafa zata nufa kofa ya miqa Mata hijab babba da jallabiya tareda kayan baccinta da Hanifa ta kawo Mata Yana cewa"


Kin gaji,kinajin bacci muje ki kwanta
Hanifa tawuce tuni.
Kama hannunta yayi suka nufa dakinsa tana son magana Amma ya girgiza mata Kai da alamar shima yagaji hutawa zaiyi Banda hayaniya.


Suna Shiga bedroom din nasa ya rufe kofa tareda rage hasken wutar dakin sosai yana aje kayanta Dake hannunsa ya nufi toilet yashige.


Wanka yayo yafito daureda towel tana ganin hakan ta dauke ido hankalinta gabaki daya ba akwance yakeba da kwana anan din,tafison ta komawarta saidai Kuma duba lokacin dayaja sosai tanajin tsoron fita ita kadai.


Da kansa yabata yakaita toilet tayi wanka tasako kayan baccinta tun acan toilet din saidai ganin kayan da Hanifan ta kawo Mata yasata tsayawa a toilet din tana yiwa kanta kallon mamaki da mamakin Hanifa data iya kawo Mata wannan shegun kayan tasaka.
Rigar baccin gabaki daya Babu abinda ta rufe ajikinta tun daga kan zamanta transparent dakuma qarancinta dako cinya daqyar takai.
Cikin bacin Rai tace"


Meye wannan Hanifa takawo?
Inama ta samo wannan kayan?


Tsoki tayi ahankali tareda cire rigar tana jefarwa qasa Yana bude toilet din yashigo.


Kallonta yayi daureda towel kafin ya kalli rigar data jefar din yana gani ya fahimci komai ya basar Yana cewa"


All okay???


Gyada Kai kawai tayi tana fitowa toilet din ta nufi jallabiyarta zata saka ya hanata ta hanyar dauko Mata shirt dinsa Mara nauyi da dogon hannu ya Bata.
Karba tayi takoma toilet tasako ta fito tana Jin wani iri Dan kusan itama duk cinyoyinta a bayyane
Bai tsaya Bata lokaciba ya dauketa suka nufi gadonsa ya kwantar da ita shima ya kwanta Yana ja musu abun rufa ya lumshe idanuwansa sbd baccin dayakeson ya daukesa.
Itama rufe idanuwanta tayi tana Dan sake rufe kirjinta da bargon ahankali bacci yadaukesu duk su dukan.
##MAMUH#




*_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*




*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar

Please Login or Register in order to submit comment