ta tare da ɗaura hannunshi akan na ta hannun kamar ƙaramin yaro ya shagwaɓe fuska sannan ya ce
"My happiness ina cikin ƙoshin kafiya tare da albarkar addu'arki da bata yankewa agare ni, ina fatan babu abin da ya ke damunki ya ke ma'abociyar haƙuri, juriya gami haƙuri, idan akwai abin da kike buƙata adoron duniya mudin zan iya samunshi ki faɗa mani ni kuma zan tabbatar da na sama ma ki shi da yardar Ubangijinmu."
A hankali ta janye hannunta daka kanshi ta safko da shi zuwa kumatunshi ta ɗan ja sannan ta saki sassanyan murmushi tare da faɗin.
"Bani kai da Allah ya yi ya isheni farin ciki, bana buƙatar komi a yanzu domin baka gazamin da komi ba sai de ina so idan babu damuwa ka samomin ƴar aiki yarinya me hankali wacce zata dinga tausamin ƙafafuwana, idan da hali ka samo min wa ta daban a waje banda wacce ta fito daga hannun Hajiya Turai." ta ƙarashe maganar da ƴar damuwa a muryarta.
Zamewa yai tare da zaunawa saman tattausan carpet ɗin da ke malale a ƙasa, a hankali ya janyo ƙafafuwan na ta ya ɗaura akan pillows da ya jera guda biyu ya shiga matsa ma ta su, yayinda ya ke tausa ma ta ƙafa tausayin halinda ta ke ciki ne ya addabi ruhinsa, ya na tsananin tausayawa mahaifiyarshi saboda yafi kowa sanin halin da take ciki, yanzu damuwoyi biyu ne ke addabar zuciyarshi daga ciwon Fadeel sai kuma damuwar halin da mahaifiyarshi ke ciki.
Ci gaba da tausa ma ta fararen ƙafafuwan nata yai yayin da ya ke ƙoƙarin jan ta da fira wacce zata kawar ma ta da damuwa, sai da ta gamsu sannan ta dakatar da shi ta na saka ma shi albarka tare da addu'o'in samun nasara akan komi, sanar da ita yai yanada tafiya yau amma zuwa jibi zai dawo insha Allah, fatan alkairi tai ma shi tare da fatan dawowa lafiya sukai sallama cike da kewar juna.
ZULAI
Ba ita ta farka ba sai bayan sallar azahar inda ta iske har Dr.Hafeez ya dawo tare da kawo ma ta abinci da kayan sakawa, ma'aikaciyar jinyar da Dr.Hafeez ya kawo akan ta kula da Zulai ce ta cire ma ta ƙarin ruwan tare da taimaka ma ta ta yo wanka a toilet, doguwar riga marar nauyi da ɗan ƙaramin hijabi ta fiddo ma ta cikin kayanda Dr. ya kawo, babu musu ta saka kayan amma bata saka hijabin ba sai ta ɗaurata a ƙugu, lafiyayyen girkin da ma'aikaciyar ta zuba ma ta ta zauna na lashe tas tare da yin gƴatsa tai gandala sannan ta haɗe gira cike da bada umarni ta kalli ma'aukaciyar ta na faɗin.
"Malamar asibiti ki buga mani kamabar likita kice ma shi na tashi yazo na shirya shi kaɗai ni ke jira." kallon bangane mi kike nufi ba ma'aikaciyar ta yi wa Zulai, aiko Zulai ta hasala ta tashi daga kishingiɗen da tai ta na faɗin.
"Dallah malama karki ra
TAKU HAR KULLUM
MARYAM STAR ⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪
👰♀️A DAREN AUREN 👰♀️
WRITE BY
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)
MARUBUCIYAR
DAFIN MACIJI🐍
AND
RAYUWAR SAMHAD🌹
Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
💙💙💙💙💙💙💙💙
A DAREN AURENA
PAID BOOK
Chapter 12
Dalla malama karki rainamin wayo, ni za ki mayar ƴar banza, ɗazu ki ce min likita ne ya turoki dan ki kula da ni yanzu kuma kizomin da maganar banza, wallahi zan zubar da ke anan wajen in mommore ki." nai maganar ina karkace baki ni a dole sai na kwaikwayi irin maganar ƴan daba.
Dr.Hafeez ne ya shigo ya na sakin mrmushi dan ya ji dukkan abin da muka yi.
Kallonshi nai na watsar tare da gomawa gefe na zauna, sallamar malamar jinyar yai ina ji ya na ma ta godiya, tsaki nai a raina ina mitar ko godiyar mi yake ma ta bayan babu tsiyar da ta tsinanamin.
Kallona yai tare da faɗin.
"Ranki ya daɗe Boss ina mai matuƙar ba ki haƙuri da jinkirin zuwa da banyi ba da wuri, hakan ta faru ne sanadin na tsaya nema ma ki katin shedar shige da fice a gidan da zan kaiki.
Fuska ba walwala na tashi ina sake gyara zaman ɗan ƙaramin hijabina a ƙugu, a gaugauce na ce. "Dan Allah likita mu tahi ka tsaya kana ɓata mani lokaco."
Baice komi ba yai gaba ni kuma na bi bayanshi fuskata a haɗe, gaban motarshi ya tsaya tare da buɗemin gidan gaba sannan ya rusuna alamar girmamawa ya ce.
"Ki shiga lafiya ranki ya daɗe." wani irin faɗi dagirma naji kaina ya yi saboda yanda ya wani bani girma, a duniya ina bala'in son a girmamani, dariya ce fal cikin Dr. dan shi yana hango yuyuwar zamana a cikin wannan cakuɗaɗɗen familyn waɗanda ba kowa ne tsoron Allah ba, duniya da mugunta gami da tuggu kawai suka sa a gaba. a gefe guda kuma ya na fatan zamana ya kawo sauri koda kaɗan ne dan hakanan jikinshi ke bashi niɗin alkairine zai kaini gidan SHUREIM MUHAMMAD IMAM.
Zaman shiru mukai a cikin motar babu me magana har muka isa MUHAMMAD IMAM ESTATE, ƙarawa manyan idanuwana girma nai ina kallon aljannar duniya, baki na saki kamar sakarai ina kallon yanda aka tsara tafka-tafkan gine-gine kamar babu mutuwa a duniya, sam bandamu da irin wajen da na tsinci kainaba sai ma ƙaguwa mu idasa isa nai dan insamu damar bawa idanuwa abinci, indai magana ake ta kallon ƙwaf daga anzo kaina anrufe ƙofa domin kuwa akwaini da yiwa abu kallon ƙurulla.
Wani irin sanyi ne ya shiga ratsa sassan jikin Zulai daidai lokacinda motar Dr.Hafeez ta tsaya a babban get ɗin shiga gidan SHURAIM MUHAMMAD IMAM, kamar wasa zuciyar Zulai ta shiga duka da tsananin ƙarfi wanda hakan ya saka sai da ta lumshe idanuwanta tare da komawa laƙwas ta kwanta a kujerar motar
Kallonta Dr.Hafeez yai azuciyarshi ya na faɗin 'Allah ne kaɗai yasan dalilin zuwanki wannan gida, wa ta ƙila zaren ƙaddararki ne ya janyo ki zuwa wannan gidan, Allah ya sa ta sanadiyyarki a samu zanci da zaman lafiya.'
Zulai bata daina jin sanyi jiki ba amma kuma lokacinda Dr. ya harba kan motarshi cikin harabar gida sai da ta hare manyan idamunuwanta ta na kallon wannan gida wanda aka narkarda zazzafar dukiya wajen ƙerashi.
BAYAN MINTUNA GOMA
Zulai ce zaune akan luntsumemiyar kujera ta na lumshe ido gami da ƙara lumewa jikin tattausar ɗujerar, ta na jin Dr.Hafeez na yiwa Mamy akan Carptain ne ya ce ya kawota wajen Baba Jummai, ta so ta saka baki ganin yanda Dr. ya karkace ya shuto ƙarya wai wajen wa ta Babah Jummai ya kawota kuma wai wani ne ya ce akawota alhalin babu wanda ta sani ko yasanta sai Fadeel shi kuma Dr. yai ma ta bayani akan baida lafiya harma yakaita ta leƙa ta glass taga yanda yake kwance magashiyyan, har hawaye sai da ta zubar ganin halinda ya ke ciki.
Ware iyakar girman idanuwanta tai ta na ƙarewa ƙaton parloun kallo tare da mamakin wai wannan gidan a Nigeria ya ke, ta na mamakin wane irin rashin sanin ciwon kai ne ze saka mutum ya kashe uwar dukiya har haka wajen gina gida, gidan da mutum yasan dole ya mutu ya barshi duk kyau da tsaruwarshi.
Kallon kyakkyawar matar da Dr. ya kira da Mamie tai jin ta ambaci sunanta raɗau a bakinta, ɗan dagowa Zulai tai tare da mere baki gefe ta fara magana.
"Zulai Mamman sunana ne amma ada banda yanzu hajiya, ki kira ni da Boss kawai zan amsa ma ki."
Yanda Zulai tai maganar ta na wani ciccije baki gefe ya bawa Mamie dariya, a fuska dai yarinya ce sosai amma yanda tai maganar kanta tsaye ya burge Mamie dan sosai ta ke son mutum irin haka masu faɗin gaskiya babu kwana-kwana, mutmushi tai tare da faɗin.
"In banda abinki ƴa ta saushe zan kira ki da wannan sunan, dade za ki faɗamin sunanki na ainahi da zanfi jin daɗin kiranki da shi."
Ƙuri Zulai taiwa Mamie da Manyan idanuwanta ta na ganin nutsuwa da kamala a wajen Mamie, yanda ta ke magana kaɗai ya isa ya tabbatar maka cewa matar ta kai ajin ƙarshe wajen haɗuwa, gayu gami da wayewa me haɗe da ilimi.
Zulai bata san sanda wa ta nutsuwa ta saukar ma ta ba daga kallon matar sai ji tai bakinta na furta.
"Sunana Zulaika A Maleek, amma a ƙauyenmu da Zulai Mamman ake kira na saboda Mamman shine wanda ya rene ni, duk da dai ba wani so na ya ke ba sosai, Mama da Iya da Anty Mardiyya giwar mata su ne kaɗai ke so na."
"Masha Allah sunanki me daɗi kamar yanda kike da kyau, za ki zauna tare da ni ko ƴata Zulaika?."
Mamie tai tambayar cike da fatan amsawar Zulai.
Zulai na kokowa da zuciyarta da ke hanata amsawa amma bakinta yaj caraf ba tare da shawararta ba ya amsa wa Mamie da "Zan zauna tare da ke."
Ƙurrrr Doctor ya ƙure Zulai da idanu ya na mamakin sauyawar tunaninta haka da wuri-wuri sai ya fara tunanin ko dan ta ga gidan ba yanda tai tsammani ba shi yasa, domin kuwa kowa yasan ahalin IMAM MUHAMMAD shahararrun manyan attajiraine waɗanɗa ake alfahari da su a Nigeria saboda irin cigaban da gudumuwar da suke bayarwa ta hanyar wahaltama ƙasa da dukuyarsu harma da ƙarfinsu.
Assalamu alaikum masu karatu, adaidai nan na kawo ƙarshen free fage dama na sanar zan tsaya da free page daga page 12 ku kasance tare da ni domin yanzu za'a fara ainahin labarin.
WANNAN LITTAFIN PAID BOOK NE AKAN NAIRA 300 KACAL, KI DAURE KI MALLAKI NA KI DAN KARANTAWA CIKIN SALAMA.
GA WANDA ZASU BIYA KUƊI DOMIN DAMUN CIGABAN LABARIN KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAYIN.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇
09136291920
Chart only
TAKU HAR KULLUM MARYAM STAR
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels