Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
babu inda suka ci birki sai a fadar mai gari, nan kowa ya zube ya na maida lumfashi, ko gama sauke numfashi basui ba suka hango zugar mutane da wa ta irin ƙura na tashi, da mugun gudu mutanen ke tafe wani azakwakwuri ya dage sai ɗaga murya ya ke yana faɗin. "Jama'a kowa yai ta kanshi yau gari ba lafiya, mata ko wace ta shige gida ta kulle yau garin nan babu lafiya." Aifa su me gari jin haka ya saka su saurin tashi tare da bin ayarin wannan tawagar aka shiga tiƙar gudu da su, kafin kace mi kowane gida an garƴame shi babu wanda ke buɗe hatta masallatai duk an kulle su, haka wannan tawagar ta mutanen suka shiga tiƙar gudunsu babu gajiyawa, abin ka da mutan ƙauye dama ansaba aikin ƙarfi hakan ya saka basu gaji ba sai da suka tabbatar da sun fice daga ƙauye sun nausa cikin jeji sannan suka ankara suka zauna maida lumfashi. A bangaren Zulai kuwa sai da tai kusan minti goma ta na morar daɗin jikin baturen matashinan sannan ta buɗe idanuwanta da suka canza launi, karaf idanunta suka karƙe dana wannan baturen dan kuwa ya ƙure ta ne da kaifafan fararen udanuwansa ya na kallonta, cike da basarwa kamar ba shine ke kallonta ba ya ce, "saukarmin a jiki". Saurin direwa Zulai tai daga jikinshi zuciyarta na tsalle kamar me shirin buɗe ƙirjinta ta fito, idanuwanta ƙememe babu wa ta damuwa ta fara rantaɓo jawabi TA KU HAR KULLUM MARYAM STAR ⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪 👰‍♀️A DAREN AUREN 👰‍♀️ WRITE BY MARYAM STAR ⭐⭐⭐ (ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪) MARUBUCIYAR DAFIN MACIJI🐍 AND RAYUWAR SAMHAD🌹 Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) 💙💙💙💙💙💙💙💙 A DAREN AURENA PAID BOOK 💙💙💙💙💙💙💙💙 FREE PAGE Chapter 4 "Malam ya da haka, kasan irin kasadar da na ɗauka kuwa wajen ganin na taimaka ma ka, shine dan na ɗan hau jikinka shine zaka wani buɗe tsatstsaman bakinka ka...." Ɗif ta yi jin yanda ya fizgota da ƙarfi ta faɗo jikinsa, cikin ƙaramin sauti mai cike da amo ya ce "Indai jikina ne zo ki kwanta ki yi birgima akai yanda ranki ke so babu mai hana ki, ni ɗan halak ne bazan mance alkairinki a gareni ba, ba dan kin taimakeni ba da yanzu bana cikin wannan duniyar ke ɗin ta musamman ce a wajena dole ne in baki dukkan abin da kike so damma dai ni ina tsoron mace mi aljannu musamman irinki mai rantalar ƙeyar maza." "Wa ya ce maka ina da aljannu, Malam bari janyo min bala'i ni lafiyata ƙalau wallahi na yi abin da nai ne dan inyi maganin waɗanan shaiɗanun mutanen baka san halinsu ba ne tsaf zasu ƙullamin shari a garin nan fita ma ta gagari iyayena da ƴan uwana, kuma dama na daɗe ina jin haushi me gari da Audu gwangwan shi yasa nai masu laga-laga ƴan kwal uban." Zulai ta katse wannan matashin daga magnar da ya ke. Wani tunani ne ya bijiro ma matashin, jinjina kai yai alamar na'am da zance zucin da ya ke hakan ya saka ya nutsu sosai sannan ya fuskanci Zulai ya fara magana a bisa umurnin zuciyarshi. "Na ji maganganinki kuma na fahimce ki sosai, sannan kin burge ni da kika tsaya kika ɗaukarwa kanki mataki har hakan ya saka na ji ina sha'awar saka ki cikin rayuwar ɗan uwanah wanda ya ke fuskantar matsaloli masu sarƙaƙiya, idan za ki amince da ni zan saka ki aiki a kanshi sannan zan biya ki miliyoyin kuɗaɗe, na yi maki alƙawarin cika ma ki dukkanin burukan rayuwarki muddin za ki amince da buƙata ta ni sunana Fadeel ina zaune ne a garin ABUJA ɗan uwana na sunanshi FAHAD...." Nan ya shiga zayyano zance tare da fatan samun amincewar Zulai dan ya hango maganin matsalolinsu a tare da ita. Yayin da ya ke magana fuskarshi caɓa-caɓa da hawaye, haka Zulai ke zabura tare da nuna tashin hankali, wa ta maganar kuma idan yai sai kaga ta tashi ta na ɓurme-ɓurmen zaki, wa ta maganar kuma sai ta ciji yatsa ta jinjina kai, bai gama kai ƙarshen maganar ba Zulai ta tseshi da faɗin. "Ya isa haka Fadil barni hakanan kar zuciyata ta buga inmutu a banza saboda baƙin cikin wannan labari na ka, ai tsaya ka ji zuwana birnin tarayya dole ne, dole inshiga cikin ahalinku dan inhidda maragurbi sannan inci uban munahwukai da ƴan iskan masheranta, amma wani hanzari ba gudu ba, yauɗin shine daren aurena bazan iya tsallake wannan ranar me daraja ba, kuma bazan iya barinka ka tafi kabarni anan ba yanzu minene abinyi?." A ɓangaren su me gari kuwa, su na can cikin daji a zazzaune kowa da abin da ya dame shi, ga ƙishirwa ta addabesu ga shi sun kasa gane hanyar gida bare su dawo, wasu daga ciki har sumfara kuka saboda gabatowar kiran magrib, ya yinda me gari yai tsuru-tsuru kamar tarko ya kama kura a tarko, zuwa can Audu gwangwan ya buɗe baki yai tambayar da ta saka kowa kallon ɗan uwanshi dan jin mi zai ce. "Wai dan Allah jama'a minene ya yo bi ake kwasar wannan gudun haka?." Babu wanda bai faɗa tunanin akan abin da ya faru ba, zuwa can wannan jibgegen matashin da ya kware baki ya dinga shela akan kowa yai takanshi ya zabura ya ce. "Wallahi Allah me gari za ku tambaya dan shi da fadawanshi muka gani sun zage sai tiƙa gudu su ke shine muma muka buyo sahu dan tsira da rayuwarmu." Kasaƙe me gari yai zufar wahala na yanko ma shi, idan tunaninshi ya bashi daidai lokacin da Aljannun Zulai suka tashi ne aka gansu su na gudun ceton rai, kafin ya ce wani abu ya jiyo muryar Sarkin aska na faɗin. "Wallahi Zulai ce ƴar gidan Mamman Aljanunta suka tashi shine ta...." Saurin daɗe bakinshi Audu gwangwan yai tare da girgiza mai kai alamar kar ya faɗi, ajiyar zuciya me gari ya TAKU HAR KULLUM MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU💪 👰‍♀️A DAREN AUREN 👰‍♀️ WRITE BY MARYAM STAR ⭐⭐⭐ (ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪) MARUBUCIYAR DAFIN MACIJI🐍 AND RAYUWAR SAMHAD🌹 Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) بسم الله الرحمن الرحيم Chapter 5 Sauke jin Sarkin aska bai idasa faɗin abin da zai faɗa ba, ƙiri kowa yaiwa Me gari su na son jin ƙarshen jawabin sai de shi da Audu gwangwan sun hana hakan faruwa. Sai da duhuwar magrib ta fara sannan Bala mafarauci ya ce ya gane hanyar komawa gida, cike da murna suke bin bayanshi har suka fito saga dajin suka kamo hanyar cikin ƙauyensu, a gajiye tuɓus suka iso kowa ka gani a harmutse saboda azabar wahalar tafiyar ƙasa da kuma uban gudun da suka tiƙa. Bayan kowa ya je gida yai wanka tare da cin abinci da sallah Ma gari ya aika aime shela akan ya na son kowa ya zo fada akwai muhimmiyar magana, da ya ke kowa a ƙage ya ke akan san jin abin da ya faru hakan ya saka kafin Me gari ya fito fada ta cika taf da mutane, ba mazanba ba matan ba har da yara matasa kowa ya zo, a gefe guda kuwa waɗannan matan da sukai faɗa ne tare da folisawa har da Auwalu da yai jage-jage da zawo, duk sun jeme sun fita a hayyacinsu kamar wasu korarri, mutane sai kallonsu ake ana mamakin abin da ya same su musamman da aka san sune sukazo tafiya da Zulai, babu jimawa sosai Mai gari ya fito tsaf da shi sai de idanuwanshi sun zurma ciki sunyi zuru-zuru, bayan ya zauna aka gaggaisa ya fara rantaɓo jawabi. "Wato dalilinda ya sa na tara ku anan shine, ina son kawo sauye-sauye da dama yayinda nike so in karrama wasu daga cikin fadawana saboda sadaukarwar da sukaimin a yau da wani iftila'i ya aukomin, sun tsaya tsayin daka wajen ceto rayiwata shi ya saka nima zan saka ma su da alkairi in nuna farin ciki da jin daɗin abin da sukai man, da farko dai ina so kowa ya maido hankalinshi akan waɗannan jami'an tsaron da kuma Auwalu ƙeya, idan kunyi duba da idon basira zaku ga sam basa cikin hayyacinsu, Auduwa ne ya tsintosu a hanyar barin gari sun zage sai ɓarza uban kuka suke su na share ciyayi da yatsun hannuwansu, shine yai da su akan su hwaɗi ma shi abin ke hwaruwa amma ƙememe sukai banza da shi sai kuka suke su na shara, da Auduwa yaga abin ya isheshi shi ne yayo waya ya sanar da sauran fadawan da suke zaune anan fada suka je suka ɗauko su kungansu sannan zube kamar ƴan banza kowa a cikinsu sai nishi ya ke." Nanfa wajen ya kaure da salati da sallallamin jama'a gami da jajanta abin da ya faru kunsan mutanen ƙauye da kara da karamci. Mai gari ne ya sake katse surutun mutanen wajen da faɗin. 👰‍♀️A DAREN AUREN 👰‍♀️ WRITE BY MARYAM STAR ⭐⭐⭐ (ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪) MARUBUCIYAR DAFIN MACIJI🐍 AND RAYUWAR SAMHAD🌹 Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) 💙💙💙💙💙💙💙💙💙 A DAREN AURENA PAID BOOK 💙💙💙💙💙💙💙💙💙 Chapter 6 بسم الله الرحمن الرحيم Babban lamarinda ya faru ɗazu a garinnan shine ita dai wannan yarinya wadda za'a ɗora ma ta arme da yaron wajena gobe idan Allah ya kaimu ita ce ke ɗauke da lalurar iskokai wanda basu bayyana ba sai yau da yake daren armenta, babban abin tashin hankalin bai wuce yanda iskokan suka maida kan yarinyar madaddalarsu ba, kanta cike ya ke taf da iskokai dan ko wajen aje tunani basu bar ma ta ba, zancen da nike muku ɗazu a asibiti ba ƙaramin ɗauki ba daɗi mukai ni da Audu gwangwan ba da kyar muka shawo kanta ta hanyar tuhe ta da addu'o'i, bayan sun bar jikinta shine suka fito fili da makaman yaƙinsu wai zasu gwabza da mu, da yake kunsan na yi gaɗon yaƙi a wajen kakan kakan kakana Zubairu sadauki shine na tsaya cike da jarumta muka fara fafatawa, abinka da sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi nan da nan suka cimu da yaƙi shi yasa mukai ta kanmu muka tsere." Wa ta irin kabbara gami da hayaniya ce ta kaure a wajen, yayinda kowa ke yabawa da jarumtar me gari da kuma gasgata labarinshi, su kansu fadawan ƙaryar da Me gari ya karkace ya shafto ta yi masu daɗi dan kuwa babban abin kunya ne ace sun kasa ceton Me garinsu a hannun Zulai. Yayinda aka shiga tattaunawa akan hukuncin da za'a yankewa Zulai a fadar Me gari ita ta na can a asibiti su na tattaunawa akan yanda za'a tabar garin ba tare da anzargi wani abu ba, dan jin labarin da Fadeel ya bata ya harzuƙa zuciyarta matuƙa inda fushinta ya bayyana muraratan sanan tai alwashin ɗaukar fansa akan yanda ake cutar da rayuwarsu shi da ɗan uwanshi. Zulai ba ta ankare da dare yayi ba sai bayan da suka cimma matsaya sannan ta tashi da niyyar tafiya gida nan ne ta ga duhu ya mamaye wajen asibitin sannan babu kowa a ciki sai majinyata waɗanda suka jiggata basu iya ko tashi bare su gudu, Fadeel da sam ba wani ƙarfin kirki a jikinshi ne ya taso suka fice a tare. BAYAN AWANNI UKU Zulaice tafe a gaba hannuwanta riƙe da fitila mai tsananin haske, fuskarta a cunkushe babu walwala ko kaɗan yayin da Fadeel ke biye da ita a baya jikinshi a kasalacen ga alamun gajiya sun tabbata ɓaro-ɓaro a fuskarshi, tafiya suke ba ummm babu umumm kowa da tunanin da ya addabi zuciyarshi. Sai da sukai tafiyar awanni biyu cir sannan suka fita daga ƙauyen YAGAWA suka isa babban titi wanda ya ke tsit babu kowa, haka suka yanki wannan titi su na bawa ƙafafuwansu hawala ta hanyar tafiya babu tsayawa hutawa, yayin da suke tafiya a ƙafa Zulai sam tunaninta baya tare da ita abin da ya faru ne tsaye cak a ranta musamman kaifafan maganganun da Maman ya faɗa ma ta, shuuuuuu maganarshi ta gifta a kunnuwanta. "Allah wadai da halinki Zulai bazan iya ci gaba da cakuɗaki da iyalina ba alhalin baƙin hali ne da ke, tun da nike a garinan kaf ban taɓa jin ko da a labari wani ko wa ta sun aikata irin abin kunyar da kika aikata ba, kamar yanda Me gari ya ce, ki tattara inaki ya naki kibar mana Ƙauyenmu bamu buƙatarki." Tsugunnawa tai a ƙasa tare da dafe kunnuwanda da tsananin ƙarfi ta saki ƙara ta na kiran "Mamman! a'a Mamman a'a a'a." sai kuma kuka me ƙarfi ya ƙwace ma ta irin wanda ke fitowa daga ƙasan zuciya. Fadeel da jikinshi yai sanyi ya ja sanyayun ƙafafuwanshi ya zauna a kusa da ita ya shiga rarrashinta duk da shima ya na cikin damuwar, sam hankalin Zulai ba ya tare da ita dan baƙin cikin abin da iyayenta suka aikata ma ta agaban jama'a ya dameta, izuwa yanzu ta fara tunanin cewa ita ɗin ba ɗiyar Mamman ba ce. Yayinda Zulai ke rizgar kuka babu tsaitsayawa wa ta dalleliyar mota ƙirar benz c class ta nufo inda suke a zazzaune, ƙiiiiii lafiyayyar motar ta taka burki yayinda aka ɓalle murfin motar da tsananin ƙarfi, wani dogon kyakkyawan matashi ne me cikar kamala ya fito daga bayan motar, fuskarshi a ɗaure tamau ya nufo inda Zulai da Fadeel ke zazzaune, zuwanshi bai yi wa ta-wata ba ya ɗago kafaɗar Fadeel ya miƙar da shi da ƙarfi sannan ya saka shi cikin jikinshi ya rungume shi tammm kamar zai bayar da shi cikin jikinshi. Ƙanƙameshi shima Fadeel yai tare da sakin tagwayen ajiyar zuciya cikin farin ciki ya ce. "Broth yaushe ka dawo? kuma ya akai ka san inda nike?." Ɗago da Fadeel matashin yai tare da sakin tattausan murmushi sannan ya kama kunnen fadeel ya murɗa da ƙarfi tare da dungure ma shi kai sannan ya ce. "Bana da isashen time zo muje kawai." Yana faɗin hakan ya juya wajen Zulai da izuwa yanzu kukanta ya daina fita da sauti sai hawaye da ke zuba kamar an kunna fanfo. YANZU LABARIN ZAI FARA DA ZAFI-ZAFIN KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZA TA KAYA. TA KU HAR KULLUM MARYAM STAR ⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 👰‍♀️A DAREN AUREN 👰‍♀️ WRITE BY MARYAM STAR ⭐⭐⭐ (ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪) MARUBUCIYAR DAFIN MACIJI🐍 AND RAYUWAR SAMHAD🌹 Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) 💙💙💙💙💙💙💙💙 A DAREN AURENA PAID BOOK 💙💙💙💙💙💙💙💙 Chapter 7 بسم الله الرحمن الرحيم. Kallon secons biyu yai ma ta sannan ya kauda kanshi tare da faɗin "Ta so muje". Yai gaba abinshi ba tare da ya ankara da ba ta biyo bayanshi ba, sai da ya taimakawa Fadeel wanda izuwa yanzu ƙafafuwanshi sun gaza ɗaukarshi, dan har wani jiri-jiri ya ke gani, har ya shigar da Fadeel front sit shima ya zauna driver sit Zulai na inda ta ke babu ko alamar ta motsa bare ta tashi, cike da zafin zuciya matashin ya tada motar da niyyar ya tafiya zai yi ya barta anan, Fadeel ne ya dakatar da shi da faɗin. "Sorry broth ita ɗin amanace a wajena ta sadaukar da komi nata saboda ta taimaka min, yanzu haka ta na cikin makamancitar matsalar da ka taɓa fuskanta a wajen Abba saboda ni, pls na damƙa amanarta a wajenka da ba dan ita ba da yanzu baka sameni a rayeba, sannan ita ɗin yanzu matar...." Bai ƙarasa maganarshi ba yai baya luuuu alamar ya suma. Cikin kiɗimewa wanda yake kira da broth ya shiga girgiza shi tare da ambaton sunanshi amma ina babu alamun zai farko, hakan ya saka ya fito a birkice ya saɓi Zulai a kafaɗa ya saka ta gidan baya sannan da mugun gudu ya taka motar ya bata wuta ya wuce fitttttttt kamar tsuntsu. ƘAUYEN YAGAWA GIDANSU ZULAI. Wacce ake kira da Mama ce ta cakumi wuyan rigar Mamman cikin matsanancin kuka ta ke faɗin. "Na rantse da sittin ta Ubangiji baka isa ba Mamman ka yi tsuru-tsuru dan kuwa ruwa ya fika kauri, na rantse da tsarkin Allah sai ka dawo min da Zulai yau ba gobe ba ko kuma ka sawaƙemin kafice kabar min gidana tunda ba da kuɗin salele aka saye shi ba ko na Jummai, imbanda son zuciya irin naka sai ka biye wancan azzalumin me garin ku aikata san ranku, kun kori yarinya cikin dare kamar de wacce tai kisan kai, koda ace kisan kai tai aibata cancanci kora ba, ko dai ka je ka dawo da Zulai ko kuma ka sallameni yau ba sai gobe ba dan bazanbi wannan tsarin na ku ba, ace yarinya A DAREN AURENTA bala'u da masifu su rikito a kanta sai kace wacce ta zagi sama, yasin dubu sai ka sake ni Mamman." kuka ne ya ci ƙarfinta yayin wannan farar tsohuwar ta taso tinƙis-tinƙis daga inda ta ke zaune ta na sharar hawaye ta nufo wajen da Mama ke tsaye riƙe da kwalar Maman. Ɓanɓare hannun Mama tai ta na faɗin "Rabu da ɗan banza Suwaiba, indai duniya ce gaka ga ta nan ta isheka wanda da riga harma da singileti da ɗan tofi, imbanda zamani ya lalace ina kai ina korar ɗan da aka baka amana dan an yarda da kai, ni dai ba zaka mai da ni tsohuwar banza ba zan tattare inawa-inawa inkama gabana dan ban san da wane ido zan kalli Audul maliki ba." Wa ta irin zufar tashin hankali ce ta shiga tsatstsafowa Mamman sai yanzu ya gane kwaɓarshi ta yi ruwa, sam ya mance da mahaifin Zulai na nan tafe nan da wasu ƴan watanni, kuma wannan karo ba iya shi kaɗai ba har da mahaifiyarta za'a zo, kafin ya gama tunanin mafita ya sake jiyo salatin matan wajen, dubawar da zai yi sai yaga Mama zube a ƙasa anrufu a kanta, cike da kiɗimewa ya isa wajen da nufin ya taɓa ta, aiko Maradiyya ta zo da iya ƙarfinta ta bangajeshi yai gefe guda zube a ƙasa, kafin ya yunƙura da niyyar tashi ya ji ƙugunshi ya amsa da wa ta iriyar azaba, ya yinda Maradiyya ta saɓi Mama kamar ta ɗauki yarinya tai waje da ita ko mayafi babu, yayinda su Inno da sauran ƴan uwa suka rufa ma ta baya su na koke-koke. KU KASANCE DA NI A CIKIN WANNAN LABARI MAI RIKITA-RIKITA SANNAN KUMA ME ƘAYATARWA DARE DA NISHAƊANTARWA HARMA DA FAƊAKARWA NAGODE 🙏🙏 TA KU HAR KULLUM MARYAM STAR ⭐⭐⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪. Chapter 8 بسم الله الرحمن الرحيم Isarsu asibitin babu ɓata lokaci likitan da ke aiki wanda shi kaɗai ne a asibitin babu kowa sai majinyata ya amshi Mama tare da bata taimakon gaugawa, cikin nasara aka samu ta farfaɗo ta na ta sambatu, allurar barci likitan yai ma ta, ganin ta samu barci ya saka likitan sallamar su, Iya badan ranta ya so ba hakanan tabi bayan sauran suka tafi amma sai faman mita take akan ita dai da ambarta wajen Suwaiba ta rarrasheta idan ta farko, rarrashinta suka yi gami da nuna ma ta idai akaiwa mutum wannan allurar sai ya kwana ya hantse ya na barci bai farka ba. Maman ne ya fito zai je wajen Me gari, isarshi kusa da fadar ya fara jiwo muryoyinsu na tashi cike da nushaɗi inda Me gari ke faɗin. "Wallahi Allah ni kaina na so yarinyarnan kuma na daɗe ina bibiyarta dan insamu dama irin haka amma ban samu ba, ganin irin wahalar da muka sha saboda ita yasanya na yanke hukuncin ko shi Audul ɗin bazan bari ya aureta ba haka kawai ya kawo ma ni annoba da jaraba cikin gida, shi kuma Mamman sakaran banza da bai da tunani ya na fama da kanshi kamar na kifi daga amfaɗi cewar amfasa auren yarinya shine ya hasala ya zuciya wai ta yi abin kunya ya kori ƴar banza, ni wallahi hakan yayimin daɗi sosai dan wallahi ba ƙaramin tsoro ta bani ba ko sanda aka taru anan ana maganar a ɗofane na zauna gudun ko ta kwana." Dariya fadawan suka sake kwashewa da ita cike da nishaɗi, dan sun daɗe basu yi fira me tsawo irin haka da me garin nasu ba, ko da yaushe fskarshi a ɗaure kuskure kaɗan mutum zai yi a sauke shi daga matsayinshi. Cikin sauri Mamman ya sha kwana ya na jin zufar tashin hankali na yanko ma shi, tabbas ya yi kuskure ya tafka babban kuskure wan da bai san ta yanda zai fara gyaranshi ba, wani sashen na zuciyarshi kuma na sake tabbatar ma shi da ya yi daidai tunda ba hakanan ya kori Zulai ba sai da ya ɗaura ma ta aure. BAYAN AWANNI UKU 03:00am ABUJA NIGERIA Da tsananin gudu ya isa babban asibitin da ke cikin Estate ɗin MUHAMMAD IMAM, kai tsaye ya danna kan motarshi cikin asibitin me wadatar haske kamar rana, mutane sai kaiwa da komowa suke saboda tsarin da aka bi wajen ginin asibitin ba zaka tantace dare da rana ba. Kai tsaye norsing suka zo suka tura Fadeel a keken tura marasa lafiya sulai emergency room da shi, taimakon gaugawa aka fara bashi kafin zuwan Doctors waɗanɗa ke bawa wa su mutane da aka kawo sun yi accident taimakon gaugawa. Babu jimawa su ka shawo kan matsalar sannan suka dawo kan Fadeel wanda numfashin shi ya tsaya cak bai da maraba da matacce, sun daɗe sosai akan shi kafin suka samu nasarar ceto numfashin shi ya dawo daidai sai de bai farfaɗo ba. Doctor Hafeez ne ya nufo inda waiting chairs suke ya taradda FAHAD zaune ya saka hannayenshi cikin sumar kanshi yana caƙudawa duk ya birkice. Dafa kafaɗarshi Dr. Hafeez yai wanda hakan ya saka shi ya dago birkitattun idanuwansa da suka rine saboda damuwa ya watsa su akan Dr. Hafeez wanda sai da yaɗan ja baya saboda kwarjinin da idanuwan abokin na shi, murmushi ya sakarwa Fahad tare da kauda kai daga kallonshi sannan ya ce. "Haba manah Man bai kamata ka dinga shiga damuwa irin haka ba, indai Fadeel ne yanzu haka ya na cikin ƙoshin lafiya." Haɗa ido suka sake yi da Fahad wanda ya sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe manyan kaifafan idanuwanshi ya na godiya ga Allah acikin zuvciyarshi. Kamo hannushi Dr. yai tare da miƙar da shi ya nufi office ɗin shi da shi. Ruwa ya tsiyaya mai masu sanyi ya bashi ya sha, sai da ya tabbatar da ya ɗan nutsu sannan ya fara bashi bayanai cikin tausasa harshe gami da nasiha da nuna ma shi dukkan abin da ya samu bawa muƙaddari ne daga Allah, sanan babu wanda ya ke gujewa ƙaddararshi, ko wace cuta ta na da magani sai de wa ta cutar takan jima a jikin mutum ba tare da ansamu maganinta ba. Cike da ƙosawa Fahad ya nemi Dr. da ya faɗa ma shi abin da ke damun Fadeel ɗin, Dr. Hafeez bai ja da nisa ba ya faɗa ma shi abin da ya nemi

Chapter 2 of 4