tsaida numfashinshi na tsawon lokaci, sai da ya ɗau lokaci yana ƙoƙarin buɗe baki yai magana amma abin ya gagara saboda tsananin tashin hankali ganin yanda ya shiga halin ruɗu da ɗimauta ya saka Dr. Hafeen fara kwantar ma shi da hankali ta hanyar yi ma shi alƙawari akan zai tsaya tsayin daka wajen ganin ya bawa Fadeel dukkan kulawar da yake buƙata.
Zafafan hawaye ne suka shiga gangarowa daga idanuwan Fahad wanda hakan ya saka Dr.Hafeez cikin ɗimauta dan tun tasowarsu su na yara bai taɓa ganin abin da ya gigita abokin nashi har ya saka shi hawaye ba sai yau, rungume shi yai suka shiga yin hawayen a tare babu me rarrashin wani dan sosai Dr.Hafeez ke tausayawa halin da Fadeel ke ciki, ko a emergency room sai da yai kuka ganin galin da ƙanin abokin nashi ke ciki.
Sun kai kusan mintuna goma a haka babu me rarrashin ɗan uwanshi kafin daga bisani Fahad yai jarumtar shanye kukanshi ya kuma rarrashi abokin na shi tare da faɗin.
"Tabbas na shiga tashin hankali da tsananin kaɗuwa jin cewa ɗan uwana mafi soyuwa a gare ni na ɗauke da wannan mumunar lalurar amma ban taɓa sa ni ba, ina jin haushin kaina da nakasa tsayawa wajen kulawa da ɗan uwana wanda ke girmama dukkan abin da ya shafi rayuwata, kaico da wannan rayuwar."
Haka yai ta faɗin maganganu kamar zarare yayinda Doctor yai shiru tare da bashi damar amayar da abin da ke damunshi, sai da yaga abin na shi bana ƙare ba ne sannan ya shiga rarsashinshi tare da nusar da shi ƙaddarar Fadeel ce a haka kuma Allah yasan dalilin ɓoye abin ba tare da kowa ya sa ni ba sai yanzu da lalurar tai nisa.
TAUFA WA TA SABUWA KUMA, TO KO MI KE DAMUN FADEEL ƊIN WANDA ANƘI FAƊI😳 NI TSORONA MA KAR ACE A GARINSU ZULAI YA KWASO CUTAR, KOMI KENAN DAI KU KASANCE TARE DA NI DAN JIN YA DA ZATA KAYA, DOMIN KUWA INA ME TABBATAR MUKU DA AKWAI ZAZZAFAR CAKWAKIYA NAN GABA KAƊAN.
TAKU HAR KULLUM
MARYAM STAR ⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪
👰♀️A DAREN AUREN 👰♀️
WRITE BY
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)
MARUBUCIYAR
DAFIN MACIJI🐍
AND
RAYUWAR SAMHAD🌹
Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
💙💙💙💙💙💙💙💙
A DAREN AURENA 👰
PAID BOOK
💙💙💙💙💙💙💙💙
MUN KUSA KAMMALA FREE PAGE INSHA ALLAH, ZAMU TSAYA A PAGE 12
Chapter 9
بسم الله الرحمن الرحيم
Ajiyar zuciya Fahad ya sauke alamun maganganun Dr. sun shige shi, zama sukai anan wajen har akai kiran sallar farko, a tare suka miƙe suka nufi masallacin da ke cikin asibitin bayan sunyi alwala, nafila suka gabatar tare da zaman tazbihi har akai sallar asubahi, bayan an idasa ne suka fito a tare fuskar Fahad ta yi wani irin jah abinka da farin mutum ga kuma rashin barci, ga damuwar halin da ɗan uwanshi ke ciki, sai da suka zo giftawa da wajen da motarshi ta ke a parke ne ya ji gabanshi yai mummunan dokawa, zuciyarshi ta shiga bugu da tsananin ƙarfi, Dr. Hafeez har yayi nisa sai ya lura da Fahad baya tare da har zai tafi ya barshi sai kuma ya juyo ganin ya buɗe mota yai saurin isa kusa da shi dan dakatar da shi.
Turus ya tsaya a bayan Fahad ya na leƙo da kanshi ya na kallon farar yarinyar da ke barci zaune a cikin motar har zai yi magana sai kuma yai shiru ya na kallon yanda Fahad ya juyo a slow ya na kallonshi.
"Please Hafeez ka taimaka ka dubamin yarinyar nan ita ɗin amanace a wajen Fadeel shine ya damƙamin ita jiya, na manta da na kulle ta amota wallahi saboda ni ne nai tuƙin jiya cikin dare, yanzu banda isashen lokaci ina so inje in kwanta dan zuwa anjima zan yi tada jirgi dole ina buƙatar nutsuwa."
"Subahanallahi! kasan kana da aiki a yau shine ka saka kanka a damuwa jiyama fa bana tunanin ko gyangyaɗi ka yi bare barci, gaskiya Captein ka dinga kulawa sosai, yanzu bara inkira a shiga da ita ciki zan duba ta kafin gari ya waye, kai kuma bara in kira driver ya maidaka gida tun da ba'a yarda ku dinga tuƙin mota ba musamman da safe."
Norse guda biyu ya kirawo suka zo da wheel chair suka shiga da Zulai cikin asibitin, sallama sukai da juna Captain Fahad ya shiga mota yana jiran zuwan driver, shi kuma Dr. Hafeez ya shiga ciki don ƙarasa sauran ayyukanshi.
Bayan driver ya zo ne ya tuƙa Captain Fahad ya kaishi har can cikin MUHAMMAD IMAM ESTATE, estate ɗin babbane sosai dan daga asibitin zuwa ainahin cikin gidajen estate ɗin dole sai a mota, a bakin wani tangamemen gida me ɗaukar hankali wanda a saman makeken get ɗin gidan aka rubuta da manyan rubutu SHURAIM MUHAMMAD IMAM da yanayin ɗaukar ido saboda yanda aka tsara rubutun, manya garadan ƙarfafa jaruman sodoji ne a tsaye suke ƙyam babu alamun wargi a tare da su, driver da ke tuƙa Captain Fahad ne ya zuge glashin motar tare da nuna wani id card sannan aka buɗe ma shi tangamemen get ɗin ya harba kan lafiyayyar motar.
Ƙaton gida ne sosai wanda aka ƙawata shi da flawres haɗi da glasis ma su ɗaukar ido, ta ko ina a cikin gidan ma'aikata ne ke shawagi cikin mabanbantan uniforms, a tangamemen parking lot driver yai parking motar tare da futowa ya buɗewa Captain ƙofar motar cike da girmamawa.
Cikin yanayinshi na izza da jinkai ya sauko daga motar hannayenshi zube a aljihun wandon suit ɗin da ke jikinshi, cike da jarumta da sadaukantaka ya fara tako har ya isa jikin wa ta kyakkyawar kofa ta glashi fari da ruwan gorld, wasu madannai ya daddana nan cikin ƙanƙanin lokaci ƙofar ta shiga buɗe kanta, danna kanshi yai cikin ƙawataccen makeken main Parlour, babu kowa sai ma'aikatan da ke ta faman kaiwa da komowa kowa na aikinshi cike da taka tsantsan da ƙwarewa.
Stairs ɗin da ke hannun hagunsa ya nufa tare da hayewa ya nufi wata hanya da ta miƙe, jikin wa ta ƙofar glass ya tsaya tare da danna maɓalan jikin ƙofar ya shige kai tsaye cikin kyakkyawan room ɗin, bai tsaya a nan ba ya nufi wani maƙeƙen bedroom wanda ke zagaye cikin glass, bayan ya shiga ya bai tsaya wata-wata ba ya shiga cire kayan jikinshi.
KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZATA KAYA A CIKIN WANNAN ZAZZAFAN LABARIN.
TAKU HAR KULLUM
MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS.
👰♀️A DAREN AUREN 👰♀️
WRITE BY
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)
MARUBUCIYAR
DAFIN MACIJI🐍
AND
RAYUWAR SAMHAD🌹
Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
💙💙💙💙💙💙💙💙
A DAREN AURENA
PAID BOOK
💙💙💙💙💙💙💙💙
Chapter 9
بسم الله الرحمن الرحيم
Murɗaɗiyar ƙirar jikinshi irinta zaratan jaruman sadauke ce ta bayyana, fatar kijinshi sulum babu alamar darty ko tabon ciwo, sai siraran kwantattun gargasa waɗanɗa ke ƙyalli da ɗaukar ido, kasancewar aikinshi Pilot ya saka duk wani gashi da ke jikinshi ya ke a tsaftace kuma a kwance, hatta gashin kanshi da sajenshi a kwance suke luf gwanin sha'awa, babban towel ya ɗaura a gurguje ya fala toilet ya yo wanka, bayan ya fita ya goge jikinshi da wani farin towel sannan ya shafa lortion ya saka gajere wando da ƙaramar farar riga ya haye kan makeken royar bed ɗinshi ya rufu da lallausan bargo ya fara barci cikin nutsuwar da ta zama dabi'ar shi.
BAYAN AWANNI HUƊU
Zulaice ta fara buɗe manyan fararen idanuwanta a slow, sai ta yi kamar za ta buɗe sai kuma ta maida ta kulle saboda hasken da ya wadatu a ɗakin, sai da tai hakan kusan sau biyar kafin tai nasarar buɗe idanuwanta gaba ɗaya tar ta na kallon komi, ba ta gane inda ta ke ba har ta fara kokarin tashi zaune, nan ne ta ji hannunta yaɗan riƙe, dubawar da zatai sai ta ga kanula maƙale a hannu ta, bin zaren kanular tai da kallo har zuwa can saman ɗan ƙarfen d aka sagaka robar ƙarin ruwa, kanta ne ya sara da tsananin ƙarfi, nan take hoton abubuwan da suka faru suka shiga gilmawa ta cikin kanta, saurin fuzge ƙarin ruwan tai tare da dafe kanta da ke ma ta barazanar ɓallewa ta buga razananniyar ƙara wacce ta janyo hankulan ma'aikatan jinyar suka shiga rige-rige wajen zuwa su duba ko lafiya.
Dr.Hafeez ne ya shigo room ɗin da hanzari dan shigowarshi asibitin kenan bayan komawarshi gida yai break fast tare da barcin awaani uku, dama hankalinshi ya na akanta ita da Fadeel da Carptain Fahad ya damƙa amanar kulawa da su a hannunshi.
Iske ta yai ta haɗe kai da gwuiwa ta na ta jujjuya kanta tare da sabbatu wanda shi sam bai gane inda ta dosa ba, ahankali ya zauna saman kujerar da ke gaban gadon cike da tausayinta duk da baisan abin da ke faruwa da ita ba ya shiga yi ma ta nasiha gami da rarrashi.
Zulai sam bata kula shi ba sai da ta gaji dan kanta sannan ta ɗago da kanta idanuwannan a soye sunyi fiƙi-fiƙi babu alamar ruwan hawaye a cikinsu, sai de yanda suka kaɗa sukai jazur zai tabbatar ma ka da cewa lallai ta na cikin damuwa wacce har hawaye suka gaga zubowa a idaniyarta.
Cike da zafin rai ta juyo ta fuskanci Dr.Hafeez ta fara magana.
"Nasan kai likita ne, ina so ka nemo allura wacce idan akaimin ita zan mance sa wancan ƙauye wanda mutanen cikinshi basu damu da kowa ba sai son zuciya da gudun abin kunya, so nike kai min allurar da zata mantar da ni kowa da komi sannan inzama gagararriyar tantiriya wacce zata addabi al'umma, so nike inyi ƙaurin suna a duniya ta yanda ko suna na aka ji sai ƴan cikin mutane sun kaɗa, so nike intsayawa kaina tare da Fadeel intayashi ƙwatar haƙƙinsu da aka tauye sannan in temaki ɗan uwanshi, ka yi sauri likita ina jiranka yanzu dan Allah karka ɓatamin lokaci dan inada abubuwan yi sosai."
Sakato Dr.Hafeeez ya saki baki da hanci ya na sauraren kalaman matashiyar yarinyar da ba zata wuce shekara sha takwas zuwa sha tara ba amma ta zage ta na zayyano irin waɗanan kalaman, ko mi ke damunta, sannan inbanda hauka irin nata ta ya zata iya shiga family SHURAIM MUHAMMAD IMAM har ta ƙwatarwa su Fadeel haƙƙinsu kamar yanda ta ce, shin wai ma a ina tasan Fadeel da Carptain Fahad?.
Zulai ce ta katse ma shi tunanin da ya ke, ta hanyar kiran "Likita!!!!". da ƙarfin gaske.
Inda-inda ya fara yi ganin yanda ta tsareshi da kaifafan idanuwanta masu kwarjini, Allah ya azawa idanuwan Zulai ƙwarjini babu me iya jure kallon cikin ƙwayar idonta, ko da a bisa kuskure ka haɗa ido da ita sai gaban mutum ya faɗi saboda kaifin kwarjinin idanuwanta, fararene tas kamar farin fenti wanda ba'aima sirki ba gasu manya sosai Ma sha Allah, ƙwayar cikin idonta ba baƙa ba ce, ash ce mai kamar zaiba-zaiba brown, ta na da zara-zaran gashin gira masu tsayi da cika gasu baƙi ƙirin, ba ƙaramin kyau idanuwanta ke da shi ba.
Da ƙyar ya buɗe baki tare da lalubo bargon nutsuwa ya yafawa kanshi sannan ya ce.
"To ƙanwata na ji dukkan abin da kika ce, amma wani hanzari ba gudu ba, ke kanki nasan ba za ki iya samon waɗannan alluran ba bare kuma ni, amma idan kina ganin za ki iya samo su babu makawa zan zauna anan ina jiranki idan ki ka samosu da hannuwana zanyi ma ki su wannan alƙawarine nai ma ki, abu na biyu kuma ya kamata kiyi nazari akan ke mace ce kuma yarinya irin waɗannan kalaman basu dace da ke ba kamata yai ace yanzu kin...."
Bai ƙarasa faɗin abin da zai faɗa ba Zulai ta katseshi ta hanyar kwatsa tsawa kamar ƙaramar yarinya, sannan cikin masifa ta ce.
"A'a malam sauraramin idan ba zaka taimaka min ba to karka sake yimin nasiha tun da nan ɗin asibiti ne ba masallacin juma'a ko islamiyya ba, idan nasiha nike so zance dan Allah likita ka kaini masallaci wajen Liman yaimin wa'azi ko nasiha, ce maka nai ina so inzama tantiriya ma'a ƴar daba ko ƙauriya irin masu yawo da gorori da karnuka, ko kuma iri ƴan iskannan ma su zama a bakin layi su na shoahalewa su busa sigari su shaƙi cocain ko wiywiy, ina ma laifin kace zaka kaini unguwar karuwai inkoyo iskanci ta yanda zan dinga yaudarar mazan banza ina ƙwace musu kuɗi, ko kuma ka ce za ka kaini gidan rawa irin wanda ake zuwa cikin tsakiyar dare mata da maza ana sharholiya tare da iskanci, tsaya ka ji Likita bokan turai ni yanzu da kake ganina bani da kirki bare mutunci, na tattarasu na watsar a bola tun A DAREN AURENA yanzu na ɗaura ɗamarar iskanci tambaɗa da watsewa dole duniya ta sanni tasan halina daga yau kuma yanzu na canza sunana daga Zulai Mamman Yagawa na koma ZULY BOSS kashe ni sai ƙarshen film."
Tofa masu karatu kuna jin wannan Zulai Mamman ɗin wai ita adole sai ta koma ƴar iska kuma harda canza suna, shin za ta koma ƴar dabar koko? ku kasance tare da ni dan jin yanda za ta kayya a cikin wannan ZAZZAFAN LABARIN ME TAKEN A DAREN AURENA.
TA KU HAR KULLUM
MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪.
👰♀️A DAREN AUREN 👰♀️
WRITE BY
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)
MARUBUCIYAR
DAFIN MACIJI🐍
AND
RAYUWAR SAMHAD🌹
Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
💙💙💙💙💙💙💙💙
A DAREN AURENA
PAID BOOK
💙💙💙💙💙💙💙💙
Chapter 10
Dr.Hafeez tun da Zulai ta fara magana ya saki baki da hanci ya na sauraron yanda ta ke zayyano zance babu tsaitsayawa sai da takai inda take so, dariya ce ta ƙwace ma shi a zuciya tuno yanda sukai da Carptain ɗazu.
"Please Doctor bazan samu damar dawowa duba ta ba amma idan ka duba kaga babu abin da ke damunta ka kaita gida can sashen masu aiki ka damƙa ta a hannun Babah Jummai ka ce ajiyata ce ta kula da ita da kyau kafin indawo, shi kuma Fadeel ina so idan na dawo inyi cuku-cukun fita da shi daga ƙasarnan."
"Insha Allah baka da matsala abokina, amma kana ganin yarinyar nan za ta iya zama cikin wannan gidan naku wanda ku kanku ya ke gagararku zama bare ita da take baƙuwa?".
Shiru yai bai bashi amsaba a lokacin, bai ji haushin abokin nashi ba dan miskiline na bugawa a jarida yanzunma yaga jaruntarshi da ya tsaya yana magana akan yarinyar da shi kanshi bai san daga inda ta fitoba.
Dabara ce ta faɗowa Dr.Hafeez dan haka ya gyara zamanshi tare da saita kanshi ya fara magana.
"To Zulai Mamman, wai ashe kin canza suna Zuly Boss na ji duk abin da kika ce, sannan kuma zan taimaka maki har ki cimma burinki ta hanyar kaiki wani gida wanda yafi dukkan waɗannan wajajen da kika lissafo haɗari, gidane a suna amma a zahiri na gida bane domin kuwa a cikinshi ba'a gudanar da rayuwa irinta gidajen da kika sa ni, sannan haɗarurrukan da ke cikin gidan da makirci gami da tuggu ya fi zaman gidan yari masifa, tabbas idan kika sadu da wannan gidan kin cika dukkanin butuka da mafarkanki."
Cike da jin daɗi Zulai ta koma ta zauna akan gadon ranta fes fara'a kwance a fuskarta ta ke faɗin.
"Yauwa Bokan Turai, ko kaifa, yanzu ace dama kasan da irin wannan gidan shine ka tsaya ɓata yawun bakinka zaka fara yimin wa'azi, aidakasan akwai irin wannan gidan da ya tara komi da nike so ba sai ka wahalar da kanka ba wajen yimin nasiha, yanzu ya kake ganin za'ayi inje gidan?." Tai maganar cike da ɗokin murna yayin da a zuciyarta ta ke faɗin ' Habawa Mamman wallahi kai da Me gari kun gama yawo, tun wuri ku fara lissafin tsayuwar watan tashin hankulanku da dana sa ni dan wallahi saina koya muku gankali alƙiyamarku ta kusa tsayawa'
Sake maida fuskarshi serious yai sannan ya ce
"Ai karki wani damu Zuly Boss ni da kaina zan kaiki gidan amma ba yanzu ba sai zuwa anjima idan na sake duba lafiyarki na tabbatar babu wa ta damuwa ko matsala sannan mu tafi, kinsan gidan ba'a zuwa kai tsaiye dole sai ansan da zuwan mutum."
Kaɗa kai Zulai tai alamar ta yarda da zancen Dr. nan yai ma ta wayo ya sake yi ma ta allurar barci a cikin sabon drip ɗin da ya saka ma ta, aiko batai minti biyar ba nannauyan barci yai awon gaba da ita.
ƘAUYEN YAGAWA
GOVERMENT HOSPITAL
Mamace kwance kamar gawa sai shaƙar barci ta ke abinta yayinda su Iya ke tsaye a kanta sunyi cirko-cirko ganin yanda ta zage ta bararraje ta na kwasar barci hankali kwance, Maradiyya ce ta ce.
"Dama hwa jiya se da Likita ya ce barci zatai ama Iya kika ƙi yarda kika wani tasomu tun da hwarar sahiya muka kamo hanya kamar korarru, to gashinan dai kin gani da idonki ba ta tashiba." tai maganar ta na tunzuro bakinta gaba.
"Oh ni Salamatu ɗiyar Suke jikar Salmai yau naga abin da ya ishi kakata Salmai, yanzu ke Madariyya ni za ki gwadawa kauɗin ido, wato ke yanzu kin giga kin gagari kowa, to tsaya ki ji, wallahi ni baki gagareni ba ko da kika ganni haka a koɗe ras nike da sauran ƙarfi a jikina tsaf zan naɗe mayafi inlakala ma ki shegen duka ta yanda za ki kasa taka waɗannan ƙafafuwan na ki masu kama da ɗanyar ɗoya."
Taɓar-tamar Maradiyya ta fice bakinan gaba kamar an zunguro kare ta ƙofa.
A gidan Me gari kuwa yau antashi da hargitsin tashin hankali domin kuwa Audul ne yai dirar mikiya tun asubar fari shi da ƙaurayen abokananshi su ka hana koma barci da iface-ifacensu, tun cikin dare suka kamo hanyar Yagawa domin kuwa labari ya riski Audul akan wai amfasa aurenshi da Zulai, wannan ya saka suka tattaro inasu-inasu suka kamo hanya tun cikin dare, Audul ne ke kutuntuma manyan ashariya ya na faɗin yau ko shi ko Me gari muddun sukai ido huɗu babu makawa sai ya ɓare shi, babu irin haƙurin da su Audu gwangwan ba su bawa Audul ba amma ƙememe ya murje idonshi da toka ya ƙi sauraren kowa, daga ƙarshe ma duk wanda ya zo da niyyar bada haƙuri sai Audul ya sa abokanshi su sakarwa mutum mahaukacin kare, ganin yanda karnuka ke wajaga mutanen unguwa ya saka babu wanda ya sake zuwa bada haƙuri kow ya ja mutuncinshi ta hanyar kamewa shi da iyalanshi cikin gida.
Audul fa ya rikice ya firgice akan shi fa dole aje a nemo ma shi Zulai duk inda ta ke idan ba haka ba ya sakawa kowa takunkumin zama a gida har sai Zulai ta dawo da kanta, idan kuma mutum ya kuskura ya fito to sunanshi gawa domin kuwa karnuka zai bawa damar yagalgala mutum, takanas Audul ya tada ɗan shela ya zagaye garin tas ya na faɗin saƙon Audul.
TOFAH, DAMA ABDUL ƊIN ƊAN TA'ADDA NE, HABA NO WONDER ZULAI KE NEMA ZAMA ƳAR DABA ASHE SHIMA ANGON NATA JAN WUYA NE.🏃🏃🏃🏃
KU KASANCE TARE DA NI DAN JIN YANDA ZATA KAYA A CIKIN WANNAN ƘAYATACCEN LABARI.
TA KU HAR KULLUM.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪.
👰♀️A DAREN AUREN 👰♀️
WRITE BY
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)
MARUBUCIYAR
DAFIN MACIJI🐍
AND
RAYUWAR SAMHAD🌹
Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
💙💙💙💙💙💙💙💙
A DAREN AURENA
PAID BOOK
💙💙💙💙💙💙💙💙
Chapter 11
بسم الله الرحمن الرحيم
ABUJA NIGERIA
Captain bai barka ba sai ƙarfe goma daidai, bayan ka karanto addu'ar tashi daga barci cike da nutsuwa ya zuro kyakkyawar farar ƙafarshi ya zula slipar ya nufi toilet, wanke fuskarshi yai tare da yin brush sannan ya fito ya cire rigar jikinshi ya saka farar jallabiya ya fice.
Kai tsaye main parlour ya nufa, tun ya na akan stais ya ke jiyo tashin muryarta ta na magana, runtse idanuwanshi yai tare da ambaton tsarin Allah daga sharrinta, kamar ba zai ƙarasa saukowaba sai kuma yai shahada tare da neman tsarin Ubangiji ya tako har zuwa inda suke, ƙamshin turarenshi ne ya nusar da su wanzuwarshi a wajen, yayinda yai sallama cikin siririyar murya kuma can ƙasan maƙoshi, bai jirayi amsawarsu ba ya rusuna ƙaɗan ya gaida kamulallen magidancin da ke zaune akan kujera fuskarshi babu walwala.
Bai amsa gaisuwarba sai ɗaga hannu kawai da yai cike da izza, kallon yanda duka ahalin gidan suka haɗu yai amma banda mutane biyu ma su muhimmancin a rayuwarshi, har zai zauna sai kuma ya fasa ya maida akalar idanuwanshi zuwaga inda wani matashi ke zaune, cikin husky voice ya ce.
"Am Abdallah Mamie fah?."
"Ta na ɗakinta yau ba anan za ta yi break ba Jummai ta tafi kai ma ta nata." muryar wa ta matashiya da ta cake cikin ɗan ubansun ado ta karaɗe wajen cike da iyayi.
Juyawa yai cikin tako me nuni da zallar jarumta da sadaukantaka ya nufi wajen wasu matattakai ma su faɗi wanda aka malale da grass carpet me zanen flower, bakin ƙofa ya tsaya tare da saka pin ƙofar ta buɗe, wani irin mayen ƙamshi ne wanda ya haɗe da sanyin na'urar sanyaya waje ya daki hancinshi, a slow ya lumshe manyan idanuwanshi tare da buɗesu sannan ya fara takawa a hankali ya nufi ainahin cikin ƙawataccen parlon, akan wa ta matashiyar dattijuwa wace a ido idan ka kalleta zaka ce bata wuce shekaru talatin ba, amma a baɗini ta wuce nan, zaune ta ke cikin shiga ta alfarma akan wa ta kujerar hannuwanta riƙe da ludayi ta na koƙarin zuba papper soup akan soyayyar plantain da dankali.
Cak ta tsaya da abin da ta ke ganin tattausan hannunshi ya sauka akan na ta hannayen waɗanɗa suka ƙawatu da jan lalle, a hankali ta janye na ta hannun tare da bashi damar cigaba da zuba ma ta, bayan ya kammala ya ɗauki glass cup guda biyu ya haɗa kakkauran tea, zama yai akan ɗayar kujerar da ke fuskantar wacce ta ke a zaune tare da ɗauko tea cup ɗin ya nufi bakinta, babu musu tai bisimilla tare da buɗe bakin ya saka ma ta tea ɗin ta kurɓa, dankalin ya tsiro a forlk ya saka ma ta a baki, idan ya bata sai shima ya bawa kanshi har suka cinye na cikin plate ɗin duka.
A jiyar zuciya ta sauke tare da jin wani sanyin salama na ratsa gangar jiki da ruhinta, ji ta ke walwala da nutsuwa na saukar ma ta gami da goge dukkan damuwar da ta wayi gari ta riska a safiyar yau, cike da ƙauna gami da alfahari ta ɗaga hannunta tai ma shi masauki akan kwantacciyar suman kanshi, cikin sassanyar kamulalliyar murya me cike da nutsuwa ta ce.
"My son fatan ka wayi gari cikin ƙoshin lafiya?."
Tattausan murmushi ya sakar ma