An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
👰♀️A DAREN AURENA👰♀️
Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
A DAREN AURENA 👰♀️❤️🔥
BY
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
SABON LITTAFI MAI ƊAUKE DA ABUBUWAN BAM MAMAKI, KU KASANCE TARE DA NI DOMIN JIN YANDA WANNNA DADDAƊAN ƘAYATACCEN LABARIN ZAI KAYA.🏃♀️🏃♀️🏃♀️🏃♀️
🩵🩵🩵🩵🩵🩵🩵
A DAREN AURENA
🩵🩵🩵🩵🩵🩵🩵
بسم الله الرحمن الرحيم.
Ranar juma'a da misalin ƙarfe hudu na yamma, wani matsaikaicin gida ne wanda akaiwa sabon fenti da sai ƙyalli gidan ke yi da ɗaukar ido, yayinda yara ƙanana da matasa keta faman danna kansu cikin gidan su na shigewa, ganin nima zasu barni a tsaye yasaka na bi bayan ayarin wasu ƴan mata da suka nufi ƙofar gidan za su shiga, nima bin bayansu nai muka shige atare.
Madaidaicin tsakar gidan cike ya ke da mutane, yayinda hayaniya ke tashi kamar ana faɗa, a gefe guda kuma wa ta matashiyar budurwace sai cika ta ke ta na batsewa tare da hura ɗan ƙaramin kyakkyawan hancinta ta na tunzuru baki gaba.
Muryar wa ta mata na ji ta na faɗin.
"Na rantse da izo sittin tsarkakakke idan na yarda ZULAIMA tabar gidannan da nufin aure ba tare da ambiya ni kuɗina ba shegiya uwata Talatu ta haifeni, na faɗi na kuma wallahi ko an ɗaura aurenan ne akazo ɗaukar amarya sai na riƙeta babu inda za ta je sai ambiyani kuɗina."
Ta na aje zancenta wa ta farar dattijuwa ta ɗauka ta fara rantafo nata jawabin itama.
"Yau ni yau ni Salamatu ɗiya Sule jikar Salmai na ga abin da ya ishe ni, wannan wace irin ɗibar albarka ce da kowace mace zata kwaso ƙafafuwa raɓai-raɓai ta zo da wani zancen banza, dan abu da kazar uban mutum mi yasa da can baya babu wanda ya zo yai magana sai yanzu a daren aurenta sannan zaku zo da wani zancen banza da wofi, na rantse da sittin ta Ubangiji duk ƙatuwar matar da ta sake zuwa da wani zance nata na iska sai na saka Maradiyya ta zaunemin ita, abin ya ishe ni hakanan."
Tsohuwar na dire maganarta wannan natar ta cakumo wuyan wannan budurwar me zumɓure-zumɓuren baki suka kacame sa kokowa.
Aifa kankace mi gidan ya hautsine da dambe dan wanda mafi yawan mutanen da ake faɗan dasune suka taru suka rufe wannan matashiyar da duka.
Uban ihu wannan farar tsohuwar ta rafka tare da neman agaji ganin yanda manyan mata kusan biyar suka taru akan jikarta ita kaɗai.
Taɓar-taɓar wa ta mace me ƙiba ta nufo wajen da hanzarinta, ta na isowa batai wa ta-wa ta ba ta juya bayanta me yalwar mazaunai tiƙa-tiƙa tai kyakkyawan tsalle bata dire ako ina ba sai saman waɗanan matan masu dambe, cikin sa'a ta murƙushe mace biyu tai zaman ƴan bori akansu.
Ihun da matan suka saki yai daidai da ihun da masu kallon faɗan suma suka saki gami da shewa su na faɗin.
"GIWAH! GIWA!! GIWA!!!"
Fuskokinsu fal nishaɗin yanda faɗan ke bata citta, matan da Maradiyya wacce ake kira da giwa ta taushene suka saki kukan azaba, domin kuwa iya wuya sun tausu dan ko lumfashin kirki basu iya fitarwa.
Da kyar Maradiyya tai wani juyi akansu tare sa mulmulawa ta sauka ƙasa sannan ta kuma yunƙurawa ta nufi wajen sauran da suka murƙushe yarinya su na ma ta dukan sakwara, sa isrta batai wata-wata ba ta ɗaga lafiyayyen hannunta me kama da cinyar Sah ta ɗakawa matar da ke ta aikin aunawa yarinyar duka kamar ta samu jaka, gantsare baya matar tai tare da zubewa ƙasa kamar yarinya ta shiga billayi aƙasa ta na susar tsakiyar bayanta da Maradiyya ta sauke ma ta duka.
Dagewa Maradiyya tai kamar ta samu jakai tahau naɗawa matan duka iya ƙarfinta, idan tai nasarar kai mace ƙasa sa tabi ta ta taushe da mazaunar ahaka ta galabaitar da matan sai haki ta ke kamar wa ta bijimar Saniya.
Ƴan kallo kuwa sai ihu suke da alama sun nishaɗantu da yanda Maradiyya ta suburbuɗi waɗannan matan.
Farar tsohuwarnance ta kamo hannun matashiyar yarinyar da waɗannan matan suka rufarmawa ta taimaka ma ta ta shi ta na ɗingishi, kafin suyi wani yunƙuri suka jiyo ƙarar jiniyar ƴan sanda wacce ta ƙaraɗe unguwar, kafin kace mi ƴan sanda mata sun shigo cikin gidan kansu tsayu, bayansu kuma wani yamusashen mutum ne sanye cikin riga da wando daban-daban wanda duk sun jeme sun fita hayyacinsu, kafin kowa yace wani abu Malam Auwalu ya nunawa ƴan sandar wannan matashiyar ya ce.
"Ranki ya daɗe ofishiya kinga ɓarauniyar can, sannan ki haɗa sa waɗannan matan da ke kwance a ƙasa dan harda su aka haura gidan nawa ta katanga duk a ɗaure ƴan banza."
Wa ta irin ƙarar tashin hankali haɗi da kuka wannan matashiyar ta fashe da shi tare da faɗin. "Na shiga uku ni Zulai wannan nace irin lukutar masifa ce ta same ni A DAREN AURENA, sai kace se Zainabu tace min jeki kya gani, da kwarankwatsi dubu bazanje ofishin ƴan sanda ba A DAREN AURENA."
Aifa sai gida ya sake kacamewa da hargowa gami da hayaniyar babu wanda ya isa yakai Zulai station a daren aurenta, da dai ƴan sandan suka gaji sai ɗaya daga cikin waɗanɗa ke waje ya ɗaga murya ya ce "Idan basu fito da waɗanda ake zargi ba ku basu wuta kawai ku suɓulɓulesu da alburushi."
Nanfa hantar cikin kowa tahau kaɗawa jin ance a halbesu da alburushi sannan gashi maccen ta saita bindiga da alama harbawa zatai, ai Zulai da sauran waɗanda Auwalu ya nuna tuni suka kai kansu wajen ƴar sandar jikunnansu na rawa, haka aka tisa ƙeyarsu zuwa waje ko hijabai babu a jikunansu aka loda su cikin mota sauran ƴan sandan da Auwalu suka hau a tsaitsaye.
Kukane me ƙarfi ya kuma kubcewa Zulai yayinda zuciyarta ke tsalle tare da zullumi akan yanda za'ayi taje asibiti yau cikin darenan dan ta sake dubo ajiyarta, tabbas ba zata bari su isa station ba dolene ta na buƙatar zuwa asibiti a yau kuma yanzu nan.
Cak ta tsaida kukanta yayinda ta ayyana wani abu a zuciyarta wanda ya kwantar ma ta da hankali.
Juyawa tai ta kalli maƙotansu da sukai faɗa, gani tai kowace a cikinsu hankalinta atashe ya ke sannan kuma ga tsoro nan ta na gani muraran a idanuwansu, a hankali ta duƙar da kanta ƙasa ba tare da ta ɗago ba kusan minti biyu.
Wa ta irin razananniyar ƙara ta saki wacce ta ratsa ilahirin hanyar gaba ɗayanta musamman da hanyar ta kasance tsakiyar gonaki, wani irin taka burki drivern motar yai tare da fara waige-waige kafin ya yi wani abu ta kuma kurma wa ta tsawar wacce ta doke ta farko wajen sauti, cike da tsananin tsoro ƴan sanda da Auwalu suka dire daga motar jikunansu na rawar mazari, matan kuma saboda tsoro sai curewa sukai waje ɗaya suka ƙanƙame junansu cikin tashin hankali.
Cikin zafin nama Zukai ta miƙe tsaye tare daka wani uban tsalle sai kace ƴar buri ta dirko ƙasa ji kake "Timmmm" har ƙura sai da ta tashi, kafin Auwalu da sauran ƴan sandan sui wani abu tini Zulai tai nasarar yin girgizar da tai fatali da kallabin kanta yalwataccen baƙin gashinta ya safko tare da rufe ma ta fuska, lankwashe yatsun hannuwanta tai tare da yin ƴar girgiza ta watsa gashin kanta ya koma baya, aifa nan Auwalu ya zufe ƙasa ya na rawar banjo tare da sakin wasu irin tusoshi masu ɗoyin gaske, sauran yan sandan ma jikinsu ɓari yahau yi ganin yanda idanuwan Zulai suka markwaɗe baƙin ya ɓace ɓat sai farin kawai ake gani.
Cikin karairaya da tangaɗi gami da lauye harshe Zulai ta fara takowa ta na tunkarar Auwalu sa Ƴan sanda ta na faɗin.
"Ku bil adama ƴan isaka marasa mutunci da sanin darajar mata, ku sa ni cewa yau ajalinku ya zo domin kuwa dole ne mu kashe ku mu shanye jinin jikinku sannan mu rataye namominku a bishiyar gidan me gari, dolene yau ku karɓi hukuncin kama goɗiyarmu da kukai ba tare da ta muku laifin komai ba saboda kawai wancen me kama da sauron ya baku cin hancin naira ɗari biyar."
Tai maganar ta na lauya kanta zuwa inda Auwalu ya ke a kwance hannuwansa a sama alamar yayi saranda sai faman sakin tusa ya ke yi tare da shan majina kamar ƙaramin yaro.
"Kai Auwalu ɗan gidan Malam Barau jikan Hassula ɗiyar Auduwa ka sa ni yau dole ne muyi gutsi-gutsi da ƙashin jikinka tunda dan sam babu tsoka a jikinka sai ƙashi lulluɓe da fata kamar wani ƙwarangwal."
"Assalamu alaikum ranku ya daɗe mutanen ɓoye masu abin mamaki ku dubi girman ubangiji ku yi man rai, wallahi na bi Allah sa Manzonsa kuma na biku, na amince zan zama baya ga goɗiyarku kuyi haƙuri ku barni d raina tunda dai kunga bani da wani nama a jikina sai ƙasusuwa, suma ƙasusuwan wallahi tauri ne dasu kamar ƙarfe Kakan kakan kakana na gado wajen rama da bushewa haka ya ke shima kamar tsinke sai ƙaton kai kamar tulu." Auwalu ya faɗa ya na fashewa sa matsanancin kuka dan harga Allah a mugun tsorace ya ke ga shi zawayi ya kubce mai irin me fitowarnan da tsananin ƙara ji ka ke "Furutsutsutautsu, futsts, fettttt ɓaratatatata." Ƙarar fitar zawo mai tsananin ƙarni.
Saurin kawar da kai Zulai tai zuwa gefe dan wani irin bala'in ɗoyi ne ya ɗumame wajen wanda ya saka saura kaɗan asirinta ya tonu dan da kyar ta hana kanta toshe hanci sa zubar da yawu, kallon ƴan sandan nan tai waɗanɗa sukai tsamo-tsamo tumbinsu sai rawa suke su kowa matan sai ƙara ƙanƙame juna su ke tare da zazzare udanuwa dan kukanma yaƙi futowa saboda tsabar tsoro, gani suke kamar Zulai Aljanna ce ba mutumba ganin yanda suffarta ta juye lokaci guda.
KU BIYONI DAN JIN WANDA ZATA KAYA ACIKIN WANNAN LABARI MAI TAKEN A DAREN AURENA.
TAKU HAR KULLUM
MARYAM STAR⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS💪)
09136291920
Whatsapp only 🤌
👰♀️A DAREN AUREN 👰♀️
WRITE BY
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)
MARUBUCIYAR
DAFIN MACIJI🐍
AND
RAYUWAR SAMHAD🌹
Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
💙 💙💙💙💙💙💙💙💙
Chapter 2
بسم الله الرحمن الرحيم
Dariya ce keson ƙwacewa Zulai ganin yanda jaruman ƴan sandan da ake ji da su a ƙauyen sun tsure daga tada aljannun ƙarya, da ƙyar ta yi jarumtar saisaita kanta tare da sake juye idanuwanta sukai sama ta fara magana cikin murya mai firgitarwa.
"Ku Bil Adama!!!!!! ina so ku bani hankullanku nan dan kuji abind zan faɗa muku, ina so ku duka mazan da matan ku tashi ku fara share wannan hanyar da hannuwanku, kuma ban yarda kowa ya zo wucewa ku faɗi ma shi abin da ya faru ba, muddin kuka saki wani ya ji wannan magana to babbu shakka sai mun zo mun ɗauki mutum mun kaishi can bayan duniya ya rinƙa yi mana gadin dabbobinmu, sannan kuma duk wanda ya sake shiga sabgar godiyarmu koda kuwa bashi ya ke binta babu makawa sai mun ɓatar da mutum mun ɓat a doron ƙasa, yanzu muna sauri ne zamue can bangon duniya mu dubo sabon jinjirin da aka haifa mana idan muka dawo nan da minth ashirin muka iske baku gama ba zamu tattare ku mu tafi da ku zan dyniyarmu."
Ta na gama faɗin gakan ta fara tafiya ta na karmaɗe jiki kamar macijiya tare da ɓaɓɓaka wa ta irin mumunar dariya mai saka tsoro a zuciyar mai saurare, da yake Allah ya azurta Zulai da zazzaƙar murya irin mai tsuwarnan kamar kuka tsumtsaye.
A jiyar zuciya mai ƙarfi Zulai ta saki lokacin da ta sha wa ta ƴar kwana, numfarfashi ta shiga saukewa gami da sharce gumin da ya tsatstsafo ma ta, fararen manyanidanuwanta sai tsiyayar hawaye suke saboda yanda ta dinga juyasu, suririn hannunta ta saka bayanta gami da tattare yalwatacciyar baƙa ƙirin ɗin sumar kanta ta tufke ta a baya, wa ta arniyar dariya ce ta kubce ma ta tuno yanda Auwalu ya tsure har da sakin zawayi a wando bayan tusoshin da ya gama kumbura ma su ciki da su, sai kuma yanda Ta Rasulu ta dinga zare ƙananan idanuwanta ta na muzurai tare da buɗe baki kamar zatai magana amma ta kasa sai wani irin tsoro da ya bayyana a fuskarta muraran kamar ba ita ba ce ta maga cika baki har da yin dambe a gidansu saboda ta na binta kuɗi.
Saurin yana gyalen rigar jikinta ta yi mayafi da shi, cikin hanzari ta ke taka fararen ƙafafuwanta da suka sha jan lalle ta na tafiya ta na tunanin ajiyar da tai a sibitin da ke garin.
Tafiyar mintuna sha biyar ta kawo ta bakin ƙaramin asibitin wanda jama'a sukai dafdala a wajen su na ta gudanar da harkokin kasuwancisu ga hayaniya da ta cika wajen saboda kai komo, babu wanda ya damu da wajen asibiti ne akwai marasa lafiya waɗanɗa ba su buƙatar hayaniya.
Cikin sauri ta janyo mayafinta gudun kar wani ya gane ta ta yi hanzarin shigewa asibitin, ba ta tsaya ko ina ba sai ɗakin da aka kwantar da majinyata maza, ɗakin sai ƙarni ya ke ga masu jinya sau surutai da hayaniya su ke babu ruwansu, ba ta tsaya kula kowa ba ta wuce fuuuuuuu ba tare da ta bawa kowa damar ganin fuskarta ba, sai da ta kai ƙarshen ɗakin ta buɗe wani yalolon mayafi da aka rufe aka raba wajen da sauran majinyatan da ke ɗakin sannan ta tsaya ta jingina ta na maida numfashi, takai minti uku a tsaye kafin a hankali ta ƙarasa gaban gadon ta tsaya tare da ranƙwafawa daidai saitin fuskar kyakkyawan baturen matashin da ke kwance idanuwansa a kulle alamar barci ya ke.
KAR KU MANTA WANNAN LITTAFIN NA ƘUƊI NE, IYA BOOK ONE NE KAWAI FREEE.
TA KU HAR KULLUM
MARYAM STAR ⭐⭐⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRUTERS 💪.
09136291920
👰♀️A DAREN AUREN 👰♀️
WRITE BY
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)
MARUBUCIYAR
DAFIN MACIJI🐍
AND
RAYUWAR SAMHAD🌹
Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
💙💙💙💙💙💙💙💙
A DAREN AURENA LABARI MAI CIKE DA TSANTSAR SOYAYYA DA SADAUKARWA HARMA DA NISHAƊANTARWA
💙💙💙💙💙💙💙💙
Chapter 3
بسم الله الرحمن الرحيم.
Zuciyarta na tsitsinkewa gami da dokawa cikin tsananin ƙarfi ta durƙusa a gaban matashin tare da fara zubar da hawayen masu tsananin zafi ta na faɗin.
"Ban san wace hikima ce Ubangiji ya ɓoye a tsakaninmu da har ya sanyoka cikin rayuwata A DAREN AURENA daren da nike fata da mararin zuwanshi tsawon shekaru, daren da nai alƙawurra da dama tare da cin manyan burika da akwashi a cikinsa, daren da nike fatan ya zama dare na ƙarshe da zan sake wayuwar gari a cikin wannan ƙauyen mai cike da mabanbantan mutane ma su mabanbantan al'adu, A DAREN AURENA da sanyin safiya ƙaddara ta haɗa ni da kai, kuma ƙaddarar aure za ta raba mu rabuwa ta har abada, daga lokacin da nai tozali da kai lissafina ya kwance, burukan da na daɗe ina ginawa suka tarwatse a ciki kuwa harda burin mallakar muradin zuciyata, lokacin da na fara tozali da kai yashe a ƙasan gona a gefen hanya cikin mawuyacin hali a lokacin ne burukana suka faɗi ƙasa wanwar tare da rugujewa gaba ɗayansu, A DAREN AURENA na haɗu da kai kuma A DAREN AURENA zan rabu da kai ba tare da nasan koda sunanka ba, zan tafi imbarka a hannun likitan birni Abdul nasan zai kula da kai sosai ina maka fatan alkairi da samu lafiya ya kai wannan kyakkyawan matashin ni ce ZULAIKA wacce ake kira da Zulai Mamman a makaranta a gida kuma ana kira na da Zulai yayinda Habu saurayina kuma mijina na gobe ya ke kira na mai lof ya ce wai sunan ƴar birni ne wanda suke kiran masoyi da shi."
Shiru ta yi tare da goge hawayen idonta ta tashi da zummar ta tafi caraf ta ji an damƙi hannunta wanda sai da tai baya tsabar tsoro kamar zata faɗi amma aka kuma fizgota da tsananin ƙarfi wanda hakan ya saka ya faɗa ruf da ciki akan wannan matashin mai kama da turawa tai flat akan shi, yayin da hakan yai daidai ta rafka salatin Iya Abu da sauran jama'ar da suka shigo wajen a tare sukai tsaye cirko-cirko sai zare idanuwa suke iya na mujiya.
"La'ilahwa ilallahu, inna atuni minal tone-tone yau ni Audu gwangwan na ga abin da ya ishi uwata Salame, wato dama labarin da ya karaɗe gari cewa kina can yawon iskanci A DAREN AURANKI, to wallahi uban kuturuma yai kaɗan yau sai munga ubanda ya tsaya maki a ƙauyen nan ƴar iskar yarinya mai halin ban...."
Bai idasa faɗin abin da zai faɗa ba Zulai ta taso da dukkan ƙarfinta tare da yin girgiza ta wancakalar da ɗan kwalin kanta ta barbaza gashinta ya zubo gaba da baya sannan ta fasa gigitacciyar ƙara tai kan Audu gwangwan da yai suman tsaye lokacin da yai tozali da juyayun idanuwanta, ɗaram Zulai ta maƙale akan Audu gwangwan da ya ke yana da jiki ma sha Allah, siraran hannuwanta ta ɗaga ta dinga tallare sontaleliyar ƙeyar Audu gwangwan wacce ta sha askin kwal da kobo sai sheƙi ta ke gami da walwali, cike da tsananin tashin hankali Audu gwangwan ya shiga kiciniyar yanda zai sauke Zulai daga jikinshi ya kasa, kyarma su mai gari da sauran mutanen wajen suka shiga yi jin yanda Zulai ke wani irin gurnani mai ban tsoro, sai da ta rantali kan Audu gwangwan san ranta sannan ta ƙyale shi ganin har ya fara kukan azaba, direwa tai daga kanshi ta nufi inda me gari ya ke tsaye ya na sallati gami da addu'o'in neman tsari daga sharrin shidanun aljannu, bai yi aune ba ya ji hannun Zulai akan gemunshi ta janyo da iya ƙarfimta, wani irin gigitaccen ihu mai gari ya saki jin yanda aka wani fizgi dogon gashin gemunshi, cike da azaba ya ke neman agajin mutanen da ke wajen amma babu wanda yai koda motsi bare akawo mai ɗauki, kuka mai gari ya saka kashirɓan tare da bawa Zulai haƙuri tare da yi ma ta alƙawurrra da yawa.
Ita ko Zulai yi tai kamar bata san abin da ke faruwa ba dan kuwa dama can ta na jin haushin mai gari da tawagarshi saboda yanda suka saka ma ta
TAKU HAR KULLUM
MARYAM STAR ⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪
👰♀️A DAREN AUREN 👰♀️
WRITE BY
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)
MARUBUCIYAR
DAFIN MACIJI🐍
AND
RAYUWAR SAMHAD🌹
Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
💙💙💙💙💙💙💙💙
A DAREN AURENA
PAID BOOK
💙💙💙💙💙💙💙💙
Chapter 4
بسم الله الرحمن الرحيم
Idanu suka hana ta rawar gaban hantsi ga wani bin diddiƙinta da suke saboda kawai wanda za ta aura ƴa na ɗan mai gari, sai da Zulai ta tabbatar da ta wajiga mai gari sosai dan shima sai da ya yi kuka sannan ta kyale shi, haka ta bi mutanen mai gari da su kaɗai suka rage a wajen dan kowa ya watse dan tsira da lafiyarshi, su ma fadawan duk sun tsure ganin yanda ake azabtar da mai gari, babu halin tserewa ne saboda muddin mutum ya gudu idan wani abu ya faru to fa ancire shi daga matsayinshi.
Zulai na sakin gemun mai gari tai baya-baya ta faɗa luuuuu a jikin wannan matashin tai ɗaiɗai abinta, a zuciya ta ke faɗin 'Wai dama wannan baturen haka jikinshi ke da laushin tsiya wallahi sai na mori wahala ta akan shi, sabo da shi ceto ranshi yau nai gwagwarmaya harda sadaukarwa sai da nai walahi, ina dalili gwara in ɓararraje in mure laushin wannan fatar.'
Yayinda a fili kuwa ta shiga yin murƙushe-murƙushe tare da sakin numfashi ta koma tai lakwas alamar ta dawo hayyacinta, mai gari tun da ta saki gemunshi ya tattare babbar rigarshi tare cire takalmanshi ya saita hanya ya kwasa a mugun guje, fadawanshi ma ganin oga ya tsere su ma suka rufa ma shi baya kamar ma su gudun tsere dan kuwa kowa fata ya ke ace ya wuce ɗan uwanshi, gudu suke bakin rai bakin fama ga rigunansu sai cika suke sa iska,