Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 5
hanya dan kuwa munyi waya yau da asuba ya sake tabbatar min da ansamu kuma ƴar uwarshi ce, ya na da yaƙini akan zata iya, to na bashi umarni akan ya ɗaukominsu yanzu da safenan kafin anjima Mu'allim ya zo." Jinjina kawuna sukai a zuciyoyinsu su na addu'ar Allah ya sa a dace, indai kuɗi za su yi aiki to a shirye suke wajen ganin sun salwantar da ko nawa ne dan samun lafiyar sanyin idaniyarsu. Bayan isowarmu da kamar mintuna goma, amma shiru babu wanda ya leƙomu, mamaki, gidadanci gami da ƙauya ci sun gama daskare man kawunanmu ni da Abba, idan Abba ya kafe abu ɗaya da ido tofa ba zai janye idonsa ba har sai ya gamsu da bayanin da kwanyarshi ke ma shi na adadin kuɗaɗen da abun ya lashe kafin wanzuwarshi, duk da iskan AC da fankoki ma su wurwurawa da tsanani gudu hakan bai yi nasarar hana gumi tsatstsafowa Abba ba, duk bayan sakanni sai ya kai hannunshi ya shafce gumin da ke barazanar jiƙeshi, sai zare jajayen koɗaɗɗun idanuwansa ya ke ya na shege lafiya, lissafi tun ya na yinshi ya na tafiya daidai har busy yaiwa brain ɗinshi yawa ta daina bashi haɗin kai saboda yanda ya takurata da lissafe-lissafe. Tsinewa rashin siyo calculator ya saka a cikin aljihu saboda irin haka da yayi yafi sau shurin masaƙi, ni kuwa tun lokacin da akai mana iso zuwa wannan danƙareren ɗakin na alfarma wanda ya ke cike da kayan ƙawa da more rayuwa jikina yai sanyi, sai na soma tunanin anya kuwa a cikin duniyar mutane mu ke, ko dai duniyar aljannu Yaya Hashim ya kawo mu, tun ina kallon kayan ƙawa da more rayuwar da aka wadata ɗakin da su cikin tsoro, mamaki gami da al'ajabj, har na ware ina bawa idanuwana abinci nima nabi sahun Abba wajen buɗe idanuwana ina kallon kayan ban mamaki, wato malam arziƙi na inda yake, talaka bawan Allah inji hausawa sukace Talaka buzun banza indan ta mutan gari sai ya mutu. Saƙe-saƙe da lissafe-lisafe babu wanda banyi ba, amma sam hankali da brein ɗina sun gaza lissafo min adadin yawan maƙudan kuɗaɗen da aka narka wajen gida wannan gida. Wa ta dattijuwar ma ta ce ta shigo da kayan uniform a jikinta, a bayanta matasan ƴan mata ne suma sanye cikin uniform kalar na ta, sai Yaya Hashim da ke biye da su waya kare a kunenshi da alama waya ya ke. Cike da fara'a matar ta ƙaraso inda muke tare da bawa ƴan matan umarnin ajiye treyn da ke hannuwansu wanda ya ke shaƙe tab da kuloli da jug na alfarma. Gaishe mu tai tare da ƙare manah kallo ganin irin shigar da ke jikinmu, duk da ba kallon raini ko ƙasƙanci tai mana ba amma sai naji duk na muzanta, musamman dana ɗaga kai na kalli yanda kayan uniform ɗin jikinta suka sha guga suka kwanta kuf, sannan fatarta luwai gwanin kyau dan harda siririn glashi a idonta, yaƙe kawai nai ma ta ina sinne kaina ina jin wani iri, atamfar jikina na kalla wacce tana ɗaya daga cikin kayan da nike ji da su, Yaya Sumayya ce ta bani ita a wani zuwa da sukai Katsina biki suka dawo da kaya niƙi-niƙi wanda ƴan uwan Umma suka basu, shine ta ɗaukota ta bani saboda rigar ta yi daidai da ni, saboda bani da ƙiba sam sai dai inada cikar jiki da ƙira me jan hankali. Janye ƙafafuwa nai tare da ƙudundune su a cikin hijabi, dan ina ɗago kai naga matar ta kafe ƙafafuwan nawa da ido, ba tun yau ba nasan Allah yai mani halitar ƙafa me kyau da tsari, sautari idan na ina ina zaune da Mama takan janyo ƙafafuwa ta ɗaura a kan cinyarta ta na shafawa wai burgeta suke. Abbana yai saurin saukowa ƙasa bayan ya amsa gaisuwar matar cike da fara'a kamar bakinshi zai yage, bayan ta gabayar mana da waɗanan kuloli wanda na tabbata cike suke da abinci na alfarma, godiya Abba ya shiga zundumawa kamar sabon maroƙi, nannaɗe hannun riga ya soma yi tare da haɗiyar yawu ji kake "Maƙwat". Kiciniyar buɗe food flasck ɗin ya soma amma ya kasa, gudun kar ya je yai ɓarna ya sa ya kalle ni tare da faɗin. "Ke Mubeenah sauko ki buɗe mana coolar muyi mu ci kafin mutan gidan su fito, dan wallahi Allah cikina ya kwakware kamar ban taɓa cin komi ba, dama dai ɗan ruwan kunu ne wanda Umma ta dama kuma kinsan halinta da baƙar ruwar tsiya ɗan kaɗan ta sammin." Banja da nisa ba na sauko, dan nasan halin Abba tsaf zai dalle ni maruka babu ruwanshi dan yasha faɗi da bakinshi cewa shi abin kunya gaba ya bashi ba bayaba, iskanci da abin kunya gadonshi sukai. Da ƙyar na iya buɗe food flask ɗin waɗanda suke ta faman ɗaukar ido da walwali, zazzafan peper soup ne wanda ke ta faman tashin ƙamshi me tado tsohuwar yunwa, ɗayar kuma soyayyen dankalin turawa wanda aka soya da kwai, jug ɗin kuma kunun madara ne fari sol sai daƙƙuwa yakemin, ban san sanda nima na bi sahun Abba wajen haɗiyar yawuba. Abba bai jira na zuba a plate ba ya suri cinyar kaza ba tare da yayi bisimilla ba ya dirar ma ta, ganin haka ya saka nima nai maza na zanyo plate na warci ƙirji da fuffuke na saka tare da ɗan tattare hijabina gudun kar ta ɓaci nai bisimilla tare da far ma ta, lokacin da ɗanɗanon naman ya ratsa kwanyata sai da nai hooking na wucin gadi, idan ma rantsuwa nai to bazanyi kaffara ba tunda nike ban taɓa cin kaza me makamancin ɗadin wannanba, ga shi ta dahu luɓus tai taushi gwanin ɗadi wajen ci, ina ci ina jinjina kwarewar wacce ta sarrafa wannan girki, ba maki ɗari ba ni dai har maki dubu ɗari na bata wallahi. Jug ɗin kunun na janyo na tsiyaya a ƙaramin cup, tare da zuba dankalin shima a plate ɗin da nike cin kaza, harga Allah ina da karah da kawaici amma banda wajen abinci, ina bawa cikina muhimmanci sosai, bare nasan idan na tsaya sanya tsaf Abba wai wawure abincinan tas ya barni da haɗiyar yawu, shi yasa nima ban tsaya cutar kainaba na saki jiki na cika tunbina tsaf. Abin mamaki duk irin mugun cin Abba sai da ya gaji ya ture kazar nan ya koma kan kunun madara, shima ya ɗaɗɗaka sosai amma bai shanye ba, yo ta ina zai iya shanye wannan kayan gara waɗanda ƙamshinsu kaɗai ya isa ya ƙosar da mutum bare ace ya ci, wani abu ɗaya da na hasaso shine, tabbas idan dai ɓangaren masu girki za'a ɗaukeni aiki zan zage in koyi irin waɗanan abubuwan dama na daɗe da burin zuwa koyan girki amma sai Umma ta sakamin mugunta, har makaranta abokin Abba ya taɓa samomin ni da ɗiyarshi amma ta shiga ta fita ta hanani zuwa sai aka ƙaƙabamin zaman shago cikin yare. Duk abin da muke Yaya Hashim na zaune a gefe yana kallonmu, kunya gami da takaicin halin Abba duk ya cikashi, dama yasan za'ayi haka shi yasa koda wasa bai taɓa nuna ga irin gidan da ya ke aiki ba dan yasan dole wa ta rana irin haka za ta faru. Bayan na gama ne na suɗe hannuna tas kaɗi da lashe pink lips ɗina kamar banci komi ba, sai lokacin hankalina yakai wajen Abba wanda ya wani bararraje kamar gidanshi, duk ya ɗiga musu miya a jikin carpet da gabanshi rigarshi da ya ɓata kamar wani ƙaramin yaro. Kunya ce ta kama ni ganin yanda tai, ina tunanin inda zan samo ma shi ko da tsumma ne ya goge jikinshi kafin masu gidan su iso, amma kash na makara dan kuwa ban gama tunanin mafita hancina ya shaƙomin wani irin sanyayyen daddaɗan turare me saukar da nutsu....✍️ IN SHA ALLAH SAURA ONE PAGE MU KAMMALA FREE, SABODA HAKA MAZA-MAZA KU HANZARTA BIYAN KUƊINKU DOMIN SAMU DAMAR KARANTA WANNAN LABARI. 9136291920 MARYAM UMAR OPAY. KU SAKA SHIADAR BIYA A WANNAN LAYIN👇👇 09136291920 Only watsapp👌 TAKU HAR KUKLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR ⭐⭐⭐ 🔥🔥ZAFIN WUTA🔥 Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥 LABARI ME CIKE DA BAN TAUSAYI,😩 MATSANANCIYAR DAMUWA,😭 KUNCIN CUZIYA,💔 SADAUKARWA,💌 ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘 WRITING BY MARYAM STAR ⭐⭐ YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR📒✍️ RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA🔥 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) Typing...📲 PAID BOOK 500 ONLY👌 CHAPTER 50-55 بسم الله الرحمن الرحيم. Me saukar danutsuwa gami da nishaɗi, kafin ingama tunani akan daɗin ƙamshi turare wa ta matashi wacce ta ƙawatu cikin uban ado kamar wacce za ta je gasar kyau ta bayyana a parloun, gayu iya gayi ta yi shi amma kuma kallo ɗaya nai ma ta na tabbatar da ta na tare da matsananciyar damuwa, fuskarta fayau babu komi akanta sai man leɓe me sheƙi, idanuwanta duk sun zurma can ciki da alama tayi rashin lafiya saboda sautari akan samu irin wannan ramarne wajen wanda yai rashin lafiya, ko me fama da matsananciyar damuwa. Siririyar sallama ta yi idanuwanta na akanmu, amsa ma ta na yi ina janye idanuwa daga kallonta, kallon secons biyu tai mana sannan ta ɗauke kai zuwa inda Yaya Hashim ke zaune, cike da girmama ya zamo daga kujerar tare da faɗin. "Ranki ya daɗe Hajiya Sulaima barka da wannan lokacin." A taƙaice ta amsa tare da bashi umurnin mu biyo bayanta, babu ɓata lokaci yai manah inkiya akan mu taso da sauri. Hakanan kawai na ji gabana ya tsananta dokawa da tsananin ƙarfi, sannan kuma kasala ta baibaye ni da ƙyar na samu na miƙe akan ƙafafuwana. Abbama tuni ya miƙe ya na ta faman sakin gyatsa da buɗaɗɗiyar muryarshi. Rufawa Yaya Hashim baya mukai har zuwa wa ta ƙofa ta glass wacce akaiwa ado da kalar gorlding, sai ɗaukar ido ta ke, bayan wannan wacce Yaya Hashim ya kira da Sulaima ta shiga muma muka rufa ma ta baya ni da Abba fuskokinmu fal mamakin irin wannan dukiya da aka narka, a wani ƙayataccen makeken parlou wanda ya gaji da gaɗuwa muka ɓulla, su uku ne zaune akan ƙayataccin kujerun alfarwa waɗanda aka ƙawata wajen da su, Dattijuwa ce zaune kusa da wa ta mata wacce taɗan jingina da jikin Dattijuwar, sai wa ni kamulallen mutum zaune a kujerar kusa da su, kusa da mutumin wacce aka kira da Sulaima ta nufa tare da zaunawa ƙasan ƙafafuwanshi. Cike ca fara'a Dattijuwar ta ke mana sannu da zuwa, yayin da na sake shiga wani irin yanayi marar misaltuwa ga zazzaɓi da ke shirin rufar ma ni nan take, a ƙasƙance muka rakuɓe ni da Abba, mu na jinmu wani iri ganin yanda muka samu mutanen wajen kamar sarakuna saboda ado da kwalliya, mu kuma sai na dinga ganinmu kamar bayi duƙe a gaban sarki ko yarima. Abba kamar zai taune harshe wajen gaisarda su,ni kuwa cike da nutsuwa na gaidasu ba tare da na kallesu ba. Mommy ce ta ɗago a hankali ta na gyara zamanta tare da kafe ni da ido kamar me kokonto a kaina, sai kuma ta kalli Pahpah wanda shima dai idonshi a kaina ya ke, ita kuma Hajjo hankalinta na wajen Abba wanda ke ta faman zare idanuwa ya na ƙarewa duk abin da idonshi ya sauka akanshi kallo, idan ya kalli abu sai ya lissafi idadin kimanin kuɗaɗaɗen da abin zai iya lashewa sannan ya jinjina kai ya koma wajen wani abun, bayan kamar min tuna biyu da zamanma Pahpah ya kalli Yaya Hashim tare sa gyaran murya sannan ya ce. "Masha Allah, Hisham wannan ita ce ƙanwar ta ka ko? gaskiya na yaba da hankalinta sosai, kuma ina da yaƙini akan za ta iya, nutsuwarta da kamalarta sun burge ni ainun, sannan ina fatan itace za ta zame mana abin alfahari anan gaba." "Dararammm" ƙirjina ya doka da tsananin ƙarfi, yayinda zuciyata ke kokowar fitowa saboda razani da fargabar da nike tsintar kaina a gaban waɗanan mutane. Aje numfashin Pahpah ya yi daidai da tabbatuwar lissafin da zuciya da kwanyar Abba ya haɗe waje ɗaya, tare da gamsar da kanshi wannan ita ce sakayyar yanda gobenshi da ta iyalanshi za ta kasance, dan haka sai ya aro bargon nutsuwa ya yafawa kanshi, tare da ƙoƙarin hana idanuwanshi kalle-kallen abubuwan da suke neman caza tunaninshi. Nutsuwarshi ta yi daidai ta kallonshi da Pahpah yai tare da fara yi ma shi magana ya na karantar yanayinshi. Babban abin da ya burge bai wuce yanda naga Abba ya kame kamar ba shi ba ya na zayyano zantuka masu ma'ana da dattako, sai na ji wani sanyi da farin ciki ya baibaiyane yau ɗaya Abba ya ɓoye hallayarshi a gaban mutane. ⭐⭐⭐⭐ BAYAN AWANNI BIYU. ⭐⭐⭐⭐ Zaune nike akan mafefen royal bed ɗin da ya mamaye ɗakin, ya yinda idanuwa ke zubarda hawaye wanda ni kaina bansan na minene ba, amma zuciyata ta tilasta ni amincewa sa lallai Abba baya so na, ban taɓa kawo afkuwar irin wannan lamarin nan kurkusa a rayuwata ba, ban san mi yasa a kaina Abba ya ke kasancewa me son kanshi ba, muddin lamari ya shafe ni to babu makawa sai Abba ya nuna son kai akaina. Ɗaure fuska na yi tare da furta "Abba kenan, ina mai tabbatar maka daga wannan karon rayuwata ta canza, Abba daga yau bazan sake kasancewa cikin baƙin cikin abubuwanda kake yiminba, daga yau zan tsaya tsayin daka wajen ganin na inganta rayuwta kamar ko wace mace." Na yi maganar kamar Abban na gabana ko ancemin ya na jin abin da nike faɗa. Rigar da aka aje kusa da ni marar nauyi na ɗauka, sai da na tabbatar da babu me kallona sannan na shiga warware ƙaton towel ɗin da aka kawomin wai in ɗaura idan zan shiga wanka, a jikin ƙaton madubin da ke shaƙe da kayan kwalliya na kalla, ina sake ƙarewa surar jikina kallo ta cikin gashin, wani irin daɗi ne da sanyi ne ya baibaye ni domin kuwa ni kaina nasan Allah yayimin baiwar tsarin zubin hallitta me ɗaukar hankali, sai na ji zuciyata na min wasu saƙe-saƙe aiko nai saurin yin A'uziyya tare da hanama kaina sake yarda da yin makamancin wannan tunanin, cikin sauri na zura rigar tare da mulke jikina da lallausan losion wanda naga an jera, ban tsaya jiran komi ba na ɗauki veil ɗin rigar na ɗaure kaina da shi, sai na kawo hijabina na saka, kallon kaina nai a madubi sai naga na yi wani irin kyau na musamman wanda zan rantse ban taɓa yin irinshi ba, tunawa da wannan matar wacce na ji sun kira da Mommy ta ce inyi sauri ta na jirana, ya saka nai hanzarin juyawa dan infita, sai de kuma na mance inda ƙofar ta ke, duk inda na taɓa sai inga ashe ba ƙofar ba ne, tashin hankali ne ya baibaye ganin ƙofa ta ɓacewa ganina, da ƙyar na rarrashi kaina banyi kuka ba, amma kuma daf ni ke da rafka ihu ko za'a samu wanda zai kawo min ɗauki idan ya jiyo ni. Ƙarar buɗe abu na ji, cikin sauri na ɗaga kaina dan ganin minene, sai na sauke udanuwa akan wacce na ji an kira da Sulaima, ajiyar zuciya na saki ina godiya ga Allah da ya kawo min ɗauki. Guntun murmushi ta sakarmin tare da ƙarasowa inda nike ta na min magana da turanci, aiko gaba na sake tsallen bugu, dan harga Allah nasan ina jin turanci amma da na ji yanda ta ke nata turancin cike da kwarewa da iyayi sai na kasa fahimtar mi ta ke nufi. "Oh sorry, Mubeenah ko! dama Mommy ce ta ce ki zo muje idan kin ƙarasa, tun ɗazu muke jiranki amma shiru baki fito ba." Zurum na miƙe tsaye ba tare da na yi magana ba, dan sai na tsinci kaina cikin tsoron buɗe baki inyi magana kar inyi ba daidaiba in kwafsa. Ganin na miƙe tsaye ya saka ta ɗauke kai daga kallona da ta ke, a ranta ta ke yabawa da irin kyawun da Allah yai min, sai de rashin gyara da ƙarancin wayewa ya disashe ƙyalin kyawun nawa, amma duk da haka kallon farko za'a sakani a cikin jerin kyawawa. Bin bayanta ni ke kaina a ƙasa har muka isa wani ɗan ƙaramin parlou wanda babu komi a cikinsa saga na'urar Ac sai ƙaramin fridge me kyau da tsari sai kujeru masu taushi. ganinmu ya saka Mommy da Hajjo miƙewa tsaye, bayan mun ƙarasa na zame na sake gaidasu ta hanyar yin jimla. Bayan sun amsa Hajjo ta matso kusa da ni tare da kama hanuna ta na faɗin. "Mu je jikata yarinyar kirki, Allah ya albarkaci rayuwarki ya haskaka ki da saiken alkairi." Amsawa na yi a cikin zuciyata ina yaba karamci irin na waɗanan mutanen. Mommy ce gaba sai ni da Hajjo da Sulaima a bayanta, sai da tai ɗan jimmm sannan ta tura ƙofar glashin tare sa Bisimilla ta tura kanta ciki, haka Sulaima ta rufa ma ta baya, yayinda Hajjo ta tura kanta tare da janyo hanuna nima na shiga. Wa ni irin mummunan bugu ƙirjina yau, wanda saura taƙi ɗaya rak ya ragewa zuciyata ta wuntsilo ta maƙogarona zuwa waje, ban san lokacin da na duƙe a wajenba na shiga maida numfashi da tsananin sauri, hannunawa dafe da ƙirjina, dokawar da zuciyata ke yi na barazanar toshe magudanar numfashina, yayin da wa ta iriyar zufa tare da sanyi suka lulluɓe ni lokaci guda, juyowar Mommy da duƙowar Hajjo a kaina ta na jijjigani ya yi daidai ta isowar Pahpah wajen, cikin hanzari ya matso kusa da ni fuskarshi na bayyanar da annuri gami da tausayina a lokaci ɗaya, kafin kowa ya samu damar cewa komi Pahpah ya duƙa tare da kamo hannuwana ya miƙar da ni tsaye, sai da ya tabbatar da na samu nutsuwa sannan cikin taushin murya gami da rarrashi ya ke faɗin. "Ki nutsu! nutsu kinji mah doughter, ki tausayawa halin da ɗan uwanki musulmi, kuma wanda ke amsa suna miji a gareki yanzu ya ke ciki, ke kaɗaice za ki iya ceto rayuwarshi da taimakon ubangijinmu, na baki yardata 100% a karo na farko a cikin rayuwata da na yarda da wani mutum na daban har na yi marabada shi a cikin familynah." Duk da yanda ƙafafuwana ke rawa su na barazanar kayarda ni, amma sauraren kalaman da suka ci gaba da fitowa daga bakin Pahpah, wanda nike wa kallon mutum me daraja da karamci, sai na ji zuciyata na bani kwarin gwuiwa, hakan ya saka na shiga gyaɗa ma shi kai, ban san wane zaren ƙaddara bane ya janyo ni zuwa cikin waɗannan ahali masu karamci, ban san cewa amincewar da na yi ba zai zama mabuɗin buɗe ƙofofin ƙaddararon rayuwata, haka kawai nike ji a jikina daga yau kuma yanzu rayuwata ta sauya, sauyi sosai wanda ya banbanta da irin faɗi tashi da tarin ƙalubalen da na fuskanta a rayuwata. Cike da tausaya Pahpah ya janyo hannuna zuwa ainahin cikin ɗakin, wanda shigata cikinshi ya zaftare abubuwa da dama daga ratuwa da burukana, ɗakin da ya zama wajen da zan kafa tarihin wa ta rayuwa me cike da rikitattun al'amurra. Duk taƙo ɗaya da zanyi, ina aje ƙafata ne tare da bugawar zuciya me tsananin ƙarfi, sannan kuma ina jin wani irin ZAFI me kama da ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 ya na fuskanto ni, a daidai lokacin da na sauke takona na ƙarshe, a lokacin ne zuciyata ta tsaya cak da bugawa, gangar jikina ta kafe akan ƙafafuwa, a sa'ilin da idanuwa suka sauka abin abin da ya nemi hargitsa duniyata a lokacinne kwanyata ta shiga maimaitomin tariyar mafarkan da suka addabe ni a cikin barci musamman kwanakinnan.....✍️ ALHAMDULILLAH🙏💃 YAU DAI ALLAH YA AMINCE NA KAMMALA FREE PAGE, YANZU ZAMU SHIGA AINAHIN CIKIN LABARIN BA TARE DA ƁATA LOKACI BA. DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA WANNAN LABARI ME RIKITATTUN LAMURRA KI DAURE KI BIYA NAIRA 500 KACAL👌 A WANNAN LAYIN. 👇👇👇👇👇👇 9136291920 MARYAM UMAR OPAY. NICE TA KU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU"MARYAM STAR⭐⭐⭐KE MUKU FATAN ALKAIRI🙏🙏🙏" WAƊANDA SUKA BIYA PAYMENT SAI MUN HAƊU A BOOK TWO... An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5