Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
on Instagram as @maryamumarkt553. Get the app and follow me https://www.instagram.com/maryamumarkt553 https://ngl.link/maryamstar https://www.wattpad.com/user/maryamumarstar?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends 🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥 LABARI ME CIKE DA BAN TAUSAYI,😩 MATSANANCIYAR DAMUWA,😭 KUNCIN CUZIYA,💔 SADAUKARWA,💌 ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘 WRITING BY MARYAM STAR ⭐⭐ YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR📒✍️ RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA🔥 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) Typing...📲 PAID BOOK 500 ONLY👌 SEASON TWO CHAPTER 15-20 Wata jaka ce ta faɗo daga sama ji kake timmm, ɗaukarta boka yai tare da faɗin. "Angaishe da hatsabibi uban hatsabiban aljannu, aikinka ya na kyau." Jakarce ta shiga buɗe kanta, wani farin abu ya bayyana acikin wata ƴar farar roba, fito da abin Boka yai tare da miƙawa matashin haɗi da yi ma shi bayani akan yanda zai yi amfani da maganin. Bayan ya amsa yai godiya gamida kirari sannan ya rumtse idonshi, nan take ya ɓace ɓat bai ɓulla ko ina ba sai gaban wannan dutsen da ƙorai ke ajiye, kayanshi ya mayar tare da hanzartawa ya nufi wajen da ya aje motarshi ya shiga ya jata da mugun gudu dan duhun dare ya fara. BANANA ISLAND Tamfatsetsen gida ne wanda ya lashe million kuɗaɗe wajen ginashi, tun daga nesa zaka tabbatar da lallai ko waye ya mallaki wannan gjdan tabbas ba ƙaramin me dukiya ba ne. Wa ta hamshaƙiyar mata ce me tsananin wayewa da gayu ta fito daga wani ɗaki fuskarta da alamar damuwa, yayinda wa ta matashiyar budurwa ke biye da ita a baya ta na zubda hawaye. Wani haɗaɗɗen ɗaki suka shiga basu tsaya ko ina ba sai gaban gadon da wani marar lafiya ke kwance yana amai, wa ta iriyar ƙara wannan matar ta saki tare da yin baya tai taga-taga kamar za ta faɗi tsabar firgicewa, cike da tashin hankali ta ke faɗin. "Sulaima kina ganin abin da ni ke gani kuwa, wuta! wuta ce nike gani na fitowa daga bakin Fauzan, please ki ce min ba gaskiya bane mafarki ne, tayaya hakan zai faru, ki gaya min tayaya mutum zai dinga amayo wuta daga cikin jikinshi." A firgice ta ke maganar hankalinta idan ya yi dubu y tashi, yayinda hawaye ke zaryar saukowa daga idanuwanta su na zuba akan kyakkyawar fuskarta. "Mommy! wallahi dagaske ne, dagaske Yah Fauzan ne kike gani a cikin mawuyacin hali, shikenan nasan zamu rasa Yah Fauzan, nasan ba lallai ya tashi ba, wayyo Allah ka kawo manah ɗauki, ya Allah ya tashi kafaɗar wannan bawan naka me tsananin biyayya ga umurninka, Ya Allah ka bawa wannan bawan naka lafiya domin ya tashi yaci gaba da bauta maka kamar yanda ya ke yi lokacinda ya ke da lafita, Ya Allah ka yanke ma shi wannan wahalar hakanan." Kukane ya ci ƙarfinta har jikinta na jijjiga saboda tsabar yanda ta ke kuka. Cike da juriya, tausayi gami da zazzafar soyayya irinta uwa da ɗa matarda aka kira da Mommy ta taka zuwa inda wannan mutumin ke kwance ya na maida lumfashi, yayinda tururin wuta ke fita daga bakinshi da hanci, zama tai a ƙasan gadon glass ɗin da yake a kwance bai ko iya motsi ta na zubarda hawaye, yayinda ta ɗaga hannunta zata ɗaura akanshi wani irin ZAFIN WUTA ya bugo ma ta, da mugun sauri ta janye hannunta tare da sulalewa a ƙasan wajen ta na sakin kuka me ƙarfi , irin wanda ya ke fitowa daga can ƙasan rai, kuka ta ke ta na surutai wanda babu me iya jin abin da ta ke faɗi. A hankali marar lafiyar ya shiga buɗe idanuwanshi tare da ƙoƙarin juyasu zuwa inda matar ke nuƙe tana kuka, wani irin ja da baya Sulaima ta yi tare da fasa ƙara me tsananin ƙarfi ta na nuna marar lafiyar, ɗagowa Mommy tai daga duƙen da ta ke, aiko ta ci karo da abin da ya kusa tsaida bugun lumfashinta. "Yah Fauzan dan Allah ka rufe idanuwanka banason gani, please bana son gani tsoro ka ke bani." Sulaima ta yi maganar ta na saka hannayenta ta dafe idanuwanta da ƙarfi. A hankali wanda ta kira da Fauzan ya fara karkata kanshi zuwa ɗayan sashen, abin mamaki duk sanda wuyanshi ya motsa da niyyar juyawa sai wajen ya saluɓe ya ƙone, a maimakon jini ko ruwa ya fito sai hayaƙi ya dinga fitowa daganan kuma sai wuta ta kama kamar wacce aka zubawa fetur ko kalanzir. Mommy da ke kallon abi da ke faruwa ɗif kukanta ya ɗauke wani irin tsoro, fargaba da tashin hankali ne suka bayyana a fuskarta, yawun bakinta ya ƙafe laɓɓanta suka bushe sai ƙoƙarin buɗe baki ta ke dan tai magana amma ta kasa, ko motsi kasawa tai sai idanuwanta da ke sake firfitowa waje. Duk irin azabar da ya ke ji baj daina motsa jikinshi ba sai da ya juyar da kanshi saitin glashin da aka kewaye ɗakin da shi, ƙur ya ƙurawa ƙwarangwal ɗin fuskarshi ido ya na jinjina girman ikon Allah, yayinda tsoro ya kamashi ganin yanda idanuwanshi da ya sa ni a farare suka juye zuwa launin jah, ga wani tururi da ke fitowa daga cikinsu, duk da ya na jin azaba a duk lokacin da yai ƙoƙarin yin magana amma haka ya daure cikin ƙarfi hali ya ke faɗi a fili. "Inalillahi wa'inna'ilaihi raju'un ya Allah ka ɗauki rayuwata dan sauƙaƙawa mahaifiyata wahalar da ta ke da ni, yah Allah ka yankewa jajirtacciyar uwa hawalar jinyar yaron da ka jarabceshi da cuta, Allah ka ga zuciya ban butulce maka ba akan jarabawar da ta same ni ba, na roƙeƙa ne dan tsananin tausayin mahaifiya me rauni akan ɗanta." Maganace ta gagareshi domin kuwa tuni bakin na shi ya dare tare da saluɓewa, yayinda Sulaima da ke kaklonshi ta cikin glass ke faɗin. "A,ah Yaya a,a please kadaina kana jiwa kanka ciwo, dan Allah ka daina magana yah Fauzan." Ta faɗi ta na kai gwuiwoyinta a ƙasa dan ƙafafuwanta sun gaza bata haɗin kan tsayuwa. Ganin halin da Mommy ke ciki na suman zaune ne ya sakata sake fashewa da wani matsanancin kukan tare da dafe saitin ƙirjinta jin lumfashinta na barazanar ɗaukewa. TAKU HAR KULLUM MARYAM STAR ⭐⭐⭐ 🔥𝑍𝐴𝐹𝐼𝑁 𝑊𝑈𝑇𝐴🔥 Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥 LABARI ME CIKE DA BAN TAUSAYI,😩 MATSANANCIYAR DAMUWA,😭 KUNCIN CUZIYA,💔 SADAUKARWA,💌 ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘 WRITING BY MARYAM STAR ⭐⭐ YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR📒✍️ RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA🔥 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) Typing...📲 PAID BOOK 500 ONLY👌 SEASON TWO CHAPTER 20-25 Kuka Sulaima ke yi bakin rai bakin fama ta na jijjiga Mommy wacce hankalinta ya gushe daga gangar jikinta. Fauzan ma kukan ya ke amma na zuci dan duk ƙarfin halinshi yanzu baya iya yin kuka saboda tsoron yanda hawaye ke zuba kan fuskarshi su na ƙona shi, jin shi ya ke bayada banbanci da gawa, azabar da yake ji kaɗai ta isheshi ya ji ya gaji da duniya da abin da ke cikinta. "Fatima! Fatima!! ke Fatima wai kina ina ne haka, wannan kukan daga ina nike jiyoshi ne wai, duk ambi an cika gida da iface-iface kamar gidan mutuw...." Kasa ƙarashe maganar tai yayinda idanuwanta sukai tozali da Mommy a ƙame, Sulaima na kuka tare da jijjigata, a ɗari da tamanin ta idasa shigowa ɗakin ta na sallati da salallami ganin halinda ta iske Mommy a ciki. " Na shiga uku ni Salamatu, mi zan gani haka, mike damunta ta ƙafe haka bata ko matsi." Dattijuwar matarda zata kai kimanin shekaru sittin ta faɗa a cikin rikewa ganin halinda wacce ta kira da Fatima ta shiga. Kafin Sulaima ta samu damar cewa komi wani itin huci me tsananin zafi ya ɗumame ɗakin lokaci guda ga wani hayaƙi baƙi ƙirin da ke tashi, cike da ɗimauta Dattijuwar ta ɗaga kanta tai duba idan Fauzan ya ke, wani gigitacen salati ta saki tare da kuka me ƙarfi cikin tashin hankalin ganin yanda Fauzan ke ƙoƙarin juyowa amma jikinshi yaƙi bashi haɗin kai, duk inda ga motsa sai wajen ya kwalje tare da feso wuta gami da baƙin hayaƙi, cike da rikicewa da ƙarfin hali irinna tsofaffi Dattijuwar ta rarrafa da ƙafafuwanta da suka gaza ɗaukarta zuwa gaban gaɗon glashin da Fauzan ke kwance. "Haba Fauzan miye hakan kake ƙoƙarin yi! mi yasa zakai hakan, shin baka tausayin halinda mahaifiyarka ke shiga idan ta ganka cikin wannan halin, mi yasa ba zaka yi haƙuri kaɗauki danganaba, ka duba kaga yanda jikinka ke kwaljewa idan ka motsa bayaga haka har wuta ke fesowa, bamusan mi kake ji ba a jikinka amma tabbas munsan kana cikin azaba me raɗaɗi wacce ka zaɓi mutuwa a kanta, ka yi hakuri ka jure ka dogara da Allah zai kawo maka ɗauki, ka ƙara haƙuri da juriya akan yanda mukasanka, tabbas kai ɗin me juriya ne tunda har ka iya shanye raɗaɗi da azabar da kake ciki na tsawon lokaci, in sha Allahu ina ji a jikina sauƙi ya zo, ina ji a jikina samun lafiyarka ya zo nan kusa-kusa, ka jure ka daina motsa jikinka ka ji bawan Allah, duk wanda ke da sa hannu a cikin wannan lalurar ta ka In sha Allahu, Allah bazai barshi ba, dole zai ɗanɗani azaba wacce ta linka wacce kake ciki a yanzu, ina maka fatan Allah ya azurtaka da lafiya dawwamanmiya wacce zaka amfanin masoya da maƙiyanka da ita." Da waɗanan kalaman tai masarar dakatar da Fauzan wanda ke ƙoƙarin juyawa ya ga halinda mahaifiyarshi ke ciki. Da rarrafe Dattijuwar ta ƙarasa wajen Mommy, a hankali ta kwantar da ita ganin jikinta yai sanyi bata ko motsi, kallon Sulaima ta yi tare da faɗin, "Kawomin ruwa me sanyi." cikin hanzari ta tashi ta nufi ƙatuwar freezar wacce ke kafe a cikin ɗakin ta ɗauko ruwan gora tare da miƙawa Datrijuwar har lokacin bata daina kuka ba. Amsar ruwan ta yi tare da buɗewa ta zuba ahannunta ta dinga shafawa Mommy tare da tofa ma ta addu'a, sai da ta shafa ma ta sau uku a cikon na huɗunne Mommy ta ja ajiyar zuciya me ƙarfi sannan ta shiga buɗe idanhwanta da suka kaɗa sukai jajur ta na kallon Sulaima data ranƙwafo ta na leƙa fuskarta lokaci ɗaya ta na dariya me haɗe da kuka. Murya ƙasa-ƙasa Mommy ke faɗin. "Sulaima! Fauzan ɗina mutuwa zai yi ko? zan rasashi ko? bazai tashi daga wannan cutar ba ko? Sulaima ina son Fauzan ɗina bana so in rasa ɗaya daga cikinku, bazan iya jure rashinku ba, ina matuƙar ƙaunarku, dan Allah ki yi min addu'a ko zan samu sassauci daga yanda ni ke ji, Sulaima zuciyata ta kusa bugawa, ina jin ciwo me tsananai." "Haba Fatima, kar ki zamo me butulci akan abin da Allah ya riga ya zartar da faruwarsa tun farkon asali, cuta ba mutuwa bace, In sha Allah Fauzan zai samu lafiya zai tsaya da ƙafafuwanshi kamar yanda ya ke a baya, ki ƙara haƙuri kuma kici gaba da yi ma shiƙ addu'a In sha Allah ƙarshen wahalarshi ya zo." Dattijuwar tai magana ta na kallon Mommy cike da tausayawa, dama ita uwa babu wanda zai kai ta ƙaunar ɗanta, kuma aduk yanda ɗa ya ke fama da lalura zaka samu uwarshi na tare da shi kuma ta na son abinta a haka. Lallaɓa Mommy Dattijiwar ta yi da kalamai masu kwantar da hankali sannan suka kama ta ita da Sulaima suka fice da ita daga ɗaƙi. AGEGE Zazzaune muku akan tabarma kowa na ci abinci cike da raha irin wacce ake yi a gidanmu, amma ni nayi shiru ina kallon gefe ɗaya ina tunani, Mamace ke ƙoƙarin yimin magana idan ta ji shirun yai yawa sai ta ce, "Mubeenah tunanin mi kike yi haka, ki ci abincinki mana karya huce." amsa ma ta nike da "to". amma badan inajin abinci zai samu muhallin zama a cikina ba, maganganun Abbane ke ta maimaita kansu a cikin zuciya da kwanyata, ga wani irin tashin hankali da ke sake baibayeni gami da tsoro me tsanani. FLASS BACK Bayan dawowar Umma da ƴan mintuna Abba ya bita ɗaki tare da fito da Yaya Habiba da Yaya Sumayya. "Umma wajenki na zo zamuyi magana." Umma ta na wani yatsina gami da shan ƙamshi ta ce, "Ina jinka amma da banda magana akan kuɗina, dan wallahi Allah sisi bazan baka ba wannan karon, sana'a zan nema nima intsaya da ƙafafuwa." "Kash ke wallahi kina da matsala, yo Allah na tuba ana gamanar miliyoyin tsabar kudaɗe ke kuma kina magana akan wash ƴan canji, ai ina me tabbatar ma ki nan gaba kaɗan zamu zama shahararun masu kuɗi, wallahi sai mun girgiza Agege ke Legos ɗinma gaba ɗaya zamu jijjiga cikin kwana biyu rak." "Na shiga ukuna!!! Abba sata ka kidnapping ka fara da kake faɗin wannan maganar?". Umma tai magana ta na zaro ƙananun idanuwanta waje ta na jiran Abba ya bata amsa. "Daɗina da ke shashanci wallahi, ke kanki hakanan ya ke suluf babu komi cikinshi, in banda hauka da rashin tunani tayaya za ki yimin wannan maganar, to ki sa ni arziki kamar nayishi na gama ne, domin kuma kalma ɗaya ce rak ta rage infurta ta inzama cikakken me arziki." Sake waro idanuwa Umma tai, fuskarta cike da tsoron kalama Abba. "kai ni fa ban gane ba, mi kake nufi da kalma ɗaya rak ta rage ka zama me arziki, ni fa ka kulle min kai tamau da kalamanka." "Yanzu dai ki nutsu ki ji abin da zan gaya ma ki, sannan sai mu nemi mafita, yaronan Hashimu ne ya zo min da wa ta magana, da farko nima na shiga yanayin ruɗu, saboda lamarin me girma ne, kuma abin ya bani tsoro, amma dana natsu nai duba da ido basira sai naga ai faɗuwace ta zo daidai da zama, yo ba dole ince haka ba Umma tun da abin da nike nema ne ya zo kuma sai abin yazo min da alkairi, dama ba komi bane, a can wannan unguwar ya shahararrun masu kuɗi inda shi Hashime ke aiki ne suke neman ƴar aiki wacce zatai jinyar wani toyayye, abin da zai baki mamaki shine wai duk ƴan aikin da ake ɗaukowa da sunje sai suce basu iyawa saboda yanda marar lafiyar ke jin jiki, babu irin ƙasashen ƙetare wanda basu je ba amma abin yaƙi ci yaƙi cinyewa, ance ana buƙayar wacce zatai jinyarshi za'a biyata da maƙudan miliyoyin kuɗin, da yake kinsan yaronan Hashimu ɗan arziƙi ne shine kai tsaye ya amsa ma su da cewar waccan shashashar zata iya, to shine fa suka turoshi dan ya zo ya sanar da mu, sunce daga miiyan ɗaya har zuwa miliyan biyar zasu iya biyanmu indai Mubeena za ta jure tai wannan jinyar." "Sai naci abu ta kazan ubanta wallahi mudin ta sake ta kawo mana wargi, yo Allah na tuba wannan ai ba maganar da za'a tsaya neman amincewarta bace, wallahi ko bata amince ba mu mun amince ma ta, babu gudu babu ja da baya." Cewar Umma tare da tattare zanin jikinta ta fara taka rawa ta na sakin buɗa me babu ko kunya. "Dammm" gabana ya doka da tsananin ƙ arfi, yayinda jikina yai sanyi ƙalau wani irin baƙon yanayi na ji ya na baibaye ni yayinda ƙarar sautin buɗar Umma ta daki dodon kunnena, ƙanƙame jikina nai tare da takurewa na sake lafewa saman gadon ƙarfen Mama. Mama ce ta shigo tare da tada ni dan in fito tsakar gida insha iska saboda zafi, sai ta iskeni a wannan yanayin, fuskarta da alamun ƴar damuwa ta kamo ni muka fito waje inda su Yaya Habiba ke zaune, ko kallo ban ishesu ba bare su nuna sun san da zamana, haka ko gaida umma basuyiba saima ƙara volume ɗin kallon da suke yi cikin faskekiyar tsadaddiyar wayar Yaya Sumayya, Mama ce ta dinga jana da fira har na ɗan saki jikina muka dinga fira cike da nishaɗi dan kuwa ina son irin labaran da Mama ke bani idan muka zauna zaman fira, Yaya Habibace ta kira ni. "Mubeena zo kiga wani abu nan yo sauri ki gani karya wuce." Yanda tai maganar ne ya saka na kalli Mama ina jin daɗin yanda ƴan uwana suka kula ni, gyaɗa min kai tai alamar inje ingani, na muskuta zuwa inda suke na leƙo da kaina dan kallon abinda Yaya Habiba ke son nuna min, banyi kyakkyawan gani ba, dan kuwa Yaya Sumayya na saka play aka nuno wani waje shiru babu kowa sai wa ta kujera da ke lila kanta, sake ware manyan idamuwana nai dan in sake kallo da kyau, aiko na kallo abin da ya saka dukannin mutanen gida a tashin hankali, wani mummunan abu ne aka nuna ya taho da gudu kamar ze kamo ni, ban san lokacin da na saka ƙara me ƙarfi ba tare da miƙewa, sai nai tuntuɓe da ƙafar Yaya Habiba hakan ya bani damar faɗuwa ƙasa timm. Sallati Mama ta saki tare da tashi ta ƙaraso inda nike kwance dan ta tada ni, kai hannunta jikina ko second ɗaya bata ƙara ba tai saurin janyewa ta na riƙe hannun wanda ke ƙyarma, idanuwa ta fiddo waje ta na kallona ta na kallon hanuna, yayin da Abba da Umma suka firfito dan sunji ihuna sannan kuma sunji salatin Mama. "Mi zan gani haka, wannan wace irin rayuwace, mi yasa ƴan gidannan kuke da baƙin ciki, yanzu mabuɗin arziƙin nawa ce kuke so ku kashe dan iyayenku." Abba yai maganar tare da ƙarasawa inda Mama ke tsaye riƙe da hannunta, yayinda ni kuma nike yashe a ƙasa kamar gawa, duƙawa yai da niyyar taso da ni ya na sababi, amma abin mamaki sai hannunshi na sauka jikina kawai akaga anɗaga Abba sama, ba,a saukeshi a ko ina ba sai a jikin dangar ɗakin umma, cike da razana kowa ya shiga ja da baya-baya ganin lokaci daya na tashi tsaye ƙam, gashin cikina ya mimmiƙe, launin idona ya bace ɓat sai kalar shuɗiya me haske da ta bayyana, kafin suyi wani yunƙuri Mama na zube a ƙasa ta durkushe tare da faɗi cikin wa ta iriyar murya. "Takawarki lafiya sarauniya Zubudiyya ƴar sarki jikar sarki, haƙiƙa kogin Sumalai na ki ne, babu me iko da shi, takawarki lafiya sarauniyar sanyi da ƙanƙara, ƙasƙantaccen bawa na miƙo gaisuwa a gare ki." sai Mama ta duƙar da kai a ƙasa kamar ta na gaban sarki, daga haka bata sake magana ba kuma bata ɗago ba, wa ta irin razananniyar dariya na fara wacce tsananin iskar dariyar sai da shanyar da akai tsakar gidan ta dinga kaɗawa da ƙarfi, yayinda wani irin sanyi ya lulluɓe wajen irin me saka maƙyarƙata, abin da ya ƙara tsorata su Abba bai wuce yanda suka ga wasu irin ruwa masu haske da sheƙi na ɓullowa daga kasa ba a daidai saitin da nike a tsaye, sai da ruwan ya zo min har wajen ƙugu sannan ya tsaya da ɓulɓulowa, tafiya na fara yi a cikin ruwan ina shawagi cike da shauƙi, yayinda idanuwana suka shiga sauya launi a hankali, sai kuma ruwan ya fara ɓacewa amma har lokacin ban daina dariya ba amma kuma yanzu sautin yana raguwa a hankali kamar yanda ruwan ke ɓacewa. Ɓat sautin dariyar ya ɓace yayinda ruwan ya ƙafe sannan kuma a hankali yanayin ya dinga canzawa daga sanyi zuwa yanayinda muke ciki, faɗuwa nai a ƙasa tim ban sake motsiba. Mama ma ɓingirewa tai daga duƙiyar fadawan da tai, ta shiga sakin munsharin barci. YANZU ZA'A SOMA CAKWAKIYA, KU KASACNCE TARE DA NI DOMIN JIN YANDA ZA TA KAYA A CIKIN WANNAN LABARIN. KARKU MANTA LITTAFINAN NA KUƊI NE, KUMA MUN KUSA KAMMALA FREE PAGES GA WACCE TA SHIRYA BIYA GA ACCOUNT A ƘASA. 9136291920 MARYAM UMAR OPAY 500 ONLY👌 𝑣 NI CE TAKU MARYAM STAR ⭐⭐⭐ YAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS💪 🔥🔥ZAFIN WUTA🔥 Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥 LABARI ME CIKE DA BAN TAUSAYI,😩 MATSANANCIYAR DAMUWA,😭 KUNCIN CUZIYA,💔 SADAUKARWA,💌 ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘 WRITING BY MARYAM STAR ⭐⭐ YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR📒✍️ RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA🔥 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) Typing...📲 PAID BOOK 500 ONLY👌 SEASON TWO CHAPTER 25-30. بسم الله الرحمن الرحيم. Cike da tsoro Umma ta matso cikin sanɗa ta jijjiga Mama gami da kiran sunanta, amma Mama ba ta amsa ba kuma ba ta motsaba, shiko Abban tafe bango ya yi tare da silalewa ƙasa ya zauna ya na maida lumfashi gami da sharce gumi, Yaya Habiba ce ta nufi inda ya ke ta na ma shi sannu ganin yanda ya diririce duk ya tsure kamar wanda yai jinya. Da ƙyar Abba yai nasarar ƙwato kalmar "Ruwa." daga bakinshi, aiko da sauri Yaya Habiba ta ɗebo ma shi wanda ke cikin randa, tun da ya kafa kofin bai sauke ba sai da ya tabbatar da yanshe tas sannan ya aje tare da lumshe ido ya na sauraren yanda zuciyarshi ke bugawa da sauri-sauri. Umma ta tsorata ainun da abin da ya faru hakan ya saka ta haɗa kawunan su Yaya Sumayya tai ɗaki da su, acewarta wai karasu kwashi jangwam. Shima Abba lallaɓawa yai tare da rarrafawa ya shige ɗakin Umma harda kullo ƙofa, ni da Mama kuma aka barmu anan kamar kayan banza. A hankali na fara buɗe idanuwana da sukaimin nauyi, kaina ne ya sara da tsananin ƙarfi wanda hakan ya tilasta ni saurin rufe idanuwan nawa, ƙoƙarin tashi na fara yi zaune amma sai naji jikina kamar anyimin tsinannen duka, ko ina ciwo ya ke min, daurewa nai na tashi ina cije baki cike da dauriya dan sosai kaina ke barazanar tarwatsewa, a hankali na buɗe idanuwa da sukai min tsananin nauyi na sauke su akan Mama da ke kwance,mamaki ne ya kama ni ganinta a kwance ta n barci gashi magrib ta kawo kai, cike da jarumta na matsa kusa da ita na shiga tashinta ganin irin kwanciyar da tai, buɗe idanuwanta tai tare da ƙoƙarin tashi, na lura itama jikinta sam babu ƙarfi, bayan

Chapter 2 of 5