Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥 LABARI ME CIKE DA BAN TAUSAYI,😩 MATSANANCIYAR DAMUWA,😭 KUNCIN CUZIYA,💔 SADAUKARWA,💌 ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘 WRITING BY MARYAM STAR ⭐⭐ YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR📒✍️ RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA🔥 PAID BOOK SEASON ONE Chapter 1-5 بسم الله الرحمن الرحيم. LEGOS NIGERIA UNGUWAR AGEGE Wani ƙwararaɓaɓɓen gida ne ginin ƙasa wanda ko arzikin shahen siminti bai samu ba, gida ne ƙarami sosai kuma marar tsayo dan dama waje za'a iya hango kaiwa da komowar mutanen gidan. Da gudu na fito daga cikin kurkukun gidanmu wa ni dattijo biye da ni hannunshi riƙe da zabgegiya bulala irinta dukan dawakai, gudu ni ke iyakar ƙarfina tare da ihun neman agaji dan saura ƙiris Dattijon ya kama ni damma ina zillewa. Shawo kwana yai hannu shi riƙe da jakar bakko, lokacin da ni ke ƙoƙarin bige shi insha kwanar nima, caraf na ji anriƙe hannuna da mugun ƙarfi, wa ta iriyar ƙara na saki tare da gantsarewa jin saukar duka a jikina, kafin in aje numfashi na sake jin saukar wa ta bulalar a bayana aiko na sake gantsarewa tare da kai gwuiwoyina ƙasa saboda yanda zafin bulalar ya ratsani, rufe ni yai da duka babu ƙaƙƙautawa yayinda har lokacin ba'asakarmin hannuna ba, birgima ni ke a ƙasa ina bayarda haƙuri tare da neman agajin jama'a amma babu wanda ya kula ta kaina. Sai da wannan dattijon yai min lis yanda ko hannuna ba na iya ɗagawa saboda tsabar yanda na daku sannan ya rabu da ni, wannan matashin kuma wanda ya riƙe hannuna bai sake ni ba har aka gama dukana, bayan dattijon ya juya ya na sababi kamar ze haɗe harshenshi saboda masifa ya koma ya shige cikin gida ba tare da ya kula da ko hijabi babu a jikina ba, daga ni sai doguwar riga irinta shan iska wacce duk ta jeme ta ji jiki, kaina ko atziƙin ɗan kwali babu sai baƙin sisilkan gashina da ya sauka har tsakiyar bayana, sanadiyar burkiɗa da nai duk ƙasa ta cika min gashi da jiki. Cike da raɗaɗin zuciya na tashi ina karkaɗe jikina har lokacin ban daina kuka ba kuma hannuna na riƙe da na wannan matashin. Baice da ni komi ba ya ja hannuna ina turjewa amma bai tsaya ba sai da ya sada ni da cikin gidanmu, a gaban wannan dattijon wanda ya yi min duka ya sake ni tare da komawa gefe inda wa ta farar matashiyar ma ta ke zaune ta yi tagumi hannu biyu. "Mama barka da wuni, munsame ku lafiya." Matashin ya katse ta daga tunanin da ta ke. "Lafiya lau Hashim fatan ka dawo lafiya ya hanya ?". "lafiya lau Alhamdulillah, ga wannan." Yai maganar ya na miƙo ma ta bakkon hannunshi. Cikin sassauta fuska ta amshi ledar tare binshi da addu'a. Amsawa yai tare da tashi ya koma wajen wannan dattijon shima ya gaida shi tare da zaro kuɗaɗe daga cikin aljihunshi ya ba shi tare da faɗin. "Abba ga wannan babu yawa anyi cefane, kuma idan andawo daga sallah idan baku komi ina son muɗan tattauna." "Ah bakomi Hashimu yaron albarka, ina gaya maka kaf gidannan babu me hankalinka ubangiji Allah ya biyaka da gidan aljanna." Ya faɗa tare da zuran kuɗin a aljihun rigarshi. Kallo Hashim yai tare da faɗin. "Mubeenah ki tashi ki yi alwala lokacin sallah ya gabato." Cikeda masifa Abba yai caram ya ce. "Yauwa Hashimu gara da Allah ya kawoka a daidai wannan lokacin, wallahi na gaji da halin wannan yarinyar, na gaji da nunamin ita yanzu ta kangare ta balage, kullum cikin janyomin hasifa da tashin hankali ta ke, ace yarinya rai ɗaya amma ta addabi rayuwata ta hana ni sakat, banda damar gindaya doka a gidana sai wannan masifatattar ta nuna ban isa da ita ba, to na gaji wallahi ta kaini ƙarshe na ƙure da bango, kodai ta nemi aiki inda za ta dinga ciyar da kanta ko kuma ta fito da mijin aure in aurar da ita in huta, Allah yana gani na gaji da riƙon wannan yarinyar." Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Hashim ya sauke, a cikin zuciyarshi ya na karanto A'uziyya jin irin kalaman da Abba ya ke jifar ƴar cikinashi kamar ba shi ya tsugunna ya kawo ta duniyar ba. Fice wa sukai daga gidan zuwa masallacin da ke cikin kayi don gabatar da Sallar La'asar. Mama ce ta tashi daga inda ta ke zaune ta nufi Mubeenah ta ɗago ta tare da kama hannunta suka shiga cikin wani ɗaki me ƴar ƙaramar ƙofa, akan wa ta jemammiyar katifa ta zaunar da ita, itama ta zauna tare da kama hannun Mubeena cikin na ta, cikin nuna damuwa ta ce. "Mubeenah! tabbas Abbanku baya kyauta, sam abubuwanda ya ke miki ba su dace ba, musamman zafafan kalaman da ya ke yawan jifanki da su masu kama da ZAFIN WUTA saboda muninsu, bazan ja da baya ba wajen sake jadadda ma ki cewa ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi a yanzu, komi zai wuce kamar ba'aiba wuya ko ƙunci basa taɓa dawwama, bayan wuya sai daɗi, kicigaba da haƙuri da ƙaddararki, jarabawace Allah ya ke jarabtar ki da ita, idan kika jure nan gaba zakiyi alfahari da hakan, tabbas Ubangiji ya na son ki tunda har ya jarabce ki da rayuwa me cike da tarin ƙalubale gami da tukitattun al'amurra, ki ci gaba da yin addu'a akan Allah ya zaɓa ma ki abin da ya ke alkairi a gare ki, da yardar Allah kina tare da nasara." Zafaffan hawaye ne suke ambaliya akan fuskata, yayinda nike tunanin shi har tsawon wane lokaci zan ɗauka ina fuskantar ƙalubalen rayuwa, har zuwa yaushe Allah zai dube ni ya sauƙaƙamin lamurrana kamar sauran mutane, ina so inyi farin ciki kamar kowa, ina so inzama kamar sauran mata sa'annina waɗanɗa ke rayuwa cike da farin ciki. Shafa bayana Mama ta ke alamar rarrashi, a zuciyarta ta na matuƙar tausayamin da irin rayuwar da na tsinci kaina. Mun ɗauki lokaci a hakan gani da Mama tai lokacin Sallah na ƙurewa ya saka ta lallaɓa ni muka fice a tare dan gabatar da Sallah akan lokaci, da kanta ta zubamin ruwa a ƙaramar butar da ita kaɗai ta rage mana a gidan, kamar talauci a kanmu ya ƙare, kullum ina Allah wadai da irin hallayar Abba ta mamaƙo da bin diddigi, Abba ya kasance cikin irin mutanenan masu hannun ƴan dambe, ga son banza muddin zai ƙyalla ido ya hangi mutum da ɗan maiƙo ba shakka sai yasan yanda yai wajen haɗa alaƙa da shi ta yanda zai yagi rabonsa. Shiga banɗakinmu wanda ya kasance ɗan ƙuƙut, sam baya da faɗi sai tsawo shima ba canba, raɓewa naj gefe na malala ruwa a ƙasa sannan na biya buƙatata na fito, alwala na gabatar cikin nutsuwa tare da godewa Allah da ya yo ni cikin hasken musulunci, yanda ruwan alwata ke bin muguji ya na gudana haka damuwar da ta cunkushemin zuciya ke kwaranyewa saboda ƙarfafa iymani na da nai a lokacin da nike alwala dan ganawa da mahaliccina. ZAFIN WUTA LITTAFIN KUƊI NE AKAN NAIRA 500 KACAL. TA KU HAR KULLUM MARYAM STAR. 🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥 LABARI ME CIKE DA BAN TAUSAYI,😩 MATSANANCIYAR DAMUWA,😭 KUNCIN CUZIYA,💔 SADAUKARWA,💌 ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘 WRITING BY MARYAM STAR ⭐⭐ YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR📒✍️ RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA🔥 PAID BOOK Season two Chapter 5-10 Bayan na kammala alwalar na yi addu'a kamar yanda manzo ya koyar, sannan na tashi na zubawa Mama ruwa na kai ma ta butar bakin ƙofar bayan gida na juya na wuce ɗan tsukakken ɗakina me kama da gidan Tantabaru, yamusashe abin Sallah na shimfiɗa sannan na janyo daguwar linkakkiyar hijabina wacce ta ke a tsarkake fes sai zuba ƙamshin turare ɗan ɗure ta ke, zura hijabin nai tare da kabbara Sallah na fuskanci Mahaliccina cike da ƙanƙan da kai, wani irin rauni ne ya ziyarce ni lokacinda gaɓoɓin jikina suka taimaka mani wajen yin Sujjada ina ganawa da Ubangijina, addu'a nike jerowa cike da fata da yaƙinin Allah zai kalle ni ya amsamin roƙona. Bayan na sallame Sallar nai tazbihi gami da azkar wanda Manzonmu ya koyar, na jingina da bangon ɗakin ina tunanon irin ƙalubalen da ke baibaye da rayuwata tun tasowata har zuwa yanzu, ko a labaran hausa da nike bibiya ban taɓa cin karo da makamanci labari wanda yai shige da nawu ba, kullum cikin fuskantar sabon babin ƙalubale da littafin ƙaddarata ke buɗe min nike, sam bansan farin ciki ba a rayuwata, abu ɗaya na sa ni shine, tarin ƙalubale da wahalhalun rayuwa. Ina a zaune ina tunanin yanda rayuwa ke gara ni kamar kwallon ƙafa na jiyo maganar Abba tun daga waje, Abba irin mutanen nan ne masu hayaniya waɗanda ba'a sirri da su, idan ya na magana muryarshi na fitowa da ƙarfi sosai, tumbama ace faɗa ya ke wayyo Allah wallahi inada tabbacin har masu wucewa a bakin hanya su na jiyo amon sautinshi, kafin in ankare na ji Sallamarsu a cikin gida shi da Hashim, runtse idanuwana na yi da ƙarfi jikina yahau tsuma kamar yanda nike tsintar kaina aduk lokacinda Abba zai shigo gida, ina jingina shigowarshi da tashin hankalina saboda da zarar ya sako ƙafarshi ya ke fara ƙirƙirar abin da zai saka ya kira ni ya yi min faɗa wa ta ranama harda duka. Zagi, gori, cin mutunci sune abubuwanda ke maimaita kansu a bakin Abba akaina, nakan cintsi kaina a cikin wasiwasi lokuta dadama idan nai Abba ya jefe ni da mummunar kalma, zuciyata na raya ma ni cewa ba shine wanda yai silar zuwana duniya ba, musamman idan na natsu ina tunani akan yanda ya ke ina nakasa ina naka aje da Sumayya da Habiba, Sumayya da Habiba yayena amma ba uwarmu ɗaya ba, Sumayya Mamace wacce ta haifeta ita kuma Habiba ɗiyar Umma ce abokiyar zaman Mama wacce ayanzu ta tafi da Habiba da Sumayya ganin gida acan Katsina. "Mubeena! Mubeenah!! ke Mubeena wannan wane irin iskanci da raini ne ace kina ji na sai faman kwaɗa kira nike amma kiyimin banza saboda ke ba yarinyar arziƙi ba ce, idan kika bari daƙiƙa biyu ta shuɗe ba tare da kin fito ba Wallahil'azim na iske ki a ɗakinan sai jikinki ya gaya ma ki." Tsulum na fito kamar wacce aka hankaɗo na isa gabanshi tare da duƙawa na ce "Dan Allah ka yi haƙuri Abba wallahi Sallah na idasa, kafin in kwashe abin Sallar ne ka kira ni." "Mtswwwww aikin banza da wofi, da anyi magana ki kama sunne kai ke ala dole ta Allah, ki buɗe kunenki da kyau ki ji abin da zan gaya ma ki, Allah ya so ki yayanku ya ceceki daga hukuncin da na zartar a kanki, ya tsaya tsayin daka ya nemo ma ki aiki a gidan wasu manyan mutane shahararrun attajirai waɗanda kowa ya san da zamansu a Legos ke harma da sauran ƙasashe da garuruwa, idan kika natsu kika yi aiki me kyau to ba shakka mun warke daga wannan addababen talaucin, idan kuma bakiyi abin da ya dace ba har suka gaji suka koroki kamar yanda akai ma ki a gidan Alhaji Ɗan Gaske to babu makawa zaɓi biyu ne ya rage ma ki, kodai ki auri Samual abokina ko kuma ki fita salin alin kibarmin gidana dan bazan iya ci gaba da riƙe ki ba tunda na lura ke me farar ƙafa ce, daga lokacinda Allah ya haɗa ni da ke na fara fuskantar matsaloli a cikin rayuwata." Ɗif na ji jina ya ɗauke na tsawon lokaci, kwanyata ta shiga maimaita min maganganun Abba da ya ce ni me farar ƙafa ce, daga lokacinda Allah ya haɗa shi da ni ya ke fuskantar matsaloli. "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, Hasbunallahu wa ni'imalwalkil, Allahumma ajirni fi musubati, Abba maimaita min maganarka dan Allah ko zan daina kokonto akan abin da zuciyata ke raya min, Abba da gaske ne abin da kake faɗi Allah haɗaka da ni yai, kenan ba kaine ka haifeni ba ko, dan girman zatin Allah ka amsa min." Tsit Abba yai ya na jin babu daɗi akan yanda na fassara maganarsa, harga Allah ba haka ya ke nufi ba, bai zata hankalina zai kai ga waɗannan kalaman da suka suɓuce ma shi ba, kafin yasan abin yi muka jiyo muryar Umma da ta shigo yanzu ita da su Habiba ta na faɗin. "Yo Allah na tuba Mubeena miye banbancinki da tsintacciya, ai wallahi baki da maraba da waɗanda ake kaiwa gidan marayu waɗanda ake yasarwa a kan kwalta, akaɗa a raya Abban dai shine ubanki wanda za ki yi taƙama da alfahari da shi, domin kuwa ya yi ma ki sutura tunda ya kasance uba agare ki." Saurin katse zancen Mama ta yi gudun abin da kan iya zuwa ya dawo idan aka tsawaita zancen. "A,ah Umman yarah kece tafe da la'asar sakaliya, lalle marhaban da isowa, Biba Sumayya ku shigo daga ciki manah kun toge a bakin ƙofa kamar wasu baƙi." Taɓe wawakeken bakinta Umma tai tare da jifar Mama da wani banzan kallo sannan ta cire yalolon mayafin cikinta ta sagaleshi a igiyar shanya sannan ta turo ɗan kwalinta gaba ta na faɗin. "Wallahi ko Zainabu kinganni nan yanzu nai ra'ayin isowa, kuma babu wanda ya isa ya mayar da ni, ya muka same ku?." Cikin rashin jin daɗin yanda Umma ke gwasaleta idan tai ma ta magana ta ce. "Muna lafiya lau Alhamdulillahi." "A,ah kaga uwar gida me Capacity, Hajiya Halima ikon Allah, anbuga da ke ambarki maƙiyanki fadawanki, ke ce ɗaya rak amintaciyya a zuciyar Ibrahima, yo in banda ƙaddara da jaraba irin tawa mi na gano a wajen sauran mata da na nace akansu harda fa ƙaro ma ki kishiya, oh ni Iroro jikan Me ƙosai, In sha Allah daga Zainabu na kulle bazan sake yo maki kishiyaba da yardar Allah." Abba yai maganar ya na zuro kanshi ya na leƙa cikin jakar Umma wacce ya ke hango walƙiyar ƴan dubu-dubu sababbi dal, kamar wuyanshi zai ɓalle saboda leƙe. Ita kuwa Umma sai wani fari ta ke da idanuwa tare da ƙara buɗe bakin jakar dan Abba ya samu damar ganin kuɗin da kyau. Cikin rashin jin daɗin abin da Umma ta yi wa Mama ta tashi tare da jan hannun Mubeena da ke duƙe cikin mawuyacin hali ta nufi ɗakinta da ita. Habiba da Sumayya ne suka shigo su na yatsine fuska a fizge suka gaisarda Abba, cike da fara'a ya amsa ya na musu sannu da hanya. "Mama bazan iya ci gaba da jurar waɗanan munanan kalaman daga bakin Abba ba, Mama ki tausayawa halinda nike ciki ki faɗamin wacece ni? shin dagaske Abba shine wanda ya haifeni, ko kuma ni ɗin ba ƴarsa ba ce, miyyasa ya ke banbanta ni da Yaya Babiba da Yaya Sumayya?." Nai maganar ina me tsareta da rinannun idanuwa waɗanda launonsu ya koma jah saboda kuka, ji nike gaba ɗaya rayuwar ta ficemin, duniyar tai min zafi, banajin daɗin komi, ga zafin zuciya ga zafin dukanda Abba ya yi min. PAID BOOK NE AKAN 500 ONLY👌 TA KU HAR KULLUM MARYAM STAR ⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪 🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥 LABARI ME CIKE DA BAN TAUSAYI,😩 MATSANANCIYAR DAMUWA,😭 KUNCIN CUZIYA,💔 SADAUKARWA,💌 ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘 WRITING BY MARYAM STAR ⭐⭐ YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR📒✍️ RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA🔥 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) Typing...📲 PAID BOOK 500 ONLY👌 Season two Chapter 10-15 Gudu ya ke shararawa a cikin dajin da babu komi sai kukan tsuntsaye da halittu masu firgitarwa, bai tsaya a ko ina ba sai nesa kaɗan da wajen wani kogon dutse, kashe motar yai tare da fito a firgice ya tsaya daidai wani waje inda aka aje wasu tsofaffin ƙorai, cikin rawar jiki ya cire kayan jikinshi tas yai tsirara haihuwar uwarshi sannan ya jefarda kayan a saman ƙoran ya rufe idanuwanshi tare da juyawa ya na karanto wasu damatsilan tsafi ya isa gaban kogon, a zahiri kogon baida wa ta ƙofa sai wa ta ƴar huda ƴar ƙarama wacce wani bakin hayaƙi ke fitowa, ci gaba da karanto damatsalan yai har wannan baƙin hayaƙin ya baibaiye inda ya ke tsaye, ɓat ya bace daga wajen bai samu kanshi ba sai a gaban wani shirgegen baƙin mutum me tsananin muni wanda ya ke tsirara haihuwar uwarshi babu ko ƙyalle a jikinshi sai wani jan abu da ya naɗe al'aurarshi da ita, a hankali matashin ya fara ruɗe idanuwanshi bayan jin saukar wani ruwa me yauƙi akan jikinsa, buɗe idonshi yai tare da yunƙurawa cikin zafin nama yai Sujjada tare da kirari ga wannan ƙaton zindiƙin bokan. Wa ta arniyar dariyace ta cika kogon wanda ke zagaye da abubuwan ban tsoro iri daban-daban, bayan ɗaukewar sautin dariyar matashin ya ɗago tare da sharce guminda ke tsatstsafo ma shi sannan ya maida hankalinshi akan bokan. "Kamar dai yanda aka saba sadaukarwar wannan karonma tayi kyau, Zuka ya ji daɗin jininda aka bashi yanzu a shirye ya ke dan ganin ya biya maka dukkanin buƙatunka." Boka yai maganar bakinshi na amayarda tururin baƙin hayaki harda tartsatsin wuta a lokacinda ya ke magana. "Ina godiya Boka uban bokaye, hatsabibi uban hatsabibai, Mutum uban Aljannu, zaka dawwama kana juya duniya da mutanen da ke cikinta ta ƙarfin ikon ka." Wani mumunan murmushi Bokan ya saki wanda ya sake bayyana munin halittar fuskarshi wacce sam babu kyan gani. "Kana tare da sa'a da nasara saboda biyayyarka agaremu, tabbas akwai shahara a tare da kai burukanka da yawa zasu cika saboda ƙarfin iymanin da ka yi da mu." Nan matashi ya zube tare da kwararo godiya sannan ya shiga lissafo abubuwanda ya kawoshi, bayan ya gama jawabinshi Bokan ya ɗaga hannunshi sama tare da karanto wasu kalmomi, nan take hanun ya shiga buɗewa har wani dunƙulallen abu ya bayyana, ɗayan hanun nashi me kama da icce ya ɗaga tare da shafa abinda ya bayyana, nan take ya shiga warwarewa yana buɗewa gamida bada tsawo da faɗi, wani madubine ya bayyana. Mutum ne a kwance kamar gawa, babu abin da ke motsi a jikinshi, babu ko tufafin kirki a jikinshi sai wani farin gyalle da aka lulluɓe iya al'aurarshi, jikinshi kamar babu tsoka saboda tsabar yanda ƙasusuwa suka firfito miraran, fatar jikinshima duk ta taƙune ta yamushe kamar tsoho, wani abin mamaki kuma gashin kanshi na nan kwance luf kamar baƙi ƙirin kamar na larabawa ko indiyawa, wani tururin hayaƙi ne ke fitowa daga ƙofofin gargasar da ke jikinshi. Wata iriyar dariyace matashin ya kece da ita tare da faɗin. "Fauzan Shareef Abdallah kaga abin da taurin kai da binciken ƙwaƙwaf ya janyo maka ko, ka ga abin da nike mama gargaɗi akashi ko, indai ZAFIN WUTAR tsafi ne yanzu aka fara, sai na ƙone gangar jiki da ruhinka da ZAFIN WUTA wannan itace makomar da ka zaɓawa kanka, duk wannan iko da dukiyar da kake taƙama da ita sai na yi sanadiyyar ƙarewarsu, sai rayuwarka ta ɗaiɗaice ta wulaƙanta, sai na maidaka abin tausayi a cikin mutane, dole ne in nuna maka nafika tantiranci da hatsabibanci." Cike da mugunta ya kalli Bokan bayan ya gama magana a fusace ya ce. "Ya shugabana Boka uban Bokaye ina so ayiwa Aljani Zuka albishirin jinin jinjirin da ƙanwata zata haifa, ina so ya sake ninka azabar da yakewa wannan kafaffen Fauzan ɗin azaba me tsanani ta yanda hatta makusantanshi zasu ji tsoron kusantarshi, so nike asa wuta ta dinga ƙona gangar jiki da ruhinshi, ina so hannu ya gagara taɓa jikinshi, ina nufin a ƙone duk wanda zai taɓa shi, sannan ina so a hana gangar jikinshi saurin ƙonewa saboda banso ya mutu da wuri, ina so ya ɗanɗani uƙuba da azaba me raɗaɗi." Dariya Boka ya kece da ita tare da dunƙule madubin sannan ya shafa, nan take ya ɓace hannunshi ya dawo daidai, har zuwa lokacin be daina mumunar dariyarba wacce ke kama da saukar aradu saboda tsananin munin muryarsa. TAKU HAR KULLUM MARYAM STAR ⭐⭐⭐ Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 I'm

Chapter 1 of 5