zafiba, amma agun pappinta kam bazata iya juraba, Hakan taketa zancen zuci harta isa gida tafaɗa babuko sallama gabaki ɗaya a hargitse take kamar wata zararriya... innawuro naganinta tataso cikin bala'i tana faɗar "ke dan ubanki nizaki wulaƙanta, tunyoshe nake jiranki amma kikayi zamanki seyanzu zaki dawomin kuma hannu rabbana, tukkunna ma ina aikenda namiki? Ko kina nufin ƙin tsayawa kikayi ki ƙarbo kika dawomin Hakan hannu rabbana? Taƙarasa zancen tana zuwa inda danejo take tsaye....Ita kuwa sema yanzu da innawuro ta tambe aikenta tatuna, dan ɗaukin Ganin pappinta yasa tayasarda saƙon.
Cikin tsawa taji saukar muryar innawuro tana faɗar "wai badake nake maganaba kinwani shareni sekace wata sa'ar uwarki....ɗib tayi tare da haɗiye sauran kalamanta Ganin yadda danejo taɗago azabure tana watsa mata waƴannan idanuwan nata dasuka gama komawa abin tsoro sabida ɓacin rai wanda yanayinta yamaidata aljanar ƙarfi dayaji. Tsorontane yashiga innawuro lokaci ɗaya Hakan yasa tazuba mata ido kawai tana kallonta domin inda ada ne dasedai taji saukar ruwan duka tako'ina ajikinta amma yanzu kam tana shakku...iskace tafara kaɗawa tayi baya da sumar kan danejo tana kaɗata sama, Hakan yaƙara ta azzara sauyawar halittarta daga mutum zuwa siffar aljanu...dasauri innawuro tanufi ɗakinta tareda maida ƙyauren tarufe gam tana faɗar "aikin banza wannan yariya ko dangin ibilisai ni wuro inaganin jarabawar duniya mlm yaɗauko mana jaraba dabe ɗauko uwar aljanar nanba daba abinda zesa tazame muna fitina kataɓa ta kuma wani bala'in yabiyo baya, Hakan innawuro keta mitarta ita kaɗai acikin ɗakinta.
Danejo kuwa nasu ɗakin tashiga tareda zubewa akan katifarta tana rushewa da matsanancin kuka metaɓa zuciya, sam takasa danne abin aranta
Wani irin ɗaci ke taso mata azuciya, tarasa ina zata saka kanta, taɗauki tsawon lokaci tana kukan kafin taji ana shafa lallausar sumar kanta....dasauri taɗago tana kallonshi cikin mamaki domin tasan dudduniya mutun ɗaya kemata Hakan kuma sam batayi tunanin ganinshi ba yanzu..aiko sukayi ido huɗu dashi yana sakar mata lallausan murmushi wanda yaƙara fitoda asalin kyawun fuskarshi ga dimple ɗinshi duka biyu sun lotsa abinda ke bala'in ɗaukar hankalinta gareshi kenan...dasauri tajuye fuskarta tana turo baki gaba kawai taƙara rushewa da matsanancin kuka.
"Ya salam shine abinda pappi yafurta ahankali yaname dafe kanshi, kafin yariƙo hannunta cikin sigar rarrashi yake faɗar"please my husnah stop crying mana, sata kigayamin miyasaki kuka, yafaɗa cikin Cool voice ɗinshi sak irinna yarima sameer domin basuda banbanci ko ƙwayar zarra ne tsakaninsu daga murya har kamanni na fuska da jiki har yanayi komai nasu iri ɗaya ne. Hakan yasa danejo keyiwa yarima sameer kallon pappinta. Shiru tayi taƙi Magana kusan minti ukku, kana tabuɗe baki cikin muryar kuka take faɗar "nikatafi bayan ɗazu ka wulaƙantani kakoreni daga wurinka dan kawai kana tareda wayancan mutanen shine yanzu zakazo min, haba pappi miyasa zakamin Hakan dan Allah? Karka manta fa Kaine ummana yayana kuma malamina idan kagujeni yazanyi? Tafaɗa tana ƙara sakin wani sabon kukan me tsima zuciyar mesauraro.
Tunda tafara magana yake kallonta tamkar yasamu tv aranshi yana ayyana Cewar ta haɗu da princes Sameer ne kenan duk yadda akayi domin duk faɗin Afirca shine kawai keda kama dashi wanda za'a iya gani ayi tinanin shine, bece mata komaiba harta gama zancenta taɗora da kuka..hannunta kawai yariƙa tareda hura mata iskar bakinshi a ido domin bayaso wani daga cikin gidan yazo yaji abinda suke magana akai, aiko suka ɓace bat kafin su bayyana bakin wani ƙaton teku, buɗe idonta tayi taga inda suke, amma batace komaiba kuma bataji tsoroba kasan cewar sun saba irin wannan tafiyar da pappi, kusan minti 15 suna ahakan kafin yajiyo gareta cikin tausasa harshe yace
"My husnah kitsaya kinutsu ki saurareni kinjiko..kai kawai taɗaga Mishi amma batace komaiba...Hakan yasa yaci gabada faɗar"kiyi haƙuri abisa korarda yarima sameer m habibullah yayi Miki, domin banine na korekiba yarima sameer ne, Shima kuma ba'ason ranshi yakorekiba sedan kasan cewarshi yatsani mata suraɓeshine da irin halayyar Ameer M habibullah yakeda Ita sam baze korekiba sabida Hakan kidena fishi da pappinki kinjiko ƙanwata, yaƙarsa zancen cikin kwantarda kai yadda zata fahimta....amma ina tun lokacinda yace bashi bane yakoreta ƙwaƙwalwarta tadena gane komai, tunani kawai take aranta to bashi bane waye? Waye takeda kama irinta pappinta? tayaya mutun biyu zasu kasance iri ɗaya? Kodai su ɗin twins ne? To koma twins ne aikamarsu tayi yawa kuma miyasa shi batasanshi ba se pappi kawai? Miyasa kuma bayason mace taraɓeshi? Miyasa ze koreta bayan ita batasan ba pappinta bane? Kuma tayaya ma zata yadda ba pappi bane? Hakama tayaya zataƙi yadda bayan pappinta betaɓa mata ƙarya ba...duk acikin ranta take jerawa kanta waƴannan tambayoyin da batada amsarsu, sedai abinda batasaniba afili take zancen zucin nata kuma koda azuci tayi pappinta ze iya sanin abinda take saƙawa....muryarshi ce takatse mata tunani inda yake fadar "duka zaki samu amsoshin wannan tambayoyin naki my husnah sedai bayanzuba dasannu Zaki fahimci komai, abu biyu saki sani ayanzu sune na ɗaya muba ƴan biyu bane hasalima bajinsinmu ɗaya ba inafatar kinsan Hakan, Sena biyu zaki bawa zuciyarki nutsuwa da bani bane kika gani ɗazu sabida zankaiki har inda yake kiganshi amma bazan bari yagankiba kin yadda? Yaƙarsa zancen yana kallonta...kai kawai ta iya ɗagawa amma takasa cewa komaiba sabida mamaki da al'ajabi. Sunjima aruwin yanata rarrashinta kafin yasamu zuciyarta taɗan nutsu yamaidata gida.
MASARAUTAR MAHAR
Sedare lis suka dawo garin MAHAR sedai agajiye liƙis suka dawo domin daga Adamawa ko ina basu tsayaba se masarautarsu, motar data ɗauko imam ce kawai tatsaya taraba ta ajiye shi kana suka ƙaraso..suna fitowa daga cikin motocin kowanne pert ɗinsu yanufa domin dare yayi sosai, koda yashigo general parlor gidansu bakowa kuma duka ankashe fitilun parlor, Hakan yasa ya haura kawai pert ɗinshi batareda yanemi mammi ba, yana shiga tun a perlor yafara fatali da kayan jikinshi harya shiga bedroom ɗin ƙarasa cirewa kawai yayi yafaɗa bathroom yasakarwa kanshi ruwa tareda lumshe kyawawan idanuwanshi, sedai arazane yabuɗe su jin saukar sweet voice ɗin danejo inda take fadar "kaine uwata, kaine ubana, kaine yayana, kaine ƙanena, kaine abokina, amma yau kaida kanka kake korana daga gareka,
"when you're coming back to me my everything.
Wani irin mugun faɗuwa gabanshi yayi yana ƙara ganin kyakkyawar fuskarta me ɗaukar hankali a ƙwayar idonshi, "hasbinallah "innalillahi wa'innailaihiraji'un wannan wacce irin yarinya ce ? Yafaɗa asaman lips ɗinshi kafin yayi sauri yayi wankan shaf'shaf yafito, kayan bacci shi kawai yazura taredayin addu'a yakwanta, sedai baccin yaƙaura cewa idonshi sam muryarta kawai yakeji tana mishi gizo idan kuma yarufe idonshi ita yake gani, yaɓata tsawon lokaci ahakan yarasa abinda yake mishi daɗi daƙyar bacci ɓarawo ya ɗauke shi, sedai ko minti 40 beyi dayin baccinba yafarka arazane yana salati, saka makon danejo dayariƙa gani acikin baccin shi tana kuka kamar ranta ze fita akan korar daya saka ayimata ɗazu, cikin wani irin yanayi yadafe kanshi yana maimaita....!
Book ɗin AL'AJABI Paid book ne akan 1k kacal zaki iya tura kuɗinki ta wannan account ɗin 👉2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA bank, kana kitura Shedar biyanki a wannan nomber 👉 07037092176 on whatsapp.
Autar alheri ✍️
🪐🐦🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦🔥🪐
🪐🐦🔥 *MASARAUTA*🐦🔥🪐
🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸
Dr Yasmeen Ahmad😚
Autar alheri ✍️
Al'ajabi, hummm
Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI.
ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃
Book 1
Page 19 & 20
"Yana maimaita innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yanajin gabanshi na tsananta faɗuwa, yajima zaune kafin yamiƙe yanufi bathroom yaɗauro alwala yafito yatada sallar nafila domin ayanzu kusanci da mahaliccinshi kawai yake buƙata yarigada yagama gasgata cewar gamo yayi, hakan yaraya wannan daren har aka kira asuba kana yafice zuwa masallacinsu dake cikin masarautar, yana fitowa yasamu yan uwanshi duka sun fito domin wannan al'adace agun ahalin wannan masarautar muddin kana cikin masarautar to doline da asuba kafito ahaɗu domin shiga masallaci, daga iyayen nasu maza har memartaba sarki habibullah dawazirinshi kuma ƙane agareshi, baba tsoho kenan, har galadima wanda yakasance shima ƙane ne agunsu, kuma dukansu sun manyanta, kowanne datashi zuri'ar,,,ahakan suka nufi masallacin dukkansu.
Bayan an idarda sallah kowa yafito ananne suka fara gaisawa da juna wato samarin gidan dakuma yayunsu domin memartaba da tawagar ƴan uwanshi tuni sunyi gaba. "Good morning yaya Naseer, cewar yarima sameer domin duk acikin yayunsu yafi ƙaunar yaya Naseer wanda baya iya shareshi kamar yadda yake share sauran. "A a morning my lovely bro yoshe agari? Naseer ɗin ya amsa yana rungumeshi. Bece komaiba yadda shima Naseer ɗin yasan bazece wani abinba, daga wannan gaisuwar, hakan duk suka gaisa da junansu kana kowa yanufi pert ɗinsu amma ameer da anwar pert ɗin mammi sukabi princes.
Bara nabaku ɗan bayani kaɗan daga cikin wannan ahalin yadda zaku fahimta.
Sarki habibullah yanada yara biyar kamar yadda kuka sani, Mansoor shine babba wato baba wanbai, yanada yara ukku Naseer, Abdul, kabeer, kuma kusan sune manyan yara agidan wato Abdul wanda suke kira yaya Abdul, sekuma yaya Naseer, da yaya kabeer, Muneer, shine kebinshi shine suke kira abbey, yanada yara ukku, Yarima Sameer, affan, Safnah, jabeer kuwa shisuke kira dady, yaronshi ɗaya Anwar, sekuma Mubarak, wanda suke kirada abba ciroma, yanada yara biyu, Ameer da Amerah, sekuma Autansu Abdullah, wanda sunanshi yaya Abdul yaci, shi bemada aure ayanzu hakan tun shekarun baya da matarshi tarasu beƙara aureba, hakanan yake zaunenshi, kuma bayama zama ƙasar yana US acan yake aikinshi, kuma shine suke kirada abban yarima ko abban princes domin tunda aka haifi yarima Sameer ahannunshi yataso shine yake kiranshi da yarima har Sunan yabishi to acan US basa cewa yarima sedai suce princes shine sunayen suka haɗe mishi...sarki habibullah kuwa matanshi ukku mebabban ɗaki itace uwar gida yaranta ukku, mansoor da jabeeer, se abdallah, se Fulani abu itako yaranta biyu mubarak da muneer, sa'annan Fulani huraira itako bata taɓa haihuwa ba,
Kunji yadda suke barana barku hakan zuwa gaba saku fahimci komai domin akwai waƴanda se gaba sunayensu zasu fito dakuma rawarda zasu taka aciki.
Suna isa general parlor mammi suka samu abbey zaune yana aikin a laptop ɗinshi, mammi kuma nagefenshi tana zuba mishi coffee, dukkansu rusunawa sukayi suna gaida iyayen nasu bayan sun amsa ne abbey yace "yaran abbey yagajiyar tafiya? Naga kunyi saurin dawowa kwana ɗaya duk nisan wurinnan. Murmushi Ameer yayi kana yace "wlh kuwa abbey domin akwai abubuwan damukeso muyine idan mundawo kafin bro yakoma US shiyasa muka dawo karmu ɓata lokaci acan.
Jinjina kai abbey yayi kana yace "shikenan badamuwa sedai babu zancen komawa US ayanzu domin memartaba yabada umurnin dukkanku kufitarda matan aure kafin yatafi sabida akwai muhimmin abu dayakeso aiwatarwa agareku kuma acikin wannan lokacin yakeso kuyi aure, yaƙarasa zancen yana kallon yanayinsu. Seyaga Anwar ne kawai yaɗago aɗan razane yana dubanshi sekuma Ameer dayace "aure kuma yanzu abbey? Amma shi gogan ko ɗagowa beyiba ga dukkan alamu bemasan akanme ake maganarba domin yalula wata duniyar, fuskar waccan aljanar kawai yake gani a idonshi hakama muryarta kemishi gizo acikin kunnenshi kuma cikin sautin kuka....da mamaki abbey ke kallonshi yana karantar yanayinshi, hakama yan uwan nashi, kusan minti 15 suna ahakan domin abbey zuba mishi ido yayi koda zece wani abu. Amma shiru, hakan yasa yataɓoshi yana faɗar"Muhammad lafiyarka kuwa? Yatambaya da mamaki kwance akan fuskarshi.
Mammi ma shitake kallo mamaki fall ranta..arazane yaɗago yana faɗar "na'am abbey. Dukkansu zaro ido sukayi yadda sukaga idonshi suyi luhu,luhu kamar wanda yasha kuka yagaji kokuma wanda beyi bacciba, abinka ga me manyan idanuwa.
Dukkansu shiru sukayi suna kallonshi kafin abbey yace "Muhammad Mike damunka? Bakada lafiya ne? Kakoma hakan? Damamaki shima yake kallon mahaifin nashi jin tambayar dayake mishi amma yakasa cewa komai, cikin ɗan tsawa abbey yace "ya inama magana kamin banza wai yoshe zaka ajiye wannan miskilin nakane Sameer? Humm toni bazan juri wannan sakarcinba kaji da kyau ina buƙatar kakawomin matar aure acikin wannan watan kafin ka koma US kuma umurni ne yanzu yajanye daga umurnin memartaba nawane kuma doline kowa yakawo idan ba hakanba toni zan nemawa mutun dakaina, yana gama faɗar hakan tamiƙe kawai yabar parlor sefamar faɗa yakeyi domin aganinshi duk laifin Abdullah ne dake biyewa shirmen sameer ɗin shiyasa yake yiwa mutanen renin hankali.
Shikuwa gabaki ɗaya mutuwar zaune yayi tunda yaji kalimar aure jinshi ya ɗauke, auren kawai kemishi amsa kuwa cikin kunne..mammi ma batace musu komaiba tamiƙe warta domin idan tatsaya zata tausaya musu ne awannan gaɓar kuwa basa buƙatar tausayi domin kuwa inba hakan aka musuba bazasuyi aurenba duka yaran gidan maza sunyi aure sune kawai sukaƙiyi dan sunga anzuba musu ido...mammi na ɗagawa suka Miƙe jiki asanyaye suka nufi pert ɗinshi kowannensu zuciyarshi na luguden tara,tara musamman princes da babu zancen aure yanzu atsarinshi.
A parlor suka zube cikin tashin hankalin da yakasa ɓoyuwa agaresu anwar yace "brother's yazamuyi da wannan zancen na abbey plesse aure fa, yafaɗa cikin alhini..."humm aini namarasa abin faɗa wlh dan banmasan ta ina zamu faraba, amma ni inaga Indai abbin yazo da hakan to kawai Nawwara zanfitar dama ita nakeso kawai banyi niyyar yin auren bane ayanzu, cewar ameer...dasauri duk suka kalleshi sedai kuma zancen ameer ya sanyaya ran anwar hakan yasa yasaki wani lallausan murmushi kawai yana shafa sumar kanshi. Da mamaki ameer yace "yadai bro? Ko kaima abin yazo maka dasauƙi ne? Humm kawai Anwar yace amma bebawa ameer amsaba, balle shi gogan dagabaki ɗaya baya cikin nutsuwarshi, fahimtar hakan yasa suka sakashi agaba da tambayar Mike damunshi amma yakasa cemusu komai, ahakan sukawini ranar a pert ɗinshi sallah kawai ke fidda su sedai yanayinda princes yake ciki yaƙara tada musu hankali hakan yasa suka yanke shawarar kiran abbanshi su sanar dashi.
DANEJO
Tunda abbey kemusu zancen aure har kawo firar dasukeyi tsakaninsu tana tsaye itada pappinta tana kallonsu cikin mugun mamaki ta kalli yarima sameer kuma ta kalli pappi, tabbas ba pappi bane amma ba wanda ze yadda da hakan idan ba yagansu hakan tadata gansuba. Seda pappi yaga tagamsu dacewar wanda tagani dai bashi bane kana yasake ɗauketa yamaidata rugarsu, shikuwa yayi tafiyarshi, amma hakan danejo takasa samun saƙat domin kuwa tunanin abubuwan datagani acikin wannan masarautar da pappi yakaita yahanata sukuni gakuma wannan dake Kamada pappi datake ganin kamar yana cikin tashin hankali kuma duk yadda taso tayiwa pappinta tambaya akan abubuwan data gani yaƙi bata damar hakan, wannan lamarin shine yamayarda danejo wata irin sukuku.
Su jauro
Tun lokacinda suka tare danejo suka shiga taitayinsu domin seda sukayi kusan mako ɗaya akwance suna jinyar abinda idonsu yagane musu sedai daga lokacinda suka tuna kalaman danejo agaresu inda take cewa duk wanda yaƙara aikata irin abinda suka mata agarin to sune dalaifi, suka ware, atake ciwo yaƙare, daganan suka koma sojojijon dole acikin rugarsu masu gadin ƴammata, Hakan yasa kowacce budurwa tasamu inci acikin rugar tasu.
MASARAUTAR MAHAR
yau dai wannan matar samu damar aiwatarda mummunan ƙudurinta akan sarki Habibullah domin tabawa wata baiwa maganin datakeson ayiwa sarkin anfani dashi tasaka acikin abincinda jekadiya zata kai masa, wannan hadimar kuwa bakowa bace face amin tacciyar hadimar me babban ɗaki wanda ita kaɗai jekadiya ta yadda da Ita kasan cewarta dattijuwa kamarsu, hadima hajjo kenan munafukar tsohowa me fuska biyu... lokacinda tazowa da matarda tasaka aikin da labarin ta aiwatarda saƙonta kuma har memartaba yaci baƙaramin Farin ciki tayiba, atake tafaɗa turakarta tareda ɗauko wani walki ta ɗaura kana tarufe idonta tana karanto wasu laziman tsafi kawai taɓace daga wurin segata ta bayyana acikin wannan ƙugurumin jejin memasifar tsoratarwa...tana sauka wurin ya ɗauke da wata mahau kaciyar dariya cikin ɗaga murya me dariyar ke faɗar "aikinki na kyau Fulanin sarki habibullah yanzu Seki zuba ido kiga yadda komai ze kasance. "Murmushi tayi cikinjin daɗi tace "godiya nakeyi yakai wannan dodo, sedai inada tambaya wadda nakeyima kullun koyanzu itace zanyi, akan babyn da gimbiya halima tahaifa shekarun baya, wai haryanzu baka gano muna wanda yaɗauke shiba dakuma inda yake? Tafaɗa cikin damuwa...ɗan shiru wurin yaɗauka nawani lokaci kafin taji saukar mummunar muryar dodo yana cewa "tabbas bamu gano komaiba gameda wannan baby domin bamuma samu tahanyar dazamu gano wani abinba atare dashi abu ɗaya nasani shine duk inda yake yana raye kuma acikin aminci da kariya ta musamman tabbas kinrigada kinyi sake Fulani dama tarigida tawuceki, yanzu sedai kishiryama yaƙarshi aduk lokacinda ze bayyana agareki domin tabbas dashirin yaƙarki zeshigo masarautar MAHAR, hhhhhh, hhhhhh,,hhhhh Hakan yariƙa ɓaɓɓaka wannan dariyar merazana duk wani meji alokacinda yakeyinta kafin kuma wurim yayi tsit kamar ba'abinda yafaru, Hakan itama Fulani taɓace kamar yadda tazo takoma turakarta sedai duk kwakwata nakasa gane wacce Fulani ce acikin matan sarki domin taƙi bada damar aga fuskarta.
US
Zaune yake acikin tangamemen office ɗinshi yasaka computer agaba yana aikinshi cikin mutsuwa da kamala, kyakkyawan dattijo mecikar haiba dakuma kamala fari tass kamar ka kwanta shi jini yafito, ahankali yake aikin yanayi yana kurɓar tea ɗin dake gefenshi, wayarshice tayi ƙara wanda yasakashi saurin dubawa domin wayar family shi daban take sabida be haɗa komai da ahalinshiba dudda baya taredasu amma yanajin sonsu harcikin ɓargon jikinshi, dubawa yayi yaga me kiran nashi afili ya furta "Ameer sekuma yayi picking yakara wayar akunne tareda sallama, "Abba inawuni. "Murmushi yayi wanda yaƙara Mishi kyau kana yace "lpy qalau Ameer sedai fa nan kam hantsine ya kuke y gidan ya memartaba? "Duka lpy qalau alhamdulillah Abba. "Masha allah, miyake faruwane Naji muryarka wani iri? Yajefawa Ameer tambayar..ajiyar zuciya Ameer yasauke kana yace "Wlh Abba akwai matsala ne, Anan yashiga bashi labarin yadda sukayi da abbey dakuma yanayinda princes keciki sedai yaƙara da Cewar amma yana Ganin ba wannan maganar ce tafi ɗagawa princes ɗin hankaliba domin tun kafin abbey yayi zancen suka ganshi wani iri....cikin tashin hankali Alhaji Abdallah yamiƙe tsaye yana faɗar "subhanallah inayake shi Sameer ɗin? "Yana bedroom Abba. "Okay bashi wayar yafaɗa aƙagare. Aiko Ameer yamiƙe zuwa bedroom ɗinshi koda yashiga yana zaune ya jingina kanshi dajikin bed sedai ba bacci yakeyiba, bece mishi komaiba yaƙara Mishi wayar akunne domin yasan koyayi magana ba tanka Mishi zeyiba... ɗagowa yayi yana hararar ameer ɗin kafin yayi wani motsin yaji saukar muryar abbanshi yana faɗar "Sameer Mike damunka? Yafaɗa hankalinshi duk atashe, jin muryar abbanshi ne yasa yariƙe wayar tareda lumshe kyawawan idanuwanshi, yana sauke ajiyar zuciya...Ganin Hakan yasa Ameer ficewa daga bedroom ɗin...shikuwa shiru yayi bece komaiba kusan minti 5 seda yaƙara jin muryar abban nashi yana faɗar"kanajina kuwa sameer waimike faruwane a,nan? Yaƙara jefo wata tambayar. Daƙyar ya haɗiye Yawun dasuka tokare maƙoshinsa kana yabuɗe baki daƙyar yace "Abba, sekuma yayi shiru. "Na'am yarona miyasameka? Naji muryarka Hakan? Mi akayima? Wani abunne yafaru? Duk ajere yake jefomishi tambayoyin. Yarima Sameer kam yakasa bashi amsa ko ɗaya daƙyar ya iya buɗe baki yace "Abba aljana gamo nayi Abba Wlh aljanace, yafaɗa yanajan wani irin numfashi wanda yakeji kamar zuciyarshi zata fasa ƙirjinshi ne tafito....ido Alhaji Abdallah yawaro cikin mugun tashin hankalin daya ƙara yimai dirar mikiya yace "aljana dai Sameer a'ina? Kai baradai ganinan zuwa zanshigo Nigeria nanda ƙarfe 6 nasafiyarku, daga Hakan ya yanke wayar tareda kwashe takashenshi ko kashe computer ɗin beyiba yabar office ɗin hankali amatuƙar tashe....!
END BOOK 1
kuma Anan free page yaƙare semun haɗu a book 2 wanda yakasance paid ne.
Humm yanzune za'afara asalin wasan acikin wannan book ɗin metaken👉 *AL'AJABIN MASAURATA*
Shin wacece HUSNAH? Miye alaƙarta da pappi?
Wacece wannan Fulanin dake neman mutane da sharri acikin masarautar MAHAR?
Shin ina labarin jinjirin da aka sace?
Miyasa aka kashe gimbiya halima?
Mi zuwan abban princes ze haifar?
Miyasa PAPPI kezuwama HUSNAH da kamannin yarima sameer?
Minene yatadawa HUSNAH hankali acikin masarautar MAHAR?
Shin minene asalin faruwa wannan abubuwan al'ajabi dake cikin masauratar MAHAR? Humm duk kobiyoni semun haɗu a page nagaba in sha Allah.
Book ɗin AL'AJABI Paid book ne akan 1k kacal 👌 zaki iya tura kuɗinki ta wannan account ɗin 👉2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA bank, kana kitura Shedar biyanki a wannan nomber 👉 07037092176 on whatsapp.
Autar alheri ✍️
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels