Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
suna kwasar gaisuwa sukabar pert ɗin...cikin tafiyarshi me ɗauke da ƙasaita yaƙarasa gun matar kyakkyawar mace masha allah, yana zuwa ya russuna agabanta tareda kawo fuskarshi dedetata ya manna mata kiss agoshi da gefen kumatunta kana ya rungumeta ajikinshi yana sauke ajiyar zuciya...wani ƙaya taccen murmushi taƙara saki tana shafa bayanshi ahankali kana tace "sannu dazuwa Muhammad sameer ka zo lpy? Tunda tafara magana yake lumshe ido yana sakin ajiyar zuciya kafin yasamu zarafin buɗe bakinshi daƙyar yace "lpy qalau mammi, ina Fatar nasameki lafiya. "Lpy qalau Muhammad kowa yana lafiya ƴan uwanka nacikin kaɗaicin rashinka ko ɗazu ameer da anwar dasukazo yin lunch se da sukayi zancen dawowarka nasan baka gaya musu zuwanka ba ko? Tatanbaya tana shafa kanshi...bece komaiba kusan minti 5 kafin yamiƙe kawai yanufi matakalar benen dake parlor cikin tafiyarshi me ɗauke da izzar mulkinshi...da kallon sha'awa mammi tabishi harya ɓacewa ganinta kafin tasauke ajiyar zuciya tanajin son ɗan nata harcikin ɓargon jikinta.....! Autar alheri ✍️ 🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥 🐦‍🔥🪐 *MASARAUTA*🪐🐦‍🔥 🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Dr Yasmeen Ahmad😚 Autar alheri ✍️ Al'ajabi, hummm Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI. ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃 Book 1 Page 7 & 8 "Ajiyar zuciya taƙara saukewa akaro na biyu tareda ɗauke idonta daga wurinda ya wuce kana tamiƙe zuwa wani bedroom dake nan ƙasa.....shikuwa yana hawa saman tun a parlor yafara cire tsadadden agogon hannunshi, yana shiga bedroom ɗin yaƙarasa cire kayan jikinshi gaba ɗaya kana yafaɗa bathroom wanka yayi tareda brush sa'annan ya ɗauro alwala yafito sanyeda rigar wanka, mirro yanufa tareda janyo kujera yazauna, hakan yariƙa ɗibar mayuka kala,kala yana shafawa ajikinshi kowanne pert danashi kamar wata mace, yaɓata kusan minti 15 awurin kafin yamiƙe yasaka kayanshi inda yasaka farar riga da farin wando 3kwata, kana yafeshe jikinshi dawani mayen turare me masifar daɗin shaƙa, seda yagama duk abinda yakeda buƙata kana yaɗauki wayoyinshi yanufi parlor cikin tafiyarshi me ɗauke da ƙasaita...yana fitowa parlor yayi arba da ameer zaune akan ɗaya daga cikin kujerun parlor yana danna wayarshi, yanajin motsin fitowar yarima Sameer yamiƙe dasauri yazo yarungumeshi yana faɗar "I miss you so much my bro saukar yoshe bako sanarwa? Se yanzu mammi takirani tana sanarmin zuwanka, yaƙarasa zancen yana ɗan sakinshi daga rungumar dayayi mishi...kallon Ameer yayi da shanyanyin idanuwanshi kana yaɗan shafa sajenshi batareda yace komaiba yariƙo hannun shi suka zauna, kusan minti 5 bece komaiba, ganin hakan yasa ameer cigaba dayi masa fira domin yasan tabbas bazeyi maganaba tunda har yazauna beyiba, sunjima ahakan ameer ne keta famar surutunshi, sedai idan yafaɗi wani abin yaɗago kawai ya kalleshi wani kuma yalumshe idonshi shine kawai amsar, suna nan zaune aka kira sallar la'asar hakan yasa duk suka Miƙe domin zuwa masallaci bayan ameer yayi alwala anan cikin bathroom ɗin dake parlor kana suka nufi masallacin. Maye balwa Tunda baffa yakai danejo dakinsu take kwance tana rawar ɗari domin lokaci ɗaya zazzaɓi mezafi yarufeta, wasu irin zafafan hawayene kezuba a idonta tana tunanin se yoshene zataji daɗin zaman gidansu kamar kowanne yaro? Mitayiwa innawuro datake tsagwamarta hakan? Miyasa bata yiwa yarta zainab Hakan se ita? Tabbas badan da tana yimata kallon mahaifiyaba data nuna mata ko ita wacece,,,Da wannan tunanin datakeyi bacci yayi awun gaba da ita. ba ita tafarka ba se kusan magarib koda tatashi tasamu leda ajiye agefenta dawasu kayan aciki, ɗauka tayi tabuɗe domin tayi tunanin kayantane da pappi yasiya mata sedai tana dubawa taga wasu daban irin wanda ake sedawa ako ina kamar irin alawar da ake rabo gun biki, ƙwallar idonta tashare tanajin son hamma Ishaq har cikin ranta domin kobata tambayaba tasan shine kawai ze yi mata wannan aiki,,,,miƙewa tayi taje tayi alwala tayi sallar magarib bayan ta idarne taji innawuro nadoka mata kira kamar zata tada gidan... miƙewa tayi ahankali tafito sabida jikinta dake mata mugun ciwo sakamakon dukan datasha agun innawuro. Tana fitowa taga innawuro na Banka mata harara kafin ta jeho mata wata koɗiɗɗiyar hamsin tace maza taje tasiyo mata ashana da maganin sauro. Faɗuwa gaban danejo yayi sabida aduniya ta tsani a turata wurin bala siyen wani abun gaya wurin danisa sosai kuma dare yayi, tanacan duniyar tunani taji saukar ruwan randa ajikinta hakan yasa numfashinta ɗaukewa naɗan lokaci kafin kuma tajashi da ƙarfi yadawo sabida mugun sanyin ruwan gaya kuma lokacin hunturu abinka ga rugar Fulani, hawayene suka cika idon danejo kafin taɗauki kuɗin jikinta na karkarwa tafice daga gidan kamar zata kifa, ga sanyin gari gana ruwan da innawuro ta watsa mata gakuma zazzafan zazzaɓin dake tareda ita duk se abin yataru ya haɗe mata wuri ɗaya. Tafiya kaɗan tayi tawuce gidansu tazo gunda babu mutane sosai taji sassanyar muryashi yana faɗar "HUSNAH ina zakije hakan? Dasauri tajiyo tayi ido huɗu da kyakkyawar fuskarshi yana kallonta da shanyanyin idanuwanshi, wani irin kukane taji yazo mata wanda yasakata nufarshi dasauri tarungumeshi tana rushewada matsanancin kukan...shiru yayi yana saurarenta hartayi me isarta batareda yadakatarda itaba, seda yaji ta tsagaita ne yaɗagota tareda share mata hawayenta kana yace "muje asiyo abinda aka aikeki, yafaɗa tareda riƙe hannunta...batace komaiba tabi bayanshi domin tasan koda maganar tayi baze tanka mataba, tafiya sukayi kaɗan segasu awani tangamemen shago me ɗaukeda tambarin Englan seety, shiga ciki sukayi kana yasiya mata wasu kayan maƙulashe waƴanda sukafi naɗazu kana yaɗauko mata wani kalar maganin sauro me kyau da faɗi shima kunnashi akeyi da ashana kamar namu, sedai ba irinshi bane amma azagaye yake kamar wancan sedai yafishi girma kuma shi kalarshi daban. Riƙo hannunta yayi suka dawo adede inda suka tsaya ɗazu yabata maganin sauron sauran kayan kuma yace taje zekai mata. Baki taɓare zatayi mishi taɓara yaɗaga mata hannu yana murmushi, hakan yasa dole tawuce tana waiwayenshi harta ɓacewa ganinshi....shikuwa be ɗaga ba seda yaga tashiga gida kana yajuya afusace yabar wurin kamar zetashi sama. Da sallama danejo tashigo gidan a tsorace sedai tasauke ajiyar zuciya yafi goma ganin baffa zaune tareda hamma Ishaq suna fira...cikin sauri taƙaraso tana miƙawa innawuro aikenta tareda takewa Zenu ƙafa ganin tana harararta,,,aiko tabuga ihu tana miƙewa tsaye...duk kallonta su baffa sukayi ana tambayar lafiya? Amma takasa cewa komai dudda cewar tanason faɗar abinda danejo tayi mata amma harshenta yaƙi ko motsawa. Ganin taƙi Magana ne yasa hamma Ishaq daka mata tsawa hakan yasa dole takoma tazauna tana fatan gari yawaye tahaɗa danejo da innarta domin tasan itadai bata isa ta tunkari danejo dasunsn rigimaba. Sunjima awajen zaune suna fira amma Banda danejo data shige dakinsu tunɗazu takuwa samu kayanta da pappi yasiya mata sunma rigata zuwa, murmushi tayi wanda yaƙara fotoda asalin kyawunta kana tabuɗe abinta tasomaci harta ƙoshi kana ta lunke sauran ta ajiye, tayi kwanciyar ta bayan tayi sallar isha...tana anan kwance takejin faɗan innawuro akan maganin sauron data siyo mata wai bata taɓa ganin irinshiba, setazo tamaida, seda baffa ya tsawatar mata tukkunna tayi shiru, shikuwa hamma Ishaq yayi ficewarshi daga gidan yana addu'ar Allah ya shirya innar tasu.....hakan suka ɓata lokaci suna fira kala tanajin maganarsu har bacci ya ɗauketa,,,can cikin dare bayan kowa yayi bacci dare yaraba sosai, tafara jiyo ihun mutun sama,sama cikin azaba ana neman ɗauki,,,azabure tamiƙe zaune ta kalli Zenu dake kwance tana baccinta hankali kwance, kana tasake kallon ƙofa jin wannan ihun na ƙaruwa, seda takasa kunne sosai kana nagano innawuro ce ke ihun mamaki tayi sosai amma bata fitaba tayi kwanciyata sedai aranta tana mamakin abinda innawuro take yiwa ihu cikin dare.....ita kuwa innawuro ihu takeyi tana neman ɗauki amma babu ko wanda yamotsa balle atemaketa har baffa dake kwance cikin ɗakin nata, gaya se dukanta akeyi tako ina duk an farfasa mata jiki kamar dukan ƙato goma bataga me dukan nataba kawai saukar bulolin takeji kamar za'a tsaga mata fata, amma sam bawanda yasan anayi domin duk ihun datakeyi bamejinta balle ba'asin temakonta......! Autar alheri ✍️ 🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥 🐦‍🔥🪐 *MASARAUTA*🪐🐦‍🔥 🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Dr Yasmeen Ahmad😚 Autar alheri ✍️ Al'ajabi, hummm Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI. ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃 Book 1 Page 9 & 10 "Seda tadaku iya dakuwa domin seda aka farfasa mata jiki tukkunna akabarta batareda tasan me duka nataba, hakan innawuro takwana awahalece daƙyar taga wayewar gari dudda sallar asuba yau kam bata samuba, dagari yawayene baffa yadawo daga masallaci yanufi ɗakinta da mamakin rashin ganinta yau a harabar gidan tunda sassafe. Sedai ayadda yaganta kwance magashiyan ya tabbatar mishi dacewar batada lpy ne. "wuro miyake damunki? Yatanbaya yana ɗan taɓa jikinta, sedai beji komaiba. Itako cikin ƙarfin hali tamiƙe zaune tana cije baki sedai duk yadda taso tagayawa baffa abinda yafaru da ita cikin dare kasawa tayi domin bakinta yayi mata nauyi, kuma duk inda yafashe ajikinta har yana fidda jini yanzu babushi yaɓace ɓat kamar befashe ba, sedai tsamin kawai dajikinta kemata. Daƙyar ta iya cewa baffa "bakomai jikinane kawai keciwo. "Ash'shakuwa tashi kiyi salla to bara nasamo maki magani cikin fadama, yana gama faɗar hakan yafice daga ɗakin...hakan ta yunƙura daƙyar taje tayi alwala tadawo zuciyarta fal fargabar abinda yafaru da ita a daren jiya. Yau dai hakan innawuro tawuni kamar wadda kawai yafashewa aciki hakan yasa danejo samun kanta agidan domin me takurata batada wata damar yin hakan yanzu sabida fargaba tagama nuƙurƙusar zuciyarta MASARAUTAR MAHAR tafiya sukeyi ahankali cikin izza da isa irinta ƴaƴan sarauta bayi nazubewa suna kwasar gaisuwa, Hakan suka nufi wani pert megirma da tsaruwa wanda yafi kowanne pert dake cikin masarautar girma da tsaruwa. Sarkin ƙofa dake tsaye suna fira dawani dogarine yahangosu tafe cikin sauri yace "ina zuwa lawwali barana sanarda zuwan yarima sameer agun memartaba kafin ya iso, yana gama faɗar hakan yajuya zuwa cikin gidan kamar zekifa domin yasan tabbas yarima sameer baze jira yayimasa isoba sabida bayason jira hasalima baya jiran kowashi sedai ajirashi, idan kuma ya shiga batareda yasanarda zuwanshiba yasan Fulani huraira baƙyaleshi zatayiba hakama Fulani abu, garama me babban ɗaki idan itace aciki bata damuwa. Yana zuwa yazube yana faɗar"Allah yaƙarama nasara da nisan kwana su yarima sameer ne keneman iso shigowa gun adilin sarki. Murmushi memartaba yasaki wanda yafito tun daga zuciyarshi, amma beyi maganaba se Fulani huraira ce tace "kace suna neman iso shida waye? "Yallaɓai ameer ne da anwar, yabata amsa cikin ladabi da ƙasƙantarda kai. Yatsina fuska tayi zatayi magana kenan suka shigo cikin parlor na memartaba, kowan'nensu da sallama ɗauke abakinshi. Amma tasu anwar kawai akeji dominshi gogan acikin ranshi yayi. Cikin ɓacin rai Fulani huraira tace "wannan wanne irin rashin ɗa'a ne? kunnemi iso bazaku jira abaku izinin shigowa ba zaku faɗowa mutane kamar wasu dawaki....Ɗaga kai kawai anwar yayi yakalleta amma bece komaiba,, yayinda Ameer yace "haba matar waike abin faɗa baya miki kaɗan? Yanzu miye laifinmu dazaki alaƙantamu da dawaki? Koda yake kekanki kinsan ingarman mazaje ne agabanki dole idonki surufe kice mana dawaki tunda munfi wannan tsohon mijin naki ƙarfi, yaƙarasa zancen nashi cikin tsokana, domin ameer duk afisu barkwanci. Baki tamere tana faɗar "wacece matar taka? Humm wlh gama tallabe dai kakeyi kayi ɗana aikin banza yara se shegen tsaurin idon masifa. Shidai memartaba bece musu komaiba domin ko lokacinda sarkin ƙofa yazo neman ison ya tabbatar ba Muhammad sameer ne yabuƙaci hakanba domin yasan halin kayanshi. Adan gajiye yamiƙe daga zaunen dayake yana sauraren shirmen Fulani huraira acewarshi, yaƙarasa gun kakan nashi tareda ranƙwafawa yarungumeshi yana sakin ajiyar zuciya domin aduk faɗin duniya agun mutun ukku kawai yake samun wannan nutsuwar idan yaraɓesu, abbanshi mammi sekuma memartaba.... murmushi memartaba yaƙara saki yana shafa bayanshi cikin kalama da dattako yake faɗar "lale da mutun ƙasar jajayen mutane laleda sarkin MAHAR nagobe lale da sanyin idaniyar Abdullah, ina farin cikin dawowarka mahaifarka adede wannan lokacin danake shirinyin murabus domin inaso nabawa duk wanda zuciyarka ta aminta dashi acikin iyayenka riƙon mulkin MAHAR kafin lokacinda shekarunka zasukai yabaka sarautarka domin kuwa tabbas mulkin garin MAHAR nakane YARIMA SAMEER M HABIBULLAH. Yaƙarasa zancen nashi da ɗan kirari wa jikan nashi. Murmushi duka su ameer sukayi amma Banda Fulani huraira dataji kalaman memartaba tamkar saukar ruwan darma azuciyarta. Shikuwa daƙyar iya buɗe bakinshi cikin wani irin cool voice yace "I miss you meran ƙarfe ina fatar nasami haske MAHAR cikin ƙoshin lafiya, yafaɗa abisa dole danson kaucewa wancan zancen da SARKI HABIBULLAH kemishi wanda sam baya buƙatar jinshi....sarai memartaba yaganoshi amma bece mishi komaiba domin yasan dama ba lallai ne yatanka mishiba sabida ba yau ne karo na farko daya fara yimishi irin wannan zancenba sedai betaɓa bashi amsa ko ɗaya ba akan kala manshi, dama koyanzu yayine domin yana kwaɗayin jin sassanyar muryar jikan nashi wanda yakeda tabbacin badan yayi wannan zancenba to har subar wurin baze taɓa buɗe bakinshi ba balle wata kalima tafito daga cikinshi. Sunjima awajen memartaba kafin suka bar pert ɗin suka nufi na sauran iyayen nasu, ko inna sunje daga ƙarshe suka yada zango agun umman ameer wato Hajiya Hafsah wadda suke kira da umma, mace me mutunci dasanin darajar ɗan Adam anan sukaci abici kuma basubar pert ɗinta ba seda zasuje masallaci bayan sun fito daga masallaci ne suka koma pert ɗin mammi mahaifiyar yarima sameer, suna shiga suka sameta zaune itada abbey suna fira, zubewa sukeyi aƙasa suna gaisarda iyayen nasu cikin girmamawa bayan sun amsa abbey ya kalli anwar yace "yaran abbey yanzu kam ganinku bazeyi wahalaba tunda ɗan uwanka yazo ko, yaƙarasa zancen yana kallon ameer. Murmushi duka sukayi kansu aƙasa domin abbey nada tsokana amma baya ɗaukar wargi kuma hukunci ɗaya yakeyi,, hakama magana ɗaya yakeyi akan komai, kuma bayason musu ko jayya, wannan shine tsarinshi..cikin girmamawa Ameer yace "habadai abbey ai mune zamu faɗi Hakan domin fa kullun Anan muke breakfast hakama lunch, da dinner amma Bama ganinka ko mammi? Yaƙarasa yaƙarsa zancen nashi yana tambayar mammi.. murmushi tayi mesauti kana tace "rabudashi yarona dankarku tuhumeshine shiyasa yarigaku.."eyee shigar musuma zakiyi? Humm yayi Miki kyau, Cewar abbey yana sakin murmushi..kafin ya Gyara zama kana yace "Muhammad tunda Allah yayi kazo to gobe idan Allah yakaimu seku shirya zuwa taraba domin kudubo aikin da abbanka keyi acan kafin kawuceko. Kanshi aƙasa ya amsa da "okey abbey, kamar bayaso kana yamiƙe zuwa pert ɗinshi, suma duk miƙewa sukayi sunabin bayanshi domin sunsan sameer bayason tafiyar mota amma kuma wannan dolice dubada umurnin abbey ne kuma aikin abbanshi ne, sedai sunsan zasusha tsaki kam kafin suje sudawo damma baya magana ne da sesun gajida mita😂.....! Autar alheri ✍️ 🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥 🐦‍🔥🪐 *MASARAUTA*🪐🐦‍🔥 🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Dr Yasmeen Ahmad😚 Autar alheri ✍️ Al'ajabi, hummm Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI. ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃 Book 1 Page 11 & 12 "Shidai yana isa parlor yafara cire kayan jikinshi domin hakan al'adarshi take kafin yaƙaraso bedroom kaya kaɗan ne zasu rage ajikinshi sedai duk wannan halayyar tashi baya cire boxes ɗinshi acikin bedroom harseya shiga wanka domin yarima sameer mutunne me matuƙar kunya dajin nauyi yanzu haka ko bindiga zaki ɗora akanshi bazecemiki ga yadda asalin halittarshi takeba domin bedamu dayasan yatakeba shidai muradi yayi wanka yawanke wurin kawai sabida atunaninshi kallon tsoraicinshi rashin kunyane...hakan yaƙarasa bedroom ɗin yana shiga kuwa yafaɗa wanka sabida duk agajiye yakejin kanshi....sukuwa su ameer a parlor suka zaune suna tattauna yadda tafiyarsu zata kasance agobe. MAYE BALWA danejo tunranarda innawuro tasha duka bata karabi takanta ba, sedai takan sakata aikin wahala wanda yafi ƙarfinta hakama bata bata'abincin daze wadaceta, kuma bata bari takwanta dawuri se salamainin dare, amma dai bata ƙara gigin dukantaba,,,sekuma abinda kebata mamaki akan danejon, bewuce yadda take ganin duk aikin data sakata bazata wuce minti ashirin ba ko talatin takama, wanda ko babbar mace ce zatayishi seta ɓata fiyeda awa biyar bata gamashiba sedai kuma dudda wannan mamakin datakeyi besa innawuro ta saurarawa danejo ba. Tafe take ita kaɗai acikin fadamar malam baffa tadawo daga kaiwa hamma Ishaq madarar data tatso mishi, tahango wasu samari tafe maƙotan rugarsu kuma sune suke shiga lambun baffa suna mishi sata, aiko tatunkaresu wanda su ɗinma ita suka tunkaro kasan cewar ta taɓa kamasu suna satar amma bata gayawa kowaba shiyasa yanzu sukeso suyi mata gargaɗi, shikuwa jauro sonta ne yakeyi amma dalalaci bawai danya auretaba, shiyasa yakeso yahaɗu da Ita a irin wannan wuraren dabakowa. Suna zuwa suka riski juna ahanya. "Hai danejo dama nemanki mukeyi aradun Allah kika sake kika gayawa wani kinganmu a lambunku semun karyaki a rugarnan, cewar sani cikin gargaɗi..sukuwa saura duka ido suka zuba mata suna kallon zallar baiwar kyau da tsarin halittar da Allah yayi mata. Wani banzan kallo danejo tayi musu kana tace "ai wlh baku isa kuyi mana satabq kuci bilis dama aranar nabarkune har muhadu domin bawai barinku zanyi kuci gaba da mana sataba, kuma dena tunanin wani zan gayawa dakaina zanyi muku hukunci Dede da laifinku yawwa. Taƙarasa zancen tana murguɗa baki cikin tsiwa darashin tsoro....aiko kamar jira sukeyi tayi magana ɗaya daga cikin samarin ya ɗauke ta tareda toshe mata baki suka yanki wani lungu da ita, tanata dukan bayanshi da wutsil niya da kafafunta amma yaƙi sauketa seda sukayi nisa sosai inda babu ko alamun mutun kana suka ajiyeta ita bayan sun kewayeta dukansu suna murmushi. Ɗagowa tayi takallesu babu alamun tsoro ko ɗar aranta wani irin kallo take jifansu dashi irin na ina tausaya muku ɗinnan...suko se zabga murmushi sukeyi kafin ɗaya daga cikinsu yace "badai muzakiyiwa rashin kunyaba humm aiko sekin gane bakida wayo aradu, nidamacan haushiki nakeji agarinnan kawai ina ɗaga miki ƙafa ne amma yau tunda kika shigo gonarmu sekin yabawa aya zaƙinta, dan Allah ku tuɓe mana ita wai mikuke jiranee? Yaƙarasa zancen cikin bada umurni...cikin sauri jauro yace "amma giɗaɗo kabari nafarayi domin nine nakesonta tunda jimawa aradu kaga idan nayi sekuyi kuma. "Shikenan naji kayi da sauri kafin wani yazo wurinnan. Aiko sunajin hakan biyu sukayi kanta domin su aiwatarda umurnin giɗaɗo na cire mata kaya kamar yadda yace, sedai basukaiga jikintaba wata irin iskar guguwa ta turnuƙe awurin wadda basusan mafarintaba kawai dai sunji tabazar dasu domin seda tayi sama dasu kana tawatsar can nesa, hakan yasa suka saki ihu atare jin sun garu dawani dutse...sekuma ta ɗauke kamar bata wanzu awurinba, hakan yabawa su giɗaɗo hango sani da gainako waƴanda guguwar tawatsar,,,,juyawa sukayi suna kallon danejo inda suka barta zaune sedai me, azaune suka ganta ko yanzu amma akan wata arniyar kujera me masifar ɗaukar hankali da sheƙi anyi mata wani matsiyacin ado na alfarma duk jikinta gwal ne da zinari ke tastas,niya sukeyi, itako se wani malalacin murmushi take jifansu dashi, taɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya.....ido kusa waro cikin mugun tashin hankali suna nunata da yatsa, kafin susamu zarafin yin magana idonsu yasauka akan kujerar datake zaune da kyau, ashe ba asalin kujera bace wani ƙaton shirgegen macijine yanaɗe tamkar kujera me hawa,hawa, danejo tazauna daga kanshi kuma yafasashi asama dashirin zara, yadda yafito tamkar kan kujerar sarki amma yana buɗar baki irinna baƙin kumurci, sekuma wasu biyu wanda basukai girmanshiba sun zagaye wurin kan nashi sunyiwa kan kujerar wani irin ado me ɗaukar hankali dajikinsu ta hanyar nannaɗewa adede kan babbansu hakan yaƙarawa kan kujerar girma da ɗaukar hankalin me kallonta tareda fiegitarwa. Daga ƙasanta kuwa wasu irin halittu ne wanda bazaka kirasu namun dawa ba kuma kai baka isa kace musu mutaneba dubada yanayin halittarsu, gasu tiƙa tiƙa tamkar samudawa sunzagaye kujerar DANEJO tamkar yadda fadawa keyiwa sarki a faɗa, se mazurai sukeyi suna kallonsu giɗaɗo da jauro wanda sukayi mutuwar tsaye tamkar mutun mutumi. Murmushi danejo taƙarasa saki akaro na ba adadi wanda ke masifar ƙara fitoda kyawunta me firgita ɗan Adam domin ba yadda za'ayi kayi ido huɗu da ita baka alaƙantata da aljanaba sabida tsananin kyawunta koda kuwa haɗe da fuska kaganta balle kuma tana jifanka da wannan shi'umin murmushin nata me tafiya da duk wata halitta me rayuwa. "Jauro, tafaɗa cikin sweet voice ɗinta me masifar daɗi tana kallon jauron... firgigit sukayi dukkansu kamar wanda suka suma, aka watsa musu ruwa suka dawo, se suka ƙara sauke idonsu akanta, amma abin mamaki kamar yadda suka ajiye ta zaune hakan take babu waƴannan halittun dasukagani yanzu atareda ita, tana zamanta tana murmushi...ai wani irin zabura sukayi kowanne yacika bujenshi da iska na shirin gudu sedai kuma sunkasa motsa koda ɗan yatsan sune ankafesu wuri ɗaya da shirin gudunsu sakamakon sakawa datayi aranta bataso sugudu shiyasa aka kafe matasu tun kafin tafurta abinda ke zuciyarta, anka cika umurnin zuciyar....murmushin jin daɗi tayi ganin an aiwatarda abinda takeso ta faɗa tun kafin ta faɗa ɗin kana tamiƙe tsaye tareda ɗaure fuskarta tamkar batasan minene dariyaba, kai baka isa kace itace ke doka murmushi ba ayanzu..takowa tayi har inda suke jikin kowannensu se rawa yakeyi gaya sun kasa gaba balle baya kuma ga danejo na tunkarosu aiko suka ɓare baki suka fashe da wani irin kukan ceton rai me wuyar saurara. Cikin daka tsaya tace "kumin shiru mutanen banza mutanan wofi kawai ɓata gari. Aiko sukayi ɗib kamar anyi ruwa an ɗauke. Ganin hakan yasa danejo ƙara haɗe fuska tace "kunsan Allah zan barku ne ayau domin kuhana sauran ɓata gari irinku aiwatarda wannan munanan ɗabi'un acikin rugarnan wato kune sata kuma abin betsaya isa hakanba hadda wiya ƴara fyaɗe ko? Humm to naƙara ganin wata ɓarna makamancin hakan agarinnan kugani aradu koba kubane to kune aruwa domin ku zan hukunta wannan nauyin daga yau yarataya awuyanku kubari ayi ɓarna agarinnan koku hana dabara yarage naku, tana gama faɗar hakan tajuya taɗauki ƴar tsumagiyarta data faɗi tun lokacinda suka kamota...tana juyawa sukaji kamar an sakesu, ai suka zura aguje tamkar zasu tashi sama sabida tsananin gudun dasukeyi na tashin hankali....murmushi kawai danejo tayi kana tanufi gidansu. MASARAUTAR MAHAR Tafe take tana sauri kamar zata kifa tana tafe tana wai wayen bayanta kallo ɗaya zaka mata kaga alamun rashin gaskiya atare da ita, ahakan harta ƙarasa pert ɗin matan sarki kaitsaye tawuce wanda ke yamma da sauran. Hakince tasamu wata kasaitacciyar dattijuwa akan kilisa tareda ciroma mubarak wato abba ciroma, wasu hadimai biyu na ɓare musu ayiba sunaci suna fira dagani kasan ɗa ne da uwarshi dudda kuwa taɗan manyanta amma mulki da sarauta sun hana manyancinta bayyana. Sallama tayi tashigo parlor tareda zubewa aƙasa tana faɗar "Allah yaƙarawa Fulani daraja da nisan kwana gaisheki nakeyi Fulanin memartaba tantabarar masauratar MAHAR. Murmushin fuskar Fulani abu ne ya faɗaɗa, kafin tagirgiza kanta alamar ta amsa kenan. Ganin hakan yasa wannan hadimar juyawa ga babba ciroma tana faɗar "Allah yaƙarawa ciroma girma da daraja ɗan sarki jikan sarki kuma sarki uba ga sarkin wata rana barka da wannan lokacin. Ahankali abba ciroma yace "yawwa barka laraba. Daga hakan yamiƙe yana yiwa mahaifiyar tashi sallama yafice...ita kuwa mayarda hankalinta tayi kan baiwa laraba tana faɗar "laraba Mike tafe dake hakan domin naga alamun akwai magana abakinki. "Hakane ranki yadaɗe a yau ne wannan yaron yashigo masarautar nan wato yarima sameer kuma sun shiga wajen memartaba

Chapter 2 of 4