Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
shida yan uwansa shine nace barana garzayo na sanar muki domin ƙila bakisan da shigiwarshiba Allah yaƙara miki daraja...ɗan shiru Fulani Abu tayi tana nazartar kalaman baiwa laraba kafin tanisa tace "aiko dai nasani domin sun shigo nan shida ƴan uwanshi,, kuma ina ta jan kunnenki laraba akan banason gulma da dakawomin zancen da ban tambekiba amma ƙinƙi kidenako? Tafaɗa cikin tuhuma..dasauri baiwa laraba taduƙarda kanta tana faɗar"tuba nakeyi uwar gijiyata amin aikin gafara. "Humm kawai Fulani abu tace kana tajanyo wata salka dake rataye agefenta ta fidda wata ƴar batta aciki tamiƙawa baiwa laraba, tana faɗar ga wannan kozakiyiwa yara anfani dashi. "Jikina rawa baiwa laraba takarɓa tana zuba godiya kamar zatayiwa Fulani abu sujjada takwashi tarkacenta tabar parlor aranta tanajin daɗin kyautar Fulani abu domin hannunta asake yake itada mebabban ɗaki domin duk sunfi Fulani huraira alkhairi.....itako Fulani abu da kallo tabi baiwa balaraba harta ɓacewa ganinta kafin ta girgiza kanta afili tace"gidan sarauta gidan gulma da munafunci kome hakan ze anfaneta dashi datazo zuwa gayamin oho? gaskiya bayi nada matsala sabida wannan gulmar tasu tayi yawa, tana gama faɗar hakan tamiƙe zuwa turakarta. Washe gari Dashirinsu suka fito dukkansu ukku sunyi kyau matuƙa kamar kasacesu kagudu musamman princes sameer da kyawunshi yakasance nadaban acikin duka family nasu domin kallo ɗaya zaka mishi ka alaƙantashi da Balarabe, kowannesu manyan kaya ne ajikinshi wato dinkin shadda nazamani daga Ameer har Anwar sedai shi gogan ƙananun kaya yasaka kuma duka farere ƙal ga dukkan alamu fari shine kalar dayafiso, daga wandonshi har rigar fararene sedai ahannun rigar kawai yakeda ratsin blue, takalmin shima fari ne hakan yaɗora cap fara wanda ta kwantarda lallausar sumar kanshi kuma tafitarda dan zagayayyen gemunshi nagayu wanda yaƙarawa fuskar tashi haiba tamkar wanda yayi makeup, duƙawa yayi yaɗauki wayoyinshi dake ajiye akan teble kana suka fito daga pert ɗin nashi, aƙasa suka samu mammi tana juye furarda tadamawa abbey, domin mammi komai itakeyin abinta Indai abinda yashafi girkine sam batason aikin hadimai. Suna gama saukowa yazo wurinta tareda rungumeta ya manna mata kiss agoshi. Murmushi kawai tayi tana kallon su Anwar domin su sungaisar da ita tun lokacinda suka shigo pert ɗin kiran princes yafito sutafi. "Ameer harkun fito? "Eh mammi munfito amana addu'a, yafaɗa yana murmushi, "to Allah yakaiku lafiya kuma yadawo daku lafiya amma kafin kutafi karku manta kushiga gadinfa domin kusan dai al'adar masarautar ku inbaso kukeyi asamu matsala ba wadda bana fata ayarana. "In sha Allah zamu shiga yanzu mammi kafin mutafi, cwar Anwar. "Yawwa Allah yayi muku albarka, kai kuwa Muhammad da ƙananun kaya zakaje? Dubi ƴan uwanka mana kowanne da manyan kaya gwanin sha'awa amma kai kasaka wannan na jajayen mutane. "Mammi zansha fura, yafaɗa kamar bayaso sabida yakauda zancenda take mishi batareda yace tama komaiba akan zancen domin yasan yanzu setace seya sauyasu kumashi bayason manyan kaya se dole. Ita kuwa sarai taganoshi hakan yasa tayi murmushi kawai tana zuba mishi furar a cup. "Kuma zakusha? "Dasauri suka girgiza kai suna murmushi domin dukkansu bacimarsu bace. Murmushi kawai tayi dama tasan bazasu shaba kawai faɗa ne tunda tasan abinda sukeso da wanda basaso...shikuwa Anan tsaye yaɗan sha kana ya ajiye cup ɗin, addu'a sosai mammi tamusu kafin suka fice daga pert ɗin, suka nufi gadin kamar yadda mammi ta umur cesu, princes na tsaki yana ƙarawa dominshi Allah yagani yatsani wannan al'adun na masarautar nan abu tamƙar tsafi..suna shiga babban get ɗin shiga gadin ɗin, wani ƙaton Shuri dage wurin yasaki algaita wadda ke sheda shigowar ahalin sarki habibullah cikin garin ɗin.cikin hanzari yarima sameer yayi saurin toshe kunnenshi jin kamar dodon kunnen nashi zefi sabida ƙara. atake tsuntsayen dake kan Shurin suka tashi sama suna shawagi.....! Book ɗin AL'AJABI Paid book ne akan 1k kacal zaki iya tura kuɗinki ta wannan account ɗin 👉2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA bank, kana kitura Shedar biyanki a wannan nomber 👉 07037092176 on whatsapp. Autar alheri ✍️ 🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥 🐦‍🔥🪐 *MASARAUTA*🪐🐦‍🔥 🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Dr Yasmeen Ahmad😚 Autar alheri ✍️ Al'ajabi, hummm Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI. ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃 Book 1 Page 13 & 14 "Suna shawagi..sukuwa takawa suka shigayi sunabin dabbobin dake cigin wurin da kallo ga tsuntsaye masu kyau da ɗaukar hankalin me kallonsu, sunyi tafiya meɗan nisa kafin suƙa isa tsakiyar gadin ɗin wurin wani ƙaton bishiyar gamji suna tunkaroshi yafarayi sama yana buɗewa kamar yadda bishiyar lema keyi wato fruat, domin dai duk wanda yasan bishiyar gamji yasan cewar katuwar bishiya takeyi kuma ganyenta ma manyane, konace kunnenta suna zubowane sumata runfa harse sunrufe kasan bishiyar wanda hakanne kebawa duk wanda besaba ganintaba tsoro ko wanda baya tu mamali da ita. Tofa ita wannan dake cikin gaɗin abinda yasa take buɗewa kamar abinda wani ke sarrafawa shine...Wato aƙa'idar wannan masarautar duk wanda zeyi tafiyar daze fita daga garin MAHAR doline seya shigo gadin yashiga cikin wannan bishiyar ta gamji tukunnah yafito yayi tafiyarshi, idan ba hakanba kuwa daƙyar kadawo lafiya qalau idan katafi, shikuwa wannan shurin aduk lokacinda wani jinin sarautar zeshigo cikin gadin ɗin to seya yimasa maraba tahanyar sakin algaita, inkuwa barene dayashigo get ɗin ze ƙara girma ya buɗe ta yadda ze ƙara komawa abin tsoro kana daga ƙarshe ya haɗiye ka tamkar anshafeka ajikinshi sa'annan yakoma mazaunin shi, kuma duk wanda yayiwa hakan tofa idan har wani daga cikin masauratar yasani ko aka sanarda sarki tun kafin ma sarki Habibullah tun magabatanshi to tabbas se ankai ruwa rana tukkunna shirunnan ze aminta yafoto dakai kuma daga lokacinda kafito bubaka babu komayin lafiya harka komawa mahaliccinka, wannan dalilin ne yasa basa taɓa bari baƙuwar fuska tashiga gadin ɗinsu koda kuwa matansune Indai bajinin sarautar MAHAR bane sedai sushiga tareda kai domin idan tareda wani daga cikin jinin sarautar kashiga ba abinda zesameka harka fito. Wannan kenan, shine kaɗan daga cikin tarihin gadin ɗin gidan sarautar MAHAR. Kafin su ƙarasa tuni gamji yabuɗe ganyenshi sunyi sama tamkar yayi lema, suna ƙarasawa ciki yasauko da gayen yarufesu rub kamar babusu awurin kana yarinƙa matsawa harya haɗe da jikinsu, kafin kuma yabuɗe kamar yadda yayi aɗazu yayi musu lema, sekawai suka fito, shikuwa yakoma yadda yake,,,Hakan suka fito cikin gadin ɗin suka nufi harabar inda motocinsu suke, suna zuwa aka buɗe musu wata katuwar mota mekamada jirgin ƙasa fadawa nata kakkaresu har suka shiga ciki su duka ukkun kana aka rufe motar, dasauri wasu dogarai suka shiga wasu motoci biyu, biyu kuwa na excout ɗinshi ne dayazo dasu daga US Hakan yasa motarsu takasance a tsakiya, ta dogarawa agabanta kana ta excout ce agaba baki ɗaya, hakama bayan tadogarawa kebin tasu seta excout takasance abaya, ahakan suka harba akan kwalta sukabar masauratar. Acan gidan kuwa pert ɗin memartaba jekadiya ce tashigo tana jerawa memartaba kayan abinci shi a ƙaramin parlor shi,,,shikuwa yana cikin turaka shida me babba ɗaki yana ƙimtsawa kafin yafito cin abinci.....ita kuwa jekadiya tanagamawa tafice bayan tasanar Mishi tagama, aiko tana fita sega wata mata ta bayyana awurin tayi wata irin shiga wadda duk tarufe mata jiki ko ina, hannayenta kawai zaka iya gani wanda tafidda wani abin ɗaure a ƙyalle tana zubawa cikin abincin memartaba, cikin sauri sauri take komai sedai ayadda jikinta keyi da yanayin Fatar hannunta zaka gane cewar dattijuwa ce bayarinya ba, tana gama zubawa taɓace ɓat kamar bata wanzu awurinba. ɗagawarta keda wuya suka fito parlor suka zauna me babba ɗaki tace "takawa mizan zubama ne? Ɗan shiru yayi kamar bazeyi magana kusan minti biyar kana yabuɗe baki cikin kamalarshi yace "banajin cin komai me babban ɗaki kawai ruwan bunu nakeso kuma wanda kika dafa da hanunki sekuma fura kitura gum gimbiya khadija akarɓomin. "To ranka yadaɗe yadda kace Hakan za'ayi tafaɗa tareda Miƙewa tsaye dudda kasan cewar ta manyanta amma Hakan besa tagazawa dawai niya da mijintaba...tana fita pert ɗinta takoma inda ta haɗa Mishi ruwan bunun kamar yadda yabuƙata dakayan kamshi masu tadawa mutum gwaɗayi wanda ko beyi niyyar shaba zeji sha'awar shanshi...hadima suwaiba tasaka aka kira mata kana taturata gun gimbiya khadija wato matar abbey muneer mahaifiyar yarima sameer, akan tanasar da Ita saƙon memartaba, aiko ciki ƙanƙanin lokaci mammi tahaɗawa surukin nata furar tabawa hadima suwaiba batareda kowacce irin fargaba ba domin da watace me babban ɗaki taturo to ba abinda zesa tabada saƙon sedai takaishi da kanta sabida tasan kafa kaɗan ake jira asamu damar illata wani acikin gidan...hadima suwaiba kuwa itace tariƙawa me babba ɗaki kayan har perlor memartaba kana tayi musu sallama tatafi bayan ta ajiye musu kayan, amin tacciyar hadima kenen me siffar salihan bayin Allah....shikuwa memartaba cikin Farin ciki yasha furarshi seda yaƙoshi bayan ya idar sukadan yi fira shida me babba ɗaki kafin yatafi masallaci sallar azahar seda yadawone yasha ruwan bununshi hankali kwance.. Azabure tamike tsaye tana faɗar "Wlh bazeyuba miyasa zakamin hakan wai wannan tsohon mikake nufi danine? ai Wlh bazata saɓuba doline kaci wannan maganin domin tahakanne kawai zakayi murabus kuma kabawa yarona sarautar bawai kaɗora wancan ɗan iskan jikan nakaba, ina sam Wlh bazeyuba to minene mafita? Tayaya zansamu yaci wannan maganin? Tayiwa kanta wannan tambayar...kamar daga sama taji wata murya marar daɗin sauraro ana faɗar "aikuwa idan so dubu zaki zubashi to bazeciba indai da hanunki kika zuba domin mutanen masarautar nan bazu barshi yaciba, sedai kisaka wani yazuba Miki domin samun cikar burinki, ana gama faɗar Hakan bedroom ɗin nata yayi tsit kamar ba'ananne ake wannan hargaginba...ajiyar zuciya tasauke akaro na ba adadi kafin tace "aikuwa doline nasaka azuba maishi Wlh, daga hakan tashige wani lungu dake cikin bedroom ɗinta. Humm wa'iyazu billah antsufa shekaru sunja memakon akoma ga Allah anemi yardarshi a'a se neman duniya kuma akeyi kamar baza'a mutu ba, Allah yasa mufi ƙarfin zukatanmu. Taraba State Tunda suka isa taraba suke yawo acikin jalingo ababban company da Abbanshi ke gini sunyi yawo sosai domin company nada girma sosai seda sukaga komai yayi Dede inda beyiba suka bada umurnin gyarawa su Anwar domin shidai yarima sameer biye kawai yake dasu, bayan sun kammala suka nufi wani tsadadden hotel suka sauka da zimmar gobe sukai ziyara makarantinnen da abbana nashi yayi na isilamiyya dana boko..Hakan suka kwana gajiye washe gari da sassafe suka nufi makarantinnen, sukayi musu zuwan bazata sedai ayadda suka samu komai lpy qalau ana koyarwa yadda yadace ya tabbar musu da Cewar malaman na aikinsu, kuma sunyi musu tarba me kyau sam basuji rashin daɗiba akan bazatan dasuka musu, seda suka ɗanyi zagaye makarantu da dama kana ɗaya daga cikin yaran abbanshi dakenan taraba yaƙaraso wurinsu tareda russunawa yace...! Book ɗin AL'AJABI Paid book ne akan 1k kacal zaki iya tura kuɗinki ta wannan account ɗin 👉2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA bank, kana kitura Shedar biyanki a wannan nomber 👉 07037092176 on whatsapp. Autar alheri ✍️ 🪐🐦‍🔥🪐 *AL' AJABI*🪐🐦‍🔥🪐 🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Dr Yasmeen Ahmad😚 Autar alheri ✍️ Al'ajabi, hummm Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI. ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃 Book 1 Page 15 & 16 "Yace "ranka yadaɗe inada magana please idan ba damuwa. "Okay munajinka Cewar ameer. "Yallaɓai Wlh dama wata makarantace acikin garin Adamawa wadda Alhaji yasiya yo yace duk lokacinda yaranshi sukazo akaisu suga wurin sabida kusan yaza'ayi aikin, shine nace kozakuzo mujecan kuga wurin? Yaƙarasa zancen cikin ladabi agaresu. Kallon princes sameer sukayi atare dominjin amsar daze bada sabida shine kawai ze iya kawo matsala tafiyar, amma se sukaga bece komaiba, dudda hakan basuyi mamaki sabida sunrigada sunsan wayeshi, juyawa Anwar yayi gun wannan matashin kamin yace "shikenan badamuwa amma bazamu samu damar zuwa yanzu ba sedai idan mun ƙara dawowa sabida yanzu daganan gida muka nufa. Dasauri wannan matashin yace "please yallaɓai Dade anduba lamarin domin Wlh mutanen wannan yankin suna matuƙar buƙatar tallafin ilimi acikin rayuwarsu gabaki ɗaya akan duhun jahilci suke rayuwa wannan dalilinnema yasa Alhaji siyan wurin domin kawo musu hasken addini, yaƙarasa zancen cikin alamun riƙo. Ido yarima sameer yaruntse daƙarfi yanajin wani irin zafi aranshi domin aduniya yatsani yaji Cewar wata halitta narayuwar rashin ilimin addini domin koba nazamani dai bazaka rasa abin kusantar uban gijinkaba. Shi kuwa Anwar ajiyar zuciya yasauke tareda buɗe baki zeyi magana kenan yaji ɗaukar cool voice ɗinshi yana faɗar "it's okay we will going to Adamawa state now. Yana gama faɗar Hakan yajuya zuwa motarsu cikin takonshi na ƙasaita wadda kallo ɗaya zakamishi kasan cewar shiɗin jinin sarautane.... murmushi dukkansu sukayi kana suka mara Mishi baya, seda suka shiga motarsu duka kana Ameer yaleƙo tareda baya ɗaya daga cikin hadiman su umurnin anunawa wannan saurayin me suna imam, motar daze shiga sutafi tare tunda shine yasan wurin. Aiko cikin sauri yacika umurnin shi kana sukaja motocinsu sukabar wurin, tareda nufar garin Adamawa state. MAYE BALWA "Danejo danejo wai kina inane? Kikabarni inata famar kiranki sekace wata sa'arki. Innawuro ce keta famar dokawa danejo kira kamar zata tsaga gidan....Ita kuwa danejo tana bayi ne shiyasa bata amsaba har seda tafito domin pappi ɗinta yahanata amsa kira abayi yagaya mata ba kyau Hakan shiyasa koda innawuro zata dafata bazata taɓa amsawaba se lokacinda tafito, to yanzumu hakance takasance, fitowa tayi dabuta ahannunta tana faɗar"na'am ganin Anan innah ina bayine...wani banzan kallo tawatsa mata kafin taja tsaki cikin takaicin yarinyar tace ungo maza jeji hayin barmo ki kaiwa hansai kuma kitsaya tagama ki karɓomin saƙona tukkunna kidawo, tafaɗa tana dungurawa danejo nera ɗari ahannu. Tokawai tace mata kana ta ɗauki ƴar sandarta tafice daga gidan, tafiya takeyi ahankali ita kaɗai tana wasada sandarta kuma aranta tana tunanin pappi ɗinta domin yau kwana biyu kenan bezoba kuma idan yayi wannan kwana biyun jitakeyi kamar shekara biyu ne yayi, amma tasan tunda har yacika kwana biyu yau to tabbas yau zezo ko gobe, Hakan dai take tafoyarta hankali kwance ita kaɗai kuma gashi wurin nada nisa sosai amma ahakan take tafiya batareda tasakawa ranta ganin nisan wurinba domin tabbas datasa Hakan aranta toda anyanke mata tafiyar sedai ahakan ma anayi ana ɗan kusantota da unguwar sabida se anfita rugarsu gabaki ɗaya anwuce ruga har biyu kana akai inda innawuro ta aiketa, kuma tasanda Hakan ammata turata sabida mugunta. Matafiya Tsaye suke acikin babban filin makarantar MAYE BALWA wadda tajima dawatsewa bakowa aciki kuma ba komai na anfani takoma tamkar kango, sunjima suna zagayen makarantar kafin su samu wani wuri daga gefen makarantar suka zauna suna tattaunawa da hakimin garin, bayan suyi magana da wani company gine,gine dake cikin garin Yola, suna jiran ƙarasowarsu domin suɗamƙa kwangilar gyaran makarantar hannunsu..basu jima awurinba manager company yazo, Hakan yake nuna musu tsare tsaren ginin makarantu dasuke dashi a laptop ɗinshi suna dubawa..shikuwa yarima sameer ya lumshe kyawawan idanuwanshi masu launin ruwan madara, yana sauraren bugun zuciyarshi dayakeji tamkar zata tsinke wani irin fargaba da faɗuwar gaba yakeji wanda besan daliliba kuma abin seƙara kusantoshi yakeyi...sukuwa sunacan suna aikinsu hankali kwance domin nema sukeyi suyi sugama subar unguwar domin babu alamun ko sunsan miye hotel balle suyi tunanin samunshi Anan kusa, sesun koma cikin gari tukkunna. Danejo Taje inda innawuro ta aiketa tadawo tana tafe tana tana tsilla sandarta sama gaya duk tazubo sumar kanta tarufe mata rabin fuska da ƙirjinta ɗaya har zuwa cibiyarta sabida tsawon sumar dakuma tsantsinta, tafiya takeyi ita kaɗai awurin domin kamar jeji hakan wurin yake sabida anfita daga cikin gari kuma ba'a ƙarasa cikin rugar Fulanin dake maƙwabtaka fawirinba,tayi tafiya menisa kafin tazo Dede inda motocinsu suke, da mamaki take kallon motocin bawai ɗan bata taɓa Ganin mota ba a'a kawai de tayi mamakin ganinsu awurinne, ahankali taƙarasa wurin cikin sanɗa tana leƙensu....Sukuwa basuma sanda akwai mutum awurinba. Tajima tana kallonsu basusaniba harta juya zata tafi sekawai idonta yasauka akan yarima sameer dake lumshe da Ido yasaka hannu ɗaya yaɗage setin zuciyarshi dayakeji kamar zata ɓalle tafoto waje...ido tawaro cikin tsananin fatin ciki dajin daɗi taƙarasa gunshi sam bata damu da mutanen dake wurinba cikin ɗauki tariƙo hannunshi tana faɗar "pappi cikin sweet voice ɗinta me daɗin sauraro...wani irin zabura princes yayi sabida wani mugun shuck dayaji lokacinda hannunta yasauka anashi, tareda buɗe lulu eyes ɗinshi akan kyakkyawar fuskarta, wanda yayi sanadiyyar tsanantawar bugun zuciyarshi. Sukuwa duka ido suka waro musamman brothers ɗinshi dasukasan waye yarima sameer dakuma yadda yake ƙyamatar mata, amma imam, Hakimi, da manager company duka kallon mamaki ne suke mata gatadai kallo ɗaya zaka mata kasan cewar ƴar fulanice ta asali wanda akasani da kunya da kawaici amma gaya tariƙe hannun namiji kuma babban mutum me daraja irin yarima sameer agansu batareda taji kunyarsuba. Shi kuwa wani mugun kallo kawai yakebinta dashi amma kasa cewa komai kowani dogon motsi yakasayi...cikin mamaki danejo kebinshi da kallo tunda tabuɗe ido aduniya take Ganin pappi ɗinta bata taɓa yimai maganaba yashareta se yau, atake gabanta yafaɗi tsoro da fargaba duk suka rufeta dara daran idanuwanta masu masifar haske suka canja kala atake suka cikoda ƙwallah, dasauri ta russuna wurin ƙasan ƙafafunshi taƙara kamo hannunshi ɗaya muryarta na rawa take faɗar "pappina bakada lafiya ne? Miyasa kayi shiru? Ko wani abun wannan mutanen sukayima? Miyasameka pappi? Kayi magana dan Allah. Taƙarasa zancen tana saka Mishi kukan dake fita har zuciyarta.. "Ikon Allah ke baiwar Allah sakeshi mana aina kika sanshi dazakiga mutum kawai kizo kiriƙeshi kinamai kuka? Cewar imam cikin mamaki...banza tayi dashi domin burinta kawai pappinta yayi magana amma shiru se ido kawai dayake binta dashi...shikuwa imam agarzuƙe yayo kanta yana masifa "waifa wannan wani lokacin Fulanin nan naruga ba hankaline dasuba tashi kibarnan kona tattakaki yanzu Wlh. "No karka daketa Cewar Ameer yana tasowa daga inda yake zaune yaduƙo kusan inda take gurfane riƙeda hannun yarima sameer yace "ƙanwata sakeshi muyi magana kinji, Yafaɗa cikin alamun rarrashi...dagowa tayi da jajayen idanuwanta masu masifar girma tawatsamaisu tareda girgiza kanta duka sumar data rufe rabin fuskarta tayi baya atake asalin fuskarta ta bayyana. Azabure ameer yayi baya sedai yayi ƙarfin halin hana kanshi faɗuwa, hakama duk wanda ke wurin seda yarazana Ganin tsananin kyawun wannan yarinyar gakuma gashi har gadon baya kana ƙwatar idonta kaɗai ta isa tashedama tabbas aljanace sabida kasan cewar ƙwayar idonta lite blue sedai acikin ido farine ƙal amma yanzu yakoma ja sabida kukanda tayi. Duk wanda ka kallah awurin natsuwa ta ɗauke Mishi amma Banda zaratan samarin dasukayi ta maza suna kallonta... ɗan seta kanshi yayi kana yaƙara cewa a'ina kikasanshi ƙanwata? Domin yaga dai taƙi ta sakeshi kamar yadda yabuƙata...ƙwallar dasuka cika idonta ne suka ƙara zubowa kana tace "pappina ne...! Book ɗin AL'AJABI Paid book ne akan 1k kacal complete ga duk me buƙata domin a complete yafito duk wanda keson posting kullun 700 ne zaki iya tura kuɗinki ta wannan account ɗin 👉2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA bank, kana kitura Shedar biyanki a wannan nomber 👉 07037092176 on whatsapp. Autar alheri ✍️ 🪐🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥🪐 🪐🐦‍🔥 *MASARAUTA*🐦‍🔥🪐 🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Dr Yasmeen Ahmad😚 Autar alheri ✍️ Al'ajabi, hummm Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI. ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃 Book 1 Page 17 & 18 "Kana tace "pappina ne kuma inasanshi banaso wani abun yasameshi, kace yayi magana dan Allah kowani abun kuka masa ne? Tafaɗa cikin yanayin tausayi domin duk zuciyarta ta karaya Ganin pappinta yaƙi cewa komai...ajiyar zuciya Ameer yasauke kana yadubi yarima sameer daya lumshe kyawawan idanuwanshi tun lokacinda kalamanta suka fara dukan dodon kunnenshi, kana yace "princes kasan wannan yarinyar ne? Yatambaya badan abashi amsaba domin yasan ba abinda yarima sameer zece Mishi idan kuwa zasu kwana awurinne, sedai ga mamakinshi yaji cool voice ɗinshi yana faɗar "I no her, yafaɗa kamar meciyon baki, kafin yaƙara motsa laɓɓansa cikin gajiyawa yake faɗar "please just sey her get from my saint, Yafaɗa, zuciyarshi ada gule. Ido danejo tazuba Mishi kawai tana kallonshi yayinda idon ke ƙara cikowa da ƙwallah...shikuwa Ameer jin kalaman ɗan uwan nashi yasa yadubeta kana yace "please ƙanwata inaga wannan Bashine pappin dakike magana akaiba kiyi haƙuri kije gida kinji zakiga pappinki acan yana jiranki amma wannan bashi bane, yaƙarasa zancen cikin rarrashi. Ita kuwa tunda taji saukar kalamanshi idonta suka ƙara zuba tamkar panpo, cikin kukanda keson kuɓuce mata tasaki hannayenshi wanda yaji tamkar lantarki ce tarikeshi amma yanzu tasakeshi sewani zutt,zutt yakeji acikin lallausan tafin hannuwan nashi. "Ni zakace akora my pappi ni HUSNAR KA? danejo ce fa? yau nikake kora? minayima dazafi Hakan? Ni pappi? Humm sabida kaga banada kowa danake raɓa naji sanyi sekai? Karka manta pappi kaine uwata, kaine ubana, kaine yayana, kaine ƙanena, kaine abokina, amma yau kaida kanka kake korana? Hum shikenan I'm going to all your life my pappi sedai zan zauna zaman tsimayen "When you're call me "when you're missing me😥 "When you're coming back to me my happiness "When you're coming back to me my everything all my life, I'll waiting for you any time my pappi. Tana gama faɗar Hakan tamiƙe tsaye tareda saka bayan hannunta tashare ƙwallar idonta, kana tajuya kawai tabar wurin. Sukuwa gabaki ɗaya sunyi mutuwar zaune tunda tafara magana domin sam basuyi tunanin zataji abinda princes yaceba balle har ta iya maida Mishi amsa da turanci ba, hartabar wurin basu saniba, sunlula duniyar tunanin ya akayi ƴar fillo ta iya Turanci kuma ƴar cikin ruga Fulanin jeji? Amma ba wanda ze basu amsar wannan tambayar tasu Hakan yasa suka ƙara gaskatawa ransu Cewar gamo sukayi da aljana... firgigit Hakan Anwar yayi yana kallon inda take gurfane da zimmar yabata haƙuri amma seyaga wayam bakowa Hakan yasa gabanshi ƙara mugun faɗuwa cikin kaɗuwa yake faɗar "kai ameer taɓace fa Wlh ajanace innalillahi wa'innailaihiraji'un...arazane Ameer ɗinma yamiƙe tareda riƙo hannun yarima sameer daya koma tamkar wanda aka zarewa lakka ajiki yamiƙar dashi tareda janshi suka fara tafiya gun motocinsu sedai duk yadda Ameer yaso sutaka dasauri abin yaƙi samuwa domin yadda yake tafiyarshi yanzuma Hakan yakeyinta cikin izza da ƙasaita tamkar yadda yasaba yin abarshi ga dukkan alamu dai hakanne tafiyar take bawai yanayi bane sabida kuɗi ko mulkinsu ba... hakama su imam tuni sun mara musu baya...hakimi kan se haƙuri yake basu domin ya ɗauka sun fasayin aikinne tunda yaga Manager company gini yacika bujenshi da iska, aranshi kuwa se tsinewa wannan aljanar yarinyar yakeyi...sukuwa dogaransu nahangosu tafe sukayi saurin buɗe musu motar, suna isowa suka shiga hakama excout ɗinsu suka shiga cikin sauri aka tada motocin sukabar yanki baki ɗaya. DANEJO Tafiya kawai takeyi batamasan ina take jefa kafartaba wani irin ɗaci takejin zuciyarta namata wanda bata taɓa jin irinshiba,,,yau ta ɗanɗani baƙin cikin dabata taɓa tunanin samuba, wai itace pappinta zece akora wai besantaba wannan wacce irin ranace me muni tazo acikin rayuwarta? tabbas wannan abin yayi mata zafi bakuma dan bata taɓa fuskantar Hakan bane a'a kawai dai ɗanta riski hakanne a inda batayi tunaniba, domin koda mutanen duniya zasu mata Hakan bazataji

Chapter 3 of 4