Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi a ido. Na rusunar da idona kawai na isa wajen zama na na zauna. Sai da ya gama karatu wanda duk rabi ba fahinta nake ba sannan ya ‘dago yana kallon y’an ajin ya furta “Bissalam, ku je ku yi sallah.” Ni ce ta farkon fita. Ana idar da sallah aka ce koda kowa ya mik’e, anan muke jin ashe yau ustaz zai yi sallama da makarantar. D’alibai da yawa ba su so ba, musamman y’an mata da suke ta maganar k’asa-k’asa. Ustaz ya yi alheri sosai ga makarantarmu. Sanda Malam Kawu ya masa godiya a madadin y’an ajinsa na Ibn Kaseer ta cikin loud speakerr Ya furta “Bayan jaddada kalmar godiyar mu, sannan ina son y’an makaranta su taya Ustaz Ahmad murnar samun matar Aure da ya yi, a cikin makarantar nan. An saka musu rana da hazik’ar mu, Hafizar mu Aysha Imam Khaleel, Head girl d’in mu ta wannan makaranta. Duk da nik’ab ne a fuskata sai da jikina ya fara rawa musamman da kabbarar mutane ta dinga shiga kunnuwa na. Na runtse idona a hankali. Ina hango yarda bakin Ustaz ya kasa rufuwa yana ta sakin murmushi. Y’an mata kuwa duk fuskokin wasu ba walwala. Har gaba na aka dinga zuwa ana sake taya ni murna. Ni dai kasa bu’de fuskata na yi na samu na na silale na gudu… Ina zuwa layin gidan mu naga yarinya ta biyo ni da gudu “Malama Aysha take ta furtawa. Na tsaya ina kallonta sai da ta d’an yi haki na alamar gudun da ta ci sannan ta mik’o min envelope ‘din mai matuk’ar kyau. Da tun kafin na bu’de na san waye saboda k’amshin mayen turarensa. “Ba ruwana da fushinki, duk da na ji haushi amma abu guda na sani dole a cika min alk’awarina zan zo shan ruwa gobe around 7:30pm. Your’s Ustazun Aysha. Ajiyar zuciya na saki. A raina ina tunanin ta inda zan rabu da Ustaz ba tare da na saka shi a damuwa ba.. Kashegari nima tashi na yi da azimin kawai na samu kai na da son yiwa Ustaz d’in girki, duk da ina ji a raina a ranar zan rok’e shi ya janye daga maganar aurena ko don dawo da farin cikin gidan mu, kuma Mami ta dawo gidan mijinta. Girkin na masa, Masa da sinasir sai miyar taushe na kuma yi kunun tsamiya da zob’o da ya ji kayan k’amshi. Haka kawai na ji gwara na masa abincin mu na gargajiya. Umma dai sai kallona take kafin ta gaji da shirun ta furta “AYSHA wa kike wa girki ne?” Kunyace ta kamani na ce “Umma cewa ya yi zai zo ya sha ruwa.” Gani na yi ta yi murmushi ta d’an’dana girkin da lemon ta girgiza kai ta furta “Kin yi k’ok’ari, sai ki ha’da masa da zogale tunda naga harkar gargajiya kika masa. Ko ke fa? Ki rabu da Mami zata dawo da ikon Allah, gobe ma Na ji Baffaninku suna za su je gidan…” Na d’aga kai kawai ba wai don zan janye maganar rabuwa da Ustaz ba da na shiryawa a yau. Daidai lokacin da zai zo kuwa sai ga Yaya Ali ya shigo d’akina yana kallona ya furta “Bak’onki ya zo kandala.” Turo baki na yi ina fa’din “Kai Ya Ali me ye haka? Kai ma ya kamata ka yi aure ka bar gidan nan.” D’alle min baki ya yi yana furta sai ki aurar da ni, ashe dai kina son mutumin ji wani uban kwalliya da kika yi har da su jambaki?” Harararsa kawai na yi na shige na sauka k’asa. Kafin na je ma har Umma ta saka an kai masa abincin sitroom. Ina shiga yana zaune na same shi. Idonsa a lumshe sai dai daga yanayin fuskarsa na tabbatar akwai abinda ke damunsa. Sallamar da na yi bai saka ya bu’de idon ba ya dai amsa nima na ga haka ne ta hanyar d’aga lab’b’ansa da ya yi. Tsawon mintu biyu bai bu’de idon ba duk da a jikina na ji yana kallona da lumsassun idanun nasa. “Zuba min ruwan tea.ban sha ruwa ba dabino kawai na ci.” Ya fa’da still idanunsa a lumshe. A daburce na fara ha’da masa shayin. Ina shirin sake zuba sugar ya furta “Enough madam, wa ya gaya miki ana son maza su dinga shan zak’i sosai?” Ya fa’da yana ware idonsa ka’dan a kai na. Maik’on k’wallar ido yana k’arawa idonsa kyau. Hawaye naga sun d’an gangaro masa. Hakan ya saka jikina ya yi sanyi. Na ajiye cup d’in shayin a kan table da ke kusa da shi. “Na gode” ya furta cikin raunin muryar da ta saka har na ‘dago na kalleshi da sauri na ce “Kuka ka ke?” Ya ‘d’aga min kai. “Kuka nake AYSHA, dole na yi kuka me yasa ba kya so na? Kike wahalar da ni, kin san kalar azabar da kika bani a kwanakin nan, Sana’a na je yi k’asar mutane amma na zama sam bani da nutsuwar da zan gudanar da sana’ar na kira waya a kashe har na gaji na kira Abba. Amma still you don’t on your phone why? Me na miki da na yi deserving this kind of purnishment a wajenki? Kin san bana k’asar balle nazo na ji dalili. Ki gaya min gaskiya me ya faru kin daina so na ne?” Da sauri na d’aga kai ina kallon sanda ya matse tea cup d’in hannunsa duk da zafinsa na runtse idona. Sai na ji ya saki ajiyar zuciya ya ajiye cup d’in. Ya furta “Na gode AYSHA, amma may I know the reason?” Ji na yi na kasa b’oye masa na ce “Mami na bata son relationships d’inmu da kai, ta fi so na yi karatu…” “Maminki?” Ya furta yana kallona kallon da yasa na ji wani mugun tausayinsa ya kamani. Sai naga ya cije leb’ensa ya mik’e kawai ya ajiye cup d’in ya fice. Ji na yi kamar na bi shi amma k’afafuna sun kasa sai b’alle war hawaye na ji daga cikin idona. Ai kuwa na saka kukan sosai ina yi ina mayar da ajiyar zuciya…. Shikkenan na san na rabu da Ustaz idan ba’a yi wasa ba rabuwa ta har abada! 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢. Kin fara karanta k’arfe a wuta kuwa? Kin ji da’din labarin Arfa da Viper? Idan baki fara ba maza ki fara tunda ke kan ki kin san Alk’alamin Aysha cool baya rubuta shirme. Rubutu ne take yi mai inganci wanda take rubuta abubuwan da suke faruwa zahiran da hanyar warwaruwar matsalar. Kada ki manta marubuciyar k’anwar Maza ce gaba da gabanta, cutarwa… maza ki fara ana kan free pages ina tabbatar muku ba zaku yi nadama ba. K’ARFE A WUTA…….. Don samun page 12 na Naga rayuwa ga wanda ba za su iya jira ba, ku duba arewabooks an saka. Ga link d’in nan. Nagode [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 10 ‎Da daddare muna zaune a ‘daki ni da Mami. Kalba take min tana sake zuga ni akan kada na yarda na auri Ustaz. Umma ta yi sallama ta tura k’ofar ta shigo. Idanunta zube a kan mu. Mami kuwa tana ganinta ta tsuke fuska. Zama ta yi a gefen gadon Mamin tana furta “Yanzu Fateema abin har ya kai haka? Ni ban ga abin d’aga hankali a wannan maganar ba, har kike neman ki tsiro da wasu halaye na daban da ba masu kyau ba. Wa’dannan abinda kike bakomai ba ne sai raina Abban su, kin koma san sarai makomar macen da ta raina Mijinta. Ni ban ga aibun Abinda Abbansu zai yi ba. Kamar fa gata ya yi muku ke da y’ar taki, auren namiji kamar Ustaz Ai duk uwa ta gari zata so wa d’anta……” Kallon da Mamin ta mata ne yasa ta tsuke bakinta tana kallonta da mamaki a fuskarta… “”Ke ce dai baki ga abin tada jijiyar wuya ba, ni na hango shi, kuma kuka d’auki maganar nan k’arama ni na shirya fito na fito da duk wanda ya ce zai mata aure a wannan y’an shekarun nata, wallahi ko Human right sai na kai mutum, in dai da gaske har zuciyarku kun bar min y’ar, ai sai ku bar ni na yi abinda zan yi da ita, sai dai idan nuna min za ku yi, ban isa da ita ba don ba ni na haifeta ba….” “A’a Fateema, duk maganar bata kai ga haka ba, Allah ya baki hak’uri.” Umma ta fa’da tana mik’ewa ta fice daga d’akin. Wani tsaki da ya tab’an zuciya Mami ta ja tana furta “So kike ta yi zaman aure da gidahumanci kamar yarda ke kike yi…” Sai na ji kalmar ta min girma a kai, na kuma samu raina da b’aci Umman ce gidahuma kenan? Sallamar Abba muka ji a kan mu bayan kusan mintuna 30 da fitar Umma, har a sannan kuma Mami bata fasa zuga ni ba. Ido ya zuba mana cikin tsukakkiyar fuskarsa da ban tab’a sanin yana da ita ba. “Tashi ki je sitroom kina da bak’o…” Mami ta ja hannuna ta rik’e k’am. Ba zata je ba..” Ta furta idanunta cikin na Abba. Wani kallo ya wurga mata mai cike da nuna zallar b’acin ransa ya furta “Kada mu yi haka da ke Fateema, kada ki kai ni bango, abin ba zai mana da kyau ba. Cika mata hannu…” Hannun ya fincike a nata hannun ya ja hannuna muka fice. Har d’aki ya raka ni. “Ki shirya sosai ki same shi a sitroom, idan kin so ki watsa min k’asa a ido ki zubar da martabar gidan nan…” Jikina kawai rawa yake, na kasa aikata komai sai share hawayen fuskata nake. Ga Abba ya ce yana tsaye a parlorn Mamin yana jira na. After dress kawai na zura akan kayan na fita duk zuciyata a furguce take ba ni da nutsuwa ko ka’dan. Don ban manta kashedin Mami ba na kada na yarda da zuwa wajen Ustaz idan kuwa na amince ta san na nuna mata bata isa da ni ba, kuma ba ita ta haifeni ba. Wannan magana ita take firgitani nake kuma rasa nutsuwa tabbas sun saka ni a tsaka mai wuya. Hannuna Abba ya sake ja, muka sauka ina kallon Mami da take tsaye ta saka hannu ta share hawayenta sai na ji nima nawa hawayen sun zubo. Na d’an tsaya Abba ya juyo yana kallona. “Kina son na b’ata miki rai AYSHA? Kada ki saka na d’aura miki aure da shi yanzun nan…” Da sauri na girgiza kai. Sai da ya ga na shiga sitroom d’in sannan ya juya ya koma cikin gida. Zuciyata kawai bugu take, musamman da na ji k’amshin turaren Ustaz ya mamaye sitroom d’in. Na yi sallama can k’asan mak’oshi. Shima a k’asan mak’oshin ya amsa yana sakin ajiyar zuciyar da tasa na d’ago na kalleshi. Jallabiya ce bak’a wuluk a jikinsa, yau bai saka Alkyabba ba. Kansa dai da farin Ihrami. Idanunsa sanye da farin glass da ya k’ara fito da kyan fuskarsa. “Shigo ki zauna..” Kamar ba zan shiga ba. Sai dai na shiga na zauna a kujerar da take nesa da shi. “Dawo wannan kujerar bana son magana da k’arfi, I feel headache zuwan na dole ne..” Na kalli kujerar da take kallon tasa na tashi na koma na zauna fuskata a tsuke ina wasa da yatsun hannuna. Shiru ya yi kansa a k’asa kafin na ji muryarsa mai cike da rauni yana furta “Ba gaisuwa AYSHA?” Sai na ji kunya ta kamani na d’ago kamar dole na ce “Ina wuni?” Bai amsa ba, wani kallo kawai yake jifana da shi da yasa yanayin jikinsa sauyawa, sai naga ya lumshe ido yana murza goshinsa ya furta “Gaya min laifina Ayshatu? Kike hukunta ni da wannan sigar, na kira waya kin yi rejecting text no answer, makaranta kin k’i zuwa, gaya min me ya faru?” Shiru na masa kawai idanuna na zubar da hawaye da zan iya a lokacin kai tsaye zan furta masa ya janye maganar aurena, amma wallahi na kasa ya min wani irin kwarjini da ba zan iya kallon idanunsa na furta masa hakan ba. Gashi a k’asan zuciyata wata irin soyayyarsa mai zafi ce take sake ragargazar zuciyar. Kallona dai yake kafin na ji ya sake kiran sunana. Kiran da naji har tsakiyar raina. “AYSHA! D’ago ki kalleni ina son mu yi maganar gaskiya, bana son k’unbiya k’unbiya kuma…. Zan baki tarihin kai na da baki tab’a tambaya ba, zan sanar da ke waye ni da k’arfin soyayyarki a zuciyata, idan kin amince da aurena to, idan kuma kin ji ban kwanta miki ba bayan sanin wanene ni sai na k’yaleki na yi fatan Allah ya ha’da kowa da rabonsa…. Ahmad Sulaiman Saeed shine Cikakken sunana, sunan da iyaye suka saka min, sunan da kowa ya san ni da shi. Sai dai a yanzu a makarantar ku da gidanmu na ji sun canja min suna zuwa Ustazun Aysha….” Jin abinda ya fa’da ya saka ni saurin d’agowa ina kallonsa. D’aga min kai ya yi “Banda tambaya har sai na gama, abu guda da na sani ina jin da’din Sunan da aka canja min, ina kuma fata ya ‘dore har abada idan da alheri a cikin zama na da ke… Mu uku kacal na gani a gidan mu, nima ban san dalilin da yasa suka zab’i su haifemu mu ukun ba kamar a k’asar turawa duk da dai d’abiun turawan suke amfani da su… na so a ce gidanmu muna da yawa kamar yarda nake sha’awar duk wani babban gida ya kasance, sai dai hakan bata samu ba. Amma na ce alwashin duk matar da na aura sai ta haifa min yara bila adadin ina son naga y’ay’ana sun kai hamsin…” waro idona na yi ina kallonsa ya ‘d’aga min kai “Don haka sai ki shirya dafatan Allah ya bamu masa albarka….” Runtse idona na yi saboda tsananin kunya a raina nake raya sai kace nace masa zan aureshi? Ahmad Sulaiman Sa’eed shine Babba, sai Khadija Sulaiman Sa’eed wanda kafin a haifeta sai da na shekara goma cif. Itama tsakaninta da d’an autanmu shekaru goman ne, shi yasa na ce miki su iyayena rayuwar turawa suke ko don a can k’asar masu jajayen kunnuwan suka taso. Mahaifina ya da’de yana aiki a Canada kafin ya dawo Nigeria ya kafa kasuwanci. Mahaifina su Talatin ne a gidansu ba zan iya jero miki su ba, sai dai na san mutanene masu zumunci masu son kuma auren zumunci, nima bijirewa na yi na musu tsallen baka’dai na gaya musu AYSHA kawai zuciyata take so. A d’akin su Abba na akwai Umma Amina itace Babba sai Umma Jamila, Daddynmu sai Abba Kabeer, Abba Ali, Abba Naseer da Umma Shatu.. autarsu kenan kuma mate d’ina ce mai sunan Ayshata… A gidansu Umma na kuwa su Ashirin ba biyu ne, sai dai a d’akinsu su biyar ne kacal. Ramla Mahaifiyar Ahmad Sulaiman, sai Saudat Tasleem, Taiba da Nihad. Nan fa wai su mahaifiyarsu balarabiya shi yasa ta sakawa yaranta sunan larabawa don Kakata buzuwar Yamen ce.. sai kin hankali da su idan muka yi aure don mutane ne masu felek’e da iyayi na gaske. Duka karatu na tun daga matakin yarinta har na girma, na yi su ne a lebanon school, sai da na gama secondary sannan na tuburewa Daddy na ce Jami’atul Madeena za’a kai ni. Ya so ya bujire don shi burinsa na zama iyalen Elizabeth ni kuma na ce nawa burin na zama dangin King Fahad ne, an kai ruwa rana kafin ya amincewa buk’atata na tattara na tafi Jami’atul Madeena ban kuma dawo ba sai a waccan shekarar… Ina isowa Nigeria na tsunduma aikin k’wadago ina ha’dawa da noma da kiwo da kuma safara daga can k’asashen waje zuwa tamu k’asar. Ranar da na fara ganinki, rana ce mai matuk’ar girma a wajena, da ba zan manta da ita ba. Kamar ba zan fita daga gida ba saboda hadari da ya lullub’e sararin samaniya sai dai wayar da Kabeer yake min ta isheni na zuwa ganin wani gida da Zan gani a layinku. Na mik’e na shiga wanka kamar ba zan yi kwalliya ba sai dai na samu kaina da tsara kwalliya ashe zan ha’du da matata ne… Ina tsaye da abokina na dinga jin zuciyata na wani irin harbawa. Mamaki ya isheni na juya don ganin dalili sai idona ya fa’da kan wata zuk’ek’iyar yarinya doguwa fara mai suffar larabawa. Numfashina ne ya kusa d’aukewa duk da na Yi matuk’ar daurewa wajen yi miki kallon da shari’a ta amince da shi kallo guda. Sai da kika wuce sannan na saki ajiyar zuciya ina kallon Kabeer na furta “Wacece wannan?” Kabeer dariya ya yi sosai yana cewa “Ai kuwa in dai sonta ka ke ka dace da macen k’warai, Saliha managarciya da kowa ke so.. duk layin nan ba nutsuwar yarinyar can wallahi…” na d’an yi dariya ina furta “Dalilinka na cewa haka Kabeer?” “Saboda kai daga gani shigarta ka san ta ha’da duk qualities d’in da ake son mace ta gari ta zama..” ya furta yana kallona cikin son tabbatarwa. Dariya na yi nace “Idan kuma Basaja take fa?” Kabeer ya ware ido ya ce wallahi ba wani Basaja idan baka amince ba kuma ka yi bincike..” “Bincike ya zama dole Kabeer, don aure nake son mu yi ta zame min Uwar yara na kaga kuwa dole na binciki sahihancin tarbiyyarta..” Kabeer ya jinjina min kai. “Ina tabbatar maka Ahmad duk binciken da zaka yi akan yarinyar nan magana guda zaka samu Mai tarbiyya ce…” Na saki ajiyar zuciya ina d’aga kai na windownku na hango kamar ana lek’e jikina kuma ya bani ke ce ko?” Waro ido na yi ina kallonsa. Ya saki murmushi yana d’aga min gira. “A jikina na san ke ce, na san kuma kema kin fa’da soyayyata daga yanayin yarda idanunmu suka sark’e da juna…” Daga ranar na kafa d’anbar bincike ka’in da Na’in. Shine dalilin da yasa na je har makarantarku neman koyarwa. Kuma daga ranar kullum a kan idona kike tafiya makaranta duk da ba na bari ki ganni, na kuma lura duk sanda kika zo wucewa sai kin dinga d’an juyowa kina dubawa. Ina sane na dinga miki duk tambayoyin da nake miki a aji sai na samu kina da matsananciya kunya. Wannan ma ya sake k’ara miki k’ima a idona. Hakan yasa kai tsaye naje gida da buk’atar azo min neman izinin fara zuwa zance wajenki. A take Abba ya ce wallahi in dai nine nake sonki ya ba ni ke, sai dai zai rok’i alfarmar a barki ki gama secondary saura shekara guda. Ba wanda ya ja da haka sai dai ni ba haka na so ba, na so a ce a yi bikin cikin wata biyu idan yaso ki k’arasa makarantar a gida na. Mommy ce ta dinga tausata. Abin kamar almara kullum Aysha k’ara min wutar sonki ake.. Yau da na ganki kina kuka a makaranta da k’yar na k’arasa musu karatun da nake musu. Allah ne ka’dai ya kai ni gida. Na dinga rok’on Daddy yazo a d’aura aure kawai amma ya k’i ya ce dole a bi maganar Abbanki ko shine ba zai aurar da y’arsa bata gama secondary ba. Still yanzu ma nazo naga kina kuka, AYSHA ki gaya min gaskiya ba kya son auren ne?” Ajiyar zuciya na sauke a hankali na d’aga kai na. Waro ido ya yi har yana mik’ewa ya iso gaba na a tsayen da yake hannayensa a k’irji ya furta “Ki gaya min gaskiya, da gaske ba kya so na, idan Kika sake tabbatar min zan hak’ura…” Jikina ne yake rawa na sake d’aga kai na.. Zama ya yi yana rik’e kansa naga sai murza goshinsa yake. Sai kuma na ji cikin sark’akkiyar murya ya furta “Ki furta da bakin ki, cewa ba kya so na…” Na d’aga leb’ena a hankali ina kallon k’wayar idonsa muryata na rawa na furta “Na ba yanzu zan yi aure ba sai na yi ko degree ne, am too young to marry…..” Ga mai son next page ya duba shafina na arewa zai samu page d’aya ko biyu bayan wannan. Page 11 @ ArewaBooks Danna link d’in nan Zai kai ka har page 11. https://arewabooks.com/chapter?id=669d122dc1b845b878dad215 Saboda yawan complain d’inku yasa na yi haka… dafatan za’a ni ha’din kai. Group 1 and 2 ya cika ga group 3 nan wanda bai samu ba ya shiga. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 12 ‎ Kashegari na lallab’a na yi shirin makaranta, don kawai na zame na je gidan su Mami na. K’arfin hali kawai nake don ko barcin kirki ban samu na yi ba. Don ma a ‘d’akin Umma nake kwana tunda Mami bata gidan. Ganin juye juyen da nake ya yi yawa, hakan yasa ina ji Umma ta saka baki ta kira suna na. “Mik’e AYSHA ki shiga toilet ki yi alwala ki yi sallolin nafila tunda barcin ya gagara. Na mik’e kuwa jikina a sanyaye na aikata abinda ta ce d’in, sai naga na samu sauk’in abinda nake ji a cikin raina. A kitchen na sameta tana dama kunun gya’da. Na furta “Umma zan tafi.” Ta ‘dago tana kallona kafin ta mik’o min cup d’in hannunta mai cike da kunun gya’da mai zafin gaske. “Shanye shi tas kafin ki tafi, kina nan kin sakawa kan ki k’wazzaba duk kin bi kin rame.” Ban mata musu ba na sha kunun don ni da kaina ina ji a jikina na matuk’ar ramewa don har kamar iska zata kwasheni. Ina shiga motar na ce da Baba Driver “Gidan su Mami zaka kai ni ba makaranta ba Baba.” Ya juyo yana kallona ya ce “Yau ba zaki makarantar ba Ayshatu?” Na d’aga masa kai, sai bai ce komai ba ya ja mota ya nufi da ni court road don anan gidan su Mamin yake. Shiru gidan har na shiga cikin harabar gidan ba kowa, don gidan sam ba yara sai Maman su Mamin duk an musu aure mazan gidan kuma wasu suna k’asashen waje karatu. Na shiga Parlorn gidan da yake k’asa inda anan step d’in benen yake. Mama ta dubeni tana bu’de baki. “Yarinyar Mami ce a gidan nan da safe haka, ina makarantar?” D’an murmushi na saki ban yi mata wasan da na saba mata ba ni jika da kaka. Na zauna a gefenta ina furta “Mama ina kwana?” Ba zan amsa ba Aysha, kin ga yarda kika dawo kuwa? Wace irin masifa ce kuka jefa kan ku haka ke da Uwar taki, ita ba nutsuwa ke ba nutsuwa, ku wato ba zaku yarda da hukuncin Allah ba kenan, dole sai kun ja da mahaifinki alhali dukkanku a k’ark’ashinsa kuke, ai ni ya min daidai wallahi wani Sokon Uba ne shi da alheri na binsa zai saka k’afa ya doke saboda wani bokon banza da wofi… ai idan nice a ranar da aka zo neman auren ma zan d’aura auren kowa ma bai ji ba bai gani ba. Mutum kamar Ustaz Ahmad da yake burge kowa, a cikin lafazin karatunsa zaka gane mutum ne mai nagarta…” idanuna ne suka kawo k’walla na yi shiru kawai ina jin zancenta. Ina ma y’arta zata zauna ta gane abinda Maman take fa’da. Amma Ai mun bari gini tun ran Zane, ni na san Ustaz ya yi zuciya ya bar ni daga yanayin kallon da ya min jiya. Ai shi ba k’aramin mutum bane da zai zauna ina masa walagigi da hankali. “Tashi ki je can wajen Uwarki, kada ki min kuka anan ba zan wani lallasheki ba, don ni bana bayan rashing gaskiya..” Na Mik’e kawai ina harha’da hanya na hau saman don na san a can zan samu Mami har yanzu yaran gidan kowa da d’akinsa. Na tura k’ofar na shiga, Mami tana kwance a saman carpet idanunta a lumshe kamar mai barci. Ta bu’de ido tana kallo na. Da sauri na isa wajenta, mik’ewa ta yi zaune tana bu’de min hannunta alamar na shiga. Na kuwa shiga ta Mayar ta rufe i ruf tana sakin ajiyar zuciya. “I missed you Mami na.” Ta lumshe ido tana furta “I mish you too Baby

Chapter 6 of 12