Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suka tafi dani wajen dinner. Wannan shine labari na da duk wata soyayya da muka gudanar da Ustaz. Hawayene ya gangaro daga idona na mik’e daga saman kujerar da nake ina bin d’akin Abba na da kallo. Tunani ne ya shiga yi min suntiri a zuciyata so nake na gano dalilin da yasa duk son da Ustaz yake min ya riki’de ya koma zazzafar k’iyayyar da ta kasa b’oyuwa a ransa har ta kai shi ga furta min kalmar saki a daren auren mu. Daren da Ustaz ya da’de yana gaya min ya ci buri iri iri a kansa. Burin ganin Aysharsa a zahirin Aysharsa ba tare da shamakin tufafi ba. Sai ga shi daren yazo mana a wani irin hagunce da namu burin. Menene sila? “MAMIN KI!” Na ji zuciyata ta amsa min a tsawace.. Da sauri na runtse idona ina girgiza kai da k’arfin gaske. Daidai sanda aka bu’de k’ofar d’akin aka shigo. Na dawo hayyacina ina binsu da kallo cikin dishi dishin idona. Yaya Muhammad, Ya Sadik, Ya Umar, fuskarsu a murtuke ba fara’a suke zubo min ido. Suka shigo cikin wani irin taku da yake nuna zallar b’acin ran da suke ciki. Zuciyata ta shiga bugu da k’arfin gaske na dinga bin su da kallo ina kallon yarda suka dogara k’afafunsu akan kujerar suka zagaye ni da idanunsu… Wani irin kallo suke jifana da shi, wanda na rasa a mizanin da zan saka kallon nasu. Na san dai kallo ne na Allah wadaran halinki… Sautin zuciyata ya sake bugu da k’arfin gaske jin Ya.Muhd ya kira sunana da sark’akkiyar muryarsa. “AYSHA! Gaya mana laifin me kika yiwa Ahmad ya sake ki a daren farko? Kada kice mana bakomai don hakan ma kin san ba zai yiwu ba. Ba auren k’iyayya aka muku ba, Ustaz kuma bai d’ora miki iddarsa ba balle a ce auren d’and’ano ya yi da ke? Me kika masa?” Ya fa’da a tsawace. Hawaye ne kawai yake kwarara daga ido na. Na shiga masa rantsuwa da a idonsa ka’dai na san rantsuwa ta ba inda ta je. Na ba shi labarin abinda na sani dangane da canja min da Ustaz ya yi a kwanaki ka’dan da Suka rage na bikin mu. “Mak’aryaciyar banza, wa kike tunanin zai yarda da wannan tatsuniyar taki? Ta yaya kike tunanin mutum ya aureki yana tsananin son ki Sannan ya sake ki a daren da aka d’aura muku aure? Dole akwai wani abu ki gaya min gaskiya kawai… kada ki bari zargin da nake a zuciyata ya tabbata don ni zuciyata na gaya min tabbas ke da uwarki sun san komai, Mami ba, tabbas akwai saka hannunta a cikin lamarin haka nake ji a raina…. Ji muka yi an turo k’ofar da k’arfin gaske, an shigo, idanuna suka fa’da cikin na Mami da suka ka’da suka yi jajur. “Umar! Ni kake zargi da mutuwar auren Aysha?” Ta furta a tsawace idanunta suna zubar da hawaye… Umar ya cije bakinsa yana jijjiga kai ya furta “Ai ba abin mamaki ba ne, tunda kowa ya san kina adawa da auren….” “Faruk!” Umma ta fa’da a tsawace tana nuna shi da yatsa. Tashin hankalin da kake son ka jawo mana kenan a gidan nan. Ta yaya kake tunanin Fateema zata cutar da Aysha ta hanyar kashe mata aure? Kada na sake ji… bana so wani irin zancen banza ne wannan..? Kana cikin hayyacinka kuwa… Gani muka yi Mami ta juya zata fita daga ‘dakin, sai dai shigowar Abba ya hanata don da k’arfi ya turo k’ofar shima idanunsa akan Umma ya furta wai menene?” Nan Umma ta shiga ba shi labari Mami dai bata ce komai ba illa ficewa da ta yi tana hawaye. Madadin Abba ya yi fa’da sai naga ya girgiza kai ya kalli su Ya. Muhd ya furta “Ku tafi masallaci Muhammad an yi sallah.” Suka fice a hankali. Umma ta dubeshi yana zama yana danna waya ta ce “Amma ka barsu suka fita baka wa Umar fa’dan abinda ya yi ba?” Jingina ya yi da kujera yana lumshe idonsa ya furta “Nima ina tunanin da Umar yake….” Ba shiri Umma ta zauna tana furta “A’a Abban Aysha kada ka fara irin wannan maganar don Allah…” wani kallo ya mata kafin ya cije bakinsa. Ya furta “Ina zargi na ce, kuma tabbas idan na tabbatar da zargina wallahi sakinta zan yi, ina jiran feedback d’in Ahmad, mun yi waya da mahaifinsa ya gaya min su basu san labarin sakin ba, amma sun yi waya da Ahmad ya sanar masa yana airport d’in Abuja zai wuce egypt, amma Babansa ya dakatar da shi ya ce ya juyo lalle a daren nan zai zo ya gaya mana koma menene…” Umma jikinta a salub’e ta mik’e tana furta “Allah ya kyauta.” Ta bar ‘d’akin. abba ya sake d’agowa a karo na biyu yana kallona ya furta “Kin tabbata baki san komai ba?” Na d’aga masa kai na. Ya girgiza kansa shima ya mik’e ya fice daga d’akin. Tausayin kaina ya sake kamani. Kuka nake sosai ba wanda ya sake bi ta kaina, tun bayan da Umma ta shigo ta kawo min tea ta rutsa ni sai da na shanye. Sannan ta fice daga d’akin. Har dare gidanmu tsit ba wani mai walwala, y’an biki tuni suka watse bayan an sanar musu ba wani abu bane, Ustaz ne tafiyar gaggawa ta same shi. Bayan Isha’i Iyayen Ahmad suka zo, Abba ya saka aka shiga da su parlorn sa na cikin gida. Ni dai gaba na kawai fa’duwa yake. Ba su wani da’de ba suka tafi. Sai ga Ya.Umar ya shigo da gudu yana furta “Umma fito Abba ba lafiya jikinsa rawa yake…” Da wani irin sauri Umma ta fito nima ban san sanda na fito daga d’akin Abba ba, na bi bayansu sitroom d’in Abban. Da wani irin tsawa Abba ya ce min “Fice Aysha haihuwar ki ba ta min rana ba, ku d’auka ku dubi hotunan nan ku ga irin b’atancin da cutarwar da ta yiwa nagartar gidan nan…..” K’afafuna na rawa na zube a wajen ina kallon takardun da Ya Muhammad ya zubo min, ido na ware ganin ba abinda ya b’uya a hoton daga tsiraicina komai na a waje, k’irji and everything gefe guda wani mutum ne zaune kusa da ni yana shafa k’irjina…. Na zunduma wani Uban ihu, ina jin numfashina na neman barin gangar jikina… Kash! Ina mai baku hak’uri, anan Book 1 ya k’are, sai dai ba zan yi jumurin kawo muku shi a kullum ba ta kafar whatsapp saboda wani dalili mai girman gaske, zan mayar da posting Litinin talata laraba da alhamis. Wato sau hu’du a sati. Sauran ranakun zan dinga posting a arewabooks. Y’an Arewabooks zasu dinga samu kullum In sha Allah. Dafatan za’a min uziri. Na gode sosai. Masu so arewa ku yi searching @nazeefah ko kuyi searching sunan Book d’in. Labari yanzu aka fara AYSHA bata ga komai ba sai nan gaba. Akwai book 2 akwai Book 3. Ganin rayuwar yana gaba… 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢✍️ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 12 of 12