Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tana furta “Ustaz!” Da mamaki a idonta, ta furzar da wani huci tana furta “Shine ma abinda ba zai yi wu ba cab’di! Kama sake nazari….” 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 9 ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR “Kamar ya?” Abba ya furta yana saka k’wayar idonsa cikin ta Mami. Amma sam yau Mamin wannan kallon na Abba na da alama bai ratsa ta ba, don tab’e bakinta ta yi murya a sama ta furta “Kamar komai ma Abban Aysha.. Ta yaya za’a aura mat Uztaz hakan na nufin makarantar da na ci buri akanta ba zata yi ba kenan? Wani Ustaz ne zai bar matarsa tana yawo a titi fisabilillah, da ma wani d’an boko ne da sauk’i. Amma wannan ha’din sam bai ha’du ba, in dai za’a min adalci akan Aysha a tuna bani da wata da nake gani a matsayin y’ata a bar Aysha ta yi karatu…” Ta fa’da idanunta suna zubar da k’wallar da ta sanya duk jikina sanyi. Amma ban hango sanyin gwiwa a wajen Abba ba, kamar yarda na hango shi a wajen Umma, don a raunane ta ce “Abban Aysha ka yi hak’uri ka janye maganar auren nan….” wani kallo ha hurgawa Umman da ya sata shiru da bakinta tana kallon Mamin a raunace. “Ba zan janye ba, har abada kuwa, don ba zan ga samu naga rashi ba, wani irin solob’iyon Uba kuke so na zama? Allah ya kawowa y’ata nagartaccen Mijin da kowane Uba yake fata sai na masa butulci sabida wani karatun boko na banza da na wofi. Mutumin da ko y’ay’a d’ari yake so za’a ba shi a rana guda, duka ta tsallake ya ce Aysha ce ta masa Aysha yake son aure sai na zuba masa k’asa a ido, Saboda wata maganar banza da wofi. Ita ka’dai ce fa y’ata mace da nake fatan ta yi dace da Mijin k’warai.. ko yanzu yake so na tsame ta a boko na mata aure wallahil azeem na shiryawa haka, ba abinda kuma zai saka ni fasawa. Karatu dai idan ya ce zata yi a gidanta falillahil hamdihi idan ya hanata ma gaba d’aya wallahi ba zan tursasa shi ba. Saboda ku iyayen banza ne ku da zaku saka ta ta yarda ku rarrasheta ku ke sakata ta bijire min? To ku je ku yi na da ku a ga wanda zai ci riba…” Daga haka yaja bakinsa ya tsuke ya kuma wanke hannunsa ya tsoma cikin tuwo ya cigaba da ci. Fuskarsa a ha’de sosai alamar duk abinda ya fa’da har k’asan zuciyarsa hakan yake. Mami ta ture kwanon tuwon da muke ci ni da ita da Umma ta mik’e fuska a ha’de ta fice daga parlorn. Jikina a sanyaye na mik’e zan bi ta Abba ya saka baki ya kira ni muryarsa a dake. “Dawo Ayshatu, zauna ki ci tuwonki, ba cutar da ke zan yi ba, har ga Allah alheri nake hango miki game da aurenki da Ahmad..” Na d’aga kai na ina wasa da zoben hannuna. “Ki kuma bu’de wayarki ki fara amfani da ita, na san ba zai cutar da ke ba. Ban kuma amince da duk wani tarkacen social media ba…” Na d’aga kaina don shima Ustaz garga’di da ya min kenan. Na san tunda suke ta jaddada min to social media d’in ba abu ba ne mai kyau. Cin tuwon kawai nake ba tare da ina fahimtar d’and’anonsa ba, don dai kada Abba ya yi magana ne na zage na ci tuwon kafin na mik’e cikin mutuwa jiki na haye sama. So nake na je naga Mami da halin da take ciki. Jikina a sanyaye na murd’a k’ofar d’akinta don bata parlour kamar yarda ta saba zama. A saman gado na sameta hannayenta dafe da k’unci da alama ta yi zurfi cikin tunanin da take. Zama na yi daf da ita ina d’ora kaina a saman kafa’darta. Sai na ji ta saki ajiyar zuciya. Ta rungumoni sosai a jikinta tana furta “Aysha, yanzu kin amince d a auren da Abba zai miki?” K’asa na yi da kaina idona na zubar da k’walla. “Mami kema ki yi hak’uri please…” Janye jikinta ta yi tana sakin wani malalacin murmushi “Na yi hak’uri Aysha? Na yi hak’uri Ustaz ya cuceni ya raba ni da duk wani farin cikina? Ya kuma ruguza min da duk wani shirina a kan ki da na shekara da shekaru ina shiryawa?” Ta girgiza kai tana taune leb’enta ta furta “Wallahi bai isa ba, mu zuba ko ni ko shi?” K’asa na yi da kaina saboda ba zan iya sake cigaba da juriyar kallon idanun Mami ba, don wani abu nake gani a cikin idon… Zamewa ta yi ta kwanta tana mayar da numfashi idanunta a lumshe. “Tashi ki tafi AYSHA, ta shi ki wuce d’akinki…” Ta fa’da a zafafe da sauri kuwa na mik’e ba fice don ban saba ko na ce ban tab’a ganinta a irin wannan yanayin ba… na lura daf take da fara Aljannu… Da safe har na shirya na gama shirin makaranta Mami bata tashi ba. Hakan yasa na nufi d’akinta ina nocking a hankali. A zafafe ta furta “Waye ne?” “Nice Mami…” ta bu’de k’ofar tana kallona idanunta kuwa da k’yar take lumshe su. Ta ja hannuna tana murzawa a hankali cikin wata irin murya ta furta “Ayshatu…” Na d’ago ina kallonta ta d’an sunkuyar da kai sai kuma ta saki hannun nawa. Tana sakin Malalacin murmushi ta furta “Har kin yi shirin makaranta?” Na d’aga mata kai “Ina kwana Mami?” Amsawa ta yi tana d’an ja baya ta furta “Wuce ki tafi AYSHA, ni ba abinda zaki ce min tunda kin zab’i farin cikin iyayenki a kaina. A jiya na yi takaicin rashin haihuwa da ni na haifeki da kaina na san ba zaki bujire min ba….” Kuka ne yazo min sosai ban san sanda na fa’da jikinta ba na saki wani irin kuka. Mami ta rungumeni sosai a jikinta ina jin yarda take sakin ajiyar zuciya. A kunne ta ra’da min “Kada ki bujire min Aysha, kada ki guje ni zan shiga wani hali AYSHA….” Da k’yar ta zame jikinta daga jikina ta juya bayanta tana furta “Je ki ki rufe min k’ofa…” Jikina a sanyaye na fice daga d’akin nata. A kitchen na tarar da Umma na tana ta aikinta ita ka’dai. Sai na ji duk ban ji da’di ba don koda yaushe tare suke aikinsu da Mami. Da wayona dai ba zan tab’a cewa ga ranar da suka yi aiki ba tare ba. Kallo guda ta min ta d’auke kanta tana amsa gaisuwata. Na juya zan fice ta furta “Ba zaki k’arya ba ne?” “Umma na k’oshi…” Umma ta bi ni da kallo mai kama da harara tana furta “Ki yi ta k’oshin mana Aysha? Cikin wa? Kin zata ni d’in uwarki ce da zan ta bin ki ina lallab’aki, kin bi kin k’i ki kwantar da hankalinki balle na uwarki ya kwanta sai kace a kan ki aka fara auren early marriage, sanda Ubanki ya auro ni 15yrs nake, ban ma kai ki ba me ya same ni? Mahaifinki dai kaifi d’aya ne, ba mai saka shi ba mai hana shi don haka ki nutsu ki san abinda ki ke. Ban tab’a jin kan Fateemah da Abbanku sai a yanzu da take son ta bujire masa, me ye ribarki idan kin haddasa sab’ani a tsakaninsu? Na ce meye ribarki AYSHA?” Shiru na mata ina bulbular da hawaye. Me yasa Umma zata ga laifina ce mata na yi bana son Ustaz? Bata san nafi kowa son haka ba? Tashin hankalin Mami ne kawai bana so nake b’oye hakan a raina.. “wuce ki bani wuri, ki shirya bujire masa kece zaki wahala don kin san ko magagin mutuwa kike Ubanki sai ya sadaki da gidan mutumin nan…” Na ja k’afata na fice daga kitchen d’in zuciyata a k’untace ranar na isa makaranta. Har na dawo daga makaranta ranar Mami bata mik’e daga saman gadonta ba. Ko kayan barcin bata cire ba. Na shiga na sameta na sanar da ita na dawo. Ta bi ni da kallo kafin ta saki ajiyar zuciya ta nuna min gefenta. “Zo AYSHA ki kwanta ki huta…” Ban k’i tayinta ba don ina buk’atar hakan na san kwanciya kusa da itan ne kawai zai saka na daina jin b’acin ran da nake ciki. Sau tari idan na saka jikina a jikinta ina samun nutsuwa idan ina cikin tashin hankali ko b’acin rai. Ta jawo ni na shiga jikin nata sosai. Hannu ta saka a bayana ta shafawa a hankali kamar yarda ta saba min. Muryata a k’asa sosai ta furta “Aysha me yasa kike son bujire min? Kada ki cuci kanki ki yi aure at your young age, zaki cuci kanki, zaki yi nadama nan gaba rayuwa ta canja. Ke ka’dai nake da hope a kanki AYSHA don Allah kada ki bujire min, ko me za’a miki kada ki amincewa auren Ustaz.. kin yarda.” Na d’aga kai sai naga ta saki ajiyar zuciya ta bani peck a kumatu tana sakin murmushi ta furta “Thanks my beautiful Baby, I love you..” Shiru na yi sai da ta d’an ja kumatu na ta furta “Ba zaki mayar min ba? Ko fushi kike da ni?” “I love you too Mamy..” na fa’da kamar yarda na saba fa’da koda yaushe idan ta furtar kalmar. Ta lumshe ido tana sake jana jikinta ta furta “Oya sleep…” zan yi magana ta furta “Shsssh!” A kunne na hakan yasa na lumshe idon dole. Take ni da Mamy barci ya d’auke mu. Barci da ba mu tashi farka wa ba sai da aka yi kiran sallahr la’asar. Na bu’de ido da sauri don na san tabbas yau na makara a makaranta. Mami bata san Ustaz yana koyarwa a makarantar mu don haka bata saka ido a kaina da zuwa makarantar ba. Ta bu’de idonta da k’yar tana kallona “Ya dai Aysha?” Na sauka daga gadon ina furta “An yi sallah Mamy, kuma zani Islamiyya.” Kanta ta rik’e a hankali tana d’aga min kai. Na fice da sauri. A gaggauce na watsa ruwa na yi shirin Islamiyya na fito da sauri. A d’aki na samu Mami daga ita sai rigar wanka. Ta mudubi take kallona ta furta “Kin shirya Aysha?” Na d’aga mata kai. “Zo ku shafa min mai a baya na.” Na isa wajenta da d’an sauri na zuba nan a hannuna ta zame rigarta na fara shafa mata. Ban wani damu ba don na saba shafa mata d’in. Kuma Mami ba ta damuwa da suturce kanta koda ina wajen abinda ya danganci k’irjinta kam bata damu ta b’oyeshi ba. Tun ina jin kunya har na saba. “Ada lafiya ta fa’da tana mik’o min chocolates masu d’an yawa. Tana furta “Ki tabbata kin cika min alk’awarina Aysha, kada ki sake ki amince da auren Ustaz..”. Na amsa na fice da sauri.. Ina shiga makarantar na tabbatar Ustaz na nan don ga motarsa nan, gaba na ya fa’di don na san na makara ba ta wasa ba. Amma haka na d’aure na nufi ajin. Harabar makarantar shiru duk an yi sallah an koma aji. Zuciyata na bugawa na isa k’ofar ajin fuskata a ha’de don ya kamata na fara janyewa Ustaz don na cikawa Mami alk’awarinta, ya zama dole na mata halacci musamman ganin ita bata haihuwa kada zafin ya mata yawa… Idanu y’an ajin suka zubo min, Har shi Ustaz d’in da ya tsayar da karatun da yake yana kallona. Na sake ha’de raina na nufi wajen zama na. “Aysha Imam Khaleel kin makara.” Ya fa’da cikin dakakkiyar muryarsa cak na tsaya ban k’arasa inda zan zauna d’in ba. Fuskata a ha’de na d’ago ina kallonsa. Ina ji kallon ne ya bashi mamaki. “Me yake damunki?” Juyawa na yi na fice kawai daga ajin. Ustaz na ji yana kiran “Aysha!” Na k’i na juyawa na koma saman step d’in na zauna kawai kaina a saman cinyata idanuna suna zubar da hawaye. “Tashi ki shiga aji.” Na ji muryarsa a kaina. Ban d’ago ba, ban kuma shiga ajin ba. “Ba kya ji ne Aysha?” Na d’ago a zafafe ina kallonsa na furta “Ni ba zan shiga ba, ka k’yale ni…” Cak ya tsaya yana kallona cikin narkakkun idanunsa ya furta “Ma Asabaki?” Wanda akan lab’b’ansa kawai na ji furucin. Ya lumshe idonsa ya furta “Tashi ki shiga..” Ba musu na mik’e jikina a sanyaye kamar zan shiga ajin sai na yi hanyar fita daga gate d’in. Ina ji Ustaz yana fa’din “Aysha tsaya…” Amma Ina na bawa banza ajiyar sa na fice har da d’an sauri na… Ina fita gate na juya naga Ustaz ya d’an rik’e kansa yana kallo na yana cije leb’ensa….. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://www.arewabooks.com/chapter?id=669e462086c5cb5aff79fe08 https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 11 ‎Runtse idonsa naga ya yi da sauri, kafin ya girgiza min kai, “Kada mu yi haka da ke Aysha, kada ki sakawa zuciyata ciwon da zai yi wahalar warkewa.” Sai naga ya durk’ushe a gabana idanunsa sun tara wata k’walla da ya k’ara idanun nasa kyau. Duk da akwai tazara a tsakani na da shi sosai ma, don na lura yana taka tsantsan k’warai da gaske wajen ganin ya kiyaye dokar Allah. “Ki taimaka min don Allah ki amince na aureki, ba yarda idan kin gama secondaryn sai Ai mana auren, duk da haka ma sai na yi k’ok’arin gaske kafin na iya daurewa, ni ka’dai na san me nake ji a kanki, ni na san irin yarda girman son ki yake a zuciyata, Please AYSHA will you marry me?” Runtse idona na yi ina jin yarda zuciyata ke matuk’ar gudu da tarin k’aunarsa a ciki, da gaske dauriya nima kawai nake da kuma son cika alk’awarin da na yiwa Mameey Amma ina ji a raina rashin Ustaz a rayuwata daidai yake da rasa rayuwar tawa. “Ki amsa min AYSHA, please za ki aure ni?” Wallahi ban san sanda na d’aga kai ba, Saboda wani irin kallo mai azababben kyau da Ustaz ya dinga zuba min da narkakkun idonsa. Gani ya yi ya dunk’ule hannunsa duka biyun yana sakin ajiyar zuciya ya furta “Shukran ya Rabbi, Shukran ilaiki Ayshata…” Ya mik’e yana sake kallon Table bayan ya ajiye wata leda a kusa da ni. Ya furta “Yau ma AYSHA ko ruwa babu?” Sai kunya ta kama ni na yi k’asa da kai na, ina wasa da zoben hannuna. Murmushi mai sauti ya saki. “Shikkenan tunda rowa kike min, na gode..” ya yi furucin da karyayyiyar murya. Da sauri na girgiza kai ina furta “Ai ban san zaka zo ba…” “Ta ya zaki san zan zo bayan kin k’i picking call d’ina, kina hora ni saboda kina tunanin kin yi yarinya sa aure ko?” Ya furta yana d’an murmushi ha’de da cije leb’ensa ka’dan. “Allah ya nuna mana lokacin, Jibi zan wuce Egypt, zan samu one week a can. Idan na dawo kashegari zai kama litinin anan zan sha ruwa. Ina jiran girki mai kyau daga wajen kyakykyawar budurwata, za ki yi min?” D’aga kai na yi da sauri ya yi dariya “Kamar gaske Allah yasa kin iya girkin.” “Allah kuwa na iya..” Ya mik’a min hannunsa “Zamu gani ai, Allah ya kai mu ranar kuma ban amince kowa ya tayaki ba. Kina girkin muna vedio call, ba ni zoben hannunki.” Na waro ido ina girgiza kai. “Ai ya yi maka ka’dan, ji fa hannunka.” Ya kai duba zuwa hannunsa “In dai ba rowa zaki min ba, ai sai ki bani na gwada na gani, ko ya yi min ka’dan ina so zai min rakiya Egypt..” Na zare zoben ya nuna min gefen kujera “Ajiye a nan, Zan d’auka.” Na kuwa ajiye ina sake girmama halin Ustaz na kiyaye dokokin musulunci. Ya ‘d’au zoben ya saka a k’aramin yatsansa sai ga shi kuwa ya ‘dan shiga. Sumbatar zoben ya yi a hankali yana lumshe ido ya furta “Ina sonka zobe, Saboda ka fito a hannun AYSHA ta..” Ban san sanda na saki murmushi ba ina jin kamar ni Ustaz ya sumbata.. Daga haka ya fice daga sitroom d’in yana sakin murmushi… Tunda na saka k’afata a benen Mami, na ji gabana yana fa’duwa, fatana Allah yasa ta yi barci. Da san’da na tura k’ofar parlorn sai dai ba kamar yarda na yi tsammani ba, Mami na nan idonta biyu. Tana zaune a kan kujera ko T.V bata Kunna ba. K’afarta ta ‘dora ‘d’aya saman d’aya tana girgiza ta fuskarta a ha’de sosai. Jikina a sanyaye na k’arasa kusa da ita na zube a gabanta… “Mami na, don Allah ki yi hak’uri ki yafe min laifi na, wallahi ban yi don na b’ata miki rai ba, na yi ne don bin umarnin Abba….” “Abba ba? Dole ki bi umarninsa tunda shi ya kawoki duniya, ni mecece a wajenki da na wuce Uwar goyo, ba abinda zaki ce min kin zab’i iyayenki a kai na sakamakona kenan a wajen ki Aysha? Duk da tarin k’aunar da na nuna miki?” Ta fa’da wata k’walla na zubo mata. Nima kukan na saki, jijiyoyin kaina suka d’aure na dinga kuka mai tafe da ajiyar zuciya. Ta matsar da ni daga jikinta tana mik’ewa ta nuna min k’ofa “Sauka min daga bene AYSHA ki koma wajen iyayenki da kika fi k’auna….” A tsorace na dinga kallonta jin furucinta kuma na hango tabbas da gaske take har k’asan zuciyar ta . Hannunta na kama da sauri ina furta “Me yayi zafi haka Mami na? Duk duniya ba ni da kamarki, Abba da Umma kawai haihuwata suka yi, amma ke kika ci dukkan wahala da ni, kika bani tarbiyya kika kula da ni da jiki da aljihunki me yasa zan bujire miki?” “Zaki bujire min ne AYSHA saboda d’a namiji, d’a namijin da nan gaba idan ya kuntaka miki iya shege sai kin yi dana sanin ha’duwa da shi, d’a namijin da idan nan gaba ta ciyoshi zai auro wayayyiya mai ilimi ke kuma ya mayar da ke Bagidajiyar gida… Ilimi shine garkuwarki don haka ki yiwa kan ki fa’da ki rabu da shi ki zab’i karatunki…” Runtse idona na yi na furta “Ya ce zai bar ni na yi karatun har sai na ce ya isheni…” “K’arya yake AYSHA yana samunki, zai manta da wannan alk’awarin, bana burin nan gaba ki zama k’ask’antacciya nafi so ki zama tauraruwa a cikin duniyar mata masu ilimi, ta yarda zaki shiga ko ina a goga da ke… Ki bijirewa auren nan AYSHA in dai ba so kike na ‘d’auka har a raina don kun san bana haihuwa ba ne bani da kuma y’ar da zata shafe min hawaye…” Fa’dawa jikinta na yi ina furta “Zan share miki Mami, wallahi zan share miki kuma na hak’ura da Ustaz ko da hakan na nufin rasa dukkan farin ciki a rayuwata…” Murmushi ta saki tana sake rungume ni a jikinta. “Ba wani farin ciki da zaki rasa Aysha, farin ciki yanzu ma kika fara in dai zaki rabu da wancan mutumin ni kuma zan baki farin cikin da har sai kin dinga mamaki, zan maye miki gurbin Uba, Uwa da shi kansa Mijin…” na d’aga kai ina sakin ajiyar zuciya a hankali. “Ba ni wayar da ya baki?” Hannuna na rawa na mik’a mata. Naga ta danna wajen kashewa ta kasheta tana murmushi “Bak’in mugu sai dai ka auri wata ba AYSHA ta ba…” ta fa’da tana mik’ewa ta shige d’akinta “Ki je ki yi wanka ki kwanta, Maganar wannan mutumin close har abada…” wani irin yawu na ha’diye da k’yar ina mik’ewa na ji kaina ya sarawa na rik’e kan da k’yar na isa cikin d’aki, ina ji kamar Mami ta raba ni da wani sashe ne na rayuwa ta.. Tun daga ranar na rasa duk wani farin ciki da walwala. Sai dai ina k’ok’ari sosai wajen danne hakan don kada Mami ta gane. W Ranar kwana uku da faruwar lamarin Mami ta fita, Umma ta hawo sama, ta shiga d’akin da nake a kwance ta sameni idanuna na kallon ceiling ta tsaya a gefen gadon. Ganinta ya saka ni yin firgitgit ina kallonta. Ajiyar zuciya ta saki ta zauna a gefen gadon tana furta “Ta shi Aysha magana za mu yi, a matsayina na uwar da ta haifeki na san kin kwana da sanin cewa ba zan cutar da ke ba.” Jikina a sanyaye na mik’e na zauna idanuna na kawo ruwa sai na ji kawai ina son na yi kuka a jikin Umma na. Fa’dawa jikinta na yi na saki kukan bata hana ni ba sai ma sake rungume ni da ta yi a jikinta. Na yi kukan sosai kafin ta ‘dago ta share min hawaye ta furta “Me ke damunki?” Girgiza mata kai na yi “Bakomai Umma.” Murmushi ta saki tana gigiza kai “Ba zai zama bakomai ba AYSHA tabbas Akwai komai, ni na san kina son mutumin nan Kuma kin amince da aurensa, me yasa kuma kwana biyu kika canja? Ga shi kullum kina d’aki ba kya walwala, Aysha ina son ki bu’de kunne ki ji ni da kyau. Bin Umarnin mahaifinki wajibi ne gareki, ki amince da auren nan kafin ki zo kina nadama, me yasa ba kya amsa wayarsa alhali kin san baya gari? Ya kira Abbanku yana tambayar lafiya idan ya kira wayarki bata yi? Ina wayar taki take?” Umma ta furta tana min kallo mai cike da k’auna da rarrashi. A hankali na furta “Tana wajen Mami.” Murmushi naga ta yi ta mik’e tana fa’din ki tashi ki yi wanka ki sauko ki ci abinci bana son zaman ‘d’akin nan.” Na mik’e a hankali na shige toilet d’in. Umma har ta tara min ruwa na shiga wankan sannan ta fita daga d’akin. ———— Kashegari da safe naga duk k’annen Abba maza sun zo gidan. Ban san me ake ba ni dai na shirya na tafi makaranta. Da na dawo kuwa rigima na tarar a gidan wai ashe ku’din aurena aka kawo da sa rana gaba d’aya.. Shine Mameey ta fito tana masifa a tsakargida na ganta da Umma tana janta da akwatin ta tana furta “Wai Fateema meye haka kina cikin hankalinki kuwa? Saboda za’a aurar da Aysha zaki bar gidan nan…” A zafafe ta janye hannunta. “Cika ni, gwara na tafi meye amfanin zama na a gidan da baa san daraja da k’imata ba, ashe dama kun bani y’ar ne don ku wulak’antani ku nuna min bani da iko da ita. Zan bar gidan tunda ba Uban da na ajiye, ku je ku yi ta aurar da ita….” Da gudu na iso wajen na zube a jikinta, jikina yana kakkarwa na furta “Please Mamy ba inda zaki, ba Zan aure shi ba wallahi, tunda dai baki amince ba…” “Ashe kuwa sai dai idan ba ni Iman ba ne na haifeki Aysha, aure ba fashi..” Mami ta juyo tana kallonsa “Kada Allah yasa ka fasa Imamu, ga y’arka nan ka aurar da ita, amma ni na gama zaman gidanka…” Hanya ya nuna mata yana juyawa a zafafe cikin parlorn sa. Mami ta wancakalar da ni ta ja akwatin ta da sauri zan bi ta Abba ya daka min tsawa da sauri na durk’ushe a wajen ina jin tashin motar Mamin. Na runtse idona da k’arfin gaske, ina jin wani irin b’acin rai Yana dugunzuma zuciyata… Wannan wani irin bal’ai ne tabbas zuwan Ustaz rayuwata ba abinda ya haifar sai fitina a cikin gidan mu, abinda ban tab’a gani ba, sa’insa tsakanin Iyayena da Abba. Ranar sam zuciyata bata da nutsuwa na ji a raina sam na shirya rabuwa da Ustaz. Nan da nan labari ya kara’de danginmu an bada ni an saka min rana. Aka yi ta zuwa Allah ya sanya alheri. Mami kuma bata dawo gidan ba tashin hankalina kenan… Ranar lahadi Ina zuwa makaranta naga motar Ustaz. Mamaki ya kama ni na fara tunanin a yau d’in da ya dawo yazo kenan. A aji na same shi a zaune da wasu tsirari daga cikin ajin. Ido ya ‘dago yana kallona sai naga kamar har rama ya

Chapter 5 of 12