kuka. Shima
Arufa sia ya rukunkume Hazila ya kama kukan. Anan
aljani Karbalu ya basu labarin abin da ya faru a can
bakin kogin tsuburin rayuwa. Kuma ya umarceta da ta je
ta sanar a fada domin a zabi sabon Sarki.
Yayin da Hazila ta isa fada ta sanar da wannan
mummunan labari, sai hankalin gaba daya 'yan majalisa
ya dugunzuma aka rasa yadda za'a bullowa al'amarin,
domin a wannan lokaci Sarki Hurmas ba shi da magaji
sai kani, wani shagalallen dan giya wanda ake kira
Himaru.
Kullum, ko yaushe, kumá dare da rana, Himari na
gidan giya. A tarihin rayuwarsa bai tafa tsinanawa
kansa komai ba. Kuma duk abin da ya mallaka sia dava
kare a gidan giya da wajen karuwai. Bisa daiilin hakan
ne ma dan uwansa Sarki Hurmas ya kore shi daga gidan
sarautar ya koma kwana a kwararo, ya wulakanya ainun,
ya zamo a cikin talauci da yunwa. Sai yaje ya yi aikin
karfi sanann yake samun abin da zai ci. Amma ana
biyan sa kudin aiki babu abin da zai fara ta kansa sai
giya. Sai da Himaru ya shekara goma sha bakwai a cikin
wannan rayuwa ta kunci da talauci, bashi da dan uwa ko
aboki face giya.
birnin Dulkar suka Lokacin da 'yan majalisar
zauna taron gaggawa bisa wannan matsala ta nada sabon Sarki, sai suka yi ta mahawara. Wasu suka ce ai dole ne
a sauya doka da al'ada, domin mutane ba za su iya karbar Ilimaru a matsayin Sarki ba: Wasu kuwa suka ce, "Ai dole abi doka, wacce ta ce babu wanda ya isa ya shugabanci wannan daula face wanda ya"zamo jinin gidan sarautar. Bayan an jima ana mabawara ne aka yanke hukuncin cewa akamo Himaru a tsare shi tsawon kwana arba'in, ya zamana baisha giya ba, sannan a sauya masa tunanin sa da rayuwarsa a cikin kwanaki arba'in domin ya zamo nutsatstsen mutun, wanda ya san ya 32
kamata. Da aka gama wannan shawarar ne kuma aka
rasa wanda ya dace a sashi ya sauyawa yarima Himaru
rayuwa, domin babu wanda ya isa ya yi masa dole, babu wanda yake shakka a duniya face dan uwansa sarki
Hurmas. Nan fa kow aya yi shiru, aka shiga tunani.
Daga dan sai Wazirin kasar wanda ake kira Kalumul
Wazabu ya ce, "Abin da za'a yi shi ne, aje ayi bincike ko
da akwai karuwar da Himaru ke matukar so daga cikin
karuwansa. Lallai ita ce kaďai za ta iya wannan aiki."
Nan take aka wakilta Sarkin doharai da Galadima
akan su je su aiwatar da wannan aiki a cikin kwana
goma. Sannan kuma aka aika wadansu zakwakuran
dakaru su arba'in aka ce su je su dauko yarima Himaru
da karfin tsiya su kaishi gidan sa na cikin gidan sarauta
su kulle shi a ciki, kuma a tabbatar da kula da lafiyarsa.
Ba dan komai akai haka ba, sai domin an san cewa
yarima Himaru karkarfa ne na gaske, in ba'a tura masa
mazan kwarai ba ba za'a iya zuwa da shi ba.
Koda aka gama zartar da wannan hukunci, sai taro
ya watse, kowa ya kama gabansa.
Wannan shi ne abin da ya faru a birnin Dulkar
bayan an gama azababben yaki acan bakin kogin da ya
zagaye tsuburin rayuwa.
***
A can birnin Sharmura kuwa, lokacin da labari ya isa
cewa an kashe Sarki Darusul Hamanu, da dakarunsa a
kusa da tsuburin rayuwa, sai hankalin jama'a ya
dugunzuma aka shiga bakin ciki da damuwa. Ba wani
abu bane ya tayar da hankalin jama'a ba face sarki
Darusul Hamanu ba shi da da ko dan uwa, face matarsa
guda daya, wacce ba ta fi shekara ashirin da takwas ba a
33
duniya. Bisa al'ada da dokar wannan daula kuwa, ba'a yarda mace 'yar kasa da shekara arba'in ta zan
sarauniya ba. laka kuma ba'a yarda wanda ba jinin
sarauta ba ya shugabanci jama'a. Ita kuwa wannan mata
ta Darusul Hamanu iya ce kadai jinin sarautar gidan.
Amma kuma gashi shekarunta ba su kai arba'in ba. Nan
fa 'yan majalisa suka zauna har tsawon kwana uku suna
ta muhawara akan yadda za'a fullowa al'amarin. Amma
ba'a sami mafita ba. Daga karshe sai aka yanke shawarar
cewa za'a yiwa matar sarki jarrabawa guda uku, idan ta
ci wannan jarrabawa shi kenan sai a bata dama ta zama sarauniyar Darul Hashmar kuma ko nan gaba idan aka
samu matsala irin ta ta irin wannan jarrabawa za'a sake yi. Nan take 'yan majalisa suka yarda da wannan hukunci.
Jarrabawa ta farko ita ce, za'a kama matar sarki a
kulleta a kurkuku har tsawon kwana goma ana yi mata azabar yunwa da ta duka, domin taji irin abin da makaskanta ke ji a jikinsu. Idan aka fito da ita sai a
tambayeta ace idan kika zamo sarauniya wace irin kyautatawa zaki yiwa talakawanki? Kuma wace irina zaba za ki yiwá masu lafi? Ana son aji abin da za ta fada
domin aji irin tunaninta kaifin basirar ta,da kuma tausayinta ga jama'a da sanin ya kamatanta.
Jarrabawa ta biyu ita ce, za'a kirkiri yaki na kwana
oma kuma a bata jagorancin yakin domin a ga iyakar kokarinta da kwazonta. Idan ta yi nasara ta haye mataki
a biyu kenan.
Jarrabawa ta uku íta ce, za'a rabata da duk jin dadi rin wanda ta saba da shi, sannan akaita tsakiyar daji mai
nisa daga cikin gari, inda babu gida gaba ko baya, dan aga yadda z ata iya ceton kanta ta dawo gida.
Da amicewar 'yan majalisa aka tashi daga taron. Sannan aka je aka kamo matar Sarki wadda a lokacin ana kiranta da suna Lubaisa, aka kaita cikin wani kurkukun duhu aka kulleta. Kullum sai an yi mata bulala goma, kuma sau daya ake bata abinci. Al'amarin da ya daurewa Lubaisa kai kenan, ya zamana ba ta da aikin yi face kuka da bakin ciki, saboda tunanin cewa 'yan majalisa sun ci amanar mijinta. Kuma tabbas so ake a
hallakata domin a baiwa wani sarautar.
Lokacin da Lubáisa ta kwana goma cif a cikin kurkuku, aka fito da ita aka kaita wani daki mai haske,
sai ta kasa bude idanunta, saboda idanun na ta sun saba
da ganin duhu, sai da kyar ta buďe a hankali. Tana bude
idanunta ne ta cika da tsananin mamaki, domi gaba daya
'yan majalisa ta gani a zazzaune bisa kujeru a gabanta.
Cikin fushi Lubaisa ta dubi waziri ta ce, "Mene ne
ma'anar wannan rashin mutunci? Idan har so kuke ku ci
amanar mijina ku yi saurin hallakani mana?".
Koda jin wannan batu, sai waziri ya yi murmushi
ya ce, "Ki gafarce mu ranki ya dade. Ki sani cewa ba
hallaka ki zamu yi ba, muna so ne mu gabatar da
wadansu jarrabobi guda uku gareki saboda wata babbar
hujja. Yanzu mun gabatar da ta farko, sai ki saurari
ragowar guda biyu. Kar ki yi gardamar komai, yanzu
muna son ki amsa wata tambaya. shin-idan kika zamo
sarauniyar Sharmura wane irin mulki za ki gudanar ga
jama'ar ki?".
Ya yin da Lubaisa taji wannan tambaya sai ta ce,
"Zan wadata talakawa da abinci, ba zan yarda a yi
yunwa a fasata ba. Kuma ba zan yiwa mai laifi azaba
ba, sai na tabbatar da laifinsa, kuma zan sassauta wajen
hukunci. 35
Koda gama fadin haka, sia gaba daya 'van
majalisar suka yi murmushi a gareta. Waziri ya ce,
"Muna taya ki murna kin haye mataki na farko."
Kafin Lubaisa ya ce wani abu an kashe fitulun
dakin, dakin ya yi dumdin. Kawai sai ji ta yi an dauketa
an tafi da ita. Sai da ta kwana a cikin wani daki daban ba
ta ga haske ba.
Kawai sai farkawa ta yi taji hayaniyar mutane
ınasu yawa, da kuma hayaniyar dawakai, kuma idanunta
a rufe suke da kyalle. Cikin sauri ta cire kyallen, kawai
sai ta ga ashe akan doki take, kuma a tsakiyar dakaru
cikin snigar yaki. A can daya bangare guda kuma wasu
dakaru ne cikin shigar bakaken kaya. Kawai sai Lubaisa
yaji daya daga cikin dakarun da take ciki ya ce, "Ranki
ya dade umarninki muke jira, ya zamu yi da abokan
gaba?".
Lubaisa ta dubi mai maganar ta ce, "Mu afka musu
kawai". Kafin wani ya yi wani yunkuri tuni Lubaisa ta
zare takobin ta ta yiwa dokinta kaimi ta durfafi inda
abokan gaba suke.
Koda ganin haka sia sauran dakarun na ta suka kai
mata fauki. Kafin su isa ma tuni ita ta fara ragargazar
su. Nan fa wuri ya yamutse, aka yi ta fauki ba dadi
kamar ba za'a daina ba.
ba
Koda masu bakaken kayan suka ga na ci karfin su
sai suka ranta ana kare, suka watse. Nan dakarun
Lubařsa suka kewaye ta suna mata jinjina. Ba zato
tsammani sai Lubaisa taji an cakumeta an daure
hannayenta ta baya, kuma an rufe idonta, aka sunkuceta
aka yi gaba da ita. Kawai sai ji tayi ana tafiya da ita akan
doki cikin gudu. Sai da aka shafe kusan sa'a shida ana
36
tafiyar
dokar
da ita, sannan aka tsaya aka ajiye ta a tsakar daji, sannan aka gudu aka bar ta. A wannan lokaci Lubaisa ta jigata ainun, sannan ga yunwa da kishirwa sun fara addabarta. Sai da ta jima a kwance tana mutsu-mutsu, ta rasa yadda za tayi, domin har yanzu hannayenta a
daure suke ta baya, kuma fuskarta a rufc take..A
hakan ta fara kokarin zura kafafunta ta cikin hannayenta da ke baya, har ta samu suka shige cikin hannayen da kyar, wanda ya zamana hannayentá sun dawo gaba. A sannan ne ta samu damar cire kyallen
da ya rufc mataidanu, ta ga ashe a tsakiyar dokar daji take, babu gida gaba ko baya. Dajin ya kasance mai duwatsu kawai, babu bishiyu, babu kogi ko fadama.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalinta kenan,
domin ta san cewa in dai ba ta samu ruwan sha ba,
nan da dan wani lokaci, tabbas komai zai iya faruwa da rayuwarta.
Nan take ta sake kokartawa, ta kwance igiyar
da ke hannunta, sannan ta kama tafiya a cikin dajin
ba tare da sanin inda ta dosa ba. Lubaisa na tafe ne
tana rangaji a hanya kamar wadda ta sha giya ta
bugu, zuciyarta cike da sake-sake. Tana mamakin
yadda ta tsinci kanta a cikin irin wannan muguwar
rayuwar bayan mutuwar mijinta. Babu abin da ke
kara ba tamamaki face maganar waziri da yake
cewa, wai suna yi mata wadansu jarrabobi ne.
"To akan me za a yi min jarrabawa? Anya
kuwa mutanen nan ba wata makarkashiya suke
shirya mini ba? Tabbas mutum da ban tsoro yake,
domin za'a iya min irin makircin da gimbiya Zalfirat
ta yi wa Abu Mansur da dansa Halifa ta zauna da su
har tsawon kwana arba'in, sannan ta yaudare su ta
kai su SANSANIN AZABA."
Lokacin da sarki Maharaz ya zo daidai nan a
labarinsa, sai jama'a suka ga sararin samaniya ta yi
bakikkirin ta cika da wadansu irin tsuntsaye marása
adadi. Koda tsuntsayen suka yo kasa, sai aka gane
cewa ashe aljanu ne dauke da dodanni da kuma
mutane. Gashi nan birjik iyakar ganin idanu, ba su
da adadi, kuma kowanne su na dauke da mugun
makami. Gaba dayansu suna karkashin jagorancin
gimbiya Abidatul azmal ne.
Ko da mutanen birnin Nurul Kalbi suka ga
wannan gagarumar runduna tana kokarin saukowa
cikin birninsu, sai aka kama guje-guje da iface-iface.
Sai da ya zamana babu kowa a filin fadar face sarki
Maharaz da su sadauki Kurbas, da kuma manyan
Malaman garin su goma.
Nan take Maharaz ya dakawa jama'a tsawa, sai
kowa ya tsaya cak a inda yake. Kawai sai ya bada
umarnin kowa ya dauko makamansa na yaki. Yara,
mata da tsofaffi kuwa, ya ce a kai su can wani gida
da ke karkashin kasa. Kafin a ce wani abu jama'a
sun bi wannan umarni.
A sannan ne fa bakin sama suka fara durowa Kasa aka ruguntsume da azababben yakin da babu shiri,
Karfin
wanda a zahiri ko ba a gwada ba linzami ya fi bakin kaza.
To amma fa babu mamaki wannan kazar ta iya daukar wannan linzami, sai dai abin da hali ya yi. Shin waye za su sami nasara a wannan gagarumin yaki tsakanin mutanen birnin Nurul Kalbi da tawagar sarauniya Abidatul Azmál?
Ya ya soyayyar Abidatul Azmal ga sarki Maharaz za ta kasance?
Shin sadauki Kurbas da Gimbiya Zuhura za su
yi soyayyar zahiri?
Ina labarin 'ya'yan yarima Himal wadanda aka
baro su a can birnin Babila?
Mu hadu a TASKAR TSAFI 3 dan jin karshen
wannan labari.
Mai debe muku kewa;
ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels