Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
TASKAR TSAFI 2

TASKAR TSAFI 2

by Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

0 Hours
26, Jan 2026
Unknown group
Not Inserted
Free
60.71 kb
TXT
37+
26+
Last download 14 minutes ago

You cannot download this book until you log in, but you can read it.

Read Now

OR

Description

lokacin bakon aljani ya tsarewa hadiman Lsarauniya Abidatul Azmal dauke da su,
Hasilatul Kurbas bai sauke su a ko'ina ba, sai
a tsakiyar wani daji mai yawan duhuwa. Ya sauka a kofar
wani dutsc.
Akan buzu a kofar kogon wani kyakkyawan saurayi
ne sanye da fararen tufafi ya rike carbi yana lazimi.
Su dai su Hasilatul Kurbaz tun da wannan aljani ya
sace su suka kasa, magana, dan tsananin mamaki duk
tsawon tafiyar da suka yi a sararin samaniya dayansu bai ce
uffan ba kawai dai sun yi zuru ne su ga ina za a kai su da
dalilin da ya sa aka ceci rayuwarsu.
Da bakon aljanin ya sauka a gaban wannan
kyakkyawan saurayi sai Hasilatul Kurbas, yarima Himal da
sadauki Kurbas suka sauko daga kan aljani suka yi tsaye
kawai suna kallon wannan saurayi da ke wannan ibada.
Jim kadan sai saurayin ya hattama ibadarsa, sannan
ya waigo ya dubi bakon aljani ya ce, "Ya Marwanul
Hasabu a ina ka samo wannan mutane haka, kuma
sabodame ka zo min da su nan?"
Ko da jin wannan tambaya sai Marwanul Hasabu ya
rusuna yana mai dukasr da kai kasa ya ce, "Ya shugabana
kamar yadda ka sani cewz ka umarce ni da na dinga kai
dauki a duk lokacin da na ga za ai zalunci, a yau ma hakan
ce ta faru gare ni. Ka sani cewa a wasu sa'o'i kadan da suka
wuce a yau na je giftawa ta nahiyar birnin Kusa da cikin
daji da aka gina wani katafaren kurkuku sai na ga wannan
mutane a cikin mugun hali, kuma sai na ga wadansu
bakaken aljanu suna shirin afka musu. Dan haka sai na yi
sauri na dauke su daga wajen. Na so na bar su a wani
wurin, to amma sai na yi tunanin cewa ya kamata na kawo
su gare ka, wata kila zuwan na su ya zamo alheri."
Sa'adda aljani Marwanul Hasabu ya zo nan a
zanccnsa, sai kyakkyawan saurayin nan ya yi murmushi,
har kyawawan hakoransa farare sol suka bayyana, sannan
ya mike tsam daga kan buzun da yakc zaunc ya tako
Kafafunsa ya taho wajen su sadaukai Kurbas fuskarsa cike
da annuri, tamkar wata dan daren goma sha biyu. Ya cc,
'Ya ku wadannan baki, muna yi muku barka da zuwa
nahiyar birnin Nuruł Kalba: Ni sunana Maharaz bin
Makawi. Ni ma'abocin addinin Musulunci ne, kuma nan
inda kuke shi ne dajin Karusa. Daga nan zuwa cikin birnin
mu na Nurul Kalbi, tafiya ce ta sa'a bakwai kadai. Wannan
bawan Allah da ya cici rayuwarku abokina ne, bisa yada
addininmu cikin duniya. Ba wani abu ne ya fito da ni daga
cikin birnin mu ba, face kokarin daukaka addinina. Ina
tabbatar muku da cewa ba zan kasance mai cutarwa ba a
gare ku, idan babu damuwa zan so ku biyo ni izuwa cikin
kogon nan domin ku huta, kumaku ci ku sha, sannan ku ba
ni na ku labarin."
Yayin da su sadauki Kurbas suka ji wannan jawabi,
sai suka kwantar da hankalinsu, kuma suka amince akan za
su bi Maharaz izuwa cikin kogo.
Maharaz ya dubi yarima Himala ya ga kafafunsa da
hannayensa a daure suke da manyan sarkoki, kawai sai ya
ce, 'Bismillahi Rahmanir rahim." Sannan. sai ya shafi sarkokin hannunsa da kafarsa. Take sarkokin suka zube
kasa tamkar dora su a kai a jikinsa ba daurewa ba.
A'lamarın da ya matukar daurewa su Hasilatul
Kurbas kai kenan, suka firgita da al'amarin maharaz. Ba
tare da bata wani lokaci ba Maharaz ya wuce gaba
izuwa cikin kogon, su kuma suka bi bayansa kamar ana
jan akalar rakumi.
Cikin kogon ya kasance wuri mai fadi, kuma a
haskake yake, alhali babu fitila ko daya a cikinsa. An
shimfida wania babban buzu a wajen, sanann a gefe
daya tulu ne na ruwa da 'ya'yan itatuwa iri-iri,kamarsu
inibi, faure, gwanda, ayaba, da sauransu.
Nan take Maharaz ya zauna akan faffadan buzun,
sannan ya yi wa su Kurbas izinin zama, suka zauna.
Maharaz ya dauko 'ya'yan itatuwan ya zube a gabansu.
sanann ya zuba musu ruwa a cikin kofunan kasa su
duka.
Nan fa kowannensu ya cika cikinsa. Bayan sun
gama ne Maharaz aya dubi yarima Himal ya ce,"Ya kai
abokina, yanzu sai ku bani labarin ku ko?".
Himal ya yi gyatsa ya ce, "Ni sunana Himal, kuma
na kasance da ga sarki Asmaru na birnin Babila.
Wannan kuwa matata ce, sunanta Hasilatul Kurbas. Shi
kuma wannan babban mutum sirikina ne, wato mahaifin
Hasdatul Kurbas, kuma shine sarkin yakin birnin
Babila".
Nan dai Hımal ya kwashe labarinsa kaf ya
zayyanewa Maharaz. Yayin da Maharaz yaji wannan
batu, sai vavi shiru yana tunani izuwa wani dan lokacı
Sannan ya dago kai ya dubesu daya bayan faya, sannan
ya cc."a ku wadannan mutane, ku yi sam cewa
rayuwar ku na dikin hadarn matuka, domin na san waye
sarkin ku, kuma na san ko wacece saraumya Abidatul
Azmal, domun ta kasance ya ga sarkı Azmal bn Taufid,
sharraen matsafin da ya mutu akan burin son ya mallaki duniyara nan gaba dayanta, kuma har yanzu 'yarsa na
kan wannan buri. Tabbas yanzu duk inda za ku shiga san
Abidatul Azmal ata neme ku ta hallaka ku. Waje daya ne za ku iya zuwa ku tsira da rayuwar ku, wannan wuri kuwa shi ne garinmu, wato Nurul kalbi".
Cikin yanayin mamaki sadauki Kurbas ya dubi Maharaz ya ce,"Saboda me ya zamana a garin 'ku ne zamu iya kubuta?".
Koda jin wannan tambaya sai Maharaz ya dubi Kurbas ya ce, "Amma fa na yi mamakin jin wannan tambaya daga bakin ka, domin a zatona kasan lokacin da
sarki Azmal ya yi gaggarumin yaki da wani sarki wanda ake kira Ayubul Hasmanu."
Sadauki Kurbas ya jinjina kai ya ce, "Kwarai kuwa
na san da wannan yaki. Amma a lokacin ban fi shekara
goma sha biyar ba a duniya Abin da zan iya tunawa shi
ne sarki Ayubul Hasanu shi en kadai sarkin da ya gagari
sarkı Azmal a duk fadin duniyar nan. Kuma kasar sa ce
kadai kasar da ya kasa ci da yaki".
Maharaz ya yi murmushi ya ce,"Sarki Ayubul
Hasanu mahaifina ne, kuma nine kadai dansa da ya bari
a duniya. A yanzu haka nine na gaji sarautarsa". Koda jin haka sai Hasilatul Kurbas ya ce, "Ya kai Maharaz-me ya sa kana matsayin sarki amma ka baro birninka ka taho nan daji ka zauna?".
Maharaz yat murmushi ya ce,"Saboda ku na baro birnina na taho nan. Domin tuntuni nayı mafarki, an
nuna min cewa zan hadu da wasu jarumai daga cikin birnin Babila anan daji, wadanda in dai na hada kai da
su zan sami nasarar kawar da zalunci a duniya. Zan so a
ce kun karbi addinina wanda shi ne addinin gaskiya na
bautar sarki guda daya, makadaici, wanda ba shu da abokin tarayya. Shi ne mahaliccin sammaı da kassai da duk .abinda ke cikinsu. Kuma shi ne ya tsare mahaifina
da jama'arsa daga sharrin sarki Azmal, tun shekarun da suka gabata a baya".
Yayin da su Sadauki Kurbas suka ji wannan batu,
sai jikinsu ya yi sanyi, suka kama kallon juna, aka rasa wanda zai ce kala. Daga can sai Kurbas ya dubı Maharaz ya ce, "Ya kai wannan sarki mai kwarjinı da kamala. Kayi sani cewa ka zo mana da babban al'amarı, dan haka akwai bukatar mu tattauna mu yi shawara. In ka amince zamu gana da junan mu.".
Maharaz yai murmushi ya ce, "Kuje ku gana". Nan take suka koma gefe daya suka sake yin zugum aka rasa wanda zai ce wani kala. Hasilatul Kurbas ce ta katse shirun, tayi ajiyar zuciya, sannan ta dubi sadauki Kurbas, ta ce, "Ya kai Abbana, shin yanzu ka amince ka bamu hadin kai wajen yiwa sarki Armus tawaye" Kurbas ya yi murmushi, ya ce, "Kwarai kuwa. Kuma dari bisa dari, domin yanzu na ga yadda sarki Armus ya yi nufin hallakani. Tabbas in ba dan wannan aljani ya kawo mana fauki ba, da tuni yanzu mun hallaka gaba daya"
Koda jin wannan bate sai farin ciki ya kama Hasilatul Kurbas da jarumi Himal, suka rungume Kurbas a lokaci guda.

Comments

Please log in to leave a comment

Login here