An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
TASKAR TSAFIABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TASKAR TSAFI 2
okacin bakon aljani ya tsarewa hadiman Lsarauniya Abidatul Azmal dauke da su,
Hasilatul Kurbas bai sauke su a ko'ina ba, sai
a tsakiyar wani daji mai yawan duhuwa. Ya sauka a kofar
wani dutsc.
Akan buzu a kofar kogon wani kyakkyawan saurayi
ne sanye da fararen tufafi ya rike carbi yana lazimi.
Su dai su Hasilatul Kurbaz tun da wannan aljani ya
sace su suka kasa, magana, dan tsananin mamaki duk
tsawon tafiyar da suka yi a sararin samaniya dayansu bai ce
uffan ba kawai dai sun yi zuru ne su ga ina za a kai su da
dalilin da ya sa aka ceci rayuwarsu.
Da bakon aljanin ya sauka a gaban wannan
kyakkyawan saurayi sai Hasilatul Kurbas, yarima Himal da
sadauki Kurbas suka sauko daga kan aljani suka yi tsaye
kawai suna kallon wannan saurayi da ke wannan ibada.
Jim kadan sai saurayin ya hattama ibadarsa, sannan
ya waigo ya dubi bakon aljani ya ce, "Ya Marwanul
Hasabu a ina ka samo wannan mutane haka, kuma
sabodame ka zo min da su nan?"
Ko da jin wannan tambaya sai Marwanul Hasabu ya
rusuna yana mai dukasr da kai kasa ya ce, "Ya shugabana
kamar yadda ka sani cewz ka umarce ni da na dinga kai
dauki a duk lokacin da na ga za ai zalunci, a yau ma hakan
ce ta faru gare ni. Ka sani cewa a wasu sa'o'i kadan da suka
wuce a yau na je giftawa ta nahiyar birnin Kusa da cikin
daji da aka gina wani katafaren kurkuku sai na ga wannan
mutane a cikin mugun hali, kuma sai na ga wadansu
bakaken aljanu suna shirin afka musu. Dan haka sai na yi
sauri na dauke su daga wajen. Na so na bar su a wani
wurin, to amma sai na yi tunanin cewa ya kamata na kawo
su gare ka, wata kila zuwan na su ya zamo alheri."
Sa'adda aljani Marwanul Hasabu ya zo nan a
zanccnsa, sai kyakkyawan saurayin nan ya yi murmushi,
har kyawawan hakoransa farare sol suka bayyana, sannan
ya mike tsam daga kan buzun da yakc zaunc ya tako
Kafafunsa ya taho wajen su sadaukai Kurbas fuskarsa cike
da annuri, tamkar wata dan daren goma sha biyu. Ya cc,
'Ya ku wadannan baki, muna yi muku barka da zuwa
nahiyar birnin Nuruł Kalba: Ni sunana Maharaz bin
Makawi. Ni ma'abocin addinin Musulunci ne, kuma nan
inda kuke shi ne dajin Karusa. Daga nan zuwa cikin birnin
mu na Nurul Kalbi, tafiya ce ta sa'a bakwai kadai. Wannan
bawan Allah da ya cici rayuwarku abokina ne, bisa yada
addininmu cikin duniya. Ba wani abu ne ya fito da ni daga
cikin birnin mu ba, face kokarin daukaka addinina. Ina
tabbatar muku da cewa ba zan kasance mai cutarwa ba a
gare ku, idan babu damuwa zan so ku biyo ni izuwa cikin
kogon nan domin ku huta, kumaku ci ku sha, sannan ku ba
ni na ku labarin."
Yayin da su sadauki Kurbas suka ji wannan jawabi,
sai suka kwantar da hankalinsu, kuma suka amince akan za
su bi Maharaz izuwa cikin kogo.
Maharaz ya dubi yarima Himala ya ga kafafunsa da
hannayensa a daure suke da manyan sarkoki, kawai sai ya
ce, 'Bismillahi Rahmanir rahim." Sannan. sai ya shafi sarkokin hannunsa da kafarsa. Take sarkokin suka zube
kasa tamkar dora su a kai a jikinsa ba daurewa ba.
A'lamarın da ya matukar daurewa su Hasilatul
Kurbas kai kenan, suka firgita da al'amarin maharaz. Ba
tare da bata wani lokaci ba Maharaz ya wuce gaba
izuwa cikin kogon, su kuma suka bi bayansa kamar ana
jan akalar rakumi.
Cikin kogon ya kasance wuri mai fadi, kuma a
haskake yake, alhali babu fitila ko daya a cikinsa. An
shimfida wania babban buzu a wajen, sanann a gefe
daya tulu ne na ruwa da 'ya'yan itatuwa iri-iri,kamarsu
inibi, faure, gwanda, ayaba, da sauransu.
Nan take Maharaz ya zauna akan faffadan buzun,
sannan ya yi wa su Kurbas izinin zama, suka zauna.
Maharaz ya dauko 'ya'yan itatuwan ya zube a gabansu.
sanann ya zuba musu ruwa a cikin kofunan kasa su
duka.
Nan fa kowannensu ya cika cikinsa. Bayan sun
gama ne Maharaz aya dubi yarima Himal ya ce,"Ya kai
abokina, yanzu sai ku bani labarin ku ko?".
Himal ya yi gyatsa ya ce, "Ni sunana Himal, kuma
na kasance da ga sarki Asmaru na birnin Babila.
Wannan kuwa matata ce, sunanta Hasilatul Kurbas. Shi
kuma wannan babban mutum sirikina ne, wato mahaifin
Hasdatul Kurbas, kuma shine sarkin yakin birnin
Babila".
Nan dai Hımal ya kwashe labarinsa kaf ya
zayyanewa Maharaz. Yayin da Maharaz yaji wannan
batu, sai vavi shiru yana tunani izuwa wani dan lokacı
Sannan ya dago kai ya dubesu daya bayan faya, sannan
ya cc."a ku wadannan mutane, ku yi sam cewa
rayuwar ku na dikin hadarn matuka, domin na san waye
sarkin ku, kuma na san ko wacece saraumya Abidatul
Azmal, domun ta kasance ya ga sarkı Azmal bn Taufid,
sharraen matsafin da ya mutu akan burin son ya mallaki duniyara nan gaba dayanta, kuma har yanzu 'yarsa na
kan wannan buri. Tabbas yanzu duk inda za ku shiga san
Abidatul Azmal ata neme ku ta hallaka ku. Waje daya ne za ku iya zuwa ku tsira da rayuwar ku, wannan wuri kuwa shi ne garinmu, wato Nurul kalbi".
Cikin yanayin mamaki sadauki Kurbas ya dubi Maharaz ya ce,"Saboda me ya zamana a garin 'ku ne zamu iya kubuta?".
Koda jin wannan tambaya sai Maharaz ya dubi Kurbas ya ce, "Amma fa na yi mamakin jin wannan tambaya daga bakin ka, domin a zatona kasan lokacin da
sarki Azmal ya yi gaggarumin yaki da wani sarki wanda ake kira Ayubul Hasmanu."
Sadauki Kurbas ya jinjina kai ya ce, "Kwarai kuwa
na san da wannan yaki. Amma a lokacin ban fi shekara
goma sha biyar ba a duniya Abin da zan iya tunawa shi
ne sarki Ayubul Hasanu shi en kadai sarkin da ya gagari
sarkı Azmal a duk fadin duniyar nan. Kuma kasar sa ce
kadai kasar da ya kasa ci da yaki".
Maharaz ya yi murmushi ya ce,"Sarki Ayubul
Hasanu mahaifina ne, kuma nine kadai dansa da ya bari
a duniya. A yanzu haka nine na gaji sarautarsa". Koda jin haka sai Hasilatul Kurbas ya ce, "Ya kai Maharaz-me ya sa kana matsayin sarki amma ka baro birninka ka taho nan daji ka zauna?".
Maharaz yat murmushi ya ce,"Saboda ku na baro birnina na taho nan. Domin tuntuni nayı mafarki, an
nuna min cewa zan hadu da wasu jarumai daga cikin birnin Babila anan daji, wadanda in dai na hada kai da
su zan sami nasarar kawar da zalunci a duniya. Zan so a
ce kun karbi addinina wanda shi ne addinin gaskiya na
bautar sarki guda daya, makadaici, wanda ba shu da abokin tarayya. Shi ne mahaliccin sammaı da kassai da duk .abinda ke cikinsu. Kuma shi ne ya tsare mahaifina
da jama'arsa daga sharrin sarki Azmal, tun shekarun da suka gabata a baya".
Yayin da su Sadauki Kurbas suka ji wannan batu,
sai jikinsu ya yi sanyi, suka kama kallon juna, aka rasa wanda zai ce kala. Daga can sai Kurbas ya dubı Maharaz ya ce, "Ya kai wannan sarki mai kwarjinı da kamala. Kayi sani cewa ka zo mana da babban al'amarı, dan haka akwai bukatar mu tattauna mu yi shawara. In ka amince zamu gana da junan mu.".
Maharaz yai murmushi ya ce, "Kuje ku gana". Nan take suka koma gefe daya suka sake yin zugum aka rasa wanda zai ce wani kala. Hasilatul Kurbas ce ta katse shirun, tayi ajiyar zuciya, sannan ta dubi sadauki Kurbas, ta ce, "Ya kai Abbana, shin yanzu ka amince ka bamu hadin kai wajen yiwa sarki Armus tawaye" Kurbas ya yi murmushi, ya ce, "Kwarai kuwa. Kuma dari bisa dari, domin yanzu na ga yadda sarki Armus ya yi nufin hallakani. Tabbas in ba dan wannan aljani ya kawo mana fauki ba, da tuni yanzu mun hallaka gaba daya"
Koda jin wannan bate sai farin ciki ya kama Hasilatul Kurbas da jarumi Himal, suka rungume Kurbas a lokaci guda.
Himal ya janye jikinsa daga na' Kurbas, suka fuskanci juna, sannan ya ce, "Ya kai sarkin yaki, ka sani cewa mu ukun nan yanzu rayuwar mu na cikin hadari, gashi 'ya'yana suna can birnin Babila, mahaifiyata ma haka. Ya'yana jikokinka ne, kuma daga Hasilatul Kurbas sai su, su kadai suka rage maka a duniya, idan 7
hadin kai ga wannan sarki ma'abocin addinin
har kana son su tsira da rayuwar su dole ne mu ba da
Musulunci, domin shi kadai ne zai iya taimaka amana
mu dauko su daga can. Kuma me za ka iya cewa akan
wannan addini na su na Musulunci? Shin ka amince mu
karbe shi ko kuwa mu dakata mu fahimce shi sosai?"
Sa'adda sadauki Kurbas yaji wannan batu, sai yai
ajiyar zuciya gami da jan numfashi, sannan ya ce
"Hakika na amince mu baiwa wadannan mutane hadin
kai, domin mu kawar da zaluncin gimbiya Abidatul
Azmal. Dangane da karbar addinin su kuwa, shima ba
zan ce komai a yanzu ba, amma zai fi kyau nu zauna da
su mu ga irin yanayin rayuwar su, idan muka gamsu da
gaskiyar su sai mu karfe shi".
Koda suka gama wannan shawara sai suka koma
wajen sarki Maharaz suka yi masa bayani. Koda jin haka
sai farin ciki ya lullube shi shima ya amince da tsarin na
su. sannan ya fara debo kayansa na cikin kogon dutsen
da nufin su hau kan aljani Marwanul Hasabu ya tafi da
su izuwa birnin Nurul Kalbi.
Suna cikin wannan shiri ne suka ji wata irin
payarumar iska ta taso a sama tare da wani irin gurnani
mai ban tsoro. Ko da suka daga kawunansu sama, sai
suka yi arba da wata irin gabjejiyar mikiya wadda ba su
taba ganin mai girmanta ba da kalarta ba. Zaune akan
mıkiyar gimbiya Abidatul Azmal ce, sanye cikin sulken
yaki, kuma rataye da zabgegiyar takobi a bayanta. Tа
daure gashin kanta a baya ya zuba har Kasan
kwankwasonta.
Abidatul Azmal bata bari mikiyar ta gama
saukowa kasa ba, ta daka tsalle daga kanta ta diřgo kasa
daf da Sarki Maharaz, suka fara kallon-kallo. Ita kuwa
wannan katuwar mikiyar, sai ta sauko kasa ta kame
tamkar gunki.
Sai da gimbiya Abidatul Azamal da Sarki Maharaz
suka dan jima suna kallon juna cikin mamaki da burge
juna saboda mamakin ganin irin kyawan kowannensu da
kuma siffofinsu na sadaukantaka.
Su kuwa su Hasilatul Kurbas tuni sun firgice da
dimaucewa, domin sun san cewa yau dai kam sai abin
da hali ya yi, domin ga annobar duniya ta bayyana
garesu, wacce basu isa su iya guje mata ba.
Bayan Abidatul Azmal da Maharaz sun morе
klallon juna bisa cewar basu taba ganin juna ba. Sai
Abidatul Azmal ta murtuke fuska ta сe, "Ya kai wannan
dan Sarki, kayi sani cewa banzo nan ba domin na
yakeka ba sai don karfar wadannan mutanen nawa su
uku, na tafi da su na yi musu hukunci bisa laifin da suka
aikata mana."
Cikin fushi Maharaz ya ce, "Dn me ba za ki yakeni
ba, alhali na kasance babban makiyinki? Ko kuwa kin
manta ne cewa gabarmu ta asali ce?". Abidatul Azmal ta
kyalkyale da dariya, sannan ta ce, "Ya za'ayi na ınanta
gabar da ke tsakanin iyayenmu? Tabbas da sannu zan
sami galaba a kanka na mallaki birninku na Nurul Kalbi
Ka yi sani céwa yanzu zamani ya sauya, don haka da da
da yanzu ba daya ba ne. Idan mahaifina ya kasa samun
nasara a kanku, ni ba zan kasa ba, domin na yi bincike
na gani hanyar da zan bi na ga bayanku, kuma a kanta
nake, saura kiris na kai ga ci."
Maharaz ya sake yin murmushi a karo na biyu, ya
ce, "Ubangijina ba zai barki ki sami nasara ba a kaina.
Kuma ina tabbatar miki da cewa ba zan bari ki tafi da
wadannan mutane ba, koda kuwa zan rasa rayuwata".
9
Koda jin haka, sai Abidatul Azmal ta murtuke
fuska ta ce, "Ai kuwa za ka gane kuskurenka, kuma za
ka yi nadama".
Kafin Maharaz ya Kara cewa komai tuni Abidaty
Azmal ta zare takobinta sannan ta dubi Maharaz ta се,
"Ina son mu yi yaki ni da kai da tsagwaron karfin mu da
jarumtakarmu. Ni na ajiye tsafina a waje guda, kai kuma
ka ajiye na ka sihirin a waje guda".
Maharaz ya yi murmushi ya ce, "Ai ni bana sihiri,
sai dai neman taimakon Ubangijina." Nan take shima
Maharaz ya zare tasa takobin yai tsayuwa irin ta
sadaukai masu ji da kansu. Abidatul Azmal ta rugo
gareshi suka kaure da matsanaicin yaki. Suka wanzu
suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama,
juriya da jarumtaka fiye da tunanin mai tunani, hangen
mai hange, jawabin mai jawabi. Duk irin sadaukantaka
ta su Sadauki Kurbas sai da suka raina kansu, suka san
cewa lallai gaba da gabanta aljani ya taka wuta.
Sai da sa'o'i biyar suka shude wadannan jarumai
suna fafatawa dayansu bai gaji ba, kuma basu sami
damar yiwa juna rauni ba, har ya zamana takubbansu
un dakushe. Al'amarin da ya fusata jaruman kenan,
suka va da takubban na su suka sake kaurewa da sabon
azababben fada, suna masu naushi da bugun juna, hannu
da Kafa. Annan ne fa Hasilatul Kurbas ta san cewa ita
karamar jaruma ce, domin akwai lokacin da Abidatul
Azmal ta fusata, ta kihkimi wani gabjejen dutse ta
dagashi sama ta wurgawa Maharaz. Koda Maharaz ya vi
tsalle sama ya shallake dutsen, sai dutsen ya fada kan
dan uwansa dutse, duk su biyun suka dagargaje. Tabbas
Hasilatul Kurbas ta san cewa ba za ta iya daukar dutse
mai rabin nauyin wannan dutsen ba wanda Abidatul
10
Azmal ta daka. Kai ko su uku ne za sua taru da iya da Kurbas da Himal ba za su iya raba dutsen da kasa ba. Babu abin da zai fi firgita mutum face irin mugun zafin naman Abidatul Azmal. To amma kuma duko da hakan sai gashi ta hadu da dai-dai ita, domin kuwa lokacin da shima Maharaz ya fusata, sai ya kama wata katuwar bishiya mai tsawo da kaurin gaske ya
kaiwa
tumbukcta da karfin tsiya ya mai da ita sanda, ya dinra Abidatul Azmal duka da ita. tooce ya samı kasa, sai ka ga kasar ta yi rami mai zurfi, wanda za'a iva binne routum a ciki. Idan kuwa wata bıshiyar ya samu. sai ka ga ya kada iya ta,fadi kasa.
Haka dai ya ci gaba da kai mata mugun duka, har bishiyar ta ratattake, yai watsi da ita. A lokacin ne suka sake rugowa da gudu suka daka tsalle a sama suka gwarawa juna kai. Sai da kowannen su yaga taurarin wuya. Maimakon su fada kasa, sai suka rukunkume juna suka ci gaba da naushin juna, har tsawon 'yan. dakiku, sannan suka fado kasa a galabaice.
Koda Abidatul Azmal taji ta galabaita, sai ta rikida
nufin
ta zama mashi, ta cillo kanta da mugun karfin gudu da ta cake Maharaz a ciki. In ba dan Maharaz ya goce ba
huda
cikin zafin nama ya kwanta kas ba, da tuni mashin ya cikinsa. Yana kwantawa kuwa ya karawa mashin gudu, ta hanyar dukansa da kafarsa, ya sauya masa hanya. Ai kuwa sai mashin ya nufi cikin wani rami mai tsanarfin zurfi. Koda ganin haka, sai Maharaz ya daka tsalle yabi mashin cikin rami ya cafe shi, kuma ya zare wata wuka a jikinsa ya lumata cikin dutsen ramin, sai gashi yana reto rike da mashin. A sannan ne mashin ya rikida ya zama gimbiya Abidatul Azmal cikin galabaita. Maimakn ta yi masa wata illar, sai ta sunkuce shi tayi 11
sama da shu, ta zama tamkar tsuntsuwa, sannan ta sauko
kasa ta auve shi a gaban su Kurbas tana murmushi, ta
co, "Ya kai Maharaz me ya sa ka ceci rayuwata?"
Maharaz va ce, "Saboda ina sa ranšeewa za ki iya daina
tsati ki karbi addinina wata rana". Koda jin haka, sa
Abidatul Azmal ta bushe'das dariya, ta ce, "Kayi
kuskure, domin har abada haka ba za ta yiwu ba. Na
varda cewa kai jarumi ne na gasko. Kuma yanzu zan
bakura na tafi ba tare da wadannan masu laifi ba, amma
ina tabbatar maka da cewa nan da kwanaki kadan zan
rabaka da su, kuma ina mai shawartarka da ka kasance
cikın shiri, domin nan da wafansu kwanaki da suka gaza
darı zan gama hattama shirina na samun nasara akanka."
ta Koda Abidatul Azmal ta zo nan a zancenta sai
sake tashi sama ta dira a kan katuwar mikiyar nan da ta
kawota Mikiyar ta bude fukafukanta ta yi sama ta
luluka a cikın gajimare suka bace bat a cikin duhun
gajimare. Faruwar hakan ke da wuya sai Maharaz ya
dubi su Sadauki Kurbas ya ce, "Kuzo mu tafi". Ba tare
da wata gardama ba suka bi bayansa. Duk su duka suka
hau kan aljani Marwanul Hasabu ya tashi dà su.
Tafiyar kwana uku suka yi bisa kan aljani
Marwanul Hasabu a sararin samaniya suka iso birnin
Nurul Kalbi. Da zuwa kofar garin Marwanul Hasabu ya
-sauko kasa, suka sauka daga kansa. A nan Marwanul
Hasabu ya yiwa Sarki Maharaz bankwana suka rabu
akan cewa zai neme shi a duk sa'adda bukatar hakan ta
taso.
Nurul Kalbi, birnine babba, wanda aka kewaye shi
da doguwar katanga. A kalla za'a sami mutan sama da
uliyan biyar a cikin wannan babban birni.
Koda masu gadin kofar suka ga saukar Sarki
Maharaz da baki, sai suka yi sauri suka bude kofar garin, suna masu yi masa barka da zuwa cikin girmamawa. Maharaz ya wuce gaba, su Hasilatul Kurbas na biye da shi a baya.
Da shigarsu cikin birnin sai su Kurbas suka cika da mamaki saboda irin yanayin shigar jama'a ta kamala da kuma tsarin rayuwar su. Mutane suna ta sha'anin
gabansu, manya da kanana, kowa na tafiyar da al'amarinsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Duk
macen da suka gani sai suka ta lullube duk jikinta ba'a ganin komai na ta face fuskarta, hannayenta da kafafunta. Babu abin da ya fi baiwa su Kurbas mamaki
fa ce ganin yadda kananan yara suke rugowa wajen
Sarki Maharaz yana rungume su yana yi musu wasa a
matsayinsa na Sarki mai iko. Kuma a lokacin da suke
wannan tafiya ne Sarki Maharaz ya ga wani tsoho ya yi
dakon ita ce, kawai sai yaje ya karbi icen ya dora a
bayansa ya kama hira da tsohon, kuma babu wnai bafade
da ya zo ya karbi kayan a hannun Sarki Maharaz har aka
isa, kofar gidan tsohon, ya ajiye masa icen yai masa
sallama suka kara gaba.
Kai tsaye Sarki Maharaz ya wuce izuwa cikin
fadarsa, inda suka iske fadar tsit ba kowa a ciki face
wadansu Dattijai su goma aune a kan shimfida suna
tattaunawa. Gaba dayansu babu dan shekara kasa da
tamanin. Koda ganin shigowar Sarki Maharaz da su
Sadauki Kurbas, sai tsofaffin nan suka mike tsaye su
duka cikin farin ciki. Mafi yawan shekarun cikinsu
wanda ya kasance gashin jikinsa gaba daya fari ne fat,
sai ya taho ga Sarki Maharaz suka rungume juna yana
mai yi masa barka da zuwa tare da tayashi murnar
dawowa cikin nasarar samo abin da ya fita nema. Ba
13
tare da wani 6ata lokaci ba Maharaz. ya gabatar da
wannan tsoho ga su Kurbas ya ce, "Wannan shi ne
wanda ya haifi uwata, ana kiransa da suna Ammar lbn Sadiyan". Maharaz ya ci gaba da gabatar da sauran tsofaffin yana fadin sunayensu. A karshe ya "Wadannan sunc manyan Malamanmu wafanda ke da ilimi na addininmu, sune abokan shawarata wajeh tafiyar da harkokin mulki da jagorancin jama'a."
Nan take Maharaz ya dubi su Ammar ya basu labarin yadda ya hadu da su Kurbas tun daga lokacin da aljani Marwanul Hasab ya dauko su ya kawo su gare shi, kawo izuwa lokacin da gimbiya Abidatul Azmal ta kawo musu mamayar bazato suka fafata gagarumin vaki. Ya yin da su Ammar bn Safiyan suka ji wannan labari, sai suka cika da mamaki, suka yi shiru suna jinjina al'amarin a cikin zuciyoyinsu, har izuwa wani lokaci. Daga bisani sai Ammar ibn Safiyan ya nisa ya
ce, "Hakika wannan takadiriyar sarauniya ba za ta hakura ba. Kuma tabbas yanzu za ta je tayi wani sbaon
shirin ne a kanmu, dan haka ya zama wajibi muma mu
zauna cikin shirin yaki, domin a ko yaushe za ta iya kawo mana hari".
Sarki Maharaz ya ce "Kwarai kuwa. To amma ai
ko ba komai aljani Marwanul Hasabu zai ci gaba da
aikinsa na leken asiri, insha Allahu duk abin da take
shiryawa zaizo ya sanar da mu."
Ammar bn Safiyan ya ce, "Anya kuwa. Hakika na
san cewa Marwanul Hasabu ya yi irin wnanan aiki a
baya, tun a zamanin mahaifinka marigayi Sarki Makawi,
to amma fa ka sani cewa masu iya magana suna cewa
mai laya ya kiyayi mai zamani. Duk yadda kake
tsammani Abidatul Azmal ta wuce nan, domin ta ninka 14
mahaifinta hatsabibanci sau goma. Kayi sani cewa a
lokacin Sarki Azmal ya samu nasarar kama manyan Rasashen duniya guda dati bakwai da tamanin. Ita kuwa Abidatul Azmal a halin yanzu ta kama kasashe dubu uku da ashirin da daya. Wannan kasa tamu ita ce kadai
ta gagareta, kuma ita kadai take shakka". Ya yin da Sarki Maharaz yaji wannan batu, sai yai murmushi ya ce, "Ya kai Kakana, ka sani cewa har kullum Allah baya
barin zalunci, dan haka muci gaba da addu'a da izinin Ubangiji har abada Abidatul Azmal ba za ta taba samun
nasara akan mu ba."
Ammar ya dafa kafadar Maharaz ya ce,
"Kwarai kuwa jikana. Hakika kayi gaskiya".
Nan take Maharaz ya kira wani hadimi wai shi
Sahal, ya ce da shi ya kai su sadauki Kurbas izuwa
masaukinsu, Sahal ya wuce gaba su kuma suka bishi a
baya har izuwa wani bangare daban na gaidan sarautar.
A kan hanyar su ne sadauki Kurbas yaga wata mace 'yar kimanin shekaru arba'in tare da mijinta wanda bai fi
shekaru sittin ba a zaune suna hira cikin nishadin da
kwanciyar hankali. Koda ganinsu sai ya tsaya kyam ya
kura musu ido, ya shiga tunani mai zurfi. Al'amarin da
ya baiwa Himal mamaki kenan. Ita kuwa Hasilatul
Kurbas sai hankalinta ya tashi, dan ta san cewa ba komai
ne ya haddasa hakan ba face tunowa da mahaifiyarta da
ya yi, wato tauraruwar kyawawa Anisa bn Imran.
Masana tarihi a birnin Balbila sun ce tun daga
farkon gina birnin Babilan kawo i yanzu ba'a taba
samun kyakkyawar mace ba kamar Anisa bn Imran,
wato mahafiyar Hasilatul Kurbas, kuma a cikin
kyawunta abin da Hasilatul Kurbas ta samu ba zai wuce
kaso uku ba daga cikin goma, duk da cewa a halin yanzu
15
in banda gimbiya Abidatul Azmal babu wadda ta fita
kyau a kasar ma gaba faya.
Lokacin da Hasilatul Kurbas taga hawaye ya fira
zuba a idanun sadauki Kurbas, yayin da ya kurawa
wadannan ma'aurata idanu, sai ta sha gabansa. sannan ta
sa hannu ta share masa hawayen ta ce, "Ya kai Abbana, ashe ni din nan ban isa na debe maka kewar mahaifiyata ba. Shin bari na da tayi a duniya bai zamo maka abin alfahari ba? Shin idan ka kalli fuskata baka ganin kamanninta?"
Koda sadauki Kurbas yaji wadannan tambayoyi