daga bakin 'yarsa, sai ya fashe da kuka yana mai cewa, "Ki gafarce ni ya ke 'yata, domin ba zan iya mancewa da mahaifiyarki ba, kuma ba zan iya daina begenta ba, domin har yau har gobe ban ga wata 'ya mace mai kyau kamar ta ba, kuma na san cewa bazan gani ba daga nan har izuwa ajalina."
Nan dai Hasilatul Kurbas ta ci gaba da rarrashin sa
ta jashi izuwa masaukinsu inda Sahal yai musu jagora. Al'amarin Sarki Maharaz kuwa, bayan ya rabu da
su Kurbas sai ya wuce izuwa bangaren da mahaifiyarsa
gimbiya Zuhura take, wato matar marigayi Sarki Makawi. Da shigarsa cikin turakarta sai ya iske ta a
zaune ruke da wata tsohuwar alkyabba ta mahaifinsa
tana shafarta da hannu, idanunta cike da kwallah. Yayin
da Zuhura taji motsin shigowar sa ta dago kai suka yi
arba, sai tayi jifa da alkyabbar ta mike tsaye ta rugo gareshi tana mai farin cikin ganinsa. Maharaz ya kama
hannunta suka zauna tare a gefen gado lokacin da hawaye ya subuto masa sannan ya dubeta ya ce, "Ya ke
ummi na, shin ba za ki daina yawan begen mahaifina
ba? Ina tsoron kada yin hakan ya haifar da wata lalura a
16
gareki".
Zuhura ta sa hannu ta share hawayen Maharaz ta ce, "Ya kai dana ka yi sani cewa mahaifinka ya cika gwarzo, kuma namijin duniya, domin a zamaninsa shi ne
ya zamo gagara badau, kuma dodo ga dukkan makiya Allah. Kayi sani cewa mahaifinka da ban yake da sauran
maza, dan haka ba zan iya rage begensa ba a cikin
zuciyata. Tabbas mutuwa ta yi min gaggawa da ta rabani
da masoyina a lokacin da muke kan tsakiyar kauna da
kula da juna. Ga shi har yanzu na kasa yin wani auren.
domin na'san cewa ba zan taba samun kamarsa ba".
Sa'adda Zuhura ta zo nban a zanceta, sai Maharaz
ya fashe 'da kuka, ya mike ya ce, "Ummina ina mai
shawartarki da ki rungumi kaddara ki yi aure, domin
koda ajalinki zai riskeki ya riskeki a dakin mijinki,
domin baki tsufan da kika wuce kiyi aure ba. Ki tuna
cewa shekaruna ashirin da bakwai kacal, ke kuma yanzu
kina da shekaru arba'in da biyar. Shin bakya son na ga
na sami kanne kafin nima nayi aure na haihu".
Koda ji haka sai Zuhura ta fashe da kuka, ta ce,
"Ya kai dana, ina son ka samu kanne. To amma ka сі
gaba da yi mini addu'a Allah ya bani mijin da ya dace
dani."
Maharaz ya yi murmush cikin yanayin farin ciki ya
ce, "Amin."
Daga wannan rana su sadauki Kurbas suka tsinci
'kansu a cikin sabuwar rayuwa, a cikin Birnin Nurul
Kalbi, rayuwar da ta zame musu mafi dadi a duniya,
domin sun ga cewa Musulmai suna rayuwa mafi inganci
da kwanciyar da hankali. Sun yi mamakin yadda mutane
suke zaman gaskiya da gaskiya, ga amana, ga adalci,
babu zancen wani yafi wani. Da attajirai da talaka da
17
mai mulki babu wanda yafi wani. Duk wanda yai laifi
komai girmansa da matsayinsa za'a yi masa hukunci irin
wanda ake yiwa kowa. Tsawon kwana ashirin da daya
da suka yi a birnin basu taba jin an ce yau ga barawo ba.
Ba su ji ance ga wani yayi fyade ko kwace ba. Kai ko
cin zali tsakanin mai karfi da mara karfi basu taba gani
ba. Kullum ko yaushe jama'a na cikin zaman lafiya,
taimako da kaunar juna. Wannan al'amari ne ya janyo
hankalin sadauki Kurbas, Hasilatu! da yarima Himal
suka ji kaunar addinin Musulunci ta shiga cikin
zuciyoyinsu, musamman ma ganin yadda mutanen gari
suka kaunace su ba da tsangwama ba.
A daren kwana na ashirin da daya ne suka kai
kansu fada a matsayin suna son su musulunta. Koda jin
wannan batu daga garesu sai farin ciki ya kama Sarki
Maharaz da manyan Malaman nan, wato su ammar bn
Safiyan. Ba tare da 6ata wani lokaci ba aka biya musu
kalmar shahada, suka maimaita, sannan aka fara koya
musu ilimin addini. Kafin Sarki Maharaz ya bar fadarsa
ya dubi su Kurbas ya ce, "Na shirya muku walima a
gidana gobe da yammaci, dan haka zan turo ayi muku
jagora izuwa gidan nawa, idan lokaci ya yi. Yayin da su
yarim Himal suka ji haka sai suka yi murna da godiya.
Lokacin da Maharaz ya isa gida, sai Zuhura ta dube shi ta ce, "Ya kai dana, wane irin abin farin ciki ne
ya sameka haka na ga fuskarka cikin annuri da annashuwa?".
Maharaz ya yi murmushi ya ce, "Ai ina murna ne saboda bakin nan nawa wadanda na zo da su sun karbi addinin Musulunci a yau din nan. Kuma a dalilin haka
ma na ke son na shirya musu walima ta musamman anna gidan gobe da yammaci."18
Sa'adda Zuhura taji wannan batu sai ita ma ta cika
da farin ciki, ta ce ai kuwa ni da kaina zan shirya
wannan walima, kuma da kaina zan karbi wadannan
manyan baki, domin yanzu sun zama cikakkun 'yan
uwanmu."
Yayin da Maharaz yaji wannan batu daga bakin
mahaifiyarsa sai ya kara cika da farin ciki fiye da da, yai
ta yi mata godiya.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin Sarki
Maharaz da su sadauki Kurbas bayan aljani Marwanul
Hasanu ya daukosu daga can kurkukun Ukubatul
Dukkan.
Al'amarin gimbiya Abidatul Azmal kuwa, lokacin
da ta koma fadarta, bayan ta rabu da Sarki Maharaz, sun
gama fafata azababben yaki. Sai ta kira maga takardarta
ta sa shi ya rubuta wasika guda daya rak, ta gayyatar
gaba daya wakilanta na kasashe dubu biyu da ashirin da
uku, wadanda ke karkashin mulkinta. Sa'adda maga
takardar ya gama rubuta wasikar guda daya, sai
Abidatul Azmal ta nunata da yatsa, take wasikar ta zama
guda dubu hudu da ashirin da uku. Abidatul Azmal ta
runtse idanunta ta fara kiran sunayen wadansu aljanu har
guda dubu hudu da ashirin da uku. Ai kuwa tana fadın
sunan na karshe, sai ga su sun bayyana gaba daya. Cikin
izza da nuna isa ta dubesu ta ce, "Ko wannen ku ya
dauki wasika guda ku rabu izuwa kasashena na
bil'adama guda dubu biyu da ashirin da uku, da kuma
kasashe na na aljanu da dodanni ku kai musu wadannan
wasiku na gayyata izuwa yaki ga birnin Nurul kalbi.
Duk kasar da kuka je ku sanar da sarkin su cewa ina son 19
ya hada min runduna ta mayakansa guda dubu dari,
kuma lallai ya hallara a nan fadata nan da kwana saba'in
zamu dunguma a wannan rana, ina son mu baje birnin
gaba daya, mu hallakar da duk mahalukin da ke
numfashi a cikinsa face mutum daya, wato Sarkin su
Maharaz. Lallai bana son koda kuda ya taba lafiyarsa".
Nan take aljanun guda dubu hudu da ashirin da
uku suka dauki wasikun nan dai-dai suka tashi sama,
suka cika sararin samaniya, kamar dangin 'yar tsewala
na shagalin biki.
Bayan tafiyar manazannin ne, wazirin gimbiya
Abidatul Azmal yai karambani ya tambayeta ya ce, "Ya
shugabata mene ne dalilin da ya sa ba kya son a taba
lafiyar Sarki Maharaz? Shin ba kya tsoron cewa idan
kika barshi a raye kamar kin kashe maciji ne ba ki sare
kansa ba."
Koda jin haka, sai fuskar Abidatul Azmal ta
murtuke izuwa tsananin fushi. Cikin zafin nama ta yiwa
waziri barin makauniya a fuskarsa da kafarta. Saboda
Karfin dukan, sai da ya yi tsalle sama ya hadu da rufin
saman fadar, sannan ya fado kasa tim, jini yana zuba ta
hancinsa da bakinsa. Ko kyakkyawan motsi bai yi ba rai
ya yi halinsa. Abidatul Azmal ta dakawa wasu dakary
biyu tsawa da ke gabanta, ta ce, "Ku dauke min gawar
wannan tsohon banzan".
Dakarun suka kinkimi gawar jikinsu na tsuma suka
yi waje da ita. Abidatul Azmal ta dubi sauran fadawanta
daya bayan daya, kowannensu sai ya sunkwi da kansa
kasa yana makyarkyata cikin fargaba.
"Daga yau duk wanda ya sake yi min katsalandan
a cikin harkokina daga cikinku, zai fuskanci irin
hukuncin da na yiwa waziri a yanzu. Ku tashi ku bani 20
wuri na sallame ku!".
Cikin rawar jiki su duka suka mike suka fice daga
fadar, kowa ya watse, ya zamana saura Abidatul Azmal
ita kadai a zaune bisa karagar mulki. In ka dauke fitar
numfashinta baka jin sautin komai a fadar.
Nan fa Abidatul Azmal ta shiga tunani mai zurfi,
inda ta dinga tuno da irin azababben yakin da tayi da
sarki Maharaz. Sannan ta tuno da lokacin da ya ceci
rayuwarta, sa'adda ta zama mashi zata soke shi da ya
doketa ta fada cikin rami mai zurfi, kuma ya bita da
gudu cikin ramin ya rikota. A lokacin da ta dawo siffarta
ta bil'adama sun sami damar kurawa juna ido, a wannan
lokacin ne ta lura da tsananin kyawunsa ta tabbatar da
cewa inda shi mace ne babu makawa sai ya fita kyau.
Abidatul Azmal ta tuno da tsagwaron jarumtaka irin ta
Maharaz sai ta ga cewa tabbas duk duniya babu da
namiji da ya fi dacewa da ita sama da shi. Nan take ta
ayyana a ranta cewa bayan taci birnin Nurul Kalbi da
yaki za ta tursasa Maharaz tayi masa dole ya fita daga
addinin Musulunci sannan ta aure shi. Haka dai Abidatul
Azmal tayi ta wannan tunani, ba ta gushe ba tana yi har
ta tsinci kanta a cikin tsanani kauna da begen Maharaz.
Koda ta dawo cikin hayyacinta, sai ta gane cewa hakika
tayi kuskure, domin babu yadda za'ayi tayi wannan
soyayya da wanda shi ne babban makiyinta a duniya,
domin gabar da ke tsakaninsu ta asali ce mai hjja. Kuma
ta ya ya' shi Maharaz zai yarda da ita har ya karbcta a
matsayin abar kauna?. Amsar da ba ta sani ba kenan,
kuma ita ce ta sake jefata cikin sabon tunani.
Wannan shi ne abin da ya faru ga Abidatul Azmal
bayan tayi kazamin fada da Sarki Maharaz na birnin/
Nurul Kalbi. 21
A can birnin Nurul Kalbi kuwa, kashe gari, wato
ranar da aka shiryawa su Kurbas walima, sai suka ci ado
suka yi shiga ta kamala irin ta addinin Musuluncu, aka
turo manzo ya yi musu jagora izuwa gidan Sarki
Maharaz.
Da shigar su babban falon gidan, suka hango
babbar shimfida cike da abinci da abin sha iri-iri. Zaune
a gefe guda Sarki Maharaz ne tare da mahaidiyarsa
gimbiya Zunura wacce ker sanye da fararen tufafi, kuma
ta rufe fuskarta da wani farin kyalle, wanda shi ne ya
lullube kanta gaba daya, kuma ya kasance mai dishidishi. Da yake jarumi Himal ne akan gaba, sai ya yi
sallama, a lokacin da Hasilatul Kurbas ke biye da shi,
sannan sadauki Kurbas. Koda jin sallamarsu, sai
Maharaz ya amsa suka mike tsaye shid a Zuhura suka
tahi bakin kofa domin taryar bakin nasu. Da zuwa aka
hadu a bakin kofa, inda Zuhura ta yaye lullubinta,
kyakkyawar fuskarta ta bayyana garesu. Nan fa su duka
sukoa kame tamkar gumaka, saboda tsananin mamakin
ganin kyawun da Allah ya ba ta.
Duk da cewar shekarun gimbiya Zuhura sun kai
arba'in da biyar, ba za ka taba cewa ita ce ta haifi Sarki
Maharaz ba, domin ta kasance tamkar budurwa 'yar
shekara goma sha takwas, domin Allah ya bata jiki mai
kyawun křra. Anna ne fa sadauki Kurbas ya tabbatarwa
da kansa cewa ya yi karya da yake zaton cewa ba zai
sake ganin mace mai kyauba kamar matarsa marigayiya
Anisa.
Lokacin da Maharaz ya fuskanci cewa su !limal
sun shiga wani hali bisa ganin kyawun mahaifiyarsa, sai
22
yayi gyaran murya da karfi, suka dawo hayyacinsu,
sannan ya gabatar da mahaifiyarsa a garesu inda suka
kara cika da mamaki, domin su a zatonsu yayarsa ce ko
kuma 'yar uwarsa. Nan dai suka koma gaba daya suka
zauna akan wannan shimfida mai dauke da kayan ciycciyc da shaye-shaye. Tun da sukoa zauna Kurbas ya
kasa samun sukuni, ya yi ta satar kallon gimbiya
Zuhura. Ita ma kuma haka taui ta satar kallonsa, amma
in banda Hasilatul Kurbas babu wanda ya lura da abin
da ke faruwa. Nan dai aka ci aka sha, tare, sannan aka yi
hira, har izuwa lokaci mai tsawo, sannan su Kurbas suka
yi sallama da godiya suka koma masaukinsu.
Tun daga wannan rana da aka yi wannan walima,
Zuhura da Kurbas suka shiga cikin wani irin sabon
yanayi na yawan tunani da damuwa. Domin a wannan
rana ma da aka yi walimar sadauki Kurbas kasa barci ya
yi saboda tsananin bege gimbiya Zuhura. Har ma
Hasilatul Kurbas ta fito daga dakin mijinta Himal ta zo
ta ganshi a zaune ya yi tagumi yana tunani. Cikin
matukar damuwa ta zo gabansa ta ce, "Ya kai Abbana,
kayi sani cewa ka daukowa kanka babban aiki, wanda
yafi karfika. Na sani cewa ba komai ne ya hanaka barci
ba a wannan dare ba face tunanin gimbiya Zuhura
mahaifiyar Sarki Maharaz. Ina mai shawartarka da ka
cire sonta a cikin ranka da gaggawa, domin banyi zaton
aure zai iya kulluwa ba a tsakaninku. Saboda na samu
labarin cewa tun da mijinta ya mutu ba ta sake sha'awar
kara aure ba."
Koda jin haka sai Kurbas yai shiru bai ce komai
ba. Har dai Hasilatul Kurbas ta gaji da surutanta ta fice.
Kamar yadda Kurbas ya zamo a cikin yawan
begen Zuhura, haka itama ta kasance, amma sai ta daure
23
ta danne abin a cikin zuciyarta, ba ta yarda wani ya
fahimta ba. Amma har satar hanya take, tayi bad da
kama ta wuce ta inda aka sauke su ta kare masa kallo ba
tare da ya sani ba.
Wata rana da sassafe, sai ga aljani Marwanul
Hasabu ya zowa Sarki Maharaz a galabaice,. kai da
ganinsa ka san ya sha bakar wuya. Marwanul Hasabu ya
fadi gaban Maharaz yana numfashi ya сe, "Ya
shugabana kayi sani cewa ga gimbiya Abidatul Azmal
can tafe da dakarun yaki marasa adadi daga jinsin
mutane, aljanu, dodanni. Tabbas wannan karon tayi
rantsuwa cewa sai ta mai da birnin Nurul Kalbi ya zama
turbaya. Duk mahalukin da ke numfashi a cikinsa,
walau mace ko namiji, sai ta zare masa ruhin numfashi,
face kai kadai kawai".
Koda jin wannan batu sai hankalin kowa ya
dugunzuma, jama'a suka rude suka dimauce, aka kama
salati, wasu kuwa suka hau surutai iri-iri da tunanin
guduwa. Koda ganin haka sai sarki Maharaz ya daka
tsawa aka yi tsit, sannan ya ce "Ya, ku 'yan uwana
Musulmi, yanzu zan baku wani labari wanda zai Kara
muku kwarin gwiwa bisa wannan al'amari."
Nan fa mutane suka yi tsit aka fara sauraren Sarki
Maharaz inda ya fara bayar da labari kamar haka.
"A wani zamani can baya, an yi wata babbar daula
mai suna Sharmur, anan yankin Kasashenmu. Daular Sharmur ta hada garuruwa da dama, kimanin dari biyu da arba'in, kuma kowanne gari yana da Sarkinsa mai iko Wani babban abin sha'awa shi ne wadannan
garueruwa guda fari biyu da arba'in suna zaman lafiya fiye da shekaru hamsin baya, babu wata kasa da ta taba yakar wata, kasancewar akwai kyakkyawar mu'amala a
24
tsakaninsu, kuma al'adar su duk iri daya ce, wasu suna butar rana, ko wata, wasu giwa, wasu dutse. Kai wasu ma basu da addini.
Daga cikin wadannan kasashe akwai wani babban gari, wanda yafi duk sauran girma, arziki da karfin mayaka, wanda ake kira Darul Hasmar. Darul Hashmar
na karkashin jagorancin wata sarauniya 'yar kimanin shekaru tamanin da uku mai suna Ummul Nisai. Ba komai ya sa ake kiranta da wnanan suna ba face 'ya'yanta bakwai, kuma duk matane budurwoyi wadanda suka kasace sako dasako.
Ummul Niusai ta gaji sarautane a wajen mijinta
sarki Darusul Hamaru, wanda farautar nenman wani
tsibiri ya zamo ajalinsa. Ance a zamaninsa babu irin
abin da bai yi ba don ya sami haihuwar da namiji, amma
abu ya gagara. Sarki Darusul Hamaru ya auri mata sama
da dari, amma babu wadda ta taba haihuwa face Ummul
Nisai. Kuma duk sa'adda tazo haihuwa sai yaga 'ya mace
take haihuwa. A duk sa'adda hakan ya faru sai sarki
Darusul Hamanu yayi gagarumi bakin ciki, sannan
kuma ya dinga kukan takaici kenan, dare da rana har
izuwa lokacin da za'a radawa jaririya suna.
Ba wani abu bane ya sa sarki Darusul Hamanu
tsananin bakin ciki da damuwa ba bisa rashin samun
haihuwar da namiji face wata gaba ta asali tsakanin
zuriyar wani sarki da ake kira Hurmas bn Salkas, wanda
ke muli a wata daula dan daban da ake kira Dulkar.
Daular Dulkar ta kunshi garuruwa sama da guda
dari uku. Kuma ita garuruwanta gaba daya a karkashin
Jagorancin Sarki Hurmas bn Salkas suke, sabanin daular
Sharmura wacce ko wané gari na da nasa sarki mai
cikakken iko 25
Asalin gabar da ke tsakanin sarki Darusul
IHamanu, wato mijin sarauniya Ummul Nisai da kuma
sarki Hurmas bn Salkas ta faru ne a wasu shekaru
kimanin sittin baya, sa'adda kowannesu ya fita yawon
rangadi tare da dakarunsa, masu tsaron lafiyarsa.
Masana tarihi sun ce a wannan lokaci Sarki Darusul
Hamanu ya fita wannan rangadi nbe da dakaru dubu da
da hamsin. Shi kuwa Sarki Hurmas bn Salkas na daular
Daulkar, ya fita ne da dakaru dubu dari biyar da arba'in.
Wato ninkin baninkin na Sarki Darusul Hamanu.
Gaba dayansu sun fito wannan rangadi ne domin
neman wnai kyakkyawan tsibiri wanda suka sami
labarinsa a wajen bokayensu. Shi dai wannan tsibiri ana
yi masa lakabi da tsibirin rayuwa.
Tsibirin rayuwa ya kasance guri ne mai yalwar
ni'ima, wacce a wannan zamani babu wani wuri mai
ni'imarsa, kasancewar yana da kasa mai albarka ta
noma, da kuma ma'adanan kasa mai yawa, kamar su
zinare, yakutu, da lu'u-lu'u. Haka kuma kogin da ya
zagaye wannan tsibiri yana da ruwa mai kyau da dadin
dandano. Gashi da haske garai-garai gwanin sha'awa.
Mutane sun canfa wannan tsuburi cewar duk abin da
yake zaune a cikin sa ko kuma ya shigo cikinsa dole ne
ya zamo a cikin-koshin lafiya a ko yaushe. Babu abin da
zai baiwa- mutum mamaki face koda mutum zai shekara
dari a wajen ba zai taba hanin kuda ko sauro ba. Haka
kuna ba za ka taba ganin kwaro ko dabba ba mai
cutarwa a tsibirin face wadda za ta iya zama abinci ga
bil'adama.
Kash! Duk wannan ni'ima da ke cikin wannan
tsibiri sai ta zamo a banza, domin masu bincike sun
gano cewa babu wani mahaluki daya taba ketare
26
wannan kogi ya isa tsibirin rayuwa har ya yi sa'a guda kacal a cikinsa. Ma'ana duk mutumin da ya sami damar zuwa tsiburin mutuwa yake yi, kuma an kasa gano abin da ke kashe mutane. Babu irin bincikend a matsafa basu yi ba, amma sun kasa ganowa.
A wannan shekaru da sarki Darusul Hamanu da
kuma Sarki Humras bn Salkas suka tafi neman tsuburin
rayuwa, a sannan ne bokayensu suka smai nasarar gano
abin da ke hallaka mutane a wajne, sanann suka sami
maganin abin.
Ba wani abu bane ya ke hallaka mutane face wasu
fatalwoyi na wadansu tsofaffin aljanu, wadanda tun
ainahi su suka fara gina fadarsu a cikin wannan tsuburi.
An ce aljanun sun fi shekara dubu hudu da mutuwa,
amma har kwanan gobe sunki yarda su bar wani
mahaluki yaji dadin wannan tsuburi.
Boka Shamnas wanda ke wakiltar Sarki Darusul
Hamanu da kuma boka Salbatu mai wakiltar Sarki
Hurmas bn Salkas, sun kirkiri wani kuttun fata wanda
suka cikashi da wata irin jar iska ta tsafi, wacce in dai
aka bude kuttun iskar ta fita a can tsibirin rayuwa, sai
gaba daya fatalwoyin nan sun kone kurmus.
A rana guda bokayen biyu suka sami nasarra
kammala wannan aiki, kuma kowannesu ya sanar da
sarkinsa da gaggawa. Bisa rashin sa'a sai sarakunan biyu
suka shirya a lokaci guda suka baro kasashen su izuwa
wannan tsuburi na rayuwa. Daga kasashen su zuwa
wannan tsibiri, nisan tafiyar iri daya ce, wato tsawon
kwana arba'in da daya ce kacal.
Ba zato ba tsammani sai wannan runduna biyu tayi
gamon bazato a bakin wannan kogi na tsuburin rayuwa.
Nan fa aka tsaya ana kallon-kallo cikin tsananin
27
mamaki. Musamman boka Shamnas da boka Salbatu,
saboda ganin cewa kowannensu na rike da kuttun jar
iska.
Sarki Hurmas da sarki Darusul Hamanu suka
kurawa juna ido cikin harara da takaici. Dama tuntuni
basa ga maciji, domin babu wata alaka ta kasuwanci a
tsakanin daulolin biyu. Kuma doka ce babba dan
kowacce daula kada ya shiga cikin dayar da ba ta sa ba.
In kuwa ya shiga a bakin ransa.
Cikin tsananin fusaya sarki Hurmas ya dubi Sarki
Darusul Hamanu ya daka masa tsawa, ya ce, "Ya kai
wannan makaskancin sarki, ka sani cewa daulata tafi
taka yawa da karfi, dan haka ina mai shawartarka da ku
koma da baya ku hakura da wannan tsibiri, in ba haka ba
kuwa yanzun nan zamu karar da ku ánan wajen.
Dayanku ba zai tsira da rayuwarsa ba".
Yayin da sarki Darusul Hamanu ya ji wannan batu,
sai ya kyalkyale da dariya, ya ce, "Karyarka ta sha karya
ya kai wannan azzalumin Sarki. Ko dai kai da jama'arka
ku janye mana ku koma da baya, ko kuma ku zama
gawa. Tabbas mune muka fiku cancanta da mallakar
wannan tsibiri".
Carafn sai bokayen biyu suka ce "Ku tsaya". Cikin
hadin baki. Daga nan sai suka runtse idanuwansu suka
shiga bincike acikin tsafi. Bayan 'yan dakıku kadna sai
kowane boka ya matsa kusa da sarkinsa yai masa
'magana cikin rada. Faruwar hakan ke da wuya sai sarki
Hurmas ya kyalkyale da dariya, sannan ya turbune fuska
kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa. Ya dubi
Darusul Hamanu ya ce, "Ya kai wannan sarki, bincike
ya nuna cewa idan muka yaki junanmu dayanmu anan
ba zai tsira da rayuwarsa ba. Zai fi kyau ka hakura ka
28
tsibirin nan domin ni ba zan iya bar maka ba" bar mını
Darusul Hamanu ya kyalkyale da dariya ya сe,
"Kamar yadda kake jin ba za ka iya bar mani ba, nima
ba zan iya bar maka ba. Abu daya zana iya yarda da shi
shi ne mu raba tsiburin biyu, kai ka dauki rabi, nima na
duaki rabi".
Cikin tsawa Hurmas ya ce, "Ba zan yiwu ba,
domin nan fadata zata dawo. Kai ma kuma na san taka
nan za ta dawo. Ka sani cewa ba'à sarki biyu a birni
guda. Na rantse da girman karagata da dai ayi haka
gwara muyi ragas."
Sarki Hurmas na gama fadın haka ya baiwa
dakarunsa umarni su afkawa su sarki Darusul Hamanu.
Al'amarin da bai yiwa bokayen biyu dadi ba kenan,
Hankalinsu ya dugunzuma, amma babu yadda za su yí,
dole suma suka aſkawa junansu domin aikin gama ya
gama. Nan fa wuri ya yamutse, kura ta tashi ta turnuke
sararin samaniya. Hayaniyar dawakai, karar makamai,
da ihun kuwar mazaje suka cika dodon kunen. Wohoho!
A wannan rana anyi azababben yaki, domin sai da
dakarun Sarki Darusul Hamanu suka bajwa dakarun
Sarki Hurmas mamaki, duk da cewar sun ninka su yawa,
domin kasuwar cinikin rayuka ce ta bude, sai ka
kawunan bil'adama na shawagi a sararin sama kamar
'ya'yan balbelu, jini kuwa ya dinga tartsatsi da fantsama
kamar cali na fesar da ruwa. Sai da aka yini ana wannan
yaki, ya zamana saura mutum hudu kadal a tsaye suna
fafatawa. Amma gaba daya wajen ya cika da
gawarwaki, jini kuwa har shanye kafafuwansu yake yi,
iya idon kofar.
Wadannan mutane hudu da suka rage ba wasu
bane fa ce Sarki Darusul Hamanu, Sarki Humras bn
291
sun
Salkas,
jigaya,
boka Shamnas, da boka Salbatu. Dukkanin su sun yi jina-jina.
Su kuwa su Boka Shamnas,
a jikinsu mai har da ma kunar wuta
sihiri. yawa ba adadi, sbaoda amfani da karfin
Hamanu
Sarki Hurmas ya sake tasowa Sarki Darusul
ya taso
masa.
da dukkan karfinsa, ya rugo gareshi, shima sai Koda suka hadu a tsakiya sai kowa ya soke kowa da takobi a ciki suka kame a tsaye rukunkume da juna kamar gumaka ba tare da sun fadi ba.
A wannan lokaci su Boka Shamnas na kwance a
kas suna haki da numfashi da kyar, sun kasa ci gaba da fada. Boka Salbatu ya dubi boka Shamnas ya budi baki da kyar ya ce, "Ya kai Shamnas, me za hana mu yiwa juna sulhu mu hakura da komai, domin mu tsira da rayuwar mu mu koma ga iyalanmu. Ka sani cewa kana da da karamin yaro guda daya, nima haka. Kuma bamu gama basu dukkanin
Boka ilimin mu na tsafi ba." Shamnas ya bushe da dariya ya ce, "Kwarai kuwa, maganar ka gaskiya ce. To amma ka sani cewa
bakin alkalami ya bushe, domin mun riga mun mutu nan da dakika biyar. Wadannan kuttun iska kuwa, suma nan
da dakika biyar za su fashe iskar ciki ta watse. Ka sani cewa duk duniya in ban da ni da kai babu wand aya san yadda za'a sake tattaro wannan iska. Daga karshe ina Kiai shawartar ka d aka rungumi kaddara kada ka yi wani yunkuri na ceton rayuwar ka, domin babu lokacin yin hakan".
Ai kuwa Shamnas biyun suka kama na gama ſadin hakan ne duk su yin amai, suna zubar da wata irin kumfa daga bakinsu. Cikin matukar Karfin hali Boka 30
Salbatu ya yi tsafi, wani gabjejen aljani babban hadiminsa mai suna Karbulu ya faso ta karkashin kasa ya
Salbatu
gabata gare shi. Cikin rawar murya da numfashi boka ya dubi Karbulu ya ce,"Yai sauri ya dauke shi ya kaishi gidansa da ke daular Dulkar." Cikin tsananin zafin nama Karbalu ya suri Salbatu ya aza shi a gadon bayansa ya tashi da shi sama. A dai- dai lokacin ne kuttunan iskar nan guda biyu suka yi bindiga, suka haifar da wata irin gagarumar wuta wadda
ta narkar da komai na wajen, har da duwatsu kuwa. Ilatta fatalwoyin nan da ke kan tsibirin rayuwa sai da suka shige cikin karkashin kasa suka buya, domin inda
sun tsaya kamshin iskar kawai zai iya hallakasu.
Sai da ya rage saura dakika goma aljani Karbatu
ya iso gidan boka Salbatu, sai rai ya yi halinsa, wato
Salbatu ya mutu akan aljani Karbalu. Sai dai kafin ya
mutu ya umarci Karbalu da ya kaiwa mutanen gari
labarin abin da ya faru a can bakin kogin tsibirin
rayuwa. Kuma ya umarce shi da ya binne gawarsa a
cikin gidansa, domin za ta yi amfani nan gaba ga dan sa
Arufa.
Lokacin da aljani Karbalu ya sauke gawar boka
Salbatu a tsakiyar gidansa, Arufa na zaune a tsakar gida
yana wasa shi kadai. A lokacin bai fi shekara biyar ba.
Koda ya ga aljani Karbalu ya sauke Salbatu, kuma jikin
Salbatu a sandare ya ke baya motsi, sai ya kwala ihu.
Nan take mahaifiyarsa Hazila ta rugo daga cikin daki a
firgice. Koda tayi arba da gawar mijinta sai ta kwala ihu,
la isa kan gawar ta tsugunna ta ci gaba da