iya kula da bayin nan ba ne? To ka sani umarni nake baka ba wai roƙonka nake ba."
Cikin rawar jiki Adaraku ya ce, "Tu..."
Ba nake ranka ya dade. Nan take Adaraku ya tusa keyar dakarunsa suka nusa cikin daji. Tun su Najwas na hango su Adaraku har sai da suka bace musu da gani.
"Ee, oe," ya dubi sauran bayi,
"Utara in kwatar 'yanci."
Kafin wani daga cikinsu ya ce, sai ya zare takobinsa ya fara. Ee, Najwas ya
suka birkashi, sammie & se@0absl a ltsailtsaye sun zare makamai. Ba shiri su Najwas suka ja linzamin dawakansu suka yi turjiya. Nan fa aka tsaya ana kallon kallo. Cikin tsananin fyshi shugaban dakaru Adaraku ya dubi sarkin yaki ya ce, "Ya kai sarkin yaki, abin da nake so daga gare ka shi ne ka cire hular kanka domin mu ga fuskarka. In ba haka ba kuwa yanzun nan zamu afka muku gaba daya mu hallaka mu." Har Najwas ya buɗe baki zai ce wani abu sai kawai ya ji Zarima ta
kyalkyale da dariya ta ce, "Karyarka ta sha karya. Ya kai shugaban dakaru ka sani cewa kai baka isa ka sani na cire hular kaina ba, haka kuma baka isa ka firgita mu da batun mutuwa ba. Don haka a shirye muke a gwabza mu da ku."
Ko da gama fadin haka sai Zarima ta zare takobinta ta sakarwa dokinta kaini ta nufi su Adaraku.
Ko da ganin haka sai bawa Najwas ya yi sauri shima ya zare takobinsa ya sukwani dokinta don ya sha gaban Zarima domin kai mata kariya, saboda ya san cewa bata iya yaki ba nan da nan za a hallakata. Wani akasi da aka samu shi ne kafin Najwas ya riski Zarima tuni ta shiga tsakiyar su Adaraku. Nan fa Najwas da sauran ‘yan uwansa bayi suka ga abin al'ajabi. Kawai sai gani suka yi Zarima ta zama tamkar shaidaniya a cikin dakarun, sai ragargazarsu take kamar birni akan bishiyar ayaba. Cikin hanzari su bawa Najwas suka kai mata dauki. Nan fa wuri ya hargitse, kura ta turnuke sama da kasa. Karafkiyar karafa da ihun mazaje ya cika dodon kunne, duk inda ka duba sai dai kaga fatan jikin dan adam da kuma jini yana malala.
Wahoho, ba a san maci tuwo ba sala miya la. Babu abin da zai burge mutum face yadda bawa Najwas ke ta kutsawa cikin dakaru yana sare na sarewa, yana banke na bankewa. Sala dai kaga yana samarwa kansa hanya...
Da ƙarfin tsiya. A saneacen sauran bayi kuwa, abokan tafiyar Najwas, al'amarin ya ci tura domin kare jini, biri jini ake yi tsakaninsu da dakarun; wato suna kashewa, ana kashesu. Amma abin da zai ba wa mutum sha’awa shi ne hakika bayin sun yi rawar gani domin gashi dai adadinsu bai fi arba’in ba amma sun zame wa dakarun alakakai domin har rabin sa’a ta shude mutum tara kadai aka kashe a cikinsu.
Abokan Najwas kuwa wato Kaumuz da Faluza suma ba ƙaramin ƙoƙari suke ba domin suma duk inda suka sa gaba sai dai kaga maza na zubewa ƙasa kamar ana sassabe a gona.
Ana cikin wannan gumurzu ne wani badakare ya shammaci Zarima ya makota. Ta baya ta fado ƙasa daga kan dokinta. Kafin ta miƙe tsaye badakaren ya daka tsalle ya fado kan ruwan cikinta, yasa kotar takobinsa ya gabza mata naushi aka. Take Zarima ta sume. Badakaren ya kai hannayensa biyu da nufin ya cire hular kanta.
A dai-dai wannan lokaci ne hankalin bawa Najwas ya zo kansa ya hango abin da yake shirin yi. Cikin matuƙar zafin nama Najwas ya daka tsalle sama sai ga kafafunsa bisa kawunan jama’a. Tamkar yana kan turba haka ya taka kan mutane yana gudu har ya iso gaban wannan badakare dake ƙoƙari cire hular kan Zarima. Tun a sama ake…
takobinsa ya sare kan badakaren. Tamkar shaho ya suf!
An tsako haka Najwas ya suri Zarima ya goyata a bayansa tare da irin ya sake daka tsalle ya haye kan dokin Zarima ya ci gaba da yaki. Hakika wannan aninta ta kai gwaninta domin ba kowane jarumi bane zai iya yin hakan ba. Duk wannan abu dake faruwa Zarima a sume take bata farfado ba. Ko da Najwas yaga Zarima na layi a bayansa zata fado sai yayi sauri ya cire damararsa ta yaki ya daure jirkinta da nasa ya ci gaba da ragargazar maza. Duk inda ya nufa dekinsa sai dai kaga yana banke mutane suna zubewa ƙasa shi kuwa idan aka kawo masa sara ko suka sai dai kaga ya kare ko ya goce, ba a sameshi ba.
Ana cikin wannan gumurzu ne shugabannin dakarun, adakaru, ya lura da irin ɓarnar da bawa Najwas ke yi musu; a kalla shi kadai ya kashe...
A sama da dakarun hamsin. Ko da fahimtar haka sai zuciyar Adakaru ta kama tafarfasa, ya fusata ainun. Kawai sai ya sakar wa dokinsa Kaimi ya tunkari Najwas. Ko da suka haɗu sai aka buɗa musu wuri, suka ware gefe ɗaya suka fara sabon artabu.
Idan gwani ya haɗu da gwani, a sannan ne juriya, gwaninta da sadaukantaka suke motsawa a banbance tsakanin aya da tsakuwa.
Da farko Najwas da Adakaru sun ja da baya, sannan kowa ya zaɓuri dokinsa suka haɗu a tsakiyar, suna masu kaiwa juna sara. Ko da takubban nasu suka buɗe sai tartsatsin wuta ya taso. Maimakon su sake ja da baya kawai sai suka ci gaba da kaiwa juna sara da ƙarfi.
Suka cikin matuƙar zafin nama da juriya, babu wanda ke nuna alamar gajiyawa a tsakaninsu.
Yayin da faɗan nasu ya ƙara tsanani, Adakaru ya fara ƙoƙarin janyo Najwas da Zarima cikin su rikito, rasa gaba ɗaya. Ko da Najwas ya fahimci manufar Adakaru sai ya ƙara zage damtse ya ƙara yarda ya faɗo ƙasa. Ko da faɗan nasu ya shiga halin tsaka mai wuya wato ya zama cewa kowa ya fara galabaita sai ran bawa Najwas ya ɓaci domin ya san cewa in dai aka ci gaba da yaƙin a haka Adakaru zai iya kai shi ƙasa. In kuwa ya kai shi ƙasa zai iya ganin fuskar Zarima.
Ba zato ba tsammani sai Adakaru ya ga Najwas ya daka tsalle daga kan dokinsa ya yi sama duk da cewa yana goyewa da Zarima a bayansa, nauyinta bai hanashi tashi saman ba. Kafin Adakaru ya ankara tuni Najwas ya doki kirjinsa da ƙafafu biyu. Saboda juriya da naƙin irin na Adakaru sai ya maƙalƙale cikin dokinsa da ƙafafunsa, yaƙi yarda ya faɗo ƙasa amma kafin ya ɗaga da kansa sama tuni Najwas ya sake daka tsalle na biyu daga kan dokinsa tamkar iska, haka ya zo ya kama gashin kan Adakaru, ya sa takobi ya yanke kansa sannan ya koma kan dokinsa ya dira hannunsa na hagu na riƙe da kan Adakaru, hannunsa na dama kuwa na riƙe da takobi, jini na diga a jikinta.
Wohoho wanda ya iya ya huta. Babu abin da ya razana sauran dakarun face ganin tsananin zafin naman bawa Najwas yadda...
Cikin dakika ɗaya ko biyu ya bar kan dokinsa ya cizge.
Kan Adakaru kuma ya koma kan dokinsa.
Finnun Najwasa shi suka firgice suka jefa wandunansu da iska suka bar gawarwakin 'yan wajen. A sannan ne fa hankalin kowa ya taƙure.
Jikinsa aka zazzauna ana haki, masu duba jikinsu na dubawa, masu kuka na ƙokawa sun paina gawar 'yan uwansu bayi. Shi kuwa bawa Naw a sai ya yi sauri ya kwance Zarima daga bayanta—gttko da ita kasa.
Nan da nan aka nemo ruty: aeyyatava Zarima ta farfado. Ko da ta bude idan: pasara sai farin ciki ya lullube ta, ta dubi Najwas.
Murmushi ta ce, “An gaishe da jarumin jarumai.
‘Kayi babban aiki, dole ne a gode maka.’ Najwas murmushi ya ce, “Ai bani za a gode wa ba, ubaige.
‘Musulunci ne abin godiya domin taimakonsa na Bers nuka sami wannan nasara. Ina sanar da ké @ews, ikacin da naga yakin ya yi tsamari Adakaru na fini, amun nasara a kaina sai na kama yin addu'a.
‘Cikia gueiyata ina mai neman taimakon gaggawa wajen Allah.’
Bisa mamaki kuwa sai naji wani irin sabon karfi da sabon zafin nama na shiga jikina. Haki duk abubuwan da nayi na bajimta a wannan yaki sain’t hasan ba yin kaina ba ne. Amma abin da kikayi shi yafi bani mamaki, ashe dama kema mayakiya ce ban sani ba.
Ko da jin wannan batu sai Zaritha ta murmushi ta ce, “Na rantse da girman ubalijji, musulunci a iya rayuwata ban taba yin yaki ba sai a wannan rana.
Kamar yadda ka nemi taleaken yi, sma kuma sal ubangijin musulunci haka nima na nem. Naga nayi abin da ban taba tsammani ba.”
Haka dai Zarima da Najwas suka ci gaba da tattaunawa har aka gama binne pawarwakin bayin da suka mutu a wannan yaki sannan suka hau dawakansu suka nusa gaba. Wannan shi ne abin da ya faru ga su bawa Najwas bayan sun fafata kazamin yaki da dakarun dake yi musu rakiya zuwa birnin Kisra.
A can birnin Rum kuwa, tun daga ranar da aka kulle sarkin yaki Uhaisu a cikin dakinsa nan na gidan sarauta, sarki Mazahir bai sake waiwayarsa ba. Kullum sai dai a b...
A shi abinci sau ɗaya a rana, haka ma ruwan sha sau ɗaya ake ba shi har tsawon kwanaki uku. A yammacin kwana na uku ne Uhaisu ke zaune a cikin ɗakin, ya yi tagumi yana tunani cikin takaici bisa halin da ya tsinci kansa a ciki. Babban abin da yafi damun Uhaisu shi ne rashin samun damar tafiya birnin Bayi don risƙar su Jarumri Najwas. Haka kuma akwai wani zobe nasa wanda ake hannun 'yarsa Zarima, inda a halin yanzu yana tare da zaoben da tuni ya kuɓutar da kansa. Kuma ita kanta Zarima inda ta san amfanin zoben, ba za ta sha wahalar komai ba. Inda aka sami matsala shi ne Uhaisu bai san cewa Zarima ta ɗauki zoben nasa a cikin ɗakin da yake ajiye kayan yakinsa sai bayan ta tafi, nemi zoben ya rasa. Tabbas yanzu Uhaisu ya sami karyar zuciya don yasan cewa duk shirinsa ya wargatse, don haka bakin ciki ya taru yayi masa katutu a zuciya.
Uhaisu a cikin wannan hali na bakin ciki ne ya ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin da yake ciki. Cikin sautin ubaṭsu a eee tsaye, tuni ya fara tunanin hanyar da zai nema sa’ar guduwa musamman idan mutum giya ne zuwa uku masu niyyar shigowa; yasan cewa da ƙarfin tsiya zai iya banke su duk da cewa hannayensa da ƙafafunsa a daure suke da sarka.
Ƙofar na buɗewa sai Uhaisu ya fara arɓa da sarki Mazahir a tsaye a bayansa, boka Amkas ne tare da wasu ɗakaru mutum hamsin. Ko da ganinsu sai jikin Uhaisu ya yi sanyi, ya kasa motsin komai. Sarki Mazahir ya tako ƙafafunsa ya zo dafaɗa Uhaisu, ya tsaya yadda suke iya jin numfashin juna. Sarki Mazahir ya yi murmushin mugunta ga Uhaisu ya ce, “Ya kai sarkin yaki, ka sani cewa na sanka, sani ba na wasa ba, don haka duk motsin da zaka yi ina iya fassara shi. Za mu yi maka tambayoyi guda uku, ina mai shawartarka da ka ba mu gaskiyar amsar tambayoyin domin rayuwar ‘yarka Zarima na hannunmu. Idan ka yi mana ƙarya, tamkar ka salwantar da rayuwar ‘yarka ne.”
Ko da jin wannan batu, sai Uhaisu ya dubi sarki Mazahir cikin firgici ya ce, “Kana nufin cewa a halina yanzu ‘yata na hannunku ne?” “Ko shakka babu, Zarima na hannunku, boka Amkas ne.”
Ya yi wannan furuci.
Uhaisu ya yi shiru, bai ce komai ba sai ya kalli boka Amkas idanu. Amkas ya karaso kusa da Uhaisu, ya dubeshi ido da ido, ya ce, tambaya ta farko a gareka ita ce: ina zobenka na tsafi yake? Tambaya ta biyu, menene ya faru har aka sameka a daure a cikin gidanka kuma Zarima tasa kayan jini-jini bayan ka umarci 'yarka ta gudu? Tambaya ta uku ita ce, a mafarkashiya kake shiryawa sarki Mazahir har da ka aikawa su bawa Najwas wasika, suka bijire? Lokacin da sarki yafi Uhaisu ya ji waɗannan tambayoyi sai ya bushe da dariya. Al'amarin da ya baiwa sarki Mazahir da boka Amkas mamaki kenan.
Sarki Mazahir ya dakawa Uhaisu tsawa ya ce, menene manufar wannan dariya taka? Uhaisu ya hade fuska ya ce, da farko dai bisa tambayar da kuka yi mini ta farko cewar ina zoben tsafin na yake, na fuskanci cewa kun yi mini karya, tabbas 'yata bata tare da ku domin zobena na tare da ita inda kuna kama ta da kun sami zobena. Game da tambayarku ta biyu da ta uku kuwa ba zan baku amsoshin su ba ko da za ku kashe ni.
Ko da jin wannan batu sai sarki Mazahir ya fusata, ya dubi dakarun da ke bayansa ya ce, ku yi ta dukansa har sai ya suma. Ko da jin wannan abu sai masu fushi da fushin wani suka bi umarni, wato suka fara nakadawa Uhaisu duka. Tun yana tsaye sai da suka kai shi as, kuma tun yana motsi sai da ya daina.
Ko da ganin haka sai sarki Mazahir ya dubi boka Amkas ya ce, tabbas hukuncin kisa ya tabbata akan Uhaisu. Amkas ya gyada kai ya ce, kwarai kuwa abin da za mu yi kawai shi ne mu jira dawowar sadauki Kumazu.
Nan take sarki Mazahir, boka Amkas da waɗannan dakarun hamsin suka fita daga cikin daki, aka sake janyo kofa aka garkame. Wannan shi ne abin da ya faru ga sarkin yaki Uhaisu a can birnin Rum.
Alamarin su shugaban birnin bayi kuwa wato Kumhas loakein da suka yi ta tafiya cikin sauri don su riski su bawa Najwas sai da suka shafe kwana uku suna tafiya sannan suka iso kauyen Hirizo. Da zuwan suka sami labarin cewa yau...
Wata uku da zuwansu bawa Najwas kuma har sun yi sallama. Sun wuce izuwa birnin Kisra don aiwatar da pasar yaki bayin. Ko da jin wannan batu sai hankalinsu Kumhas ya dugunzuma, ko hutawa basu tsaya yi ba suka ci gaba da tafiya ba sassautawa ya zamana babu yadda zango, duk da rana. Ko abinci za a ci a tafe ake ci, ba a tsayawa face idan anga dawakai sun sare. Cikin gaggawa sai a tsaya a basu abinci da ruwa, da sun koshi sai a ci gaba da tafiya. Cikin kwana daya da rabi suka iso dajin nan inda aka fafata yaki tsakanin su Najwas da su Adakaru. Da zuwa suka ga gawarwakin su Adakaru har sun rube, tsuntsaye sun ci rabonsu. Ko da zuwa wannan wuri sai su shugaba Kumhas suka sauka daga kan dawakansu suna dudduba gawarwakin. Nan take suka shaida gawarwakin, don haka sai hankalinsu ya kara dugunzuma suka yunkura da nufin su gaggauta ci gaba da tafiya. Kwatsam sai suka hango wani abu daga can sama kamar tsuntsu yana sunƙowa kas. Ko da abin ya dira kan turba sai suka ga ashe Sadauki Kumazu ne bisa aljani Hukumul Ansabu rife da sandar tsafi. Ko da ganinsa sai su Kumhas suka risina a gare shi suka kwashi gaisuwa, Sadauki Kumazu ya dubi Kumhas ya ce: "Yaku wadannan dakaru ku yi sani cewa sarki — .... zuwa inda zamu riski su Najwas mu kamosu." Gama fadin haka, ke da wuya sai sandar hannun Kumazu ta juya ta dubi gabas kawai. Sai aljani Hukumul Ansabu ya kada fuka-fukansa ya nufi gabas din. Suma su Kumhas sai suka nufi gabas din.
Shin su Najwas zasu sami nasarar zuwa kauyen Harmut inda zasu boye Zarima? Shin za a kashe sarkin yaki Uhaisu? Wace irin cin amana Sadauki Kumazu ya yi wa marigayi sarki Samrus? Tsakanin sarki Mazahir da bawa Najwas, waye zai auri gimbiya Zarima? Mu hadu a littafi mai suna Raba Gardama don jin ci gaban wannan labarin.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels