Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
ya kwashi gaisuwa sannan ya ce, “Ya shugaban bokayen wannan nahiya, wace bukata ce da kai a gareni ka kirawo ni a irin lokacin da ba ka saba kirana ba?” Boka Amkas ya yi murmushi ya ce, “Hakika wannan kira da na yi maka na gaggawa ne. Ina son zaka ɗauki wani babban barde ne yanzu domin ku tafi neman wasu manyan abokan gabar sarki Mazahir sannan ku tabbatar da cewa kun taho tare da Zarima ‘yar sarkin yaki Uhaisu.” Ko da jin wannan batu sai aljani Hukumul Ansabu ya bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da saukar aradu sannan ya tsuke bakinsa ya ce, “Na rantse da darajar tsafi cire silin gashi a cikin tandun mai yafi wannan aiki wahala a wajena, don haka ina mai rokon alfarmar ka gaggauta sallamata, domin nima ina kan wani gagarumin aiki ne na cika burin rayuwata. In ba don kai ne ba hafika babu wani mahaluki da ya isa ya tsaidani akan wannan bukata tawa.” Rufe bakin aljani Hukumul Ansabu ke da wuya sai ga Sadauki Kumazu ya shigo cikin turakar sarki Mazahir sanye cikin kayan yaki. Hakika Sadauki Kumazu ya cika gabjejen mutum mai kwarjini da ƙirar sadaukantaka. A gaba ɗaya birnin Rum, in banda sarki Uhaisu, babu wani sadauki wanda a ƙin yaki Kumazu farfi. SEAEESE Le ee WCET Ss EOE C NENG TAe beewae weewe FARMAKI 3 da Kirar jarumtaka. Wani abin mamaki shi ne ko kadan marigayi sarki Samrus bai taba jan sadauki Kumazu a jikinsa ba, ko yaki za a tafi sai sarki Samrus ya ce ya yafewa Kumazu. Babu yadda yarima Muzahir bai yi ba akan ya janyo Kumazu zuwa cikin harkokin sarauta amma sai sarki Samrus yaki yadda. Yarima Muzahir ya sha tambayar sarki Samrus dalilin da ya sa baya ƙaunar Kumazu amma bai taba gaya masa dalilin ba. Akwai wata rana da yarima Muzahir ya fashe da kuka a gaban sarki Samrus ya ce, lallai sai ya sanar da shi laifin da Kumazu ya yi masa ya tsane shi. Lokacin da sarki Samrus ya ga yarima Muzahir ya tayar da hankalinsa akan hakan sai sarki Samrus ya dubeshi idanunsa cike da ƙwalla ya ce, akwai zargin cin amana tsakanina da Kumazu don haka har abada ba zan taba yarda da shi ba. Ba ni da tabbacin Kumazu ya ci amanata amma har na mutu jikina na bani cewa ya ci amanar tawa inda ina da yakini akan hakan da tuni nasa an hallakashi. Babu irin abin da ban yi ba akan na gani gaskiyar al'amarin amma abu ya gagara. Nayi yawo wajen bokaye da yawa amma duk sun kasa gano mini gaskiyar lamarin. Ya kai dana ko bayan raina ka ci gaba da bincike akan wannan cin amana da nake zargin Kumazu ya yi mini domin idan ta tabbata cewa ya ci amanar tawa tabbas ya yi maka illa babba. Yayin da yarima Muzahir ya ji wannan batu daga bakin mahaifinsa Samrus sai ya matsawa sadauki Kumazu da tambayoyi akan ko yasan abin da sarki ke zarginsa da yi na batun cin amanarsa? Kullum abin da Kumazu ke 17 CC aon. ee eee! gon dt® Abdul'aziz Sani Madakin GIF" wata dukiya da dadewa, ... at ne akwal x hy gayawa Muzahir shi ne aƙwá yaraga aka bashi ajiya tun kafin sarki Samrus ya ce sirri ce a cikin ajiya to akan daga baya ɓarayi suka biya : zargin sa cowa ya boye wannan dukiya ne sarki nai i ba. Sa'adda yarima dukiyar ne amma ba sirri a ciki masu da haka - bayani sai ya 84 - Muzahir ya ji wannan Day - uku da ... Kawari cowa duk ranar da ya kuma ya yiwa Kumazu auke" daya d Aga cikin zama sarki zai janyoshi a jiki ya ƙamƙama. Manyan fadawa. Yau ita ce rana ta farko da Kumazu ya ji an kirashi zuwa fada tun kafin rasuwar sarki Samrus. — Ko da ganin sadauki Kumazu sai sarki Muzahir ya dubeshi ya danka masa wannan sandar tsafi wacce boka Amkas ya ba shi sannan ya umarce shi da ya hau kan aljani Hukumul Ansabu. Ba tare da gardamar komai ba, sadauki Kumazu ya hau kan Hukumul Ansabu ya zauna. Sarki Muzahir ya ƙara kallonsa ya ce, na umarce ka da ka riƙe wannan sanda da kyau kada ka yarda ta salwanta a hannunka. Ko da gama faɗin haka sai sarki Muzahir ya dubi boka Amkas ya ce, sai kayi masa bayani. Amkas ya dubi Kumazu ya ce, amfanin wannan sanda ta hannunka shi ne, kukaje da kanta zata dinga nuna maka yadda za ku cimma makiyan sarki. Abin kai da wannan aljani kyautayiya ce ga gimbiya Zarima nan da kwanaki. Wannan shi ne ilimin da woka ta koya gare su nan. Ko da arki ya tura aka gama. Muzahir ya dubi sadauki, da wannan jawabi sai sarki Muzahir ya ce, Kumazu, idan har ka sami nasara bisa wannan aiki da na baka, kana dawowa zan baka sarautar sarkin yakin birnin Rum kuma zan baki kyautar dukiya mai yawan gaske gami da barori da kuyangi guda dubu. Gidan sarkin yaki Uhaisu kuwa ya zama naka kuma kai zaka aurar da gimbiya Zarima a gareni. A ranar da na auri Zarima za a rataye sarkin yaki Uhaisu. Ko da jin wannan batu sai sadauki Kumazu ya cika da tsananin farin ciki ya dubi sarki Muzahir ya yi godiya sannan ya ce, ya shugaba, ina rokon alfarma guda ɗaya a wajenka. Wannan alfarma ba kome bace face ina son a ranar da za a rataye Uhaisu, na zamo ni ne wanda zai zarge igiyar da zata shakeshi ya mutu. Ko da jin haka sai sarki Muzahir ya dubi Kumazu cikin mamaki ya ce, kai kuwa menene dalilin da yasa kake son naka kashe Uhaisu da hannunka? Kumazu ya ce, a duniya bani da makiyi wanda yafi Uhaisu domin shi ne asalin sanadin gabar dake tsakanina da mahaifinka, kuma shi ne mutumin da ya cusa mini bakin cikin rayuwar duniya ya hanani zama sarki ya... Aikin Kasar nan. Babu abin da ban yi ba sai na samu wannan sarauta, amma sai Uhaisu ya tarwatsa dukkan shirina. Ina tabbatar maka da cewa yadda na tsani Uhaisu haka na tsani mutuwata. Gabata da Uhaisu tsohuwa ce tun kafin a haifeka, ya shugabana kuma labari ne mai tsawo ba zan iya sanar da kai ba a yanzu. Ko da gama faɗin haka sai sarki Muzahir ya yi murmushi ya ce, "Kar ka damu, kai ne ajalin Uhaisu kuma zan kasance mai cika alkawari a gareka muddin ka samu nasarar aikin da na baka." Sai boka Amkas ya Abdul'aziz Sani Madakin Gini. Gama faɗin haka ke da hole. Nan take Hukunci zunguru aljani Hukumul Ansabu a yi sama shi da Ansabu ya buɗe fuka-fukansa ya tashi ta sama sadauki Kumazu suka ɓaƙa haske suka haskaka ikin sararin sama zuwa CiN'™ : rufin turakar suka yi bin da ya faru tsakanin — 3 | ani samaniya. Wannan shi ne Amkas a fad iwi sarki Muzahir da bokansa. Al'amarin “au-bawa Najwas, kawar lokacinsu da suka sakarwa dawakansu linzami suka zaburesu da udu sai suka wanzu suna ta taftiya, ba su tsaya ba sai __ Bayan sa'a uku bayan Zarima ta tabbatar da cewa sun yiwa su shugaba Kumhas nisa, wato sun basu tazara mai yawa yadda ko da sun biyo bayansu ba zasu cimma su ba tunda dole ne su ma su dunga ya da zango don tita gajiya. A inda su Zarima suka yada Zango a cikin wari aramin Rauye ne da ake kira Hitiza. Ko da shigarsu cikin Kauyen na Hiriza sai hakimin dake riƙon Kauyen ya rigo da gudu har yana ci abinci a an neman tse ne fa. Yarfa ya faɗi gaban Zarima a zatonsa sarkin ya ri Uhaisu ne. Bayan Hakimi ya kwashi gaisuwa sai ya yi wa Uhaisu barka da zuwa. Kauyen Hiriza kuma ya tambaye shi dalilin kawo wannan ziyara. Ko da jin wace: Zarima ta yi magana cikin nitsé ee ee. ta ce hanya ce ta biyo daman ukawaj Actin yard. Zango. Muna kan hayarmu rie te ee ni mu ie on Cikin murna Hakimin ya yi wa sy Zarima min fs ee gidansa. Da zuwa yasa aka kawo musu sha, amma sai ya ware sarkin yaki ya kaishi cikin wani daki daban. Shi kuwa sarkin yaki sai ya kira bawa Najwas ya jashi. Izuwa cikin wannan daki suka shiga suka rufe ƙofa wato suka kadaita. Da shigar Zarima da Najwas cikin wannan daki tare da abincinsu da abin sha su sai suka zauna. Zarima ta cire hular ƙarfe dake kanta ta saki dogon gashin kanta mai santsi da sheƙi ya zuba ƙasan kafadunta — lokacin da ta kalle Najwas idanu tana mai murmushi. Shi kuwa Najwas tuni ya ɗimauc saboda ganin tsananin kyawunta domin a yau ne ya sami damar yi amta kallon tsaf amma don kada ta gane cewa kyawunta ya tafi da imaninsa sai ya kau da kai ga barin kallon fuskarta. Zarima ta dubeshi ta ce, to yanzu magana zamu fara yi ko kuwa abinci zamu fara ci? Ba tare da Najwas ya ɗago kai ya dubeta ba sai ya ce, ranki ya daɗe ai abincin ya kamata mu fara ci domin mu sami nutsuwa. Ba tare da wata gardama ba sai Zarima ta buɗe kwanon abincin ta kai hannu da nufin ta soma ci. Cikin sai Najwas ya riƙo hannunta ya ce, dakata ranki ya daɗe ai baki wanke hannunki ba bare ma ki yi bismilla kamar yadda addinin Musulunci ya tarbiyantar da mu. Ko da jin wannan batu sai Zarima ta janyoshi hannunta cikin sanyin jiki ta dubi Najwas ta ce, ya kai abin begena kayi sani cewa saboda amincewa da kai a cikin zuciyata duk abin da ka zo mini shi zan kasance marhaban da shi. Duk da cewar ba ni bayanin komai ba akan wannan addini na Musulunci na gamsu cewa shi ne addinin gaskiya tunda har kaima kayi jima'i da shi. Ka sani cewar labarin da Ukasha ya ba mu na rayuwar sa da Laaqi'a ya nuna cewa Musulunci ya tserar da rayuwarsa da ta a kan ƙa'ida, yasa na ji a jikina cewa addinin Musulunci shine addinin gaskiya don haka yanzu sai ka gaggauta shigar da ni wannan addini. Ko da baiwa Najwas ya ji wannan batu sai farin ciki ya lullubeshi. Nan take kuwa ya biyawa Zarima kalmar shahada ta maimaita sannan suka wanke hannayensu suka kama cin abinci. Sai da suka ci suka koshi sannan suka sha ruwa suka sake wanke hannayensu sannan Zarima ta ɗan kishingida tana mai fuskantar Najwas ta ce ni kam duk kayan... Yakin nan dake jikina sun isheni, so nake kawai na cire su. Najwas ya yi murmushi ya ce, ai dole ne su ishe ki saboda baki saba sasu ba. Ki yi hakuri mu gama magana, idan na fita sai ki kwabesu. Au kana nufin cewa ba tare da kai zan kwana anan cikin wannan daki ba? Najwas ya ce, ai ba zai yiyu ba mu kwanta waje ɗaya ba domin haramun ne a Musulunci baligi da baliga su kwanta tare muddin basu kasance muharramai ba. Da sannu zaki fahimci dokoki da nasihohin wannan addini da kuma yadda ya kamata ki bautawa Ubangijin Musulunci. Ni kam babban farin cikina shi ne da kika gane gaskiya cikin anfani lokaci kuma kika karɓeta. Yanzu dai wace magana kike so mu yi? Ko da jin wannan an tambaya sai gimbiya Zarima ta numfasa ta ce, ya kai ma so gimbiyu, a halin yanzu rayuwarmu a cikin haka ka sani cewa halin Yarima Muzahir a ko'ina yake yanzu. Ni nasan inda yake yanzu. Hankalinsa na kaina duk inda nake sai yasa an farauto ni. Bugu da kari hankalina a matuƙar tashe yake saboda rashin ganin isowar mahaifina garemu. Tabbas shima rayuwarsa na cikin haɗari domin Sarki Mazahir ya iya ganewa cewa shi ne ya shirya mini dabara na gudu. Abu na uku shi ne, ya za mu yi da waɗannan ɗakaru mutum dari da hamsin waɗanda ke tare da mu. Kaga dai har yanzu basu san cewa ni ce na yi shigar mahaifina ba. Idan muka ci gaba da yin wannan tafiya tare da su, babu mamaki nan gaba su gane ni. Lokacin da Zarima ta zo nan a zancenta sai bawa Najwas ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya ce: hakika duk abin da kika faɗa gaskiya ne kuma nima hankalina a tashe yake bisa rashin ganin isowar mahaifinki. Abin da nake zargi shi ne Sarki Mazahir ya gane shirin mahaifinki, yasa an tsareshi. Tabbas mahaifinki na cikin haɗari, ya zama dole mu yi tunanin ceton rayuwarsa. Dangane da batun waɗannan ɗakaru guda dari da hamsin, tuni na yi tunanin hanyar da zan bi mu kawar da su. Abin da yafi damuna shi ne ko shakka ban yi a halin yanzu shugaba Kum... Has ya sake turo wasu dakaru masu yawa sun biyo bayanmu, kuma shima sarki Mazahir ya turo wasu dakarun daban don ya sanar da cewa ke ma kina birnin bayi tare da mu. Yanzu abin da za mu yi shi ne mu tashi da sassafe mu kara gaba. Ki sani cewa kafin mu je kauyen Harmut sai mun wuce kauyuka uku nan gaba. Ya zama dole mu kara saurin tafiyarmu domin mu yi saurin zuwa kauyen Harmut inda zan rabu dake a hannun Ukashat. Ba zan sadu da mahaifinki inaji da yadda za mu sami nasara cikin abin da ke gabanmu ba. Zancensa san jikin Zarima ya yi sanyi, nan da nan idanuwanta suka kada kamar zata yi kuka. Ta ce, “Yanzu kana nufin cewa a kauyen Harmut za mu rabu? Ni kam babu abin da zai raba ni da kai face mutuwa.” Najwas ya ce, “Ai kuwa rabuwarmu ta zama dole, in ba haka ba kuwa gaba daya shirinmu zai iya tarwatsewa. Abin da nake so dake shi ne ki kwantar da hankalinki, ki sani cewa rabuwar tamu ta zuwa na ɗan lokaci ne. Ke kanki kin sani cewa akan dole zan iya nesa dake, kuma duk inda na tafi sai na dawo gare ki.” Haka dai Najwas ya yi ta rarrashin gimbiya Zarima cikin tattausan lafazi har ya samu nasarar kwantar mata da hankali. Ko da yaga hankalinta ya kwanta sai ya yi mata sallama ya fice daga dakin ya ja mata ƙofa. Ko da Zarima taga Najwas ya fice daga cikin dakin sai ta mike tsam ta cire gaba ɗaya kayan yakin dake jikinta, sannan ta bude jakarta ta ɗauko wata doguwar riga mai shara-shara mara nauyi ta saka sannan ta hau kan gadon ta kwanta. Ko da kwanciyarta sai barci ya kwashe ta saboda gajiyar dake jikinta. Kashegari kuwa da sassafe gimbiya Zarima… An tambaya sai ya yi murmushi ya ce, ai a hankali na buɗe ƙofar nan shiga. Juma na rufeta don kada na tashe ki daga barci. Zarima ta ce, ai da ka sani ka tasheni ko don ma ka fara koya min yadda ake yin wannan bauta ga Ubangijin Musulunci. Najwas ya juya ya fuskanci Zarima sosai sannan ya ce, ai ba zai yiwu ba na koya miki wannan aiki a nan domin abokan tattaunarmu za su iya gano sirrinmu. Ki sani cewa da farko ma akwai wanka da ya kamata ki yi na janaba domin ki zama mai tsarki, sannan na koya miki karatun wasu daga cikin ayoyin alKur'ani. Zarima ta ce, menene kuma alKur'ani? Najwas ya ce, shi ne littafi mai tsarki wanda ke ɗauke da kalmomin Ubangijin Musulunci kamar yadda kikaji a cikin labarin da Ukashat ya ba mu. Yanzu dai abin da nake so daga gare ki shi ne ki yi sauri ki shiga kewaye ki yi wanka kafin Hakimi ya aiko miki da abincin ƙalacin ki domin mu tuni an aiko mana da namu. Akwai wata magana mai muhimmanci da nake son mu tattauna yanzu. Ko da jin haka sai Zarima ta mike da sauri ba da gardamar komai ba ta shiga kewaye ta yi wanka. Ko da fitowarta sai Najwas ya yunkura da nufin ya fita daga cikin ɗakin. Zarima ta dubeshi ta ce, dakata, ina kuma zaka tafi? Najwas ya ce, zan ba ki wuri ne domin ki sami damar sauya kayan jikinki ki sa na yakin. Zarima ta ce, baka tsammanin cewa yawan shige da fitarka a cikin ɗakina zai iya sa ɗakarun dake tare da mu su fara zargin akwai wani abu na sum da muke shiryawa? Kayi zamanka anan kawai in yaso sai ka juya baya ni kuma sai na sauya kayan nawa. Kamar bawa da Ubangijinsa, haka Najwas ya bi waɗannan umarni wato ya juya baya ya sunkuyar da kansa. Ita kuwa Zarima sai ta kwabe kayan jikinta tsaf cikin kwanciyar hankali tamkar ita kaɗai ce a cikin ɗakin. Sannan ta sanya waɗannan na yaki. Ga ma hakan ke da wuya sai suka ji ana ƙwankwasa ƙofar ɗakin. Ko da jin hakan sai Zarima tayi sauri ta ɗauki hular ƙarfenta ta sa a kanta. Shi kuwa bawa Najwas sai ya mike ya je ya buɗe ƙofar. Tsaye a bakin ƙofar wata kyakkyawar baiwa ce rike da farantin. Abincin ƙalaɗɗen Sarkin ya ƙi. Fuskarta cike da murmushi tana yiwa bawa Najwas wani irin kallo mai tattare da alamar tambaya. Ko da Zarima ta lura da irin kallon da baiwar ke yiwa Najwas sai kishi ya kamata, don haka sai ta yi gyaran murya. Ko da jin gyaran muryar sai Najwas ya ratse ya baiwa baiwar hanya ta shigo cikin ɗakinsa. Baiwar ta zo gaban Zarima, ta tsuguna cikin biyayya ta ajiye farantin abincin kuma ta kwashi gaisuwa sannan ta mike tsaye ta nufi bakin ƙofa inda Najwas ke tsaye. Ko da ta zo gillaɗawa ta gabansa sai ta sake yi masa irin kallon da tayi masa da farko, wannan karonma har sigina tayi amsa tana mai yi masa inkiyar cewa in ya fita ya nemeta a waje. Duk wannan abu da ke faruwa tsakanin baiwar da Najwas Zarima na lura. Fitar baiwar ke da wuya sai Zarima ta ce, rufe ƙofar ka zo mu zauna mu tattauna maganar da za mu yi. Najwas ya rufe ƙofar sannan ya zo ya zauna a gefe ɗaya daɗe da Zarima, ya ce ai sai ki hanzarta cin abincin domin mu yi maganar da za mu yi mu fita saboda tuni abokan tafiyata sun gama shiri, mu kawai suke jira. Zarima ta dubi Najwas cikin murmushi mai taushi ta ce, kayi a hankali wannan baiwar da ta fita yanzu sonka take. Najwas ya yi murmushi ya ce nima na lura da haka amma bata san cewa ta makaraba tuni wata ta rigata mallakar zuciyata. Zarima ta ce, wacece ta rigata? Najwas ya ce wadda ke tambaya yanzu. Ko da jin haka sai Zarima ta bushe da dariya ta ce, idan har gaskiya ne na mallake zuciyarka to ka ciyar da ni da yatsun hannunka yanzu. Ba tare da gardamar komai ba kuwa Najwas ya yi bismillah ya tsuma hannunsa cikin farantin abincin ya dinga debo loma yana sawa a bakin Zarima. Ita kuwa ta dinga cin abincin tana mai Kura masa idanu tana murmushi. Har ya gama bata abincin ta koshi, bata daina kallon fuskar sa ba, ko kifa ido ma batayi; shi kuwa saboda kunya har sun kôi da kansa kas yake. Ko da ƙarfe bata abincin sai Zarima ta ce, ya kai – masoyina hakika ban ga laifin wannan baiwar ba. Ba da ta kamu da ƙaunarka faɗat ɗaya yanzu: yanzu. Cikin mamaki Najwās ya ce, "Ke kuwa, saboda me kika faɗi haka?" Zarīma ta yi murmushi ta ce, "Na rantse da girman Ubangijin Musulunci, ƙyawunka ya wuce yadda duk kake tsammani, kuma ga shi Allah ya yi maka sura mai ƙyau wadda ka iya jan hankalin kiwace irin mace. Ina tabbatar maka da cewa komai ƙyancin mace da matsayinta, in dai ta tsaya ta kalle ka tsawon dakika, tace sai dai idan ba ta da lafiya sai ta ji tana sha’awarka." "Haba Zarīma, kada ki rashin lafiya," Najwās ya yi dariya. "Ƙwarai fa, na manta cewa zũgani da yawa manē." Sai Zarīma ta sake yin murmushi a karo na biyu ta ce, "Na san cewa naka ƙyau ya fi nawa, wa maza ba mu domin ba kasafai ake samun ƙyawa ne." Najwās ya yi dariya sannan ya haɗe fuska ya ce, "Maganar ɗa mu yi, ɗa ke shi ne, da zarar mun bar wannan kauye mun yi nisa a cikin daji, ina so ki bai wa dakaru nan da nan biye damu umarnin su tafi neman ice a cikin daji mai yawa domin a gina miki ɗakin gaggawa inda za ki yi wanka ki huta. Ina nufin bayan yamma, tayi mun yada zango." Hikimata anan shi ne, da zarar sun tafi neman ice sai mu kama dawakansu mu yi gaba mu barsu a baya, babu yadda za a yi su iya cimmana. Kinga mun rabu da su kenan. Ko da jin wannan batu sai Zarīma ta yi dariya ta ce, "Hakika fa, kai ma ka cika mai basira, yaya aka yi ka yi wannan dogon tunani baka?" Inda fa an murmushi ya ce, "A wajen Ubangidansarkin yakin, kum pa sami irin wannan basira." Lokaci a can wani bangare kuwa inda sauran abokan a ns gidan Hakiai, wato bayi da dakaru, an ware ba ae ke zaune a waje. Suma dakarun sun koma shida nesa kaɗan da su suna gadin bayin. Shugaban dakarun dake gadin bayin tare da ɗaya daga cikin yaransa sun ware gefe ɗaya suna tattaunawa. Ya rno nasa mai suna Humaisu ya dubi shugaban yace, "Shugabana, nifa akwai wani abu guda ɗaya da yake daure mini kai a cikin wannan tafiya tamu. Wai shin me yasa sarkin yaki Uhaisu ya ja bawa Naj..." Wasu matuƙa a jikinsa kusan ko yaushe suna tare. Abu na biyu kuma, tun da muka fara tafiyar nan, ban ga sarkin yaki ya cire hular kansa ba ko sau ɗaya ba. Menene dalilin hakan? Ko da jin wannan batu sai shugaban Adaraku ya yi shiru yana juyar da al'amarin a cikin zuciyarsa. Daga can sai ya dubi Humaisu ya ce, "Jahika biri ya yi kama da mutum, kuma ruwan ba ya tsami banza. Ya kai, Humaisu, ka sani cewa yadda na san yunwar cikina, haka na san halayen sarkin yaki Humaisu. Na sha yin tafiya tare da shi kuma na ga sauyin al'amura a tare da shi wannan karon, don haka zarginka zai iya zama gaskiya cewa wannan ba Humaisu ba ne." "Abin da nake so daga gare ka shi ne ka gaya wa sauran dakarun cewa su zuba ido da kyau akan sarkin yaki kuma kada mu saki jikai da su." Humaisu ya risina ya ce, "An gama, ya shugabana." Gama fa ɗin haka, ke da wuya sai ga sarkin yaki da bawa Najwas sun fito a daidai lokacin ne, kuma Hakimi ya fito daga cikin gidansa don a yi sallama. Ba tare da ɓata lokaci ba, Hakimi ya kawo ƙarin guzuri ya bai wa sarkin yaki, yana mai godiya suka yi sallama a ka ci gaba da tafiya. Najwas ya isar a wa Jarima haɗa..., to sai bayan sun yi tafiyar sai ba da umarnin a tsaya a huta. Tsayuwar tasu ke da... Kamar yadda jariman ya kasance wike uku, sannan Zari ta a zango domin a ci abinci. Sai Zarima ta dubi shugaban dakarun ta ce, "Ina buƙatar ku shiga daji kai da yaranka gaba-cikin ku saro itatuwa ku kawo mini nan domin a gina mini ɗaki da zan shiga na yi wanka." Ko da jin wannan batu sai Adaraku ya dubi Zarima ya ce, "Ya shugabana, yanzu idan ni da dakaruna muka tafi cikin daji gaba ɗayanmu, waye kuma zai yi gadin bayin nan? Ka sani cewa ba a bai wa bayi yarda domin a ko yaushe za su iya bijirewa ko su ce za su gudu." Ko da jin haka sai Zarima ta dakawa Adaraku tsawa cikin muryar mahaifinta ta ce, "Shin kana tsammanin cewa ni kadai ba zan

Chapter 2 of 3