Bawa Najwas sun gama yiwa Ukashat addu'a, "Allah ya sa ya sake saduwa da matarsa." Amaila’ da mahaifinsa Hanafi da sirikinsa wato Shalhab sai kuma suka shiga tattaunawa akan abin da ya kamata su yi kafin sarkin yaki Uhaisu ya karaso ya riske su.
Ukashat ya dubi Bawa Najwas ya ce, "Ya shugabana, ni a nawa tunanin, ina ganin cewa duk shirin da za mu yi mu yi shi a yanzu lokaci guda, tunda ba mu san halin da sarkin yaki Uhaisu ke ciki ba. Tabbas idan gari ya waye, sarki Mazahir bai ga Zarimata ba zai iya sawa a tsare sarkin yaki Uhaisu. Duk dabarar da za mu yi mu yi ta a yanzu."
Ko da jin wannan batu, sai Kaumuz da Faluda suka ce, "Kwarai kuwa, wannan shawara da Ukashat ya kawo itace mafi alheri a garemu." Zarima tayi ajiyar zuciya sannan ta dubi Najwas ta ce, "Ya kai masoyina, kayi sani cewa ni bana shakkar mahaifina, domin na tabbatar da cewa duk halin da zai shiga zai iya fitar da kansa. Ni yanzu tamu rayuwa nake ji, domin tabbas da ni daku yanzu duk muna cikin hadari; don haka ya zama wajibi mu gaggauta barin wannan birni yanzu, don a koymushe zamu iya ganin dakarun sarki Zarima."
Bawa Najwas yayi, shi ne baice komai ba, ya shiga nazari da tunani a cikin ransa har izuwa wani dan lokaci. Daga can sai ya daga murya ya kira gaba daya bayin dake cikin gidan. Cikin biyayya suka taho gaba daya gareshi, kowa ya yi shiru wajen yayi tsit.
Ya yi gyaran murya ya ce, "Kamar mutuwa ta ritsa."
Najwas ta tsaki, ta ce, "Ya ku'ya uwana bayi, ban kira ku ane ba. Rinmu ga domin na wayar mana da kai bisa da 'a 'ahekaru da uka dade ana yi tsawon shekara da a wannan babban birni Rum. Da yawa daga cikinmu nan, yayenmu da kakanninmu ma sun rasa asali a cikin wannan tafarki na bauta. Shi kenan rayuwarmu zata zamo har abada a cikin bauta? Yaushe ne zamu samu 'yancin kanmu? Shin tsoron mutuwa da azaba sune zasu hanamu neman 'yancinmu? Lokaci ya yi da zamu zage damtse, ko mu mutu ko mu rayu domin neman 'yancin kanmu. Abin da nake so damu yanzu shi ne gaba dayan..."
Mu za mu tafi zuwa birnin Kisra bisa jagorancin gimbiyar Zarima a matsayin ita ce sarkin yaki Uhaisu domin gabatar da gasar yakin bayi. Ta wannan hanya ce ka dai za mu iya fita daga wannan birni kai tsaye mu wuce can birnin Kisran, kuma lallai za mu yi wannan gasa. Hikimar yin wannan gasa ita ce mu sake neman haɗin kan ‘yan uwanmu bayi na kwatar ‘yancinmu.
Suka rude da faɗin cewa sun yarda face Aine be ta aji.
Wannan shawara kuma a shirye suke su ba rayuwarsu don ganin sun ka su sallama wa ƙaƙƙarfan wahalar da ya addabi rayuwarsu. Ko da bin wannan cikakken lokaci, sai ya sami haɗin kan ‘yan uwansa bayi nan da nan cikin ɗan fannin lokaci, sai ya cika da farin ciki. Nan take ya dubi Ukashat ya ce, “Ya kai Ukashat, yanzu za mu tafi tare da kai da Zarima gaba ɗaya. Yayin da muka isa kauyen Harmut, za mu karɓi kayan Zarima nasa a jikina domin na je birnin Kisra a matsayin ni ne sarkin yaki Uhaisu. Kai da Zarima sai ku buya a cikin kauyen Harmut, kayi amfani da wannan dama wajen neman matarka Amaila. Lallai kada ku yarda a ganku har sai bayan hakanmu ya cimma ruwa.”
Ko da gama wannan jawabi sai Najkwas ya ba da umarnin a fara shirye-shiryen tafiya. Nan da nan dukkanin bayin suka yi shiru. Bayan an gama shiri tsaf sai Najwas ya dubi Zarima cikin matuƙar damuwa ya ce, “Kina masoyiyata, yanzu fa matsalarmu guda biyu ce kaɗai. Muna buƙatar dawakai da kayan yaki wanda za mu tafi da su zuwa birnin Kisra. Ta yaya za ki je ki yi wa shugaban wannan gida bayani a cikin muryar mahaifinki domin ki karɓo mana waɗannan kayayyaki?”
Ko da jin wannan tambaya sai gimbiyar Zarima tayi murmushi ta ce, “Kar ka damu, baní wajen ka gani.” Ko da gama faɗin haka sai Zarima ta ɗauki hular ƙarfe ta rufe kanta sannan ta tafi kai tsaye zuwa sashin da shugaban gidan bayi yake. Da zuwa sai ta iske shugaban a zaune, daƙaru sun kewaye shi, ya shagala da shan giya ana kade-kade da raye-raye a gabansa, yana ta ƙyalƙyala dariyar nishadi. Ko da shugaban ya hango sarkin yaki Uhaisu daga nesa, sanye cikin sulken yaki, sai ya mike tsaye zumbur ya nutsu.
Hauwa Sarki Zaria
Ismail Abdullahi
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Mansur Usman Sufi
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Musa A Dembo
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Ismail Abdullahi
Mansur Usman Sufi
Abdulaziz Sani Madakin Gini
by Jamila Sama'ila Yusuf
by Jameela Musa
by Janafty
by King Boy Isa
by Ummu Maher
by Ummyn Yusra
by Sumayya Abdulkadir Takori
by Zahra Muhammad Mahmud Surbajo
by Miss Xoxo
by Sadiya Garba Yakasai