Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Bawa Najwas sun gama yiwa Ukashat addu'a, "Allah ya sa ya sake saduwa da matarsa." Amaila’ da mahaifinsa Hanafi da sirikinsa wato Shalhab sai kuma suka shiga tattaunawa akan abin da ya kamata su yi kafin sarkin yaki Uhaisu ya karaso ya riske su. Ukashat ya dubi Bawa Najwas ya ce, "Ya shugabana, ni a nawa tunanin, ina ganin cewa duk shirin da za mu yi mu yi shi a yanzu lokaci guda, tunda ba mu san halin da sarkin yaki Uhaisu ke ciki ba. Tabbas idan gari ya waye, sarki Mazahir bai ga Zarimata ba zai iya sawa a tsare sarkin yaki Uhaisu. Duk dabarar da za mu yi mu yi ta a yanzu." Ko da jin wannan batu, sai Kaumuz da Faluda suka ce, "Kwarai kuwa, wannan shawara da Ukashat ya kawo itace mafi alheri a garemu." Zarima tayi ajiyar zuciya sannan ta dubi Najwas ta ce, "Ya kai masoyina, kayi sani cewa ni bana shakkar mahaifina, domin na tabbatar da cewa duk halin da zai shiga zai iya fitar da kansa. Ni yanzu tamu rayuwa nake ji, domin tabbas da ni daku yanzu duk muna cikin hadari; don haka ya zama wajibi mu gaggauta barin wannan birni yanzu, don a koymushe zamu iya ganin dakarun sarki Zarima." Bawa Najwas yayi, shi ne baice komai ba, ya shiga nazari da tunani a cikin ransa har izuwa wani dan lokaci. Daga can sai ya daga murya ya kira gaba daya bayin dake cikin gidan. Cikin biyayya suka taho gaba daya gareshi, kowa ya yi shiru wajen yayi tsit. Ya yi gyaran murya ya ce, "Kamar mutuwa ta ritsa." Najwas ta tsaki, ta ce, "Ya ku'ya uwana bayi, ban kira ku ane ba. Rinmu ga domin na wayar mana da kai bisa da 'a 'ahekaru da uka dade ana yi tsawon shekara da a wannan babban birni Rum. Da yawa daga cikinmu nan, yayenmu da kakanninmu ma sun rasa asali a cikin wannan tafarki na bauta. Shi kenan rayuwarmu zata zamo har abada a cikin bauta? Yaushe ne zamu samu 'yancin kanmu? Shin tsoron mutuwa da azaba sune zasu hanamu neman 'yancinmu? Lokaci ya yi da zamu zage damtse, ko mu mutu ko mu rayu domin neman 'yancin kanmu. Abin da nake so damu yanzu shi ne gaba dayan..." Mu za mu tafi zuwa birnin Kisra bisa jagorancin gimbiyar Zarima a matsayin ita ce sarkin yaki Uhaisu domin gabatar da gasar yakin bayi. Ta wannan hanya ce ka dai za mu iya fita daga wannan birni kai tsaye mu wuce can birnin Kisran, kuma lallai za mu yi wannan gasa. Hikimar yin wannan gasa ita ce mu sake neman haɗin kan ‘yan uwanmu bayi na kwatar ‘yancinmu. Suka rude da faɗin cewa sun yarda face Aine be ta aji. Wannan shawara kuma a shirye suke su ba rayuwarsu don ganin sun ka su sallama wa ƙaƙƙarfan wahalar da ya addabi rayuwarsu. Ko da bin wannan cikakken lokaci, sai ya sami haɗin kan ‘yan uwansa bayi nan da nan cikin ɗan fannin lokaci, sai ya cika da farin ciki. Nan take ya dubi Ukashat ya ce, “Ya kai Ukashat, yanzu za mu tafi tare da kai da Zarima gaba ɗaya. Yayin da muka isa kauyen Harmut, za mu karɓi kayan Zarima nasa a jikina domin na je birnin Kisra a matsayin ni ne sarkin yaki Uhaisu. Kai da Zarima sai ku buya a cikin kauyen Harmut, kayi amfani da wannan dama wajen neman matarka Amaila. Lallai kada ku yarda a ganku har sai bayan hakanmu ya cimma ruwa.” Ko da gama wannan jawabi sai Najkwas ya ba da umarnin a fara shirye-shiryen tafiya. Nan da nan dukkanin bayin suka yi shiru. Bayan an gama shiri tsaf sai Najwas ya dubi Zarima cikin matuƙar damuwa ya ce, “Kina masoyiyata, yanzu fa matsalarmu guda biyu ce kaɗai. Muna buƙatar dawakai da kayan yaki wanda za mu tafi da su zuwa birnin Kisra. Ta yaya za ki je ki yi wa shugaban wannan gida bayani a cikin muryar mahaifinki domin ki karɓo mana waɗannan kayayyaki?” Ko da jin wannan tambaya sai gimbiyar Zarima tayi murmushi ta ce, “Kar ka damu, baní wajen ka gani.” Ko da gama faɗin haka sai Zarima ta ɗauki hular ƙarfe ta rufe kanta sannan ta tafi kai tsaye zuwa sashin da shugaban gidan bayi yake. Da zuwa sai ta iske shugaban a zaune, daƙaru sun kewaye shi, ya shagala da shan giya ana kade-kade da raye-raye a gabansa, yana ta ƙyalƙyala dariyar nishadi. Ko da shugaban ya hango sarkin yaki Uhaisu daga nesa, sanye cikin sulken yaki, sai ya mike tsaye zumbur ya nutsu. U ya kame kamar gunki. Yayin da Uhaisu ya matso daɗa shi sai shugaban ya risina ya kwashi gaisuwa yana mai cewa, "Ranka ya dade, me kake da buƙata ka taho gareni da kanka? Ai da ka aiko an kirani." Uhaisu ya buɗe baki ya ce, "Yakai shugaban, wannan birni na bayi kayi sani cewa a yau mun kammala horon yaki kuma yau din ne zamu wuce zuwa birnin Kisra don tunkarar wannan gagarumar gasa. Don haka muna buƙatar dawakai hamsin da kayan yaki na mutum hamsin gami da isasshen guzuri." Ko da jin wannan batu sai shugaban ya sake risinawa ya ce, "An gama ya shugabana, kaje ku fita kai da jama'arka zuwa babban fili yanzun nan za a kawo muku wadannan abubuwa." Gama faɗin hakan ke da wuya sai Zarima ta juya ta nufi inda ta baro su bawa Najwas tana yin tafiya iri daya sak da ta mahaifinta. Zuciyarta cike da tsananin farin ciki da mamaki bisa ganin yadda ta iya sarrafa harshenta tayi murya irin ta mahaifinta sak. Lokacin da Zarima taje ta shaidawa su Najwas abin da ya faru tsakanin ta da shugaban birnin bayi sai gaba ɗayansu suka cika da mamaki. Najwas ya dubeta ya ce, "Ke kuwa da wace irin murya kikayi magana da shi a? Ya ane dake?" Cikin murmushi ba ta ce komai ba, kawal Saluɗi baki iri muryar mahaifinta; Nan 2 eee caine su Najwas suka kimtsa suka fito zuwa babban fili na cikin gidan. Da isowarsu babban filin, tuni an kawo musu dawakai, kaya... guzuri. Cikin hanzari dukkaninsu suka yi shiri, suka hau dawakan suka dora guzuri bisa dawakan. Bayan sun gama shiri tsaf sai shugaban gidan bayin ya zo gaban sarkin yaki Uhaisu ya ce, "Ya shugabana yanzu dakaru nawa kake buƙata wadanda zasu yi maka rakiya zuwa birnin Kisra?" Ko da jin wannan tambaya sai hankalin Zarima da nasu Najwas ya dugunzuma. Zarima ta dubi shugaban a cikin wannan murya irin ta mahaifinta ta ce, "Ai ni a yau bana buƙatar rakiyar dakaru domin na tabbatar da cewa ni kadai din nan zan iya tsare wadannan bayi tunda ba..." Su da yawa. Shugaban ya dubi Zarima cikin alamun damuwa yace, “Ya shugabana, ka sani cewa doka ce na a barka ka tafi tare da bayi ba tare da dakarun rakiya ba. Idan sarki Mazahir ya zo yaga nayi haka zai iya hukuntani, don haka kayi hakuri mu bi doka ni da kai.” Ko da jin wannan batu sai Zarima ta ce, “Wannan gaskiya ne, to shi kenan ka bani dakaru adadin yawan fursunonina.” Shugaban ya ce, “A'a ai dole ne yawan dakaru ya ninka yawan fursunoni sau uku, don haka zan baka dakaru dari da hamsin.” Zarima ta ce, “Shi kenan, hakan yayi daidai.” Nan da nan cikin kankanin lokaci aka shirya dakaru guda dari da hamsin suka sa Najwas a tsakiya sannan aka bude babbar kofar birnin bayi. Gaba ɗaya wannan zuga tasu Najwas da ta dakaru suka fita. Lokacin da Zarima ta zo giftawa ta gaban shugaban birnin bayi tana bisa dokin sai idanunsa suka kai ga kan ‘yan yatsun hannunta ya gansu sirara irin na mata. Al'amarin da ya jefashi cikin tsananin mamaki da kaduwa. Har ya ce Najwas ya ƙada dokin don ya tsaida ita. Dokinsa domin ya yi ƙaimi yay! aa shugaba ne a masa kafa. Shugaban ya rusa ihu saboda tsananin ogi; kallonsa bai yi da radadin da yaji. Shi kuwa Najwas ko faru sai ta ba. Ita kuwa Zarima ko da taga abin da ya auku, ba da umarnin a sukwani dawakai da gudu. Nan gaba ɗayan tawagar suka sakarwa dakansu mage suka zabura aguje. Ko da ganin haka sai shugaban birnin bayi ya dakawa sauran dakaru ntsawa ya ce, “Yamaza, suje su hau dawakai su bi bayan wadannan ayi su dawo da su.” Cikin gaggawa da dimauta dakaru nasa suka bi umarnin amma da yake na gaba yayi gaba, na baya sai labari ko duriyarsu basu gani ba. Maimakon dakaru nasu dawo da baya sai suka ci gaba da bin sawun dawakan su Najwas domin su riskesu. Wannan shi ne abin da ya faru ga su bawa Najwas bayan gimbiya Zarima ta riskesu a can birnin bayi yayin da tayi shiga irin ta mahaifinta Uhaisū Sarkin yaki. A can birnin Rum kuwa bayan sarki Mazahir ya hau kan karagar mulki an ci gaba da ha... Rokon Bikin Tayasih murna sai aka ga ko kadan babu walwala a fuskar sarki, kuma tunda aka fara bikin bai sha ko da ruwan sha ba. Ba komai ne ya haddasa hakan ba face bakin ciki na rashin ganin amaryar da zai aura wato 'yar bibiya Zarima. Gaba ɗaya hankalin sarki Mazahir ce ke akwai, babu abin da ƙazalika tashe cikin ransa face fasadace da dakarunsa waɗanda ya tura can wajen ganin arewacin bayi. Baya ga wannan kuma yana ta tunanin irin matakin da ya kamata ya ɗauka a kan sarkin yaki Uhaisu. Sarki Mazahir a zuciyarsa baya raba dayar biyun cewa tabbas da haɗin bakin Uhaisu a guduwar 'yarsa daga cikin gidansa. Wannan ne ya tabbatar masa da cewa sarkin yaki Uhaisu baya son ya aurar da Zarima gareshi. Idan kuwa haka ne to baya kaunarsa a matsayin sarki. Mazahir ya ce a ransa tabbas Uhaisu makiyina ne kuma tabbas ya gane cewa ni ne na kashe sarki, don haka a yanzu zai iya yin komai don ganin ya rushe mulkina. Tabbas Uhaisu matsala ce ga rayuwata. Abin da zai yi kawai shi ne, da zarar dakarun sun dawo ba tare da Zarima ba da Najwas kawai, zai sa a rataye Uhaisu a gaban jama'a a matsayin mai cin amana. Nayi masa sharrin cewa bincike ya nuna cewa da sa hannuna a mutuwar ubansa. Ko da sarki Mazahir ya zauna a zancen zucinsa sai wata zuciya ta ce da shi, ai kuwa idan ka zauna jiran sai dakarun sun dawo sannan zaka ɗauki mataki, kayi babban kuskure domin sarkin yaki Uhaisu mutum ne mai kaifin basira, a sanin tuggun. Babu mamaki ya shirya maka wani tuggu acan birnin bayi, don haka ya zama dole ka san halin da su bawa Najwas ke ciki a yau ɗin nan. Ko da Mazahir ya zauna a zancensa sai hankalinsa ya dugunzuma nan take ya mike tsaye ya bar fadar ya shiga cikin gida. Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan, gaba ɗayan fadawansa suka cika da mamaki. Dama tuntuni ana ta tsegumi da surutai akan yadda aka ga sarki ya turo an kama Uhaisu a wulaƙance, an je an kulleshi a cikin wani dakin duhu dake cikin gidan sarautar. Dama shi wannan daki a ka'ida duk mutumin da aka sa... A cikinsa ya yiwa sarki babban laifi ko ya ci amanar sarki, walau dai a kasheshi ko kuma a yanke masa hukuncin daurin rai da rai a kurkuku. Bayan sarki Mazahir ya shiga cikin turakarsa sai ya kama kuma ya kasa zaune ko tsaye yana ta tunanin abin da ya kamata yayi. Yana cikin wannan halin ne ya ji an bushe da dariya a cikin dakin. Da farko Mazahir ya firgita da jin wannan dariya domin bai ga mai yin ta ba, amma da ya shaida muryar mai dariyar sai murna ta kamashi domin abin nema ne ya samu. I, tabbas mai wannan dariya shi ne kadai mutumin da zai iya magance masa matsalar dake gabansa. Ba wani bane mai wannan dariya ba face boka Amkas Ibini Bauzul. Fiye da shekara goma sha biyar baya akwai kyakkyawar alaka tsakanin boka Bauzul da Mazahir, kuma sun taimaki juna a rayuwa. A takaice dai kowannensu ya ji dadin alafarsu. Boka Amkas ya biyawa Mazahir a da yawa, shi kuma ya ba shi duka iyaka mai yawan gaske. Suna cikin y... lokaci guda Mazahir ya dauke Rafa... boka Amkas ba tare da wani dalili ba sai kawai wani hali irin na dan adam na rashin hangen nesa, domin shi mutum sai yana da bukata sannan yake cigs (?), wanda zai biya masa ita. Mazahir ya shaida ny... Ta... ciki ya ce, "Ya ƙaɗal amintaccen boksi na Umarceka, ka fito fili mu gana domin kana da matukar mahimmanci ga rayuwata a yanzu." Ko da jin wannan batu sai boka Amkas ya bayyana tsulum kamar an jefa shi daga sama yana mai kyakkyatar dariya. Ko da baiyanarsa sai sarki Mazahir ya ruga gare shi suka rungume junansu. Bayan nan sai Mazahir ya janye jikinsa daga na boka Amkas suka fuskanci juna. Mazahir ya bude baki da nufin ya ce wani abu amma sai boka Amkas ya yi masa nuni da ya yi shiru, Mazahir ya tsuke bakinsa ba ce wa kalma ba. Boka Amkas ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Hakika ka so makara, domin saura kiris makiyanka su gama da kai — kuma hakan ta faru ne bisa sakacinka na yin watsi da ni. To amma ka sani cewa ni mai alkawari ne kuma ba zan taba mantawa da alherin da kayi mini ba a baya. Ka sani cewa duk halin da kake ciki..." Ina sane da shi kuma tabbas zan taimake ka, amma ka sani cewa sai mun zage damtse, mun yi da gaske kafin mu sami nasara akan makiyanka, domin sun kama wani babban abin dogaro wanda dukkanin matsafin duniya na shakkarsa. Ko da jin wannan batu sai Sarki Mazahir ya dubi Boka Amkas cikin tsananin mamaki, ya ce, "Yanzu har akwai wani abin dogaro wanda yafi tsafi da allolinmu da muke bautawa?" Amkas ya ce, "A'a, ba wai ina nufin yafi tsafi da allolinmu ba, amma dai shima abu ne mai karfin sihiri. Ba komai ba ne, ba kuwa face addinin nan da ake yiwa lakabi da Musulunci. Ina sanar da kai cewa a halin yanzu babban makiyinka, Bawa Najwas tare da wasu abokansa biyu bayi, sun karɓi addinin Musulunci." Sarki Mazahir ya ce, "Ban san haka ba. Shin kana ganin hakan zai zama matsala?" Amkas ya ce, "Ka ga zahiri nan, bari na nuna maka." Da hannunsa ya yi nuni zuwa ga bango, sai ga hoton abubuwan da suka faru tun daga Ukashat da su Bawa Najwas a birnin bayi, lokacin da Najwas da Ukashat suka fara yin musulinci, har zuwa lokacin da Najwas da su Kaumuz suka karɓi Musulunci. Ko da gama ganin wannan al'amari, sai Boka Amkas ya sake nuna bangon da hannu, sai ga hoton abin da ya faru tsakanin Sarkin yaki Ukashat da ‘yarsa Zarima, lokacin da ya shirya mata dabara, tayi shigar yaki irin tasa ta gudu daga cikin gidansu. Ko da ganin haka, sai Sarki Mazahir ya dimauce, ya dubi Boka Amkas a firgice, ya ce, "Maza ka nuna mini abin da ya faru ga Zarima bayan ta bar nan birnin Rum, da kuma halin da su Bawa Najwas ke ciki a yanzu." Ko da jin wannan batu, sai Boka Amkas ya tsandara ihu sannan ya ce, "Ai abin da ba zan iya ba kenan saboda wannan matsala ta karɓar addinin Musulunci ta Bawa Najwas. Yanzy haka babu mamaki ma, itama Zarima ta karɓi addinin. Abin da zai iya nuna maka kawai shi ne batun dakarunka seifends ka tura can birnin bayi domin kamo Zarima da Bawa Najwas." Sarki Mazahir ya ce, "Yauwa, maza ka nuna mini al'amarinsu." Boka ya saka murmushi, yace: "Ake..." Nuna bango da unsa sai ga hoton dakarun sarki: bisa dawakansu a guje tamkar za su ce suna tafe dafa da shiga cikin birni. Abu kuma suna ga cikin birnin Bayi. Haka dai suka wanzu suna ta gudu har suka iso Kofar birnin. Ko da isowarsu sai suka iske shugaban birnin Bayi tare da wasu dakarunsa a tsaitsaye a Kofar birnin sun yi zugum cikin yanayin bakin ciki tamkar za su fashe da kuka. Cikin sanyina jiki dakarun sarki Mazahir suka ja tunga a gaban shugaban birnin Bayi. Shugaban dakarun barde Salkuf ya sauko daga kan dokinsa ya zo gaban shugaba Kamhas ya risina cikin girmamawa ya kwashi gaisuwa sannan ya ce, “Ya kai shugaban wannan birni na Bayi, kayi sani cewa sarki Mazahir ya umarcemu da mu zo nan domin mu nemi gimbiya Zarima sannan ka bamu bawa Najwas mu tafi da shi.” Ko da jin wannan batu sai hankalin shugaba Kamhas ya dugunzuma ainun ya rasa abin da ke masa dadi a duniya sannan ya dubi Salkuf ya ce, “Ya kai wannan barde, kayi sani cewa Zarima ta zo a cikin shiga irin ta sarkin yaki Uhaisu, wato mahaifinta, kuma tayi magana da ni da irin muryar mahaifinta ta debi Bayi da kayan yaki sun tafi izuwa birnin Kisra don gudanar da wannan gasa ta yakin Bayi. Kayi sani cewa ban ankara cewa yaudarata tayi ba sai lokacin da suka fara fita daga cikin Kofar birnin nan. Ko da na yunkura da nufin na tsai dasu sai bawa Najwas ya zaburi dokinsa ya taka kafata. Kafin na dawo cikin haiyacina Zarima ta umarci bayin da duk dakarun rakiyar da na basu sun zaburi dawakansu da gudu. Nan da nan na tashi wata rundunar ta dakaruna suka bi bayansu. Bayan sa’a uku sai ga wannan runduna ta dawo suka shaida mini cewa sun nemi su bawa Najwas sama da ƙasa sun rasa. Ina cikin bakin cikin wannan bakin labari ne kuka zo yanzu don haka hankali na a tashe yake na rasa abin da zan yi don tsoron abin da zai biyo baya sakamakon fishin sarki. Yayin da shugaba Kamhas ya zo hana zancensa sai barde Salkuf ya kawo gwauron numfasbi ya ajiye sannan ya dubi Kamhas ya ce, “Hakika ni da kai muna cikin tashin hankali domin...” Mun bamu isa mu koma ga sarki Muzahir ba tare da cikakken labarin su jarumi Najwas ba. Walau dai mu bi bayansu izuwa birnin Kisra ko kuma mu tafi nemansu izuwa cikin kauyukan dake kan hanya kafin a isa birnin Kisran. Kumhas ya numfasa sannan ya ce, ai dole ne mu yi duk abu biyun wato dole ne mu je mu bincika cikin kauyukan sannan kuma mu wuce izuwa birnin Kisra amma babban abin da zai taimake mu shi ne mu yi ta bin sawun dawakansu. Ko da jin wannan shawara sai murna ta kama shugaba Kumhas nan take ya shirya sabbin dakaru ya jagorancesu suka hadu da su barde Salkuf suka bar birnin bayi don tafiya nema su bawa Najwas da gimbiya Zarima. Ko da gama ganin hoton wannan al'amari a jikin bangon turakar sarki Mazahir sai sarki Mazahir ya rusa ihu na bakin ciki cikin tsananin takaici bai san sa'adda ya cakumi boka Amkas da hannu biyu ya ce yanzu ya za a yi, nayi sauri a duk inda suke? Yayin da boka Amkas a cikin dale tambaya sai ya sunkuyi da kansa, ras cikin alamar karayar zuciya bai ce komai ba. Daga can kuma sai ya zura hanunsa a cikin aljihu ya fiddo wani dogon itace wanda shi kadai sauya launi yake, ya mifa wa sarki Abdul'aziz. Mazahir ya ce, kaga wannan itacen shi ne kadai zai iya nuna hanyar da za a bi a riski inda su jarumi Najwas suke, don haka yanzu sai ka zabo wani daga cikin gakwakuran baradunka ka ba shi wannan itace ya hanzarta ya je ya riski su barde Salkuf su tafi nema tare. Sarki Mazahir ya dubi boka Amkas cikin matuƙar damuwa ya ce, ka sani cewa tuni su Salkuf sun yi nisa ta yaya barden da zan tura zai iya zuwa ya riske su a cikin ƙankanin lokaci? Ko da jin wannan batu sai boka Amkas ya bushe da dariya ya ce, kar ka damu akwai taimakon da zai yi akan haka. Abin da nake so da kai kawai yanzu ka tura a kirawo barden da zamu bai wa wannan aiki. Kafin boka Amkas ya ƙara fadin wani abu tuni sarki Mazahir ya ƙwalla wa waƙti bawa kira. Aguje bawan ya shigo cikin turakar ya zube kasa a gaban sarki. Mazahir ya dubeshi a fusace ya... Ce maza, ka ruga zuwa gidan Sadauki Kumazu ka shaida masa cewa ya yi sauri ya kimtsa ya zo nan turakar yanzu yanzu. Kafin Mazahir ya gama rufe bakinsa, tuni bawan ya mike ya ruga waje har yana tuntuɓe kamar zai faɗi. Bayan tafiyar bawan ne boka Amkas ya runtse idanunsa, kawai sai ya fara kiran sunan wani aljani waishin Hukumul Ansabu. Bayan shudewar dakika sittin sai kawai suka ga rufin turakar ya tsaye, wata irin walkiya da tsawa mai ban tsoro ta faɗo ƙasa. Duk a taurin zuciya irin ta sarki Mazahir sai da ya ja baya kaɗan cikin alamun tsoro. Wannan walkiya na dira a ƙasa sai ta rikide ta zama wani jibgegen aljani mai siffar Alhudahuda. Bambancinsu da Alhudahuda shi ne yana da fuska irin ta batoyi kuma fukafukansa manya manya ne kamar allon jirgin ruwa. Ko da bayyana aljanin sai ya risina a gaban boka Amkas

Chapter 1 of 3