Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
banza ya nufi d'akin Ammi....wlh An cuci yaya kamarsa kyakykyawan gaske me Aji da kud'i da mata ke rubi binsa za'a had'ashi da y'ar k'auye"cewar moon"wayace miki y'ar k'auye ce? charanchi ai LG ce"kuma yarinyar tayi karatu"kuma Ahaka yana son kayarsa"cewar zarah"wai dama shike sonta?"Eh mana"to Anty suhan fa?"oho musu....murya can ciki yayi sallama ya shigo cikin d'akin"mama na tsaye gaban mirror tana shiri zata tafi Asibiti"ta juyo taga yadda ya wani had'e rai tayi d'an murmushi tana fad'in kai babanah haka zakajema y'ar tawa kana wannan d'aure fuskan?"kaida yakamata kaje da fara'a"to nidai kace Ina gaisheta ,sannan ka kula ku gaisa cikin mutunci kana jina?"da k'yar yace uhmm"sbd yafahimci har yanzun mama bata fahimci yadda yatsani Auren bane"kuma itama yarinyar saita gane kuranta.... ringing d'in wayarsa ya katse masa tunani "yana dubawa yaga mohd ne"yaja k'aramin tsaki yana yanke kiran"mama ta kallesa taga shida waya ne"beyi mgn ba yafita"Allah yasa yarinyar nan me wayoce da hikima ta haka kawai zata canza mana kai sadeeq....yana fitowa bakin get ya lura da motar mohd"hakan yasaka yakoma had'e rai"mohd dake can baya tsaye yana waya da sarah yana sanar mata labarin Auren ya kallesa yayi murmushi yana yanke wayar "saidai kawai sadeeq dake k'ok'arin shiga mota yaji muryar mohd yana fad'in Abokinah idan bazaka nemeniba ni gashi nazo nemanka"komai yayi zafi maganinsa Allah yin dogon fushi ko gaba banaka bane"sadeeq beyi mgn ba yashiga cikin motar ya zauna "shima mohd saiya zagayo ya shigo ya zauna gefensa yana fad'in yanzun tafiyar ce shine kafi k'arfin kasanar mun?"wai meka d'auki kankane Lamid'o?"look mlm ! idan zakaje muje idan baraka kajeba kawai kabarni"ita kuma wlh saita sani"kamarya saita sani?"wlh kaji tsoron Allah karka cutar da y'ar mutane"banza sadeeq yamasa"driver yashigo yajasu....motar ta d'auki shiru sbd ba fira suke ba"saidai mohd ne ke waya da sarah"sai sadeeq daya mak'ala earpiece a kunnansa sbd beson jin surutun mohd"koda yagama wayar saiya fara tsokanarsa wai karyaje ya kama y'ar mutane yabari sai Ankawota"tamkar sadeeq yarufesa da duka haka yaji"saiya masa banza kawai" ...tafiyar Awa biyu sukayi suka iso charanchi" saidai ganin masallacin juma'a a hanya yasaka suka tsaya sukayi sallar juma'a.....tun bayan mlm yasanarwa yasmeen zuwan yau sadeeq zaizo"ta fara gyara soron,bayan ta share ta goge sumintin ta kunnah turaren wuta ta shimfid'a darduma sabuwa ta mlm"ruwan roba da lemo ta tanada sai snacks da sukaje wani shago bakin titi suka siyo itada lami"sannan suka soya musu kaza"basuyima gigin dafa musu Abinci ba sbd ran yasmeen yabata su y'an gayune bazasuci Abincin suba"saidai sun dama musu fura dataji kayan Hadi"lami nata tsokanarta wai idan mijin mummunane yaya zatayi?"itadai saidai tayi murmushi kawai"cikin fargaba tayi wanka ta shirya cikin k'uru adakarta"sabuwar Atamfar sallarta datake matuk'ar jida ita light green da ratsin black"batayi make up ba "saidai tayi masifar kyau "lami na zaune tanata kallonta"tana yaba kwawunta Aranta"yasmeen ta d'akko hijab gogaggiya ta fesa mata turare ta Ajiye "kina nufin hijab zaki saka?"Eh mana "dakin b'ata kwalliyarki wlh"sannan ki shafa lips stick hjy sbd nasan idan kikayi make up tamkar ba indiya kike komawa"nifa lami ki k'yaleni bazanyiba"bana buk'atar yasoni sbd kyawuna dan kyau yana gushewa"ta hanyoyi guda ukku na (1) tsufa" na (2) rashin lafiya)na (3)talauci.....wannan gaskiya ne"bara nide nayi sallah tunda ke kinyi"dato ta Amsa"Adaidai lokacin da yasmeen taji horn d'in mota"gabanta yadinga wani irin mugun fad'uwa"mlm da dawowarsa kenan daga sallar juma'a "yana sanye da kayan mutunci ya fita k'ofar gidan..... sadeeq da mohd na tsaye gefen motar"mohd nata Aikin rarrashinsa kan yayi Abinda yadace kar yayi Abinda zai zubda mutuncin iyayensa "kasancewar dama yasan fuskar mlm dukda yajima began saba Amma yana hangosa yaganesa"Assalamu Alaikum! wslm baba sannu da fitowa"cewar mohd"sadeeq yak'ak'aro murmushi suka duk'a suka gaishesa"ya Amsa fuska Asake yana fad'in ku shiga ciki "yak'are maganar yana yin gaba"gaba d'aya suka bi gidan da kallon tausayi "suna shigowa k'amshin turaren wutan yadaki hancinsu"sadeeq yatab'e baki yana zare takalminsa suka zauna "Masha Allah! kasamu irin wacce kakeso wato me tsabta"banza sadeeq yamasa yacigaba da danna waya "baba yafito yasanar musu tana zuwa kafin yafita"sadeeq yaja tsaki yana kallon muhd yace"duba time kagani "wani aji ne da ita dazata shanyamu"koda cikakkiyar mace ce ita ta Isa tajamun aji balle ita k'aramar yarinya?"d'aure fuska mohd yayi bece komai ba sbd hango wata yarinya dayayi rik'e da tray"Ahankali lami ta musu sallama mohd ya Amsa ta Ajiye tray d'in tana murmushi ta gaidasu"kallo bata ishi sadeeq ba jikinsa yaba shi ba itace bace yasmeen"sannunku da zuwa ya hanya?"Alhamdulillah"Masha Allah ga k'awar tawa nan tafe"Ina Angon namu ne?"tafad'a tana satar kallon mohd ta d'auka ko shine sbd lura datayi yafi sakin fuska"da hannu mohd ya zunguri sadeeq"yana fad'in gashi nan ni Abokinsa ne kamar yadda kike k'awar Amaryar tamu"kallonsa kawai lami keyi cikin mamaki had'e da rud'ewa " dukda taji haushin sharetan dayayi saita kauda kai ta mik'e tsaye ta wuce ciki tana tunanin gaskiya wannan me girman kan yafi k'arfin yasmeen.....ka kyauta kenan Lamid'o?"wace irin zuciya ce dakai?"shikenan kaga zatace bakada kirki ko?idan ta shiga zata fara sanar mata halinka na k'yaliya.....saime dan wata banza tace banida kirki ne? shikenan kayi duk yadda kakeso wata rana sai labari.....da sauri lami ta shiga d'akin tana fad'in yasmeen kingan shi kuwa?"kinada matsala lami?"Ina ruwana da muninsa?"ta k'are maganar fuska bbu walwala tana gyara hijab d'inta"bafa haka nake nufiba "ke nifa tunda nake ban tab'a ganin mutum d'an gayu Ido da Ido me tsananin kyau kamarsa ba"ga wani irin mugun k'amshi sunayi shida Abokin nasa"har yanzun ban dena jin k'amshin suba"kuma shima Abokin nasa wlh ya had'u"dan Allah ya Isa haka muje mana"Ina ?"can wajensu ko?"ah ah wlh kije kedai wajen mijinki"k'ilan ya rungumeki"tsaki yasmeen taja tana saka plate shoes nata ta fito tsakar gidan"wani iri takeji Ajikinta"tana jin kamar karta fita"tsoro,fargaba , fad'uwar gaba duk sun mamaye mata zuciya"da k'yar ta daure jikinta na kirma ta nufi soron d'auke da sallama cikin y'ar siririyar muryarta me tsananin dad'in sauti......✍️ wannan book d'in na kudine regular grp 300 vip grp 1000 special group 2k wato 3pages in a day zaku biya kud'in ku ta wannan acc numberπŸ‘‰2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251 300 kawai ake turo kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne banason transfer d'in kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kira ? y'an nijar ku tuntub'i wannan number πŸ‘‰ +227 88 01 90 50 normal grp 500f vip grp 1000f special grp 2000f dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biya ba 2/26/24, 14:08 - Ummu: 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 ❀‍ ? NIDA BARRISTER SADEEQ ❀‍ ? 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story &written by mommyn fareesa free page 7&8 ........tun daga nesa Yasmeen ta hango mohd daya gyara zamansa yana kwasar dad'i yana lumshe Ido"yayinda uban gayyar ke zaune yana kallonsa yana yatsina fuska"can yaja gajeran tsaki ak'ule yana fad'in wai mlm meye haka?sai kace wani bak'on cin wannan Abin?"karma yarinya tasameka kana irin haka tace zata rainani na tattakata wlh...kaga idan zakaci muci kawai ,idan baraka ciba kabarni naci na kuma kaima driver sauran....shiru sadeeq Lamid'o yayi sbd jin sautin siririyar muryar yasmeen data musu sallama "be Amsa sallamar tataba"saidai rai daya koma had'ewa yana jin zuciyarsa na wani irin bugawa"yana kuma mamakin meyasa yaji hakan??.....saima ya d'auke kansa cikin basarwa...wa'alaikissalam ran Amaryar mu yadad'e"irin wannan jan Aji haka ?"duk Abokinah ya k'osa ya ganki"yak'are maganar yana murmushi had'e da satar kallon sadeeq yaga ya murtuke fuska kamar zai had'iyi zuciya"itadai yasmeen d'an tak'aitaccen murmushi ta saki tana d'an zama gefen tabarmar zuciyarta na wani irin harbawa da sauri da sauri"yayinda hancinta ke shak'o mata ni'imtaccen k'amshin turarukan su..masha Allah! masha Allah!! shine Abinda mohd yafad'a Azuciyarsa sbd ganin baiwar nutsuwa,kyau , tarbiya da sanyin hali Atattare da yasmeen "yatabbar da cewa tafi suhan komai"Abinda kawai suhan tafita dashi shine" wayewa da ilimin boko me zurfi...sannunku da zuwa"ta fad'a da k'yar cikin fargaba"sbd gaba d'aya wanda ta fahimci shine mijin nata taji yacika wajen" yauwa Amarya ya gida?"Alhamdulillah" Ina yininku?"lafiya qlau mohd ya Amsa da fara'a saman fuskarsa"yana d'aukar kwanon furan ya sha ya Ajiye"yasmeen kanta na'a k'asa "uban gayyar kuwa danna waya kawai yakeyi kamar besan da zamanta a soron ba"sbd ko gaisuwar data musu mohd ne kawai ya Amsa "yasha Alwashin muddin bazata gaishesaba su kwana Anan bazai tanka taba.... yasmeen! baby nah sarah tana gaidaki"Ina Amsawa sosai"to Alhamdulillah "sunana mohd b salis" nine babban Amini kuma d'an uwa ga mijinki sadeeq "Ina fatan kinyi murna da zuwan mu"sannan zakiyi Alfahari da Abokinah daya kasance Amatsayin miji Agareki"d'an murmushi kawai tayi tama kasa d'ago kanta balle tayi masa mgn"ya d'an girgiza kansa, sbd ya lura tanada kunya sosai" masha Allah! bara naje daga waje na kaima driver Abincin nan "muna godiya k'warai da gaske"irin wannan kayan dad'i haka....wani irin kallo irin na zamu had'u dakai sadeeq Lamid'o yajefesa dashi"shi kuwa nunawa yayi bema san yana yiba"saiya mik'e tsaye yana kallon sa yace"Abokinah bara na baku waje tunda baka son yimata mgn Agabana"yana fad'in hakan yafita......soron ya d'auki shiru,ita kanta a sunkuye, k'irjinta nata bugawa sbd tsoro da fargaba"shi kuma yana danna waya"kallo bata isheshiba"har yanzun kuma be kalli fuskartaba" jin shirun yayi yawa yasaka ta dago Ahankali ta d'an kalli gefen dayake zaune da idanuwanta ta bud'e baki cikin muryarta me taushi da nutsuwa tace"Ina wuni?"yatsina fuska yayi yak'i yin mgn "Ina wuni?"ta koma furtawa Akaro na biyu "gajeran tsaki yaja"gabanta ya fad'i tabishi da kallo "sai Akayi sa'a shima ya d'ago kansa"sai suka had'a Ido "k'irjinsa yabuga!ita kuma gabanta yafad'i "tayi hanzarin kawar da kanta gefe fuskarta babu walwala"saidai itama tayi mamakin kyawunsa da had'uwarsa "Uwa Uba kuma daddad'an k'amshin turarensa daya tsaya mata Azuciya....saidai taji shakkun irin mugun kallon daya watso mata" sadeeq kuwa kallon second 3 yamata ta d'auke kanta ya tab'e baki yana sauke numfashi cikin cool voice d'insa yace"bana buk'atar gaisuwar taki"meyasa tun farko dakika shigo baki gaisheniba?dukda koda kin gaisheni d'in bazaki burgeni ba"hakama Ake gaida mutane babu ladabi ko?...."sbd kina tak'ama kega Amarya ko?"uhmm! sannu kinjiko?"me kake nufi?"bansani ba "daga yau na koma mgn kina tambayata zaki gane kuranki"stupid kawai"innalillahi wa inna ilaihir raju'un! wane irin mutum ne wannan ni yasmeen?"ta tambayi kanta"saidai zuciyarta ta dau zafi"dukda tasan ba kyau miji na fad'a kana fad'a saita girgiza kanta tace" banyi zaton hakan daga garekaba"Akwai hadisin monzon Allah S W A daya ke cewa" wanda yabada gaskiya da Allah da ranar lahira ya fad'i Alkhairi ko yayi shiru"inaso ka sani umarnin mahaifina nabi shiyasa harka kasance miji Agareni"bayan haka dabaka ganniba balle harka wulak'antani....ta Ida maganar kuka na sub'uce mata"sadeeq yaja tsaki yana kuma dana sanin Abinda yayi sbd gudun kar babanta ya shigo yagani kota sanar masa"Amma dayake d'an renin wayone"sai yaja tsaki yana fad'in wlh ko kimun shiru kona fashe miki bakin dakike ma mutane kuka"kin Isa kimun rashin kunya ne?"yafad'a cikin tsawa yana matsowa gefenta"da sauri ta matsa tana fad'in dan Allah kayi hak'uri wlh nadena"ya tab'e baki ya zauna yana jin kamar ya rufeta da duka"yana kallon hijab d'in jikinta yakoma Jan tsaki Aransa yace"sai kace wani abu gareta da zata b'oye"kina jina?"uhmm"kika sake kika sanarwa wani Abinda yafaru wlh sai kin sani"batun fita bance kije gidan uban kowaba sai idan nine nace kije"gayan mgn kuma bazance ki denaba zakizo har inda nake"in bacin haukanki Anfada miki na dace dake ne?"ki rubuta ki Ajiye bazan tab'a sonkiba"kuma inada muradin raina da kikayi sanadin k'in shigowarta hannuna "Amma very soon zata shigo tanan zaki gane matsayinki name Aikinta yasaka kikayi gigin Aure mata miji"yana fad'in hakan yaja tsaki yamik'e tsaye"uhmm Allah yaka mata kaji tsoro ba mutum ba" batun fita kuma idan yazama.....shiru tayi sbd tunkarotan da yayi ta rintse Ido jikinta na b'ari"yaja tsaki Adaidai lokacin da mohd ya shigo cikin soron....da kallo yabisu one by one"saidai yadda yaga yasmeen tayi k'asa da kanta shi kuma yanata cin magani yatabbar bakak'en maganganu masu zafi ya gaya mata"beko kallesa ba yace"yasmeen zamuje muyi sallar la'asar sai mudawo muyi sallama ko Akwai Abinda kike buk'ata ne??"k'ok'arin b'oye yanayinta tayi batare data d'ago kanta ba tace"bana buk'atar komai"shiru yayi domin yadda yaji muryarta ya tabbatar da kuka sadeeq yasakata"saiya daure yace"kinada waya ne?"ah ah"okay bara muje ga kayan nan ki mayar mun gode"daga haka ya Ajiye kayan beko kalli gefen da sadeeq yakeba yafita yana tunanin wace irin zuciya ce da sadeeq?"wani irin tausayin yasmeen yaji"yaso Ace tanada zafi kodan sbd halin sadeeq Lamid'o saidai yalura tanada sanyin hali"yana tsaye gefen motar sadeeq ya iso yanata Harare Harare be tankasaba suka wuce masjeed Ak'afa "suna fitowa mohd bebi takan saba yanufi bakin titi"kai tsaye wani shago da ake siyar da wayoyi sabbi da second hand da sim card yatsaya"waya me kyau sabuwa k'irar spark 10 yasiyama yasmeen da sabon layi"bayan ya sallamesu yanufo gidan"sadeeq na zaune saman mota yana waya da wani mutum"kallo be isheshiba ya wuce soron.... yasmeen kuwa mohd na fita sadeeq yaja tsaki shima yanufota yana fad'in maimaita mun Abinda kika fad'a?"wai meyasa dukda masifa yakemun Amma muryansa da dad'i ne?"ta fad'a Azuciyarta....da sauri ta d'ago kanta jikinta na kirma sbd ganinsa dab da ita yana binta da wani irin kallo yana huci"da sauri tafara k'ok'arin ja da baya"yayi hanzarin take mata k'afa guda"tasaki k'aramin kuka tana yarfe hannunta guda sbd Azabar zafin dataji....zaki koma mgn Ina mgn?"yafad'a cikin isah yana hura hanci"kasa mgn tayi sai kanta datake girgizawa da sauri"yaja tsaki ya janye k'afarsa ya fita"kwashe kayan tayi ta koma cikin gidan da k'yar tana d'angyasa k'afar"tana ganin lami ta fashe da kuka tana fad'in lami bazan iyaba gaskiya! idan baba yadawo zan sanar masa "zan iya jure komai Amma banda wulak'anci lami"kinga yadda yatasani Agaba yana mun masifa?kamar zai dokeni"wlh ni tsoronsa ma nakeji"kinga wanke fuskarki muje d'aki muyi mgn kar baba ya shigo"batayi mgn ba ta wuce wajen da suke Ajiye ruwa ta wanke fuskarta suka shiga d'akin yasmeen d'in "lami na binta da kallon tausayi tace"ba farar d'aya ba Ake samun nassara Arayuwa ba k'awata, dole sai Anyi hak'uri da ganin jinkiri"ni kaina kallo d'aya na masa na fahimci zaiyi girman kai"saidai wannan Aganina bata kai matsalar da zaki gayawa baba sbd kinsan yanada hawan jini"kuma mutuncin mahaifinsa zaki duba"koda rabuwa zakuyi yasmeen inhar zaku rabu bayan kin kammala karatun dakike da buri da sauk'i"balle bana miki fatan rabuwa da mutum kamar wannan"lami kenan! duk kyau,ko dukiya ko mulki idan babu hali basuda Amfani "dana zauna da wanda zai wulak'antani me tarin dukiya, gara na zauna da wanda koda zaiyi garuwane yabani in har zai mutuntani"tabbas inada burin cigaba da karatu Aduniya"inhar zai zamemun Alkhairi kamar yadda nake yawan Addua"naji dad'in shawarki lami"sai yanzun na tuno da Alkhairin mahaifinsa"banaso nayi Aure da wata manufa Araina nafiso nayishi da zuciya guda"zan dage da Addu'a kamar yadda baba kemun"yauwa hakan shine daidai"kinga kuma dama kince Agidansu zaku zauna bana zaton zai iya cutar dake"kedai ki d'auki shawarwarin da ummanah ta baki"kuma in sha Allah nima bazan sanarwa da kowa komai ba..... yasmeen na k'ok'arin mgn sukaji knocking"ko waye kuma?"inaga sune sbd dama masallaci Abokinsa yace zasuje"to kije mana"gaskiya wannan Abokin nasa yanada kirki sosai"hakane lami bara naje"daga haka ta fita ta nufi soron"mohd na tsaye ya Amsa sallamar data masa cikin tausayawa"ya kalli idanuwanta ya kauda kai ransa na bashi taci kuka"ledar hannunsa yamik'a mata yana fad'in gashi wayace yasmeen kisaka chargy"sannan Akwai takarda na rubuta number d'ina da sunana saita sarah idan kin bud'e wayar kin kirani"dan Allah kayi hak'uri kabarshi yaya mohd"ah ah yasmeen ki Amsa mana indai da gaske ni yayankine"kuma sadeeq ne yasiya miki ba nib....da sauri ta girgiza kanta tace"bana son duk Abinda zai fito daga hannunsa"kiyi hakuri dan Allah yasmeen ga wanda be fahimci halayen Lamid'o ba zai masa fassara daban daban"tabbas nine na siya "kuma tanada Amfani gareki wayar damu gaba d'aya"shawarata dake shine kiyi hak'uri dan Allah komai zai wuce wata ran"banaso kisanarwa da baba komai sai Alkhairi"kuma sannu a hankali sadeeq zai dena miki hakan"kanta Ak'asa ta Amsa tana masa godiya"yayi murmushi yace"karki damu fatana shine ki shigo cikin gidan Abokinah da zuciya guda da niyar zaman Aure kikazo yi"zaman Aure kuma kinsan ibadane"karki damu da wasu kalamansa babu Abinda zai miki"batace komai ba tayi dai shiru"yauwa batun kud'in hidimar da zakuyi keda friends naki dubu d'ari nawa kuke bukatane ??"da mamaki tace"dubu d'ari nawa?"Eh ko sun kai million ne?"tayi d'an murmushi tana fad'in ah ah bama buk'atar ko sisi sbd babu Abinda zamuyi da kud'in"hakanma mungode Allah yatsare hanya"da matuk'ar mamaki mohd ya Amsa da Ameen yamata godiya yana fita"lallai tun kafin tafiyar tayi nisa yatabbar da yasmeen mace ce ta gari me gudun duniya da Abinda ke cikinta"Atake yatuna lokacin da suhan tayi bath day Millon 5 tacema sadeeq yabata zasuyi party itada k'awayenta"in bacin yamasa mgn yabata million 2"hakan ba daidai bane tun kafin ya Aureta zai shagwab'a ta da kashe mak'udan manyan kud'ad'e irin haka" da bemasa mgn ba million 5 d'in zai bata.... sadeeq na ganinsa yatab'e baki yana drowa daga saman motar yace"na d'auka k'ilan kwana zakayi a soron?"idanma k'ayata ta kamaka to meye zaka mun??"baka canka daidai ba"yasmeen bata cikin irin wa'annan matan"wanda Ayanzun ba lallai ka ganeba hakan ba"k'ilan saika had'a wuta da ruwa sannan zaka gane.....sosai sadeeq ke k:ok'arin fassara kalaman mohd Aransa saidai yakasa"saiya tab'e baki yana d'age kafad'a irin ko Ajikinsa d'in nan ya bud'e motar ya shiga"tunda suka shiga motar har suka iso gida Anata sallar magrib mohd be tanka saba"sbd haushinsa yakeji"driver na gama parking yafito yanufi wajen motarsa ya bud'e yashiga"sadeeq yaja tsaki yace"kayi ka gama indai sbd wannan k'azamar yarinyar ne"yana fad'in hakan ya nufi side nasa ta k'ofar baya"Agaggauce yayi wanka da sallar magrib yanufi masjeed yayi isha'i"yana idarwa yanufo cikin gidan sbd wata iriyar yunwa ke damunsa rabonsa da Abinci tun break fast d'in safe"tun kafin ya iso cikin parlourn yaji surutun y'an gidan nasu"ya yatsina fuska ya shigo fuska Ad'aure"tuni su moon suka nutsu suna gaishesa be Amsaba ya kalli Anty dake zaune tanata wani shan k'amshi su salma da hafsat na gefenta zaune" sadeeq sai yanzun kadawo ne daga wajenta?"cewar salma uhmm"Anty sannunku da gida"yafad'a kamar Ammasa dole"kaine keda sannu kaida kaje k'auye "wai sadeeq dan Allah me ka gani jikin y'ar k'auye ne?"cewar hafsat tana jan tsaki"mama dake kitchen ta fito tana fad'in Abinda namiji ke gani jikin mace shine yagani"shashashar banza "maza ku tashi ku koma gidajen mazajenku"yanzun dan Allah sbd tayi mgn mama kike korarmu?"muna ji muna gani ba'a yi shawara damuba d'an uwanmu zai kwaso mana gayyar tsiya"ga suhan daya dace da ita"yarinya me aji y'ar babban gida"saiya kwaso mana y'ar mlm taje ta mallakesa"sadeeq dai tab'e baki yayi ya wuce dining area"mama kuwa kallonsu tayi batayi mgn ba ta wuce d'aki "hakan yasaka suka biyota Anty ta raka bayansu da harara"tare dashan Alwashin saita sanarwa mahaifiyar suhan sbd k'awarta ce.... Ashe bakuda mutunci salma?"gaban kishiyata kuke wannan rashin wayon?"wato ku Abin duniya shine gabanku ba mutunciba"to yana sonta Ahaka "ku fita daga idona na rufe tunda wuri ko kuwa wlh ranku yab'aci"karku sake ku yadda Alh yaji kuna irin wannan maganar banzan"maza ku tashi ku tafi gidajenku"kowace tayi k'asa da kai tana bama uwar hak'uri"saidai a zuciyarsu basusan Auren..... kwana 2 da faruwar hakan mohd yayi bala'in daukema sadeeq kai"ga Bilal lamis daya kama ya rufe ya gudu"wanda Ana zaton daga cikin ma'aikatan wasu suka bashi hanyar guduwa yabiyasi kud'i"Abin tashin hankali ya gudu washe gari yayima k'aramar yarinya fyad'e"yanzun haka sadeeq yaje wajen iyayen yarinyar dake gadon Asibiti ya musu tambayoyi da ita kanta yarinyar sannan yabasu umarnin suyi k'ara shine zai shige musu gaba"yakuma sha Alwashin sai yayi sanadin dayakai bilal mak'argama....Ayau friday Lamid'o na zaune a office nashi suna mgn da wasu maza guda biyu"yasha gayunsa cikin k'ananun kayan da sukayi matuk'ar haska choco skin nashi"gaba d'aya beda walwala sbd wannan Aure "daurewa kawai yakeyi...suhan ta turo k'ofar A haukace ta shigo babu ko sallama"idanuwanta sunyi jajir Alamar taci uban kuka ta k'oshi"ga wuk'a sabuwa dal Ahannunta.....k'irjin sadeeq yabuga! yabita da kallo Atake ransa yabashi taji labarin wannan kaddararran Auren"wanda kullum da b'acin ran Auren yake tashi ya kuma tashi dashi.....baby ni zaka ciwa Amana?inane gidansu y'ar iskar yarinyar koni ko ita wlh saidai kowa yarasa"ta kare maganar tana kurma wani uban ihu tana nuna masa wuk'ar"gaba d'aya mutanan dake zaune suka bita da kallo kamar TV.....✍️ wannan book d'in na kudine regular grp 300 vip grp 1000 special group 2k wato 3pages in a day zaku biya kud'in ku ta wannan acc numberπŸ‘‰2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251 300 kawai ake turo kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne banason transfer d'in kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kira ? y'an nijar ku tuntub'i wannan number πŸ‘‰ +227 88 01 90 50 normal grp 500f vip grp 1000f special grp 2000f dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biya ba 2/26/24, 14:08 - Ummu: 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 ❀‍ ? NIDA BARRISTER SADEEQ ❀‍ ? 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story &written by mommyn fareesa Last free page9&10 πŸ™Œ ......wata rikitacciyar tsawa sadeeq Lamid'o yadaka mata yana zaro mata fararen idanuwansa da sukayi jajir lokaci guda ya nunata da yatsa yace"Are you mad?"Eh" indai Akanka ne na yarda banida hankali sadeeq "ya kakeso nayi da raina ne?"ka fad'amun da saka hannunka aka kullah wannan shegen Auren ko kuwa? ta k'are maganar tana sakin wani irin malalacin kuka...shout up suhan! ya katseta cikin zafin rai yana mik'ewa tsaye murya babu Alamar wasa yace"get out of my office now! yak'are maganar yana nuna mata k'ofar fita"yayinda yakejin kunyar mutanan dake zaune suna kallonsu.....ni kake kora sadeeq?"doguwar tsuka yaja ya matso ya fisgi hannunta suka fito waje"tun kafin tayi mgn taji saukar lafiyayyan mari"ta dafe kuncinta tana binsa da kallo with a very chock tana girgiza kanta hawaye na tsiyaya saman fuskarta"yaja tsaki yana huci ya kauda kansa"uffan batace ba saidai kawai tayi k'ok'arin barin wajen....sai kuma yaga kamar be mata Adalciba"da sauri ya rik'e hannunta guda yana fad'in suhan meyasa kin kasa fahimtar halayena ne?"batayi mgn ba sai juyowa datayi ta rungumesa tana rushewa da sabon kuka"Ina sonka sadeeq! bazan gaji da sanar maka da hakan ba"kaima kasan dole nadamu da wannan rikitaccen tashin hankalin danaji tunda aka sanar da mugun labarin An Aura maka wata banza"pls kasanar mun kana sonta ko kuwa??....saida ya janyeta daga jikinsa batare daya kalletaba yace"banida wannan Amsar"and last one karki koma zuwamin office da irin wa'annan maganganun"sanin kankine bazan k'i bin umarnin iyayena ba sbd ke"idan kinyi hak'uri bayan na Aureki zan saketa"ta rintse Ido tana sauke Ajiyar zuciya cikin muryarta data shak'e wacce ke nuna Alamar taci kuka ta gaji tace"pls baby kamun Alk'awari bazakayi sex da itaba..... mitsssssuww ! yaja doguwar tsuka had'e da binta da kallon bakida hankali" yana yatsina fuska yajuya yakoma ciki batare daya k'ara cewa komai ba"sbd Aganinsa ta gama dashi datayi zaton zai iya had'a shimfid'a da yasmeen....suhan ta sauke Ajiyar zuciya tana juyowa suka had'a Ido da mohd daya iso wajen yaga komai Akan idonsa dg nesa, saidai bejin me suke fad'a"yana sanye da kakinsa na y'an sanda"ba k'aramin kyau suka masa ba"kallon ukku saura kwata suhan ta jefesa dashi taja tsaki ta wuce sbd ranta yabata dashi aka had'a baki aka kullah wannan shegen Auren"danta jima da fahimtar mohd baya san Alak'arta da Lamid'o"mohd kuwa yaji zafin Abinda ta masa"ya k'yaleta ne kawai sbd sadeeq Lamid'o"bayan haka da wlh saiya rufeta yaji dalilin da zata masa kallon banza harda tsaki"Afusace ya nufi cikin office d'in"yana k'ok'arin shiga b'akin dake ciki suka fito.... sadeeq kuwa cikin bad mood yashigo office d'in yana jin tsananin k'in yasmeen Azuciyarsa sbd itace sanadin komai "fuskarsa babu walwala ya zauna kan kujerah tana juyawa dashi"kusan second 5 kafin da k'yar ya iya cewa"pls zaku iya tafiya Anjima zan nemeku"daga haka ya

Chapter 3 of 6