Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
yasmeen yana washe baki yashigo"tana zaune tanata kuka"wai har yanzun baki dena wannan kukan ba Amarya ta?"ta yaye mayafin ta kallesa hawaye na zuba tace"kayiwa Allah ka sallameni bana sonka na tsaneka! zan iya kasheka"ya d'aure fuska yana Ajiye ledar hannunsa yana fad'in koda zan rabu dake dole na mori sadakina"yana fad'in hakan yanufeta"da sauri ta sauka daga saman bed d'in"yakama dariya yana koma nufarta"ta d'auki kwano nashan ruwa sabo dake saman mirror ta kwad'a masa iya k'arfinta a tsakkiyar kai"yafasa k'ara zai rik'eta ta turashi tana sakin ihu ta fito daga cikin d'akin Aguje ya biyota"matansa da yaransa suka fito tsakar gidan"lami ta dinga dariya tana fad'in bakaji kunyaba yanzun dan Allah?afusace yanufeta yafara jibgarta"tasaki ihu tana fad'uwa k'asa "saidai ganin bata motsi dayake Akwai nefa yasaka yatsaya da dukan nata,yana kallonta shida uwar gidan da sauran yara"yayinda yasmeen na daga tsaye gefen k'ofar fita daga cikin gidan.... innalillahi wa inna ilaihir raju'un ta mutu wlh! cewar uwar gidan tana girgiza ta"babban d'an Laure yafita yana kururuwa babansa yakashe mamansa"yasmeen najin hakan ta fita daga cikin gidan ta nufi gidansu k'awarta lami "hankalin rabe yatashi matuk'a da wannan Aika Aika da yayi" Adaren ranar aka kamashi"washe gari Aka mik'a Laure makwancinta"iyayen lami suka b'oye yasmeen babu wanda yasan inda take"hankalin bala yayi bala'in tashi"kwana 3 da faruwar haka rabe ya Aiko da takardar sakin yasmeen da cewar bala yabiyashi kud'insa daya kashe yabama iyalansa"sbd shi Anyanke masa hukuncin shekara 20 Agidan yari tare da horo me tsanani sbd yayi kisan kai bisa rashin sani"kasancewar babban d'ansa bejin mgn yatarama bala mutane k'ofar gidan sunata Aikato masa da jifa da zage zage "ana cikin wannan yanayin mlm da matarsa suka dawo garin"hankalinsu yatashi da suka sami labarin Abinda yafaru"mlm yaje yayima bala tas,da sanar masa duk inda y'arsa take yaje nemota nanda kwana 2 ko yayi k'ararsa"iyayen lami najin labarin dawowar mlm sukazo suka damk'a masa y'ar sa"sati ukku da faruwar hakan jummai ta rasu"mlm yakamu da hawan jini"ga halin rashi da suke cikinsa"wani daga cikin d'alibansa yamasa hanya yasmeen tafara koyarwa wata a islamiya dake Anguwar" duk wata Ana biyanta dubu goma"dasune suke samun rufin Asiri"mlm kuma yak'iyin Aure sbd beson Amatsama yasmeen"kullum da dare gidansu jummai take zuwa ta kwana"da safe saita dawo gida....tun bayan hakan yafaru manema har daga birni sunata zuwa Amma yasmeen sai tasaka kuka ita batason su"hakan yasa mlm yazuba mata Ido"da wuya ta fita batare datayi saurayiba....mlm na dasa Aya Azancensa yashare y'an guntayen hayawayen sa"shi kansa Abba yayi kukan zuci"kuma yasha Alwashin saiya d'aga darajar yasmeen ta zama Abin kwantance a wannan k'auyen nasu"Abban na k'ok'arin mgn yasmeen ta shigo soron da sallama cikin sanyin muryarta ta duk'a gaban Abba"ta Ajiye ruwa pure water guda biyu dake cikin wani plate da gidauniyar fura"tanata d'an murmushi "godiya nake y'ata kinji?"zoki Amsa "yafad'a yana zaro rafar y'an 1k guda biyu yamik'a mata"sbd yasan koya bama mlm da wuya ya Amsa "dan tun suna yara yasanshi me gudun duniya ne"itama murmushi tayi cikin ladabi tace"dan Allah Abba kabarsu"zan dai Amshi dubu d'aya sbd babu kyau maida kyauta"ta fad'a kanta Ak'asa" indai da gaske ni Abbanki ne ki Amsa yasmeen"mlm kasaka baki y'ata ta Amshi kyautata"Ai Alh sunyi yawa Asali tunda take bata tab'a ganin irin wa'annan kud'ad'en ba"hakane nidai kyauta na bayar kuma dan Allah na bayar"shikenan Allah yasaka da Alkhairinsa"ki Amsa mama nah"cewar mlm yana kallonta"yasmeen ta Amsa itama tana godiya ta koma cikin gidan....bayan Abba yasha ruwan da furan babu nuna wani k'yama"sbd kallo d'aya zaka yiwa gidan da ita kanta yarinyar kasan sunada tsabta"hak'ik'a na tausayawa yasmeen dakuma kai"saidai Ayanzun inada wani mgn me girma idan harka Amince"idan Abin ya tabbata dole na kwana Anan zuwa gobe in sha Allah saina koma dakai muje kaga likitah"to Masha Allah! Ina jinka"Abba ya sauke numfashi yana fad'in idan har zaka Amince mun inaso kabama sadeeq Auren yasmeen....dam ! k'irjin mlm yabuga"ya kalli Abba da sauri batare daya furta komai ba"kayi shiru?"ya sauke Ajiyar zuciya yana fad'in Ina mamakin yadda ka Aminta dani baka gujeniba sbd tazarar dake tsakaninmu Ayanzun"sannan kuma Ina tsoron kar na Amince sadeeq yanuna baya sonta kasan yaran zamani"dukda nasan halin mamana koda bataso idan dai na bata umarni zata Amince ta kasance meyin biyayya"idan har kabama yasmeen irin wannan shedar nima na bama sadeeq irinta"bazai musamun ba nasani"to Amma bayada wacce yakeso?"yanada ita zancen gaskiya"kuma tarbiyan yarinyar bemun ba"saidai zan barsa in har yana buk'atar Aurenta ya Aureta"ta hakan zai iya canzata"batun tazarar dakace ka hango niban gantaba"sadeeq befi k'arfin yasmeen ba"in sha Allah Ina ji Ajikina zamuyi Alfahari da wannan had'in mlm"kasaka Albarka kamusu fatan Alkhairi " inaso Ad'aura Auren gobe kafin na wuce"may be daga baya sadeeq zaizo suga juna sannan Akawo kayan lefe saita tare"kuma Anan wajenmu zasu fara zama sbd naga irin zaman nasu"sannan zan saka yanema mata university Acan ta dinga zuwa.....kukan farin ciki mlm yasaka yana yiwa Abba godiya"karka damu yiwa kaine"dama kai tsaye Anan nafara zuwa"zan wuce gidan kawu isihu(k'anin mahaifinsa) saina sanar masa goben su kawo kud'in sadaki dana neman Aure Ad'aura da k'arfe 2:00pm"daga nan zuwa dare saika sanarwa mutane"to shikenan saima Ad'aura a masallaci "inaso abiya sadaki dubu 50"dubu hamsin mlm ?"eh sadaki mafi k'aranci yafi saka Aure yayi Albarka"hakane Amma kayi hak'uri ko dubu 100 abiya"sannan babu Abinda muke so sai yasmeen banda wasu kayan d'aki"nine zan mata komai Amatsayin kai kayi batare da kowa yasaniba"gaskiya hidimar tayi yawa Alh Amadu"karka manta mlm kaima kabama rayuwata gudun muwa ,kataimakeni lokacin danake buk'atar taimako.....ninama manta da Anyi hakan"Toni Ai ban mantaba"yafad'a yana murmushi ya mik'e tsaye yana gyara malun malun d'in sa sukayi sallama yafita"mlm ya sauke Ajiyar zuciya yana fad'in ikon Allah kenan! kira ya k'walama Almajiransa guda biyu ,bayan sunzo yace"su kwashe kayan Abincin su wuce ciki dasu"har suka mayar da kayan yana zaune yana tunani"dukda k'asan zuciyarsa gani yakeyi kamar sadeeq bazaiso yasmeen ba sbd tana y'ar k'auye"saidai zai sanar mata idan har Akwai wulak'anci ta sanar masa sbd shi baya kwad'ayi"yana jin tausayin y'arsa kodan maraicin rashin uwa datake dashi.....baba gashi kaci Ankusan kiran sallar la'asar"yaji muryar yasmeen "yakalleta yaga plate d'in jalop na taliyar Hausa ne ta Ajiye masa da spoon Asama"da Alama yanzun tagama"dama suna rayuwane idan Akwai suci idan babu su hak'ura "zauna mamana muyi mgn kinjiko?"babu musu ta zauna"kinga mutumin nan daya tashi?"babban Abokinah ne tun muna yara"sai Allah yasa yatafi kano....baba ko shine Alh Amadun danaji kana yawan fad'a?"Eh shine"yazomun da zance me girma yasmeen"yazomun da zancen yanaso nabama d'ansa sadeeq Auren ki....zaro Ido tayi k'irjinta na wani irin mugun bugawa"kanta a sunkuye batace komai ba"na Amince masa mamana sbd nasan keme biyayya ce"kuma naji yace"zaki cigaba da karatunki Acan"dukda haka zanbi dare nayi istihara naga ko Akwai Alkhairi Aciki"sbd gobe da rana za'a d'aura Auren....gobe kuma?"ta fad'a tana d'ago kanta da sauri"yanata kallonta yace"k'warai in Allah yasa"saidai bawai goben zaki tareba ,saima yazo kunga juna"karki damu inaso ki nutsu ki kwantar da hankalinki sadeeq saurayine beda mata, ba tsoho bane kamar rabe"kuma Agidansu zaku zauna zuwa gaba ku koma gidanku kamar yadda mahaifinsa yasanar mun"kinfi kowa sanin halina yasmeen bana kwad'ayi Akwai manyan dalilai da suka saka na Amince da wannan Auren"saidai idan naga da matsala wlh da kaina zance Arabashi ba fata nake ba"babu komai baba duk Abinda kayi game dani daidai ne"ta fad'a cikin k'arfin hali tana b'oye hawayen dake mak'ale cikin k'wayar idanuwanta"Allah yayi miki Albarka yasmeen"insha Allah zakiyi farin ciki da wannan Auren...... washe gari misalin karfe 2:00 pm jama'a suka shaida d'aurin Auren *Sadeeq Ahmed Lamid'o da Fatima Auwal charanchi* Akan sadaki nera dubu d'ari.....Ana gama d'aurin Auren bayan sallar la'asar mlm da Abba suka d'auki hanyar komawa kano"bayan mlm yabar yasmeen gidansu k'awarta lami"bayan sallar magrib suka iso gida"kai tsaye wata private hospital aka nufa da Abba"bayan sun gama bincikarsa suka bashi gado sai yayi kwana 2 ana kulawa dashi"bayan Abba yabiya komai yamasa sallama da nufin da safe zai zo...... Agajiye Abba ya iso gidan"sai Akayi sa'a doctor keda girki"sadeeq na zaune kan kujerah da lap top Agabansa da Alama wani Aiki me mahinmanci yakeyi"Farooq na zaune kan carpet ya nutsu sbd tsawa guda yamasa yanutsu"su zarah kuwa tsoronsa yasaka suka kasa zama cikin parlourn"yana sanye da fara k'ar d'in jallabiya Ajikinsa wacce tayi matuk'ar yimasa kyau "gaba d'aya parlourn ya rikice da k'amshin turarensa"Aikin yakeyi ya tura lip nasa na kasa cikin bakinsa yana tsotsa"tun wayewar safiyar yau yakejin fad'uwar gabar dabai san dalili ba"ga suhan ta damesa da zafin waya be picking, sbd ita yakashe babbar wayarsa gaba d'aya"yana cikin Aikin Abba yashigo da sallama yana rik'e da ledoji"farouq yasaki ihu yaje ya rungume Abba "mama ta fito tasha shirinta tana murmushi tace"Alh sannu da dawowa ,ta fad'a tana Amsar ledojin hannunsa"yauwa Dr "yafad'a yana satar kallon sadeeq daya rufe laptop d'in ya sakko k'asa cikin taushin muryansa me dad'in sauti yace"Abba sannu da dawowa"yauwa babanah"dama kuwa inason mgn dakai da safe"tsintar kansa sadeeq yayi dajin fad'uwar gaba,itama mama haka"sai kawai ta wuce ciki"yayinda sadeeq ya Amsa dato yana d'aukar laptop d'in yanufi side d'insa"kai tsaye had'ad'd'en bed room d'insa ya tura k'ofar yashiga"ya Ajiye laptop d'in ya kwanta rigingine saman bed d'insa dayaji shimfid'u na Alfarma masu taushin gaske"yayi matashin kai da hannayensa"kodai Abba zancen suhan zai mun ne ?"yafad'a Azuciyarsa sbd jikinsa yabashi jiya yagansu tare"ya girgiza kansa yana jin mugun haushinta"yana ganin inhar iyayensa bazasu so ya Aureta ba saiya hak'ura "dama shi SO ba matsalar bace"yana wannan tunanin yabud'e babbar wayarsa ya hau online "tsaki yaja daya shiga what's app yaga suhan ta turo masa vedio d'inta da kayan bacci Ajikinta kanta bbu d'an kwali"tayi parking shukun da aka mata da gashin doki"rintse Ido yayi da sauri sbd jin yadda take k'aramin kuka na zallar tab'ara tana bashi hak'uri sai turo kirji takeyi"tsabar takaici da yanayin dayaji saiya koma kashe wayar"yanada burin hanata saka attached bayan ya Aureta"zai kuma sanar mata karta koma turo masa vedios tana a haka"gaba d'aya da b'acin ran data haddasa masa bacci ya kwasheshi batare daya yi Addua ba.....washe gari yana dawowa daga masjeed ya nufi d'akin dayake motsa jiki"ya kwashe kusan Awa guda yana motsa jikinsa duk yayi uban gumi" saidai yasaka handcheef yagoge"yana k'ok'arin fitowa daga ciki zarah ta shigo da sallama"ya had'e rai yana fad'in lafiya?"dama yaya Abba yace kazo"Ina zuwa"batayi mgn ba ta fita"tana gulmarsa Aranta"wai duk wacce ta Auresa ta shiga ukkunta.... Abba na zaune A parloursa da jallabiya Ajikinsa da farin tubarau yana karatun jarida"Ahaka sadeeq Lamid'o ya shigo da sallama cikin nutsuwa ya zauna kan carpet"Abba na murmushi ya Ajiye jaridar ya kallesa yace"sadeeq! k'irjinsa yabuga"sadeeq!! yakoma maimaitawa Akaro na biyu murya babu Alamar wasa"kansa ak'asa yace"na'am Abba "yafad'a zuciyarsa nasanar masa akan suhan Abba yakirashi"kasan mlm Auwal Abokinah dake charanchi?"da mamaki yace"nasanshi Abba"to Masha Allah"na had'aka Aure da y'arsa yasmeen! Ayau aka d'aura Auren "nayi hakane sbd yabawa da ingantacciyar tarbiyar yarinyar da ilimin addini datake dashi"na kuma nema maka Aurenta ne sbd nasan baza kamun musu ba"in sha Allah sadeeq zakayi farin ciki da wannan Auren.......✍️ Ana wata ga wata πŸ€“πŸ˜Ž wannan book d'in na kudine regular grp 300 vip grp 1000 special group 2k wato 3pages in a day zaku biya kud'in ku ta wannan acc numberπŸ‘‰2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251 300 kawai ake turo kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne banason transfer d'in kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kira ? y'an nijar ku tuntub'i wannan number πŸ‘‰ +227 88 01 90 50 normal grp 500f vip grp 1000f special grp 2000f dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biya ba 2/26/24, 14:08 - Ummu: 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 ❀‍ ? NIDA BARRISTER SADEEQ ❀‍ ? 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story &written by mommyn fareesa Free page 5&6 .........wani irin dummmm sadeeq Lamid'o yaji cikin kansa had'e dajin fad'uwar gaba! zuciyarsa na tsananta bugawa da k'arfi! yafara furta inna lillahi wa inna ilaihir raju'un Aransa" fatansa Allah yasa maganganun nan dayakeji Abakin Abba A mafarkine bada gaske bane"lokaci guda zufa ta fara keto masa Ajiki ,yayinda kansa ke Ak'asa Abba na binsa da kallo yana jiran jin ta bakinsa.....*ni sadeeq aka yima Auren dole*? ya tambayi kansa da kansa....kayi shiru ko baka jine?"da k'yar ya iya jarumta tattaro haruffan kalmar nagode Abba! yafad'a zuciyarsa Acunkushe" gaba d'aya ji yakeyi kamar An buga masa guduma saman kansa sbd tsananin sarawar dayake masa lokaci guda"saidai dayake namijin gaske ne,me tsananin dakiya da jarumta sai yab'oye yanayin daya tsintsi kansa Aciki"sbd baya fatan yakasance meyin musu da mahaifinsa har k'arshen numfashi.....kayi hak'uri babanah ! nasan ko yaya zakaji wani iri kamar yadda itama yasmeen d'in zataji"sbd daga kai har ita kowane biyayya zai mana"inaso ka rik'e yasmeen da Amana da mutunci"sannan bayan ita in har kana buk'atar k'ara Aure zaka iya k'arawa in har zakayi Adalci"Ina ji Ajikina sai yasmeen ta cika gidan nan da jikoki na....rintse Ido sadeeq Lamid'o yayi yana gizon lip nasa na k'asa kamar zai hudashi"Abba yaci gaba da cewa"yasmeen ba wata babba bace zasuyi age mate da zarah"ranar friday inaso kaje ku gaisa da ita kaji koda Akwai Abinda take buk'ata"sbd banaso tarewar taku ta wuce sati 4 zuwa ukku haka"kuma Anan gidan zaku zauna"bana so ka nunawa duniya baka son yasmeen "sannu a hankali zaka sota in sha Allah"da k'yar ya d'ago kansa yana fad'in to Abba zan wuce"shikenan Allah yayi maka Albarka yabaka masuyi maka biyayya kaima"be samu damar Amsawa ba yamik'e tsaye yana had'e hanya sbd jirin dayake d'ibarsa"babbar matsalarsa yanzun itace suhan"yasan halinta game da zafin kishi ba hankaline da itaba"karma taji labari tasamesa a office cikin mutane ,ko tace zata kashe kanta"sannan taya zai gujema wannan Auren?"kamarshi gemai gemai za'ayima Auren dole.....bakaji ne wai?"yaji muryar mama"da sauri yajuya yagansa Ashe har ya iso main parlour "saidai ganin su zarah zaune suna break fast a dining area yasaka yanufi d'akin baccin maman kawai"saman bed side drower ya zauna yana furta why Abba? nizan rayu da macen da bana so"kuma k'aramar yarinya sannan villager girl?? it can wlh!! yafad'a da k'arfi yana furzan da zazzafan huci daga bakinsa "mama ta turo k'ofar ta shigo fuskarta bbu walwala"sbd bataso yamata k'orafi game da wannan Aure "kafin yasani ita Abba yafara sanarmawa"yakuma fad'a mata tayi Addua da fatan Alkhairi in sha Allah ko bata san Auren wata ran zata soshi har tayi Alfahari dashi.....dukda sadeeq Lamid'o yakasance be cika yawan kamata k'orafi ko k'arar waniba saidai yau k'wayar idanuwansa kawai data kalla ta tabbatar mata da cewa yakawo k'orafe k'orafe masu matuk'ar yawa....mama Abba yasanar miki Abinda yafaru?"yafad'a cikin wani yanayi yana kallonta da jajayen idanuwansa "yasanar mun wani abu ne yafaru?"haba mama! bazaki nuna masa illar hakan ba?"okay so kakeyi nayi takara da hukuncin Allah,ko kuwa so kakeyi nace kabujirewa maganar Alh??"karka manta matar mutum kabarinsa "tun jiya nake sanarwa Allah idan babu Alkhairi a wannan Auren Allah yarabasa"idan kuma Akwai Alkhairi Allah yasaka muku son junanku kaida ita....yatsina fuska yayi yana girgiza kansa "mama ta zauna gefen bed d'in cikin rarrashi tace kayi hak'uri babanah ka kasance meyin biyayya kamar yadda itama yarinyar tayi"karka manta namiji mijin mace 4 ne idan kana ra'ayi saika k'ara Auren ka agaba"Amma bana baka goyon bayan ka bujurema umarnin mahaifinka"sannan bance kanunama kowa baka son Auren nan ba , musammun hafsa da salma "shiru yayi yak'i mgn dan beso ana wani cewa yak'ara Aure"sbd tsarin mace guda yake dashi"kusan mintina 3 beyi mgn ba yamik'e tsaye yabar d'akin "mama ta girgiza kanta itadai fatanta Allah yasa sadeeq karya cutar da y'ar mutane ,sarai tasan halinsa idan baya son Abu...yana fitowa yasami moon itada Amira suna guje guje....wata rikitacciyar tsawar da y'an hanjin cikinsu suka kad'a yasakar musu"Atake suka nutsu"yaja doguwar tsuka yafita yana bar musu daddad'an k'amshin turarensa"directly part d'insa yanufa zuciyarsa na wani irin had'ewa "yana tunanin dole yaje yaga mohd suyi mgn Asami mafitar dazai gujema wannan kaddararran Auren" Amma gsky bazai iyaba...... jallabiyar jikinsa yacire ya d'aura farin towel iya k'ugunsa"nabi manyan k'wanjinsa da kallo Masha Allah"ba k'aramin karfaffan mutum bane"gaba d'aya bashida walwala Ahaka yashiga bath room d'in,yafi mintina 30 yana wankan yana tunani had'e da jan tsaki"wani irin mugun tsanar yasmeen da haushintane dank'are Aransa, dukda kasancewar besan taba "komai nasa Atsare kan lokaci yake gudanar dashi Amma yau gashi daga wanka zuwa shiryawa yabata kusan Awa guda sbd haushin wata kucaka.....dukda a bad mood yake Amma milk suit d'in dake jikinsa ba k'aramin kyau da karb'an sa sukayiba"ya hade rai sosai fuskarsa babu walwala"yafito yana rik'e da wayoyinsa da keys d'in motarsa"lokacin k'arfe 8:34 am"bayan kuma k'a'idarsace 8:00am a office take masa"ko daya fito tacan k'ofar baya yabi ya iso parking lot ,sbd beson ya had'u da mama tamasa zancen yatsaya yayi break fast.... Asukwane driver ya iso yana kwasar gaisuwa ya Amshi key d'in motar ya bud'e masa back sit ya shiga"batare daya ce kanzil ba"hakan yasaka driver d'in jan bakinsa ya tsuke be furta komai ba"yana ganin kiran mutane a babbar wayarsa da k'aramar Amma duk ya musu banza yana jan tsaki"da k'yar yace police station zamuje! to yallab'ai"suna gab da isowa wasu motoci suka iso Aguje zasu bangajesu"driver d'in yayi saurin kaucewa....maza ka gangara kayi parking! yafad'a murya adake yana huci"tun kafin yagama parking motocin suka zagayesu"sadeeq Lamid'o yasaki tattausan murmushin daya nuna Ainahin baiwar kyawun halittar sa"driver d'in na k'ok'arin fitowa Lamid'o yayi saurin dakatar dashi wajen cewa yi zamanka"daga haka yabud'e k'ofar da k'arfi ya fito.....hahahahahahahaha!! yaji suna kecewa da wata mahaukaciyar dariya"kusan su goma k'atti majiya k'arfi"duk suna tsaye da manyan makamai Ahannunsu "yayinda Bilal lamis ke zaune saman mota yana busa sigari"yana bin sadeeq da mugun kallo "yana kuma mamakin da bega tsoro a k'wayar idanuwansa ba....sadeeq kuwa tsaye yayi yana binsu da kallon k'asan Ido yana shafa lallausan b'akin sajensa d'aya zagaye kyakykyawar doguwar fuskarsa.....me kukejira da bazaku afka masa ba ne?"inaso kasani zan wulak'antaka Agaban bainar nasi kuma gab da police station bbu Abinda zai faru"cewar Bilal cikin kurari da d'aga murya "kusan mutum biyar suka nufi sadeeq da makamai a hannunsu"hankalin driver d'insa dake zaune yana kallon komai ta glass yatashi"yana ganin kamar sadeeq bazai iya dasuba"saidai tun kafin su iso yayi tsalle guda yashaki k'ato guda yabuga masa kansa ya Amshe wuk'ar hannunsa yana karashi gefensa wad'anda suka kamasa suka suka yankesa a k'ahon zuci ya sulale cikin jini"cikin mintina 5 sadeeq yabazar dasu duk yamusu rauni"sai gashi sauran biyar d'in suka fara ja da baya"shi kuwa fuskarsa d'auke da k'ayataccen murmushi yanufi wajen Bilal"cikin tafiyarsa irinta kas'aitatun mazan da suka Amsa sunansu maza"dallah banzaye ku hau kansa mana"cewar Bilal gabansa na fad'uwa yadiro daga saman motar"mutum biyu suka nufi sadeeq Atare yabazar dasu k'asa ya iso gaban Bilal"Ido cikin Ido ya kallesa yasaki malalacin murmushi sannan ya had'e rai ya fisgosa yafara bashi zafafan puncher's kota Ina"yayinda mutane sunfi 30 zagaye dasu suna kallonsu"cikin zafin rai sadeeq ke furta zan wulak'antaka naje dakai na rufe naga shegen daya Isa yafito dakai"shashasha lusarin namiji"yafad'a yana fisge rigar dake jikin Bilal yayi saura daga shi sai dogon wondo da farar vest"yayinda sauran kantin ukku suka gudu"Bilal kuwa fuska ta kumbura,hanci da baki duk sun fashe"jibgarsa kawai sadeeq keyi babu tausayi Aransa yana jansa k'asa kowa nagani"wasu suka fara binsu wasu kuma basu bisuba"tafiyar mintina 10 yayi da Bilal yana dukansa har suka iso police station d'in"yana huci ya halbasa da k'afarsa me takalmi sawu ciki "da kansa yakaisa cell ya rufe yana nufar office d'in mohd yaja kujerah ya zauna yana furzan da zazzafan huci daga bakinsa"yayi bala'in had'e rai sbd wasu mata biyu daya gani suna mgn sai kallonsa sukeyi"dama haka yakeyi idan yaga mata"tamkar mohd yayi dariya yadai dake ya sallamesu "dama tun farkon fara fad'an su da yaran Bilal Aka kira mohd Aka sanar masa"bejeba be kuma tura kowaba"sbd yasan waye Abokinsa ko sun kai su 50 zai iya dasu cikin ikon Allah....tun bayan fitar matan yake kallonsa yana nazarinsa"Atake ya fahimci yanada damuwa"dama kuma yasha Alwashin bazai neme saba saidai shi ya nemesa tunda be masa laifin komai ba"Ayan zun ya tabbatar da Lamid'o yanada damuwa"sbd yasan indai sbd Bilal ne yana rufesa office d'in commissioner zashi bazai neme saba"kuma sbd Bilal bazai saka damuwa Aransa ba..... Abokinah barka da Asuba! cewar mohd sbd yasan zafin kan Lamid'o da wuya yatankasa"d'ago kansa yayi yazuba jajayen idanuwansa saman fuskar mohd murya asark'e yace"inada damuwa Abokinah me tsananin girman gaske" pls kabani mafitar yadda zanyi"saidai kasake kamun dariya wlh saidai ran kowa yab'aci"d'an murmushi mohd yayi yana sauke Ajiyar zuciya sbd jin kalaman Lamid'o na k'arshe "hakan yatabbar masa da cewa" matsalar ba wata babba bace ba"tunda gashi yana zancen wai karya masa dariya"okay tell me......cikin wani yanayi sadeeq yamasa bayanin komai"ya d'ora da cewa" inda ba k'aramar yarinya bace zan iya hak'ura bayan y'an watanni nasan yadda nayi na rabu da ita"Amma bazan iyaba, ga suhan kasan halinta Akaina babu Abinda bazata iya ba"banaso ta tashi hankalinta"pls tayaya kake ganin zamu bullowa Abin?"kodai zuwa zamuyi mu biyata kud'i tacema mahaifinta bataso yasaka nasaketa??.....da wani irin shock mohd ya kallesa yana girgiza kansa yace" wannan shine babban kuskuran da zakayi musammun idan Abba yagane"meyasa kai bazaka bujureba sai ita kakeso ka yaudara da kud'i?"tabbas mutanan yanzun sunayin komai sbd kud'i"saidai ba duka Aka taru aka zama d'aya ba"nidai idan zakaji tawa ka hak'ura ka Amshi Auren nan da daraja insha Allah zakayi farin ciki dashi Ina jin hakan Ajikina"sannan bazan b'oye makaba Lamid'o wlh naji dad'in Auren.....wani banzan kallo sadeeq yajefa dashi"yasaki d'an murmushi yana fad'in dama nasan yanzun bazaka ganeba"wacce zuciyarka take kanta itama ba sonta kakeba burgeka kawai takeyi"inaso kasani !ba'a sanin maci tuwo sai miya ta k'are"kuma d'an hakkin daka raina shine ke tsone maka ido"sbd wata suhan karka yadda ka bujurewa iyayenka"inda zakaji shawarata daka hak'ura da ita Ango ,sbd sam bata dace da kamili kamarka ba"wai yama sunan Amaryar tamu ne?? yak'are maganar yana b'oye dariyarsa sbd yasan yakai Abokin nasa mak'ura,yakuma d'auresa da kalamansa.....doguwar tsuka yaja ya mik'e tsaye yana fad'in wlh sbd kana mun irin hakan zamu iya rabuwa dakai har Abada"Aikin banza kawai"yafad'a yana doka table d'in gabansa ya mik'e tsaye yafita afusace"mohd ya girgiza kansa yana jin tausayin yarinyar data zama mata ga sadeeq "da hanzari ya d'auki landline phone yakira yasanar Arufe cell d'in da Bilal ke ciki, sbd kar sadeeq yaje ya huce haushinsa kansa"yasan halinsa da bak'ar zuciya kar yaje yayi kisan kai.... ****** kimanin kwana 3 kenan da faruwar hakan"mlm yasami lafiya sosai"sun bashi magunguna"Abba yasaka driver yakawosa har gida da Abin Arzik'a"yasmeen kuwa dukta tashi hankalinta sbd gudun kar wanda aka Aura mata baya sonta"lami kuwa da mahaifiyarta murna suka dinga taya yasmeen "sbd sunsan mahaifinta bazai mata zab'en tumun dare ba"dandanan umman lami tafara bama yasmeen kulawa da shawarwarin yadda Ake zaman Aure"ita dai ji kawai takeyi"wani irin mugun tsoron Auren da wanda ta Aura d'in takeji"tana gani babanta yazo yayima iyayen lami godiya yabada kud'i afara yimata gyaran jiki sbd dangin mamanta ba'a nan sukeba"gashi baba yasanar mata ranar friday sadeeq zaizo"gaba d'aya batada walwala wani iri takeji Azuciyarta... Ab'angaren uban gayyar kuwa gaba ya d'auka da mohd baya kiransa baya zuwa wajensa"yayinda har yanzun Bilal na'a rufe"mutanan cikin gidan su kuwa kowa yaji labarin Auren,wasu sunyi murna wasu akasin hakan"suhan kuwa jiya suka shirya da mutumin nata yagaji da fushin dayakeyi da ita.....tun wayewar garin yau zuciyar sadeeq a cunkushe take sbd yau zai tafi charanchi wajen yasmeen "gashi yana fushi da mohd"besan waye zai masa rakkiya ba"kuma Abba yasanar masa yaje yayi Abinda yaka mata"muddin beje ba ransa zai b'aci"tun wajen k'arfe 10 yagama shirinsa cikin milk d'in shadda sabuwa"wacce akayima Aiki da dark brown d'in zare"komai yasaka brown"yanayin yadda wankan ya Amshesa zaka d'auka yau aka d'aura Auren"har wani haske da shek'i fuskarsa keyi"su moon na zaune a main parlour ya shigo"suka bishi da kallo suna gaishesa yamusu

Chapter 2 of 6