musu kallo sama da kasa.
Sannan tace "Or sorry! Dama ku ne kuka tafi
makaranta? Ta nuna Nusaiba da tafi ganin damanta,
tace "Ke ce Naziyatu? Nusaiba ta girgiza mata kai, ta
nuna mata Naziyatu da hannunta.
Murja tace "O.k, ke ce Nusaiba kenan? Nusaiba
ta kuma daga mata kanta, ba tare da ta bude baki tayi
mata magana ba, dan ita Nusaiba a rayuwarta, bata
kaunar wulakanci da rainin wayo.
Ta kuma fuskanci Murja mai irin halayen ne.
Murja tace "To ya kuke? Sannunku fa student." Ta
kwalawa Lanti kira. Sai gata ta shigo da sauri. Murja
tace "Lanti ki samowa wadannan yaran abin da za su ci.
DA SANNU... 93
Duk da dai ba baki bane." Ta jawo wani fingilallen gyale
da bai wuce nayi dan kwali da shi ba fari kal!
Da shi kamar takarda, tace "Lanti, in nawan ya
dawo. Ki fada masa na tafi bakin Asibiti. Na kira Mama
mu yi magana. Ni Wallahi wannan bala'in ya fara isata.
Mai ake yi da zaman kauye, in ba kaddara ba, ace kana
son yin zumunci da 'yan-uwanka.
Sai ka fita ka je wai wani bakin Asibiti. Ina
amfani haka?Wannan kaddaran tayi yawa. Bari nawan
ya dawo. Ni fa kauyen nan ya isheni. Me ake da zaman
kauye? Sai lalura. Ni kam na gaji."
Naziyatu ta tunzura tace "Ke tsaya fa ki ji.
Rainin arzikin naki da walukancinki ya tsaya haka nan.
Ya isheki. Na tabbatar da kike wannan kumfar bakin, na
san gidan ubanki da yake birni, bai kai gidan ubana da
yake kauye ba.
Kuma ke ba ki isa ki raina kauye ba, dan nan ne
mafarin tsoho da tsohuwa. Dan haka ahir dinki, kada ki
kuma neman raina mana kauye. Dan kauye ba abin
rainawa bane, ga mai hankali da tunani da asali." Ta
nunata da dan yatsa, kamar zata tsole mata ido, tace.
"This is the last warning! Sannan ta kamo
hannun Nusaiba ta jata suka fita. Ni kaina yau masifar
Naziyatu ta birgeni, dan na kan so wanda ke son asalin
shi. Na kan kuma so, wanda ke gudun wulakanci da
raini arziki. Ba ka zamo saboda abin duniya.
Wani ya maidaka wulakantacce ba, ya kuma
raina maka arzikin da Allah ya ba ka ba. Ina amfanin irin
MAMAN FADILA 94
wannan masu mataccen zuciya? Wanda muddin ba su yi
yaki da zuciyarsu ba.
To sai dai su mutu a wulakanci. Allah ya ganad
da masu irin wannan dabi'u, su guji son abin duniyar da
bana su ba, na wani can, don su ke kaimu ga wulakanta
da tozarta, har a raina maka naka arzikin da Allah ya ba
ka. Dan ko wane bawa da arzikin da Allah yayi ma shi. Ta
bangarori da dama.
Rashin hakurinmu ne na 'Yan-Adam da har sai
mun kai ga inda ake wulakantamu. To Allah ya ba mu
ikon tsayawa a matsayin da Allah ya aje mu. DA
SANNU... Ba abin mamaki bane wata ran Allah ya kaika
ga wani matsayi da mafarkinka da tunaninka.
Bai taba raya maka za ka taka wannan
matsayin ba. To amma ma sai ka bi da sannu. Babu
yadda Allah baya ikonsa. Ya mayar da talaka
gawurtaccen mai kudi. Ya kuma mayar da mai-kudi
gawurtacen talaka. Tafiyarsu Naziyatu.
Lanti ta dunga ba Murja hakuri "Ki yi hakuri,
haka halin Naziyatu yake. Babu wanda take ragawa, sai
iyayenta da mijinki a cikin gidan nan, ki daina kulata. In
ba haka ba rashin kunya zata dunga yi miki."
Murja tace "Amma kuwa yarinyar nan zata gane
kuranta, za ta raina wayonta."Wayar da dai Murja bata
je ta kira ba kenan, tayi jifa da wayarta. Ta shiga rera
sabon kuka. Taf! Aiki ko ya sameki. Ni ban iya wannan
kissan namu na mata ba. Sai na nufi sasan Hakimi, dan
na ga me suke. To ina shiga, na ga Hajiya Safiya.
DA SANNU... 95
Tana tafa hannu, tana sallalami "Yanzu
Naziyatu zagerancin naki ya kai ki ki je har dakin matar
kanin Babanku ki yi sa insa da zuwanki. To zan kuwa
bata miki rai ke ma." Nusaiba tace "Hajiya ba fa laifin
Naziyatu bane, wai kin ga yadda matar nan ta ke neman
raina mana arziki ne.
Wallahi ni kaina kiris ya rage in ragargajeta, ke
dai kawai Hajiya hakuri za ki yi. Wannan ta faru. Kowa
ya kama kansa." Hajiya S afiya tace "To na ji, kada na
kuskura na sake jin makamancin haka. Komai ya wuce.
Allah ya kyauta gaba."
Murja tana daki, ko abinci ta kasa ci, sai aikin
kukan kissa da tasa kanta. Magaji ya shigo, ya ci karo
da Gaje Zaune a falo. Abin ya so ya ba shi mamaki. Sai
bai kula ba.
Ya wuce abin shi dakin Murja, yadda ya ganta ya
sosa masa rai sosai. Ya je kusa da ita, ya kamata. Yayi
lallashin Juniya ta fada masa kome aka yi mata? Amma
ta ki yin magana. Sai kawai ya kwalawa Gaje kira "Ke
Habiba zo nan."
Tayi sallama ta shigo, tace "Sannu, gani." Daga
idon da Murja tayi, ta ga irin shigar kwalliyar da tayi, shi
ya bata mata rai. Magaji yace ma Gaje "Ke Habiba me
ya samu Bebi?
Naa Gaje tace "Ni ma ban san abin da ya
sameta ba." Da sauri Murja tace "Munafuka, ba ki sani
ba kika ce? To uban wa ya turosu, su zo su zazzaga min
tsiya." Magaji yace "Su waye suka zo, har daki suka
zageki? Murja tace "Su Naziyatu, duka ma suka so su yi
MAMAN FADILA 96
min. Lanti ce ta taimaka min. Ba su dakeni ba." Ai da
gudu ya fita, ya nufi cikin gida.
Naziyatu da Nusaiba suna cin abinci. Suka
mike zumbur za su gudu daki. Hajiya Safiya da ke zaune
bakin kofar, ta kare, tace "Ina za ku? Sai kun yi ma shi
bayani. Babu inda za ku gudu."
Magaji ya fallawa Naziyatu mari. Ya kuma daga
hannu ya faliawa Nusaiba. Sannan yace "Gaba
dayanku, ku ba ku da hankali ko? Hajiya kin san kuwa
abinda yaran nan suka yi wa Murja?
Suka je zasu daketa. Lanti fa ta hanasu, suna
biyewa 'yar kauyen yarinyar nan da bata da hankali.
Murja fa ciki ke gareta. Amma kuke kokarin tada mata
da hankali. To Wallahi ku bi ta a hankali, kada na kuma
samun kun bata mata rai. Dan juna biyu ke gareta."
Hajiya Safiya tace "Asibiti kuka je aka fada
muku ciki gareta? Magaji yace "A'a ita da kanta ta
fada min, wai tana jin kasala, tana kuma yin amai,
kuma bata ga batan watanta ba."
Hajiya Safiya ta kada kai, tace "Allah ya rabasu
lafiya. Ita kuma Gaje fa? Magaji yace "Ita ban yi
tsammanin tana da ciki ba." Hajiya Safiya tace "Uhm!
To ita ma Allah ya bata."
Magaji yace "Amin." Ya nuna su Nusaiba da
hannun shi, yayi kawai yace musu "Next time, kada
kuka kara." Ya fita da hanzari. Naziyatu tace "Wallahi
ga dukkan alamu, maganan Baba Magaji suna cutar
gidanku da rowa." Hajiya Safiya tace "Ni ma na ga
DA SANNU... 97
5
alaman haka. Amm ku bari zan tambayi Lanti tayi min
hayani."
Nusaiba tace "Wallahi in har haka ne kafin mu
koma makaranta, ita ma Gaje sai ta ba su mamaki." Ita
rayuwa ba a mata garaje, komi ka bi a hankali, ka bi shi
DA SANNU... Sai ka ga ka kai ga samun duk abinda
kake so, kake kuma nema.
Murja dai ta gaza sukuni. Ita dole haihuwa take
so. Ita ce koyaushe zaryan asibiti kullum yi ma miji
karyan ciki. Kuma cikin ya ki samuwa. Ita ce wankin
ciki, shan kwayoyi. Ba miji kai a ko wane lokaci, babu
hutu. Sai ka ce agogo.
Tun Magaji yana zillewa, harya gaji, ya saba, ya
fara zame masa jiki. Kamar in fada mata dama ta
saukaka musu yin wannan baya kawo saurin daukar
ciki, shi ciki DA SANNU...
In lokacinsa yayi, to ko akan hanya a tsaye cikin
sauri. Ba ma a cikin daki ko kan gado, ko katifa ba. In
Allah yayi, lokacin shigar ciki yayi, sai ya shiga. Don
haka Murja a jira lokaci. Duk wani gaggawarki ba inda
zai kaiki.
tunda Hajiya Safiya ta nemi Lanti. Ta kuma gaya
mata abinda ta sani. Sai ta samu Gaje tace ta gaya
mata gaskiyar lamari. Hatta kuwa shekara dayan data
karawa Murja duk sai da ta zayyane mata komai. Ai
koda Hajiya Safiya ta ji wannan batu, sai ta ja bakinta
tayi shiru.
Domin muddin Hakimi ya ji wannan magana. To
hatta ita kanta komai zai ruguje mata. Don kullum
MAMAN FADILA 98
maganar Hakimi bata wuce cewa ta rika sanya idanu
akan zamansu Gaje. Ta tabbatar da cewa dukkansu Magaji bai taka hakkin kowa a cikinsu.
Ai babu shiri. Hajiya Safiya ta shiga koyar da Gaje yadda ake zama da miji. Da kuma kishiya. Ta san yadda ake zama da ita. Ta dalilin littafin tauraruwarta
A'isha A Tanimu. Mai suna KIRSOSHIN ZAMA DA MIUI DA KISHIYA
Lokacin da Hajiya Safiya ta kaiwa tauraruwar
tata, Ta tarar ta gama rubutawa. Amma ba a kai ga
bugawa ba. Saboda muhimmancin littafin Hajiya Safiya
ta gaza hakuri, ta bari a fitar da shi ta dunga magiya
akan a taimaka mata ta je da littafin gidanta, ta duba.
Sai ta aiko da shi.
Abinka da ba karaman mace ha. Akalla ta haifi
A'isha. Dole ta cika mata ido ba tare da ran ta yaso ba,
ta dauka ta bata, dan bata da nayi. Dan bata haka wani
ya karanta mata littafi, ba tare da ta fitar da shi kasuwa
ba. Amma tace (Next time) ko Kakanta ce.
Ba haihuwarta tayi ba. Ta daina yarda da
wannan cika idon. Tunda ga shi har yanzun Hajiya Safiya
ta kasa maido mata littafin. Sai fito da wasu sababbi
kawai take. Shi ko kirsoshin zama da miji da kishiya.
Shiru, wata kila sai A'isha ta je da kanta.
Kila ta dawo da abin ta. To dalilin wannan littafi.
Gaje yanzun ta sake. Kyar take kallon kowa. Bata da
matsala, in dai na iya zama da miji da kishiya ne. Sai dai
bata fara aiki da su ba tukuna. Saboda 'yan zamani sun
Naziyatu basu gama nasu shirin ba, dan suna ta koyar
DA SANNU... 99
da Gaje tsaftar jikinta, iya sa kaya, koya mata girke
girken zamani kala-kala.
Sannan kuma da koyar da ita hausan nan dai
ta fara ganewa. Amma ban da turanci, dan basu da
isashen lokaci, saboda lokacin komawarsu makaranta
ya karato.
Shi kuma turanci, dan son natsuwa ne sosai da
isashen lokaci, dan yaren da ba naka ba ne, za ka ara.
Cikin ikon Allah, duk abin da su Nusaiba suka koyawa
Gaje tana fahimta sosai. Ranan da su Nusaiba da
Naziyatu suka koma makaranta. Ranan Gaje ta fara aiki
da kirsoshin da Hajiya Safiya ta karanto mata kuma ta
fara aiki da koyin 'yan zamani, su Naziyatu.
To fa daman 'Ya mace, in har namiji ya nemi
juya mata baya. To bata iya kirsa bane da takunta. Ta
tsaya sanya ne. Magaji fa ya fara kwadayin matar shi. To
amma kuma Murja bata kula ba, dan ita ba wannan
bane a gabanta ba. Ita haihuwa ne a gabanta, dan ta
kosa ta ga ta zama Magaji. Shi ma ya zama ita.
Dan ga alamu, dangin Magaji in har bata haihu
da Magaji ba, ta tabbatar ba za ta iya cimma nasaran
akan Magaji da 'Yan-uwan shi ba, dan haka yanzun
Murja ba wai ta tsaya ga asibiti bane. Hatta
magungunan gargajiya.
Ita ce jika wannan, ta sha, kwaba wancan, ki sa
kafin miji ya sadu da ita. To a haka Mommy mahaiiyarta
ta samu wani tsohon Malami da aka yi mata kwatancen
shi aka ce su je tare ita da Murja, dan haka Murka tayi
wa Magaji karyan an yi musu rasuwa.
MAMAN FADILA 100
Na dangin Mamanta a wani kauye. Sai sun
kwana biyu zasu dawo. Magaji ya amince mata. Sun tafi.
Allah Sarki! Dama Magaji tuntuni yake kwadayin son
mata shi Gaje. Ya rasa yadda zai yi ya bullowa lamarin.
saba irin takun da Murja ke ma shi.
Sai ga shi tayi tafiya, ta bar shi. Magaji ya
sakarwa Gaje jikin shi sosai. To amma kuma yayi
dauriya, dan ya kasa kusantar Gaje. Har kwana biyun da
Murja ta dauka yayi. Shiru babu Murja, bata dawo ba.
Ranan kwana na uku. Magaji ya kasa hakuri,
saboda Murja tayi masa koyi, ko wane lokaci cikin
harkan gamsar da junansu suke. Ya shiga har cikin (Bed
room) din Gaje.
Abin ya ba shi mamaki, bai yi zaton samun dakin
Gaje irin haka ba. Duk abinda Magaji zai yi da Gaje,
tunda ya aureta, sai dai ya tsaya tsakiyar falo su yi. Bai
taba shiga (Bedroom) dinta ba.
Misalin karfe goma sha daya da rabi na dare. Ya
shiga dakin Gaje. Amma abin mamaki, sai ya samu tanа
sallah. Nan ma yayi mamaki. Ya kura mata ido tana jan
tasbaha. Sai yayi mata murmushi. Shi ma ya shige
(Birt room) din dakinta, yayo alwala ya fara nafila.
Kafin ya fara nafilan, yace "Habiba ina son cikin
addu'ar da kike yi, ki sa mu ciki."
Gaje ta gama nafila, ta mike ta bude durowa, ta
dauko wasu sababbin kayan barci da Hajiya Safiya ta
sayo mata da su ka je Saudiya. Tana faman sa kayan
barcin.
DA SANNU.... 101
Ta kalli kanta a madubi. Sai tayi sauri ta kara
daurawa akan kayan barcin da tasa. Sai kawai ta ji
Magaji ya fisge zanin da karfi, yace "Daura zanin nana
gareki yanzu, babu amfani, dan daren yau ne nake son
ya zamana mana darenmu, na farko ni dake."
Gaje cikin koyin maganan tsofaffiin hannu irin
Hajiya Safiya, tace ma shi "Kada ka manta, ni na kara
maka kwana daidai har kwana 365. Ko ka manta ne?
Magaji ya rufe ido, yayi dariya, sannan ya bude, yace
"Ban manta ba, amma wannan ku ta shafa. Ni ban
amince ba." Gaje tace "To mai yasa da ka amince?
Magaji ya girgiza kai. yayi dariya har da
kyakyatawa. Abin da Magaji bai taba yi a gabanta ba.
Sai dai taji shi yana yi a wani waje. Yau ga shi a gabanta
yana mata. Ita ma sai ta shiga yin dariya, saboda irin
birgeta da sha'awa da ya bata.
To ni dai daga dariyar nan, sai kawai na ga suu
dare. Sauran bayani na bar wa mai karatu. Dan ni abin
ya sha kaina. Ni dai da safe. Na lura da Gaje dingisawa
take. Lallai Gaje na san ta ji jiki.
Kuma yadda na ga Magaji yana haba-haba da
Gaje, baya kaunar ko kuda ya rabu da ita. Na san ba
karamin ni'ima Magaji ya samu ba wajen Gaje.
Magaji gaba daya ya manta da Murja. Da namiji
kenan! Koyausheyana manne da Gaje, ko sasan Hakimi
ya hanata zuwa. Hajiya Safiya bata damu ba, dan Lanti
ta tsegunta mata komi.
Murja bata dawo ha. Sai da ta samu kwana
bakwai, sannan ta dawo. Ti-ki-Sa! Boka ya basu
MAMAN FADILA 102
magunguna kala-kala. Boka ya fada mata da zaran ta
gama amfani da magungunan, to za ta samu ciki. Sun
kuma yi alkawari da Bokan. Da zaran ta samu ciki, zata
dawo. Kuma ya bata taimako akan kishiyar ta Gaje.
Ya mayar da ita nakasashiya da rabata da
Magaji. Sam kada su taba jituwa. Dan ta ga alaman
Magaji kamar ya fara son matar shi. Da sharadin da
Boka ya bata, na wannan maganin da ya bata, cewa in
har ta san Magaji ya yana saduwa da Gaje. To kada tayi
amfani da maganin, dan reshe zai juye da mujiya.
Saboda maganin amarai ake yiwa. A rabasu da
mijinsu. Sai ka ga ango yayi sabon amarya. Da zaran ya
shiga gonar shi sau daya. Ya fito. To fa ya fito kenan, shi
da amarya, sai tsana, har sai sun rabu, zai samu
kwanciyar hankali.
Koda Murja ta dawo ta ga rawan kafar da
Magaji yake yi. Sai ta yake wa, ko ya kula Gaje, bata
damuwa, dan tana ganin nesa ta zo kusa. Kafin dare
yayi, duk Murja ta gama sarrafa maganin a jikinta,
kamar yadda Boka ya bata umarni. Dare na yi, ta
matsawa Magaji suka shige daki. Suka fara sarrafa
junansu, yadda suka saba.
To amma fa yau sam bai ji dadin yadda
auratayya tasu ta kasance ba. Amma bai san ko menene
dalili ba. To Murja ta gama shirinta, dan haka wai ita
zata yaudari Magaji da Boka ya fada mata, duk yadda
zata yi, bayan ya sadu da ita. Cikin hadin maganin da
tayi wa jikinta, to ta tabbatar kada ta kuma yarda da
shỉ, har sai ya sadu da Gaje tukuna.
DA SANNU... 103
Sannan kuma asirin zai ci Gaje, dan haka Murja
ta fara magana cikin shagwaba "Ni dai gaskiya shekara
dayan nan ta isheni. Don haka gobe dakin matarka,
wancan yarinyar za ka kwana.
Ka bata hakkinta na aure, ka bar tausaya mata
kamar yadda kake fadi. Kada mu zama masu tauye
mata hakki. Allah ya kamamu da laifinta." Magaji
murmushi yayi, yace "Bebi-na ayi haka kuwa? Kin fa
sanni jarumi ne. Yarinyar can zata iya min kuwa?
Murja ta kashe ido, tace "Haba nawan, kada
wannan ya dameka.Yanzu ake kai yara gidan miji, ba su
fi shekara sha biyu ba, wani a shekaran ka gansu da
goyonsu a baya, ballantana ko da kallon Gaje, in bata
kai shekara ashirin ba. To ba kuma zata yi kasa da
shekara sha tara ba, dan haka ban jin komi, ni dai nace
ka je kawai."
Allah Sarki! Murja da kin san abin da ke
tsakanin Gaje da Magaji da ba ki yi tunanin tura shi
wajenta ba, dan yanzu batun da suke. Gaje na da
shigan ciki. Ti-ki-Sa! Wannan fa shine da gamo da
kasawa. Wannan ciki shine DA SANNU...
Gaje ta sha mamaki da ta ga Magaji ya kwana
daya dakin Murja ya dawo mata. Sam bata yi tunanin zai
saurin dawo mata ba, sannan abin da ya daurewa Gaje
kai, shine yadda suka farantawa junansu rai da gamsar
da kansu, ya fi darensu na farko. Shi kansa Magaji abin
ya gigita shi.
Koda gari ya waye. Magaji ya fita ya shiga dakin
Murja. Suna yin ido hudu. Ya ji gaba daya duniyar baya
MAMAN FADILA 104
fhi
kaunar ya sake ganin Murja. Ai da gudu ya juya da baya,
ya koma dakin Gaje. Yana shiga, kamar hadin baki, ita
ma suka yi ido hudu.
Sai ya ji wani annashuwa da farin ciki. Ya
karasa gareta ya rungumeta, yana jin dadi. Tun daga
wannan rana. Ruruwan so da kaunar Gaje ya dauwama
cikin bargon jikin Magaji.
Ita kuma Murja ruruwan rashin son-ta da
kaunarta ya tabbata cikin bargon Magaji. Ranan
girkinta, sai dai ya kulleta cikin (Bedroom) dinta. Shi
kuma ya kwana a falo. Sai ya gama abin da yake.
Da safe. Sannan in zai fita. Ya budeta. Cikin
wannan halin, su Naziyatu suka dawo. Don sun gama
zana jarabawan-(J. S3) dinsu. Shi kuma Auwalu shi ma
ya gama (S.S.3). Dukyanzún suna gida. Gaje cikinta sai
bunkasa yake, yana gwadawa duniya kansa. Kowa a
gidan nan, Gaje yake so. Uban gaiyar kuwa cikin nan
kamar ya dawo da shi jikin shi.
Auwalu ya shigo yana fadin "Gaje yunwa nake
ji." Magaji yana matsawa Gaje kafa da ta kumbura,
yace "Kai Auwalu, kada na kuma jin ka kira Habiba, ka
ce Gaje. Daga yau dukkanku, ka fadawa sauran nace
Anti Habiba za ku dunga kiranta."
Gaje tace "Kira min Lanti, ta ba ka abinci."
Auwalu bai cika cin abincin cikin gida ba.Ya fi cin na su
Gaje. To tunda Murja ta ga yadda abin ya koma. ta san
an samu kuskure. Ta kuma san cewa lokacin da tayi
tafiya, lokacin Magaji ya san matar shi. Dan haka ta
kuma shiri, ta koma wajen Boka.
DA SANNU.. 105
Abin da Boka ya fada mata. Asiri ba zai karye
ba, har sai ta koma ta jira ranan da Gaje ta haihu. Ta
dibo masa jinin haihuwar Gaje, ta kawo ma shi. Ya kuma
sadu da ita, shine zai iya karya asirin.
Ta dubi yanayin Bokan da wai zal kwanta da ita.
Kuma ya zama mata dole ta yarda da shi din, in har zata
samu Magajinta ya dawo gareta. Murja ta kema gida,
tana jiran haihuwar Gaje. Ta dibi jinin. Murja yaazu bata
da katabus a wurin kowa a gidan. Gaje ce kawal he
tallafawa Murja. Sam Gaje bata yarda ta wulakanta
Murja ba, dan yanzu Murja lallaba Gaje take.
Don ta cinma burinta. Kwatsam! Ashe ita
Murja ranan da ta sha wankan magunguna. Cili ya
shiga. Yana ta karakaina, ya rasa tudun dafawa. in ya
shiga nan, ya shiga can.
An wayi gari Murja bata san wanda ke kanta ba.
Kafin Gaje tayi wani abu. Murja ta suma. Ga shi ta yhwa
Magaji magana ya zo su je asibiti. Amma ya i
sauraranta.
Da gudunta ta shiga sasan Hakimi, tana kuka,
tana fada musu halin da Murja ke ciki. Hajiya Saflya ce
kawai ta rude, ta shiga dakin Hakimi. Su ke Ya'yan
gidan, ko a jikinsu. Sai ma suka dunga yiwa Gaje surutu.
"Su Anti masu tausayi. Anti Habiba. Allah ya bar mana
ke, tare da Baba Magaji.”
Hakimi ne ya fito tare da Hajiya Saflya.Va daka
masu tsawa, "Kanku guda kuwa? Kai Auwalu, ka dauhi
makullin mota, ka kai su asibiti. Sai ka ga kemi yoyl
MAMAN FADILA 106
daidai, sai ka ze ka sanar da mu. In Magajin Hakimi ya
dawe zai blyoku, tunda yanzu Gaje tace baya gida.
Karyan da Gaje tayi. Allah ya taimaketa. Ashe
kawe tona aufa cikin sasa. Shi kuma yana nufa wajen
na shi sabgar.
Hajlya Saffya da Gaje da wata mai aikin Hajiya
Saftya su ne suka tafi da Murja asibiti. Hakimi yay!
neman Magaji, ta sake, ta waya.
Amma shiru, ba a samu ganin Magaji ba.
Nakimi tare da wasu mutanen shi, suka nufi asibiti.
Suna zawa. Likita yayi masu bayanin dole za ayi wа
Murja tiyata, saboda tana da ciki, amma dan dake cikin
nata, ya rasa wajen zama.
Dan haka nan da wasu awoyi, in har ba a fede
cikin Murja, an kwashe magungunan gargajiya da na
asibiti da suka toshe mata inda yaronta zai kwanta.
To komai na lya faruwa da ita. Da yaron cikinta.
Hakimi da kansa yasa hannu aka shiga da Murja dakin
tlyata. Auwalu ya koma gida ya dubo ko Magajiya dawo.
Yana kwance da Magazine yana karantawa.
Auwalu ya fada ma shi halin da Murja ke ciki.
Da sauri yayi jifa da Mujallar hannun shi, yace "Ciki ta
he da shi. Ita ma? Ya mike ya wuce, yace "Zo mu tafi
asibitin."
Sun isa da dadewa. Sannan aka fito da Murja
daga dakin tiyata. Kowa a wajen zurun! Tunda haryanzu
bata farfado ba, duk suna tsaye bisa kanta.
Bayan wani dogon lokaci. Murja ta bude ido,
tare da fadin "Kalmar shahada. Tabi kowa da kalio. Sai
DA SANNU.... 107
hawaye ke zuba mata. Ta kama hannun Magaji tace
"Nawan, ka yafe min, mutuwa zan yi. Ina Gaje?
Dan Allah ki yafe min. Na nemi cutar da
rayuwarki, ga shi yadda abin ya koma min. Ki yafeni. Ba
zan tashi ba. Ina Mommy na da Daddy na? Yanzun zan
mutu, ban gansu ba?
Hajiya Safiya tace "Ki yi hakuri. Hakimi ya tura
a taho da su. Sun kusa zuwa suna hanya. Yanzu suka
bugo waya." Tana cikin lallashinta. Mommy da Daddy
tare da Direban daya je ya fada masu. Suka shigo. Suna
zuwa gabanta. Ta mika masu hannu. Suka kamata.
Dariya kawai ta yiwa iyayenta. Sai ta cika.
Da kalmar shahada. Allah ya gafarta mata. Ya
yafe mata kura-kuranta. Wato da Gaje ta ja dogon
salati, sai ta fadi sumammiya. Jini yana zuba.
Nan take Magaji ya kuma rude masu yana fadi
"Inna-lillahi-wa-inna-ilaihir-raji'una! Duk ni daya, lokaci
guda na rasa mata biyu. Da "Ya'ya biyu? Ya zan yi. Ni ma
zan bi su, na huta."
Da sauri Likitoci suka sa aka shiga masu da
Gaje. Suka fara bata taimako. Aka rirrike Magaji da
yake ta sambatu. Su Hakimi suka sa aka hada masu
Murja aka sakata mota, tare da Magaji. Aka bar Hajiya
Safiya da Auwalu jiran tsammanin Gaje.
Su Hakimi ba su dade da tafiya ba. Likitaya fito
ya sanar da Hajiya Safiya Gaje ta haifi 'Ya mace. Amma
wata bakwai ne. Amma duk da haka 'Yar tana da koshin
lafiyarta. Haka ma uwar 'yar. Lafiyarta lau. Kodayake
MAMAN FADILA 108
tana dai tare da damuwa ne. Amma a basu kwana biyu,
zata warware.
To yanzu dai kwana uku da mutuwar Murja. An
samu kwanciyar hankali. Ganin an samu Gaje da
bakwaini. Diyarta kamar ba bakwani ba, sun samu
cikakken lafiya. Sun yi kyau abinsu.
Ranan suna, saboda mutuwa, ba ayi wani
gagarumin taro ba. Amma duk da haka Naziyatu ta je
har Zariya ta sanar da tauraruwar marubuciyarta. Dan
ta gayyato mata marubuta ta jihar Kaduna, don su yiwa
jaririya da Murja addu'a. Ai kuwa tauraruwar tata, ta
garzaya,
KUNGIYAR MATA MARUBUTA LITTAFAN HAUSA
TA JIHAR KADUNA. Watau (WOMEN HAUSA NOVELS
WRITERS ASSOCIATION OF KADUNA STATE).
Sun kuma amshi gaiyatar tata hannu biyu. Dan
sun je mata. Sun dauki jaririya da ta ci sunan Murja.
Sun yi mata addu'a. Sannan ita ma Murja sun yi mata
Allah ya kai ladan kabarinta.
Gaskiya wannan Kungiya ta Marubuta. Sun
birge kowa a wajen. Su zama abin sha'awa a wurin. Abin
kallo. Shekaru biyu. Sai ga Gaje da tsohon ciki. Zaman
Gaje da Magaji, ya zama abin sha'awa ga kowa. Soyayya
mai tsafta suke gudanarwa.
Murja kuwa ta zamá tasu Nusaiba da Naziyatu.
In dai suna nan. To tasu ce su kadai. In kuma ba sa nan,
tana like da Hajiya Safiya, ko Auwalu.
Da Hakimi ne ba sa shiri, dan bata barin shi
sukuni, tana wahalar da shi. Dan haka suke yawan fada.
DA SANNU... 109
Shi da ita. lyayenta kuwa, ba ruwanta da su. Sal ta
kama.
Allah Sarki! Ga shi dal DA SANNU... Gaje,
Magaji ya zama nata. Ita daya, sannan kuma ga shiyau
ta kuma haihuwa Danta namiji, mal kama da uban shi.
Magaji yayi tsalle, yayi murna. Ya ci sunan Hakipi
Ibrahim.
To ita dama rayuwa. In har ka bi ta da sannu. Sai
ka samu duk abin da kake so. Amma da zaran ka ceza
ka nuna garaje, ko aikin gaggawa. To kwa za ka ga
garaje. Za ka iya samun abin da kake so na dan lokaci.
Daga karshe ka ga ba daidai ba.
To wannan karon ma an kuma gayyato manyan
Marubutan. Dan Magaji ya ji dadin irin addu'ar da suka
yi wancan zuwan. Dan ya gani a cikin kaset din sunan
Murja. Abin ya ba shi sha'awa. To ni dai ina gefe, ranan
sunan, ina kallon irin shigar alfarman da Anti Habiba ke
yi, dan ni ma ba zan ce Gajen ba yau.
Ihun da tsalle da na ga jama'an gidan sunan
suna yi. Suna fita waje. Shi yasa ni ma fita waje. Sai na
ga ashe manyan Marubutan ne, suka iso. To ni dal daga
nan, sai nayo hanyar garinmu.
Dan na sha wuya wancan zuwan nasu. Wajen
masu zuwa ganinsu. An