Gaje kamar daga sama ta zo wajensu,
suka kalleta sama da kasa. Suka tabe baki, sannan
Lante tace "Yau kuma kin ga daman fitowa ne? Ai mun
yi alkawari ba za mu taba binki gida ba, dan mu
tambaye ki ko mai ke hanaki shiga cikinmu ba.
Daga mun tambaye ki tsakaninki da Lamido, ta
hs kenan kike gudunmu. To kin dode ba ki daina shiga
.nıru ba" Su Kandala suka ce "Ke ma kika
NMANEADILA 22
saurareta, har ma kike mata bayani, sai kace in babu
ita, za mu daina abinda muke yi ne." Gaje na tsaye tana
jin su kawai, sai hawaye ya shiga gangaro mata a
kumatu.
Binto tace "Haba Gaje, daga magana, sai kuma
ki ka yi mana kuka? To kiyi hakuri." Gaje tayi ajiyar
zuciya tace "Ku ba ku san tashin hankalin dana
fuskanta bane da irin bakin cikin da nake ciki ba."
Suka ce "Ya zamu yi mu sani, tunda ba ki sanar
da mu ba." Gaje tace "Wai Lamido duk garin nan, ya
rasa wacce zai ce zai aura. Wai sai ni." Kandala tace
"A'uzubillahi, Lamido ya zama mijin aurenki. Da kuwa
kin yi asara babba." Binto tace "To yanzun Me gidanku
suka ce?
Gaje tace "Kin san Babana yaron Baban Lamido
ne, dan haka shi goyan bayan abin yayi sosai. Kuma kun
san Ummah bata da wani abun da ta isa tace akan duk
hukuncin da Baba ya yanke.
Komi rashin kyan abin, to amma duk da haka
dai tana dan tabukawa, sai dai na san zai yi wuya ta ci
galaba akan Baba. Ni dai yanzun kawai ku tayani
Addu'a. Allah ya kawo sauki akan lamuran."
Binto tace "Ai ko zamu tayaki Addu'a. To ke ma
ki dage ki koyi rashin mutumci, ki shiga karanta ma
Lamido, ba sansanci." Kandala tace "Ki gwada masa ba
ki kaunar shi." Lante tace "Balle ma ya sa ran za ki aure
shi."
DA SANNU... 23
Sannu ahankali watan Ramadan ya kama.Azumin yayi
nisa, dan har ya kai goma ga wata ma. Mata da Maza
kowa yana shirye-shiryen zuwa yin tashe, to su ma su
Gaje ita da kawayenta shirin tashen suka yi. Ga sunan
su shiga wannan gida, su fita wannan gida.
In sun ga jama'a zaune, su yi musu tashe. Sun
samu kyauttukan hatsi, babu laifi, abin ka ga kauye. Ba
sai nayi dogon sharhi ba. Su Gaje ba su samu kudi wajen
tashen ba.
Dan haka. Suka zauna, suka yi tunanin ina za su
je su samo kyautar kudi. Da duk suka gama tunanin
nasu, sai suka rasa inda zasu su samo kyautar kudi. Sai
suka yanke shawarar su ketara su tsallaka su je gidan
Hakimi su yi masa tashe, kila ya basu kudi, tunda
mutumin kirki ne.
To amma kuma ba zuwa gidan Hakimin ba,
kowa yana tsoru. Nan suka dunga muhawara, ko waye
zai ba da tashen in sun shiga gidan Hakimin? Tirkashi!
Daman haka yake. Wani lokaci mai hakuri kan yi saurin
kawo masa raini ba. Duk kowa ya ki yarda ya ba da
tashe a gidan Hakimi.
Sai suka sanya Gaje a gaba da nufin cewa ita
zata bada tashe a gidan Hakimi. Sai kawai suka dungu
ma, suka mika zuwa gidan Hakimi. Dan ba karamin
tazara ke tsakanin gidan Hakimin da cikin unguwarsu
ba. Suna isa bakin get. Masu gadi suka fara tambayarsu
abinda ya kawosu?
MAMAN FADILA 24
Cikin fargaba suka ce "Mun zo yin tashe ne? Da
yake Hakimi daman ya fada ma masu gadi, duk dan
tashen da ya zo, su bar shi ya shiga, musamman Hakimi
da iyalan shi suka yi shinfada ta alfarma, suka baje
tsakar gida suna sauraran masu zuwa yin tashe.
Ga akwati na mussamman gefen Hakimi. Kudi
ne cike cikinsa. Su yake rabawa duk wanda suka shigo.
Koda su Binto suka shiga, suka tsaya daga zaure.
Sai Gaje tayi shiru. Kandala tace "Ke fa muke
saurara. Kuma ba ma son ki mana wanda aka saba ji,
sabo za ki yi mana." Gaje tace "To ai ni ban iya ba."
Kandala tace "Dole ko ki iya." Gaje tace "To komi nace,
ku ce tautaushe." Gaje ta fara.
"Ina zamu kwana?
Suka ce "Tautaushe!
"Ina mazanku?
"Tautaushe!
"Ina matanku?
"Tautaushe!
"Ina 'Ya'yanku?
Tauttaushe!
"Allah ba ku, mu saти."
"Tautaushe!
Gaje ta gaji, ba ta ji ance ku zo ku karba ba. Ita kuma
bata da sauran wata kalmar da zata ce. Sai kawai ta ci
gaba da fadin:
"Gidanku da rowa."
"Tautaush....
DA SANNU... 25
......Ba su karasa ba, suka yi shiru, zasu gudu. Sai ga
"Ya'yan Hakimi su biyu mata Naziyatu da Nusaiba. 'Yan
biyu ne. Sun yi sa'an su Gaje, suka ce "Kai ku zo Hakimi
na kiranku? Ai duk sai suka tsure. Lante tace "Wallahi
ba ruwanmu."
Kandala tace "Gaje ke kadai za a a daure,
tunda ke ce kika ce ma Hakimi gidansa da rowa." Binto
tace "Dama mun sani, ba mu zo ba, ga shi kin ja mana
za a dauremu. Sai Allah ya saka mana." Ita dai Gaje
kwaba-kwaba tayi, kamar mai shirin yin kuka.
Su kuwa su Naziyatu da Nusaiba, in ban da
dariya, babu abinda suke yi, suka tasa keyansu Gaje,
suka gurfanar da su gaban Hakimi. Duk a tsuren.
Hakimi da uwargidan shi, suna ta dariya, yace "Ina
wacce ke ba da amshin tashen? Da sauri su Binto suka
nuna Gaje. Suka ce "Ga ta nan, mu babu ruwanmu."
Gaje ido ya raina fata, tace "Wallahi ba ka da
rowa. Ban iya bane, suka ce dole sai nayi. Ni kuma ina
tayi ba a kiramu ba, kuma in-har muka koma ba mu
samu kudi ba anan gidan.
Wallahi zasu yi ta yi min masifa ne. Su dunga jin
haushina, shine kawai na ji bakina yace gidanku da
rowa. Dan Allah ayi min hakuri."
Naziyatu tace "To ke ba kwayenki bane? In sun
yi miki masifa, ba sai ki dunga ramawa ba" Lante tace
"Ta rama me? Wacce kanninmu ma in sun yi mata ba iya
ramawa zata yi ba, balle kuma mu."
Gaje tace "Ni bana son tashin hankali, shi yasa
ba zan rama ba, gara kawai in kyale. Ba sai na rama
MAMAN FADILA 26
ba." Nusaiba tace "Kin ko kyautawa rayuwar ki, ina
amfanin tashin hankali. Wallahi ma kin zama kawata
daga yau." Naziyatu ta dubi Nusaiba tace "Ai sai ku yi ta
kyalewa, ni dai babu wanda ya isa ya raina min hankali,
na kyale shi.
Mahaifiyarsu, uwargidan Hakimi da suke
kiranta Hajiya. Tace "To ya isa haka nan, ba dogon
surutu mu ke so ba." Hakimi da ya rasa bakin magana,
ba ya ga murmushi da yake ta yi tun farkon fara tashen
Gaje.
Dan shi ba wai ya ji haushin abinda Gaje ta fadi
bane, dan shi mutum ne mai son raha sosai, kuma dama
tashe ya gaji haka. Ka ji mai ban dariya, ka ji mai ban
haushi. Dan haka shi Hakimi.
Gaje birge shi tayi, musamman dama ya ga ita
mai hakuri ce, ba mai son rigima bace. Hakimi yace
"Duk na ji bayaninki. Ya sunanki? Gaje ta fada masa
sunanta, yace "To da dai nayi niyyar na tura ku can birni
ne a daure min ku. To amma yanzun na fasa. Anan zan
sa a kulleku."
Gaba dayansu suka firgicewa Hakimi, suka
kuma yiwa Gaje ca da surutu. Hakimi yace "Ya isa haka
nan." Yana dariya, yace "Ina Gaje? Tana mutsu-mutsu
tace "Ga ni Hakimi."
Yace "To zo nan." Ya bude akwati, ya ciro kudi,
yace "Ke Gaje, karbi wannan dubu daya ce. Na ki ne ke
kadai. Kuma ga kawa kin samu anan gidan. Wato
Nusaiba. Tace tana son ki zama kawarta.
DA SANNU... 27
Dan haka kada ki damu, wannan kawance, mun
amince da shi, kuma duk lokain da kika ga kin shiga
cikin wani hali, wanda kike neman taimako, to ki yi
gaggawan zuwa, ki sanar da ni. Da yardan Allah in har
taimakon, bai fi karfinmu ba. Na yi miki alkawarin zan
taimaka miki."
Ya kuma ciro wasu kudin ya ba su Kandala. Dari
biyar-biyar ko wacce a cikinsu, yace "Korafi ya kare,
kada na samu labarin cikinku wata ta tayar da wannan
magana, komai ya wuce."
Nan suka yi godiya, kowa baki har kunni.
Hakimi ya sallame su. Nusaiba tace "Kawata, bari, na
taka miki, zuwa bakin get." Naziyatu tace "Ko ni ma da
bani da kawa a cikinsu. Sai na taka musu zuwa get din."
Koda suka je bakin get, suka yi sallama.
Sai Naziyatu tace ma Gaje "Gidanmu da rowa.
Bye-bye! Duk sai suka yi dariya. Su Nusaiba suka shige
gida da gudu. Su ma su Binto da gudun suka nufi
unguwarsu, suna murna. Kowa rike da kudin shi a
hannu.
ASALIN HAKIMI
Yaa gaji kujeran ne waje mahaifin shi da ya mutu.
Saboda ya cancanci ya maye gurbin mahaifin nasa, dan
irin kwazon shi, tun yana yaro.
Shi mahaifin Hakimi, kafin ya mutu. Shi Hakimi
ne a birni. Sai suka samu wata matsala da ainihin Mai
MAMAN FADILA 28
Martaba babban Sarki, bisa rashin biyayya da yayi a
cikin rashin sani.
To da yake duk inda sarauta ta ke, sarauta се,
kuma sarauta bata yarda da raini ko rashin biyayya ga
na gaba ba. Dan haka fada ta gargadi Hakimi da
ladabtarwa da ya koma Hakimin kauye. Shine aka turo
shi nan kauyen Yan Warin Daji.
Sarauta ba ayi mata musu, ko gardama. Sai dai
godiya, ko wane irin hukunci ta yanke maka, dan haka
Hakimi ya koma kauye da zama. Amma ban da iyalan
shi.
Sai dai yana yawan zuwa ya ga iyalan nasa, yа
koma. Babban Dan Hakimi a lokacin yana karatu e
jami'a, har ma ya kusa gamawa. Abin mamaki, koda ya
kare jami'arsa. Sai kawai yayi zaman shi tare da
mahaifin shi anan kauye.
Sai dai ya je birni, ya gaida mahaifiyar shi da
sauran dangin shi. A wannan lokaci ne abokin Hakimi ya
ba shi kyautar 'yar shi aure. Dan ya zauna da ita anan
kauyen. Hakimi duk da ya manyanta, haka nan ya karbi
kyautar 'yar abokin shi, ya aura. Suka zauna nan a
kauyen.
Allah ya hada jinin Ibrahim. Babban Dan Hakimi
da yake zaune tare da ubansa da matar uban nasa, dan
tana da kirki da biyayya. Dan Mahaifiyar Ibrahim har
nan kauye, ta kan zo ta ci zarafin Asabe amaryan
Hakimi.
DA SANNU... 29
Amma sam bata ko damuwa. Sun samu shekara
biyu, har yanzun Asabe bata haihu ba. Sai ga shi
kwatsam!
Allah ya bata shigan ciki, kuma lokacin shi ma
aka sha ruguntsumin shagalin biki Ibrahim. A birnin ya
auri yarinyar suka zauna nan tare da matar nasa a
kauyen, cikin gidan Hakimi. Kuma Allah yasa yayi dacen
mata, ita ma mai hankali ce. Dan haka zamansu yayi
daidai da Asabe, zama mai tsafta.
Wata rana mahaifiyar Ibrahim ta shiryo zata zo
kauyen, tayi ma Asabe halin irin nata, tsarin kishin da ta
iya. Dan kishi, tabbas akwai shi. Sai dai kowa da irin
nasa kishin, dan duk mace da tace bata kishin
kishiyarta. Karya take. Ni na karyatata, sai dai kawai
tace ni ba irin kishin wance da wancan na ke yi ba.
Ko kuma bana kishin zuwanta, amma ba zai
hana kishin mijinki ba. Dan ma fi yawanci mata, kadan
Mace tace tana son mijinta ya kara aure. To ba fa tace
bata da kishi bane akan mijinta.Jama'a ina son ku gane
haka. Namiji don ya kara aure, duk taimakon juna ne, ta
bangarori da yawa.
Kishi ke hanamu gane haka din, dan ya dauko
asali ne tun zamanin matan Manzon Rahama. To tunda
matan Manzon Rahama suka yi, mu su waye da zamu ce
mun fi karfin kishi? Sai dai 'Yan-uwa ku tuna, ku kuma
gane kishin matan Manzon Rahama, shi ya kamata mu
kwaikwaya, mu dan kwatanta. Ba kishi irin ntamu na
wannan zamani ba.
MAMAN FADILA 30
Kishin kafirci, ki zauna ke da kishiyarki, zaman
gaba, babu taimakon juna. Ki rika banbance Ya'yanki
da Ya'yan kishiyarki, a rika kishi na shedanci, kishin
jahilci da hauka da dabbanci. Dan Allah Yan-uwana
masu hankali, ku fahimceni.
Kada ayi mini wata fassara. Ace (Mrs. Abdullahi
Dan-fali). Tace kada mata su yi kishi akan mijinsu, ko
kuma ace nace bana tsoron kishiya. Ko ba ni da kishi.
To ina gudun kishiya ne, kuma ina tsoronta, in
har mai mugayen halaya ce, mai bin gidan Bokaye. Ban
fatan Allah ya hadani da irinta, koda dai na kan ji wasu
matan suna cewa, duk kyawawan halayyan kishiya, gara
dai babu ita.
To mu yi hakuri da addu'a. In Allah yasa zata zo.
Ya zama mai kyawawan halaye ne Allah ya bamu. Ba mu
dunga kiran za a kawo mana masifa da bala'i ba. To ke
mijinki ya tashi yin aure, ki na furta mijinki zai kawo
miki jaraba. Wacce zata rabaki da 'Ya'yanki da Mijinki,
to ba ke kika dunga furtawa da bakinki ba.
Dole ki ga kuwa ba daidai ba, in har kishiyar ta
shigo. Mu daina kiran ma kanmu alkaba'i da sharri,
gara mu dunga kiran ma kanmu alheri. Sai abin ya zo
mana da sauki.
Haka kuma ni (Mrs. Abdullahi Dan-fali). Ina da
kishi sosai. Ina kuma addu'a kullum kishina, kada ya
kaini ga kauce hanyar gaskiya, ya jefani hanyar karya.
Kada kuma kishina yasa na biyewa sharrin
zuciya. Ina fata kishina, in yi koyi da kishin Matan
Manzo Muhammad (S.A.W.).
DA SANNU... 31
Dan haka mu guji rudin zuciyarmu. Na dai san
wanda suka yi nisa a kishi. Suna nan suna min dariya,
da tsaki, suna dai karantawa ne kawai.
Na cika su da surutu kawai. To ayi hakuri. Muna
da kanni da Ya'yan da ba mu aurar dasu ba. To dan
Allah 'Yan-uwana da ba su yi aure ba, kada ku yi kishin
da za ku kaucewa hanyaа.
Ku yi koyi da Matan Manzon Rahama. Wanda
kuma suka yi auren, suke da irin wannan tsananin
kishin na kafirci. Mu dunga yi musu addu'a. Allah ya
ganar dasu, don ance wandada suka yi nisa. Ba sa jin
kira. To Allah yasa ni dai su ji kiran da nayi musu, ba dan
na isa ba.
Koda oda mahaifiyar !brahim uwar gidan Hakimi, ta fito
dan zuwa kauye 'Yan Warin Daji. Motar da mahaifiyar
Ibrahim ta shiga, ta fada hannun bata gari ne masu
satar mutane. To ashe kuma an sami sabanin tafiyar da
shi ma Hakimi ya nufi birnin, dan ya ga saùran iyalan
shi.
Koda ya isa, suka fada masa. Ai ita ma ta tafi
can kauyen. Sai kawai ya dan yi wasu lalurorin ya koma,
koda ya je, ya ga bai ganta ba. Sai ya tambayesu, ko ta
zo nan? Suka sanar da shi ba ta zo ba. Abu sannu-sannu
har gari ya waye bata, ba dalilinta. Sai Ibrahim ya shirya
ya tafi birnin. Tirkashi!
Wasa, sabon girki. Da Ibrahim ya isa garin. Nan
hankalin kowa ya tashi. Nan aka ba za rahotannin
MAMAN FADILA 32
nemanta, ko ina birni da kauye. Amma ina! Kwana
bakwai. Shiru, wata daya shiru. Daga nan Hakimi ya
kwanta ciwo, saboda tsananin damuwa da tunani.
Ciwon da bai tashi ba kenan. Sai makwancinsa.
Gidan gaskiya. Ya Allah ya gafartawa tsohon Hakimi. Ita
kuma mahaifiyar Ibrahim, har yanzun babu wani
kwakkwaran labari a kanta.
Kanni Ibrahim da suke can birni wajen Hakimi
mai rasuwa. Shi ya ci gaba da rikonsu. Kullum suna
addu'a. In mahaifiyarsu tana raye. Allah ya bayyana
musu ita.
Ita kuwa Asabe ta ci gaba da zama tare da
Ibrahim, har ta haifi Danta namiji. Aka mayar masa da
sunan Hakimi Abdullahi. Suna kiransa Magajin Hakimi.
Koda Asabe ta ga ta haihu lafiya.
Ta so ta koma wajen iyayenta. Amma Ibrahim
yayi ta rokon tayi hakuri, har sai ta samu wani mijin. Sai
ta bar gidan. Mussamman ya je ya roki iyayenta suka
amince da haka din. Cancantar Ibrahim da dacewar shi,
yasa aka nada shi. Ya ci gaba da zama Hakimi.
Kwanci tashi, babuwuya wajen mahaliccinmu. Asabe
tana yaye Magaji. Ta samu miji a birni. Aka daura mata
aure, ta koma can birni gidan sabon mijin ta, ta bar wa
Hakimi Ibrahim Danta Magajin Malam.
Saboda irin shakuwar da suka yi da Ibrahim da
matar shi Safiya, tana samun matsala da zaran ta dauki
ciki. Sai ya bare.
DA SANNU... 33
Suna ta dai faman zaryan Asibiti, dan haka
gaba dayansu suka kwallafa rai akan Magajin Hakimi.
Suna gwada masa kauna da soyayya, dan haka suka сі
gaba da rainon Magajin Hakimi. Bai san kowa ba, sai
su. Har ya kai shiga makaranta. Aka sa shi. Yana
(Primary 3). Allah ya ba Safiya ciki.
Ya zauna. Har ta haife shi. Da namiji, ya ci
sunan Auwalu. Har Auwalu ya gama (Nursery). Ya shiga
(Primary). Sannan Allah yasa Safiya ta haifi tagwaye,
duka mata. Naziyatu da Nusaiba.
Ga shi yanzun halin da ake a ciki Auwalu yana
shekaran shi na karshe a (Secondry). Nusaiba da
Naziyatu suna (J.S 3). Duk sun dawo gida hutu ne. Yayin
da Magajin ke can birni yana digirinsa. Su Naziyatu
suna da Kanni uku. Yakubu, Amira. Sunan mahaifiyar
Ibrahim. Sannan Jamilu. Shine auta. Rayuwar gidan
Hakimi a yanzu.
Rayuwa ce mai kyau, mai tsafta, mai tattare da
adalci da kaunar talakawa. Babu kyama a tare da iyalan
Hakimi. Kowa nasu ne. Cikin gidan Hakimi babu mai
tsiwar Naziyatu, tana da kirki, tana da masifa sosai.
Haka kuma, duk cikin gidan Hakimi, babu mai hakurin
Nusaiba, bata da fada, ko kadan.
Yayin da Auwalu safgar gaban shi kawai yake.
Haka su Yakubu da Jamilu. Ita kuwa Amira rigima ke
damunta da shagwaba. Ita uwar masu gida. Yayin kuma
da Magajin Hakimi ya gaji mai sunan, dan ya tsare gida.
Dan gaba daya gidan, in har Magajin Hakimi ya
yanke hukunci, babu wanda ya isa ya ja. Duk wani iya
MAMAN FADILA 34
shegantaka, babu wanda ya isa yayi shi kusa da
Magajin Hakimi.
Gaba daya gidan Hakimi da Hakimi suke kiran
Ibrahim. Ita kuma uwargidan Hakimin, suna ce mata
Hajiya. Magajin Hakimi yana matukar kaunan Dan-uwan
shi Hakimi.
Duk wani abun da zai yi, ya batawa Hakimi rai.
To ya na saurin kauce ma abin. Duk kuma abinda zai yi
ya faranta ran Hakimi. To yana sauri yayi shi.
Gajeaje fa ta dauki shawaran su Lante, dan tana ta
turzawa, tana nuna ma Lamido ya rabu da ita. Abinda
yake ba Lamido mamaki sosai, irin yadda Gaje ke masa.
Wata rana da yamma ne. Binto da Kandala sun
dawo talla. Lamido ya tsaresu, yace "Kai, ku dakata
anan. Duk wace ta jirga daga nan. Sai ta gane kurenta."
Nan fa suka tsaya cak! Suna kyarma, har ya zo
ya samesu. Shi da abokan shi guda biyu. Lamido yace
"Ku dan ubanku, ku ne kuke koyawa Gaje rashin
mutumci, ku ke zugata ko? Na samu labari. Yau ubanku
zan ci, in yaso ku sake. Ni kuma ba zan fasa karta muku
rashin mutumci ba. Ni dama ba mu gaji mutuncin ba."
Duk suka yi narai-narai da fuska, zasu yi kuka.
Lamido yace "Duk 'yar da yarda, shegiyar na ga kwaran
hawaye bisa fuskarta, to....
'Yan koran Lamido da suke tare, suka ce "Kawai
oga, ba sai mu afka musu ba, tunda sun yi mana rashin
DA SANNU... 35
mutumci. Mu ma mu yi musu. Shegu, kananan
munafukai."
Lamido ya daka musu tsawa, yace "Na sha fada
muku, bana son ku dunga cewa zaku fadawa yaran
kauyen nan namu. Yanzu abun da nake so da ku, shine
ga wani fashashen galan can da kwano, ku dauko ku yi
ta yin musu kida, suna rawa, har sai sun gaji."
Masu nema a duhu. Nan suka shiga doka musu
kida. Lamido na rike da tsumagiya. Haka su Binto suka
rinka cashewa, sai ka ce mahaukata. Da zaran sun nemi
su huta. Lamido zai daga tsumangiya.
Lamido bai rabu da su ba, sai da ya ga sun yi
tubus! Sun yi zufa sosai. Sannan yace "Kai, in na kirga
goma, ku bace daga nan. In kuma ba haka ba, na sa a
kamo min ku, na sake muku wata tarbiyyar."
Su Binto da suka zamiye takalmansu, suka
rantaya da na kare, ko waiwaye basu yi ba, suka nufi
gidan iyayensu. Lamido ya je ya samu mahaifin shi, yana
zaune yace "Baba ina son na sanar da kai. Ni fa na
samu diyar da nake son na aura."
Dakaci yace "Alhamadullahi. Haka nake so.
'Yar gidan uban waye yarinyar? Lamido yana wani daci,
ya kwaba fuska, sai kace Biri, yace "Ba 'yar kowa bace,
face 'yar mai unguwa Dan-tani."
Dakaci yace "To shi kenan, daman Dan-tani ya
zo yayi min bayani, na ce masa babu abinda na ji. Sai in
har kai ne ka yi min bayani da kanka, shine zan yarda.
To yanzun kamar yaushe kake da bukata a daura muku
aure?
MAMAN FADILA 36
Lamido yayi mika, yace "To ni Baba, in dai son
raina ne, ai ko nan da kwana bakwai." Dakaci yace
"Haba Lamido, cikin azumin? Lamido yace "To menene
Baba?
Allah ya haramta yin aure a watan azumi n?
Dakaci yace "A'a Allah bai haramta ba. Halas ne, sai dai
kawai dan dai baki a bude, za a fi sakewa, yadda ake
so."
Lamido yace, "A kuma ji dadin yin bidi'o'in, shi
kenan, babu matsala. Ni ma kaina na san dole ne mu yi
bidi'o'i kala-kala. Da waskewa.
Ba komai, bayan sallah ko ad kwana bakwai sai
a daura mana auren." Lamido koda yake tantirin Daл
iska ne, amma duk da haka yana da ilimin
Muhammadiya da na boko, wanda ba a rasawa.
****
Gaje da mahaifiyarta sun saki jikinsu sosai, dan tunda
Dan-tani yaje wa Dakaci da maganan Gaje da Lamido.
Dakaci ya gwale shi, dan yana ganin Dan shi ya fi karfin
Gaje.
Karya yake fada masa, sai shi ma Dan-tani ya
watsar da maganan, bai kuma cewa kowa komi ba. Shi
kuma Lamido tunda ya ci uban kawayen Gaje. Bai kuma
kula Gaje ba, balle ya zo wajenta.
Rashin sani dalilin hak,a yasa suke ganin maganan
ta mutu. Ba zai yuwu ba, shi yasa suka saki ransu, basu
ko tunani. Kwatsam! Dan-tani ya shigo da dariyarsa
yace "Lantana, anjima bayan an sha ruwa, gidan Dakaci
DA SANNU.... 37
zasu kawo goron sa ranan Gaje da Lamido. Dan haka ki
na iya sanar da danginki, dan su zo, a sa ranan dasu."
Gaje da karfi tace "Ummah na shiga uku! Ya zan yi?
Wallahi gara na mutu.
Da na auri Lamido." Dan-tani yace "Don uwarki
za ki mutu. Daura aure tsakaninki da Lamido, babu
fashi, dole ayi shi." Ya kai mata duka.
Lantana ta kare, tace "Wallahi Maigida. Allah
zai tambayeka hakkinmu, muddin ba ka canza
halayyarka ba. Ya za'ayi yaron da bai da tarbiya, bai san
mutumcin kowa ba, ka ce shi zaka hada aure da 'yar
cikinka? Gaskiya ba ka yi mana adalci ba. Allah ya
ganad da kai."
Dan-tani yace "Na ji ban da adalci. To amma in
dai kan wannan auren ne, sai dai kada na taba yin
adalcin. Marasa fahimtar gaskiya Ni dai na gama
magana, babu canji, dole abi yadda nace." Yasa kai, ya
fice gidan, yana sababin da ya saba.
Lantana tace "Ai kuwa in dai akan maganan
auren nan ne, ba zamu taba fahimtar gaskiyarka ba."Ta
kama Gaje ta rungume tana lallashinta "Ki yi hakuri
Gaje, babu yadda zamu yi da halin mahaifinki, dole mu
yi biyayya a gare shi. Mu dunga masa addu'a. Allah ya
ganad da shi, ya kuma zaba mana abinda zai zama
alheri a garemu."
Gaje tana hawaye, tace "Ummah na shiga uku!
Ni ce zan zama matar Lamido? Ni ba zan iya zama da shi
ba. Ni dai ki san yadda za ku yi da ni. Wallahi gara ku
aurar da ni ga kowa da dai ace Lamido nake aure."
MAMAN FADILA 38
To kamar yadda Dan-taniyayi niyya, ya kuma so.
To haka ta kasance. An raba goro. Makwabta da dangi
na kusa da na nesa, ciki har da Hakimi duk sun halirci
kofar gidan mai unguwa wajen sa ranan Lamido da
Gaje.
Bayan sallah da kwana bakwai. Ti-ki-Sa! Gaje
ta shiga cikin halin kaka nika yi, domin Gaje ta fito daga
gida, ta nufi inda suke zama ita da kawayenta suna
tauttauna abin da ya damesu. Gaje ta tafi, domin samun
shawaran kawayen nata. Abin mamaki kawayen Gaje
suna hangota, duk sai suka tarwatse.
Gaje tana fadin "Ku tsaya mana, lafiya kuke
gudu? Lante dan Allah ke ki tsaya." Lante tace "Allah ya
tsareni, na tsaya. Abin da ya samu su Binto.
Ni ma ya sameni. Lamido da abokin shi. Su
tsareni, ai ki yi hakuri kawai. Allah ya baku zaman
lafiya."Tana fadin haka, ta kara da gudu. Gaje ta tsaya
tana tunanin maganan Lante. "Me su Lamido da abokan
nasa suka yi ma su Binto da bani da labari?
Wata sabuwa! Gaje bata koma gida ba, sai ta
nufi gidan su Kandala, tayi sa'a ta sameta. Da yake
daman ita bata je inda suke zaman ba, bata san abinda
su Binto suka yiwa Gajen ba. Yanzun anan ma Gaje bata
fada mata ba. Sai ta fara fada mata matsalar da take
damunta.
Kandala tace "Gaje ki je ki rungumi kadaran da
Allah ya dora miki, kin ga duk mun sa abin da yake
faruwa dake, kuma Wallahi dukanmu muna jajanta
DA SANNU... 39
miki, ba kuma mun rabu dake bane akan wannan auren
naki da Lamido ba, sai dan ba mu da yadda zamu yi ne.
Muddin muna son mu tsira da mutumcinmu.
Wallahi in ba dole ba, ko hira ba ma son ta hadamu da
ke. Saboda muna gudun kada Lamido ya kuma cin mana
mutumci. Da kyar muka sha.
Nan gaba in har ba mu ba mu yi hankali ba,
muka kuma shiga hannun Lamido. To Allah kadai ya san
yadda zai yi da mu. Ki dangana kawai."
Gaje ta dafa kirji, tace "Wai mai Lamido yayiu
muku ne? Kandala duk ta kwashe yadda suka yi da
Lamido da abokan shi, ta fada mata. Gaje tana hawaye
tace.
"Ku yi hakuri, ni na jawo muku. Ki ba Binto
hakuri. Ni zan hakura na ci gaba da harkokina na daya.
Kuma Allah zai saka min, tunda haka kuma ya bullo, dan
ya rabani da kawayena." Gaje sosai ta ci gaba da
lallashinta, ita ma har tana zubar da hawaye. Tana bata
hakuri.
Haka rayuwa ta kasancewa Gaje. Bata zuwa
ko'ina, tana gida. In Lamido ya aiko kirata, ta ki fita. In
mahaifinta na nan ta fita, tana guna-guni. Da sassafe
Gaje tana ta juyi bisa gadon bononta, ta kwana cikin
bakin ciki, ta tashi cikin shi. Ta rasa tudun dafawa. Yau
saura kwana uku sallah.
Ita kuma saura kwana goma bikinta. Zuciyarta
na bata shawaran ta gudu. Amma sai tayi tunanin gudun
bai da amfani. Wata zuciyar tace bayan an daura mata
aure da Lamido, ta mamaye shi ta kashe shi.
MAMAN FADILA 40
Nan na ta tuna haduwarta da mahalicinmu.. Ta
rasa mafita. Sai kawai ta tuno da Hakimi, wanda take
ganin shine ya isa da kauyen baki daya.
Dakaci ma a karkashin Hakimin yake, dan haka
ta san Hakimi yana da ikon ya takawa Dakaci birki,
akan aurenta da Lamido. Kuma dole yasa Dan shi
Lamido janye. Haba ai wannan tunani yana zuwa mata.
Gaje bata san lokacin da tayi zunbur ta mike ta
nufi kofar