Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
gida ba. Lantana dake tsakar gida tana dama salala. Fadi tke "Ina za ki? Ba dake na ke magana bane." Amma ina, Gaje bata san tana yi ba, ta riga ta mika. Nusaiba tana bakin get, tana magana da wasu yara, ta hango Gaje da gudu ta nufi wajen Gaje. Tana fadi "Oyoyo kawata. Daga ina haka? Ko dammara babu, ballantana gyale." Gaje tace "Ke dai kawa, ko ma yaya ni za ki ganni. Na zo na ga Hakimi ne. Ya taimaka min." Nusaiba tace "Wane irin taimako ne, in baifi karfina ba, na taimaka miki? Gaje tace "Wannan taimakon ya karfinki, ke dai kawai ki kaini na ga Hakimi. Taimakon da za ki iya min kenan." Nusaiba ta kama hannunta ta ce "Allah ya kyauta, mu je na kaiki." Koda suka karasa cikin gidan, suka shiga dakin Hajiya suka sameta ita da Naziyatu. Tun kafin su karasa sallama. Naziyatu ke fadin "Gidanku da rowa. Ke ce da safen nan, ko (Break fast) ba mu yi ba." Nusaiba tace "Ke ce kika san wannan. Hajiya kin ga daga shigowarmu, bata bari ta ji dalilin zuwan ba, zata fara DA SANNU... 41 ko? Ke fa 'yar rainin wayo ce, ce miki ta yi ta zo ta yi (Break fast) anan gidan? Gaje tace "Kawa wai mai take cewa ne? Na zo nan gidan ba ku yi ba." Nusaiba tayi murmushi tace "Rabu da ita, wai cewa tayi ke ce anan gidan ko wanka ba mu yi ba. Kin san ita 'yar kwalliya cе." Gaje tace "Ai don ma ku ne, mu ba sai ma kwana biyu, ba mu yi wanka ba. Sai dai in za mu je dandali ko talla, mu wanke fuska da kafa, mu yi kwalliya. In kuwa mun yi wanka da sassafe, to sallah ne, ko biki. To amma yanzun menene abin surutu, dan na zo baku yi wanka ba. Shine ta damu? To ayi hakuri." Hajiya da ke jinsu, tana dariya tace "Rabu da ita Gaje, ita ma iya yi ne. Sai fa ta kwana bakwai bata yi wanka ba." Naziyatu tace "Kai, kai Hajiya, to Allah zan fasa kwan." Duk suka yi dariya. Hakimi ya shigo yace "Amira ta zo tace min ga gidanmu da rowa nan, ta zo. Shine na taso da kaina in tabbatar." Nusaiba tace "Zuwan kuma taka ce ba." Hakimi ya nemi waje ya zauna yace "Ni kaina? To duk ku tashi ku ban waje." Hajiya tace "Har ni? Yace "Dukkanku na ce." Duk suka mike, suka kama gabansu, suna dariya. Gaje tace "Ai dama ka rabu da su, duk daya ne. Babu komi." Hakimi yace "To 'ya-ta, ina sauraranki, me ke tafe da ke? Gaje ta mutsuke idonta, ta fara magana, tana kuka. Duk anan ta zaiyanewa Hakimi duk halin da take ciki. Tana gama zaiyanewa masa, ta kuma rushewa MAMAN FADIL.A 42 da kuka. Hakimi tunda Gaje ta fara masa bayani yake tausaya mata, saboda Hakimi yana da tarihin Lamido. Yana kuma samun labarin irin halayyar mahaifin Lamido Alhaji Bara'u. Dan yana matukar taka ma Alhaji Bara'u birki, akan wasu aiyukan, yana takura masa saboda irin kararrakin da mutanen gari ke kawo masa, na Dakaci. Hakimi ya bude baki ya fara lallashinta "Ki yi shiru, ki daina kuka. Yanzun mai kike so ayi miki akai? Gaje tace "Hakimi, dan girma irin naka da adalci, da karama da bin hakkin kowa, ka taimaka min, wannan aure ka hana. Ka ceto rayuwata daga fadawa cikin mugun yanayi da bala'in rayuwa, ka taimaka min. Wailahi ko wanene, ku canzar min, zan amince na aure shi, пa zauna da shi lafiya. Ni bana kaunar Lamido Dan Dakaci." Hakimi ran shi a bace, yace "Gaje diyata. Ni Hakimi na san ina da ikon da zan iya sawa Lamido ya janye hatun aurenki. To amma kada ki manta, kin ce in sa adalci irin nawa, in har na rushe maganan aurenki da Lamido. Ban yi masa adalci ba, ki yi tunani, aure fa sunnan ma'aiki ne. Ya za ayi na zama mai rushe Sunnar Manzon Rahama? Gaje ni kaina bana farin ciki da wannan aure na ki da Lamido, ko lokacin da na zo wajen sa rananku, ban yi farin ciki ba. Kuma ni ban san haka abin naku yake ba a lokaci da ba za a kai ga sa muku rana ba. DA SANNU .... 43 To amma bakin alkalami ya bushe. Ki yi hakuri. Allah kadai ya san dalilin hada wannan aure naku da yayi. Allah ya kadara shine mijinki, kuma kila wannna daman ita ce Allah ya kaddara sanadiyar shiriyarsa. Kada ki damu da halin shi, ki zama mai biyaya ga zabin iyayenki, ki zama mai dauriya da halin da iyayenki suka sakaki, ki yi biyayya ga mijinki, ki zama mai tattalin shi da ba shi dukkan hakkin shi na aure, ki zama mai kulawa da duk abinda yake na shi ne. Yin haka gare shi, sai ki ga Allah yasa ya karkato gareki, duk wasu mugayen halayyen shi, sai ya daina. Ki sa dangana, ki yi hakuri, ki zama mai runguman kaddara Allah mai kyau da mara kyau. Da zaran kika yarda da hakan, ba za ki taba tabewa ba, sai kin ga Allah ya musanya miki. Gaje ina son ki yi min alkawari. Daga yau din nan za ki yi hakuri da wannan kaddaran aure da Allah ya daura miki, ba za ki kuma bata ranki ba. Kuma ki bi umarnin iyayenki, ki kuma yi biyayyar aure wajen mijinki. Ki yarda Allah ne ya hadaku, in har kika yi min haka, ki ka daukar min alkawarin nan Gaje, ba karamin jin dadi zan yi ba. Zan kuma kasance kullum cikin miki addu'a da fatan sauyi mai kyau." Gaje tana hawaye tace "Na hakura da kaddaran Allah, kuma zan so zabin nasu. Sannan kuma na amince da duk abin da ka fada min, nayi maka alkawari, daga yau na yarda da aurena da Lamido." Muryarta na rawa ta fadi. Lamido. MAMAN FADILA t Ta ci gaba "Na kuma gode da irin shawararka da nasiharka gareni. Da kuma kaunar da kuka gwada min, kai da iyalanka, ban taba mantawa da ku. Ni zan koma. Babu wanda ya san inda na je a gidanmu." Ta share hawaye. Tirkashi! Tsananin birge Hakimi da Gaje tayi. Yasa shi ya dunga sa mata albarka, yana yaba mata da irin mutunta shi da tayi, ta kasa yin masa musu. Yace "Gaje diyata, ina son in kin koma gida, ki sanar da iyayenki, ni Hakimi nace ko tsintsiya kada su saya. Gaba daya komi na amarya, tun daga jere da gara. Ke komai ni na dauki nauyin zan miki shi. Saboda jin dadin biyayyan da kika yi min, wanda ki 'yar da na haifa, sai haka. Wata 'yar tawa ma, ta yuwu ta ki yarda da abinda na fada miki, tashi ki je gīda. Gobe zan ma zan tura a zo min da mahaifin naki." Hakimi yace Direba ya mayar da Gaje gida. Tace "A'a bata son a san ta zo nan. Hakimi yayi mata alkawarin koda mahaifin nata ya zo, ba zai sanar da shi ta zo ba. Nusaiba ce kadai ta raka Gaje har bakin get. Suka yi sallama ba tare da Nusaiba ta kurma tambayarta ba. A gidansu Gaje Dan-tani Mahaifinta ya rufe Lantana mahaifiyarta da ruwan bala'i da masifa. "Abin da za ku yi min kenan, ki daurewa yarinya ginoi ta gudu. DA SANNU..... 45 To bari ki ji, ki ma yi shiri ke ma duk inda kika tura min 'ya, to ki tabbatar kin bi ta, kun dawo tare. In kuma ba ki ganta ba, ke ma ki shiga duniya. Kada ki dawo nan. Dan za ki ga tijara da tozarta da gara ke ma ki shiga duniyar." Lantana ta bude baki zata yi magana. Dan-tani yayi mata tsawa, wanda karfin tsawan ne ya ji shigowar Gaje da gudu a firgice, saboda bata san dalilin yin tsawar mahaifin nata ba. Lantana ta rungume ta tace "Alhamdulillahi. Ina kika je ne? Nayi ta magana, kafin ki fita, ba ki saurare ni ba? Gaje tace "Mun yi alkawari ne da Lamido, mu hadп ni da shi da safe. Ban san dalilin da yace min haka ba. Ni ma na dauka ya sanar ne." Dan-tani dake gyara baki, yana shirin wani sabon masifa. Ai da ya ji abin da Gaje ke fadi, sai ya fasa, ya shiga washe baki, yana fadin "Ai babu komi. Ba Mijinki bane? Tuncla an sa muku rana, ba gara da kika je ba. Kun hadu dai ko? Gaje tace "Na yi ta zaman jiran shi, bai zo ba, shine na gaji na dawo gida. Dana ga rana tayi sosai." Dan-tani yace "Me yasa kika dawo? Gaskiya ba ki yi daidai ba, sai ki koma ki ci gaba da jiran zuwan shi, ko zai kai dare, ai kya jira shi. Zan sayo abinci in kawo miki, ki sarıar da ni wajen." Lantana dake tsaye ta rasa shin lafiya kuwa Gaje take da har Lamido zai bata uzuri, kuma ta bi? MAMAN FADILA 46 Sannan kuma duk ba wannan ba, wai ta koma ta ci gaba da jiran Lamido. Dan haka Lantana tace "Gaskiya Maigida ka yi hakuri kawai, tunda yarinyar nan ta je, bai zo ba, babu amfanin ta koma, babu inda zata koma." Ta kalli Gaje, tace "Ke wuce daki, ga kayanki can ki dauka, ki shiga da shi ciki." Dan-tani yace "Ke јe ki daki, babu komai, ai yanzun gaskiya tayi halinta. Na san inda nake samun baraka, mai ruguje min shiri. Na san dai kin ji kunya, kuma aure babu fashi. 'Yar bakin ciki. Sakarya kawai." Ita dai Lantana bata ce masa uffan ba, har ya fice gidan. Sannan da sauri ita ma ta shiga dakin da Gaje ke ciki, ta na zaune tana tunani. Lantana tace "Haba Gaje, me yake faruwa da ke ne? Abin da kika fada mana, ba gaskiya bane, ki sanar da ni inda kika je? Uwa ta gari kenan. Da ta san mai take yi. 'Yarta ta zo mata da maganar karya. Ta yi saurin fahintarta, kuma ta tsaya cikin lumana ta kama bincike, bata yi zage-zage ba. Ita dole karya aka fada mata. Dole a fada mata gaskiya. Tafdijan! In dai 'Ya'yan yanzun ne, za ko ki yi bindi, don Wallahi tsiyarki da bala'inki ba su isa ba, sai dai su kara zurmaki. Lantana yadda ta bullowa Gaje cikin dabara da lumana. Shi yasa Gaje zayyanawa mahaifiyarta duk abinda ya faru tsakaninta da Hakimi, tace Amma don Allah kada mahaifiyar tata ta sanar da mahaifinta. Gaje tana hawaye, ita ma mahaifiyar tana hawaye. DA SANNU... 47 Gaje ke fadin "Ummah na hakura da kadaran da ta sameni. Na yarda da nasihar Hakimi, ya zan yi? Na dangana." Lantana tana lallashinta, tana tausaya mata, tana mata addu'a. Allah ya musanya mata da ma fi alheri. Haka ake so, a koyaushe, mu iyaye mata mu kasance cikin yiwa 'Ya'yanmu addu'a da fatan alheri. Sai komi ya dunga zuwa ma 'Ya'yanmu da sauki. Allah sa mu dace, amin. Alllah sarki! Gaje ta koma rayuwar sai yadda Allah yayi da ita kawai. Tsakaninta da Lamido, babu yabo, baku fallasa. Ita dai ga ta nan, tana shawara, ta saduda haka nan suka ci gaba da hada-hadan sallah da na biki. Kowa a garin yana mamaki, irin tawakallin da Gaje tayi. Sai labari abin ake a boye. Labarin abin ake a boye, labari har kunnen Hakimi. Hatta iyalan gidan Hakini da yake basu san komi akai ba. Don Hakimi bai sanar da su ba. Da labarin ya iskesu. Sai suka tausaya ma Gaie, duk da dai ana raderadin wai asiri Dakaci ya yiwa Gaje, ta so Lamido. Koda aka yi shagulan sallah, aka gama. Sai Hakimi ya nemi Dakaci da Dan-tani. Suka gurfana gabansa. Suka dan yi korafe-korafe akan wasu 'yan abubuwan da ba'a rasa ba. MAMAN FADILA 48 Da suka je birni wasan sallah. Su ce dawakan Hakimi can garin, sun yi barna. Su ce Yarima wane, bai yi mana adalci ba. Kai ga dai su nan. Abinka da marasa godiya. Hakimi dai ya kwabesu, yace komi ya wuce "Ku jira babban sallah. Kuma yanzun abin da yasa na taraku, shine na ga bikin yaranku ya zo, dan haka nake so kowa na ba shi gudunmawata." Ya ciro makuden kudade wanda ni dai ban fahimci ko nawa ne ba, saboda yawansu. Ya mikawa Dakaci, yace "Allah yasa ayi wannan aure da mu." Sannan ya dubi Mai unguwa Dan-tani, yace "Kai kuma taso mu je. Na baka taka gudunmawar." Suka mike dukkansu. Suka bi Hakimi a baya. Suka isa wani gareji. Hakimi yayi umarni aka bude kayan alatu ne, na zamani kala-kala na dakin amarai, har da su garan abinci. Ni dai da yake malamaciya ce, ina da son jiki na da yawa, tunda na kyalla idona hango kayan da ke cikin garejin nan. Sai na ja da baya, na koma gafe ina tunanin inda zan dosa? Dan gaskiya ba zan iya shiga cikin garejin nan ba, in ce zan iya zaiyane muku abin da yake ciki ba. Sai kawai na nufi Lamido. Yana can cikin gona shi da abokan shi, suna zukan taban wiwi. Da yake ni din ma jaruma ce, sai na kutsa ko shakkar kada ta bugar dasu. Su dankeni. Wai wa ya ga DA SANNU... 49 A'isha a hannun kauraye? Ai sai dagewa da addu'a kaw.. Can kuwa ta fara aiki. Lamido yace "Kai Bayo, ya ka ganni ranan biki? Nan Bayo yace "Akwai aiki dai barna daya fi na sallah da muka yi." Wani kuma a cikinsu yace "Gaskiya fa da sallah nan mun yi barna." Lamido yace "Na bikina, sai ya fi haka." Bayo yace "Sa'a dai, sa'a dai." Lamido yace "Haka nake sonka, kai ma za ka sha romon amarya. Darenmu na farko." *** DA SANNU..... Bata hana zuwa. Sai dai a dade ba aje ba, ga shi dai gobe daurin auren Gaje da Lamido. Ana ta shagulguan biki. Hakimi ya aiko Dakaci ya zo da sauri yana nemansa. Abin mamaki, koda Dakaci suka isa gidan Hakimi. Motar 'yan sanda (Police) da ya gani kofar gidan, shine ya dan sosa masa zuciya. Abinka ga, mara gaskiya, suna zuwa gaban Hakimi, suka tarad da 'yan sanda su uku zaune gaban Hakimi. Ga kuma guda uku tsaye a kansu. Dakaci ya tsuguna yayi gaisuwa, gaban Hakimi. Ya koma ya zauna. Hakimi yace "Dakaci an samu matsala a birni wajen yin bikin sallah. An samu barna sosai, kuma ana ganin da su Lamido a ciki. Dan haka yanzu za a tafi da Lamido can birn. (Police Station). Dan ayi masa wasu tambayoyi. Da zaran şun gama, zai dawo, kada ka damu, ku ci gaba da hidiman bikinku, babu fashi. Ka tashi ku je, MAMAN FADILA 50 ka kai su su tafi da shi. Ni ma daga baya sai mu bi su. Insha-Allahu babu wata matsala." Tirkashi! Gaje da kawayen ta suna can bakin kogi sun je yawon gudu. Sun dawo, sun tsaya wanka cikin kogi. Da gudu Lawal ya iso yana haki, yana fadin "Gaje 'yan sanda da yawa a cikin mota, sun tafi da Lamido can birni." Kandala tace "Ka san abin da kake fadi kuwa? Binto tace "To menene sabo? Yau aka fara." Lante tace "Ku ba su awa daya, in ya dade za ku ga ya dawo." Gaje da tayi zugum! Tana sauraransu da kyar ta bude baki, tace "Ku duk ba wannan ba. 'Yan sandan birni ne aka ce sun tafi da shi fa." Gaba dayansu, sai duk jikinsu yayi sanyi, suka hada komatsansu, suka nufi gidansu Gaje da yake da yake bankar da mutane, sai ka ce ranan ne biki. Koda su Gaje da kawayenta suka shigo cikin gidan, babu abun da ya ragu na shirye-shiryen biki. Sai ma abin da yake karuwa. Haka ma can gidan Dakaci. Shi ma babu abin da aka rage na shirin bikin. Duk dalilinsa kuwa na yin haka din, shine 'Yan sanda sun saba zuwa su tafi da Lamido, ba tare da daukan dogon lokaci ba. Lamido zai dawo ya ci gaba da harkokin shi, ba tare da ya sauya hali ba. Allah sarki rashin sani. Aka ce ya fi dare duhu! Ni dai dana bi su Hakimi can Birni, sai gamu a (Police station). Tirkashi! Ni ce da shiga (Police station). Ofishi 'yan sanda. Ya zan yi? Tunda dai ina bayansu. Kuma halina ya jawo min na son farantawa DA SANNU... 51 masu karatu rai. Kuma ina ganin tunda ga Hakimi da Dakaci, ina ganin ba abin da 'yan sanda zasu yi min. To ga su Hakimi nan. Dakaci yayi tsuru-tsuru da shi, fuskar Hakimi da Dakaci babu sauran haske. Zaune suke kawai gaban shugaban 'Yan sanda (Kwamishina). Hakimi yace "To wai yanzun meye abin yi? Kwamishinan 'Yan sanda yace "Babu abin yi, sai abin da (Court) ta yanke, kuma kun riga kun san hukuncin da shari'a zata yanke. Wannan abu da ya faru, na fada muku dama ace dukkan 'yan-matan sun mutu ne. Da sai mu yi nasara, mu cire Lamido a ciki, tunda babu kwakkwaran shaida. Da sai kawai a yankewa yaran shi hukunci, ba tare da an sa Lamido a ciki ba. Kun ga mahaifin yarinyan nan. Lauya ne, dama ace 'yar lauyar ce kwance a asibiti da abin ya zo da sauki, tunda ita daya yarinyar ance ubanta tallan gauta yake a faranti. Ka ga irin wadannan an saba fatali da shari'arsu a dannesu. Amma gaskiya hakkin Lauya ba zai taba dannuwa ba. Ita kenan masa diya mace. Duk 'Ya'yan shi maza ne, dan haka ina ba ku shawara, kada ku batawa kanku lokaci. Dole ne hukuncin kisa ya tabbata akan Lamido. 'Yan mata biyar fa suka yiwa fade. Biyu sun mutu, uku suna gadon asibiti, babu sauki, sai na Allah. Da kyar suke magana. Kuma Lamido shi ne shugaban yin komi. A hannun shi ma 'yar Lauya MAMAN FADILA 52 Bashir ta mutu. Allah shi kyauta gaba. Ranan litini za ku gurfana gaban shari'a. Dakaci ka yi hakuri. Allah ya jikan yaronka, ya yafe masa. Ku ke jawo ko ma menene, ku na iyaye. Yaranku su yi ta jawo rigima koyaushe, kuna tunkahon kuna da kafa, ko hanya. Sai dai a sasanta ba tare da kun dauki wani kwakkwarar mataki akan yaranku ba, tunaninku kuna da hanya. To. duk hanyarka, wata rana bacewa take, matukar ka shiga hanyar wasu." Hakimi ransa a bace yace ma Dakaci "Ka ga abin da nake fada maka kenan akan Lamido. Sai ka ce min wai ba ruwan shi da kowa. An dai sa masa ido ne, halayyar shi suna da kyau. To yanzun ina kyawun yake? Ga shi zai yi mutuwar wulakanci, sakamakon halayyarsa. Sai ka tashi mu koma. Allah ya kyauta. Yanzun kuma sai mu koma mu sanar da gidan mai unguwar 'yar shi ta hakura. Maganar aure an fasa." Kwamishina yace "Auren wa za'a fasa? Hakimi yace "Auren Lamido da 'yar mai unguwa." Kwamishina yace "Ba iyayenta sun gama komi na aure ba? Dakaci da sauri yace "Wallahi an gama, ko dan haka a tausaya man Kwamishinan 'Yan sanda. Yayi murmushi, yace "Hakimi, tunda iyayen yarinyar nan sun shirya, to abin da yakamata ku yi, tunda dai ko kun fasa auren nan a yanzu, dole wani da ban yarinyar zata aura. Dan Lamido matacce ne, ba komawa kauyen nan zai yi ba. Sai lahira. DA SANNU.... 53 Ku je ku nemi uban yarinyar, na ku ce masa ya kira yarinyar cikin samarin ta ta fito da wani a daura musu aure da shi. Ina ganin yin hakan shine zai fi kawo kwancyar hankalin ita budurwan da irin surutun jama'a da zata fuskanta." Hakimi yace "Gaskiya ka kawo shawara mai kyau. Dan ina ganin yin haka zai kawo saukin komi. Dakaci ina ganin shawaran Kwamishina za ka bi, yanzu in mun koma, sai ka je ka samu mai unguwa ku tauttauna akan haka din." Dakaci yana hawaye yace wa Hakimi "Ka taimaka min, ka aika a zo da mai Unguwa gidanka, sai mu yi komi a idonka.” Hakimi ya gyada kai, yace "Babu damuwa, mu je gidan nawa. Sai in tura a zo da shi din. Kai har ma da ita yarinyar." Hakimi da Dakaci sun ga Lamido an fito musu da shi. Abin mamaki da rashin sani. Lamido ya dauka kamar yadda ya saba dauko rigima awarwareta. Haka ma wannan rigiman take. Bai san ba haka bane. Bana 'yar Lauya aka tabo, dan haka fuskar Lamido babu wani damuwa a cikinta. Sai dan kadan wanda ba a rasa ba. Tun kafin su yi masa magana, yace "Baba ina fatan dai an ci gaba da shagulgulan biki, har can gidansu Gajen? Dakaci kasa magana yayi, yana zubar da hawaye. Hakimi ne yace "Yi mana shiru, mutumin banza kawai. Wanda baya jin magana. Ai in ba wani iko na Allah ba, kai da aure, sai a lahira, don rigimun da kake daukowa, kana yin nasara. To bana ka dauko mai zafi. MAMAN FADILA 54 'Yar Lauya ka kashe. Dama 'yar talaka ga Ya'yan Attajirai can bisa gadon asibiti, dan haka maganar aurenka da Gaje. Babu, mun soke, don ba zata auri gawa ba. Kai dai Allah ya yafe maka kura-kuranka, ya kuma gafarta maka. 'Yan baya masu irin halayyanka. Allah ka shiryesu, ya ganad da su hanya mai kyau." Ya mike yace wa Dakaci "Ka sameni a waje, ina jiranka, mu tafi." Ya barsu nan gaban Kwamishina da kuma wasu (Police) guda biyu, suna tsaye bisa kan su Lamido da mahaifin shi. Babu wani maganan kirki, sai kuka da suke yi. A haka aka rabasu, gwanin ban tausayi. Ko da dai su suka jawowa kansu. A can kauye kuwa, ana ta ruguntsumin wasannin gobe biki, har yamma babu ango, babu kuma uban ango. Nan fa hankula suka fara tashi. Mai Unguwa ya nufi gidan Hakimi, ko shi ya dawo. Ya ji yadda abin yake. Faduwa ta zo daidai da zama. Yana isa kofar gidan Haikimi. Su kuma nasu motar na isowa. Suka fito daga motar mai unguwa yayi gaisuwa, ga Hakimi. Ya shiga cikin gida wajen iyalan shi. sannan ya fito ya samesu zaune a falo, suna jiran fitowar shi. Koda ya fito bayan yar gajeruwar magana da suka yi. Sai Dakaci ya fara wa mai unguwa bayanin komai. Yana yi, yana zubar da hawaye. Mai Unguwa ciki jimami da tausayawa yace "Yanzu babu wata hanyar mafita da za mu samu? DA SANNU... 55 Dakaci yace "Tunda ka ga mun dawo da Hakimi, ai babu ne." Mai unguwa, yace "Allah ya kyauta, bari in je in kirawo ita Gajen, mu ji ko tana da wanda take so." Ya fita, ya bar Hakimi da Dakaci, suna dada tattaunawa kan batun. Ba wani dogon lokaci mai Unguwa ya dauka ba. Sai ga shi ya dawo tare da Gaje. Hakimi yace "Ina fatan ba ka tsaya ka fadawa kowa abin da ake ciki ba? Yace "Babu ma wanda ya san na taho da Gaje nan." Hakimi ya dubi Gaje. Bayan ta gaidasu, yace "Gaje diyata, yanzun idan aka ce an fasa aurenki da Lamido ko kina da wani daban da za ki kawo mana shi, mu daura muku aure da shi? Gaje ta girgiza kai tace "Ba ni da wani." Mai Unguwa yace "To aure tsakaniki da Lamido, babu shi, an fasa." Caje bata san Jalilin fasa aurenta da Lamido ba. ita a tunaninta Lamido kada ya dawo ace za'a daura musu aure da shi. Dan haka ita ma bata son a daga auren nata, gara koma waye ta aura. Yanzu da dai a daga. Da sauri tace "Baba, ni ba ni da samari, ko daman dan haka na ba ka zabi, ko ma waye, ka daura min aure da shi, na amince." Gaba daya sai Gaje duk ta burgesu, dukkansu suka sa mata albarka. Hakimi yace "Gaje diyata, sakamakon biyayya irin ta ki. Ni na zaba miki miji. Kanina Magajin Hakimi, za a daura miki aure da shi. Ina fatan za ki amince da shi? Da sauri Dakaci yace "Godiya muke Hakimi. Wannan abu yayi daidai." MAMAN FÁDILA 56 Mai Unguwa yace "Allah ya kara maka tsawon kwana, muna godiya. Yarinya ta amince, ta kuma gode." Ita dai Gaje rufe fuskarta tayi da jin wannan magana da Hakimi yayi. Yace "Abin da nake so da ku, wannan magana mu barta anan, kada mu bari kowa ya santa. Ni kaina cikin iyalaina babu wanda zan sanar da shi. Sai gobe. Bayan an daura auren tukuna. Sannan zan yi musu bayani. Saboda haka kowa gobe in an daura auren, sai su ji koda wa aka daura auren. A lokacin koma menene jama'a sai su fahimta." Ita dai Gaje tafiya kawai take zuwa gida, tana tunanin wannan aure nata da Magaji. Mutumin da bata san ko waye ba. Ita bata ma san yana da wani Dan-uwa ba, sai yanzu. Anya kuwa shi wannan Magajin, zai amince da ita a matsayin matar shi? Tirkashi! Ni kaina abin da nake tunani kenan. Ga dai ni nan biye da su Gaje. Don haka ta kwana cikin tunanin abinda zai biyo bayan auren nasu. Kowa owa ya hallara wajen daurin auren Lamido da Gaje. Waliyyai su na ciki. Abin da maroki ke fadi, shi ya gintsewa kowa tunanin shi, yana fadin "An daura auren Abdullahi da Habiba. Asalin sunan Gaje. Mata da suke cikin gida, suka fara surutu. Lantana da yake da safe Dan-tani yayi mata bayani, saboda irin haka. Abin da Lantana ta fadawa mutane, DA SANNU... 57 shi ne an fasa da Lamido, yanzu da kanen Hakimi aka daura. Daga wannan magana, bata kuma furta komai ba. Ta ja bakinta tayi shiru. Kowa na fadin albarkacin bakinsa. To haka ma kofar gida. Su ma da suka fara surutu. Sai aka yi musu bayanin Allah bai yi da Lamido ba. Da Magajin Hakimi Allah yayi. Mutane suna ji, suna gani, suna son su yi bincike akan abin. Amma babu dama. Sai dai kuskus suka rika yi, kowa ya watse kafin Hakimi ya koma gida. Har labari ya iske kowa na gidan. Zuwan Hakimi kawai suke jira. Hakimi yana zuwa gida. Auwalu da yake shi ma yana gida bai koma makaranta ba. Tunda ya dawo hutun sallah. Haka su Naziyatu da Nusaiba su ma suna gida, basu koma makaranta ba. Duk cikin satin nan zasu koma. Shi ma Magajin Hakimi kwanan shi biyu da komawa. Auwal yace "Baba Hakimi, wai da gaske an daurawa Baba Magajin aure da wannan 'yar kauyen? Hakimi yace "Da gaske ne. Dan birni, kana mamaki ne? Naziyatu tace "Baba yarinyar nan fa gidanku da rowa. Amma gaskiya Baba Magaji ba zai amince ba. Yarinyar da tace sai ta kwana uku bata yi wanka ba. Ita ce za ace matar Baba Magaji? Wanda duk kwalliya irin tawa, kusheta yake, yana cewa ban iya kwalliya ba. Hala dai Baba ba ka taba ganin hotunan Baba Magaji da yake yi da 'yar matan shi bane a makaranta. Kuma ma ina ganin 'yan matan MAMAN FADILA 58 Baba Magaji, ai sun kusa haihuwar gidanku da rowa. Ko ni fa na girmeta. Taf! Na san zata sha yanka kuwa, don ba'a iya masa." Nusaiba tace "To wai ku duk kuna bata bakinku ne, duk kudinka da mukaminka da

Chapter 3 of 7