Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
Mata ciwo ba,yana fad'in haka yayi tafiyarshi d'akinsa zuciyarshi nayi mishi k'una. *Gidan Hamisu* "Yanzu Zeenat kinsan girman laifin k'auracewa Mijinki tsawon kwana ki, kuma akan wani abunda bai taka Kara ya karya ba?. Cikin tsiwa Zeenat" Tace to sai me Kaine mai raba lada kome?DA zama zo ka isheni da wani wa'azi i'ta wadda ka shigarwa d'in har kazo kana yimun tujara agaban Jama'ah kaje ta baka k'anwarta ka Aura tunda abun ya zama rashin mutunci. Shiru Hamisu yayi ba tare da yace komai ba yabarwa Zeenat d'akin baki d'aya,Rabon da kwanta da matarsa Zeenat don raya sunna i'dan bai manta ba,tun A Daren da yace Mata ba zai siya ABayar Sallah ba,tun ranar Zeenat ta gujesa koda yaje kusa da i'ta zagi ne da mumunan maganganu ke shiga tsakaninsu yau ma abunda yasa ya nemeta Sha'awarsa ce ta fito sosai,Amman koda ya samu Zeenat gaggasa mai maganganu tayi. *Unguwar Tudun yola* wata yarinya na hango wadda ba zata wuce shekara sha 18 ba tana sanye DA Riga da zani Na atamfa,ga k'aton hijabin ta na mutunci kyakkyawa ce Amman black beauty ce,ga Jan lallen DA Tasha y'an yatsun k'afa da hannu abun gwani sha'awa. Tabarakallahu Ahsanin kalik'in🀲🏻☺️❀️ Hamisu ne ya fad'i hakan a lokacin da yake kan lifan d'insa dai dai zai shiga gidansa,yaga ta shiga gidan Jamila wadda suka yi fad'a da matarsa Zeenat. A hankali ya jingine mashin d'in Nasa da yake ankusa Fara kiran Sallar magariba,Har lokacin kallon k'ofar gidan ya keyi kamar wani tsohon maye,hannu yaji a jikinsa yayi firgigit kamar wani Wanda ya dad'e yana bacci. "Lafiya kuwa Hamisu?naga kana ta kallon k'ofar gidana ba dai fad'an suka k'ara yi ba?. " A'ah ba fad'a bane Tukur Alkhairi kasan ni bana b'oye gaskiya ta fad'in ta kawai na keyi kasan asalin sakkwatawa basu da rufi. "Eh kuwa gaskiya ne me ya faru? " Hamisu Yace a gaskiya wadda ta shiga gidan nan daga ganinta k'anwar Jamila ce kuma wallahi Ina muradin Aurenta don gaskiya tana da hankali.. *πŸ₯ΊπŸ˜”πŸ€”Tab gaskiya akwai chakwakiya a wannan littafi Mijin Zeenat nason k'ara Aure* Ku Fad'a mun irin rigimar da za'ah kwasa🀣🀣🀣🀣 *Yawan sharhi* *Yawan rubutu* *Miss greenπŸ’šπŸ€ͺ* πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ *A SANADIN A BAYAR SALLAH* πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ Gajeren labari Na *Rabi'atu(Ummu Maher)* Miss greenπŸ’š πŸ’…Shalelen Jarumai Writer's AssπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒβœπŸ» ________ πŸ’«πŸ’« *πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_ *πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«* *Shafi na 10&11* *Gidan Hamisu* Tukur ya yi Shiru alamar tunani ya ke yi a ga me da wannan maganar da abokinsa Hamisu,Shi dai ya San Zeenatu ba za ta yarda Mijinta ya Auri Rabi'atu ba k'anwar matarsa Jamila,biyo bayan rikicin daya shiga tsakaninsu. "Tukur lafiya kayi shiru ko dai zancen Dana zo maka dashi ne kake tunani akansa?Ko kuma kana tunanin Zeenat ba za ta yarda da Auren K'anwar matarka ba?to wallahi ka ji na rantse Neman wannan yarinyar yanzu na shiga yi kuma ba Zan fad'a wa kowa komai ba har zuwa lokacin da za'ayi Auren,don haka kata ya ni Neman Auren nan saboda KO babu komai Kai mijin Jamila ne ko babu komai zata sakko tun da Kai mijin tane...." "Babu komai Hamisu zanyi i'ya bakin K'ok'ari na duk yadda ake ciki Zan sanar da kai,Insha Allah kuma komai zai zo mana da sauk'i Kai dai ka cigaba da Addu'ah komai zai zo cikin Sauk'i." Godiya Hamisu ya yi wa Tukur sannan ya nufi gidansa cikin farin ciki dafatan Allah yasa yayi nasara acikin Neman wannan Auren,kuma daman yana saka ran wasu kud'i za su zo masa nan kusa. *Gidan Malam Tahir* "Salma ki bani da ma in nuna miki I'rin son da nake yi miki,saboda naga kamar baki yadda cewa inason kiba?sai wani d'a_ri d'a_ri ki ke dani,kuma kinga ni a tsari na ma a d'aura mana Aure nan da Wata d'aya. Cikin tsoro Salma ta kalli Sooraj a ga me da abinda kunnu wanta suka jiye Mata. " Haba Sooraj sai kace wata y'ar tsana da za kace wai na Aure ka nan da wata d'aya Ina laifin ma wata 5 Amman yanzu wata d'aya A'i ya yi kad'an..." "Kinga Salma ba fa bariki na ce muyi ba Aure nace muyi saboda inasonki don haka bana son irin wannan maganar kinji KO?ya fad'i hakan yana mai zare idanu kamar tsohon maye. Nan dai suka cigaba da hirarsu,sai dai ta kula Sooraj yana da wasu irin halaye saboda yana da Saurin fushi ga shi yanzu ya Saba da tab'a jikin ta tun tana Hana shi har ta gaji ta k'elesa saboda gaba ki d'aya yanzu abin ta Saba dashi i'tama har so ta keyi. " Wai Salma me ki ka d'au ke ni ne?KO kuma shashan uba ki ka d'au keni da zaki zauna kina gaya mun abunda ranki yaso,to ki bud'e Kunnu wanki ki ji ni dole ne ki rabu da wannan d'an iskan yaron me yi wa mutane kallon y'an iska Alhali shine cikakken d'an iska Mara mutunci kawai" "Cikin ra zana Salma ta mik'e tsaye tana hawaye don wallahi kome za'ayi ba zata i'ya rabuwa da Sooraj d'inta ba. *Yawan sharhi* *Yawan rubutu* *Miss green ceπŸ’š* πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ *A SANADIN A BAYAR SALLAH* πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ Gajeren labari Na *Rabi'atu B Abdullahi* (Ummu Maher)Miss greenπŸ’š πŸ’…Shalelen Jarumai Writers Ass✍🏻 πŸ’«πŸ’« *πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_ *πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«* *Shafi na 12&13* "Rabi'atu ki yarda cewa inasonki kuma babu ranar da ba Zan yi begenki ba,Ki kawar da tunanin da ya ke ranki na sab'anin dake tsakanin Yayarki da Matata,sab'anin fahimta ne idan ki kayi la'akari da Ada cen baya Jamila k'awar Zeenatu ce sosai".. " don haka don Allah Rabi'atu nazo wajenki don Neman Soyayyarki har ta kaimu da Aure,saboda so nake yi miki na tsakani da Allah,kuma so nake yi miki na Aure. "Kayi hak'uri Hamisu ba zance bana sonka ba,Amman kuma wani Dalila zai saka ink'i yarda da Aurenka saboda Zeenat ma'ana matarka,tun kafun ka furtamun so Zeenat tak'i jinina don kwata kwata bama shiri da Zeenat". " To ta yaya kake tunanin Zan Aure ka Alhalin matarka ta tsaneni kaima kasan hakan ba zai tab'a faruwa ba,Amman don Allah Hamisu kayi hak'uri don Kai mutumin kirki ne kuma i'na d'aukarka A matsayin Yaya na. "Kuma a yanzu na yiwa wani Alk'awarin Auren sa munyi Alk'awari da juna,don haka kayi hak'uri don Ina fatan ba kaji haushi na ba" Wani i'rin ciwon Kai Hamisu yaji kansa ya shiga yi mishi yawo acikin sararin samaniya,saboda yana yiwa Rabi'atu wani irin son da bai tab'a ji koda akan matarsa Zeenatu ba. Cikin zafin rai Hamisu ya hau lifan d'insa da ya sha wanki yayi tas,Rabi'atu kuwa wani tausayin Hamisu ne ya d'arsu a zuciyarta,tabbas ta San Hamisu yana cikin Wani hali saboda matarsa bata kula dashi a matsa yinsa na Mijinta na sunna. Kuma ba don ta yi wa Saurayinta Alk'awarin Aure ba DA babu abinda zai Hana ta Auri Hamisu kodon ceton ranshi,kada kuce Hamisu mummuna ne?A'ah Hamisu kyakkyawa ne son kowa k'in wanda ya rasa farin ba fulatani ne do gone mai yalwar hanci da d'an karamin baki. Hamisu sanyayyan mutum ne ta yadda ba zaka tab'a ganin fushinsa ba Sam,don mutum ne me yalwar ilimin addini Dana boko,ma'aikacin gwamna ti ne yana koyarwa a makarantar y'an Mata. Sannan Hamisu yana son kula da iyalansa duk Albashinsa idan ya d'auka a hidimar iyalinsa Dana y'an uwansa ya ke k'arewa ba ya yi wa kansa Abu KO na kobo saboda ya ceto Rayuwar iyalinsa Dana y'an uwansa DA mahaifansa. ya kasance yana son Matarsa Zeenat duk da kasan cewarta bata haihuba,y'an uwansa da mahaifansa har sun gaji akan ce masa yayi Aure Amman fa fur yak'i yarda k'arshe duk Wanda ya yi masa magana akan Zeenat b'a tawa suke yi. Sai gashi yanzu da gumi tayi gumi yana son k'ara Aure don Zeenat bata tsoron Allah KO kad'an ta d'auke shi ba a bakin komai ba,duk a SANADIN ABAYAR SALLAH. *Gidan Malam Tahir* Malam Tahir yayi shiru yana kallon mutanen da suka zo Mutanen da y'arsa ta zab'i su zama surukai A gare ta, tabbas bai tab'a yi wa yi wa wani d'an sa ba ki ba Kuma Allah ya sani ba shi ne ya haifi Salma ba sun d'auko ta ne a Gidan marayu a lokacin basu samu haihuwa ba,suka d'auke a lokacin tana zanin goyon ta,Bayan wasu watanni da d'auko Salma matarsa ta samu ciki bayan wasu watanni ta haihu. Amman duk wannan abun babu Wanda ya San cewa Salma ba y'arsu bace,kowa d'auka ya ke Salma y'arsu ce don haka babu Wanda ya tab'a sanin wannan tsohon sirrin. Kuma ba zai tab'a yarda Salma ta Auri Wanda ba shida tarbiyya ba k'arshen ya sakar musu y'a. "Gaskiya ni dai ba muyi haka da Salma,don bata sanar mun wasu bak'i za suzo ba,Amman don Allah kuyi hak'uri." daga inda Salma take b'oye a soron gidansu bayan k'ofa ta jiyo wannan mummunan furucin daga bakin Mahaifinta. tabbas ta tabbatar a yanzu Mahaifinta baya Sonta Kuma baya son Sooraj,i ta kuwa babu Wanda take so take muradin zama dashi a matsayin Mijinta sai Sooraj... *Yawan rubutu* *Yawan Sharhi* Ummu Maher ce✍🏻 πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ *A SANADIN A BAYAR SALLAH* πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ Gajeren labari✍️ _Na *Rabi'atu.B.Abdullahi* (Ummu Maher) Miss green_ πŸ’šπŸ’š *Alk'alami yafi ta kobi✍️* πŸ””πŸ“šπŸ”” *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *⚜️©J.A.WβšœοΈπŸ“šπŸ–ŒοΈ* ________ *Shafi na 14&15* *Gidan Hamisu* Sai da Hamisu ya yi kwana biyar bashi da lfy kuma baya fita Sam sai dai Sallah saboda k'aunar Rabi'atu ya ke yi ba kad'an ba,Saboda a yanzu ba bu abinda ya keso I'lla yaga ya yi Auri saboda masifar Zeenatu ta ishe shi. D'an zaman da ya yi na rashin lafiya sai da Zeenat ta Addabe shi saboda ko Alwala i'dan ya fito sai ta yadda mishi da magana ba bu ruwanta KO tayi mai da d'i ko kada tayi mai ba bu ruwanta. Duk abinda Zeenat ta ke yi Hamisu yana kallon ta ba tare da ya ce Mata komai ba shi dai ya barwa kansa sanin Mata kin da zai d'auka akan matarsa Zeenat. *Gidan Malam Haris* "Haba Salma kina son ki mayar damu k'ananun mutane da zaki turo mun Mutane wai sun zo Neman Auranki? ko kuwa kin manta ce wa akwai kud'in Bashir a kanki kuma harda sada kinsa ma a kanki.? " To Bari kiji Wallahi baki isa ki jawo mun abun kunya ba sakarai kawai Mara tunani." Wani i'rin kuka Salma ta fashe dashi na tausayin kanta, tabbas ta San i'tace ta zab'i Bashir a matsayin Mijinta ba wani ne ya zab'a Mata ba. Amman ta rasa dalilin da yasa yanzu bata sonsa kwata_kwata? don yanzu ta tsanesa sosai,Baya burge ta ko kad'an. Hmm Salma kenan ga dalilin nan kud'i abun duniya,kuma daman Hausa wa sun ce kuda wajen kwad'ayi ake kashe shi. Y'an Mata Ku daina Auren kud'i Ku dinga Auren Can_can ta ba Auren son abin duniya ba,don komai na duniya fa _rarre k'a _rarre,Kuma komai na duniya yana k'arewa ya barka da mutum. *************** "Aunty kizo Yaya Bashir yana kiranki?". Habiba ce tsaye k'ofar d'akin tana kwalawa Ya yarta Kira Amman ko kusa bata amsawa Habiba kiran da ta ke yi Mata ba. Sai da Habiba ta sa da kanta zuwa cikin d'akin don kiran Yayar ta. A kwance ta samu Salma ta yi nisa cikin wayar da suke yi i'ta da Sooraj. Suna magana a kan mutanen da ya turo d'azu Abbanta ya ce bai San da zuwansu ba. "Hmm kada ka da mu saboda Mahaifina ya ce haka ka k'ara mun lokaci Insha Allah komai zai yi setling,tunda ka yarda ce wa ina sonka kada ka da mu komai zai wuce".... " Haba Aunty Salma i'na magana Amman kinyi shiru kin da ge kina magana da wannan sha_shan Mara sanin hakkin d'an Adam".... Wani Mari Salma ta wanke Habiba da shi wanda ya sa sai da Habiba ta durk'u she a wajen hannun ta na rik'e da kuncin ta,tana zubar da kwallah. Tana yi wa Yayar ta wani kallo mai ci ke da ma maki,tabbas ba don karta k'arya ta ba to da sai ta ce can jin Salma a ka yi musu,don a i'ya sanin ta tasan ba halin Salma bane san zugar k'awa ye ce da kuma sharrinsu. "Yanzu Yaya saboda na zagi wanda baya sonki,kuma bazai tab'a sonki ba sai dai son sha'awar da ya ke yi miki,Ga wanda ya ke sonki ya ke k'aunarki tare da tausayinki kin k'i ki Aure shi sai mai kud'i"..... " Don Allah Habiba ki fitar mun a d'aki saboda ba hiruminki ne ki zab'a mun mijin Aure ba don haka daman i'dan son Bashir d'in ki ke yi to kije ki Aureshi kinji. Salma tana fad'in haka ta fice a d'akin tana zagin K'anwarta Habiba a kan shish shigin da ta ke yi mata. "Salma Ina zaki je?. Malam Haris ne tsaye a kan Salma yana tambayarta inda za taje,kuma duk ya ji i'rin zagin da Salma ta yi wa K'anwarta Habiba. " Ki je ki kirawo mun Mahaifiyarku i'na son yin magana daku mai mahimmaci. Cikin jin kunya da sunne kai Salma ta wuce don ki rawo Mahaifiyar ta su,tare da tunanin wannan wacce i'rin magana ce Mahaifinta ya ke son suyi,Cike da zargin kanta Ta ki rawo Mahaifiyarta . "Malam ga ni Salma ta ce kana kira dafatan dai lafiya klau.? " Eh to lafiyar dai zan ce domin A yau zan yanke wani hukunci a tsakanin Salma da Habiba,Hukuncin kuwa ba komai bane i'lla na dawo da Auren Bashir zuwa kan Habiba......" *UMMU MAHER CE* Vote Share And CommentπŸ“² πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ *A SANADIN A BAYAR SALLAH* πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ Gajeren Labari✍️ Na *Rabi'atu.B.Abdullahi* (Ummu Maher)Miss greenπŸ’šπŸ’š *✍️Alk'alami yafi takobiβš”οΈ* *πŸ’«πŸ’«πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_ *πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«* *Shafi na 16&17* *Gidan Malam Tahir* Ba ga Habiba ba hatta Salma sai da lamarin mahaifin na ta ya gir_giza ta matuk'a,wani tsohon son Bashir ya d'arsu a zuciyarta ka fun kace me har ta ji kamar ta ma k'ure Habiba ta kashe ta kowa ma ya huta don ba za ta jure cin mutunci ba, don ta ce ba ta son Bashir shi ne za'ah d'auki wannan mummunan matakin a kan ta?to wallahi ba za ta sab'u ba bin diga a ruwa. πŸ€”oh ka ji fa mai sauraro Salma fa da kanta ta ce ba ta son Bashir yanzu kuma ganin an baiwa k'anwarta Bashir d'in shi ne ta ke ba k'inci. Malam Ya ce"to ku ta shi ku fita na gama magana ta don haka ku fita zan sha iska, ke kuma Salma ki tsaya za muyi magana." Har lokacin ban i'ya ce wa komai ba kuma ban d'ago kaina ba, saboda tsananin da muwar da na ke ciki, har ga Allah har yanzu i'nason Bashir don ba don son da na ke mishi ba da bazan yi kishinsa ba. "Salma i'nason ki yi wa wannan yaron magana ya turo a yi zancen Aurenku Saboda ba na son abun ya yi ni sa don tare na ke son had'a ku keda y'ar uwarki." Sai alokacin ne na yi saurin d'ago idanu na na kalli Malam, shi kuwa bai ma san i'na yi ba saboda shi sha'aninsa kawai ya ke a lokacin ya d'auko qur'ani yana du bawa kuma da alama karatun zai fara, don haka dole in ta shi in ba shi waje. Da k'er naja k'afa funa da suka fara yi mun tsami tsaba gen zama a kan k'afa ta,don ji na ke yi kamar k'afa funa ba za su i'ya d'au ka ta ba, ga damuwar da ta cika cikin zuciyata, na fi kowa sanin halin Sooraj da mugayen halayensa amman a haka na keson Auransa don kud'insa, wa su hawaye ne masu sanyi da zafi suka sauka a kan fuskata na go ge na shiga d'akin mu na yi rub da ciki i'na kuka. sai a sannan ne na kula da Habiba da take Zaune tana kuka, don har cikin zuciyar Habiba bata ji da d'in abinda ya faru ba, ba bu yadda za'ayi ta ce ba ta son Bashir don duk wata nagarta da A ke so Namiji ya kasance da i'ta to fa Bashir yana dasu kuma yana da rufin asiri dai_dai ba kin k'ok'a ri, Amman sai dai tana da wanda ta ke so wato Sa'ad k'anin Bashir Amman ba bu yadda za tayi ta karb'i k'addarar ta ba bu wanda ta ke ji Sai Sa'ad sai dai tana yi mai fatan samun mace ta gari da fatan hak'uri da dan gana tare da juriya. Wani haushin yarinyar ne ya d'arsu a zuciyata don haka na tashi na yi tsaki tare da ce wa"Hmm muna fuka kina so kina kaiwa kasuwa wai kema kin girma kina son Aure to bismillah, Auren talaka har wani Aure ne ballan tana a ce wani abu, don haka ba gilin gilin ba ta yi mai, Salma ta wuce fuu tare da jin haushin kanta da haushin k'anwarta Habiba. Habiba ta kalli ya yar ta ta tare da mamakin yadsa a ka yi ta canza halayenta, don ta san a da ba haka ya yar ta ta take ba ko da ya ke ance a bokin b'arawo b'arawo ne saboda kaf duniya yanzu Ba bu mutumin da Salma ta fi jin maganar i'rin Zulaiha wato Zuly, Kuma kaf unguwarsu ba bu wanda bai san Halin Zuly ba na Yawan tara samari ga saka ma tsatstsun kaya tare da shegen son kud'i. *Gidan Hamisu* Mahaifiyar Hamisu ce ta gyara zamanta ta re da Ce wa "Wallahi tallahi Hamisu ba ka da kirki ko ka d'an yanzu da man Rabi'atu ka keso shi ne ka k'i fad'amun saboda ta ce maka anyi mata miji." "Bazan ce maka ba'ayi mata miji ba tabbas anyi mata miji sai dai ba kowa ne mijin ba wanda ya wuce kai, saboda ni na yi maka ka mu sannan na nu na kada a fad'a maka hat sai yarinya ta amin ta tana son ka sannan komai ya tabbata." "Kuma a da cen ba ya suna soyayya da wani yaro sai dai Mahaifiyarsa ta hana Auren wai ta fi son ya Auri y'ar k'anwarta to kaji yadda a ka yi." "To Alhamdu lillahi tunda yanzu kai da kanka ka furta kana son ta don zan cen da na ke yi maka har an saka ranar Aurenku kai da Rabi'atu nan da wata uku masu zuwa." Murna tare da wani ni shad'i tare da jin son Rabi'atu ya yi matuk'ar sha k'uwa a cikin zuciyarsa, ya ce"kai Inna ta kin gama yi mun komai wallahi tunda ki ka ba ni Rabi'atu Allah ya k'ara arzik'i." ********* To kwana biyu da yin haka Hamisu ya fara zuwa zance suna soyewarsu da Rabi'atu don yanzu ga ba ki d'aya ya fita hanyar Zeenatu i'ya karsa ya ajje mata kud'in ce fanen ta kan windo ya yi tafiyarsa don gudun fitanar Zeenatu. *Ummu Maher miss greenπŸ’š* *Vote* *Share* And *Comments* πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ *A SANADIN A BAYAR SALLAH* πŸ‘˜ πŸ‘˜πŸ‘˜ Gajeren LabariπŸ“– Na Rabi'atu Bashir Abdullahi *(Ummu Maher)Miss greenπŸ’šπŸ“—* πŸ’«πŸ’« *πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_ *πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«* *Shafi na 18&19* Gidan Hamisu Zeenat ta ga abin Hamisu ya fa ra wuce gona da i'ri saboda gaba ki d'aya ya fita daga sab gar tun abin ba ya da munta har ya fa ra da munta don haka ta sa mu k'awar ta Hauwa don taba ta shawara akan Mijinta Hamisu don i'ta tana ganin ci baya ne ta ba wa Hamisu hak'uri saboda i'ta a ganinta ba wa Miji hak'uri tamkar ka zubar da mutuncin ka ne. "Hauwa so na ke yi ki ba ni shawara akan wani hali da Hamisu ya d'auko Sam yanzu ya daina kula ni i'ya kacinsa dai ya ajje min kud'in ce fa ne ya fita,A i'ya Sani na kuma ba bu abinda na yi mai da zai dinga yi mun wannan abubuwan." Hauwa Ta ce"Zeenatu ko dai tun a kan Matsalar nan ce ta Abayar nan? Tun da ya nu na fushinsa tun a lokacin ke ma kuma kin yi mai Rashin mutunci a kan wannan". "To sai me don na yi mai rashin mutunci?". " Shi ba kiga abinda ya yi mun ba shi bai yi rashin mutunci ba sai ni?" "To na yi d'in ke tunda an yi miki A'i dole ki ce haka tunda ke da man mutun ba ya shawara da ke." Shiru Hauwa ta yi don ta San halin mutuniyar ta Sam ba ta son ka fad'a mata gaskiya sai dai ka zuga ta,idan kuwa tsau_tsayi ya saka ka fad'a mata gaskiya to duk yadda Ku ke da i'ta sai ta zage ka son ranta,Zeenatu ke nan bata da mutunci ko kad'an. Hauwa tana cikin wannan tuna nin. Zeenatu Ta ce"don Allah Hauwa idon ba za ki ba ni shawara ba ki rufe mun ba ki ko kuma ki ta shi ki fita uwar yawo da man deeni ya kusa dawowa. Nan fa Hauwa ta fara zuga Zeenatu nan kuwa Mutuniyar ta fara zuguwa tana jin da d'i tamkar an ba ta kyautar kud'i. Gidan Malam Tahir An kai kud'in Auren Salma da Sooraj an kuma saka ranar su i'ta da k'anwarta A Habiba tare da angonta Bashir. In da a gefe d'aya gidajen Amaren da angwa yan a ke ta shirye shiryen Auren Su. Hamisu ma an kai kud'i har da saka rana don haka Hamisu ya fa ra shirye_Shiryen yin Aurensa shi da Rabi'atu a cewarsa Sai yanzu zaiyi Auren Soyayya tare da k'auna. ************ Hauwa ta ce "Zeenatu wata jarida na kawo miki da d'umi _d'umin ta don wallahi maganar da na ke yi miki Hamisu na nan yana shirin yin Aure"....... A'i tun Hauwa ba ta k'arasa zan centa ba Zeenatu ta ta shi tsaye tare da ce wa" Wallahi tallahi Hamisu bai i'sa ya k'aro wata shegiya gidannan ba ko ya manta gidan nan Gidan mahaifina ne?to wallahi sai in ga ta inda zai kawo wata tsinanniya gidannan don wallahi ba zan yarda ba ko da na ke yi mai wulak'anci Ai inason abina". Hauwa Ta ce"nima haka na gani dai,kuma kin san wa zai Aura?". "K'anwar Jamila wato Rabi'atu wannan yarinyar da ba kwa shiri da i'ta saboda girman kan ta". Zeenatu ta mul_mulo wani bama gujen zagi sannan Ta ce"wallahi Hamisu zaiga bala'in da bai ta b'a ganin irinsa ba. Ana cikin haka Hamisu ya shugo Gidan. Daga *Alk'alamin Ummu Maher* Vote Share And CommentsπŸ’ŒπŸ“©βœ‰οΈ πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ πŸ§šβ€β™‚οΈπŸ§šβ€β™‚οΈπŸ§šβ€β™‚οΈπŸ§šβ€β™‚οΈ πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ πŸ§šβ€β™‚οΈπŸ§šβ€β™‚οΈ πŸ‘˜ *A SANADIN ABAYAR SALLAH* πŸ‘˜ πŸ§šβ€β™‚οΈπŸ§šβ€β™‚οΈ πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ πŸ§šβ€β™‚οΈπŸ§šβ€β™‚οΈπŸ§šβ€β™‚οΈπŸ§šβ€β™‚οΈ πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜πŸ‘˜ Gajeren Labari *Na* *Rabi'atu Bashir Abdullahi* (Ummu Maher)Miss greenπŸ“—πŸ’š *_Shafi na 20&21_* *Gidan Hamisu*

Chapter 2 of 4