___________________
Da sauri Zeenatu ta sha gaban Mijinta Hamisu tare da fara rattabo mai tambayoyi kamar haka:
"Hamisu wai Aure za ka yi"?
"Wacce shegiyar za ka Aura?"
"To wallahi ba bu y'ar iskar da ta i'sa ta zauna min a gidana tunda ba Gidan ubanta ba ne e he".
Da mamaki Hamisu ya ke kallon Zeenatu a ko da yaushe sai yana yi wa matarsa Zeenatu kallon mahaukaciya saboda idan ta yi maka wani abin tilas ka ce mahaukaciya.
" Zeenat are u sense"Shin kina da hankali? and whatrong with u"?
Dariya Zeenatu ta yi harda buga k'afa sannan Ta ce"Hhhhh da man tabar mar kunya da hauka a ke na d'e ta,saboda ka raina min wayo shine ka ke yi mun wani turancin iska."
"To bari kaji Idan ma da gaske ne gwara tun wuri ka fa sa wannan Auren tunda ba dole ba ne,idan kuma ka ce dole za ka yi?to wallahi tallahi ko ni ko kai?".
Zeenatu tana kai wa nan ta yi tafiyar ta d'akinta ta barshi a nan,Hauwa kuwa tana ganin Zeenatu ta shiga d'aki ta rufe gefen fuskarta ta wuce ta gefen Hamisu simi_Simi kamar munafuka.
Wata uwar Harara Hamisu ya gallawa Hauwa sannan ya yi kwafa ya Hau mashin d'insa sai Gidansu ma'ana Gidan iyayensa don ya ga abin na Zeenatu idan ba had'a ta ya yi da Hajiyarsa ba komai zai iya faruwa don Hajiyarsa kad'ai ta ke tsoro,don ya San ko da ya kaiwa iyayenta k'ararta k'arshe su ba shi hak'uri kuma ba za suyi mata fad'a ba a game da laifin da ta yi ba.
👘🧚🏻♀️👘
*A SANADIN ABAYAR SALLAH*
👘🧚🏻♀️👘
Gajeren Labari✍🏼
*Na*
*Rabi'atu Bashir Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green💚🍀
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 22&23*
Sooraj ta gani da budurwarsa a kan screen d'in wayar sannan ga sunanta nan b'aro² akan wayar.
Saurin d'aga wayar Salma ta yi don taji me y'ar rainin wayon zata ce?.
"Wallahi Sooraj idan baka zo gidana ba yau komai zai iya faruwa wato shine zaka mayar dani y'ar isaka ko saboda kana ganin ka yi sabuwar Amarya wannan y'ar matsiyatan shiyyasa ka keson ka raina min wayo ko?"
"Sooraj da kai fa na ke magana shine ka yi shiru?.
" Hello"
"Hello"
Da sauri Salma ta kashe wayar tana haki,a take ta rik'e kanta da ya ke Sara Mata,Zuly tana ganin haka ta matso kusa da k'awarta tana tambayarta me ya faru?
Wata kwalla ce ta fitowa Salma daga idanunta ta ce"Zuly Sooraj ya cuce ni ya ci Amanata sai Allah ya sa kamin Allah yabi min hakkina".
"Ki bud'e bakinki ki fad'a min menene ya faru kina ta ce min Sooraj ya cuce ki da ya yi miki me"?.
Nan Salma ta fad'a wa k'awar ta duk abinda ta gani da abinda taji,Zuly ce ta ringa tausarta da bata hak'uri,sannan ta ce mata komai yazo k'arshe da zarar anyi Auren zasu je wajen boka a mallake Sooraj sai yadda suka yi da shi.
Sannan ta umarci k'awarta da kada ta kuskura ta nuna wa Sooraj abinda ta gani idan ya nemi yasan waye ya ki rasa ki nuna bakisan waye ba,kinga yanzu saimu goge kiran kwata²,da haka suka yi wa Sooraj wayo suka yi shiru da bakinsu har aka tashi daga Dinner d'in sai dai har aka tashi cikin zuciyar Salma tana jin babu dad'i a game da abinda Sooraj ya yi mata.
Zuly tafi kowa son ayi Auren nan saboda tasan Sooraj bakin aljihunsa a bud'e ya ke zata ringa samun Alheri shiyyasa tun farko ta had'a Auren don i'ta ma ta kwashi romon damukara d'iyya.
To wannan kenan.
A haka aka yi yini Amarya Salma zuciyarta babu dad'i don ma Zuly tana tausar k'awar ta,don tun safe tana kusa da k'awarta Babu inda taje a Daren ranar ne kuma aka kai amare gidajensu sai muce Allah ya bada Family na gari.
*Gidan Hamisu*
A b'angaren Hamisu ma yau ya ke angon ce wa da Amaryar zankad'a d'iyya zilla_Ziyya adawiyya matar Malam Hamisu.
Idan kaga bakin Hamisu kamar an bud'e gonar auduga saboda farin ciki jinsa ya ke kamar yau aka haifesa saboda murna yau ya yi Aure,Auren da ya ke fatan samun kwanciyar hankali acikinsa.
Zeenatu kuwa da k'awayenta sun cika gida ana ta famfa Zeenatu akan kada ta yadda ta basu k'ofar da zasu zauna lafiya,tunda har ya zab'i ya yi Aure.
Kunji fa mai karatu acikinsu fa harda mai kishiyoyi biyu akwai mai uku ma'ana wacce su hud'u ne awajen mijinsu.
Amman saboda Zeenatu mai do d'ad'd'iyar kwakwal wa ce sai ta ringa Hawa kan zugarsu tana hango yadda za ta yi wa Hamisu da Amaryarsa.
Gida mai kyau Hamisu aka bawa Hamisu ogan sa ne ya basa bisa don Allah ya had'a jininsa da Hamisu suna harkar mai wato man fetur kuma Alhmdh yanzu Hamisu yana samu.
plate ne Gidan kuma set contant ne,ma'ana mai komai aciki.
Abinda Zeenatu bata Saniba an da
d'awa Hamisu matsayi awajen aikinsa,kuma Alhmdlh yanzu yana samu,sai dai bai yi gan_gancin gaya wa Zeenatu ba don yasan halinta.
An d'aukowa Hamisu Amaryarsa inda aka kawota gidanta mai kyau Wanda aka cika mata kaya dashi mai kyau da tsari.
Bayan y'an kai Amarya sun tafi Hamisu ya shigo gidansa cikin farin ciki a cen k'arshen gadon ya hango ta ta rufe fuskarta tana kuka mai ban tausayi.
A take Hamisu yaji ya k'ara son Rabi'atu tare da jin tausayinta don shi Hamisu Allah ya d'ora mishi tausayi da jin k'ai Hamisu mutun ne shi mai sanyi hali da wuya kaji abinda zai had'a shi da wani sai dai abin babba ne ko Zeenatu ma halinta ne yasa suke fad'a da Hamisu Amman yasan Zeenatu ko giyar wake tasha baza ta tab'a iya rabuwa da Hamisu ba don ba za ta tab'a samun miji kamar Hamisu ba a wannan time d'in.
K'anshin turarensa ne yasa Rabi'atu sanin cewa Gwarzon Mijinta Hamisu ya iso gareta.
Sallama ya yi ya shiga yana mai samun waje a bakin gadon ya zauna yana k'ara kallon fuskar Rabi'atu da ke rufe.
Amincin Allah su tabbata ga wannan halitta mai kyau da zati ma'abociyar kyau da kwarjini,dafatan Amaryata tana cikin k'oshin lafiya kamar yadda angonta ya ke.
D'agowa ta yi a hankali tana mai kallon fuskar Mijinna ta ya yi kyau cikin shigarsa, shadda fara k'al har wani shek'i ta ke kyaunsa da kwarjininsa sun k'ara fitowa sosai,sajensa Wanda ya gaji da gyara ya yi kyau yana shek'i pink lips d'insa tabi da kallo Wanda ya yi kyau kamar Silva.
Murmushi Rabi'atu ta yi Wanda ya k'ara fito mata da kyaunta,azuciyarta kuwa tana jin son Mijinta har k'ark'ashin k'ahon zuciyarta tana ji aranta rana da zafi Inuwa da k'una,ba zata tab'a rabuwa da Mijinta ba.
Matsowa Hamisu ya yi yana k'ok'arin k'ara sa d'aga mayafin jikin Rabi'atu, inda ita kuma ta yi saurin rik'e hannunsa tana mai gyan gyad'a masa kai alamun ya bari,dariya Hamisu ya yi sannan ya rik'e hannun Rabi'atu wani yar ya ji tunda ga kansa har kwakwal warsa.
*✍🏻Real Ummu Maher ce*
Vote
Share
&
Comments.
👘🧚🏻♀️👘~
*ASANADIN ABAYAR SALLAH~*
~👘🧚🏻♀️👘
~Gajeren Labari~✍🏻
Na
*Rabi'atu Bashir Abdullahi*
(Ummu Maher)miss green💚☘️.
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*24&25*
*Hamisu*
"Masha Allah muna yi wa Allah godiya da ya nuna mana wannan rana,Allah ya bamu zaman lafiya ya kad'e mana duk wata fitina."
Cikin jin kunya Rabi'atu ta ce"Amin ya rabbi".
Nan ya umarce ta da suyi alwala suyi sallah don nuna godiyarsa da Allah mad'aukakin sarki da ya azurtasu da yin Aure bautar ubangiji.
Bayan sunyi Sallah Hamisu ya dafa kan Rabi'atu ya yi mata addu'ar da Manzon Allah(S.A.W) ya koyar damu aranar da ka yi sabon Aure.
Daganan ne fa zancen ya sauya salo,ni kuwa Ummu Maher na ce Asha amarci lafiya.
★★★
Zeenatu
Da k'arfi ta ke bugun k'ofar gidan kamar za ta b'allasa Allah² ta ke yi su bud'e au kwashi ruwan bala'i rabon da ta ga Hamisu tun jiya da safe.
Hamisu
Da magagin bacci ya ta shi Rabi'atu tana kusa da shi tana baccinta cikin kwanciyar hankali,ya shafi gefan fuskarmasifa yi murmushi ya tuno Daren su na jiya a ta ke yaji wani murmushi ya bai baye shi.
Jin k'arar bugun k'ofar bai tsagaita bane yasa shi fitowa da sauri yana mitar waye wannan da safiyar nan.
Turus ya yi ganin wacce ta yi musu Daren mikiya da sassafennan,Ya yi kamar bai gan ta ba ya shigo abinshi cikin gidan.
Zeenatu
"Wallahi tallahi baka i'sa ba Hamisu saboda ka mayar dani wawiya wacce bata San abinda ya ke damunta ba shine zaka barni a cen kai ka taho nan kai ga me Amarya ko?".
Har lokacin Hamisu bai da Zeenatu cikanki ba hakan ne ya bata damar cigaba da sirfa masifa had'e da rashin mutunci.
Rabi'atu tana cikin baccinta mai cike da wahala yadda kowacce mafi yawancin Amarya ta ke kasan cewa,kawai sai taji ana zage² daga i'ta sai sleeping dress ta fito ta tufke gashinta ta yi doughnut dashi tana tafiya da k'er kamar zata fad'i k'asa.
Da sauri Hamisu ya taro Amaryarsa Rabi'atu cikin so da kulawa ya ce"oh Sorry Baby da Sauri ya rungumeta had'i da d'aukarta kamar jaririya ya shigar da i'ta d'akin sannan ya lullub'eta ya rufo mata k'ofar.
Ganin Rabi'atu acikin halin da take ciki ba k'aramin d'agawa Zeenatu hankali ya yi ba,wai daman haka kishin ya ke oho,ni kuwa Ummu Maher na ce Zeenatu wa ya gaya miki barni gabas ta ke.
Damk'ar wuyan Hamisu Zeenatu Ta yi sannan ta ce"wallahi Hamisu yau sai dai ko ni ko wannan y'ar iskar matsiyaciya".....
Da sauri Hamisu ya d'aga hannunsa zai mari Zeenatu Amman kome ya tuno oho?don haka kawai sai ya janyo hannun Zeenatu sannan fita da i'ta gaba d'aya daga cikin gidan sannan ya rufe k'ofar yana mamakin hali irin na Zeenatu.
Salma
Kuka ta ke yi mai cike da nadama da Dana sanin Auren Sooraj,da ta yi rabonta da tasa Sooraj a idonta tun ranar da aka d'aura Auren su da safe bayan sun shigo gaisuwar iyaye,yau kwananta biyu a gidan shi ba bu kuma wani d'an uwanshi da ya tako gidan yazo abin yana matuk'ar bawa Salma mamaki,to waishi Sooraj Bashi da kowa ne kome?.
Tambayar da ta ke ta yiwa kanta kenan Amman ta kasa samun Wanda zai bata amsar kuma ko Zuly bayan da tazo da safiyar da aka kaita bata k'ara ganin ta ba.
Kanta ta rik'e da ya ke wani azababben Sara mata ta rik'e tana tuna irin cin amanar da ta yi,tasan Allah bazai tab'a barinta da hakkin Bashir akanta ba domin kuwa ta cuce taci amanarsa,Allah sarki yanzu yana cen da Amaryarsa k'anwarta Habiba.
Ta tuna sanda ya ke ce mata matuk'ar ya yi Aure sai ya yi sati biyu ba tare da ya fita Aiki ba,saboda ta bawa Amaryarsa kulawa.
Wani gumi ta share da wasu zafafan hawaye,yunwa ta ke ji kamar cikin ta zaici babu,rabonta da abinci tun jiya da rana, bawai don babu abincin bane A'ah akwai kawai dai tunani ya hana ta cin abincin.
Tun kafin a kawota Sooraj ya ajje mata kayan abinci kala² masu yawa hatta fridge an zuba komai na more rayuwa.
Sai dai kash!gidan babu wani armashi bare aji dad'in zama acikin sa.
Sooraj
Haba Momi me zaisa kiyi min haka kawai don bakison Salma sai ki saka a kulleni a d'aki.....
Yasin bazan k'ara sa zan cen ba idan banga ruwan Comments ba🤔🤔🤔🤔🤔🤔.
*REAL UMMU MAHER CE✍🏻*
👘🧚🏻♀️👘
*🌹ASANADIN ABAYAR SALLAH🌹*
👘🧚🏻♀️👘
~Gajeren Labari~✍🏻
Na
🌹Rabi'atu B/Abdullahi🌹(Ummu Maher)Miss green💚☘️
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*26&27*
"kai Sooraj kasani duk abinda na yi niyya babu Wanda ya i'sa ya hanani don haka yanzu yanzunnan na keson ka Rubuta wa wannan y'ar talakawan takaddarta don ba gidan ubanta bane wannan k'azamin Malamin don na Riga da na yi maka mata don haka ka Rubuta ta kadda yanzu.
Babu wasa a idon Momin Sooraj Sam,ta mrtuke fuskar kamar ta shanu,cikin k'ara ji ta k'ara cewa zaka Rubuta mata ko sai na tsine maka Albarka!"?
Hannu na rawa Sooraj ya fara Rubuta ta kaddar cikin mamaki Momin ta kallo shi taga abinda ya Rubuta da Sauri ta wafce ta kaddar sannan ta yaga ta,sannan ta fallo wata ta bashi.
" Saki 3 na keson ka yi mata idan kuma ka k'i yanzu in a'i watar da Mummunan k'idirina akanta don bani da imani ballanta na mutunci."
Da Sauri Sooraj ya amshi ta kaddar yana Rubuta wa yana kuka,don yana son Matarsa Salma so mai tsanani don kamillaliyar yarinya ce y'ar gidan mutunci ko hannunta bata yadda ya tab'a mata ba.
Dariya Momi ta yi sannan ta wafce ta kaddar ta gani sannan ta ce"ta shi muje gidan yanzu ka kai mata agabana don ban yarda kaje kai kad'ai ba ta lashe maka kuruwa d'iyar mayu.
*****
*Gidan Hamisu*
Rayuwa suke mai dad'i mai cike da so da k'aunar junansu.
A y'an kwanakinnan idan kaga Hamisu ya yi k'iba ya yi kyau tsofan dole da ya fara yanzu duk ya baje farinsa da kyaunsa ya k'ara fitowa.
Kwanansa Bakwai agidan Amaryar tasa ya fara had'a kayansa don komawa gidan Zeenatu,saboda cika umarnin ubangiji Amman hat zuciyarsa ba ya jin dad'in komawar da zaiyi gidan Zeenatu.
Rabi'atu ta fuskanci hakan don haka ta fara kwantar mai da hankali har k'ofar gida ta rakoshi tana mai bye bye har ya wuce a sabuwar motar da ya siya.
Kamar kullum a cike gidan ya ke ana ta zuga Zeenatu ana mata zugar keken b'era i'ta kuma tana d'auka,kamar kada ya shiga gidan Amman ya daure ya shiga.
Da Sauri Zeenatu ta juyo tana kallon Hamisu, shima ya yi mata irin kallon gefen idon nan,idonta ya hango daya kumbura tsabar kuka,ta rame ta yi wani fayau da i'ta.
Tausayinta ne ya tsargu a zuciyarsa harga Allah har yanzu yana son matarsa Zeenatu Amman halinta ne ya ke saka yaji haushinta.
Bata ce cikanka ba ,shima baiyi mata magana ba ya yi shigewarsa d'akinsa,kamar kullum yauma haka d'akin ya ke babu ko gyaran arzik'i dole ya cire rigarsa ya fara Aikin d'akin ya kunna Room freshener, nan da nan d'akin ya yi kyau gwanin sha'awa.
Aiki ne a laptop d'insa don haka ya fara dubawa bai k'ara bi takan Zeenatu ba don har ga Allah yana tsoron masifar ta.
"Haba Zeenatu yanzu kina kallon Mijinki ya wuce babu sannu da zuwa Ballan tana ma kibi mijinki don ki nemi yafiyarsa abisa duk abinda kika yi mai".
Mama mai magani sunan matar ta shahara awajen gyaran ma'aurata tare da basu magunguna ingantattu na mata.
Duk tsiyar Zeenatu saida jikinta ya yi sanyi ba tayi magana ba kuma bata tashi daga wajen ba.
" Zeenatu Mijinki har yanzu yana sonki kuma kina damar ki gyara abinda ki ka yi abaya don haka ki faran tawa Mijinki kafin kishiyarki ta kwace miki miji kinga wataran sai ki zama y'ar kallo."
Nan fa Mama ta ringa bawa Zeenatu shawarwari kuma akayi dace Zeenatu ta d'auki shawarar don gaskiya ba zata zauna wata ta kwace mata miji ba.
Nan fa Mama ta bata wasu magunguna a take Zeenatu ta fara amfani dasu ta tashi ta gyara gidanta tsaf ta gyara gashinta bayan ta wankeshi daman Zeenatu ga kyau ga komai,tsiyarta ce ta saka bata gyara wa sai yanzu da akayi mata kishiya.
*ANAN NAKE JANYO HANKALI MATA AKAN KADA SAI KINJI ZA'AYI MIKI KISHIYA KI FARA GYARAN KAWAI,TUN KAFUN AYI MIKI KISHIYA YAKAMATA KI GYARA DON HAKA MATA DON ALLAH MUDINGA GYARA HALINMU DA JIKINMU MATA.*
Ta gyara jikinta sosai sai tashin k'amshi sannan ta zira rigar baccinta mai shara shara mai kyau kalar white.
Ta yi kyau sosai ta zumbula hijibinta har k'asa sannan ta d'auka tiren abincin ta yi hanyar d'akin Hamisu.
A hankali ta bud'e handle din k'ofar d'akin ta shiga d'auke da sallama hatta magana aranar sai da Zeenatu ta canza ta.
Kallo Hamisu ya bu Zeenatu dashi kamar ranar ya fara ganinta.
*By*
*Real Ummu Maher ce✍🏻*
👘🧚🏻♂️
*🌹A SANADIN ABAYAR SALLAH🌹*
👘🧚🏻♂️👘
*~Gajeren Labari~✍🏻*
Na
*🌹Rabi'atu B/Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green💚☘️.
_*📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION💪🏻*_
_Mãrubutã Mãsu Aikî dà Jãrûmtã wãjãn îlimãn tãrwã bîsã hãrshén Hãûsã✍🏻_
3∅
Kallon Zeenatu Hamisu ya shiga yi kamar yau ya fara ganinta,sosai ta yi mishi kyau saboda daman Zeenatu kyakyawa ce gyarawa ne kawai ba ta yi.
Hamisu bai San sanda ya ware mata hannayensa ba alamun ta shigo,don yadda ya ganta ko ba'ah gaya masa ba yasan ta nitsu don yadda fuskar ta,ta nuna cikin happy ta shiga cikin jikin Mijin nata tana shak'ar k'amshinsa mai dad'i.
"Don Allah My dear ka yafemin abubuwan da na yi maka na rashin kyautatawa".
Kuka ta ke abin tausayi ya yin da Hamisu ya d'aga hannunsa yana godewa Allah na gyaruwar matarsa Zeenatu tare da jin wani irin sabon sonta ya dawo mai fil.
Bayan yaci abinci ne fa salon ya canza don a ranar masoyan sun nuna sun Dad'e basu had'u ba don sun nuna wa junansu kulawa.
Bayan komai ya lafa ne Hamisu yaga kiran Amaryar hau sau 5,Zeenatu tana kallonsa taje ta rungume shi nan fa aka fad'a sabuwar soyayya,ya yinda Amarya abin ya bata haushi sosai kishi ya tashi,Amman da ya ke Hamisu ya iya lago sai ce mata yayi wayarce ta fara samun matsala shiyyasa, haka Rabi'atu tana ji tana gani ta hakura.
Kwana biyu Hamisu da Zeenatu suka yi suna cin amarcinsu,sannan ya koma gidan Rabi'atu.
Watansu uku da Aure Rabi'atu ta samu ciki,cikin ikon Allah i'ta ma Zeenatu Allah ya kawo mata na ta.
Rabi'atu wata uku Zeenatu wata biyu,kuma a yanzu Hamisu ya had'e matansa ya yinda ya siyar da Gidan da Rabi'atu ta ke ya siya mai part biyu.
Zeenatu a yanzu duk ta yarda makaman yak'inta kula da Mijinta kawai ta saka agabanta,k'awayen banza kuwa duk ta zubar dasu kuma ayanzu ta nemi afuwar Rabi'atu da yayarta Jamila da kuma Mahaifiyar Hamisu.
*MU WAIWAYA SALMA KUMA*
🅱️ack to Salma.
Murd'a handle d'in falonta taji anyi cike da tsoro ta k'urawa k'ofar idanu,don rabon da ayi sallama agidan tun ranar da Zuly tazo.
Kafin ta k'arasa tunanin da ta ke yi kawai sai ganin Sooraj ta yi agabanta,ta dafe k'irjinta kafin ta gama tunanin kawai sai taga wata mata a bayan Mijinta Sooraj.
"Kai soko bana san haukar taka,ka mik'a mata ta kaddar ta ka taho mutafi don ba kallon kallo na ya kawo mu ba.
Ya bud'e bakinsa zaiyi magana Matar ta wafce ta kaddar ta cullomin tana ce wa" Ga shinan mun yarda kwallan mangoro mun huta da k'uda".
"Sai a koma cen gidan Malam mai almajirai a Auri dai dai mutum don kin san ance kwarya tabi kwarya."
Tunda matar ta fara magana Salma ta ke kallon ta don kawai hango kamar da ta ke yi da matar,kuma ta lura i'ta ma matar kallon ta ta ke yi sosai.
Tana fad'ar haka ta fita waje fuuuuuu,ta kama hannun Sooraj suka fita kwallah ce ta fara fito min daga idanuna sannan ina tunani wai yau nice aka yi wa wannan cin mutuncin.
Da k'er ta iya bud'e ta kaddar tana zubar da hawaye lallai tun kafin akai ko'ina ta fara ganin sakamakon bijerewa iyayinta duk kuwa A SANADIN ABAYAR SALLAH.
★<><><>★
"Salma daman nasan dole ne irin wannan ta faru saboda tun ba yau ba nasan ce wa hakan zata iya faruwa yanzu ga y'ar uwarki nan salin_alin suna zaman lfy da Mijinta".
Kuka na ke yi INA Neman gafarar Malam da Umma.
" Tashi ki shiga d'aki ki share ki zauna Allah yabi mana hakkinmu".
Tofa tun daga wannan rana ne Salma ta fara zawarcinta ya yinda ta fita a hanyar Zuly ko kusa bata shiga sabgarta.
★<><>★
Cikin bacci ta yi mafarkin Matar d'an nata wadda aka saka,tana Cewa "Umma me yasa kika rabu dani tsahon shekaru kika zab'i ki zauna ke kad'ai".
Cikin razana ta tashi tana dafe da k'irjinta,tunda ta saka Sooraj ya rabu da wannan yarinyar take mafarki da i'ta gashi yanzu duk ta rasa sukunin ta,tun y'arta tana jaririya ta Rabu da i'ta a sakamakon Auren Mahaifinta da ta yi ya sake aranar da ta fara nak'uda sanadiyyar haka i'ta kuma ta zab'i rabuwa da yarinyar saboda jin tsanar yarinyar ta ke har cikin zuciyarta bisa abinda Mahaifinta ya yi mata.
🤔Ni kuwa Ummu Maher na ce daman laifin uba yana shafar y'ay'a ne.
Oho umman Sooraj ta bani amsa.
Mahaifin Sooraj tun yana k'arami ya mutu,shahararren mai kud'i ne don haka ya mutu ya barta da dukiya mai yawa.
Shekarar Sooraj Tara9 ta samu Miji ta yi Aure shima kuma don kudinta ya Aure ta, shekara su biyu da Aure ta haihu shine fa ya gudu da duk wata kadarar da ta Tara.
Sai dai Allah ya taimaketa,bai had'a Dana Account d'inta ba.
Bayan shekara biyu kuma sai gashi ya dawo da wani mahaukacin kud'i Ashe shi d'an sarauta ne ya yi mata haka ne don ya jarabta ta.
Amman koda ya dawo ya tambayi y'arsa ko d'an sa ce masa ta yi babu rai y'ar tasa tazo.
Baiyi wani bincike ba tunda yasan halin Jamila wato matarsa yasan baza ta tab'a yi masa k'arya ba,sannan satinsa d'aya da dawowa ya kaita Bauchi don ya nunawa iyayansa matarsa daya Aura bayan da aka yi mishi kurciya ya bar gida, iyayansa sun aminta da i'ta suka yi musu fatan Alkhairi suka ci gaba da zaman Aurensu tsakanin mata da miji sai Allah.
Hajiya Jamila ta sharce wata uwar zufa da ta karyo mata.
Washe gari da sassafe ta shirya ta kirawo Sooraj,ta ce mai zai raka ta gidansu Salma,bai k'i ta ta ba saboda yana tsoron Mahaifiyarsa sosai.
Bayan sunje ne suka samu Mlm a k'ofar gida yana alwala.
By
*Real*
Ummu Maher ce✍🏻
👘🧚🏻♂️👘
*🌹A SANADIN ABAYAR SALLAH🌹*
👘🧚🏻♂️👘
*~Gajeren labari✍🏼~*
Na
*🌹Rabi'atu/B Abdullahi*
(Ummü Mãhër)Mïss grêên💚☘️
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
Ending✍🏼😜
31&32
Da mamaki Mlm ya ke kallon su duk da baisan Maman Sooraj ba Amman yasan Sooraj,bai nuna yasan su ba ya cigaba da alwarsa har suka k'ara so, Sooraj ne ya tsugunna har k'asa ya gaida Mlm Cikin ladabi kamar ba Sooraj ba,Umman Sooraj ma ta d'an rusuna kuma ko babu komai ya girme mata.
Mlm Ya ce"zanje Sallah ne na d'an makara"ya fad'i hakan yana gyara zaman bottle d'in rigarsa,don yana sane baice su shiga gidan ba,don Allah yasa ni ji ya ke kamar ya Zane su saboda yadda suka cuci yarinya marainiyar Allah.
Suna tsaye har ya fito daga masallaci,sannan suka zauna a tabarman da ke k'ofar gidan.
Har lokacin Hajiya Jamila bata ce komai ba tunanin ta ta ina zata fara,Sooraj kuwa kallon Momin sa kawai ya ke yi saboda ya matsu ta yi magana don yaji da wacce tazo.
Har lokacin kuma Mlm bai ce komai ba yana sauraron yaji da wacce tazo don ya lura mutanen suna da rainin hankali da kuma wayo.
"Mlm daman Na zo ne a game da matar d'ana,Ina zargin akwai wani k'ulli Wanda Allah ya b'oye,shiyyasa ma na tilas tawa d'ana ya saki Salma."
Da Sauri Mlm ya kalleta cike da matsanancin haushinta Amman baice komai ba,ba ya son ya katseta yafison yaji har k'arshen lamarin.
"Mlm tun da nake ko y'ay'a na ban tab'a basu wannan labarin ba sai yanzu,ta kai ga bana iya bacci tun ranar da naga Salma.
Nan fa Hajiya Jamila ta fara bada labari tun daga farko har k'arshe,tana yi tana kukan nadama da Dana Sani Wanda masu iya magana suka ce k'eya ce.
Shiru Mlm ya yi yana nazarin maganar ta,har ga Allah tun da Mahaifiyar Sooraj ta zauna ya ke hango tsantar kamannin da Salma suke yi da wannan matar.
Kuma babu shakka wannan itace mahaifiyar Salma Amman duk da haka sai anyi bin cike.
Baice k'ala ba ya tashi ya shiga gida don sanar da wannan maganar ga matar shi,Sooraj kuwa kallon Mominsu kawai ya ke yi yana