mamakin hali irin nata kayarda d'an da ka Haifa a cikinka.?
Koda Mlm ya shiga gida Salma ya samu tana wanke wanke,ya ce" Salma ta shi ki saka hijabinki zamu je unguwa ne?.
Da Sauri ta d'auko hijabinta ta zura Mlm kuma ya k'arasa shiga gidan.
Babu abinda ya b'oyewa Umma,ita ma ta yi mamaki sosai.
Koda suka fito waje Sai da gaban Salma ya yi mummunan fad'uwa Amman bata ce komai ba iya ka dai kallon banza da ta ringa aika musu.
Gidan marayu suka nufa inda gaban Salma da Mahaifiyarta ta cigaba Da fad'uwa,Momi tana tuno ranarda ta kawo y'arta cikin wannan gidan tun tana jaririya.
Straight office d'in mai kula da sashen sunayen yaran marayu suka i'sa.
Nan Mlm ya fad'a musu abinda ya kawosu,gaban Salma kamar zai fashe saboda tashin hankali
Babu b'ata lokacin aka dubo file d'in Salma da kawo kwanan wata sa kuma wacce ta kawo ta.
Nan Momi ta hango hoton y'arta ta d'auka tana kuka ya tabbata ce wa Salma y'ar ta ce.
Rungume Salma ta yi tana kuka Salma kuwa zama ta yi kamar wata gawa don gani ta ke yi kamar shirin film.
Mlm ma kukan ya ke yi nan ya war_ware wa Salma abinda ya shige mata duhu.
Suma Salma ta yi,nan fa kowa na wajen ya fara salati aka d'auki Salma sai asibiti.
Koda Salma ta farfad'o kuka ta ringa yi tana kiran sunan Allah,yanzu daman ba Mlm da Umma ne suka haifeta ba duk yadda suka rik'eta amana basu tab'a nuna mata ban_ban ci ba tsakanin ta da y'ar su.
Ga kukan rashin dacen uwa da ta yi,babu uwarda za ta tsani y'arta har ta yi tunanin jefar da i'ta,ranar dai haka Salma ta yini tana tunani.
Ko kafin A sallami Salma Alhaji yazo Mahaifinta da k'annenta Safiyya da Mohd.
Kuka sosai ya yi na hak'ntarsa da matarsa ta yi Amman a tsakanin miji Da mata sai Allah ya ya fewa Hajiya Jamila,su Mlm ma sun yafe mata.
Sai dai har yanzu Salma bata yarda da Mahaifiyar ta ba,Hajiya Jamila kuwa wani so da k'aunar y'ar ta,ta ke ji har cikin zuciyarta sannan tana nadamar abinda ta aikata.
Har kullum Neman yafiyar y'arta ta ke yi har sai da Mlm da Umma suka saka baki sannan ta hakura ta sakko tasan Allah ya kawo Mata Sooraj ne rayuwarta don komai ya gyaru,shiyyasa ma har tak'i Auren Bashir ta Auri Sooraj Yayanta sai gashi Allah ya taimaka babu abinda ya shiga a tsakaninsu hasa lima
Ko kwana agidan bai tab'a yi ba.
Koda Salma ta warware Alhaji Mahaifin Salma bai b'oye wa y'an uwansa komai ba sai dai ya ce musu an sace yarinyar ne aka kaita gidan marayu sai yanzu Allah yasa aka ganta,ya yi hakanne saboda kada su zargi matarsa.
Mlm yasa aka kirawo Bashir da Habiba don ya shaida musu abinda ke faruwa don yanzu y'an uwa kaf sun San abinda ya ke faruwa harma da mutanen gari kowa ya shaida Mahaifan Salma.
Koda Bashir ya koma gida wani Abu yaji yana mishi yawo a game da Salma son Salma sabo ne yadawo mai yarasa Wanda zai nema don ya fad'a mishi don harga Allah har yanzu yana son Salma ita ma Salma a nata b'angaren haka yake.
Ayanzu Salma ta koma wajen Mahaifanta Do haka Mahaifin nata ya zab'a babu yadda Mlm ya iya dole ya yarda don Mahaifinta yana da hakk'i akanta.
Tana jin dad'in mahaifanta har cikin zuciyarta yadda suke ji da ita ga k'annenta da Yayanta Sooraj shima yana kyautata mata Wanda ayanzu shima ya shiryu har ansaka ranar Auren su.
Abinda ban Sani ba tare aka saka ranarmu da Yaya Sooraj da Na'ima,ni kuma da Bashir.
Habiba ma tasan da zancen Auren kuma tasan ya halatta Bashir ya Auri Salma,tunda ba iyayensu d'aya ba kuma sune suka shayar da Salma ba.
Habiba tana yawan zuwa wajen Salma sushq hira gwanin ban sha'awa kamar yadda suke ada cen baya.
Kullum Mama na tana bani wasu abubuwa amman ni bansan na meye ba?.
da masu gyaran jiki na musamman nan danan na yi wani kyau da haske kamar ba niba,Momina har Habiba sai da tasa aka yi mata gyaran jiki sannan ta canza mata dukkanin kayan d'akinta, su Mlm suka dinga godiya.
Ana gobe d'aurin Aure gidan ya cika da bak'i,Mahaifina ya sanarmin da komai kuka na dinga yi INA tunanin yadda zan zauna da K'anwata Habiba.
★<><>★
Bayan Aure
Bayan y'an kai Amarya sun tafi Salma tana zaune kan makeken gadonta na alfarma Bashir ya shigo cikin da kakkiyar shadda gezna fara k'al shi daman gashi fari ga kyau da kwarjini,Ahankali ya yi mata Sallama ta amsa cikin voice d'inta mai dad'in sauraro.
Ya hayo kan gadon ya yaye mayafinta,sai da gabansa ya fad'i ganin yadda Salma ta koma kamar ba ita ba.
"Allah Nagode maka da wannan baiwa sa kyautar da ka yi min na Auren Salma."
Salma tana jinsa ita godiyar ta ke yiwa Allah da ya bata Bashir Namiji acikin maza.
Nan ya rik'e hannunta suka nufi sashen Habibq,itama taci kwalliyarta nan fa ya fara yi musu Nasiha mai ratsa jiki.
Koda suka dawo shida kansa ya dinga ciyar da Salma daganan zancen ya canza,koda Safiya Kafin su fito Habiba da kanta ta yi musu GIRKI ta kawo musu.
Salma tana lullub'e da blanket tana baccin wahala don jiya Tasha azaba,dak'er ta sakko taci abinci kamar zata yi kuka Bashir Da kansa ya wanke matarsa tas tare da tausaya mata,kuma yana gode wa Allah d'aya karb'i budurcin Matarsa ba wani ba.
To wannan kenan.
Rayuwa mai dad'i kuma mai cike da k'aunar junanmu Mike yi,bana k'aunar abinda zai b'atawa Habiba itama kuma haka,haka ma mjinmu yana yi mana adalci,
Allah sarki rayuwa a yanzu Bashir har gidan Maine dashi tsabar arzik'i.
Shekara ta d'aya na haihu d'a namiji Wanda Habiba ma tana da ciki wata biyu.
Matar Yaya Sooraj ma ta haihu Twins duk maza.
Zuly kuwa rayuwa ta juya mata baya yayinda da k'er ta samu Wanda ya Aureta Amman matansa 3ita ce ta 4.
To wannan kenan.
*Back to gidan Hamisu*
Zeenatu ta haihu Y'an biyu duk mata,Rabi'atu kuma ta haifi Namji sune zaune cikin aminci da k'aunar junansu.
*ALHAMDULILLAH*
Ana na kawo k'arshen wannan LABARI nawa na ASANADIN ABAYAR SALLAH.
Wanda fad'a karwa ce akan Matansa basu hakuri akan talaucin mazajensu da kuma y'an matan da suke raina arzik'in samarinsu.
Domin sharhi akan wannan littafi kuneme ni a wannan number.
07068606171
Sai na jiku.
Taku har kullum
*UMMU MAHER MISS GREEN*
Sai kun ji ni asabon littafina mai suna
*AISHATU HUMAIRA*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels