Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
Abba ya shige a fusace, ita kuwa Fiddausi sai hawaye ne yake zuba. Shi kuwa Mustapha sai ba ta hakuri yake yi, ya ce, "Ni ne na jawo miki ko me akai miki." Fiddausi ta ce, "Dama na gaya maka, kuma ga shi ka gani da idonka, ai ni ce zan ba ka hakuri, kuma ta ce ni barin gidan ma zan yi. Karshenta kuma duk sanda na shirya zan zo na gaya/maka, ko kuma ni na dunga zuwa tunda kai an hanaka zuwa, suka yi bankwana. Koda Fiddausi ta shiga cikin gida, sai Hajiya Gaji ta fara harararta sannan ta mikawa Alhaji bulalar da yake dukanta.. 34 Abba ya karba ya dunga bugunta sai da ya gaji. Tun tana kuk har ta daina. Bayan da gari ya waye ta yi wanka ta yi sallah yi addu 'a da Allah ya saka mata bisa abin da ake 'mata, bay ta shafa sai ta je gaban Abba da mai dakinsa ta durkusa ta gaishe su bayan sun amsa ta karbi kayan karin kumallonta dama tuni wannan dare ta shirya kayanta bayan ta kom dakinta ta karya, sai aka sami wani lokaci bayan rana ta dag sai Gaji ta ce zan dan kwanta, amma idan sha biyu ta yi to k dora abinci,, Fiddausi ta ce, to, Hajiya ta yi kwanciyarta abinta, koda ta dade da kwanciya sai Fiddausi ta dau kayanta ta gudu gidan kakanninta. Bayan ta dade da guduwa sa Hajiya Gaji ta tashi daga barci ta nifi bandaki ta wanke baki ta Kwalla karar kiran Fiddausi amma ba ta ji an amsa ba, Hajiya ta ji shiru ta ce lalle ta raina ni, a ce in sa ta girki ta y tafiyarta. To amma ta dawo ta same ni. Ta dora abincinta ha ta gama amma Fiddausi ba ta dawo ba, kuma ga Jamila ba ta dawo ba. Abin duniya duk ya dami Hajiya. Can sai ga Alhaj Abba ya dawo. A nan ne Hajiya take cewa ka ga yarinyar nar ta fita tun safe na sata aiki ta ki yi har yanzu ba ta dawo ba Ya ce wani gurin ta tafi? Ta ce yo! Ni na sani. Nan ya fusata ya ce duk inda ta tafi ta zo ta same ni haka suka kasance Abba da Gaji sukai ta zuba ido wai ko Fidausi ta dawo amma ina! Lamarin Fiddausi lokacin da ta bar gidan Alhaji Abba sa ta rasa inda za ta, ta dunga ttnani tana cewa ko naje gidan su Hajiya ko na shiga duniya, nan wata zuciyar ta ce bari kawa kije wajen Mustapha, nan ta nifi wajan masoyinta don t sheda masa cewar ita ta bar gidan Alhaji Abba saboda wahala ta isheta. Nan Fiddausi ta tafi, tana isa sai ta shiga, tana shigr cikin soro sai ta tsaya cak tana tunanin abin da za ta ce idan ta shiga. Sai da ta sami lokaci mai tsaho tana tunani akan shiga. Sanan ta shiga ta yi/sallama, Hajiya ta amsa sannan Fiddasi ta durkusa ta gaida Hajiya, Hajiya ta ce Fiddausi yanzu ke ce 35 kika zama haka ko bai da lafiya ne, a lokacin Fiddausi ta се lafiya kalau nake. Bayan sun sami lokaci matsakaici suna hira, a inda Fiddausi take amsawa Hajiya tambayarta da cewa abin da ya sa ta rame shi ne sharrin duniya da mutanen cikin ta, ta cе wallahi Hajiya wahala ce ta mai da ni haka ashe baba bai gaya miki ba. Ta ce ya gaya min amma ban tsammanin abin ya kai haka ba. Hajiya ta ce to yanzu ina za ki? Fiddausi ta ce ni kam na gaji da wahala, a gaskiya kuma ba tausayina suke ji ba don haka ni dai na bar gidan kenan, don haka na zo na shedawa Baba ni dai na yi gaba don ma kada hankalinsu ya tashi wajen nemana. Hajiya ta ce to yanzu gidan wa za ki? Fiddausi ta ce inda Allah ya kai ni, domin akwai randa na ce da Baba ya dawo da ni gidan nan ya ce a'a, wai saboda gudun kada jama'a su yi da shi su ce ya karbe ni daga gidan kanin mahaifina ya dawo da ni nan gidan. Don haka na san ko ya dawo mayar da ni zi yi, don haka ba zan bari ma ya dawo ba ina nan. Hajiya Tafada abin duniya ya yi mata zafi ganin yarinya karama an takura mata ga shi tana neman shiga duniya. Hajiya ta ce hakuri za ki, domin kin ga gidan Abba shi ne mutuncinki, don haka ni shawarar da zan baki shi ne ki koma watarana sailabari, Fiddausi ta ce da kin ga irin wuyar a nake sha da ba za ki ce in koma ba don haka wallahi ni dai kam ba zan koma ba, Bayan sun gama wannan magana sai Fiddausi ta ce Mustapha yana nan? Hajiya ta ce ai ya tafi kasuwa, sai an jima zai dawo, ya karbi abincin Alhaji, kin ga sai ki dakata idanya zo sai ku yi sallama don ni ma ina tausaya miki irin halin da kika shiga kuma Allah zai saka miki,Ttn a diniya bamasaian je can ba. Amma don Allah ko kin barnan, ki tafi gidan su Hajiya-mahaitiyarki, kada ki je ki fada mugun hannu. 36 Fiddausi ta amince da wannan batu, a haka suka yi ta hira, har ta gama abnci, ta zubawa Fiddausi ishasshe ta ci ta koshi, abinka da wandaba ya koshi sosai,koda ta gama cin abıcin sai ta yiwa Hajiya godiya, domin ta ji dadi sosai, bayan wani lokaci matsakaici sai ga Mustapha ya yi sallama ya zo daukan abincin Alhaji, yana shiga faki sai kawai ya ga Fiddausia a zaune ya ce Fiddausi yau ke ce a gidanmu, tun da Allahı ya yi wa Hajiya Zainab rasuwa sai yau, Fiddausi ta ce lafiyamana sannan ta gaishe shi ya amsa, Hajiyata ce ai zuwa yi bankwana domin ta gaji da zaman gidan Alhaji Abba, shi ne na ce baka nan ta dan dakata, Mustapha ya ce to yanzu ina za ta, Hajiya ta ce ni dai cewa na yi ta dakata ka dawo. Mustapha ya ce to yanzu ina zata? Hajiya ta ce ni dai cewa na yi ta yi tafiyar ta gidan kakanninta, don da cewa ta yi za ta duk inda Allah ya kait a, to shi ne na jiye mata kada ta fada wani mugun hannu. To amma yanzu ta yarda zata fin. A lokacin Hajiya ta basu guri, suka sake gaisawa, bayan wata gajeriyar hira, Fiddausi ta ce to ni zan tafi, Hajiya ta ce kifa je can. Fiddausi ta ce to, a lokacin Fiddausi ta ce don Allah Hajiya koda baba ya tambaye ki sanar da shi inda na tafi, kuma don Allah koda ya je kada ya ce ga inda na ttafi, Hajiya ta ce to in Allah ya yarda babu wanda zai sani, nan ta kawo kudi ta bawa Fiddausi ta amsa ta yi godiya, ta ce sai wata rana. Lokacin Mustapha ya rako ta har kofar gida ta ce sai yaushe Mustapha ya ce sai kin ganni domin na san gidan. Amma kwanan nan za ki ganni, suka yi sallama ta tafi, shi kuma ya koma gida. Al'amarin gidan Alhaji Abba kuwa, suna can suna sa ido a hanya amma shuru-shuru babu wanda ya san inda take ma balle ya ganta ma! Har yamma ta yi dare ya yi shiru, nan Abba da mai dakinsa suka gane cewar guduwa ta yi. Abba ya shiga nemanta amma ba inda bai neme ta ba makota amma ina shiru ba bayani. Abba bai yi katarin ganiba. Kash 'yanuwa makaranta wannan littafi nan zan dakata, sai mun hadu a 37 littafi na biyu. Za ku ji shin Fiddausi za ta dawo gidan Abba ko kuwa, kuma wai shin idan ta dawo Gaji za ta ci gaba da takura mata ko ko a a, kuma wanne mataki zata dauka don karekanta. Shin kuma yaya rayuwar Jamila da Jamilu za ta kasance, shin za su ci gaba da iskancinsu ko za su ladabtu. Kuma shin idan Fiddausi ta dawo Abba zai ci gaba da matsanta mata ko sausauta? Kuma batun su GIZAGO shin ballin zai tashi, ko ko asiri ne zai tonu? To don neman amsa nemi littafi na biyu `MAI RABON GANIN BADI NA BIYU, NA BIYU" Bissalam. 'Yar uwarku. (Hauwa A. Bashir A. Bashir Ayagi Kano State.) E * MASOYINA NA BIYU Nafisa! ta fito tana ganin Aliyu ta 6ata ranta, ta yi musu sannu da zuwa, ta ce me ya kawo ka gurina ka zo Aliyu ya се gluimki na zo, Nafisa ta ce kai Malam ka dakata a ji abin da zan gaya maka, ba na son mai sonka, to wai na ce ka rabu da ni, ko nima ruda ta zaka yi, kamar yadda ka rudi Kakata, to a nan ba ka ci nasara ba,to duk inda zaka ka fada cewar bana sonka Umar nake so!, dube ka fa kai ma ka san ban dace da kai ba, kawai dai hali ne irin na dan kaďafi. To ka nemi 'yar uwarka talaka, Nafisa sai Umar daga yau kada ka sake zuwa nan gidan, kadan kenan daga cikin MASOYINA NA BIYU na HAUWA A. BASHIR AYAGI. MASOYINA NA DAYA Nafisa ta numfasa a cehaske maganin duhu a gare ni hakikana saurari jawabinka kuma na yi na'am da shi don haka ina son ka kwantar da hankalinka domin kwanciyar hankalinka shi ne nawa, in Allah ya yarda ba zan ba da kai ba, za ka yi mamakina, nan ba da dadewa ba ta kara da cewa masoyina 38 sabulu ko Omo sun yi kadan komai tudu da nuyinsu su wanke sonka a zuciyata domin kafi gamsarwa a tsakiyar dandalin zuciyata, mai karatu nemi littafin don ka ji yadda ta kasance. HAUWA A. BASHIR AYAGI. * * SO SARTSE NA DAYA DaSAlimya isa gidanya kwankwasa kofa jimawa kadan kenan aka bude anabudewa Salima ya hada idoda SAMIHA ya kalleta sama da kasa ya na mamaki ko mafarki yake yi ko. kuwa SAMIHA ce, abin da ya faru gare shi, ita ma shi ya farugare ta. Tace Salimina bai sanma tana magana ba. KADAN DAGA CIKIN SO SARTSE NA BIYU Haire ta tashi ta ce me ya kawoka dakina? Salim ya rasa abin da zai ce (ya kasamagana). Haire ta kwallawa Malam Yusif kira, abinka da dare sauti yana tashi sosai. Malam Yusif ya ce, "Lafiya a wannan dare ake kirana?" Ya tashi ya fito, sai ga Salim Haire tana yi masa fada. Baban Salim ya shiga ya ce, "Lafiya na ganka a nan?"" Salim saboda bakin ciki ya kasa cewa komai ga shi dai ka gani da idonka in ji Haire da ba mutmin banza bane mai zai kawo shi dakina Malam Yusif ya ce ki yi hakuri ya kama hannun Salim suka koma. BAKIN CIKIN RAYUWATA NA DAYA Na ce Abalhasan tana jin na fadi haka, sai ta sake rushewa da kuka, sai ta ce min lokacin da muka tafi gidan Sarki Zalimu da shi bai dawo ba. Tana fadar haka sai na gigīce na kidime hankalina ya tashi na fito a fusace Maryam - tana kirana amma ko waiwayawa ban yi ba. Da na fita na tafi gidan sarki Zalimu a fusace a inda aka je aka gayawa Sarki 39 Zalimu na dawo, sai ya sa yaransa su zo sų kashe ni, ina cikin tafiya sai na ga motar gidan Sarki Zalimu ta yiwo kaina na kauce, na fa na dunga gudu motar tana bina, da Allah ya bani sa'a sai na kauce daga kan titti su kuma suka ci gaba da tafiya, sai na ga a cikin motar da aminin babanmu Lawan. Sai na ji jikina ya yi sanyi, sai ga motar ta dawo kusa gare ni sai na ji an jefo wani abu daga cikin motar kasa tim! Sai suka yi tafiyarsu ni kuma na karasa gurin wannan abun. Na bude sai na ga ashe gawar Abal Hasan ce, sai na kwalla kara na zama kamar mahaukaci ina ta surutai na fada kan gawar bakina yana kumfa. Kadan kenan daga cikin BAKIN CIKIN RAYUWATA NA DAYA. NA HAUWA A. BASHIR AYAGI * * * * BAKIN CIKIN RAYUWATA NA BIYU Lokacin da Gimbiya Kairiya ta isa 11ambun shakatawa ita da kuyanginta bayanta zauna suka kewaye ta suna ba ta labari mai dadi. Sai ga wata kuyanga ta yi sallama ta durkusa a gaban Gimiya ta ce,JABIR neya ce na fada miki ya zo." Gimbiya KAIRIYA ta yi murmushi ta ce, "ya shigo." Yayin da ta sallami sauran kuyangi. Bayan sun fito suka ga JABIR suka gaishe shi ya amsa. Gimbiya KAIRIYA ta ce, JABIR na ce duk lokacin da ka zo ka shigo amma kaki. JABIR ya yi murmushi ya ce ki yi hakuri. Kadan kenan daga cikin littafin BAKIN CIKIN RAYUWATA na biyu kenan kada ka bari a barka a baya. * * * * * SO A AJIYAR ZUCIYA A'isha ta ce Muhammad duk lokacin da ban ganka ba hakalina tashi yake yi ga shi zaka tafi karatu ka bar ni. yau 40 yaya zan yi da rayuwata, yayin da hawaye yake zuba daga idonta, koda Muhamad ya gani sai hankalinsa ya tashi yayin da ya dauko wani kyalle daga aljihunsa yana share mata, yana cewa ni ma ba a son raina zan tafi na barki ba, amma zan rike ki kema ki rike alkawari......nemi littafin SO AJIYAR ZUCIYA don jin sauran bayani. NA HAUWA A. BASHIR AYAGI. * * * * * RAYUWAR SOYAYYA Sai ta leka ta leka ta ganshi a wannan hali ta ce lafiya me ya same ka ABAL KASIM ko baka da lafiya ne, ya ce Baba wallahi tunanin SAFIYA nake yi, ASIYA ta ce wacece SAFIYA,ya ce 'yar gidan kwamishina Jafar ce, ASIYA ta ce me ya hada ka da ita, ya ce ai ita nake so. ASIYA ta yi salati ta ce kada ka jawo mana masifa da bala'i muna.....nemi littafi RAYUWAR SOYAYYA don jin yada zata kasance. NA HAUWA A. BASHIR AYAGI 41 Fiddausi ta gaya mata dukkan abin da take ciki, a nan ne Bilkisu ranta ya yi mutukar Gaci ta ce babu komai duk mutumin da ya cuci wani to Allah zai saka masa komai dadewa. Bare ma ke da kike marainiya. Ina za su kai hakkinki." Ta сe, "To amma yanzu idan na koma zan sanar da Mama da babanmu koda yake ba su da iko dake, to amma sa yi magana a sassauta miki don jin irin wadannan nasiha ba jinata suke ba.""Irinsu ne masu aure don samun gado ba sunna ba ita Gajin. Shi kuma Abban irin su ne masu halakaka don su samu a gareka. Tur Allah wadai da irin wadannan mutane. A lokacin ne Bilki ta mike ranta a 6ace - tana cewa ni zan koma sai an kwana biyu, Fiddausi ta kale ta idanunta cike da hawaye ta ce, to Yakumbo ki gaida gida kuma ki gaishe min da 'Kudisiyya" da "Mahsusu" da kyau. Kuma don Allah duk lokacin da za ki zo ki taho min da su. `Hajiya Bilkisu ta fito ta yi sallama da su ta koma gida. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4