Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
ya je ya shedawa sauran rasuwar Alhaji nan da nan sai kowa ya kama salati da yi wa Alhaji addu 'a, Alhaji ya zo sa'i. Sai kowa ya kama kuka. Abbas ya koma daki ya yiwa Alhaji Hamisu waya ya sheda masa rasuwar Alhaji, bayan ya gama sai ya ajiye waya, ya shiga gida, lokacin da ya shiga ciki Hajiya ta dukufa tana addu 'a, ya yi sallama Hajiya ta katse addu 'a. Ta nufi kofa da sauri sai ta ga Abbas! Ta ce yaya Abbas, sai taga yana kuka, ta tambaye shi lafiya, ya ce dazun nan Alhaji Abba yai yo min waya ya shaida mini cewar Allah ya yiwa Alhaji rasuwa, nan da nan Hajiya ta dafe kirjinta tana y in kuka tana mai yi wa mijinta fatan Allah ya jikan mijinta, ta ci gaba da yin kuka mai tsanani hade da yin salati ga Annabi (SAW) koda 10 Fiddausi ta tashi daga barci sai ta ji mahaifiyarta tana kuka sai ta tambayeta, nan ma Hajiya ta sake 6arkewa da kuka. Fiddausi ta sake tambayarta, sai Hajiya ta sanar da Fiddausi cewar mahaifinta ne ya rasu, nan da nan Fiddausi sai ta dunga fashewa da kuka, kuka kuma har da shidewa, har ya kasance ta shiga wani hali. A wannan lokaci ne da Hajiya taga 'yata ta shiga wani hali, sai ta dunga yi mata addu 'a tana shafa mata a fuska da haka har ta farfado, a wannan lokaci ne zazzabi kuma ya ru feta, to Allah ya sauwake lamarinsu kenan. To ama shi kuwa direba Abbas kuwa lokacin da ya fita saı ya zarce gidan limamin masallacin kofar gidan ya sanar d shi labarin rasuwar, liman ya yi ta jimamin rasuwar sannan ya yi masa addu'a, da sauran magabata, sannan ya gayawa ladan cewar idan ya yi kiran salla ya sanar da rasuwar Alhaji Bello, Abbas kuwa bi ya yi ta yi ko ina yana sanar da labarin rasu war Alahji Bello., Nan da nan ladan shi ma ya dunga yi wa Alhaji Bello addu 'a, koda lokacin kira ya yi bayan ya yin kira sai ya fadi rasu war Alhaji Bello kowa idan ya ji sai ya yi ta yi addu 'a gare shi kasancewarsa mai adalci ga jama'a ga shi Musulmi. Bayan da aka idar da sallar asubahi sai kofar gidan Ahaji Bello ta cika makil da jama'a can bayan karfe biyar da rabi sai ga gawar Alhaji Bello da dubban jama'a ana tafe ana ta zikiri da Hailala, yayin da aka shiga da gawa cikin gida jama'a akai jigum ana ta tunaninsa, bayan da aka kammala yi wa Alhaji Bello suttura aka fito da shi don a yi masa sallah bisa ka'idar Musulunci, sannan bayan da aka gama sai aka nifi makabarta da shi inda aka yi masa addu 'a da fatan Allah ya ji Kansa, sannan aka rufe shi aka sake yi masa addu 'a. Bayan an idar jama'a suka juya gida domin karbar gaisuwa, nan da nan labari ya game dun nahiya game da labarin rasuwar Alhaji Belo, jama'a sai zuwa suke ta yi don yin ta'aziyya, jama'a zuwa suke ba su fasa ba har daga kasar waje, koda aka sami kwana bakwai ana ta zaman makoki, sai aka tara malamai aka Π sauke masa Kur'ani mai tsarki, bayan, bayan an kamala jama'a suka koma harkokinsu na yau da kullum. Allah Sarki dukkan mai rai mamaci ne, Allah ka sa mu cika da Imani, mu tashi da Imani, da haka dai har Alhaji Bello ya cika kwana arba'in aka yi masa fidda'u, a wannan lokaci ne Alhaji ya dunga hura wutar a raba gado a bashi hakkinsa. Jama'a kowa ya ji sai ya dunga yin Allah wadai da halinsa da rashin Imani irin nasa. Haka lamarinsa ya dunga tafiya ckin murna don samun gado ba wai jimamin rasuwar yayansa ba Bayan da aka dauki lokacin magajarci Alkalai suka duba duk kayan da Alhaji ya bari, kasancewar dukiyarsa da y awa, nan dai su ka raba aka bawa Abba nasa, matar Alhaji nata, sannan Fiddausi, Alhaji Abba bai ji dadin rabon da aka yi ba, domin a cikin Kamfarin ba a bashi ko daya ba, don kuwa saboda su ya tada hankalinsa shi ne yake ta bakin cikin wadannan Kanfanonin don bai same su ba, don haka sai ya dunga shiga malamai don su yi wani abu akai to amma ina Allah bai nufa ba, domin shi Allah ba azzalumin Sarki bane, kuma ya san manu farsa. Don haka bai yadda da al'amarin Abba, haka Alhaji Abba ya yi ta bawa Malamai da 'yan bori kudi suna shan gara, shi kuwa yana ta hauka wai sai ya karbi kamfanoni, don haka Alhaji Abba ya yi ta asarar kudinsa kai na takai ce muku labari, haka kuma duk abin da ya samu sai da suka kare, hatta abin da yake da shi sai da ya kare, sannan ya hakura. Kai Allah ya kare mu da azzaluman mutane irin wadannan amin. Bayan shekara daya da rasuwar Alhaji Bello! Sai Alhaji Abba ya dawo babu tsiya ba arziki dukkan abin da ya mallaka sai da ya kare wato ya kasance abin cefane ma sai da ya gagare shi. Don haka ya kasance wani lokaein sai ya yi maula yake samu, wata rana Abba ya yi yawo har ya gaji amma bai samu ba sai ya tsaya yana shawarar cewa ko zuwa gidan Hajiya Zainab zai yi ko zai sami wani abu, a inda yake cewa 12 anya kuwa naje! domin tun da aka bani rabona na daina zuwa gi dansu. Can dai ya yanke shawarar cewar bari ya je gidan, don ya san Hajiya Zainab ba mai wulakanci ba ce, mai yiyuwa ya dace, haka ya kama hanya ya nifi gidan ba ko tsoron Allah. Koda ya isa gidan ya yi sallama Zainab ta amsa a inda ta leko ta ga mai sallamar, sai kawai ta yi ido hudu da Abba, nan dai ta yi masa maraba kasancewarta mai kirki da rashin riko, nan dai ya shigo, Hajiya ta ce zauna, ashe talaka na ganinku yayin da Abba ya nitse a gujera yaa mai murmushi ya ce Hajiya ina wuni, ta ce lafi ya lau, ya ce yaya Fiddausi Hajiya ta ce tana makaranta ba ta dawo ba, Hajiya ta ce ina su Jamila da Jamilu, da Gaji ya ce suna nan kalau, ta ce yaya harkoki ina Abba ya yi shiru, Hajiya ta ce lafiya na ga ka yi shiru. Abba ya ce lafiya amma ba lau ba, yayin da Hajiya Zaináb ta gyara zama ta ce mene ne ya faru, Abba ya gaya mata komai bai ko rage wani abu ba Hajiya ta tausayawa Abba ta ce Allah ya sauwake, suna cikin hira da Abba akan matsalar da ya shiga, sai Fiddausi ta yi sallama, ta ga Abbanta sai ta durkusa ta gaishe shi cikin ladabi da biyayya ta ce Alhaji ina jamila da Jamilu Alhaji ya ce Fiddausi 'yan makaranta y aushe ne za ki wajan Jamila ta ce sai an kwana biyu a lokacin ne ta ce Abba ya na daina, ganin Jamila a makaranta ne ko ba ta da lafiya ne. Abba ya ce za ta je ne, haka dai suka yi ta hira har wani lokaci, nan Alhaji Abba ya ce Hajiya ni zan tafi, sai an kwana biyu. Hajiya ta ce bari na zo ta shiga ciki ta dauko bandir din kudi na wazobia ta bashi, nan ya yi matukar farin ciki tare da godiya, sannan ya tafi a inda Hajiya take cewa ya gaida Gaji ya ce sa ji, nan bayan fitarsa Hajiya ta zauna tana tunanin Abba da yadda duniya ta yi wancakali da shi, nan take ta godewa Allah da ya rufa mata asiri. Lamarin Alhaji Abba kuwa bayan da ya koma gida da kayan miya, yake gayawa Gaji yadda suka yi da Hajiya 13 Zainab ,ya ce ban yi tsammani za ta karbe ni hannu biyu ba, amma abin ya bani mamaki dormin ya kasance ta yi murna da zuwana, Abba ya ce hata fi da kyau, domin ko lokacin da Alhaji yake da rai ta fi haka yanzu, Gaji ta ce to mai zai hana ta yi kyau ta sami kudin gado, tana siyen abin da ta ga dama, Alhaji Abba ya ce ba ki ga yadda raina ya baci ba da naga gidan yana nan yadda yake ba. Kuma komai kika sani yana nan yadda yake ba wani haufi, ita kuwa yariny ar nan Fiddausi ta yi kyau idanunta kamar madara don yanzu ta fi Jamila komai babu mai hada su, ya ce kin san da ba ta fi Jamila komai ba, ba ki gani ba an yi wanı kitso gashinta ya zubo har gadon baya abin abin ban haushi, don ba ki ga yadda Fiddausi ta zama ba, kuma na yi matukar bakin ciki da naga Fiddausi har yanzu wata matsala ba ta hana ta zuwa mąkaranta ba, wai har take cewa ba ta ganinsu Jamila a makaranta ko ba su da lafiya ne, bayan ko ba ta san kasa siya musu littafi na yi ba shi ya sa. Gaji ta ce to me ka ce da ita ya ce cewa na yi lafiyarsu lau za su je ne Alhaji Abba ya ni kam Gaji na gaji da talauci da bakin cikin duniya, Gaji ita ce to yanzu ya ya za mu yi hakuri ya kama ta mu yi, ta ce domin idan ba hakuri ba, ban ga yada za mu yi ba, Alhaji Abba ya ce to ai da ni so nake Fiddausi ta dawo hanunmu, Hajiya ta ce babbar magana wai dan sanda ya gawar Soja. Abba ya ce ai ba don komai neke so ta dawo ba, sai don na ji labarin akwai kudinta masu yawa a banki, kuma duk shekara hukumar banki tana ware mata riba mai tsoka. Kuma wannan munafikin shi ne yake karbowa. Hajiya ta ce waye? Alhaji Abba ya ce Hamisu mana. Ke baki ga cewar ubanmu daya da Alhaji Bello ba! Amma sai ya ki bani amana ba ya bawa wani amininsa, daman kin san an ce naka shi ke ba da kai, yanzu kin ga duk inda na shige sai an yi da ni ana ganin cewa ni macuci ne, tunda dan'uwana bai yarda da ni ba, ga shi ya bawa wani amana, amma ni ko ohu. Hajiya ta ce dama na gaya maka, to yanzu ba gashiba. Amma 14 raına idan ya yi dubu ya Gaci, Hajiya ta ce yanzu wacce dabara kake da ita, ta dawowar Fiddausi gidanmu ni dai na san da cewar idan dai Hajiya Zainab tana da rai na tabbata ba za ta iya rabuwa da ita ba kuma ai ko shari'a ba za ta iya ba ka ita ba balle ma ka ce za kai Kara/da dai ba 'yarta ba ce za'a iya baka domin kaine madadin mahaifinta, a wannan lokaci ne Abba ya ce lallai ku mata ku aka sani da dabara da hikima yanzu ke baki da dabarar da za ki yi, Gaji ta fan yi shiru sannan ta ce, dillaliya ta bani labarin cewa a kullum Hajiya Zainab tana shiga lambu da yamma da ita da Fiddausi a nan suke shakatawa kuma babu wanda ake bari ya shiga sai da izini, bayan gurin lungu ne babu wanda yake shiga, ka ga ai sai a bi ta nan a shiga babu wanda ya sani, ka ga sai ką nemi fitsararrun yaran nan su GIZAGO a yi tsada da su su kashe ta. Ai dole Fiddausi ta dawo hannunka, kuma ka gargafe su idan za su su badda kama do min kada a gane su kada su tona mana asiri ko ba za ai nasara ba, bale ma na san za'ai. Hajiya Gaji ta ce ka ji hikimta, yayin da Alhaji Abba ya yi murmushi ya ce shi ya sa nake sonki wajan iya makircinki, ya ce daman ai su GIZAGO su ke kashe mutum a banza bare ma a basu lada. Allah Sarki Allah ya raba mu da son abin duniya amin. Yanzu saboda dukiya suke ta kulla wannan mugun aiki. Haka su ka ci gaba da hira ai inda Hajiya Gaji take cewa to yanzu yaushe zaka nemi su GIZAGO din don ka sanar da su bukatarmu domin ya hanzarta. Abba ya ce sai gobe da safe zan neme su a majalisarsu. Gaji ta ce to Allah ya nuna mana, Allah Sarki Hajiya Zainab, tana zamanta. ana nan ana kulla mata sharrin da bata ji ba bata gani ba. Babu kuma mai kubutar da ita sai Allah, kada gari ya waye Alhaji Abba ya yi wanka ya kintsa ya sanar da Gaji cewar zai tafi, ta ce Allah ya sa ai nasara ya ce amin, Koda ya isa inda su GIZAGO suke yana zuwa ya yi sa'a ya same shi amma sauran basa nan. Gizago ya hango shi, ya co, kai wannan KARFANFANA FA! 15 Sai Alhaji ya ce zo man, sai Gizago ya ce mai zan zo na yi ma, yanzu KUNKURU ya ci mutum fa! Bana son NAЛ YAMU FA! Nan dai Abba ya ce haba Gizago lafiya mana wata alfarma nake nema, ta me fa! Abba ya ce to zo mu kebe mana, nan dai su ka kebe, Abba ya kwashe labari ya sanar da shi, ya ce yaya ka gani? Gizago ya ce wannan abu ne mafi sauki a wajanmu, to amma kasar aiki ne mai hatsari don J'AL! me za ka bamu? Alhaji ya dan yi shiru ya ce to fadi abin da zan baku mana, Gizago ya ce to kaga bani kadai bane don haka du bu talatin zaka bamu ka ga kowa sai ya dau dubu gema, goma kenan, ko Alhaji Abba ya ji sai ya ce haba Gizago, ka san fa yanzu ba harka fa sosai amma da a ce da ne da na baka ba tare da na nemi ragi ba amma ka sausauta, karbi wannan kudin kuma idan har bukata ta biya to kaga gidana na baku shi. Gizago ya ce to. Gizago ya ce kar na yi maka rana kat min dare, kai ma ka san ba za ka ji dadi ba. Abba ya ce aba Gizago ai ba trinku ake yi wa rashin mutunci ba, а okacin Abba ya ce na gode, ya kawo Naira dubu goma a irin Kudin da Hajiya Zat bashi ya bawa Gizago ya karba ya ka ga kullum tana wannan lambun kaga ko yu ka iya aikata aikinsu in kuma ba'a sami dama ba sai gobe sai kuje, domin ka ga su NAMUZU sun tafi farauta kuma sai da magariba za su dawo. To amma goben zamu aikata, kada ka ji komai. Abba ya yi murmushi ya ee ya yi (Gizago, na fa gode Allah ya taımaka yayin da Abba ya ce sai an jima Gizago ya ce to, har Abba ya yi nisa! sai ya dawo ya ce idan zaku fa ku yi badda kama, Gizago ya ce ai-babu damuwa, nan ya tafi shi kuma ya koma inda suke shaye-shayensu. na marasa jin magana ksda Abba ya koma gida. Hajiya Gaji ta yi masa barka da, uwa ya amsa a inda ta kawo amsa koko da kosai ya durka. sat abba ya kwashe labarin duk yadda suka yi da su Gizago ya gaya mata lamarin su kenan yadda ya kasance. 16 AFamarin su Gizago kuwa lokacin da su Namuzu su ka dawo daga farau ta, sai ya basu labarin zuwan Alhaji abba da kuma bukatar da ya neme su da su ya nuna musu kudin da kuma alkawarin gida da ya yi musu, lokacin da DANDARE ya ji wannan labari sai ya mike da murna ya ce lalle mur, warke ko yaya ka ce NAMUZU! Ya ce kwarai kuwa yayin da suke zukar sigari a bakinsu suna fitar da hayakin ta hanci, suna cowa komai ya yi daidai da gari ya waye yamma ta yi, susa shirya suka nifi gidan Abba doai n su gaya masa cowsun tafi koda suka isa, suka yi sallama suka yi sa'a yana orkayan jimawa kaſan ya fito, koda ya gansu ya yi muzmushi ya ce Gizago Sarkin himma har an fito, Gizago ya ce amma ba vanzu zamu sake kama ba sai mun je loko domin Kat a garua san abin da mu ke ciki Abba ya amince, koda endan marigayi Alhaji Bello, sai suka haura ta 小 bu seka dua a hankali suka buya a bayan .n ayaba a wannan lokaci ne kowane ya sa fuska ta rashim Ima ni, a lokacin Hajiya Zainab, tana zaune tana karatun Al-Kur am mai tsarki. A lokacin, Fiddausi ta koma gida don dauko. w.asu littattafan na addinin Musulunci. bayan da su Gizago suka gama shirin sai suka shiga bayan lambu a hankali. suka yi sa'a suka yi ta suka bi ta bayan Hajiya Zainab. ita kuwa Hajiya ta mai da hankalinta kan karatun da take yi don kuwa ko motsinsu ba ta ji ba yayin da suka isa gareta sai Namuzu ya yi hanzari ya rufewa Hajiya bakiu da hanci don kada ta yi kuwwa a kawo mata dauki, shi kuia DANDARE fito dà wata sarka ya shake Hajiya wadda suke faure kainukan su da ita, shi kuma Gizago ya zage tun karti sai nausar cikinta yake yi. Hajiya sai shure-shure take yi tana neman Ganbare İnamnun Namuzu anma ina, suna cikin haka sai suka ji motsi. nan da nan Gizago ya Ishi ya buya a cikin gwandojin da yake nwotsin. Allah Sarki Fiddausi bata san irin halin da 17 Amma a can gidan Alhaji Bello kuwa tuni 'yan sanda da manema labarai sun hallara ana ta daukar hoton gawar Hajiya bayan gama Alhaji Abba sai matsematsen i do yake! amma a ransa murna kawai yake yi, bayan nan ne sai aka dauki gawar hajiya aka kaita asibi tin kwararru na `MURTALA MOHD don yin binciken gano sanadiyar rasuwar ta. Sanda za'a tafi Abba sune kan gaba, ka ji munafuki wanda shine sanadiyar mutuwarta jama'ar unguwa sai salati su ke suna yiwa Hajiya addu 'a da fatan Allah ya tona asirin mutanen da su ka yi mata haka. Bayan sun isa ne likita ya dubata ya gama yin bincike a tare da ita, a inda ya gano cewar Hajiya dai wata guba aka sheka mata har ta rasu. Ya mika sakamakon binciken da ya yi sannan 'yan sanda su ka nada hukumar bincike ta gaggawa ga wadanda suka yi wannan danyen aikin, a lokacin ne ya roki alfarma da a ba su gawar Hajiya don ayi mata suttura, bayan sun y i cirko-cirko, sai aka basu suka taho da gawar gida Koda hukuma ta tambayi iyayen Hajiya ko za su shigar da kara sai suka ce su a'a sun kai kara gurin mai du ka wanda baya zalinci kuma ya haramta zalunci a tsakanin ba yinsa (ALLAH). Sannan suka yi bakin ciki da rasuwar diyarsu mai kula da su suka kuma yi mata addu 'a, nan akai wa Hajiya wanka akai mata suttu ra akai mata sallah aka kaita kabarinta da fatan Allah ya jikanta ya wa bakin wahalar kenan amin. Bayan an yi zaman makoki na kwana bakwai Fiddausi ta fara samun sauki, aka yi wa Hajiya addu'a kowa ya watse, a inda iyayen Hajiya suka ce su za su ta fi da Fiddausi, Alhaji Abba ya ce shi sam ba za su tafi da ita ba. Yana da ran amma za su tafi da ita da fa ya mutu ne in ji Abba! da sai ku dauka ama tunda yana da rai shi zai dauke ta. Don a fadarsa shi da Alj ji Bello duk daya ne, don haka ba inda za ta, kakanni Fiddausi su ka ce to Allah ya raya ta! amin in Abba. Bayar wata uku da rasuwar Hajiya Hukumar bincike ta gano da hannun Gizago a kisan da aka yiwa Hajiya don haka aka 19 kamo shi aka tsare, aka yi tuhumarsa amma don tau rin kai ya ki fadan yadda aka yi, balle ma ya yi bayanin su NAMUZU da DANDARE, lamarinsa kenan. Alhaji Abba kuwa shi duniya sabuwa domin gidansa wanda yake cikai ya ci kawa su GIZAGO alkawari da kuma sau ran cikon kudinsu, sannan ya hada ya nasa-yanasa ya koma gidan Alhaji Bello marigayi, bai ko jima da komawa ba sai duk ya kori ma'aikatan gidan yasamu wasau sababbi Fiddausi ta ci gaba da zamanta a hannun BAFFANTA, wato macuci Abba, da ku ma 'yan uwanta Jamila da Jamilu su ka ci gaba da zama da 'yan uwanta suna tafiya makaranta, Yayin da Fiddausi ta cika shekara sha biyu, kuma a wannan shikara ne za ta shiga sikandire wanda a wannan shekara ne aka fara canza mata hali. Wanda a da ba haka ake mata ba, kuma Alhaji Abba ya sami sakewa don ko neman abinci ba ya zuwa don ya san akwai a sama, wata rana Fiddausi ta shirya za ta tafi makaranta, sai Hajiya Gaji ta ce maza ki ajiye jakar nan ki zo ki yi mini shara da wanke-wanke Fidausi ta ce don Allah hajiya ki bari sai na dawo, kin san yanu na tsaya makara zan yi kuma ban saba ba, Gaji ta harari Fiddausi ta ce lalle kin rainan ni haka kike cewa ma sai kin dawo za ki yi min aikin da na saki ko, Gaji ta ce to bara na fada miki makaranta ba za ki ba kuma ki je na gani, da Fiddausi ta ji haka sai ta yi bakin ciki. tana ta yin hawaye, ba wani abu ne ya sa Fiddausi take kuka ba illa a gabanta Alhaji Abba ya sa Jamila da Jamilu a mota ya kai su, amma ita da kafarta an ce ba za ta ba. Allah Sarki Fiddausi babu yadda zata yi haka ta dau kwanuika tana ta wankewa tana kukan bakin cikin rashin zuwanta, makaranta. yiniyin da Abba ya shigo sai ya tambayi Gaji ko lafiya Fiddau si take kuka, sai ta ce ashe kuka take yi, don na sata wanke-wanke, sai ta zo kusa da Fiddausi ta ce don Allah ki fashe ko ki narke don kuka, aiki ne yanzu kika fara shi a gida..an, kuma ko ba kya so sai kin yi, shi kuma Abba 20 nan dama ni ce na dakatar da ita do min ya dan huta tukuna. sai suka fito da ita da Fiddausi, koda suka zo gare shi Fiddausi ta durkusa gare shi ta gaishe shi cikin ladabi da biyayya da yake Fiddausi yarinya ce mai hankali ba ta nuna wa Alhaji Hamisu abin da take ciki ba yayin da ta zauna kan kujera amma da Alhaji Hamisu bai zo ba ko kusa da kujerar ba ta isa ta zo ba. Kuma bayan ta san kujerar gidannan na mahaifinta ne, saboda an fi karfinta shi ya sa ake mata iko don haka kome na gidan ba ta iko da shi, amma idan aka ce su Jamila da Jamilu ne sune masu iko da kayan gidan domin sune 'ya'yan masu gidan na yanzu, ku ma sai su yi abin da suka dama da kayan gidan Alhaji Hamisu ya ce Fiddausi baba ya ce babu abin da yake damunki ni kuma na ga bakya walwala, Fiddausi ta ce "E, babu abin da yake damu na," Alhaji Hamisu ya ce, na ji dadi, to yanxu me kike so na baki?" Ta yi dan shiru can sain suka hada ido da Hajiya Gaji sai Fiddausi "E, da ma kudi ne bani da shi," ko da Alhaji Hamisu ya ji haka, sai ya bude akwati ya debo mata kudi masu yawa, ta sa hannu biyu ta karộa. Yayin da ya ba da takarda ta sa hannu ta karbi kudi, Alhaji Hamisu ya yi wa Abba da mai dakinsa godiya bisa wannan amana da suka rike, Abba ya ce haba Alhaji mene ne abin godiya ai Fiddausi 'yar mu ce idan ban rke ta ba waye mai rike ta, Alhaji ya ce gaskiya ne, ni zan koma sai an kwana biyu. Fiddausi ta c e to baba ka gaida gida da su Hajiya da Mustapha. Alhaji ya ce to sa ji da kyau, Abba ya ce bari na dan taka maka, inda suka fito tare ya shiga cikin mota shi kuma ya koma cikin gida, ko da Abba ya shigo cikin gida sai shi da mai dakinsa suka kwace kudi daga hannun Fiddausi. Gaji ta ce maza ki koma ki mayar da kayan jikinki ki aji,e wannan. Fiddausi ta ce, don Allah Hajiya ki bar mini wadannan, kin ga wadancan sun yi dauda, kin ga sai na wanke su, wayyo! Ka ji yarinyar da bata saba da wanki ba, amma saboda rashin imani na Abba da mai dakinsa da bakar 22 ta wahalar da suke bata, har Allah take hada su da shi abarta yi wanki don gudun zama cikin dauda, amma hakan ya ci tura. Gaji ta kalle ta bawai yayin da ta dauke ta da mari, ji kake kas! Wai ita ranta ya 6aci, Fiddausi ta rike kunci tana kuka, duk da haka Gaji ba ta rabu da ita ba maimakon ta yi nadama, sai ta kama zanin ta kwace dan-kwalin da mayafin, sannan ta hankade ta ta fadi har ta fasa goshi, lokacin ne Fiddausi ta fashe da kuka ta nufi dakin marigayiya Zainab ko da Gaji ta ga haka maimakon ta yi nadama ta kuma nuna cewar fa ita ma tana da 'ya'ya ba ta san hannun wanda za su fada ba. Kawai sai ta ce da Fiddausi ki tube rigar jikinki katin na shigo dakin nan. Lokacin da Fiddausi tana kallon hoton marigayiya wanda yake kan kanta bas" nan Fiddausi ta sake fashewa da kuka yayin da take yiwa Hajiya addu'a, kuma ta kewa kanta addu'a da cewar Allah ya karbi ranta ko ta huta da bakin cikin wannan gida. Bayan ta gama kukan ne ta share hawayenta, ta nemi kyalle ta share goshinta ta daure. Nan da nan Fiddausi zazzabi ya kamata da ciwon kai, amma saboda rashin Imani babu wanda ya kula da ita, bayan ta sami mako daya a kwance cikin rashin lafiya, Allah ya sauwakę mata, kuma Hajiya Gaji ta ci gaba da azabtar da ita, don haka duk kayanta sai da Hajiya ta karbe

Chapter 2 of 4