Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
ta bawa 'yarta Jamila, sai kadan ta bar mata. Wata rana Fiddausi ta yi wanka ta daura atamfa 'yar Holand, ta fara kodewa kaďan don bata da kaya, bayan ta gama daurawa, sai ta dau abin taje kai daman nata ne, sai ga Jamila nan sai ta ce Fiddausi ban Kum zan taje kai, sai Fiddausi ta ce bari na Karasa. Sai Jamila ta fita a fusace ta je ta ce da Hajiya, "Kin ga na ce da Fiddausi ta bani kum na taj e kaina, ta ce wai sai ta gama nata ko!" Ka ji shagwababbiya da sharri, dama kun san an ce Barewa ba za tai gudu ba kuma 'yarta ya kasace ta yi rarrafe lalle Bahaushe ya yi gaskiya. Koda Hajiya ta ji, sai ta ce yanzu Fiddausi ta hana ki, to dama 23 Jamilu yana fakin a zaune, sai ya mike tsaye ya ce mu je, sai kawai suka dunguma zuwa dakin, bayan da suka isa dakin ne sai su ka ga Fiddausi tana taje kai. Dama idan mai karatu bai manta ba, na sanar da ku cewar Fiddausi yarinya ce mai yawan gashi. Shigarsu kenan sai Gaji ta daka wa Fiddausi tsawa, har madubin da yake hannunta ya fadfi ya fashe. Hajiya Gaji ta kwace kum din dake hannunta, dama wannan shi ne Jamila ta ce ki bata kika hana ta saboda isa da mulki,don wannan tsinannen gashin naki, mai kama da uwar makera. To bari ki ga gashin ma yanke shi zan yi na ga abin da za ki, ta je, Fiddausi ta ce don Allah ki yi hakuri, don Allah ki ba ni idan na gama na bata. Hajiya ta ce sai kin gama ma za ki bata, Jamilu ya ce wai don Allah me ya sa kika taya sau raronta ne Hajiya! Ai kawai ki yanke gashinta a raba fada. Hajiya ta ce gaskiya ne. Jamila da Jamilu suka bintsire Fi ddausi, su ka danne ta, Gaji ta dau almakashi ta yanyankewa fiddausi gashi ta ce,` Gobe ma kya sake,." Nan da nan dai suka yi ta yi wa Fiddausi dariya da gwalo. Fiddausi tana ta kukan bakin cikin da ba zai misaltu ba. Dalilin da ya sa Gaji ta yanke wa Fiddausi gashi shi ne saboda 'yarta bata da shi sosai, ka ga kenan za'a kirawao h akan da su na (HASSADA) kuma to ai 'MAI RABON GANIN BADI KO ANA DAKAWA A TU RMI SAI YA GANI.' Fiddausi ta ci kukanta ta koshi ta share hawayenta ta ci gaba da harkokinta. Koda gari ya waye, ta yi wanka ta yi sallah ta karya kumallo ta gai da Gaji da Abba sai ta shiorya za ta tafi makaranca, har ta sauka kasa sai Gaji ta ce,"Ina za ki." Sai Fiddausi ta ce makaranta! Hajiya ta ce,a "To aiken ki zan yi, Fiddausi ta ce, "Don.Allah ki bari na dawo kin ga yau kwanana bakwai rabona da makaranta." Hajiya ta ce, "Yanzu dai ki ce ba za ki ba." Fiddausi ta ce, "Ni ba cewa na yi ba zani ba." Suna cikin haka sai ga Abba ya shigo, sai ya ce, 24 "Yaya," sai Gaji ta ce, "Ga ta nan ta gaya maka abin da ta ce "Abba ya juyo gurin Fiddausi ya ce, "Me kika fada?" Ta cе, "Ni ba abin da na ce, kirana ta yi ta ce za ta aike ni, na ce don Allah ta yi hakuri idan na dawo daga makaranta na je, ni abin da na ce kenan." Abba ya harari Fiddausi ya ce, Wato duk gargadin. da nake miki ba kya ji ko?" Sai ya kwace jakar makarantar ya ce, "Ba za ki ba," ya kama hannunta ya haye da i ta sama, ya huce dakinsa da ita, ita kuwa sai kuka take yi. Abba ya sa bulala ya zane Fiddausi sai da ya fasa mata fata sannan ya sake ta. Ya dau littattafan nata ya kunna musu wuta ya ce, `Kin daina makarantar ma gaba daya, sai na ga yadda zaki yi." Fiddausi ta koma dakin mahaifiyarta tana ta kuka da rokon Allah da ya karbi ranta ko ta hu ta da bakin cikin duniya. Tana cikin wannan kuka ne sai ga kanwar mahaifiyarta wato Bilisu, ta yi sallama. Yayin da Abba da Hajiya Gaji su ka ji muryarta sai suka ji jikinsu ya yi sanyi. Nan da nan suka sh irya yadda za su gaya mata i dan ta tambayi dalilin kukan Fiddausi. Bilkisu, koda ta h awo sama, suka yi mata maraba suka gaisheta, ta tambaya ina Fiddausi, sai suka ce tana daki tana kuka. Hajiya Biki ta ce 'wanne irin kuka ko ba ta da lafiya ne?" Abba ya ce, "Ai lafiyarta kalau," Gaji ta ce "Alhaji ne ya doke ta, nema take ta lalace, an yi fadan an yi fadan, amma ina! She ne alhaji ya ce yau jikinta ya gaya mata." Sai Bilkisu ta ce, To Allah ya shirya mana yaran don yanzu ba sa ji, sai da addu 'a." Lokacin da ta mike ta shiga dakin da Fiddausi take, koda ta shiga sai ta tarar da ita ta yi rub da ciki tana kuka. Yayin da Hajiya Bilkisu ta dafa bayanta ta ce, `Ai sai ki yi hakuri." Koda Fiddausi ta dago kai don ta ga mai yi mata magana sai ta ga YAKUMBONTA, a inda ta tashi zaune ta rungume ta tana kuka. Bilkisu ta ce, "Ai hakuri za ki yi, ki dunga jin maganar da aka yi miki, domin rashin ji babu dadi." 25 A nan Fiddausi ta gaya mata dukkan abin da take ciki. Nan ne Bilkisu ranta ya yi matukar baci, ta ce babu komai duk mutumin da ya cuci wani to, Allah zai saka masa komai dadewa, bare ma ke da kike marainiya, ina za su kai hakkinki. To amma yanzu idan na koma zan sanar da Mama da Babanmu koda yake basu da iko dake, amma sa yi magana a sassauta miki, domin irin wadannan nasiha ba jinta suke ba. Irin su ne masu aure don samun gado, ba Sunna ba. Shi kuma Abban irin sune masu halaka ka don su samu a gareka, tur, Allah wadai da irin wadannan mutane!" A lokacin ne Bilki ta mike ranta a 6ace - tana cewa, "Ni zan koma sai an kwana biyu." Fiddausi ta kalle ta idanunta cike da hawaye ta ce, "Tо, don Allah duk lokacin da za ki zo ki taho min da kayan sawa kuma ki gai mini da su Hajiya." Bilkisu dai ta fito rai a face, ta yi sallama da su ta koma gida. Bayan da ta fita ne, Gaji ta yi kiran Fiddausi ta fito idanunta duk hawaye sun yi jawur, ta ce, "Gani" Gaji ta bata kudi-ta ce, "Ki siyo kayan miya" Fiddausi ta karba ba tare da ta ce kala ba. Na san mai karatu zai ce ina masu aikin gida! To idan baku manta ba, lokacin da Abba zai dawo gidan ya kori duk wani ma'aikacin da ya tarar a gidan, ya dora nasa, don kada su ga abin da ake wa Fiddausi su tona musu asiri. Domin shi abba so yake Fiddausi ta mutu, ya ce gadoanta. Shi ya sa suke mata azaba iri-iri, ba ji ba gani. Lamarin Bilkisu kuwa, bayan da ta koma gida sai ta gaya wa mahaifiyarsu, domin mahaifinsu baya nan. Ta ce, "Ba ki ga azabntar da ita da ake yi ba, ta rame sai ki ce ba ita ba. Don Allah a san abin da za'a yi domin a gaskiya Fiddausi ta shiga wani hali, domin da idona na gano abin da take ciki. Kuma a cewa Baba ni na zo da kaina don haka ki sanar da Baba don ya je ya yi magana, ko ta huta." Binta ta ji dadi da jin wannan magana, domin ba su san abin da ake ciki ba, sai yanzu. Hajiya Bilkisu ta yi sallama mahaifiyarta ta koma gidan mijinta tana tunanin Fiddausi. Koda Fiddausi ta dawo 26 daga siyen kayan miya ba ko wanda ya kula da ita, sai kawai aka ce da ita ga wanke-wanke nan, kuma fa akwai mai wankewanken kuma fa don cuta wai sai a ce ita za ta yi. Kuma aka ce idan kin gama ki yi shara kuma ki goge leda, kuma ki kade kafet. Fiddausi ta kama wanke-wanke ta gama ta dau shara ta share saman tas, ta dawo kasa! Can kuwa ga Alhaji Abba da Hajiya Gaji sun zauna su da 'ya'yansu suna cin abinci da kayan marmari iri-iri a gabansu sai wanda suke so shi za su ci. Bayan Fiddausi ta gama shara sai ta fara goge leda. Allah Sarki ai dama allah ba azzalumun Sarki bane. Fiddausi tana cikin goge leda, sai ga Alhaji Hamisu ya yi sallama. Yayin da ya leka dakin da Fiddaausi take goge leda, sai ya ce,Ke! Fiddausi menen ne haka, yaya da gatanki da komai za ki ringa wannan aiki. Ba sai a kawo miki mai aiki ba." Lokacin da Alhaji Hamisu ya shigo Abba da matarsa da 'ya'yansu suna ciki suna bushasharsu, sun manta yau ne ranar ziyararsa, da yake Allah ya tona musu asiri ko sallamarsa ba su ji ba. Lokacin da yake wa Fiddausi magana yake cewa mai yake damunta, ita kuma Gaji ta fito ta baranda za ta shiga wani daki. Koda ta ji mury arsa sai ta koma da sauri ta sanar da Abba cewar ga Allahji Hamisu ya zo, kuma ya ga Fiddau si na y i aiki, "Mu ko yau me za mu ce masa." Abba ya cе, "Kowa ya y i sa uri ya sa kayan aiki mu shiga aiki.. Don kada ya ce ita kadai take yin ai kin gida." Dukkansu suka zage suna ta aiki, wai su ma'aikata amma fa na ganin ido. Da yake sun iya makirci da kisisina. Sai Abba ya I ekao ya ce, `Sannu da zuwa," yayin da y ake rike da tsintsiyar shara a hannu, irin ta yanar nan. Alhaji Hamisu ya ce, "Yauwa, yayion da ya hawo saman. Koda ya hawo sai ya tarar da Gaji tana wanke tu kunyar girki. Shi kuwa Jamilu yana ta wanki, Jamila kuma tanadafa abinci. Alhaji Hamisu ya ce, "Yau aiki ku ke yi ne?" Abba yana fara'a ya ce, `E." Alhaji Hamisu ya ce yana da 27 Aau, koda yake dai ya gane makirci suka shirya, amma bai ce Jumai ba. sun gaisa, ya ce, "Dama zuwa na yi na ga Bayan afiyarku, ni zan koma, sai an kwana biyu." Ya yi sallama da yafita, ya ce, "To Fiddausi, sai an kwana biyu," ta ce "To agaida gida da su Mustapha da Hajiya." Ya ce sa ji. A pannan lokaci Alhaji bakin ciki ya ishe shi a inda ya tsare riddausi ya ce sai ta kawo kudin da aka bata, ta ce bai bata komai ba. Nan dai saboda mugunta Abba ya yi wa Fiddausi gukkan tsiya. Bayan lokaci kadan da yin haka, sai ga Alhaji haban marigayiya, ya yi sallama. Alhaji Abba ya fita bayan sun gaisa, Baba ya ce, "Dama zu wa na yi na yi muku nasiha, kai kuma ka yi wa mai dakinka nasiha," ya ce `Baba nasiha kamar ta me?" Baba ya ce, "Nasiha akan ku rage irin abin da kuke wa Fiddausi, ku sassauta domin idan kukai adalci lalle Alah zai baku lada. Ko kun san duk wanda ya cuci maraya, akwai azaba mai girma a kansa, kuma duk wanda ya kyautata masa, akwai lada mai yawa, don haka nake mai rokonku da ku sassauta ko kwa sami gidan rahama!" Abba ya ce, "Af! Ashe matsa mata ake yi. To na san ba mai fadar hak asai Bilkisu, domin ita ce ta zo a zuriyarku, kuma ka sheda mata idan dai munafinci zata dunga zuwa nan gidan, to, kada ta kara zu wa. Sannan kuma nashiharka na ji, a sauka lafiya." Alhaji Abba ya koma gida ya bar Alhaji LAWAN a tsaye ya rasa bakin magana, yayin da ya ce, `To Allah na gani, kuma Allah ka shirye mu amin.,"ya yi tafiyarsa. Bayan da Alhaji Abba ya koma cikin gida sai kawai ya kama Fiddausi da duka ba ta san hawa ba, ba ta san sauka ba, yana cewa, "Wato ke ki ka gayawa Bilkisu cewar muna cutarki ko, to yanzu na fara cutarki don ubanki, kuma ki fadawa duk wanda za ki fadawa, ya zo y a y i miki magani. Idan yana da iko." Nan Abba ya farfasa mata jiki, sannan ya kyale ta, Allah Sarki Fiddausi ta ci kykanta ta gaji, a inda take 28 20 cewa Allah ka raba mu da masifa ka kubutar da n da ka sharrin wadannan mutane. da 1 AlhaFidedmah abinni damik zam bau ita. gag Bayan an dan yi kwanaki da yin haka, sai Jamilu ya tafi Amurka, don yin karin karatu, Jamila ta ci gaba da karatu mai zurfi. To masu magana sun ce, ka so naka duniya ta ki shi, haka ka ki naka duniya ta so shi. Haka Fiddausi ta zama baiwa a wannan gida, Jamila da Jamilu k uwa tun kafin su yi, karatu mai zurfi su ka fara lalacewa, domin shi Jamilu babu gidan rawar da ba'a san shi ba. Ga shaye-shayen miyagun Kwayoyi, don su KOKYEN ai an zama j iki, babu kuma gidan matan da bai sani ba, a "KANO" to ga shi zai je Turai inda zai ci karensa ba babbaka, kasar da kowa yake abin da ya ga dama. Haka ma Jamila ta lalace sosai, domin a cikin Kawayenta watsatstsu ita ce ja-gaba. Wata rana Fiddausi ta yi shara ta share sma, ta sauko kasa za ta share kafar bene ta fara shara sai ga Jamila ta dawo daga makaranta ko da ta shigo! Ita Fiddausi ba ta san ta shigo ba, ita kuma Jamila ba ta yi magana ba ta ce za ta hu ce, ina! To a lokacin Fiddausi tana shara ba tare da bari ba, koda Jamila taga haka sai ta dauke Fiddausi da mari, ji kake tas. Fiddausi ta rike kunci ta waiwaya ta ce "Jamila me na yi miki kika marre ni." Jamila ta ce, "Don iskanci kina ganina ba za ki ba ni hanya ba, in shige Fiddausi ta ce, ``Kin yi min magana ne, kin san fa ba ya ba ta gani balle ki ce na ganki." Jamila ta ce, "SUMВАКАSAWA" Kawai ta shige abinta, Fiddausi ta ce babu komai, wata rana sai labari. nan ta ci gaba da aikinta. Lamarin ta kenan. Wata rana Alhaji Hamisu ya kawo ziyara, koda ya yi sallama sai ya ga Fiddausi ita kadai a kas! Koda ta ganshi ta yi masa sannu da zuwa. Ta gaishe shi hawaye yana zuba mata da ta share hawayenta, ta ce "Don Allah Baba, ka taimake ni ka raba ni da gi dan nan in huta da masifar gidannan, don Allah kamar yadda ya taimake ka ka mayar da ni gidanka idan 29 ka zan K gidya ya ku sa ra bak Π b da hali" yayin da hawaye yake zuba daga idonta. Yayin da Alhaji Hamisu ya ji haka sai ya yi shiru, sannan ya ce, "To Fiddausi zan iya yi miki alfarma ko ta menene, amma banda ta wannan. Dalili kuwa shi ne kin ga alhaji Abba kanin nahaifinki ne kuma ko mahaifinki yana nan zai iya yi miki abin da ya fi wannan, do min yana da iko da ke. Kin ga ni ba ni da iko da ke don haka, zan taya ki addu 'ar Allah ya kawo miki sauki." Fiddausi ta ce, "To yanzu Baba anya kuwa zamana zai y iyu kuwa a gida bana ko zuwa makaranta sai dai bautar gida! Kamar baiwa, ai ko baiwa da imani ake tafiyar da ita." Alhaji ya ce, "Fiddausi, Allah zai kawo miki sauki cikin gaggawa," ta ce "Amin Baba, amma kada ka yi mamaki įdan ka zo,ka tarar baka same ni a nan gidan do min komai dadewa zan bar gidannan don wahalar ta kai wahala." Alhaji ya се, "Ki yi hakuri komai ya yi zafi zai yi sanyi yanzu idan kin bar gidan nan i na zaki?" Fiddausi ta ce, "Inda zan huta." Alhaji ya ce, "Ki yi hakuri, komai ya yi zafi zai yi sanyi, in Allah ya yarda." Ashe daman duk maganar da suka yi Abba ba ya nan, kuma ita Gaji tana sama tana sharar barci a, don haka ba ta san wainar da ake toyawa ba. Koda Alhaji Hamisu ya rarrashe ta, ya kawo Naira Hamsin ya bata. Don yanzu ba ya bata kudi a cikin nata, don ya san kwacewa ake yi. Fiddausi ta karba ta yi godiya. Alhaji ya ce, "Kin dai ji abin da na gaya miki." Yayin da Fiddausi ta ce na ji baba! ya ce, sai an kwana biyu suka yi salama ya fita y ana mai tausayawa wannan yarinya tare da yi mata fatan na gari lamarinsu kenan. Lokacin da Hajiya Gaji ta tashi sai ta ce Fiddausi ta je ta siyo kayan miya! Sai ta karba ta fita, bayan da ta isa ne ta gama siyo komai sai ta juyo, to a hanyarta ta dawowa ne sai ta hadu da Mustapha dan gidan Alhaji Hamisu da shi da abokinsa. Sai ta ce, La Mustapha, dama ana ganinku?" Sai ya ce, "La Fiddausi, dama talaka na ganinki." Suka tsaya su na masu gaisawa da juna! To dama kowannensu yana da ta cewa 30 ga dan uwansa, domin tuni ba kuma tun yau ba kowa yana begen kowa, abin ne kowa ya ajiye. Kuma ga nunarsata zo domin duk ruhina biyun sun motsa, ta mai karba da mai tanadi. Wannan shi ne Fiddausi ta ce, "To sai an jima ko!" Mustapha ya ce, "Saurin me kike y i ne," ta ce, "ba ka ganin aike na aka yi." Kada mai karatu ya manta cewar ta dade tana begen shi domin duk sanda Alhaji Hamisu ya je gidan su sai ta ce a gaishe shi don haka a wannan lokaci ya ce ina son zan fada miki wata magana, a inda ya zarce da cewar batun y au ba nake son yi miki maganar ba to amma saboda wasu dalilai na kasa cewa komai sai fa yau to amma fa kada na cikaki da surutu ga shi kuma aiken ki aka y i. Wannan shi ne ina son ki sani cewar so da kaunarki sun shiga zuciyata kuma ba ko tun yau ba. Kuma abin lura a nan shi ne ki lazimta cewar babu wasa a lam arina. yayin da Mustapha ya ce ko yaya ka gani Yusif. nan ya ce wannan gaskiya ne, Mustapha ya ce ban jikin ce komai ba, kin san dai yadda Babana suke da mahaifinkí don haka ba batun wasa ko yau dara a tsakanímu, yaya na sami karbuwa a tare dake!" Fiddausi ta yi murmushi ta ce, "Tuni ka sami karbuwea a tare da ni, ka sani cewar ka mallaki yardajjen masauki a ruhina na har abada." Ta ce, "Hasali ma, ni na fi ka son kanka da kanka, da a ce za ka shiga zuciyata kai kallo da ka ga yadda nake soyayyarka, da ka yi mamaki sosai. Fiddausi ta ce bari na tafi don kar a yi m ini fada, domin kun san na ce da ku fa aike na fa aka yi. Mustapha ya ji dadin maganar Fiddausi ya ce to yaushe za mu zo, ta ce ni ko yaushe kuka zo ai ina nan. In dai ba aike na aka yi ba." Mustapha ya ce, 'Sai jibi za m u zo in Allah ya yarda!" Ta ce sai an j ima,Allah ya kawo ku. Suka ce a gaida mutanen gidan yayin da Mustapha ya ce, "Kai turkashi!" Ya bi ta da kallo, ya ce "Allah ya mallaka mini" Yusif ya ce, wai yaya aka yi Fiddausi ta dawo haka ne, sai ka ce ba 'yar masu kudi ba, 31 gashi kuma ya mutu mahaifinta ya bar mata dukiya mai tarin awa." Mustapha ya ce, "haka ne, to amma ai kanin mahaifinta ne ya hau kan dukiyar yake ta zalintarta, ka san mahaifinta amana ya bawa babana ita, ka san duk wata sai ya je ya duba ta ya ba ta kudi to amma sai kanin baban nata ya (wace ya yi harkar gabansa da kudin dan ma Allah ya yi ta kyakkyawa ai da ba za ta ganu ba. Ba ka ga duk kamanninta sun canza ba, kamar ba ita ba, koda Yusif ya ji haka sai ya ce, "Lalle lahira da kallo kuma idan bai dena haka ba to karshensa ba zai kyau ba." Lamarinsu kenan, amma ita kuwa Fiddausi lokacin da ta koma gida Abba ya dawo akuma H aj iya gaji tana fada masa tun lokacin da Fiddausi ta fita, amma sai ga shi yanzu ta dawo, Alhaji Abba ya ce a ina kika tsaya, sai yanzu kika dawo, Fiddausi ta ce, "Abb wajan ne da mutane shi ya sa." Abba ya ce to shi kaďai ne mai-ya hana ki ki sake guri ko shi ne me kayan miyar! Fi ddau si ta ce a'a, don Allah a yi hakuri ba zan sake ba, amma ina! Saboda rashin Imani da rashin mutunci da bushewar zuciya sai da ya bawa Fiddausi kashi sosai. Baya lokacin alkawarin da su Mustapha suka yi wa Fiddausi, sai ga su sun zo, sai su ka aika cewar ana sallama da Fiddausi, bayan ta fito ta gaishe su suka amsa sannan Yusuf ya ce, "Fiddausi gashi to Allah ya kawo mu, yayin da Fiddausi sai ta yi murmushi anan ne suka ci gaba da hirarsu irin ta masoya, to amma sai ya kasance ita Fiddausi ba ta son a dunga zuwan yamma domin kada Jamila ta dawo ta same su da baki ta je gida ta yi mata sharri ta sa a dake ta, koda suka sami lokaci mai tsaho suna hira sai Mustapha ya ce mu za mu tafi sai an kwana biyu nan Mustapha ya bata Naira fari biyar. shi kumna Yusif ya bata Naira dari biyu nan su kai sallama ta yi godiya, suka juya suka tafi. Wata rana Musatapha yake gayawa Fiddausi cewar tun da ga soyayya ta mika kuna ba wanda ya sani, to shi fa zai 32 gayawa Alhajınsa ya zo gurin Abba a yi magana. Nan ne Fiddausi hankalinta ya tashi domin ta san rashin Kauna da Abba yake nuna mata anya kuwa ya yarda. Nan Fiddausi ta shiga tunanin abin da za ta gayawa Mustapha, ta shiga kogon tunani har ta manta da cewar tare da Mustapha take sai shi ne yake tambayarta cewar tinanin me kike yi ne. Nan Fiddausi ta ce tunani na yi, ka san yanzu Abba ba kaunata yake ba to shi ne nake tsoron zuwa Alhaji wajan Abba! Amma ka yi hakuri sai lokacin da na ga yana walwala sai na fada masa kai ku ma sai ka fada masa lokacin da za su yi maganar. Mustapha ya се amma na ji dadin wannan maganar na gode Allah ya kara soyayya, ta ce amin suka yi sallama, ya nifi gida da murna. Bayan lokaci mai tsaho Mustapha da Fiddausi suna ta yi soyayya sai Abba ya sami labarin komai, nan Abba ya y i kiran Fiddausi ta zo ta ce, gani, sai ya ce wanne yaro ne yake zuwa gurinki? Sai ta ce Mustapha ne dan gidan Alhaji Hamisu! Abba ya ce "Mene ne dalilin zuwansa gurinki?" Fiddausi ta yi shiru, Abba ya ce, "Tambayarki nake ba ki ce da ni komai ba." Nan dai Fiddausi ta ce, "Ai shi ne wanda yake sona kuma ya ce zai turo Alhajinsa gurinka ku yi maganar." Alhaji ya ceMustaphan me?" Ya harari Fiddausi ya ce, "To duk lokacin da na sake ganinki da shi sai na lahira ya fi ki jin dadi. Tashi ki bani guri maras kunya.' Fiddausi ta mike ta koma dakin marigayiya tana kuka tana rokon Allah da ya fitar da ita daga wannan kangi. Shi kuwa abin da ya sa yake jin haushin Mustapha shi ne saboda yanzu Alhaji Hamisu ya daina bashi. Kuma bashi da ikon tambaya shi ya sa ya ce ko ganinta ya yi sai ranta ya 6aci. Kuma dama ita kanta haka ta guda shi ya sa ma take dari-dari: Lamarinta kenan. Al'amarin Jamilu kuwa lokacin da ya tafi Amuruka karin ilimi to babu abin da ya ke yi sai shashancin banza, don yanzu ya zama dan duniya, don ko wata biyu bai yi ba ya fara sheke aya, don ya san babu abin da zai faru ko ya komo gida. Jamilu 33 Hon Hak a Co sa b a sar idaDu m ha g S H sami wasu abokai marasa mutunci, to Allah ka shirye mu in. Haka ma Jamila iskanci ya yi nisa don har gidan rawa e zuwa kamar su "AMINGOS" ita da kawayenta karuwai idan ka ga Jamila ta tsuke sai ka ce ba 'yar Musulmi ba. aka ta kasance a h alin watsewa babu mai yi musu magana aboda halin watsewar babu kuma wanda zai hana ta ga shi aira a zauna da gindinta. Bayan wasu kwanaki kadan, sai Mustapha ya zo suna hira da Fiddausi kamar yadda su ka ba, ta sanar da shi komai, ta ci gaba da cewa, "Domin na n haka za ta faru, don haka sai ka yi hakuri don a gaskiya dan har Allah ya yi za mu yi aure to fa ba yadda zai yi. Domin ni na san ba ya kaunata don haka idan Allah ya baka ni shi bai isa ba." Mustapha ya yi matukar bakin ciki da maganar da masoyiyarsa a fada masa kuma ya tausaya bisa halin da take ciki. Kuma ya ce na ji dadi da kika gayan gaskiyar abin da yake faruwa a tare da ke, kuma idan Allah ya yarda za mu yi aure dake, koda ya ga Fiddausi da Mustapha shi wa? Shi Alhaji Abba, sai ya ce ban hana ki fita ba. Mustapha ya ce ina wuni! Abba ya ce ba da kai nake ba Fiddausi ta yi shiru ba ta ce komai ba. Shi kuwa Mustapha yana tsugune, Abba ya juya gurin Mustapha ya ce "Kai ka sanni kuwa, to kada na kara ganinka a nan AHIR!!! Idan har na sake ganinka a kofar gidannan sai na ci mutuncinka. Ke kuma za ki shigo ki same ni."

Chapter 3 of 4