An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
MAI RABON GANIN Bно
1
Hainna
ABashir
MAI RABON GANIN BADI
NA
HAUWA A. BASHIR AYAGI
KANO STATE.
GODIYА
Da sunan Allah mai rahama mai Jin kai Tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi, Annabi shugabanmu Muhanımadu
(SAW) da Sahabbansa da wadanda suka yi riko da sunnanrsa
da wadanda suka yi riko da su nnarsa har zuwa ranar
sakamako. Ina gode Allah da ya azurta ni da lafiya da basirar
rubuta wannan littafi mai su na MAI RABON GANIN BADI"
yanzu ga shi har ya kammala Ina matukar godiyata ga
mutanen da suka taimaka min yayin rubuta wannan littafin
irin su mai gidana ALHAJI BASHIR, da BABA INUSA
SANI MAINAGGE. da TIJJANI DISO, da MALAM
NASIRU DAHIRU zage na shashen harsunan Nigeria Jami'ar
Bayaro Kano. da LAMI AL HAJI BASHIR da SALWA
HAMISU KANO da Hajiya Hauwa Kulu Musa, Ina godewa
duk mutumin da ya taimaka mini ta kowace hanya Allah ya
saka da alherinsa amin. Wassalamu Alaikum. HAUWA A.
BASHIR AYAGI KANO STATE.
* HAKKIN MALLAKA CM) НАAUWA A. BASHIR
AYAGI. MAI RABON GANIN BADI AN FARA
BUGAWA 1993.
* SADAUKARWA, NA SADAUKAR DA WANNAN
LITTAFI GA MAHAIFINA ALHAЛ MUНАAMMAD.
ALLAH YA JI KANSA AMIN SUMMA AMIN.
WASSALAMU ALAIKUM HAUWA A. BASIIIR.
* DOKA. BA A YARDA WANI YA BUGA KO YA JUYI
WANNAN LITTAFI TA KOWACCE HANYA BA SAI DA
IZININ MAI SHK A RUBUCE. DON HAKKIN MALLAKA
YA RATAYA A KANTA.
11
* LITTATAFAN DANA WALLAFA SUNE KAMAR
HAKA:- SO SARTSE NA DAYA, DA NA BIYU,
MASOYINA NA DAYA DA NA BIYU BAKIN CIKIN
RAYUWATA NA DAYA, MASU FITOWA NAN GABA
SUNE - SO AJIYAR ZUCIYA, RAYUWAR SOYAYYA,
BAKIN CIKIN RAYUWATA NA BIYU. Ana iya samun su a
Garba Mohd. Bookshop, kofa mai kallon BATA, kasuwar
Sabongari, No. 92, Sauki Bookship No 92 Jan Bulo, No 25
Jakara Bookshop.
B
ayan da Alhaji Bello suka idar da sallar Isha a
masallaci, sai ya isa gida, ya na mai yin sallama!
Hajiya Zainab ta amsa, ta yi masa barka da zuwa kuma ta
hada m asa kayan abinci ta kawo masa, a yayin da diyar ta
FIDDAUSI take biye da ita. Hajiya ta ajiye kayan abincin
tana mai murmushi ga sashin wato mijinta,. Fiddausi ta yi wa
Babanta barka da zu wa ya amsa. Ya fara cin abincinsa nan ne
Fiddausi take eewa Baba nima zanci! Idan ci za ki yi, zo mu je
in zuba miki. Alhaji ya ce Hajiya rabu da ita mu ci tare, take
nan Fiddausi ta zauna su ka ci gaba da cin abincin tare, bayan
da su ka gama cin abinci Alhaji ya ce Hajiya dama ina son in
gaya miki cewa zan je Umarah. In sha Allahu do min na gama
duk shirye-shiryen da ya kamata na yi. Kuma ina kyautata
tsammanin cewar ranar Alhamis za mu tafi in Allah ya yarda,
koda Hajiya ta ji, sai ta yi matukar farin ciki da jin wannan
zance, ta ce, Allah ya kai ku lafiya kuma ya dawo da ku lafiya
amin. In ji Alhaji. nan dai suka ci gaba da tattaunawa.
a
Abin lura da fahimta shine Alahaji Bello wani
hamshakin mai kudi na da kashin arzuki yana zau ne ne
wata unguwa mai suna `SANI MAINAGGE" a cikin binin
Kano. Alhaji Bello Allah ya bashi hakuri da rikon amana ga
alheri ga kowa. Hajiya Zainab ita ce matar Alhaji Bello! Mace
ce mai hankali da nutsuwa ga ladabi da biyayya ga hakuri
sannan tana da son jama'a sosai. Alhaji Bello Alah ya bashi
'ya'ya maza da mata, amma duk Allah ya karbi abinsa. Sai
wannan yarinyar ita kadai wato Fiddausi Allah ya bar musu
ita. Alhaji Bello yana da 'yan uwa da dama, amma mafi
yawancinsu sun rasu yanzu su biyu suka rage shi da kaninsa
wanda suke uba daya kuma duk iyayensu sun rasu tun wani
zamani da ya huce. Alhaji Bello y ana da kamfanoni masu
yawa a wannan Jiha kuma kowacce takardar mallakar
kamfani da ciniki sunan Fiddausi ne, a jiki. Kuma ya kafa
shedu cewar koda ya rasu, to wadannan kamfanoni ba sa cikin
gado. Domin ya mallakawa Fiddausi su duka.
Fiddausi yarinya ce karama kimanin shekarunta na
haihuwa biyar. Fidddausi yarinya cea kyakkyawa son kowa
kin wanda ya rasa. Allah ya bata hakuri ga ladabi ga biyayya,
ga nutsuwa sannan tana da kwazo a makaranta, kuma da it da
mahifiyarta halinsu daya. A halin yanzu Fiddausi tana
makaranta ne a "Nursery/Primary School" dake Gwauron
Duse, kuma tun lokacin da aka sata a makaranta bata taßa yin
fada da yara 'yan uwanta ba. don haka malaman su suke kau
narta bayan wasu kwanaki da maganar tafiya "UMRAH" sai
Alhaji ya kintsa domin lokacin tafiya ya yi da gamawarsa, sai
ga wani abokinsa mai suna Alhaji Hamisu. Ya yi sallama
koda Alhaji ya ji sai ya gane muryarsa,, inda ya fita, a inda
yake ce m asa kai mai isa kake haka ne ai nan gidan kane, me
ye abin tsayawa ka shigo mana Alhaji Hamisu ya yi
murmushi. Suka shiga falon Alhaji Bello. Nan ne Hajiya
zainab ta zo ta gaishe shi har kasa, ta yi masa barka da zuwa,
nan ma Fiddausi ta zo ta gaishe shi, nan ne Alhaji ya bawa
Fiddausi biskit, ta ce an gode. nan dai Alhazawan suka gaisa
da juna. Bayan da su ka gama gai sawa Alhaji Bello yake
cewa dama yanzu nake shirin yi maka waya. Sai ga shi Allah
ya kawo ka. Alhaji Hamisu ya ce lafiya! Alhaji Bello ya ce au
har ka manta da tafiyar da zan yi, Alhaji Hamisu ya ce na
sha'afa. Nan Alhaji Bello ya ci gaba da yiwa Hajiya Zainab
gargadin cewar ta kula da gida. Kuma ta kula da Fiddausi
sosai Hajiya Zainab ta yi na'am da maganar mai gidanta,
kuma ta yi alkawarin rike dukkan abin da ya umarce ta da ta
yi.
Bayan gama wannan gargadi sai Alhaji ya mike, ya buga
kararrawa nan da nan sai ga m ai gadi y a zo ya ce gani,
Alhaji ya ce dauki akwatin nan ka kai ta cikin mota ni ma ina
fitowa. Nan da nan mai gadi y'a dauki akwatin sai cikin mota.
2
Hajıya da diyarta Fiddausi suka. shirya domin su yiwa Alhaji
rakiya, suka fito gaba daya, lokacin da suka fito ne duk masu
gadı suka fito suka gaida Alhaji da abokinsa. Yayi mus
gargadi da cewar su kula da aikinsu sosai. Kar a sami wani
cikas. Nan dai suka yi masa a dawo lafiy a, kuma su ka
tabbatar masa da cewar idan Allah yarda babu abin da zai
faru. Direba ya bude musu kofa da Alhaji da abokinsa hadar
da Hajiya da 'yarta Fiddausi suka shiga a wannan lokaci ne
direba ya ja sai filin Jirgin saman "MALAM AMINU KANO
INTERNATIONAL AIRPORT" Bayan da su ka isa direba ya
tsaya ya yi parking" duk suka fito. Nan Alhaji ya y
bankwana da iyalinsa da amininsa da diyarsa Fiddausi, ya
shiga dakin bincike. Bayan da Alhaji ya fito suka yi masa a
dawo lafiya, nan ne Alhaji ya ce wa da Hajiya Zainab ta
aikawa da Kaninsa Alhaji Abba cewar ya tafi sai ya dawo nan
ne ya shiga cikin jirgi, lokacin da da jirghi ya cika, ya farn
zarya a titinsa sai nan da nan ya daga suka tashi gaba daya da
sauran maniyyata.
Bayan da su Alhaji suka tashi ne, Hajiya da diyarta
Fiddausi da aminin mijinta da direba suka juyo gida. Alhaji
Hamisu ya yi sallamna da Hajiya, ta ce ya gaida Hajiya ya ce
ya ji. Bayan tafiyarsa Hajiya ta yi kiran direbansu wato Abbas
ta aike shi gidan Allahji Abba don ya isar da sakon. Bayan da
Abbas ya ji sakon sai ya tafi, da isarsa sai ya tarar da Jamila
da dan uwanta Jamilu, ko da suka ga Abbas sai suka ce masa
sannu da zuwa, ya ce yauwa. Suka ce ina Fiddausi ya ce tana
nan kuma tana gaishe ku. Sannan Abbas direba ya ce ina
abbanku suka ce yana nan, ya ce ku je ku yi min magana da
shì nan da nan suka shiga bayan jumawa kadan sai ga Alhaji
Abba ya fito fuskar nan ba ko annuri, sai Abbas ya ce dama
Alhaji ne ya ce na zo na gaya maka ya tAfiUMRAH
AMMA MAKO DAYA ZAI YI. Daga nan Abbas a mike
tsaye Alhaji Abba ya ce to a gaida mutanen gidan. Ya ce sa ji.
3
Shi Alhaji Abba mutu n ne mai mummunan hali domin ba shi
da kirki ko kadan, halinsa ya banbanta da na Alhaji Bello.
Kuma duk abin da Alhaji yake masa a raine yake ganinsa.
Kuma shi bai ki Alhaji Bello ya mutu ba, don ya ci amanar
wannan 'yar tasa Fiddausi ba. Haka ma matarsa Hajiya Gaji
ita ma Allah ya ba ta son abin duniya sosai. Amma shi Alhaji
Bello duk bai damu da haka ba. Haka zalika duk abin da zai
yi tare yake hada 'ya'yansu gaba daya yake yi musu. Amma
duk da haka a banza domin shi Alhaji Abba a banza yake
ganin komai da aka yi masa Wannan shi ne kadan daga cikin
tarihin Alhaji Abba.
Lamarin gidan Alhaji Bello kuwa, bayan da Abbas
direba ya koma ya sanar da Hajiya cewa ya sanar da su sakon
Alhaji kuma sun ce a gaishe ku, yayin da Hajiya Zainab ta ce
muna amsawa sai ta ci gaba harkokinta. Amma ita Fiddausi
kuwa ta ci gaba da zuwa makaranta kuma tana ta kokari so
sai. Shi kuwa Alhaji Bello bayan da ya sami sati daya, a
Saudia, sai ya fara shirin dawowa gida. Bayan ya gama
shirye-shiryen da suka dace, sai ya biyo Jirgin adalici wato
"DAN KABO" Bayan tafiyar awa hudu sai suka iso Kano,
bayan da suka sauka, sai Alhaji Bello ya shiga dakin hutawar
baki, dama kafin ashinsa sun yi da amininsa Alhaji Hamisu ya
ce za zo ya dauke shi, bay an da aka sami kimanin awa biyu
da saukar Alhaji, sai ga Alhaji Hamisu ya zo daukarsa, da
shigarsa sai ya ga Alhaji, nan da nan suka gałsa yana mai
tambayarsa yaya hanya. Ya ce na dawo lafiya kalau Suka sa
aka dauko musu kaya aka kai mota, sannan Alhaji Hamisu ya
tuka mota sura tafi. Bayan da su ka isa gidan Alhaji Bello, sai
masu gadi su ka bude musu kofa suka taryi Alhaji da murna
mayalwaciya. Kuma suka je gindin "but" din motar suka jido
kayayakin da aka zo da su, su kuwa Alhaji Bello suka shiga
gida suka yi sallama, koda Fidausi ta ji muryar mahaifnta sai
ta fito da sauri tana mai yi masa barka da zuwa, Hajiya ma ta
4
fito da vauri tana mai yi masa barka da zuwa domin lokacin
tana banſaki a nan ne ta ji Fiddausi na yi masa sannu da zuwa
shine ta fito ita ma Alhaji ya shiga falonsa yana hutawa, sai
ga Hajiya Zainab ta shigo tana yi masa barka da zuwa a nitse.
Ta kuma yi musu barka da zuwa bakidaya, ta koma ta hado
musu kayan abinci iri-iri masu inganci. Da lemo mai sanyi: ta
ajiye miisu, a bisa tebirin dake gabansu nan dai suka fara cin
abinci suna masu nishadi.
Bayan da suka gama, Alhaji Hamisu ya ce ni zan koma
rida, Alhaji Bello ya ce na fa gode, nan ya tashi suka fito tare,
li ajiya Zainab! Ta ce har zaka tafi ya cc, "E," ta ce to a gaida
Ilajiya Tafadan" suka fito ya shiga mota Alhaji Bello ya leka
taga ya ce na rode sai na zo. nan Alhaji Harnisu ya ja mota ya
nıfi gida. Alhaji Bello ya koma cikin gida ya dau
TI LEPHONE" ya yiwa kaninsa waya, a lokacin Alhaji Abba
va dauka ya ce "Waye"Alhaji Bello ya ce ni ne, nan da nan
ya gaishe shi. Ya ce, yaushe ka dawo? Alhaji Bello ya ce dazu
na iso. Alhaji Abba ya ce ka dawo lafiya, shi kuwa ya се
sumul Kalau, Alhaji Bello ya sanar da shi cewa ya auno kaya
masu yawa, kuma za'a sami alheri sosai, sai nan da nan Alhaji
Abba ya dunga murma, ya ce ni ma yanzu zan taho domin
maganar taa li karfin TELEPHONE" Yayin da suka vi sallama
ya ajiye waya, ya gayava Hajiya Gaji cewa Alhaji ya dawo
kuma ya auno kaya kuma za a sami alheri, nan da nan ita ma
ta yi muma, kuma nima yanzu gurinsa zani ta ce a gaishesu.
Abba ya ce za su ji. Ya in da Alhaji Abba ya fito da dau mota
ya nifi gidan Alhajı Bello, bayan da ya iso ne masu gadi suka
bude masa kofa, ya shiga sannan suka rufc, Alhaji Abba ya
ajiye mota yayin da masu gadi suka gaishe shi, Abba ya
shiga ya yi sallama Hajiya Zainab, ta ce kai! Ashe babban mai
maigida ne shigo mana da ka mant da ni ne, ko kudin cefane
ba a kawo min, Abba ya yi murmushi ya ce yanzu duk wanda
nake kawo miki kin raina ne, ta ce a'a ni ba wanda ya kawo
5
Ta ce da shi shiga min ko (asi) suna wasa da dariya. Ta ce yana
wanka, a nan suka gaisa, ya shiga yana jiransa ba'a dade ba
Alhaji ya fito ya ce Abba ha: ka iso ne, ya ce, `E" Alhaji ya
kintsa ya zauna suka sake gaisawa nan Abba ya ce ka dawo
lafiya Alhaji ya ce, lafiya kalau. Alhaji ya ce, ina Jamila da
Jamilu, ya ce suna nan lafiya Gaji ma ta ce a gaishe ka, ya ce
ina amsawa, nan dai suka ci gaba da hira. A inda Alhaji Bello
ya ke bashi labari Saudia da irin canje-canjen da aka yi mata,
Abba a ce yaushe kayan za su zo, Alhaji ya ce sai ranar
Talata. Abba ya ce Allah ya kaimu. Nan suka yi ta yin hira har
wani lokaci. Abba ya ce ni zan koma, sai da safe! Suka yi
sallama da Alhaji da Hajiya Zainab, nan ne ta ce ya gaishe
mata da Hajiya Gaji ya ce ta ji, ya fito ya hau mota sai gida.
Bayan da Alhaji Bello ya sami kwana biyu da komowa sai ya
bude akwatin da ya zo da ita ya raba, ya bawa Fiddausi nata.
Wanda suke kaya masu yawan gaske, haka ma Jamila da
Jamilu ya ware musu nasu, ya bawa Hajiya Zainab "Set" na
yari-da sarka. Ta yi mutukar farin ciki da godiya da fatan
Allah ya kara arziki. Alhaji ya dannan kararrawa sai nan da
nan direba, masu gadi, da sauran ma'aikatan gida suka zo,
suka shiga su ka gaida Alhaji ya amsa, ya raba musu kaya
kowanne ya karba ya yi godiya. A lokacin ne ya aiki Abbas
direba ya kaiwa Alhaji Abba nasa da shi da iyalansa, nan dai
Alhaji ya yi ta rabawa jama'a kaya. Abokan arziki da sauran
jama'a Musulmai danganta ga wanda rabonsa ya tsaga, ya
aikawa amininsa Alhaji Hamisu nasa, sannan, bayan komai ya
nutsa, Alhaji ya koma harkokinsa na yau da kullum.
Lamarin Fiddausi kuwa, ai ba'a cewa komai domin, tana
nan tana bada kokari, gashi a wannan shekarar ta gama, NURSARY/PRIMARY" a hade. Bayan da sakamako ya fito
sai ya kasance ta yi sa'a, amma saboda Fiddausi yarinya ce karama, Alhaji ba zai batta ta je makarantar Sikandire ba.
Bayan d aka nutsu, sai Alhají ya kai Fiddausi wata makarantar
6
koyon TAJWID, mai suna TAHAFISUL QUR'AN, do min ta
sami ilimin dahir, nan dai Fiddausi ta ci gaba da bada himma
wajen karatu, kasancewarta mai himma, bayan ta sami
shekara daya a makarantar sai suka fara gasar karatun Kur'ani
na Lokal Gammen din jiharsu. Fiddausi tana daya daga cikin
wadanda aka dauka, bayan an sami kwanaki ana gasa aka
kammala, alkalan gasaa suka fadi wadandaa suka yi nasara,
sai ya kasance karamar hukumar su Fiddausi ita ta yi nasara,
domin makarantarsu ce ta yi nasara. Fidddausi ita ce dama
yarinyar da ta wakilci makarantar don haka aka dunga raba
kyaututtuka ga wanda ya yi nasara, Fiddausi Bello ta yi na
daya, ta biyu Salwa Abdullahi ta uku Hafsat Hassan, bayan da
aka yi kwanaki da yin musabakar, sai Alhaji Bello ya shirya
walimar murnar Fiddausi ta yi nasara, aka shirya komai guri
ya hadu domin an shirya kujeru tsarin ya yi kyau. Jama'a da
dama suka hallara ciki har da Malaman TAHAFIZUL
QUR'AN, kamar su Mlam Bature - ya sami halarta har da
Malama Lubabatu duk sun je domin taya dalibarsu murna.
Bayan taro ya nutsu sai aka bude taro da addu 'a. Sai dalibai
suka yi ta karatu. Kowanne yana karanta ayar da yake
haddarta bayan sun gama sai Fiddau sai ta karanata Suratul
"MALIKI JALLA WA AZZA," har karshen ayar mutane
suka yi ta yabon Fiddausi
Yayin a ta gama karatu sai Alhaji ya bada umarni da
kowa ya ci abinci. Nan aka dunga wadabge da abinci iri-iri.
Wanda a wannan lokaci ko da cokali kake yawo to ka yi
hani'an. aka dunga daukar hotuna iri-iri, har bidiyo kaaset sai
da aka yi a wannan walima mai dimbin tarihi wajen kowa
musamman Alhaji Bello, yayin da aka gama wannan taro
kowa ya koma gida, Fiddausi ta ci gaba da karatunta ba ji ba
gani bare wasa, ana ta bada hazaka. Wata rana sai aka wayi
gari Alhaji Bello bashi da lafiya, wato cutar ciwon Sukari ce
take damunsa, kuma dama tana yawan damunsa, Hajiya Zai
7
nab, hankalinta ya yi matukar tashi sosai,nan da nan ta yi wa
Alhaji Abba waya ta sanar da shi abin da ake ciki, ya ce Allah
ya sauwake nima gani nan tawowa, sannan ta yiwa Alhaji
Hamisu waya ta sanar da shi abin da ake ciki. Bayan da ta a
jiye ne sai ga Alhaji Abba ya yi sallama, Hajiya ta amsa masa
suka gaisa, yayiwa Alhaji sannu, ya cer da Hajiya wanne
Hospital ya kamata a kai shi.. Hjiya ta ce da dai da ya yi
AHMADIYYA aka kai shi, amma yanzu akwai wani da aka
bude, Alhaji Abba ya ce wanne kenan, Hajiya ta ce,
INTERNATION CLINIC," Abba ya ce sabo ne amma, ta ce
"E sabo ne a gurinka domin ya dade saninsa ne baka yi ba."
Ya ce a ina yake ta ce yana nan "AIR PORT ROAD." Alhaji
Abba ya ce to ai shi kenan.
Lokacin da suka dauki Alhaji-suka fita da shi suka saka
shi a cikin mota sai can asibiti bayan da suka kai shi. Likita ya
bashi kwanciya, sai ya kasance Hajiya ita take zama a g urinsa
ta wuni, shi kuma Alhaji Abba idan ya dawo daga kasuwa sai
ya zo ya kwana tare da shi. Idan ka je asibitin daki mai lamba
"No 30" aka bashi. Haka Alhaji ya yi ta shan maaganai,
amma ina babu batun sauki, domin duk 'yan uwan Alhaji sun
fitar da rai da shi. Wata rana Alhaji yana kwance Alhaji
Hamisu yana kusa da shi kuma ita ma Hajiya Zainab tana
kusa da shi tana kuka saboda halin da mijinta yake ciki na
rashin lafiya mai tsanani, lokacin ne shi Alhaji Hamisu yake
bata hakuri, a wannan lokaci ne Alhaji ya dan daure ya yi
magana, Hajiya Zainab ta share hawayenta domin ta ji abin da
Alhaji zai sanar da ita, Alhaji Bello ya ce, "Alhaji Hamisu!
Zan baka amana idan zaka rike," Alhaji Hamisu ya ce, `'Zan
rike," ya ce amanar da zan baka ita ce ta i yalina baki daya
gasu nan a hannunka domin wannan cutar ba za ta bar ni ba
kuma ku yafe ni bisa abin da na y i muku wan dana sani da
wanda ban sani ba." Alhaji Hamisu ya ce, "Na karba kuma
Allah ya bamu ikon rikewa amin," in ji Alhaji Bello,
8
nan
Alhaji Hamisu ya ce, "Ai mu baka yi mana komai ba, kuma
ko ka yi mana mun yafe maka duniya da lahira, kuma Allah
ya baka lafiya, amin," in ji Hajiya Zainab! yayin da take zubar
da hawaye.
Alhaji Bello ya sanar da Alhaji Hamisu inda
Kamfanoninsa da takardunsu suke ya ce ya rike a wajansa ya
ajiye su amana, daga nan Alhaji Hamisu ya yi sallama da
Hajiya Zainab! Ya fita ya ce Allah ya sauwake, ta ce amin. A
lokacin ta ci gaba da zubar da hawaye da rokon Allah ya bashi
sauki, lokacin da yamma ta yi sai Alhaji Abba ya taho da
Fiddausi da 'ya'yansa Jamila da Jamilu don su gai da Alhaji,
don tun da aka kawo shi basu taba zuwa ba. Kasancewar ita
Fiddausi tunda aka kawo shi bata taba zuwa taga abinda yake
ciki ba domin a lokacin ta koma gidan Alhaji Abba, koda
suka shigo dakin da aka kwantar da shi sai Fiddausi ta fara
hawayen tausayawa mahaifinta, ta gai da mahaifinta ta yi
masa sannu, sannan Jamila da Jamilu suka yi masa sannu da
fatan Allah ya bashi lafiya, Zainab ta ce amin. Bayan sun
sami lokaci mai tsaho ku ma dare ya yi so sai, sai Hajiya
Zainab ta ce wa da Alhaji Abba zamu tafi sai da safe. ta cewa
su Jamila sai ku zo mu tafi, sai suka fito za su tafi, Hajiya ta
kallo Alhaji a kwance ta sake hawaye, direba Abbas ya ce sai
hakuri, dalilin da ya sa Hajiya take kuka shine saboda jikin
Alhaji ya yi tsanani. Tana sharre hawaye, suna tafiya har suka
isa gida. Bayan da suka isa gida ne Hajiya ta ce da direba ya
huce ya kai su Jamila gida, ya sanar da Hajiya Gaji cewar
jikin Alhaji ya yi tsanani, ya ce to ya fita don kai su Jamila
gida ya kuma zarce don ya sanar da mahaifin Hajiya cewar
jikin Alhaji ya yi tsanani.
Lokacin da Hajiya, ta zauna a gida sai ta rasa abin da
yake mata dadi a duniya, Hajiya ta kasa zaune ta kuma kasa
tsaye, tana cikin haka har Abbas ya dawo ya ce na gayawa
alhajin ya ce Allah ya sauwake kuma ya ce zai zo da safe ya
ita duba shi. Sannan Abbas ya koma waje ya bude dakinsa,
kuwa hajiya Zainab ta kasa barci domin ita yau ji kin Alhaji
ya bata tsoro, tanan nan zaune cikin rashin sanin halin da
Alhaji yake ciki, tana ta yin kuka, kuma tana share hawaye,
nan ta duba agogo taga har karfe biyu da kwata na dare,
Hajiya ta yi alwala, ta yi Kiyamul Laili, bayan ta idar ta yi wa
mi jinta addu'a Allah ya bashi lafiya. Lamarin da ta kasance
kenan. Amma shi direba Abbas yana can shi ma wajan jinyar
Allhaji, ya kasa yin barci, yana ta yi wa Alhaji Bello addu 'a,
sai ya ji an bugo waya, "TELEPHONE" sai nan da nan
gabansa ya fadi ya kasa dauka, sai da aka yi bugowa ta biyu
sanan ya dauka hannunsa yana rawa, ya yi sallama ya ce daga
ina? Sai Alhaji Abba ya ce ni ne Alhaji Abba daga asibiti, ya
ce Allah ya yi wa Alhaji Bello rasuwa da misalin karfe uku, ai
tun da Abbas ya ji bai san lokacin da wayare ta subule daga
hanunsa ba. Sai gumi ya dunga karyo masa yana cewa I nna
lillahi wa inna ilaihirraji'un. Yana cewa Allah ya ji kan Alhaji
kuma ya yafe masa kura kuran da ya yi amin. Ya ce wai ni
dannan yanzu yaya zan shiga na cewa Hajiya, kafin Abbas ya
shiga duk sai ya tashi masu gadi wadanda ba sune da aiki a
ranar ba ya sanar da su, sannan